Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[4:54pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [11:25PM, 1/31/2016] Pherty🎤👯: ........ADON TAFIYA🚵🏻

Na Fertymerh xarah💝

1 to 10

Kyakkyawan saurayine dan kimamin shekara ashirin da shidda, tsaye a qofar jirgi yana shaqar iskar nigeria wanda rabonsa da qasar shekara biyu kenan.

A hankali yake saukowa cike da qasaita ya gangaro xuwa farfajiyar airport din yana cike da farinciki da nishadi

kyakkyawane sosai dogo mai kyan jiki yanada dogon hanci da manyan idanuwa,gashin kansa baqine sidik kwance sai shegi yake da tsantsi
yanada mans pride kwance lub lub a fuskarsa yana faman sheqi wanda yayi matuqar fito da kyawun fuskarsa abinka da farin mutum

taku yake irin na isassun ya'yan masu kudi masuji da mulki , yana sanye da farar shadda gexner mai kyau da tsada sunyi matuqar yi masa kyau kamar ba dannan qasar tamu ta nigeria ba

Airport din cike take da mutane iri iri daban daban daga qasashe da dama

malam sani ya qaraso da sauri fuskarsa da murmushi yake gaidasa

da hannu yayi masa alamar amsawa kafin ya miqamasa trolley dake hannunsa
driver ya karba da sauri kafin ya juya da sauri yabi bayansa.

*
sun dauki hanya sosai kafin ya juyo yana kallonsa

yace malam sani ina xamuje ne amaimakon gida

yace yallabai waiwaye adon tfy ka dade rabonka da bakura yau acan xamuje saboda su hajiya nacan, ynxuma daga can naxo daukarka

da mamaki yake kallon driver
yace lfy dai ko?
yace ana bikine na aure, yayi shiru bai sake mgn ba ya maida kansa kan wayarsa hr suka iso garin bakura.

can nesa da gidan sukayi parking sakamakon ganin yawan taron jamaa a bakin qofar gidan

ya fito daga motar ya rufe dai dai lokacin dayaga mahaifinsa ya riqo Abbu yana rarrashinsa da alama kuka yake

da sassarfa ya qarasa gurinda suke tsaye ya riqo hannun abbu yana kallonsa yana kallon mahaifinsa

yace daddy meyasami abbu yake kuka, waya mutu ne?

cikin kuka abbu
yace dole nayi kuka irin wannan toxarcin da akamin, sai dana tara dubban jamaa saboda wannan auren amma ace anfasa
[11:46PM, 1/31/2016] Pherty🎤👯: meyasa xasumin haka, meyasa basu sanardani tunda wuri kafin na tara mutanena ba, bnsan ynda xngayawa mutanena anfasa wannan auren ba😭

cike da mamaki idanunsa a bude

yace abbu auren wa akeyi? kuma meye dalilinsu na fasawa?

cikin kuka
yace bansani ba, wlhy bn sani ba inaji dama sunyi niyar toxartani ne bayan tun farko su suka nemi aurenta daga garemu

daddy ya dafa qafadarsa
yace idan ina raye baxaka taba toxartaba , kai dan uwana ne najini, bayan kai banida wani dan uwa danake dashi a duniyarnan, ban rageka da komai daga cikin jin dadin rayuwar duniya ba duk da kana xaune a qauye ne, baxan so ka toxarta a duniya ba tabbas wannan auren baxaa fasa shiba sai an daura sa.

Da waye? Abbu ya tambaya bayan ya tsaida hawayen idanunsa

batare da yayi mgn ba yaja hannunsa suka bar wurin xuwa wajen daurin auren suka barshi anan tsaye

ya jingina ga jikin motar yana kallon mutanen garin, wasu na sauri su halarci auren yayinda wasu k harkar gabansu

kamar daga sama yaji ana fadin
An daura auren Nusayba Abubakar MaKama da Abidina Umar Makama, laqadan ba'ajalan ba

wayar dake hannunsa ta subulce daga garesa ta fadi, lokaci daya xuciyarsa na shiga harbawa baibi takan wayarba yayi cikin gida da sauri xuciyarsa a dagule yarinyar dayasani 14yrs xaace an aura masa, yarinya rigimamma irinta metasani akan rayuwar aure inbanda qurciya.

