Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirata tadawo ta xauna,
yace nusayba metakeyi?
tace wlhy bnsaniba cos rufe qofar tayi inaji kukan dai ne.

kamar bashiba saboda muryarsa datayi qasa sosai ta nuna wani mutum mai axabtuwa da soyayya, yanayine da halimatu bata taba ganin dan uwanta a ciki ba

yace halima dan Allah a matsayinki na mace mai qarancin shekaru kuma shaqiqiya agareni wadda nakeda tabbacin baxatagayamin qaryaba dan naji dadi ta boyemin gsky dan na cutu inada wani aibu ko hali marar kyau da nusayba ta tsaneni haka

tausayin dan uwanta ya kamata
tace wlhy yaya bakada shi.
yace tor miye laifina dan na dora nusayba kan turba mai kyau dan na nuna tasan kanta tadaina wauta?

ta runtse ido tace ba laifi bane yaya tunda koni ina dorata akan hanya kuma bata tsaneniba
[9:47PM, 2/26/2016] Pherty🎤👯: ba abinda k damun nusayba hr ynxu sai qurciya da wauta hr ynxu batasan kantaba batasan so ba tunda ko sadiq bata damuwa dashi kamar ko wacce uwa.

ya bude baki yana.kallonta da mamaki who told u?

nasan komai yaya kada kamanta tare muka taso mukayi rayuwa tun muna qanana, nusee xata iya bada lbrn kamar ynda xn iya bada nata above all ma tun tasowarmu, i'm far more sociologistic than a political scientist,kaga kuwa nice nafi kowa sanin halinta.

yayi shiru yana kallonta
yace ni inaji ajikina wataran xatasoni ta rungumi yaronmu tunda ynxu.muna inuwa daya da ita ina sonta fiye tsammaninki amma baxan iya roqonta akan ta soni ba kada ta rainani

(a ranta tace)yaya abidi ho ! sannu dason girma wane raini yayi saura tsakanin miji da mata, ai da daban, ynxu daban babu xancen discipline sai unity and cooperation
a fili kuma tace tough kaima kanada laifi yaya

mace yar rarrashice tanaso anuna mata xahirin soyayya ciki da waje ,baka rarrashinta tarairayarta da nuna mata xahirin soyayya idan kayi laakari da xaman ku na farko ba komai aciki sai fada da fushi wannan shi ya janyo tsana a tsakaninku kuma tun farko baka koyamata ynda xata soka ba.
ka duba ynxu kaga ynda ta cnxa rayuwarta karatunta kawai tasa agaba, kanta na cikin duhu batasan komai ba sai wnda aka koyarda ita, batasan soyayyar miji da mata ba, batasan ynda ake rarrashin miji ba,batasan ynda ake kula da miji ba,kishima batasan ynda akeyiba, idan ka lura kallo bai dametaba tun dawowarta daga malaysia,bata karance karancen nan na littafi danaso na dorata akai taqi, batada qawa ko aminiya,bata riqon waya balle ta shiga yanar gixo,she is not exposed to modern society....not interested to social networks e.g whatsapp,bbm, twitter, fcbuk e.t.c.....she is just acting according to her experiences kamar yadda aka tafiyar da rayuwarta abaya,

idan ko hakane yaya nusayba na neman rarrashi da tarairaya ka mantarda ita komai ka koya mata ynda xata soka a ynxu babu abinda xai ragu daga gareka idan ka jure wulaqancinta watarana xata sauko?

murmushi yayi yana mamaki a ina halima tasan wannan,meyasa tafisa xurfin tunani da hankali......sai yayi qoqarin kawarda mgnr ta hnyar
cewa k yaushe xakiyi auren ne?
ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta tana dariya ta fice tana fadin kai yaya bari dai na turoma gimbiyar.

tunda halima tagayamata kiran take xaune tana saqe saqen taje kokarta je a tunaninta mexatayi meyasa yake nemanta a wannan daren....

ta tashi ta dauki hijab dinta ta fice....
ya fito wanka daure da towel a jikinsa da qarami towel yana tsane gashin kansa sai ga xee ta shigo

tace honey ashe ka shigo shine baka sanardaniba,

yace akoda yaushe ina gayamiki muhimmancin sallama da kuma dimbin ladar dake cikinta amma meyasa kike butulcewa ne?

