Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taso tafi uwarta wulakancima sosae balaraban taso abbah sulaiman yabar asiya tafita kasar waje tayi karatu ammah yahana saboda dokane haka tsarinmu yake sosae take lalata asiya kome tayi bata ganin laifinta ganin tana shirin lalata masa tarbiyyar yarinyane yasashi yimata aure tunkan tagama karatuba,
To alokacinda manyan gidanmu suka tsunduma harkar siyasa lokacin kuma farin cikinmu yasoma tangarda saboda tashin hankalinda muka shiga kullum cikin kawoma hari ake mussam dani da 'yar uwata wannan dalilinne yasa aka zuba matakan tsaro agidanmu ake bamu tsaro dama islamiyyanmu tana cikin gidanmu sedae karatun bokone muke fita yowa alokacinda mukayi saukar alkur ani megirmane mahaifinmu yayimana kyautar gwal saitinsa kuwa daban yasa aka kera masa su donya bamu asaukarmu iri dayane masu kyau munyi matukar farin ciki sosae mahaifinmu yana dasawa da safiyya sosae saboda hakurinta sam batada hayaniya sabanin nida nake 'yar hayaniya nima banida hakuri kome akae mana sena narama mana koda kuwa mahaifiyata akawa wannan dalilinne yasa bama shiri sosae dashi, tunda muka taso muka zama 'yan mata kowa a family yasoma samari suka yinkuro domin aurenmu to abudul halim marigayi dukya buge ragowan masoyan na safiyya saboda yana mata wani irin so naban mamaki tamkar ze mutu akanta sedae kash ita kuma 'yar uwata bata sonsa ko kadan nayi nayi alokacin tafadamin wanda takeso amma taki abu kamar wasa har lokacinda muka gama makaranta mahaifinmu yatashi aurar damu dama yariga yazaba mana mazajen aure wato 'yan biyun yaya babba sedae sam alokacin 'yar uwata tayi abinda yabawa kowa mamaki don tace batason zabin mahaifinnamu dukda beji abinda abinda tayiba yace to shikenan tafadi wanda takeso acikin family din shi ze aura mata nanmadae taki magana harseda ran mahaifinmu yabaci tukunna tukunna tace ai ba ah cikin family yakeba aranar babanmu yataba dukan safiyya saboda takaishi karshe yakumace maganar biki babu fashi abdul halim zata aura mari gayi seda kuma yatitseyeta tafadi wanda takeso tashaida masa cewar imam takeso babban drivern gidanmu kowani gari mukasiyi kaya imam ke kawo mana allah yazubawa imam kyaune naban mamaki shiyasa 'yar uwata tamutu akan sonsa sunkwashi shekaru suna soyayya amma bawanda yasani sewannan lokaci data bayyana, abin yamatukar tunzura mahaifinmu aranar yakira imam yaymasa zagin cinmutumci ya muzan tashi sannan yakore daga aiki, ranar haukane 'yar uwata kawae batayiba kullum cikin kuka muke nida ita ina bata hakuri ina nusar da ita tayi hakuri taiwa