yana shiga gidan ya tsaya cak sakamakon hada ido da yayi da ummansa

nan da nan hawaye na taru a idajuwansa ganin haka yasa umman ta qaraso da sauri amma kafin ta iso, nusayba da akema wankan lalle ta qaraso da sauri cike da murnar ganinsa tayi tsalle ta fada jikinsa tana fadin

oyoyo uncle! oyoyo uncle!!!
da qarfi ya finciketa daga jikinsa kamar wnda aka xubawa garwashi a jiki, yana kallom jikinsa farar shaddarsa duk ta baci da jan lalle

ya dago manyan idanuwansa da suka rine xuwa ja yana kallonta jiyake kamar ya rufeta da duka musamman ma data tsaya ta xuba mishi idanuwanta kamar xata cinyeshi........

Sadteeyash💝

📝Hausa novel📚
[4:54pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [4:52PM, 2/2/2016] Pherty🎤👯: ..........ADON TAFIYA🚵🏻

Na fertymerh Xarah💝

11 to 15

Umma ta tsaida idanunta akansa
tace mekakeyi haka abidi, meye laifinta aciki

batare da yayi mgn ba ya juya ya fice kicibis sukayi karo da daddy ya fada jikinsa ya rungumesa hade da sakin kuka

hakan yayi matuqar sanyaya jikin daddy yana ganin rashin kyautawarsa akan auren dole da yayiwa yaronsa, yaja hannunsa suka fita gidan, cikin mota suka nufa ya juyo yana kallonsa

am sorry my son, kai da nusayba duk dayane agareni nadauka inada iko akanka xn iyasaka abu kamin batare da gardama,

nasani nusayba yarinyace qarama kuma rigimamma, kuma nasan akwai wadda kake so ka aura dan haka na yarjema ka auri waccan da kakeso aduk lokacin da ka tashi amma dan Allah kada ka wulaqanta nusayba ka kula da ita pls abidi.....

abidi ya share hawayen fuskarsa, batare da ya kallesa ba

yace xn koma skul gobe,
yace meyasa abidina ba yau kadawo bane,
yace i can't stay any more,baxan xauna ba, dama wayo akamin aka aura min ita, ni bana sonta, she x not wise inada wadda nakeso xn aura..... batare dayaji amsar da mahaifinsa xai bada ba ya fita daga motar ya nufi motar da suka xo tare da malam sani ya shiga suka dauki hanyar sokoto
[1:17PM, 2/3/2016] Pherty🎤👯: Da dare su daddy suka baro bakura tareda amarya nusayba

sanda suka iso gidan basuyi tsammanin yana gidan ba.

halimatu itace qanwar abidina, sa'anin juna ne da nusayba kai tsaye sukayi part din halimatu,

daddy ya xauna anan falon yaciro wayarsa xai kira abidi sai gashi ya fito daga dakinsa sanye da farar jallabiya

daddy na ganinsa ya taso ya nufesa
abidi ashe kana ciki da har xn kiraka ne...

yayi shiru kamar baxaiyi magana ba
yace ina halimatu ne takawomin coffee

daddy ya riqo hannunsa
yace xoo abidi xo kagayamin dalilin fushinka
yace daddy bana son wannan auren, bana son villager, pls help me

daddy yaja ajiyar xuciya kafin
yace tunda rarrashi baxai yima ba shikenan, gobe xn mata bixa itada halimatu tare dasu xakaje acan nakeson suyi karatu kuma wlhy idan kaci amanar halimatu ban yafe ba...ya juya ya fice

yayi shiru yana kallonsa har ya shige part dinsa, ya sadda kansa qasa cike da tashin hankali dajin kalaman mahaifinsa......cike da tunani iri iri ya kwanta

washe gari kamar baxai fita ba, sai kuma ya fita duk sun hallara dianing caraf suka hada ido da nusayba tana ganinsa kuwa ta saki murmushi (abinka da sabo, sun saba dashi suna wasa tsakaninsu kuma hr ynxu bata fahimci komai daga dangantakarsu ta aure a yanxu ba)

nan da nan ya daure fuska ya dauke kansa aciki ciki ya gaida iyayen nasa yaje ya xauna kusa da halimatu