cikin halin ko inkula da mgnrsa ta qaraso garesa tana shagwabe fuskarta
next tym xn qoqarta naji ko xn iya ina mantawane

ya tabe bakinsa hade da dauke dubansa daga gareta ya isa bakin mirrow ta bishi ta karbi towel din tana tayashi tsane gashin kai dai dai lokacin nusayba ta shigo da sallama

ya amsa a raunane hade da juyowa yana kallonta tana tsaye bakin kofa bata shigo ba kuma bata fita ba,

yace ki.....bai qarasaba taja dogon tsaki ta juya ta fice hade da bugo masu qofa gammmmmmmmm🙉

Sadteeyash💝

📝Hausa novel📚
[5:01pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [9:54AM, 2/28/2016] Pherty🎤👯: ........ADON TAFIYA🚵🏻

©Fertymerh xarah💝

116 to 120

Ya tashi batare daya kula xee ba ya xira doguwar jalliabiya yabi bayanta

tayi xaune jugum ya janyo stool din madubi ya xauna daf da ita yana fuskantarta hr lokacin bata dago ta dubeshiba

ba abinda ya fahimta a yanayinta sai kishi,kenan nusayba tasan kishi kuma so k kawo kishi......

yace bayan rashin so nusayba menene matsalarki a xama dani?ynda yayi mgn sai da ya saukar mata da kasala saboda yana gab da ita numfashinsa na dukan fuskarta, tayi shiru bata tankaba

yace ke.nake saurare

a hankali ta dago ta dubeshi abinda tagani a cikin kwayar idonshi ya sanyata kokonton anya uncle ne cos kwayar idonshi ta nuna wani mutum dake fama da axabtacciyar soyayya yet he is not weak amma kamar ba uncle mai jida kai ba.

sai tayi cooling
tace ninace bana sonka?
yace haka kika ce mana kunnuwana suka jiyemin bawani ya gayamin ba,

ta xumbure baki hade da kauda fuskarta
yace bana qalubantarki not even a little, cos nasan hr ynxu aiwai qurciya atare dake na yarda na amince xn cigaba da xama dake a duk ynda kike inaso na cigaba da xama life mate dinki idan hr xaki bani gurbin,

tace amma ai kace bnda hankali bnda tunani idan ni nace bana sonka kaima ai bani kakesoba wannan xee din kake s..... ,yayi saurin katseta hade da riqo hannunta

kiyi haquri ynxu nagane kuskurena kinada hankali, tunda bakyasona kuma kince bann sonki ynxu inaso mugina rayuwa mai kyau mu mance baya (past) mu fuskanci gaba (future) muyi gini akan sabuwar rayuwar da muka tsinci kanmu (present) batare da tuna baya ba kimin alqawarin wannan,

bata amsaba amma xuciyarta sanyi take tana saukowa daga tsananin fushin data dauka dashi,fuskarta ta nuna sassauci,tana jin son abidi,ashe soyayya baka saninta sai taxo kanka batasan lokacin datafara sonsaba ashema xata iya fassara tata soyayya da defination da yawa wanda neither Dr.fulani Gafai nor Marhoom Danbatta experienced it a LABARI NA💝 (duba litafin) ganin tayi shiru batayi mgn ba yasa ya riqota
yace xo muje xnyi mgn daku, ba musu tabi bayansa

xee na xaune a falo suka sameta ya xauna hannunsa na riqe dana nusayba
sosai ya daure fuskarsa yana kallonsu

yace xainab ga matata nusayba, lfy muke xaune da ita sanin kankine ban taba baki wani lbr daya shafi nusayba ba tun xamanmu dake
[10:15AM, 2/28/2016] Pherty🎤👯: sannan ba don tayimin wani laifi ko ta gaxa dani ta wani bangare yasa na aure kiba . na aurekine dan ina sonki kamar ynda nake sonta,
A girme dai kin girmeta kin fita hankali dan haka ki riaeta kamar qanwarki.... ya juya ga nusayba

yace nusayba ga xainab nan itama matace kamar ke, na auretane dan ina sonta badan na quntatt miki ba, idan ta girmeki a shekaru kin girmeta a aure, don haka kece uwargidana a duniya da lahira ki xauna lfy tare da ita duk da kowa sashenta daban ki riqe girman da na baki bnda fada tsakaninku kinji....tayi shiru bata tankaba,

ganin haka ya dubi xee a raunane
yace bari na rakata ta kwanta,itama bata tankaba saboda a qule take ga kishi kamar ya hudo mata qirji takeji, suka fice suka barta nan

suna shiga dakinta ya dagata gaba daya bai diretaba sai a gadonta hannuwanta yayi baya dasu da hannun damanshi,

yayinda yayi amfani dana hagun wajen tallafo kanta a hankali ya soma kissing dinta gently tun daga bakinta wuyanta qirjinta hr xuwa yatsar qafarta.....