iyayenta biyayya ta auri abdul halim din tunda yana matukar kaunarta mahaifiyarmu tayi rarrashin harta gaji sam idanun 'yar uwata sun rufe taki saurarar kowa tadena cidasha sedai kuka gashi anata shirin biki wata rana da asuba tasoma aman jini cikin gaggawa aka kira doctor dinmu yazo yadubata asanan yashaidawa mahaifinmu cewar abawa safiyya abinda takeso inba hakaba zuciyarta nabarazanar bugawa bada jumawaba don tana cikin matsala ran mahaifinmu yay matukar baci yakule yace sedae to ta mutu kuwa amma baze fasa aurenba
To mahaifiyarsuce tace sam baza ah yi hakaba yakashe 'yarsa dakansa tunda baharamun bane to yabata wanda takeso dolenshi kuwa ya ilahi mahaifinmu yazuciya iya zuciya aranar yakira imamu da mahaifiyarsa aka daura auren da imam din yasa aka debo komae nata yaci to tabi mijinta daga wanaan rana yacireta acikin family din mu ita ba yarsa bace mahaifiyar imamu itace uwarta itace ubbanta, koda abdul halim yasamu labarin abinda yake faruwa yabazamo cikin tashin hankali yazo cikin kuka yatsugunna agaban safiyya yana rokonta tayi hakuri awarware auren ya aureta inba hakaba wlh mutuwa zeyi ta temaka masa yana matukar kaunarta kada tayi masa haka 'yar uwata sam taki saurarar sa tariga tayi nisa banifa kaf 'yan gidanmu ranar seda mukaji haushinta agaban kowa agidan yake mata magiya amma ko kallonsa takiyi haka dan uwansa mahaifinku yazo yanata yimata magiya amma sam taki saurarar kowa dama mahaifiyarmh ko fitowaba bataiba tana ciki tana nata kukan itama hannunta yadamka ahannun mahaifiyar imam yace gatanan yasallama musu ita dagayau sosae yakara ciwa imam mutumci dacin zarafi saboda aganinshi shine ya hirewa 'yarsa kunne bayan kuma yarigada yasan dokar gidan ba ah taba shiga tashin hankalimda muka shigaba awannan rana don 'yar uwata suna tafiya abdul halim ya yanke jiki yafadi ya babba kuka take tana sambatu tana tsinewa safiyya tana mata mugun fata bayan kwana hudu ta tafiyar su safiyya allah yaywa abdul halim cikawa ya rasu saida yaya babba tazauce malamae aka kira suka tsaya akanta tanata kururuwan setaje takashe takashe safiyya itama itama tabar duniya daga masu zagin safiyya se masu yimata fatan tsiya haka gidan fulani yadauka harseda wannan abun yashafi shiyasar mahaifinmu anata yamadidi agari cewar 'yarsa tagudu tai aure mahaifiyar su babanmu inno sam bata iya jure tashin hankali yanzu zata rude bare wannan babban al alamari ranar ukun abdul halim ita inno taraso, kowa yashiga tashin hankali mahaifinmu kuka yake kamar karamin yaro abinda yakara bawa kowa mamaki sam ba safiyya babu alamunta....


TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’–
RABON KWADO....
BOOK 2


NA NANA BMB


page 39
Se aranar addu ar bakwae sega 'yar uwata kamar anjehota ko hijab babu cikin tashin hankali ashe batasan abinda yake faruwaba shiyasa bata zoba koda mahaifinmu yay arba da ita aranar seda yay mata duka gami da mugun fata sosae yake furuci marasa dadi akanta saboda tsananin fushin da yakeyi da ita muna ciki muna zaman jugum jugum ajikina naji 'yar uwata ta iso nabazama nafito naga halinda take ciki hankalina yay matukar tashi mahaifinmu yakuma janyeni yahanani zuwa inda take inaji inagani natafi nabarta yasa aka fita da ita daga gidan yakuma ce koda wasa securities suka kuma barinta tashigo to seya koresu a aiki,
Tundaga wannan rana haka muka cigaba da rayuwa farin cikinmu yayi karanci musamma ma madaeni ga gulmar marmu da akeyi agidan na abinda 'yar uwata tayi kullum cikin zubar hawaye nake bayan rasuwarsu akayi bikina nida mahaifinku anyi taro naban mamaki alokacinne 'yar uwata takuma zuwa sedae koda muka ganta seda muka tsorata yadda takoma tarame ta kojale nida mahaifiyata munyi kuka mahaifinmu ko gezau yahana abarta tashigo cikin gidannan sede hange daga nesa haka ta tafi tana kuka mecin rae tundaga wannan tafiyar tata rayuwata tashiga matsala narasa farin ciki da walwala ahaka nacigaba da rayuwata dukda mahaifiyarmu itama tana damuwa da 'yar uwata sedae bayadda zatayi awata rana 'yar uwata takuma dawowa nanma dae aka hanata shiga gidan tayi musu magiyan harta gaji tana kuka haka takoma sebayan kwana uku tadawo da letters tace abamu,
Koda aka kaewa mahaifinmu wasikar cayay baze amsaba se mahaifiyarmuce ta ansa takaranta abinda takunsa dukanmu seda zuciyarmu ta raunana harda mahaifinmu damukaji halinda take ciki tayi bari har sau biyu kuma ahalin yanzu mijinta zetafi da ita legos abinda tayi mana kuma mutemaka muyafe mata koda inta mutu tasami rahama ta ubangiji awanan lokacin hawan jini yakamani shine naketa fama dashi haryanzu nakasa samun sauki alokacin yayi tsanani hartakae ina kasa tabuka komae dakaena Dr yace amagance damuwata itace samun lpyta mahaifina yatambayine shin menake so? nashaida musu cewar 'yar uwata sutemaka su dawo da ita gida inringa ganinta barin farin cikinace ita sutemaka suyafe mata haka tunda tagane kuskurenta kowama yana kuskure ayafe masa jikin abbanmu alokacin yay sanyi alokacinne shine governor nagarinnan hajiyama taringa lallaminsa daban hakuri sannan yasa aka tafi legos neman safiyya sedae kuma babu ita ba dalilinta anyi neman iya nema basacan koda aka tambayi mahaifiyar imam itama tace suna legos tunda suka tafi basuzo gidaba haka akaci nemansu har gaji haka nacigaba darayuwa yau da lpy gobe babu har allah ya azurzani da haihuwarku kullum da tunanin 'yar uwata nake kwana nake yini bamu sake jin labarinta har kawo i wannan lokaci da ciwona yamotsa abbanku yahadu da imamu ashe yasaki 'yar uwata besan inda takeba shima cikin kuka ummi takarashe maganar haka su meenal suma sun kankameta suna kuka dakyar tayi jarumtar rarrashinsu sosae meenal tashiga kogin tunani wanda batasan randa ze kareba dolane ayanzu tafito tafadi gaskiya koma meze faru yafaru,
CI GABAN LABARI
Tome karatu yau friday takama kuma ranar dawowar muhammad daga China mujaheed da su mummy dasu inna duka sunzo domin tarbar shalelen nasu....