tace mrng yaya, ba yabo ba fallasa ya amsa mata
nusayba tace uncle jiya ka tureni na fadi naji ciwo a gwiwata(tasoma qoqarin nuna masa umma ta dakatar da ita)tace kidaina nusayba bakisan mijinki bane

ta xaro ido tana kallonta kafin ta maida kallonta fa abidi, sai ta tunxure baki ta shagwabe fuska sai ga hawaye

niba shine mijina ba Ado ne mijina bana sonshi ado nakeso

abidi ya tabe bakinsa alamar ko a jikinsa ya maida hankalinsa gun hada tea

daddy yayi caraf yace waye ado, ado baida kyau da kudi bakiga uncle yafisa kyau ba, gashi dan gaye kuma xaije dake yawo har acikin jirgi

sai ta soma dariya ba kakkautawa kafin ta rufe fuskarta da tafukkan hannayenta alamar taji kunya, sai ta tuna a qauye inna tagayamata da safe ana ba miji fura akai masa ruwa yayi wanka yaje gona

sai ta juya tana kallon abidi
tace uncle mijina xaka sha fura, tashi muje kayi wanka inna tace xakaje gona kayi aiki inka dawo nabaka abinci nace sannu da xuwa angona sai ta rufe fuska cikin jin kunya

abidi ya shagwabe fuska cike da takaici ya tashi yabar gurin

umma tace qurciya nusayba, waya gaya maki haka akeyi

tace inna ce, bara naje inda uncle.....

Sadteeyash💝

📝Hausa novel📚
[4:54pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [6:31PM, 2/4/2016] Pherty🎤👯: .......ADON TAFIYA🚵🏻

Na fertymerh xarah💝

16 to 20

Yana shiga dakin tana shigowa, a xatonsa halimatu ce batare da ya juyo ba

yace pls halimatu get out bana son damuwa wlhy

tace uncle kamanta banajin turanci ne?

lokaci daya ya juyo idanunsa akan nata
yace ke fita
tace inna tace idan mijina ya shiga daki na bishi shiyasa naxo

kalaman mahaifinsa ke masa yawo a kwakwalwa ya juya batare da yayi magana ba tabiyo sa a baya tana fadin

yanxu uncle xamuyi soyayya ne kamar yanda inna tace mata da miji sunayi.....keeeeey ya juyo yana kallonta idanunsa jawur fuskarsa ba alamar wasa ya nuna mata hanyar fita

ta juya tana tunxure bakinta cike da tsoronsa ta fice idanunta taf da hawaye ta nufi dakinsu ta sami halima tana xuba kayansu a trolley

ta xauna a kusa da ita
tace Qawa meyasa ni mijina baya sona shiyasa nakeson ado yana min murmushi banda uncle meyasa?

halima ta dubeta, batasan komai kan soyayya a matsayin shekaruntaba hassalima batasan wata dangantaka tsakanin mata da miji ba tana daiji ana fadane

tace nima ban saniba nusayba amma ke wake gayamiki haka

ta share hawayen fuskarta
inna tagayamin tace xnyi aure inyi biyayya inkula da mijina, amma bansan yanda xn kulashi ba

halima ta ajiye kayan hannunta tana fadin ko xamuje bakura ne inna tasake gaya mana nima inaso nayiwa mijina

tace kinada mijine? waye mijinki ko uncle ne?
ta yamutsa fuska
ni bashine mijina ba bana sonsa abbu nakeso😊

nusayba ta soma tsalle tana fadin hahhhaha abbu ya tsufa baida gayu baida mota nibana sonsa

halima ta tunxure baki
tace shima xai fara gayu kamar yaya abidina amma kixo mu hada kayanmu umma tace damu uncle xaije malaysia acan xamuyi skul

nusayba ta tabe bakinta
tace ni baxanjeba baxan iya xaman mota ba akwai nisa ko?

halima tasoma dariya tana fadin baqauya a jirgi ake xuwa bada mota ba kintaba shiga jirgi

ta girgixa kanta tana murmushin jin dadi
[10:11PM, 2/5/2016] Pherty🎤👯: halima tatashi tana fadin mubar sauran umma xataxo ta hada mana,
itama nusayba ta tashi tana dariya.

*
Washe garin ranar jirginsu ya daga xuwa malaysia

tym din dasuka iso nusayba duk ta jigata saboda tsoron jirgin sai amai datayi tayi a jirgin halima natayi mata dariya

Abidi duk inda ransa yake ya baci musamman idan ya kalleta wani haushinta dayakeji ya tsani yarinyar soyayya tun sanda aka aura masa ita.

cikin yinin xaxxabi mai xafi ya shigeta ba abinda take sai kuka tana qudundune akan gado,

tausayinta ya cika halima sai ta tuna idan batada lfy jikinta yayi xafi umma nasa tsumma da ruwa tana tausa mata jiki, taje ta debo ruwa ta dauko dan qaramin towel taxo tana tausa mata, nusayba kuwa sai faman ajiyar xuciya take tana kallon halima tana hawaye (abinka da yarinta itama halima sai ta soma hawaye).

a hakan barci ya daukesu, jin shirun yayi yawane yasa ya biyosu dakin ga mamakinsa sai ya sami halimatu a jikin nusayba tana barci ya matsa ahankali har inda suke ya dauki halimatu ya gyara mata kwanciya anan yaji jikin nusayba da xafi rau, hr ya juya ko tunanin me yayi oho sai ya dawo ya tadata xaune hr lokacin idanunta a lumshe bata bude ba

cikin murya qasa qasa
yace nusayba, a hankali take bude idanuwanta ta dorasu akansa ta qago murmushin yaqe mai dauke da ciwo
tace mijina..... ya bata fuska
yace niba mijinki bane inada wadda nakeso xan aura kar naqara jin kinkirani mijinki

ta tunxure bakinta sai ga hawaye sharrrrr
tace uncle ni waye mijina? ai inna tace inada miji.
yace inna tana miki wasane bakida miji inkin girma xakiyi miji, idan kinaso mushirya muriqa wasa kamar da sai kindaina kirana mijinki.

tayi shiru ta juya tana kallon halimatu kafin ta kallesa
tace tor ni bana so ma kaxama mijina Ado nakeso.....ya tabe bakinsa yana fadin yaran qauye nan da nan idanuwansu k budewa da so saboda iyaye dake saurin batasu gun yi masu maganganun auren da basu daceba musamman ma irin nusayba da inna ke xaunar da ita tana gayamata wasu abubuwa, bai kulataba yaje ya dauko mata magani da ruwa yabata tasha kana ya kwantar da ita yaja masu bargo ya lullubesu kafin ya fita.

kwanansu biyu a garin ya nema masu admission cikin ikon Allah suka samu, xasu fara ne daga j.s2 sanda suka xo skul din yana tare da principal suna tattauna kan yaran...
hankalin nusayba yayi xurfi daga inda take jiyo hayaniyar yara suna jumping jumping, i am jumping yarane qanana primary 1 tare da malamarsu....

abidi ya soma bayani wannan itace halima umar makama, sai dayar nusayba abubakar makama danakeso akula da ita sosai saboda rashi......yayi shiru sakamakon rashin ganinta gurin da yayi

ya xare idanu yana kallon halimatu
yace ina nusayba ne?
da hannu ta nuna masa yaran dake harabar makarantar suna jumping.....can ya tsinkayota babba acikinsu tanayi tana dariya da sauri ya isa gurin ya janyota hade da ja mata kunne daya

halima tace pls yaya ka kyaleta kada tayi kuka
ya cikata yana fadin intayi kukan sai me?
nusayba na riqe da kunnuwanta bakinta a tunxure.....
a hakan aka nufi class dasu yarane xalla girmansu sai dai mabanbantane a yare da kamanin gu daya aka basu subiyu su xauna

nusayba sai dariya take bakinta yaqi rufuwa saboda.kujerun datake xaune akai bata taba ganin irin suba

halima sai bata rai take tana jin haushin nusayba yanda taga ana kallonsu sai a dauka su qauyawane,
tace nusayba kibari kinga ana kallonki fa sai kowa yasan daga qauye kikaxo....
ai kuwa sai ta nutsu ta fara bata fuska tana dauke kai ita ala dole ba yar qauye bace........
[10:32PM, 2/5/2016] Pherty🎤👯: 2 weeks later

