Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki bude muhammad yasoma kallonta cikin rashin fahimta yace banganeba, se a time din tagyara zamanta jiki a sanyaye tace insha allahu meenal tana gidanmu itama tana rayuwa amatsayina kamar yadda nakeyi anan allah ne kadae yasan nufinshi daya kaddara hakan takasance al amarinmu akwae ban mamaki seyau nakara tabbatar da hakan nakara ganin hotonta, muhammad yace mekikenufi kenan kikace insha allah baki tabbacin tana gidan naku kenan why dazaki yaudari iyayenmu haka tunda nafara dora idanuna akanki nasan bakye bace meenal dita wannan abun yadauremin kae meyasa hakan zata kasance taya kamanninki yazamo irin nata? mimi duka abinda yafaru da ita tasanar masa da irin mafarkin datakeyi da meenal da soyayyarsu da mujaheed, mamaki yahashi magana illah kallon ta dayakeyi, girgiza kae yay yace koda akasanar daddy bashi yahaifi meenalba sam baki shiga tashin hankali akan hakan bah wannan dalilinne yasa shima daddy fara tantama akanki, sesae daga rana irinta yau komae yazo karshe gayamin awanin garin kike inda meenal take rayuwa yanzu, mimi tace gombe! gombe ina? yola, tabashi amsa, yajin jina kae yace shin kece wadda mujaheed yafara furtawa so ku kuma sunfara soyayyane da meenal kafinke?mimi ta girgiza masa kae tace nice yafara furtawa so kuma na amshi soyayyar sane saboda nagani meenal tanada masoyinta shiyasa na amince masa tunda ina matukar kaunarsa nima, cikin daga hankali muhammad yace kina nufin meenal tanada masoyi yanzu haka?
Mimi takalleshi a takaece tace eh nagane hakanne saboda irin kalaman bakinsa da sunan datayi masa saving, cikin mamaki muhammad yace to wanene wannan nikuwa dabansaniba, broda din nadiyane aminiyarta shine suke soyayya, muhammad ya rintsu idanunshi yace kada nakuma jin kinfurta wannaa maganarma dole zuwa adamawa yataso mana,
Mimi cikin tashin hankali tayi bayi tana girgiza masa kae tace pls kada kumaidani gida yanzu batareda na auri ya mujaheed bah katemaki rayuwata,muhammad yace why?setayi shiru tana tunanin aurenta da bassam bashakka yanzu wannan auren yakusa, seda tahadiye yawo tace saboda mu bama auren bare sedae a family, da mamaki muhammad yace saboda me wani irin tsari gareku haka ko ince danku komadae meye kada kidamu ni nace namiki alkawari insha allah zaki auri mujaheed cikin tashin gamsuwa tace nidae katemakeni kada kamaidani gida batare da na aureshi zuwa yanzu seda yagama nazartatta tukun yace haryanzu da akwae abinda kike boyemin so kada kidamu sansan komae idan munje gidan naku kitashi kije kiyi bacci kikuma sawa ranki cikin kwanakinnan zaki koma gida, mimi tasaki kuka tadago zata kuma yimasa magana yadaga mata hannu, cikin daure fuska yace bazan kuma jin tabakinki bafa so jeki kwanta idanma karya kikayi duka zansan komae mimi cikin cikin bacin rae tafita daga dakin tana kuka,lumshe idanunsa yayi yana ganin wannan abun kamar a dramatic allah sarki auntie safiyya ga wani muhimmin abu yana shirin faruwa dake amma bakya nan allah yajikanki da rahama koda yabude idanunsa tafda kwallah yace kema mahaifiyata allah ya kyautata makwancinki yau gashi danki yayi aure barabon kiga jikokinki...
Koda mimi tashiga bedroom dinsu sam batabi takan kurarda tadebo nana bah tana gefe tanata charting fadawa kan bed tayi cikin kuka mimi tafara magana da fillanci gamida hausa harda turanci tana cewa meyasa zakayimin haka sam bakasan halin mahaifina bane dole nakoma seyamin aurennan nikuma banason ya bassam dinnan ya mujaheed nakeso kumashi zan aura ni kuka take me tsuma guciya, zuwa lokacin nana tagama firgicewa jin mimi na yarenda bata san ta iyashiba bakaramin tsorata tayiba tamike tayi wane da mugun gudu saboda ba makawa tasawa zuciyanta meenal aljanune suka shigetaπŸ˜‚πŸ˜‚ ....

TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: πŸ€πŸ’žπŸ€πŸ’ž
RABON KWADO....
BOOK 3
πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


NA NANA BMB.
🀍❀️🀍❀️
page 10-11
Sebayan 'yan mintuna dasuka shude tukunnah ummi tasauko fuskarta daukeda fara ah tunkan tazauna meenal ta cinmata tana cewa ummi meya faru ne don allah kigayamin,ummi tayi murmushi takalli bassam tace kaje kasanarwa da family you munada manyan baki a gidannan,shima haka yatashi cikeda mamaki yafice, meenal takara rike mata hannu tace suwaye zasuzo ummi?kigayamin,itadae kallonta kawae take tana zuba murmushi tace bakine zasuzo mana kuje ma kubada oder irin girkin daza a fara yanzun kibar komae se idan sunzo zaki ga komae, itadae meenal addu ah kawae take allah yasa tunaninta yazamo gaskiya,tashi tayi don cika umarnin na ummi,
Tafiya tayi tafiya su muhammad bakaramin gudu suka shararaba kafin su iso cikin garin yola,mimi itace take musu jagoran tafiya ayanzu har suka iso GIDAN FULANI,anan tunanin kowa yasoma zama abin mamaki da aljabi mimi dakanta tafito tayiwa securities magana sannan aka bude musu gate suka wuce, zuwa gate na biyu anan aka bincikesu tas sannan sannan suka wuce bakin kowa asake da mamaki suketabin gidan da kallo, har parking space takaesu suka aje motan nasu sedae kowa yakasa fitowa acikin motar se mimi kadae data fito cike da farin ciki dajin dadi ko ina takebi da ido kobakomae tayi missing gidansu matuka gaya, muhammad ne yafara fitowa yazo gurin mimi zeyi mata magana ashe mujaheed yafito shima cikin jin haushi yace waekae meyake faruwane wannan wani irin gidane ko ince gari donyafi karfin gida wannan mezamuyi anan? muhammad yay murmushi batareda ya tanka masaba haka mimi adae dae time din bassam yafito daga bangarensu nasu mimi yanata balbalin bala ei da alamu shida hasana ne, cikin tsatstsan farin ciki mimi takwala masa kira,YA BASSAM! koda bassam yaji wannan kiran seya tsaya cak kamar baze waigowaba sekuma yajuyo ahankali yadora idanunsa akansu yakasa tantance wadda yake gani saboda 'yar tazararsu hakanne yasashi tunkaraso itama mimi tanufeshi harda gudunta, tana karasawa tarike masa hannu da yakuwa rintse idanunsa yaname cewa Oh! allah my meems gizo kuma kika farayimin yanzu,cikin dariya mimi tace bagizo nake makaba nice mimice take maka magana kabude idanunka ka ganni dakyau,cikin firgici bassam kuwa yaware idanunsa akanta don bashakka wannan muryar ta kalbinshi ce ba tantama dafe zuciyansa yayi kawae yaja baya yaname kallonta cikeda da rashin fahimta ko zurfafa tunaninsa yakasa, tsoro sosae yashigesa tace ya bassam shin kundrna tarbar bakone yanzu agidannan cikin in ina bassam yace bari nakirasu jiki nabari yajuya yana waigen mimi don atunaninshi wannan anya ba aljana bace mekama da mimi saboda yanzu yagadae yabarsu agida yafito,
Ganin hakanne yasasu daddy fitowa daga cikin mota dasu auntie al ummar data soma fitowa daga cikin gidanne yakara daure musu kae tako ina mutanene suke bullowa,
Mimi asanda tayi arba da ummi ya ilahil alamin! cikin wani irin gudu mimi tanufeta taje ta daneta btasan tafara kukan farin ciki bama, I MISS U I MISS U I MISS U I MISS U!ummi ashe darabon nakara sakaki a idanuna ummi nayi kewanki sosae ummi,cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa ummi tayiwa mimi kyakkyawar runguma tana zubar da hawayen jin dadi tana zuba addu ah ga ubangini daya dawo mata da diyarta lpy,kowa TV yamaidasu agurin nan, adae dae lokacin hasana tafito da meenal bassam yariko hannun twins,zuwa lokacin mamakin bassam yagama karewa kallon meenal kawae yake,asanda mimi tadago kuwa suka hada ido da meenal jiki nabari tasaki ummi taikanta tarukumkumeta tana ya allah meenal ashe darabon zamu gana, wannan abun kamar a mafarki ya allah kaene kadae kasan nufinka dakayi haka, meenal kallonta take tanata yashe baki yaki rufuwa addu arta ta amsu shikenan tarabu da gallababben auren nan na mimi zata koma gida duka azuciyanta take wannan tunanin,cikin farin ciki tace Oh allah abin godiya shin kina ina kekuwa duk wannan lokacin?mimi tasaki murmushi tarike mata hannu suka nufi inda su muhammad suke tsaye sudukansu,wayyo ay meenal wata fincika tayiwa hanunta saura kadan tayarda mimi akasa cikin gudunta nabara tafellah, tana kwalawa yayan nata kira YA MUHAMMAD! muryanta kuwa gaba daya seda taratsa ilahirin jikin sa ya lumshe idanunsa yaushe rabon duniya da ayyare dayaji muryar sweetiansa, cikin tsananin farin ciki muhammad yasoma zubawa allah godiya seda takusa karasowa kuwa ya isa gareta cak yacafe abarsa sama yana juyata cikin nishadin dabesan yanayibama,(da alamu yamanta dasu daddy) meenal tana dariya ahankali yasauketa takarasa fadowa jikinshi yay mata kyakkyawan rumguma kuwa sosae taji yadda yake sauke ajiyan zuciya, idanun jama ah kamar ze fado kansu don sun burge kowa dake gurin,sunkuyawa yayi yasoma yimata rada akunne yana cewa sweetie haka kika koma masha allah!cikin jin kunya tace ya muhammd haka ka koma kaema gaba daya kasauyamin,yasaki 'yar karamar dariya yace bawani zaki wayance kinji nace kingirma koh kema irin ta yaya ta yaya kin girma kin fara....Toshe masa baki meenal tayi tana rintse idonta don kunya tana cewa pls kar ka fada wlh bangima bama ni,muhamma yashagala da kallonta ma baduka abinda tafada ba yaji yana mamakin ganin meenal dinshi yadda takoma,daddy ne yakaraso yace oh muhammad bazaka sakar min 'ya mugaisabane? cikin mamaki meenal tadago tana tana cewa lah daddy harda kae akazo tarike masa hannu atime din taga mujaheed yana tsaye kamar gunki,tasaki kara tai kansa tana cewa ya mujaheed harda kae dama ay ban gankabah, alokacin kuma nana takaraso don tagaji dashan mamakin haka cikin rudu tariko ta tana cewa meenal! habawa wani tsalle tayi ta dafe nana saura kadan su fadi tana cewa yaya haka kika dawo ya allah kowa ya sauyamin asannan tahango su mummy dasu inna tace oh allah farin ciki kasheni don murna daya bayan daya meenal taje tana rumgumesu saboda tsananin farin cikin datake ciki bata kula da yanayin da auntie tashigaba sakamakon mugun gamo datayi,haka muhammad suman tsaye yayi ganin wadda take tunkarosa, ummi ce fuskarta dauke da fara ah tamaraso gurin muhammad, tace ikon allah kenan kaene wanda meenal kullum take ambato a cikin baccinta,tabbas bakawa yanzu yatabbatar da wannan auntie safiyya ce cikin firgici yace auntie safiyya!dama kina raye? itama cikin kidama tarike masa hannu tace muhammmad menaji ka ambata yanzu? lips dinsa yana kar karwa idonsa tafda kwalla yace auntie safiyya dama kina raye? Ya allah jikin ummi yana bari tace wlh ba ita bace muhammad ba safiyya bace 'yar uwartace ni sosae tarikesa tasaki kuka tace na rokeka tana ina ina take safiyya 'yar uwatace,tunranda nafara ganin meenal nasan ba mimi bace nayishiru dabakinane saboda wannan tunanin danakeyi kuma gashi yazamo gaskiya tabbas bakawa itace tahaifi meenal tana ina dukda kullum ina kuka idan natuna da 'yata mimi bansan tana cikin wani haliba bansan waca irin rayuwa takeba haka na hakura sabod jikina yana bani nakusa ganin 'yar uwata safiyya!tana ina kagayamin tana maganar tana girgizashi shikuwa muhammd kamar dolo haka yasau baki yana kallonta,
A time din motocin abbansu yasawo kae cikin gidan kae tsaye yafito don yasan ba lafiyaba,ganin muhamma d bashida niyyar tanka mata yasata sakinsa tanufi gurin meenal, to me karatu lamarin Dr se addu ah gaba daya tanemi kuka tarasa tadafe zuciyanta cikin girgiza kae tace impossibls baze yiwuba cikin kidima takara maimata BAZE YIWUBA! taya hakan zata kasance sosae jikinta yake kar karwa tana fiddo maganaeπŸ˜‚πŸ˜‚ su mummy dukse suka zuba mata idanu ganin tana shirin ficewa a hayyacinta,
Cikin kuka ummi tarike meenal tace meenal narokeki kigayamin ina mahaifiyarki take? cikin jin tausayi meenal tace ummi lpy kike kuka?girgiza mata kae tayi tace meenal ina mahaifiyaki take? hannunta meenal takama suka nufi inda auntie take tsaye....




TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: πŸ€πŸ’žπŸ€πŸ’ž
RABON KWADO....

BOOK 3
πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


NA NANA BMB.
🀍❀️🀍❀️
page 12- 13
Suna tun kararta tana jadabaya cikin firgici numfashinta yan shirin daukewa saboda tsoro tana girgiza kae tana cewa baze yiwuba impossible meyake shirin faruwane? dakkyar take iya fusgo numfashinta motan data cikaro da itane ta baya yasata tsayawa taname dafe zuciyanta,
Cikin tsananin mamaki meenal tariketa tana cewa auntie lpy meyake faruwa dake haka?Ummi batabi takan yanayin da auntie tashigaba saboda itama a kidime take hannunta zata rike aikuwa tafasa wata irin kara taja gefe, cikin zubar hawaye ummi tace mekikeyi haka ina mahaifiyarta take kugayamin don Allah,jiki asan yaye meenal tace Ummi, itace mahaifiyata fah! mekike tunani akanta meyake faruwa? naga auntie kamar bata cikin hayyacinta,
Da mamaki Ummi take kallon meenal,tace itace mahaifiyarki fah kikace!meenal tadaga mata kai cike da mamaki,sam Ummi batasan sanda ta cakumi auntie bah cikin kuru kuru da idanu tace, bazan yardaba karyane,wlh bagaskiya bane sekin fadamin inda 'yar uwata take bake kika haifetaba karya kikeyi sekun gayamin gaskiya yau, saboda meenal jini nace ita zancenku karyane cikin hargowa take magana da fitar hayyaci tuni auntie tadade da sumewa, tayi yaraf kan mota din amma dukda haka Ummi jijjigata take tana cewa karya kikeyi kitashi sekin gayamin gaskiya zan kyaleki,
Kuka meenal tafashe dashi jin wani batu daya daure mata kae, alokacin abbansu yakaraso, inda Ummi taketa faman yagulan auntie yasoma kokarin janyeta daga jikinta, sedae bakaramin riko tayiwa Dr bah πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„, cincin karfinsa yasa ya bambare hannunta ajikin auntie yana gama janyeta kuwa tafi jikinshi ba alamun numfashi atare da ita,
Gaba daya mutanen gurin nan mamaki da al ajabi ne suka hanasu koda motsi bare suyi yunkurin temakon auntie, seda abbansu yayi magana tukunna kowa yayi tamaza kuma, akazo aka tattaro auntie akayi cikin gida,
TOme karatu gidan fulani ya yamutse.
Cikin dan kankanin lokaci aka hada babban meeting kowa ya hallara, mujaheed kuwa dole yabaka tausayi idan kakalli fuskansa saboda halinda yashiga, meenal da mimi su akasaka agaba kowa yana furta albarkacin bakinshi akansu, Ummi tana jikin hajiya mahaifiyarsu inbanda kuka babu abinda takeyi kankameta,
Auntie kuwa koda Dr dinsu yadubata yace babu wani matsala tsananin firgitane datayi,amma zata iya farkawa akowani lokaci,
Cikin wani wani irin yanayi mimi ta tashi tazaiyano duka abinda yafaru, kowa se salati da sallallami ana zubawa meenal odanu, ita kuwa tayi sukui da ita azaune se aikin raba idanu,
Seda ta kammala tukunna, aka nemi jin tabakin mahaifin na meenal wato daddy,
Yakuwa mike yasoma zaiyanomusu abinda yasha kansu da mamaki zuwa haduwarshi da safiyya irin abinda take fiskanta gurin imam dasakin daya mata dakuma zaman datayi agidanshi harzuwa lokacinda allah yay mata rasuwa sedae bata taba fada masa inda danginta sukeba tace ita marainiyace wannan dalilinne yasa yarike meenal amatsayin 'yar cikinsa saboda kada tafuskanci halin rayuwa,
Sosae muhammad yakejin tsananin tausayin meenal azuciyansa saboda dole yasan zata shiga cikin mawuyacin hali dawannan bakon al amarin datakeji,
Sosae ta kankame mimi tana kuka metsuma zuciyan mumini tamkar numfashinta ze dauke tunowa da irin abubiwan da auntie keyi mata, nana ma hawaye kawae take sharewa saboda tausayinda meenal tabata,
Haka ummi tamkar zatayi bori tana cewa wlh safiyya bata rasuba bazan yardaba wlh data rasu datuni bana duniyar nan nima su sukasan inda suka kaita bazan yardaba ace tamutu,
Cikin wani irin yanayi yaya babba tamike tasoma ibar albarka,
Haba koda naji ashe wannan yarinyar ba jikatace bace bajinina vace dole tayimin ibar albarkar datayi awashegarin data dawo gidannan ashe 'yar gidan sallamammiyace dole zatayi abinda yafi haka, badole safiyya taga karshenta arayuwaba ay wlh dama bazata taba samun farin cikiba,
Jin hakanne yasa hajiya takama Ummi sukabar gurin su daddy kallon mamaki kawae suke wa yaya babba jin furucinda takeyi akan safiyya, seda gwaggo ta tasoma tasoma sauke mata ruwan bala ei tayi shiru,
To kowa da abinda yake furtawa agurin nan shikuwa mujaheed ko kalma daya takasa fitowa daga bakinsa saboda irin zafin dayakejin zuciyansa tanayi masa su meenal kawae yake kallo, abbansu meeanal cikin farin ciki ya rumgume daddy yana godiya ga ubangiji,
Seda aka kira sallan magrib taro yawatse domin yin sallah....




TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: πŸ€πŸ’žπŸ€πŸ’ž
RABON KWADO....
BOOK 3
πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
NA NANA BMB.
🀍❀️🀍❀️
page 9
GIDAN FULANI
Menalce kwance adakinta tana kan gado hawayene kawae yake bimata fuska dukta rame saboda ta tashi hankalinta sedae jikinta yayi suwae har kyalli yake da gashinta sunsha gyara fuskarnan tayi suwait tayi kyau sosae tana cikin wannan halinne aka buga mata kofa tanadaga kwancen tace "enter" hasana ta turo kofan tashigo tazauna gefenta taname cewa yayarmu banason kullum ina ganinki cikin wannan halin kinji yau saura 'yan kwanaki yakamata ki fawwalawa allah komae meenal bata tankataba don ita seyanzun take bakin cikin yin shiru datayi tunfarko datayi bayani komae dahaka bata faruba hankalinta gaba daya yana gidansu, tana daga kwancen tace hasana inason muyi magana nidaku baki daya harda abbanmu idan yadawo kije kihayawa ummi,hasana cikin fargaba tace wani magana yaya badae cewa zakiyi kinfasa aurenba cikin fushi meenal tace ina ruwanki da abinda zan fada kije kigaya mata, jiki a sabule hasana tace to ay itace ta turoni nakiraki masu kunshi suna jiranki tundazu tace kifito yanzu, kafin takarasa magana meenal tamike tanufi hanyar fita hasana tace pls yayarmu kigyara fuskarki kada kifito ahaka kinji, fita tayi tabata guri ita kuwa dama ta kudurce aranta komene zefaru sedae yafaru don tabbassa kafin a daura aurennan setabar gidannan,
Koda hasana zasanarwa ummi sakon meenal setayi murmmushi tace aydama nayi shirune inji ta ina gaskiya zatayi halinta dole nasan taga za ayi auren nan tafadi gaskiyar al amari irin wannna kudira ta ubangiji, cike da mamaki hasana tace bangane ummi kinsan abinda zata fadane meke faruwane wae, ummi takalleta tace anjima kibari zakiji komae ay dakanta zatayiwa kowa bayani,
Kunshi tsan tsararre ake yiwa meenal nagani nafada sedae sam hankalinta baya kansu, wayan ummi ce tashiga ruri wayar na hannun hasana tana daga kwance tace ummi ana kiranki da bakuwan number, waca number ce? hasana takaranto number din meenal koda taji number dinda hasana ta karanto zuciyanta tai wani irin harbawa jin an ambaci number irin tata hankalinta inyay dubu yatashi ummi harta share sekuma tace kawomin wayar koda ta amsa kiran ya tsinke se ta aje wayan abinta, allah allah meenal take acire mata kunshin ta dauki wayar umman nasu gashi sun tsaya mata fi ili turaruka kala kala akewa kunshin tana jikuwa kamar tashakesu πŸ˜„
bayan tafitone awanka tazauna gaban mirror tana kallon kanta ita har mamakin kanta take yadda takoma ayanzun ga girmann data kara seda karewa kanta kallo tashirya sboda sauri ko dankwali bata dauraba tarikoshi ahannu tafito, sam bata kulada bassam ba a parlour sejitae yace Wooow my meems narasa wani irin kyaune wannan kike karawa haka tubar kallah batareda tajuyoba tasoma tura baki tabude dankwalin nata tarufe kanta, kallonta kawae yake da mamaki shi yarasa meyasa meenal takeyi masa haka yanzu insuna cikin jama ah tayita zuba masa surutu amma idan sukadae suka kasance ko maganar 'yan mintuna bata bari suyi tunda tadawo,murmushi yayi azuciyansa yana cewa komadae meye kinkusa zama tawa komae yazo karshe ay,
{KOMAE YAZO KARSHE KUWA TUNDA GAME ITANAN ZUWA!}
tana shirin wucewa ne tajiyo rurin wayan ummin taso ashema ta nan parlour din dasauri kuwa tajuyo zuwa inda take alokacin kuma ummi tasauko itama, tace wake kirana? koda meenal taji haka jikinta a sabule tadauko wayan takawo mata ganin nunbern din nan dae tadazu yasata daga wayan tana me neman guri tazauna, tome karatu koda ummi taji me magana tacikin wayan tamike tsaye cikin bakon yanayi da al ajabi tace MIMI! juyowa ummi tayi takalli meenal dakyau kawae tahaye sama, jiki nabari meenal tamike zata biza bassam yace no mimi kada kiyi haka, damamaki takallesa jin yakirata da mimi abinda bata tabajin yayiba sedae yace meems, dole takoma tazauna jiki bakwari....


TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: πŸ€πŸ’žπŸ€πŸ’ž
RABON KWADO....


BOOK 3


πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


NA NANA BMB.
🀍❀️🀍❀️

page 14
Tsegumi kuwa kowa da abinda yake furtawa akan su mimi, masauki na musamman aka bawa su daddy abinci da abinsha kala kala sewanda suka zaba ga wata lafiyayyar fura da nono nata zuba kamshin ayaba da kwakwa cikin kwarya an aje musu tanata nason sanyi,seda kowa ya kimtsa tukunna aka azauna aka soma maida magana kuma,muhammad yana sane da halinda mujaheed yashiga amma seya shareshi betanka masaba abincinma kasa ciyayi dayawa fuskarnan tamau da ita,
Hakima Dr kuwa har kawo i wannan lokaci taki farkawa tana room dinda aka shimfideta ita kadae
meenal tana jikin mummy takoma abar tausayi haryanzu kuka take idanunta duk sun kumbure don bakaramin girgiza tayiba wae daddy ba mahaifinta bane ganin abin take kamar a drama sunyi rarrashin harsun gaji takiyin shiru, su daddyn kuwa abbansu mimi ne da alhj aliyu mahaifinsu ummi, se kakan bassam sune sukaje suka samesu daddy suka fahimtar dasu tun silsila abinda yafaru da safiyya,
Daddy kuwa ya girgiza dajin labarin safiyya,azuciyansa yake magana.lallae seyanzu ya yarda da wannan kalmar ta bahaushe dayake cewa "RABON KWADO... Baya hawa sama" donkoyaje zefado yasameshi, tabbas imam kayi asarar rayuwarka dakayiwa safiyyar irin wannan sakayyar lallae kayi kuskure kuwa wanda ahalin yanzu nasan kana kan gani, Allah me iko kenan meyanda yaso dabayinsa,
Koda yakara gwada musu hoton safiyya anan suka kara gasgata al amarin sede jikinsu duk yay sanyi saboda safiyya bata raye, muhammad mamakine yahanashi furta komae yana tunanin to a ina daddy yasami hoton auntie safiyya? sosae kanshi yakulle akan wannan al amari,
Ummi tana kwance kusada hajiya abin duniya ya isheta inbanda aikin kuka babu abinda takeyi dakyar suhajiya suka rarrasheta domin ta dage setaje tasamu auntie ay ita tasan inda
'yar uwarta take, su hasana da twins suna gurinsu mummy da mimi wadda zuciyanta take cike da fargaba ganin yanayin gogan nata datayi babu annuri,


Sewajan 9 da wani abu su muhammad suka shiga inda aka sauki su mummy yanata zalkin ganin amaryarsa,sam barka kuwa yahangeta jikin mummy anata rarrashi, soyake kawae ya rarrashi abarsa amma babu hali tana gun mummy,seda suka zauna tukunna mummy tace muhammad gara dakuka shigo yanzun munkasa shawo kan meenal, kazo kaji da ita don Allah, muhammad yay murmushi yataso yazauna gefenta yana cewa haba sweetie meyasa zakiyita wahalar dasu mummy ki fawwalawa allah komae kinji duk yadda kikaga bawa haka allah yatsara masa, toke seki godewa allah kinji bakuka zakiyiba kada kuma ki kuskura kisawa zuciyanki maraeniyace ke ko kadan karki fara,


Zuwa lokacin kukan meenal ya tsananta yanzu dagaskendae wanda taji ana ambata shine mahaifinta meyasa aka boye mata kam,koda muhammad yadagota rintse idanunta tayi gam tana shahshsekar kuka, itadae mummy tasamu tamike tashiga toilet don mararta acike take, hakanne yabawa muhammad damar janye meenal daga room din, mimi tayi tsamo da ita don inda take mujaheed be kallaba hasana baki sake kuwa take kallon ikon rabbi, takasa dena kallon meenal yanzu dama bada yayarsu suke rayuwaba wannan wani irin abin mamakine haka?


TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: πŸ€πŸ’žπŸ€πŸ’ž
RABON KWADO....


BOOK 3


πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


NA NANA BMB.
🀍❀️🀍❀️


page 15 - 16
Muhammad da meenal suna zaune kan steps, ba fita sukayi ba,kunshin hannun ta yaketa shafawa don bakara min tafiya da imanin sa yayi bah, ita kuwa inbanda shashe kan kuka babu abin da takeyi,gajiya yayi da kukan nata ya kwanto da ita kan shoulder dinsa, yana mata kalami masu dadi yana rarrashin ta, se a lokacin ta dago tazuba masa dara daran idanunta cikin kuka tace.


"Ya muhammad why! why! meyasa haka zata kasance dani? koda wasa ban taba tsamma nin hakaba a rayuwata wlh yanzun nadena ganin laifin

Please Login or Register in order to submit comment