TAKU A KULLUM NANA BMB


08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’–
RABON KWADO....
BOOK 2


NA NANA BMB


page 40
Tunda gari yawaye ake girki da soye soye kala kala su mardy dama sammakon zuwa akayi don tarbar masoyi πŸ˜„harda nadiya sedae mimi tayi lake da ita kamar wadda akacewa yaune ranar mutuwarki sam batada kuzari ganin yanayinne nata yasa daddy cewa meenal meke damunkine naga baka murna sam da dawowar yayan naki mummy tace nima dae abinda nagani kenan shiyanacan yana allah allah yadawo yaganta ita ko ajikinta itadae mimi murmushine nata daddy yana kulada yadda mimi take shigewa mujaheed haka shima yake mata to sedae yana daurewane baya nunawa,daddy da daddyn mujaheed ne suka tafi airport din se mujaheed dake driven dinsu,
Koda sukayi harba da muhammad suduka se suka sau baki suna kallon shi kamar shashashu harya karaso garesu cikin tafiyarsa nakasaeta sumar kannan nasa tanata zuba kyalli skin dinshi kamar zaka taba jini yafito yaji hutu yay kubul bul dashi dariya sosae yaringayi harda rike ciki ganin irin kallonda suke masa sannan yace tunda babu wanda zeyi welcoming dina mutafi gida se a time din mujaheed yasaki ihu harda tsallensa ya rungumesa yana zuba masa shakiyancinsa dagowa yayi yanadan yamutsa fuska yace yana gannka kae kadae ina sirikar tamu muhammad yakaemasa duka yazille shige mota yana dariya gaisawa sukayi dasu daddy suma sunata zolayansa suka shiga mota yabankawa mujaheed harara yace kada kadamu indae sirikace zamuje kataho da ita baseka damemuba, shidae mujaheed yay murmushi yaja motan sukatafi gida azuciyanshi yana cewa yau zakaji komae sha kuruminka,
Cikin tsananin farin ciki nana tafara tarbar yayan nata ta rungume tana cewa wayyo allah ha ya muhammad haka ka dawo sam hankalinshi baya kanta mimi kawae yazubawa idanu wadda tayi masa sannu dazuwa cikin sanyinta, tuni auntie ta hassala tace kinata zumudinshi bayanshi batake yake bama se alaokacin yadagota yana fara ah yace nana enyee girma yakaru haka aka zama manya dafatan nasameku lpy cikin jin kunya nana tasunkuyar dakanta yagaishe da auntie da mummy su mardy anata kwarkwasa da iyayi aka gaisa harda wani gift donneman suna gurin kakannin nasu yakarasa cikin jin dadi yana cewa oh baba ashe darabon zandawo nasameka nazaci zaka karasa ay kafin nadawo baba yace allah kahadamu da jikokin zamani se du ah ei to mujaheed ma yayi yakyaleni kaema saura kae muhammad yace hajiya inna kedama ay tamuce ba abinda zamuce sedae allah yaja kwana, daddy yace to seme donkayiwa inna ita kadae 'yan amin sun ansa hardashi kuma kakiyayeni shida mujaheed sukasa dariya baba yace barni dasu nine daedae dasu wlh mimi nagefe tazuba musu ido ta lula duniyar tunani daddy yace meenal zonan, jiki asanyaye tamike ta isa inda yake ta tsugunna yace menene yahadaki da yayanki?shiru ba amsa seda yakuma maemaita mata tambayar sannan tace babu komae dadd y kaenane yake saramin shiyasa sam muhammad bekara kallon inda takeba tunda tazauna seyanzu da daddy yake mata magana meenal nazaci idan muhammad yadawo zaki warware to sekuma naga kinfi takurama kifadamin gaskiyar abinda ke damunki, muhammad ne yace daddy ka kyaleta kawae ay bataso dawowata gidanba se alokacin tadago tana zubar hawaye koda taga irin hararan dayake zuba mata seta maida kanta kasa mujaheed yazo zekama mata hannu daddy cikin fada yace menene haka mujaheed koma gurinka kazauna shima jiki a sanyaye yakoma yazauna yana karayin mamakin daddy tafi daki meenal ki kwanta kihuta kinji tunda bakyason hayaniya ay zuciyan mimi kal da farin ciki tamike dasaurinta tahaura sama muhammad yabita da kallo yana murmushin mugunta bajuma sega yayan auntie shima da iyalansa 'ya'yansa 'yan mata sewani yauki ake ana yanga gurinsu muhammad hakan bakaramin bakanta ran mardy yayba suduka sukaci abinci aka koshi akayi hira nayaushe gamo, koda suka dawo daga sallan la asar mujaheed yajashi daki shikuma yasoma cirewa kayanshi ze shiga wanka mujaheed yace muhammad daddy inyay min wani abu kan meenal inayin mamaki sam bayason narabeta kuma gashi itace abar kaunata adum duniyar nan ita kadaece macen danakeso kuma nakefatan rayuwa da ita har abada tsayawa muhammad yay da daure towel dinda yake a kugu jin kalaman namujaheed yake suna dukan kunnensa....


TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’–
RABON KWADO....
BOOK 2


NA NANA BMB


page 41- 42
Tsaiwa ce ta gagari muhammad yanemi gefen bed yazauna yana kallon mujaheed yace shin mujaheed meenal tasan kana sontane?wani kallo mujaheed yay masa yana murmushi tunyaushe nawuce gurin soyayyafa mukeda meenal fiyeda yadda kake tsammani, cikin mamaki muhammad yace shin mujaheed yaushe duk akae hakan bansaniba meenal koda wasa bata taba gayaminba, mujaheed yace mun boye soyayyarmune ga kowa sekadawo zamu baiyanata sabida mahimmancin da kake dashi agurin meenal, muhammad ya jinjina kae yace muhammad baka ganin yanzu meenal bata daukeni abakin komaeba yanzu, gyara zama mujaheed yay yace inason ka gayamin dama pls muhammad meyasa kakewa meenal hakane yanzu? mikewa yay yashiga bathroom yana cewa ita zaka tambaya tabaka amsa yarufo kofa abinsa mujaheed yabisa da kallo,
Sakarwa kansa ruwa muhammad yay yadafa bango sosae ya lula duniyar tunani tabbas jin furucin mujaheed dayayi yanzu yakara tabbatarwa dakansa ba meenal bace wannan shin meyake faruwane haka wacece wannan ne? tabbas akwae babban al amarin dake faruwa shin ina meenal dinshi takene yasan baze yaudari zuciyansaba yana tsananin kaunar meenal amma dole yaboye nashi son saboda yadda ta daukeshi uwa daya uba daya yayanta dukda idan yayi shiru yasan ze cuci zuciyansa, yajima a ciki yana nemarwa kansa mafita dason gano gaskiya amma abin ya gagareshi haka yafito sam yarasa walwala dukda abokansu dasuka hallara sam hankalinshi baya gunsu,
Koda daddare bayan sallan ishah suna bedroom yanajin mujaheed yadda suke waya da mimi yashaida masa cewar su hadu da garden yana zaune mujaheed din yay wanka yashirya yafita, muhammad yanata zagaye dakin yarasa nutsuwa tunda mujaheed din yafita, kasa jurewa yayi shima yanufi garden din kallo daya yamusu yasan sunyi nisa a love amma kuma mimi tana hangoshi annurin fuskarta yadauke zujiyanta tafara lugude, yana karasowa yazauna gefenta yana kallonta yay smile yace mujaheed pls dan bamu guri muyi magana ta fahimta nida,mujaheed be kawo komaeba sema dadi dayaji don bayason abinda muhammad kewa mimi, fitsarine kawae mimi bataiba don tsoro wani irin gumine yasoma tsatstsafo mata mujaheed yana mikewa ta mike itama zata bishi ya rike mata hannu yadawo da ita mazauninta kuma yaki sakar mata hannu kanta akasa shima yana yimata kallon kurrillah yana nazartarta, meenal yakira sunanta, tayi masa shiru yakara kiran sunan nata muryanta narawa tace na am, dago ki kalleni mana mimi daurewa tayi tayi tamaza tadago sedae takasa kallon kwayar idanunsa menene a tsakaninki da mujaheed?tayi masa shiru, badake nakeba, yana sonane, ke kumafa?kanta a sunkuye tace inasonshi nima ina kaunarsa dayawa, muhammad ya jinjina kae yace good, ina ajiyata dana baki bafin natafi China?sosae yake ganin gumi yadda yake fimata wuya daga cikin gashinta saboda yadda yake magana ba alamun wasa afuskarsa, idanunta nazubar hawaye tace tananan,koda yaji haka seya saki murmushin mugunta yace maganar dakikace zaki gayaminfa sena idan nadawo ina saurarenki yanzu,mimi tadanyi shiru sannan tace dama maganar ya mujaheed ne zangaya maka muna soyayyane,ok yanzu ke kin iya soyayyane kinsan yadda take? dukda halinda mimi take ciki furucinsa seda yasa tasaki murmushi hakan kuwa yawa muhammad dadi yakara ganin wata shedar,batae tsammaniba taji yarike mata hannuwa yana murzawa cikin nashi cikin jin tsoro tadago tana kallonsa se sannan yaji yadda jikinta yake rawa, kasa jurewa kallonsa tayi tasunkuyar dakae tana hawaye, yasauke ajiyan zuciya yakara matse hannunta cikin kakkausar murya yace banason raininin hanakli zaki iya rainawa kowa hankali amma bandani kafin kowa yafahimci wacece ke inason yanzu kifadamin asalinki kifadamin abinda yake faruwa kuma shin ina kika kaemin meenal ditane kamar kowa yamakance kowa yaki fahimtar bake bace meenal banason muyi rigima dake yanzu kifadamin ko waceceke,mimi ji take kamar kasa tabude tashige ciki, murya tana rawa tace nice meen.....
yatsansa yadora akan bakinta yace karmuyi haka kada kiyimin gaddama wannan al amarin yadauremin kae, zakiyimin bayani tasauki ko kuwa,kukan da mimi takerikewa ne yakufce mata tamike zata ruga ya kuma fincikota ta dawo tazauna cikin shashhseka tace wae meyasa yaya kakemin haka kawae saboda nacanza kace bani bace mimi banason haka karabu dani, sosae muhammad ransa yabaci daganin raenin hankalinda ake shirin yimasa, kafansa yasa yatake mata yatsun kafarta tasaki kara cikin zare idanu yace shut off malama kifadamin gaskiya konayi miki abinda yafi haka, cikin dakiya mimi tashare hawayenta tace nice meenal! muhammad yay murmushi yace ok tunda kece meenal inason gobe kafin su daddy mujaheed sutafi agaban kowa ki shaida musu cewar kinason mujaheed da aure idan dae kina sonsa tokiyi haka gobe, cikin sauri taga masa ya jinjina kae gud gal tashi kishiga ciki semun hadu goben koh! da gudunta nabara mimi tae cikin gida yabita da kallon mamaki al amarin nan yana matukar daure masa kae zuciyansa a cunkushe yarasa meyasa kowa yaki fahimtar abinda yake faruwa ne....


TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’–
RABON KWADO....
BOOK 2


NA NANA BMB.




page 45
Abinda muhammad yace tayine tasa mujaheed yayi cewar yasanarwa su daddy yana sonta se aureta,mujaheed yayi mamaki dajin wannan furucin daga bakinta haka da wuri beyi mata musuba ya amsa mata zeyi domin baya shakkar tunkarar kowa indae akantane, to haka yadawo parlour yanata tunani yakasa aiwatarwa don kalamin yamasa nauyi kusada muhammad yakarasa yazauna yafada masa abinda mimi tace yakuwa saki kayatatccen murmushi yana kallon mujaheed yaname kara mamakin yadda idanuwan mujaheed suka rufe haka daya kasa fahimtar abinda yake faruwa koda yake kauna dole yamasa uzuri tarufe masa idanuwa, gyaran murya yay yace tome kazauna jira kaje ka aiwatarmana time yana tafiya,mujaheed yarike hannunsa yace pls muje karakani nagaya masa cikin shan kunu yace indae sedani ne to kafasa bama son abin kakeyi bah kenan,mujaheed gajiya yayi yatashi yanufi gurinsu daddy suna zaune da nashi daddyn sunata fira tunda ya tashi muhammad yake kallon ikon allah sosae yakejin zuciyansa tana dancing, koda ya karasa yazauna agabansu kamar me neman gafara yasunkuyar dakansa kasa zuciyansa tana wani irin bugu haka meenal shikawae tazubawa idanu,haka suma su daddy shi suka gubawa idanu ganin irin usmanda yayi agabansu cikin ladabk yace daddy dama inada maganane, kallon juna sukayi su daddy don basu san cikinsu dawa yakeba dagowa yay yakalli daddy sannan yakuma sunkuyar dakansa hakanne yasa yatabbar dashi yake,seya gyara zamansa yace to mujaheed ina saurarenka kaf dakin yadauki shiru kuwa aka zubawa mujaheed idanu, Dama maganace....Mujaheed yay shiru secan yakuma cewa dama maganace akan meenal daddy, tunda yaji ya ambaci meenal yarintse idanunsa cikin wani irin yanayi don yasan meze furta ayanzu,
Dama ina sontane daddy kuma itama tana sona iname rokonka daddy kabani auren meenal tazememin abokiyar rayuwa ta har abada,
Wani krin takaecine yacikawa auntie zuciya jitake kamar ta harbe mujaheed kallon kuma seya koma kan daddy ana tsumayin hukuncin daze zartar, muhammad jiyay kamaryashige huciyan daddy yaga wani hukunci zeyanke ne?bude idanunsa yayi sannan yay gyaran murya yace
Mujaheed!
Na am daddy
Mujaheed inason kasani yadda nadauki muhammad haka kake agurina babu bambamci komene ne kakeso agareni indae dayiwuwarsa to bashakka sena yimaka, to amma batu akan meenal inason daga yauma kasoma kokarin cireta azucinka saboda abinda kukeda muradi bame yiwuwa bane....


TO ME KARATU MUHADU A BOOK 3 INME DUKA YAKAEMU DONJIN YADDA ZATA KASANCE!

SHIN MEYASA DADDY YAHANA MUJAHEED AUREN MEENAL?

TAKU A KULLUM NANA BMB.


MASOYANA INA MIKA DUNBIN GAISUWATA AGAREKU DA GODIYA TA MUSAMMAN.


08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: πŸ’πŸ’–πŸ’πŸ’–
RABON KWADO....
BOOK 2


NA NANA BMB


page 43-44
Meenal ce kwance a kan bed tayi lamo inbanda tunani babu abinda takeyi abin duniya gaba daya ya isheta tarasa mafita kullum cikin damuwa take harta soma ramewa, tayj zurfi cikin tunaninta tajee ana knocking seda ta gyara kwanciyarta sannan tabada izinin shigowa, hasana tashigo dauke da cup ahannanunta tana murmushi tazauna gefenta tana cewa yayarmu tunda kika gama school damuwanki takaru kullum bakida sukuni kuma ummanmu tace ki kwantar da hankalinki akan aurennan naku keda ya bassam nasan bakya sonsa kawae kinawa abbanmu biyayyane kuma baze taba canza maganaba kinsani so kiyi hakuri kada kisa damuwa aranki tadameki ko bakomae ya bassam yana matukar kaunarki zakiji dadin zama dashi kema kuma nan gaba zaki soshi,
Hawaye meenal tafara don yanzu ba abinda tafi tsana samada ai mata maganar aurennan danasani kullum tanayinta dabata yimusu bayani tunfarko kota wani hali kuwa bazata bari ta auri ya bassam be kome zefaru sedae yafaru yayanta kawae yake fado mata arae tasan yanzu yadawo gida saboda bata taba bata a lissafintaba tunda yatafi,hannun hasana tariko tace hasana ina cikin wani hali bazaki ganeba nasa yadda zanyi da rayuwata, jikin hasana a sanyaye tace kiyi hakuri yayarmu ki fawwalawa allah komae tamika mata cup din tace gashi ummi tace kisha akae mata cup din,ran meenal yakara baci saboda bata kaunar irin abubuwan nan da ummi take bata tunda aurensu yakusa fuska adaure ta anshi abin cikin cup din tshanye tabata cup din, hasans tafito cike da tausayin yayar tasu kods tasauko tasami bassam azaune suna hira da twins da ummi cikin cukurkude fuska tanemi gu tazauna cikin ko in kula yace ke jeki kiramin yayarku, hasana ta tabe baki itama tace yayarmu tayi bacci,
Bai kukalataba yadauka wayansa yacilla mata yace jeki kaemata inason muyi magana ne nakira ta ta wayan akashe cikin tura baki tadauki wayan kuwa takoma gun yayar tasu sam itama bataji dadin kawo wayanba don sabodashi takashe wayanta seda suka gama wayan tabawa hasana wayar tamayar masa koda tasauko twins kawae tasamu a apalour din ummi tana dakinta shikuma yafita answer waya da dayan wayan nashi hakanne yabata damar zama tasoma bincieke awayan tana shiga inda ranta yamata tana cikin kallon pictures a wayan taganowa kanta abinda yadaga mata hankali tamike dasauri tashige dakinta tacigaba da kallon hotunan jikinta har bari yake saboda tsoro duk rabin hotunan bassam ne shida mata fitsararru babu kayan mutumci ajikinsu wanda dasuma gara babu wasu sun makale masa ajiki hawaye kawae taji yana bimata ido,
Koda bassam yadawo yace wae twins hakasan bata sauko bane haryanzu suduka sukace tasauko mana tundazu tashige bedroom, jiyay wani daram kirjinshi yaharba inibin dayake shirin kaewa baki ya saki tsam yamike ya nufi daki, kallonta kawae take tana hawaye tana cewa allah ya isa ya bassam wlh yau allah ya toni asirinka bazaka taba auren yayarmuba ashe kae dan iskane dama tokuwa sena kaimata taga abinda kake aikatawa yaudararta kakeyi tanata masa ibar albarka, tadagowar dazatayi taganshi jingine a kofanta yana kallonta saboda firgita tamike batasanma tasaki wayanba tasaka kuka tana cewa kuma wlh kome zakayimin sena gayawa yayarmu don bazan bari ta auri dan iskaba hakanne yasa yasoma nufuta ahankali tanaja baya fuskarsa babu alamar rahamar annuri atare da ita seyanzu yake danasanin bawa hasana wayarshi dayay don yamanta ba security, harseda tadangane da jikin bango yazo dafda ita ya nunata da yatsa yace kewacece dazaki hanani auren my meems yarinya duk duniyar nan babushi sannan kuma wayace kiyimin bincike awaya?cikin zafin rae tadago btace saboda allah yatoni asirinka wayanka tazo hannuna yau tasss bassam yadauketa damari tasa hannu biyu kuwa tadafe fuskannata tana kuka cikin bakin ciki yace ke wace irin dakikiyace saboda kinganni da mata zaki kirani

Please Login or Register in order to submit comment