A tare suka fito da halima sanye da uniform dinsu kowane da jikarsa a hannu, suka samesa xaune yana breakfast kowacce taja kujera ta xauna hade da gaidashi

bai amsa ba ya xubawa nusayba ido
yace jiya yaron da kika daka a skul kigayamin dalilin dukansa

ta tunxure baki bayan takai arish a bakinta
tace ai shine ya karyamin pencil nikuma na dakesa

yayi shiru kamar baxaiyi magana ba
yace daya karya maki pencil ba malamine a ajin, nan fa ba qauye bace dakike dukan yaran mutane ana kyaleki nan iyayensu baxasu barki ba kuma malamai xasu dakeki nima xan dakeki idan kika sake......

tayi shiru batare datayi magana ba tacigaba da cusa kwai a bakinta

halimatu ta kwantar da kanta
tace kayi haquri yaya baxata sake ba pls ka yafe mata kada kayi fushi da ita,

ya dauke dubansa ga halimatu ya maida kallonsa ga.nusayba
yace ko bakya jine ina magana kinmin shiru

ta dago manyan idanuwanta ta xuba.mishi cikin shawaba batare da tayi mgn ba takai tea a bakinta

cikin tsawa yace nusayba....
a raunane ta ajiye cup din ta tashi tana tunxure bakinta

ni gsky uncle kadaina kirana nusayba ai ynxu niba yar qauye bace na canxa sunana nusee ita kuma halimatu taxama halimcy......ta dauki jakarta tafice.

Sadteeyash💝

📝Hausa novel📚
[4:54pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [12:12AM, 2/7/2016] Pherty🎤👯: .......ADON TAFIYA🚵🏻

Na fertymerh xarah💝

21 to 25

Gab da xata bar falon ya kira sunanta

yace xo nan nusayba...
cak ta tsaya batare data juyo ba jakarta na hannunta

mamaki ya cikasa ya tashi ya nufeta dai dai lokacin halimatu ta kammala brkfst dinta ta sunkuci jakarta

jin takunsa a bayanta yasa tayi saurin juyawa tana tsoron ya kaimata duka, ta bata fuska
tace amma uncle ynxu nagama gayama sunana nusee not nusayba ko?

halima tace yaya abidi kaxo muje kada muyi late pls

ya girgixa kansa kawai cike da mamaki ya fita..

tun xuwansu garin idan xasu fita ko xaa kaisu skul nusayba ce mai xaman gaba koda shi xai kaisu ko driver amma yau ga mamakinsa gidan baya tashiga inda halimatu ke xama

yaya kace tafito tabani wurina ta xauna inda take xama

ya sunkuyo ta qofar motar yana fadin kifito

ni abaya xn xauna frnds dina sun gayamin mai xama abaya shine hajiya mai kudi wanda k xama a gaban mota driver ne da mai aiki😏

ya bude murfin motar yana kallonta cikin mamaki
yace wato ni yanxu driver ne ko?
tayi shiru bata tanka ba
olryt tor halima shiga mota driver xai kaiku ni baxan tuqata ba kamar yanda takeso

nan ma shiru bata tankaba illah dauke kanta datayi gefe daya, yaje yakira driver ya kaisu, a sanyaye halima ta shiga motar idanunta taf da hawaye hr suka iso skul din

suna shiga class din kamar wata malama duk daliban ajin suka tashi suna fadin mrng nusee

ta ya mutsa fuska tana xama suka xauna(kakaf tsoronta suke yanda takewa mutum dukan tsiya ya xamana duk abinda tace shi xaayi, tuwan qauye ai ba wasa bane😂)

ta bude jakata ta xaro littafanta dama bata note a class sai dai tabi desk desk tana kallon note din kowa wanda yayi mata kyau shi xai mata note din ranar, ta raba littafanta iya subjects dinda xasuyi ranar taxo ta xauna idan an tashi duk wanda tabaiwa note xai maida mata

idan kuma assignment ne batayi ko a gida idan abidina yana koyawa halimatu idan yace kefa baxa kiyi bane xatace nayi nawa tun a skul halima ce takwala dake xuwa dashi gida anayi mata

idan ya tambaya ta dauko ya gani xata tashi tashige daki tasa key baxata sake fitowa ba sai lokacin xuwa skul sanda shima yake qoqarin xuwa skul

tana isa class xatace kowa ya fidda assignment din ko kuma ayimata submitting a desk dinta ta duba duk wanda ya kwanta mata tor me wannan assignment din shi xai mata na ranar.
[11:11AM, 2/7/2016] Pherty🎤👯: tym din da aka tashi skul driver yaxo daukansu....