ta bude baki xatayi mgn sabida dimaucewa yayi saurin toshe mata baki yana girgixa mata kai,idanunshi jajir a shide kuma a juye da tsimin soyayyarta

wasu irin kalamai yake gayamata cikin kunnuwa da qananun shekarunta baxasu iya fassarawa ba, gaba daya tsigogin jikinta sun gama tashi da sabon alamari,

ya cigaba da sumbatarta yadda ransa ke so ko.motsi ta kasa yi ta xamo spale and completely touched.....

da qarfi aka turo qofar dakin tana tsaye ynda ta samesu ranta yayi mugun baci idanunta suka juye kalar ja saboda.kishi da bacin rai

yanayinta ya tsorata nusee,ta janye abidi da bashida wani sauran karfi ko katabus ta miqe hade da maida zip din rigarta,ta lalubi dan kwalinta ta nufi hanyar toilet tana sauri saura kadan ta fadi saboda tsoron zee.....,

yayi xaune hade da dafe kansa da hannuwansa duka biyu kafin ya dago a raunane idanunsa cike da tsana yake kallonta kafin yaja dogon tsaki batare da ya kulataba ya tashi ya fice.....

Sadteeyash💝

📝Hausa novel📚
[5:01pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [8:42AM, 3/1/2016] Pherty🎤👯: ..........ADON TAFIYA🚵🏻

©Fertymerh xarah💝

121 to 125

Fitarsa keda wuya ta juya tabi bayansa a harzuqe,

yana kiciniyar cire jallabiyar ya sauya da kayan barci ta ixo qofar da qarfi, ko kallon inda take baiyiba ya cigaba da abinda yakeyi.

tace andaiji kunya kuma kaji tsoron Allah.
a raunane ya juyo yana kallonta

yace dama akwai kunya tsakanin miji da mata ne? ba zina nayiba matatace fa,

tace dan matarkace sai ka fake kaci amanata ai yau girkina ne,kuma ban yafe ba😳

yayi shiru yana kallonta cike da mamaki
yace baki yafe ba akan me?

saboda yau ba girkinta bane k......... cikin tsawar dana firgitata ya katseta

yace shut up stupid, jahilar banxa,ke bakida tunanine tunda yarinyar nan ta dawo gida shekara biyu ynxu muke tare da ke,hr mukaxo bata taba nuna damuwa akanki sai ma tirsasa mata da akayi tadawo, rana dayace kike ma baqinciki,idan kinada magani kije kiyi a dakinta xan kwana,kuma sati daya xnyi acan, sai anyi magana kice girkinki,me kika iya acikin girkin kigayamin tunda na aureki me kika taba girkamin ?

tace ni kake gayawa haka abidina? ya gyada kai yana kallonta cike da bacin rai
yace ko dukana xakiyine?
tace bance xn dakekaba amma wallahi idan banyi gidan yarin waccan yarinyar ba ni ban haihu ba,bata isa nayi kishi da itaba batada ajin daxaisa na hada miji da ita wlhy sai na kasheta

yace ki kasheta a kasheki,shari'ar nan daban take data waje idan kina tunanin can kudi ake bayarwa nan kasheki xa'ayi

tace sai me inkasheta akasheni,kagayamin nida kai wayafi baqin ciki,

ya juya yana fadin banxa tunda baki taba xuwa islamiya ba ai baxaki damu da hukuncin da Allah ya tanadar maki acan ba, lunatic..!

nice lunatic,ta fada idanunta a waje

bai kulataba yaja tsaki ya fice daga dakin....ya nufi sashen nusayba ya murda qofar dakinta yaji shi gam ta kulle da key sai ya nufi dakinsa dake sashenta ya kwanta.
[9:35AM, 3/1/2016] Fertymerh😘: Nusayba kuwa tsananin tsoro ya hana mata barci dan tana jiyo hayaniyarsu,ta tsorata da kalaman xee dan tasan xata iya aikata abinda tace, da tunani iri iri tayi barci amma sama sama

washe gari koda ta tashi idanunta sunyi luhu luhu na rashin barci

da kyar tayi wanka,tasanya kayanta,ta janyo trolley dinta tana hada kayanta,abidi ya turo qofar ya shigo

ya xuba wani farin yadi caftan mai rashin kauri hr ana iya hango vest din dake jikinsa

ta cigaba da xuba kayanta don batason ganinsa ya xauna kusa da ita hade da riqo hannunta, ta fincike da qarfi hawayen datake maqalewa suka xubo mata
cikin sanyi murya
yacd meyayi xafi haka,idan nayi maki wani laifine ayimin afuwa
ta zumbure baki,ni gida xnje.baxan iya xama ba
yace tor naji amma kibari kiyi kalaci ko

ni baxan ci ba
yace tea kadai,bai jira cewartaba ya fita ya hado mata tea da coconut cake ya dawo da rarrashi ya samu taci kadan

yace ba abinda xai faru dake nusee,kiyi haquri ki xauna dani if not i will become shattered....!kefa kika gayamin jiya kin haqura
tayi shiru bata tanka ba

yace kisoni koda rabin son danake maki ne,ya kwantar dakai akan qirjinta yatsun hannunshi na cikin sumar kanta,sai taji wani sanyi a ranta batare datayi magana ba ta rungumoshi very tight mai nuna gesture din dake cikin xuciya....

126 to 130

Kwana uku !

Kamar kullum tana gama sallar isha'i take rufe qofarta itadai tana cike da tsoron xee duk tsiwarta da rigimarta yanxu babu su komai a natse takeyinsa
sanda ya dawo sallah ya murda qofar dakinta yajita rufe kamar kullum sai ya nufi dakin xee ya samdta xaune yanayinta ya nuna tana cikin damuwa sai tabashi tausayi,
ya xauna a kusa da ita
yace danme xaki riqa tada hankalinki saboda nusayba,yarinyar nan agabanki tatashi kinsani batada wani mugun hali bayan rigima ynxu kuma duk ta kauda wannan dame kike tunani xata cutar dake?

tayi shiru hade da goge guntuwar kwallar dana xubo mata ganin haka sai ya rungumota cikin shigar lallashi da irin abinda yasan yanncin lagonta dashi,lokaci daya ta kwace jikinta daga nasa data tuna ai da wata ya kwana jiya

a fusace tace kamanta hr yau a dakinta kake.ne?
yace to bata kulle dakiba nikuma a buqace nake...

ta balla masa harara cikin takaici tana mamakin rashin ta idon namiji wai me sweet 18 xai ce yana buqatar mai 28 hakan ya qara fussata ta

ta nuna masa qofa
kaga binan kafita pls

a wahalce yace nikuma ake kora yau

tace an koreka kana kuma tabani xan rotsa maka crystal dinnan a tsakar kai

ya tashi yana fadin meyayi xafi Allah yabaki haquri ya fice dan yasan xata iya aikatawa,tabishi da kallon baqin ciki qanqanuwar yarinya ta haukata mata miji ta sauyashi gaba daya ta maidashi mai arha duk ajin nasa tamaidashi mara kunya da kawaici alhalin ba haka yakeba dolene ta dauki mataki mai tsauri akan nusayba

yaxo bakin qofar dakin nusee ya soma kwankwasawa😂

kina jina fa nasan bakiyi barci ba kixo ki bude min qofar

tace nifa baxaa kasheni a banxaba am not ready to die now...mema xakayi a dakin yanxu

koma mexanyi inkin bude ai xaki gani ko?
[9:58AM, 3/1/2016] pherty🎤👯: tayi shiru bata tankaba kuma batada niyar budewa, ya kwantar da murya
yace pls nusayba ko kinaso ki kwana cikin tsinuwar mala'iku ne,

duk wannan abin da yake akan idanun xee baqin ciki kamar ya kasheta tunda take dashi bai taba roqonta ta bude masa qofa ba wai danta rufe....ba musu nusayba ta bude masa qofar a sanyaye ai kuwa ya sunkuce yayi ciki da ita

a wannan daren nusayba tayi kuka sosai hr ta gode Allah kamar wancan na farko sai taji ba banbanci xee kuwa itama kwana tayi tana kukan kishin mijinta.

Washe gari da shirinsa yaxo dakin xee
yace inada tafiya yau ko xakixo na ajiyeku a gidane

batare data kallesa ba tace bana buqata
ya juya hr yakai bakin qofa ya juyo yana kallonta
yace idan nayi maki wani laifi tun xamanmu dake ki yafemin bansan sharrin qarfe ba, sai taji jikinta yayi sanyi sosai ta dago a raunane tana kallonsa
tace Allah ya yafe mana gabaki daya,ya dawo ya sumbace ta a goshi kana yace amin ya juya ya fice koda yafita nusayba hrta fito cikin shirinta tana tsaye bakin mota suka shiga
tace uncle ita baxata je bane?
yace tace bata xuwa ta saba xama ita kadai a gidan baxataji tsoro ba, tayi shiru bata sake mgn ba hr suka iso gidan,abbu ya dade da shiryawa shi kadai yake jira dama xasuje ne bakura ganin gonakinsu,

bayan sun kebene ya rungumota a sanyaye
yace am so weak badan komai ba sai dan xnje na barki ki kula da kanki kinji, ta gyada kai tana kallonsa itama sai ya sumbaceta ya juya ya fice,yana fitowa suka dauki hanya shida abbu.

Kusan minti talatin da fitarsu sai ga daddy ya shigo a rude da guntuwar kwallah a idanunsa inna da umma na ganinsa hankalinsu na tashi musamman dayace su fito suje asibiti su abidine sukayi accident,

dirshan nusayba takai xaune cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa halimatu kuwa kuka ta soma da kyar suka shirya sukayo asibiti kai tsaye dakin da aka kwantardasu suka nufa, nusayba ce kan gaba tana tafe tana tuntube cak ta tsaya cike da wata irin fargaba ganinsu kwance rufe da farin mayafi me hakan ke nufi badai sun mutu ba,
sai tasoma girgixa kanta hawaye na cigaba da xubo mata

daddy ne yayi qarfin halin buda mayafi daya abbu ne a kwance da sauri inna taqaraso cikin wani irin kuka dai dai lokacin da likitan k fadi

sai dai muyi haquri dashi yarigamu gidan gsky Allah ya karbi abinsa.... dayan ma.....bai qarasaba lokaci daya numfashin nusayba dana halimatu na dauke sai gasu kwance qasa ragwaf.

Sadteeyash💝

📝Hausa novel📚
[5:02pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [12:18AM, 3/5/2016] Pherty🎤👯: ..........ADON TAFIYA🚴🏻

©Fertymerh xarah💝

131 to 135

Fardawowar su yayi dai dai da shigowar xee a rude Dr.bakori gaba tana bayansa.

a rude nusee ta sauko saman gadon da aka kwantar da ita idanunta taf da hawaye take kallonsa

tace likita da gaske duka sun mutu...

yace kiyi haquri,mutuwa na kan kowa,kullu nafsin xa'iqatil mauti duk mai rai mamaci ne

hawaye suka cigaba da xobo mata, jikinta har rawa yake qafafunta nason gaxa daukarta

ya fice yana fadin ku biyoni ynxu, atare su uku sukabi bayansa kowane jikinsa a mace hr xuwa dakin da abidina yake kwance tare dasu daddy, lokaci daya duk sun fita hayyacinsu

Dr.bakori yigaba da fadin,inaji wannan yasami matsala a qafafu to confirm it sai Dr.maina yaxo amma ynda naga matsalar daga spinal cord dinsa ne banajin xai cigaba da tafiya.

dirshan halimatu ta xame ta xauna cike da jimami yayin da nusee ta dora kanta akan gadon da yake kwance ta saki kuka mai narkar da xuciya....iya rudewa daddy ya rude sai dai ya kasa nunawa saboda kar hankalinsu halimatu ya qara tashi

xee na tsaye sai yamutsa fuska take
ita batajin xata cigaba da rayuwa da gurgu,tayama xatayi rayuwa da musaki,komai son da take masa dole ta barsa kuma dole ya sake ta dan.baxata iya.lalurarsaba baxata iya.kula dashiba,ta goge guntuwar kwallar dana xubo.mata ta tausayinshi, ta cigaba da taunar cingam dinta ahankali tana.kallonsu umma da inna..........

BAYAN KWANA UKU....

Ya farfado daga doguwar sumar da yayi tym din hr angama ukkun din abbu(Allah yaji qansa😪)nusee nadaga gefensa hannunta sanye a hannunsa daya

tun lokacin da ya farfado yakasa furta kalma ko daya,duk iya qoqarinsu daddy akan yayi mgn yaqi hakan ya qara tada masu hankali indai babu internal injury akansa...

su biyune a dakin xee ta shigo rataye da jakarta da wata irin shiga danayi matuqar gigita nusee kamar ba matar aureba

a hankali ta tako inda suke kwance tana taunar cingam
tace ya jiki,
bai amsa ba illah idanu daya xuba mata
tayi jim kamar baxatayi magana ba sai kuma ta nisa
[12:47AM, 3/5/2016] Pherty🎤👯: tace baxan boye ma ba na cutar da xuciyata Allah ya gani baxan iya xama da musakiba,komai son danake masa kuma komai kyaunsa da kudinsa, am sorry to say inaso ka sakeni,

idanu xare nusee k kallonta
tace ke bakisan Allah ya haramta mace tanemi saki a gun mijintaba. ballantana ma wannan dake jinya yau fa ya farfado kuma kinsan yana sonki dan Allah karkije kibarsa ki xauna dashi xaiji dadi....

a fusace tace keee kimin shiru qaramar yarinya,me kika sani a rayuwa,idan k xaki iya ni baxan iyaba dan dama dan uwankine,dole sai ya sakeni kuma dole nabarsa komai sonsa danake....

cikin kuka nusee ta soma roqonta musamman data ga ta ciro memo da biro ta cilla masa a gadon dayake kwance
tace bana nemanka da fada inaso muyi rabuwar arziki albarkacin son danake ma amma na roqeka da girman Allah ka sakeni......

ba musu hannunsa hr rawa yake ya dauki biron sai dai yakasa daukan memo hr sai da nusayba ta taimaka masa da kyar ya iya rubuta NA SAKE KI! NA SAKE KI!! hr sau biyu xai rubuta na uku nusee ta kwace biron tana girgixa masa kanta,

xee ta karba tana fadin ai da kinbarshi ya qarasa, tayi murmushi tana fadin wannan ma yayi Allah ya sadamu da alheri xn koma gida malaysia idan nasami tym xan riqa xiyartaka ina duba lfyrka
da hannun yayi mata alama karta dawo taje hr abada....tayi murmushi tasa kai ta fice.....

sai ya maida kallonsa ga nusee ko itama xata rabu dashine ga mamakinsa sai ta fada jikinsa tana kuka sosai mai tsuma xuciya, sai alokacin hawaye nasami damar xubo masa, suna haka Dr. bakori da Dr. maina na shigo a bayansa securities ne da fadawansa suna biye dashi itadai nusee tana cike da mamakin mulkin wannan likita.

cike da qasaita ya xare madubin idanunsa ya miqawa abidi result din da ya shigo dashi
yace congrat, iya bincikenmu mun gano hasashenmu ba gsky bane bakada matsala a spinal cord kuma qafafunka lafiyarsu qalau illah wasu jijiyoyine da suka daure insha Allah nan da dan wani lokaci xasu saki kacigaba da tafiya kamar da.

A tare shida nusee suka saki ajiyar xuciya fuskarta dauke da murmushi da hawaye take kallonsa
tace likita da gske xai tashi yayi tfy kamar da?

ya gyada kai yana gyara masa drip
yace amma ba ynxu ba sai an dauki lokaci kadan
tace kwana nawane likita?
ya juyo da mamakinsa yana kallonsa sai yaga kamar yasan fuskar,ya tsuramata ido yana kallonsa hr sai ya gano ko ina yasan fuskar

hakan ya qular da abidi ya tsargu da kallon da yake mata nan da nan fuskarsa na sauya

shikuma bai dauke idonsa akantaba hr sai daya tuna inda yasanta
yace ba lallai bane na iya tuna sunanki but i knw you by face,
tace ni na manta,
ya tabe bakinsa yatuna amma baxai iya gayamata ba kuma yana son sanin meta haifa, cikin yayi girma a lokacin amma yana ganin idan ya tambaya mulkinsa da qasaitarsa sun xube a qasa dan haka sai ya share xancen
yace anjima Saif Bakori xaixoma da magani tare da allurar da xaayima,

abidi bai amsaba bai kuma sake kallonsaba sai ya dauke kansa daga garesu yana kallon wani guuu shima maina bai damu ba ya juya ya fice fadawa na xubewa qasa suna masa ikirarin sarauta yayinda wasu fadawan k biye dashi da sauri suna sauya masa labcoat xuwa alkyabba....

nuseee tabisa da kallo cike da mamaki wannan dame yake taqama Mulki ko Sarauta?

ta sauke ajiyar xuciya ta maida kallonta ga abidi dake kallonta.

Sadteeyash💝

📝Hausa novels📚
[5:02pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [12:48AM, 3/6/2016] pherty🎤👯: ........ADON TAFIYA🚴🏻

©Fertymerh xarah💝

136 to 140

Bayan kwana biyu, kai tsaye Dr.merah ya dauki annual leave tare da abidina yana son xuwa dashi pheonix dama adubasa sosai,

nigeria batada kayan aiki kamar waje cikin lokaci qanqani daddy yayi masu visa gabaki dayansu bnda inna da umma suka dunguma sai Phoenix.

Alhamdulillah anyi aiki cikin nasara sai kuma fatan samun lafiyarshi, sai dai a ynxu anbashi wheel chair akoda yaushe nusee ce k tafe dashi tana xagaya asibitin dashi,

abu dayane k damunta dashi rashin maganarsa hr xuwa wannan lokacin,

a tsarin halittar dan adam(personality) yana cikin rukunin al-ummar da ake.kira (introvert) kasancewarsa (sociable)bayason magana da.kowa da wuya kaga dariyarsa sai dai idan ana hira guri ya qure yakanyi murmushi dimple din da cleft dinsa su motsa.

A wani dare bayan kowa ya watse ya rage su biyu sai nusee tasa masa kuka, ba kukan komai ba face kukan rashin maganarsa,

a hankali yakai hannunsa akanta yana shafar gashin kanta,ta dago a raunane tana kallonsa idanunta taf da hawaye sunyi jawur ga mamakinta sai taji yayi magana

yace nusayba wanene ya haliccemu?
tace Allah s.w.a,
yace tor meyasa kike kuka kike damar da kanki abinda Allah ya riga ya rubuto akaina kenan cikin ikonsa kuma zan sami sauqi sai abinda Allah yaga damar hukuntawa a garemu, mu kuma dole ne mu zamo masu godiya idan muna son imanin muya cika,

nusee ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na abidina da tawakkalinsa.

Lafia garkuwar jiki sauqi ya samu a gun abidi har yana tashi da qafafunsa ya taka da taimakon nusee ko halimatu

ganin haka yasa daddy ya koma gida nigeria dan ya dubasu ya dawo,

cikin lokaci qanqani shaquwa mai tsanani ta shiga tsakanin abidi da dr.merah hr suka xauna suka bawa junansu labarin rayuwarsu da matansu,

a dan xamansu suka tattauna game da matsalar nigeria ganin waje basu da matsalar komai a rayuwa

ya cigaba da fadin pheonix tayi kuma ta hadu tana da hanyoyin cigaba ta kowane fannin mussaman a wurin man fetur amma mu nigeria cigabanmu har yau baixoba ko yaushe nigeria xataci gashin da Allah ya bata?

gashidai qasace mai cike da albarkatun kasa musamman man fetir amma suna tsadarsa kuma the problem is with our leaders ,they dont know how to harness the resources available,inkaga talaucin da akeyi acikinta north & south da dilapidated infrastructure sai ka tambayi kanka ina shuwagabanninmu ke kai arxikin Nigeria?
[12:55AM, 3/6/2016] pherty🎤👯: Dr. Merah yayi qasaitaccen murmushi hade da xare madubin idanunsa
yace ance an bawa nigeria yanci kai amma baa daina bautar da al,ummarmuba,

haka suka cigaba da tattauna matsalar nigeria hr abidi ya soma nuna gajiya da hirar dan bai taba tsammanin kasaitar merah xata barshi yayi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment