Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma mine na gode, na gode , na gode, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya sama dukiyar ka albarka da rayuwar ka gaba daya, Allah ya jiqan iyayen ka ya sa su cika da imani" " Shhhhhhh wai wannan godiya haka kamar na sai maki mota?" " hmmmm kai ka ga bai kai ai.wannan godiyar ba, kai ma kasan ina da son waya, a matsayina na wacce ba ta taba riqewa ba yau na samu ai sai godiya ko, beside macen kwarai dole ne ko tsinke mijin ta ya kawo ya bata ta nuna mai godiya da murnar ta, in ba haka ba taiwa kanta baqin ciki dan gaba ba zai ci qwarin guiwar kawo wa ba" " wannan haka yake macen kwarai, mace daga cikin matan aljanna, Juwairah in dai ta dalilin miji ake shiga aljanna na maki alqawarin na yarje maki" wani irin hawaye mai dumi ne ya ke bin fuskar ta na tsantsanr farin ciki da nishadi, ga wani son shi da ke ratsa shi, " Yah Jabeer, na gode sosai Allah ya bar mu tare , mu je aljannar tare, domin kaima ka shiga cikin alqawarin Allah duk mai kyautata wa iyalin shi zai shiga aljanna, kana daya daga cikin mazan da suke koyi da halayen Annabin rahama da sahabbai" haka sukai tai ma junan su dadadan kalamai, ( abinda aka rasa a wannan zamani kenan, saurayi zai tai ma budurwar shi daddadan zance kan aure, amma da anyi kwanaki ya daina kenan, itama haka, sai a dawo kowa na dana sanin auren dan uwan shi, auren duk da muke ganin yana dadewa wallahi ba sa dai na neman junan su kamar ranar suka fara haduwa, kowa a kullum yana son ya fidda sabon salon da zai faran ta ran dan uwan shi ne, dan haka mu ci gaba da nemawa juna farin ciki sai auren mu yai qarko).




Bayan an kwana biyu Suwaiba da Saudat sun fara sabawa da wannan mummunan labarin da suka juyo wa kansu, Saudat ta fara neman dalilin da zai sa ta san me ne ne silar rashin haihuwar su, watarana Alhj Kalla zasu tafi meeting gidan Oga Zaks , domin a wannan yana yin da ake ciki ta fuskanci ko su su waye, sai dai ta qi gayawa Suwaiba dan ita akwai wauta, da ta sani zata fasa kowa ya san sun sani, ta ko jawo masu masifa, sai da ta gama jin komai wani member suka samu da zai shiga qungiyar tasu amma bai san location ba, take Alhj Kalla ya fara bashi address, Saudat na kwafewa, tana gamawa zata tura riga Alhj Kalla ya fito, gaban ta ya fadi amma ta dake, ta ci gaba kamar tana gyaran rigat ne," Ohhh mata kenan, daga kwalliya sai saka kayan ado, sai gyare2 kawai kar dai aga munin ku" dariya sukai gaba dayan su," ina ta kiran ki ina palo banji kin amsa ba" take ta gane wayo yake son mata," ai ban jiba Alhj na, ni da nake nan kana can,wataqila ma da ka daga murya dana jiyo ka, tinda kai ba zakai amfani da waya kana kirana ba , sai kai ta kira in ban ji ba kace nai laifi" murmushi yai a ranshi ya tabbatar bata ji komai ba, "k shikenan je ku dakkon ruwa na sha anjima kadan zan fita" tashi tai tana kada jiki tana yauqi tana isa kitchen ta qarasa da hanzari ta ciro takardar ta wulla a bayan fridge din dan ya fi kusa, motsin shi ta ji ya biyo ta, budewa tai kan ya qaraso ta dakko ruwan da cup, yana isowa tace" hmmmm Alhj na kana sona da yawa na kula 'yan kwanakin nan kamar ka maidani rigar sawa ko ina zaka sai dani" murmushi yai yace" ai ke kk koma haka shiyasa na koma hakan" ya karbi cup din ya hade da hannun ta, ya matse saida tai qara, ya zaro mata idon shi jajaye yace" ki kiyayi bincike domin yana kai maiyin shi ga halaka" " Bannnn......ban ganee...baaa" " dalla malama rufen baki, ji kk ban san kina bin waya ta ba? Ko in da na fita, ki gani? Ina nake zuwa me nake yi? Me kk son sani yau na sanar dake? Dan ba tsoron ku muke ji ba? Auren kwadayi auren kudi kukai, kuma kuna samu, to meye na sai kun ji kwakwaf?" Jikin Saudat sai rawa yake wani ruwa2 taji na tsattsafo mata ta qafart ta batai aune ba taji ya kwada mata bari" Dan uban ki fitsari kikai a tsaye? Ji yanda kk batan takalmi ni da zan fita? Me kk sani game da mu?" " Alhj ban san komai ba, sai dai zargi da nake" aje cup din yai ya zaunar da ita a kujerar dinning dake kitchen din " ehen ina jin ki zargin me kk?" " dama ina zarkin ko ku yan damfara ne, kai da Alhj Salihu" " kin tabbata zargin da kk kenan?" "Allah shine" " to bari kiji, zargin ki ya tabbata, amma idan na ji wannan maganar ko a wajen waccan doluwar yayar taki da ba abinda ta sani sai barin zance, da soj kudi, kin mutu, kinji ko baki ji ba" cikin tsawa ya qarasa zancen," Nnnnaaajii..."" Good,ni na fita, miqon takardar da kk boye kan na karya ki" tashi tai ta dakko ta miqa mai, ficewa yai ya barta ta durqushe tana ta kuka, lallai yau data gaya mai abin da ta gano game da shi da fa shikenan kashe ta zasui, yanzu ta gudu ma nan ma har gidan su zashi wataqila ma ta jawa uwar su a hada da ita a kashe, ta zauna tai shiru sui ta cin kudin haram kudin jini, "kaiiiiii wannan Abuja ba tai ba, inaaaa" ni dana sani a Damaturu nai aure na ma" ta fada tana share majina.




Salma ido ya kumbure dga zaunen tai baccin wuya ba shi ya dawo ba sai wajen la'asar, riqe da koko da qosai dan yamman nan da ake yi, sai wata leda mai kaya a ciki kala uku da takalmi kala biyu sai jaka daya, da yan kayan kwalliya da ba a rasa ba, miqa mata yai, ta tashi ta isa ta karba, leqawa tai ta yamutsa fuska, " baki daku ba kenan ko, gar da zan baki abun da ban sai wa Marka a shekara goma ba, ke kin samu ma kk kyabe baki ko" a tsorace tace" na gode" ta tashi ta shiga dan bandakin dake maqale a dakin tai wanka ta canja kayan ta fito, koko da qosan ta dauka ta ci ta sha, sannan ta koma ta zauna, " kin iya cewa wani yai sallah amma ke bata dame ki ba, ji kk ban gane ki ba, wa'azi a baki amma ke baki aiki da shi munafuka, irin kune kuna da yara kuna sa su sallah su qi, to basu ga kuna yi ba" miqewa tai zalo zalo taje tai alwala tai sallar ta koma ta zauna," zuwa gobe ogana zai dawo shi kadai yake zama anan, matan shi suna maiduguri, aiki ke kawo shi nan, dan haka in ya dawo da yamma ki shirya muje mu gaida shi, in muka dawo na gan ki a waje ko kusa da wajen dakinnan kin mutu ranar, dan na san ki idon ki idon kudi, kice zaki maqale ma bawan Allahn da bai san neman mata ba, na kula akan kudi komai yi zaki, tinda an iya bin qattin qauye masu bada dari da hamsin" hawaye take sosai sunqi tsayawa, haushin ta bai wuce yanda yama qi ya saurare ta ba sam, ya tsaya ta mai baya ni yaqi, kawai sai ta maida kanta ta kwanta, bata qara furta komai ba har ya shirya ya fice, kuka take mai ban tausayi" Oh ni Salma na saiwa kaina wahala daga yar shawarma da motar dana gani duk na rude ga inda na kawo kaina, Abuja ko wahala?"




Da kyar Marka ta miqe ta je ta hada wuta ta shiga ruwan dumi ta gasa jikin ta, komawa tai ta ci gaba da kwanciya, wani qaramin yaro ne shafi'u daya daga cikin yaran da Talle ke auri saki ya shigo zai kai shekara goma, baya jurar yunwa shi, dan ko da su Huwaila na baccin gajiyar iskancin su da suka sheqewa da dare, ita Marka takan tashi tai abin kari da wuri, to yau sunji shiru kowa dif a gidan, tura kai yai ta ware qafafu tana ta firfita da mafici," Marka yunwa muke ji" da sauri ta sake zanin ta juyo kan shi," me kace?" " cewa nai yunwa muke ji" habaaa ina wuta na saka wannan yaron, inji Marka, kiran shi tai tace zo ka karba, yana isa data damqe shi ta hau duka, tana" sai na fashe dukana akan ka, dan uban ka, banda wannan ta'annutin da uban ka ya min, har abinci kk tambaya? Ga shi tinda ya dauke waccan jaja amaren sai da na gan shi kuma, to ko xaka ci abinci har ka qoshi, amma na duka" dim dim dim kk ji" Marka lfy me ya miki haka" cewar Haule kenan, tana qoqarin kar bar shi, wani mari itana ta karba, kai na taqaice maku duk wanda ya shiga sai ta saki wani ta kama wani haka tai tayi kamar mahaukaciya, sai da ta gaji jikin ta yau laushi sannan ta kwanta tana kuka, ita ta shiga uku, ta hada sharri kuma ya zame mata tsiya......
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ ' YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ



BY HAERMEEBRAERH



Masoya novel din 'YAN ABUJA dan Allah ku min hakurin jina da bakuyi akai2 yanda na saba, inshaa Allahu in komai yai normal zan ci gaba ba da tsaya ba har sai na gama dika. Na gode. Love u all❀





Page 17:





" wa'alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya saimin" Juwairah ke fadin hakan cikin murna da kuma zumudi, Nafeesah ce ta qara sa shiga itama cike da dokin ganin me za a nuna mata, sanda ta gani itama yar qarar murna tai ta haye kujerar da Juwairah take" kaiiiii amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye" " to malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa" " hhhhhh Allah baki hakuri ai wannan wayar inna dauke ta yanda kk san jariri sai kin nema na miqo maki, ko in tana buqatar a sa mata kudi" dariya suke sosai, " yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na ga kin saka a garwashi?" " Oh ban cire ba dama je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki hajiya tambaya" " ah to dan kin san in baki fadan ba baki da zaman lfy yau" fita tai ta sauke mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, xama tai tare da tanqwashe qafa agaban Juwairah tace " To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi" " ke ko, ke ko, hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci gaba da karatun ki kike ni fa ina zaune a gida kullum" " kema zaki ci gaba ne komai lokaci ne sis oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?" Dariya Juwairah tai sosai sannan tace" ke dai ba ki mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan wallah" " to naji magani ne amma ai baki fadan ya ake hada shi ba ko" haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen garahuni, da 'ya'yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani da wannan zai masu magani duk da ba wai yana dauke shi dika bane kwata2 amma yana ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin" " yauwa ko ke fa ba ga shi kin qara min ilimi ba ni ina ma san wannan abun,in ba yanzu ba, yauwa rannan naji kina fadama shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba game da warin gaba" " Oh k wannan, dama muna magana ne akan macen da take fama da warin gaba na farko dai akwai na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta" "hhhhhh kaji Matar yaya wai mace ta jawo wa kanta kamar yaya? Kana sane kabar jiki yaita tsami" dariya sukai sosai suka tafa, " Allah da gaske nake, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant daya a jikin ki, kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai kk mayar wa, ki fadan pant din dan uwan ku ne da zai qi wari?" " hhhhhhh wallahi dole yayi amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi ba a canja gaskiya a saka Salma" " wulaqanci yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana shan dadi an manta da dangi" " hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi alkairi" " Ameen dai" " to yanzu fadan ya za ai ai maganin wannan warin dan Allah dan akwai yar makarantar mu, kin zauna kusa da ita sai kinji wannan warin, dan ba zanji kunyar fada mata ba, da azo ana ta gulmar ta tana jin haushi" " Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki na gari ke wayar da kan abokin shi, kina ji ba, a rana a baki canja pant a ki canja sau uku, ya zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in kikai fitsari ko bayan gida zaki tsane wannan ruwan, sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki komai ba, sannan baya, karki hade wajen wajen wankewa, in kk gama kk goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana tayi kikai wanka sai ki canja, da dare ma haka, ba yanda za a same ki da wari ko da baki shafa misk, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da kk zuba zuma asalin me kyau, wannan wanke gaba da ruwan zuma ya samo asali ne daga Annabin rahama yana daga taskar magungunan daya bayar muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki Hajiya tambai" " hhhhh wallahi kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah ya barki da yaya, ya sauke ki lfy" cikin jin dadi tana shafa cikin ta ta amsa, tashi tai ta tafi bayi da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee" Nafee gobe ne kin san ranar gyaran jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare" karki damu zan samo maki kan gobe, ji cikin ki ya fa girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana" " Tab aa ni dai ki samo min, in babu ma ina da zuma da sugar kawai ki samon lemon zaqi ko daya ne ko biyu" " to Allah ya kaimu, bari nai wanka na fita makaranta" "to Allah ya bada sa'a, bari na dan huta nima".







" Alhj wannan itace mata ta da kuka karba min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan ne dan na dinga samun kulawa, zama ni dayan ba dadi" Talle kenan ya fada yana sosa qeya, murmushi uban gidan na shi yai yace" Allah sarki ai ba damuwa, hakan da kai kayi tinani, kuma ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri'a dayyiba" " Ameen" gaida shi salma tai kanta a qasa tana wasa da gyalen ta, ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kudi ya qirgo dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa tai hannu na rawa, rabon data riqe kudi haka ai ta manta, tashi sukai suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu, fuskar nan ba walwala," me zan maka kuma" ta fada cikin tsiwa, " dan uban ki ni kk tambaya me zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan" alamun da ta gani na ba wasa yasa ta miqa mai tana hawayen baqin cikin ga samu ga rashi, murmushi ya fara yi jin dumus da yai," Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin qauye masu baki dari da hamsin ko" juyo wa tai cike da bala'i tana kallon shi kuma sai ta fasa dan wani tsoron shi daya kamata, gani tai yana cire kayan shi, ita ko bata shirya ba, ga ciwon jiki da take fama da shi, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da mutum, kuka ta fara tana" ni na barma dari biyar din dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na gaji banda lfy" dariya yai sosai ya maida kayan shi" da kyau matar manya matar Dan Abuja kenan, ku baku da buqatar kudi ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma" nera dari ya wurga mata ya fice yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka ta durqusa tana yi, " wai ni ina yan uwana ne, suna can suna jin dadin su sun manya da rayuwa ta, basu san a halin danake ciki ba,Oh Allah ka kawon dauki, na tuba, Juwairah kin huta, dabaki zabin aure ina zaki ba, gani ina cin ubana a garin da na taso da kwadayin yin aure cikin shi" kuka take mai ban tausayi, yunwar dake cin ta ce ta dawo da ita daga tinanin da take, tashi tai ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo garin ta da sugar da gyada, hadawa tai tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su ba su shan gari a gidan su amma yau gata da gari, share hawayen ta tai, ta jingina da katifar su, a haka baccin wuya ya dauke ta.






" Adda Suwaiba ya kamata fa mu je ganin gida yanzu haka, haba tinda muka zo yau watan mu na takwas kenan fa, muna cikin na tara, bamu taba zuwa gida ba, ba a taba zuwa mana ba, ga labarin Salma shiru, har yanzu" " hakane kam ya kamata muje muga ya su Goggo suke, batun Salma ki daina damun kanki tana can suna cin amarcin su, kin san mijin ta ma ba laifi akwai kudi, wataqila ma basa qasar nan" " haka ne Allah ya jiyar da mu alkairi, amma nikam na tambaye ki?" Ina jin ki" " dan Allah baki zargin komai game da mazan nan namu kuwa?" Kamar ya fa?" Tina wa da tai in ta sake Suwaiba ta san me ake ciki kashin su ya bushe ya sa tai saurin kauda zancen ta basar tace" ba komai yanzu dai mu tambaye su, yaishe zamu gida" " Ba rana balle wata" amsar da suka ji kenan ana basu bayan an bude qofa an shigo, " ke tashi mu tafi gida, ai an sada zumuncin haka, ku da kuke son Abuja kamar ran ku, in ban manta ba, Saudat kan mui aure cewa kikai, in Allah ya baki miji kuka tare a Abuja sai kin shekara biyar baki je ganin gida ba, ko ba ai haka ba?" Cikin qunar rai da kwallar da ta maqale mata tace" anyi haka, amma a da ai ban da isasshen sanin ya Abujan take kuma gani nake zan iya amma ni yanzu gaskiya gidan mu nake son zuwa naga uwata" wani hatsabibin kallo ya watsa mata, ba ta san sanda ta durgusa ta dau jakar ta ba tai hanyar fita, sallama yai wa abokin shi wanda daga jin warin da suke sai da suka biya sukai tatul, nikam nace Saude Allah shi kyauta karki daku yauma.......πŸ˜‚
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ




BY HAERMEEBRAERH



MAMAN YOUSUP
Mutan Gwambe ina godiya sosai da nuna so da qauna, kuma saqo daga Salamemen Talle tace a sanar dake bata da qawa sama dake tana son ki sai kin isa ABUJA adama da keπŸ˜‚πŸ˜ ME LOVE U XOXO❀




Page 18:






Goggo Sarai ce ta qame kan kujera tsabar ba a iya samun wajen ba ma, da nuna ita bata gaji arziqi ba, iyakar wajen ta aka shata aka gyara, baqin cikin da kanta da kanta take, dan ko ba wanda ya kula da ita, ita amma gani take all eyes on her, ita a dole ga uwar masu kudi, mijin Salma kawai take jira su dawo daga waje a yo mata kabakin arziqi na waje, Ammar na hango yana tafiya dugui2, dan ba wai ta gama kwari bane, ya zo wajen randar ruwan Mama Bilki, da dikkan alamu qishirwa yake ji, Mama Bilki na daka tana baccin tsakanin azahar da la'asar( bacci ne da in bawa yayi shi yake samun lada daga wajen Allah) ita ko hakimae ana zane ana kora jus da meatpie, ga mafici a hannu irin wanda ake kamar zuge shi dinnan ta kwama uban baqin glass a ido na ba mutunci dinnan, Abban su shi ke da bangaren ta yau amma gudun wulaqanci sai dare yake shigowa, kan tace ita ke ci da gidan, ko makamancin haka, dan haka yana qofar gida, Ammar ne ya dakko cup yai ta buqawa a jikin randar," Yauwa yaro fasa wa uwar ka dan arziqin da ya rage mata ka huta gadon mugun abu kawai" bata gama rufe baki ba ya saki fitsari, gangarowa yai qofar ta, habaaa ai kamar an watsa mata ruwan zafi, ta miqe kafin ta isa ya fara qoqarin tafiya yana kuka, da alama ba iya fitsarin zai ba, daidai fitowar Mama Bilki da shigowar Abban su, hannu ta sa ta wanke Ammar da wani lafiyayyen marin da ko Maman akai wa sai jikin ta ya gaya mata," ganin wannan kini babbun iyayen naka masu son abin duniya da har suke ganin Da namiji ya fi Ya mace daraja ba zai hani cin uban ka ba, in banda baqin ciki da aka koyawa yaro qarami tin yana ciki, duba fa ku ga yanda ya tsanyaran fitsari a qofata yai gaba, to ba zan lamunta ba" Ammar tsabar kuka ya gigice sai ga kashin ya biyo baya, zuciyar Mama Bilki tafasa kawai take ba iyaka, tin da Abban su yake da ita bai taba ganin bacin ranta haka ba, ita kanta Goggo Sarai ta tsorata , wandon Ammar Mama Bilki ta cire ta wurga a jikin qofar da aka canja wa Goggo Sarai, qofa ce irin ta qarfen nan mai kauri milk color, ta aje Ammar din ta isa jikin qofar ta samu wandon ta goga sosai har labulayen, sannan ta dawo ta daga hannu zata wanka mata mari, amma sai naga ta tsaya,( nace kash dama kin qarasa mun sha kalloπŸ’ƒπŸ») me ya tsaida ta oho, daukar Ammar tai da yake ta kuka yaqi shiru ta je ta fara gyara shi sai da ta gama taje ta dauke wandon nashi ta wanke ta shanya, sannan ta qara wanke mai jiki dika, ta bashi ruwa da abinci ta goya shi sai bacci, yana yi yana ajiyat zuciya, wata irin wuta aka dauke a gidan gaba daya , ba mai iya cewa komai, Goggo Sarai na tsoron tace kanzil yanda Mama Bilki ta bata rai bata san me zai

Please Login or Register in order to submit comment