sunyi tfy suka iso babbab titi inda yaxamana hanyar kowace musamman ma'aikata

a tsakiyar titin tace driver yayi parking ba gardama kuwa yayi tunda tsoronta yake tun ranar data mareshi

halima ta juyo da mamakinta itama cike da tsoronta
tace meyasa nusee?
ta fiddo cingam batare datayi mgn ba ta bude murfin motar ta fito, saman motar ta hau tana kallon motocin dake tsayawa

kafin kace me go slow yayi yawa a tituna tunda babban titi aka toshe

fararen mutane suka fara tsuki wasu su daki sitiyari da yawa basusan dalilin tare hanyaba

tana tsaye saman mota tana taunar cingam tana dariya ta juya gabas da yamma sai ta kwashe da dariya idan taga motocin da suke jere ita kanta batasan adadinsuba

nan aka somayin horn da alama sun soma gajiya da tsayuwa, lokacin da hankalinsu nakai gareta suka soma fitowa suna xaginta da yare daban daban akan ta sauko

halima na xaune tsoro ya cikata acikin mota

abidi na daya daga cikin mutanen da go slow ya hana masu tfy, yaja dogon tsaki hade da duba agogon hannunsa

kamar ance ya daga kansa sama ta glass ya tsinkayota tsaye kan mota sai faman dariya take riqe da qugunta mutane nabata haquri wasu na xaginta

yafito daga cikin motar da sauri ya nufesu, tana tsaye ta tsinkayosa yana nufosu da sauri ta sauka kan motar ta shiga tace driver yaja

daya daga cikin mutanen ya cire takalminsa ya jefi glass din motar sai daya tarwatse Allah yaso halima na gaba ita kadaice a baya shima dan tayi saurin duqewa da glass din sai yamata illah

suna isowa gida ta shige daki tasa key tana tsalle abin ya birgeta

shima daya shigo baibi takanta ba amma ya qudira aransa sai yamata duka inyaso duk abinda xata dauka ta dauka dama haka take idan ya daketa abinsa mai muhimmanci take daukewa ta boye dole sai ya dawo yana rarrashinta da bata haquri kafin ta bashi....

kwana biyu basu haduba sai yau sunday datafito cikin wata shiga ta xubo gashinta a doron bayanta, sanye da wata yar mitsitsiyar riga iya gwiwarta da wasu irin takalmi masu tsinin gske ta rufe idanuwanta da darkspace, ga bakin yasha janbaki (ko ina xaaje haka) sai jakarta data riqo a hannu.

ta gabansa taxo ta dauke kanta daga garesa
xn fita....
yayi shiru kamar baxaiyi mgn ba can
yace xuwa ina?
kai tsaye
tace church...
yace what😳

Sadteeyash💝

📝Hausa novel📚
[4:54pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [4:19PM, 2/7/2016] Pherty🎤👯: ......ADON TAFIYA🚵🏻

Na fertymerh xarah💝

26 to 30

Church xnje cos naga nan garin wayewa ce kawai da kudi basa addini sai na xtian kuma ni inaso naje na iya waqoqi da rawa.

yace waya gaya miki hakan, kin nemi kiyi addinine kika rasa ko kuma kinnemi malaman addini anan qasar kin rasa,

idan baa addini anan garin xaman me musulmai keyi acikinsa sannan shi wancan massallacin dake kira church dinne ko me? idan k kin kafirta sai aka gaya maki kowama ya kafirta ne....

ta juyo tana kallonsa fuskarta da alamar bacin rai ta jefar da jakarta da takalmanta ta xauna a kusa dashi sai hawaye sharrrr

ni shikenan komai sai ace bnyi dai dai kullum sai anyimin fada kamar baa sona

yayi shiru bai tankataba
tace nasan abinda nakeyi fa inada hankali

yace i see kinada hankali kike musulma xakije church ko, wonder shall never end abin yana dauremin kai

halimatu ta matso tace yaya nusee tanaso taje church ne dan rawa kawai ko a class haka takesa suna mata waqa tana rawa

what... a class kuma?
ta gyada kai tana kallonsa komai batayi yaya bata note bata assignment sai dai tabada ayi mata kuma haka take dukan yara idan mutum yakaita qara inda uncle xata qara dukanshi....

abidi yayi shiru xuciyarsa sai xafi take shi dai wannan karon yayi asarar tfy nigeria amaimakon ta xamemasa adon tfy sai taxamemasa bala'i

yace tashi daga jikina marar kunya xo nan kimin n-down

tacigaba da share hawayen fuskarta tana tunxure baki ta sauko ta rungume qafafunsa tana kuka

qarya takemin uncle kuma sai namata duka mukaje skul gobe

karki daketa ki kasheta ma idan kin iya

tacigaba da kuka sosai tana fadin Allah sai namata duka sai na jimata ciwo na fasa mata baki kamar yanda nayiwa monitor dinmu, kuma ni ynxu ba qawata bace na canxa qawaye, serdiyer, miss aysher, xarah dange da hassyna ne kawai qawayena,

cikin maxa kuma paul, thug da tiger ne kawai qawayena, kuma daga yau baxan qara xama dakeba tunda kikemin qarya.....ta cigaba da kuka sosai😭

yayi shiru cike da mamaki idanunsa akanta mafita dayace kuma ita xaibi yana ganin hakan shixaisa ta shiryu

ya rungumota xuwa jikinsa
yace yi shiru qanwata kibar halimatu nasan qarya takemiki shiyasa baxan dakekiba kema kiyi haquri kada ki daketa kinji
[6:31PM, 2/7/2016] Pherty🎤👯: amma wadannan qawayen naki maxa ki canzasu kinji nusee baby

ta gyada kai tana murmushi
tace xn canxasu uncle amma kai xaka xama abokina
ya gyada kansa idanunsa akanta
ta kyalkyace da dariya ta tashi tana fadin uncle kasan banyi wanka ba nasa wannan kayan nayi kwalliya, nace halima ta cudani taqi shine naqi nayi wanka

yace jekiyi wanka yanxu kixo ina jiranki

tor muje ka cudani.
ya yarfe hannuwansa
yace halima jeki cudata baxan sakewa kowa wanka acikinku ba

ni yaya baxan cudataba itama bata cudani

yace jeki nusee kicire kayan xn kira junaina ta cudaki (mai aikinsu)

tafice batare datayi mgn ba, yabita da kallo kawai yarintace nan da wasu shekaru yasan baxata kwatanta hakan ba abu daya ya tsaya masa arai shine wasu arna data kira a matsayin qawayenta maxa, mafita dayace boarding xai kaita gobe....

washe garin ranar ya kwashe su yaje yayi mata provision da komai ya kaita skul bata fahimci komai ba sai sanda taji yana fadin ita kadai xatayi boarding halima kuwa day

a raunane ta juyo tana kallonsa
tace uncle ni xnyi boarding Allah bana so...sai ga hawaye sharrrr

tor ya xnyi nusayba, ba kyaji idan ba boarding na kawokiba baxan sami sauqi a rainaba da qurciyata kinaso ki haddasamin damuwa

cikin kuka tace nabari uncle baxan sake ba plsss kayi haquri

halima sai tsalle take tanajin dadi tana mata gwalo

taxo ta rungumeshi tana kuka sosai hr cikin ransa yakejinsa
pls uncle nabari baxan sake ba iya tausayi yaji tausayinta amma ba yanda ya iya

karo na farko daya kaimata sumbata a goshinta yasa hannu yana shafar gashinta cikin wani irin yanayi
yace kiyi haquri ki xauna ba abinda xai sameki ba wanda xai dakeki bakiga duk kayan dana siyomiki ke kadai bada halimatu ba

ta fisge jikinta ta soma shurin trolley din tana kiran bana so ni banaso gida nakeso da uncle dina

yayi shiru hade da riqota yace i promise u gobe idan naxo daukan halima xan wuce dake amma for now ki kwana koda sau dayane kinji

tayi shiru tana cigaba da kuka ta juya batare da ta sake magana ba tafice ko kayan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment