Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a tashe matuqa, ya kama ta tai ta kwarara amai, sai da ya zamana bata iya fitar da komai sai yunqurin azaba, sannu kam ta shata har bata iya amsawa,idon Jabeer sunyi jaa saboda tausayawa matar tashi,tabbas in hasashen shi gaskiya ne wannan karon da alama mai wahalarwa ne, dan ya kula kwana biyu kenan tana fama da wannan wahalhalun, ga zazzabi dake addabat ta, haka ya jata suka tafi toilet,kayan su ya cire masu,ya saka su a bathtube,ruwa ya cika masu suka dauraye jikin su sannan ya tsiyaye ya saka wani, wanka ya musu suka fito, bayan ya shirya ta ne ya kwantar da ita a agado yaje ya shirya shima,zuwa yai kusa da ita ya kwanta ta bayan ta" Honey kaje kaci abinci everything is ready at the dinning area" " I know,but i can't eat when u are like this, me ke maki ciwo, me kk so, dan daga ganin ki da kuma aman da kikai,bakici komai ba in ba wainar flour din da kikai mai manja ba da safe," turo baki tai daga baya ta kwabe shi irin na shagwababbun nan, shi kuma yana jin yanayin saukar nunfashin ta ya san na kuka ne, saurin juyar da ita yai, " What is wrong my love,pls tell me ur problem,or what you want, i will provide you with anything i have inshaa Allah" kukan da take son yi ne na shagwaba ta fara, rungume ta yai yana kissing wuyan ta a hankali yana shafa bayan ta,sai da tai ya ishe ta tai shiru tana ajiyar zuciya, a hankali ta fara magana" Yah Jabeer banda lfy, kwana biyu jikina ciwo yake sosai, ga zazzabi da amai, abubuwan danake so sai naji vana son su," sai ta qara saka kuka, " Shhhhhhhh, yi shiru my bby, ki daina kuka, ko zaki gwajin ciki a gida ne, tinda muna da abin yi" jimmmmm tai kafin ta wuntsila daga gadon cikin doki da zumudi, binta yai a baya yana mata dariya, dan ya kula bata kawo hakan ba sam, sai yanzu, zuwa tai tai gwajin ta fito, layukan na farko ya fito radau na biyun ga shi nan dai, amma tabbas akwai shi, kwabe fuska tai tace" ni ban gane komai ba," " to ko asibiti zamu?" " ehhhh haka za ai ina zuwa" fita tai da hanzari taje ta sake kayan jikin ta zuwa doguwar riga da babban mayafin da zai rufe har mazaunan ta, bayan ta gama ne ta juyo taga shima shiryawar yake, a tare suka fita, sun isa wani makeken asibiti, a unguwar tasu ta Jabi, suna zuwa sukai mata gwaje2 inda suka dau wasu yan lokuta, likitan ya tabbatar masu da tana dauke da ciki ne na sati biyu, wata irin murna ce ta kama su, Jabeer ba ko kunya ya daga ta sama ya hau juyi da ita, ita ko sai dariya take, kissing din ta yai kadan sannan ya aje ta, godiya ya hau ma Doc da bakin shi ya qi rufuwa shima, yana mamakin irin soyayya ta wadannan mutane, bayanan yanda zasu kula da cikin ya musu, wanda sun riga sun sani,amma sai suka koma kamar ba su taba ma sanin ya ciki yake ba tsabar murna, bayan sun gama ne suka fito Jabeer na wanilallaba ta kamar kwai, " Babe me kk so ki ci kinga kar kina barin kan ku da abinda zaki haifa mana da yunwa" kada kai tai a hankali tace"ni ba komai kawai ina son wainar flour ne irin ta dazu," aiko ba wata wata ya saka ta a mota sukai gida, suna zuwa ya shiga kitchen, ya hau mata wainar, daukan, abinda ta kasa sha yai shi kuma bayan ya gama mata, tana ci yana sha,"lallai babyn nan, da qoqarin shi,da gaske so yake kar ana shan abubuwan da zasu qara mai kuzari" dariya suka saka dikkan su" ko kuma abubuwan da zasu qara ma Abban shi kuzari ba" qara fashewa da dariya sukai( hadin kantu da madara ko da nonon Raqumi hadine tested and trusted dake saukar da ni'ima sannan yai maganin wasu cututtukan jiki in baka da nonon Raqumi sai kai da madarar shanu).

Saudat ce na hango ita da angon ta suna ta zagaye gidan suna guje2 cikin tsantsar so da qauna tare da begen junan su, wani irin shaquwa ce ta musamman a tsakanin su,tare da tausayawa juna, dan suna cikin gudun ne santsin tiles ya kusa kwasa Saudat a qasa, amma da ikon Allah sai bata fadin ba, ta dai tsorata ne kawai, da hanzari ya isa gare ta,yana wani juya ta" Sweet one baki ji ciwo ba,ta ina kk bige??" Kamo fuskar shi tai gaba daya a hannun ta, ta matso lips din shi irin yanda mutum zai iyayi da hannu ko da bakin shi ya tsuke su sui tsini, haka ta mai itama, sannan ta kai nata bakin tai kissing din shi, sai da taga suna neman faduwa ta tsaya" me ma kk tambaya ta dazu?" Ta fada cikin qunshe dariya,da daga gira,cikin in-ina ya fara bata amsa" Ammmmm..... immmm.... damaaa... cewa... nai.... imm.... can u pls kiss me again" dariya suka saka sosai har tana riqe ciki,daga ta yai ta bayan ta cikin nata suka samu wajen zama a kujerun nasu, bayan ya kwantar da ita a kujerar ne ya kwanta ta bayan ta,ya rungumo ta ta ciki,suna ci gaba da dariya, a hankali sukai shiru yana mata wasa da gashin ta" Babe me yasa baka damuwa da batun rashin haihuwar da kasan ba zan yi ba, saboda rashin mahaifa, bayan kai baka taba aure ba, ar u planning to have another wife ne nan gaba?" " My dear ina so ki san cewa da auren da haihuwar duk nufin Allah ne, tayu a baki da mahaifan mu haihu, ta yu ba za mu haihun ba, to ina son ki sani, haihuwa is a blessing that everyone will love to have it, amma ni bana daga cikin wadan da suke ganin in mace bata haihuwa bata da amfani,to ina soyayyar da yake mata? Dama dan Yara kawai ya aure ta? Ita ce take ba kanta? Idan zan maki kishiya saboda baki haihuwa tabbas na zama daga cikin azzalumai, na kuma zama daga cikin masu butulci ga Allah, domin ya min kyauta countless, to me zai sa dan akan abu daya danaoe so ban samu ba na mai butulci? Ba zai yu ba, daga ranar da kk ji na qara aure Saudat ban qara shi dan baki haihuwa ba ne, sai dan itama ina son ta,kuma Allah ne ya halatta mana qara auren, dan haka ki kwantar da hankalin ki ni ba mai ra'ayin tara mata bane, bana.son hayaniya, bqn son takura, mata da yawa na saka ni damuwa dan bana son raba fada kullum," ya qarasa ta yanda tabbas yasan hankalin ta ya kwanta da maganganun shi, amma hawayen dadi sun kasa tsaya mata, tabbas Allah ya azurta ta da namijin gaske, Allah ya qara mai hakuri da juriya akan hakan ta ayyana a ranta, ci gaba da shafa wuyan ta zuwa bayan ta yai ita kuma tana wani miqewa tana juya jikin ta anashi, tini ta burgita shi,ni kuma na ja sayyarar qafata na waje a 100😟



"Ki taho da fidar yarannan, da tissue love" amsawa tai shi kuma ya zauna yana masu wasa, bayan ta iso ne ta zauna kusa da su," ni dai gaskiya ban yarda ba nima sai an min wajen zama a nan, dan wayo kullum ni a qasa ko gefe su a cinya"ta fada tana turo baki,dariya ce ta kama shi, sai ya dauki Muhammad ya dora a wuya, sannan ya dago ta ya saka a cinyar shi,murna ta saka tana mai kiss a kumatun shi, " Na gode na zaci ai ce min za ai nai hakuri yaran su zauna da ba zan yarda ba sai dai a maida su daki ni na hau" ta fada tana sauka, dariya yake sosai, dan Salma ba dai kishi ba, kishi take da yaran nan sosai , dan gani take gaba daya ya kwashe soyayyar ta ya basu, lokacin shi gaba daya nasu ne in yana gida, amma a qasan ranta ba qaramin dadi take ji ba, hankalin ta a kwance yake dan bata tsammaci hakan a wajen saurayi da bai san ya zai gama kula da kan shi ba bare wasu yaran har biyu, kujerar basu abinci ya saka su,ya dorawa kowa a gaban shi, ya basu cokula a hannun su na dama,sa kyar suke riqewa saboda rashin iya hakan, amma yana tsaye in zasu karkace ya gyra masu, ta baya ta ziro hannun ta ta tsugunna itama ta kwantar da kanta a bayan shi ta furta"I love u" shima waiwayar da kan shi yai suka hada ido yace mata" i love u more" kiss ya mata a goshi ya juya ga yaran su( da na kowa ne, baka san wa zai more shi ba, dan haka bahaushe yace, da da dukiya ba a masu mugunta, in ka lalata wataqila kai zaka amfana a gaba,ka bata to da me zakai amfani, in ka gyara kuwa ka amfana, wani ma sai ya gama gyarawar ya zamana ba shi zai mora ba ya gyarawa al'umma ne, ladan shi na a wajen Allah, wani kuma sai ya bata ya mutu ya barwa al'umma annoba, yana qasa ana rubuta mai zunubin mummunan upbringing da ya ba wani,mu gyra duniyat mu lahirar mu ta amfane mi)



Talle ne ya shirya tsaf da yar jaka a hannun shi, wadda ta qunshi kayan yara mace da namiji dan bai san me Salma ta haifa ba, incase ko wace gender ta haifa za a samu na ta kayan, sallama suke da Marka inda qasan ranta kishi ne danqare, amma yanzu halin ta mai kyau data koya ya danne kishin, miqamai leda tai da ta daka kuka daddawa, sa kubewa, tace ya kai masu, godiya yai mata,Huwaila ce ta leqo da gyada soyayya itama dan sana'ar ta kenan yanzu, tq bashi tace ya gaida su ya nema masu gafar ta, amsa yai ya sa kai......




*To masu karatu Talle fa yai shiri, wa zai bishi ya fada mai bata gidan kar yai wahalar banza*πŸ˜‚
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ





BY HAERMEEBRAERH







Page 35:



Talle ne ke ta kwada Sallamah a qofar gidan su Salma, da ga can Ammar ne ya fara leqowa, like a big bo he is, da tsamin bakin shi yake tambayar wa ake nema, yaro yana da kaifin hankali, shekara biyu da watanni amma akwai qoqari ga karatun qur'ani a bakin shi tar, na bokon iyakar shi A B C D, sai counting da Mama Biliki ke dan koya mai, komai akai yana sane da shi kuma yana ganewa, murmushi talle yai, aranshi yace wannan yaro da ya dan da Salame zata haifan ya kai shekarun shi ai sai nace dana ne suna kama, " Yaro ina malam," " faya nan" ( Baya nan), Talle ne yaga yaron ya kalli gaban.shi yana dariya ya fita da gudu yana " Abbana Oyoyo" shima wajen ya kalla sai yaga ashe Abbam su Salame ne ya dawo, saurin isa yai wajen shi, inda gaba daya Abbam ya sauya fuska, daga fara'a zuwa bacin rai, " me ya kawo ka?" Tambayar da ya wulla mai kenan" Abba dan Allah dan son Annabin rahama kai hakuri, ka yafeni, tabbas na kasance daga cikin jahilai, marasa sanin Allah a baya, sakamakon jahilcin da ya mamayi zuciyata, kuma naqi na nemi sanin Allah da dokokin shi, ina jin girman kai, da ganin na wuce wajen ai, hakan tasa na aikata munanan abubuwa a rayuwata, kala2 wadan da naga isharar su Abba, babbar isharar shine mutuwar 'ya ta, kama dan uwana yaya na da mata ta suna zina, daya 'yar tawa ga ta can da dan gaba da fatiha, ga abinda ke dagan hankali rabuwa da Salame d nai, ta tafi da cikina na rabunda ita rabuwa cikin rashin tausayi da imani, a yanzu nayi nadama, na koma islamiyya ni da iyalina dika, ka yafe min ba dan halaye na ba sai domin Allah" kalaman shi sun saka jikin Abba yai sanyi amma ya wuce cikin gida kamar bai ji shi ba, yana shiga Mama Bilki ta sauke shi da ruwa da abinci, ga kuma ruwan wanka ta kai mashi,tana goge masa zufa ne tare da jera mishi sannu da zuwa cikin rattausan lafazi, umartar ta yai ta kira yayar tata,miqewa tai ta tafi, ta kira Goggo Sarai da tai zurfin a cikin tinanin baya, yanzu da hankali ke qara shigar ta, ba qaramin kunyar Mama Bilki take ba, tasowa tai kamar wadda kwai ya fashe ma a cik, ta biyo ta, " Gamu Abban su" dagowa yai ya kalle su cikin sha'awar yanda suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishinnan, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya zauna a cinyar ta, shafa kanshi tai tana mai murmushi, Abba labar ta masu komai yai sannaj ya sanar da su Tallen na qofar gida ma yanzu, haquri ya ba Goggo Sarai da yaga ranta ya baci, yama juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a bace, domin shi mijin Salma shima ba qaramin azzalumi bane kwantar masi hankali tai da dadadan kalamai sannan suka hakura, aika Ammar yai yace yaje ya shigo da baqon nan, tafiya yai ya sanar da shi, Talle ya shigo qafa duk ta sage mai saboda tsaiwa, waje Abba ya matsa mai kan tabarma, tayin abincin ya mai Goggo Sarai ce ta qaro ruwan sha da wani abincin, ci sukai suka qoshi, sannan Abba ya kira su again, " da farko dai ina son sanar da kai dukkan mu nan iyayen Salma mun yafe maka, kuma muna saka ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalumce ta, amma duba da cewar muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana, banga dalilin qin yafe maka da zamui ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kudi gidan hutu ita da yaran ka dan biyu ta haifa, kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar mallakin shi, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin......." " ban katsi nunfashin ka ba Abba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a daidai wannan lokacin, tabbas, na amince su ci gaba da rainon yara na, lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa nan din, ana gaisawa,ga address dina saboda wataran ko za a buqaci hakan," takardardaya rubuto tun a gida ya zaro ya miqa ma Abba, idon shi ya kada yai jawurr, tabbas har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda tin da ya dauka sha'awa ce kawai, miqawa Abba ledar Hannun shi yai ya mai sallama dan komai dare gida yai, ya ma yaran shi addua, an nuna mai hotunan su, inda Mama Bilki ta dakko mai wasu ajiyayyu tin na jarirantar su,har randa zasu tafi, hawaye kawai yake sharewa, duk yaran shi ba mai kyaun wadannan da ya koro, dan duk macen da ya aura in zata tafi sai ta dire mai da ko yar shi, ko in taje gida ta haihu zata dawo mai da shi, Haule ce kawai take itama kyakkyawa saboda uwar ta, yana tina ta sai zuciyar shi ta qara tsinkewa,ya kula yara uku ya bari yanzu, amma wannan na daga cikin horon da Allah zai masa ya raba shi da yaran da yafi qauna, tashi yai bayan ya sake masu sallama ya isar da saqon su Huwaila,godiya suma sukai masa, ya kama hanya sai qauyen su.






*BAYAN SHEKARA BIYU*


Salma ce ke zaune da jaririya a hannu da suke kira da suna Faiha, gefe Juwairah ce tana riqe da hannun yaron ta qaqqarfa mai kuma barna, Salim, Sai Suwaiba da ke ma Abrar kitso a lallausan gashin ta mai tsaho, gefe kuma a kwance a kujera Saudat ce ke latsa waya tana ta doka murmushi, Maganar Juwairah ce ta katse shirun nasu" In baka tsaya ba Salim zan kira Daddyn ka ya dauke ka ku tafi kona huta," da sauri yaron ya zauna a cinyr ta ya nutsu, dan a cewar shi Daddy is no fun to be with, amma Mummy, yana son zama da Mummyn shi ko da duka zatai mai in yai halin nashi na barna, ' Yan biyu ne sika shigo da gudu, suna haki" Mummy Daddyna yace wai ki bada Faiha, Salim da Abrar mu je park" kowa a cikin su daidai lokacin da kowa yace Daddyna sun kalli juna da harara,ba su fada a tsakanin su sai akan abu biyu, chocolate da kuma Daddyn su, sai kace kaya haka ake rabon shi a tsakanin su, wannan yace nashi ne wannan yace nashi ne, fatima ce tace" kaiii wannan Muhammad din sai son yi min kwace kk kullum for how long zaka gane cewa Mummy ce taka ni kuma Daddy nawa" " Fateema ke ce baki san komai ba hat yanzu" ya fada yana mata kallo wai shi harara, dan kwata2 bai kaita wayo ba, ga shi fadan ma bai iya ba" kai ni ku karbe ta sarakan rabon iyaye,kada Allah yasa ku zaben din ga Faiha in ta girma zata zaben ai" miqa masu ita tai suka karbe ta,dariya saudat tai sosai tace" Mummy ar u jelouse ?" Dariya dika suka dauka, Juwaira ta sauke Salim ya bisu,daidai an gamawa Abrar kiston ta, miqewa tai tace" Tanx Mum" tai kissing kuncin Suwaiba ta fita a guje, murmushi tai mai nuna alamun jin dadi ta bita da"ku dawo lfy kui adduar fita daga gida kan ku fita, kar a manta da yin addua in zaku dawo," daga nesa ta amsa mata da" inshaa Allah mum, i love u," " i love u too baby" nan ma Saudat ce dake ta Chatting da mijin ta ta sake dagawa tace" lovers kenan" nan ma dariya sukai, juwairah ce ke kallon ta da Yan uwan ta cikin farin ciki da nishadin da Allah ne kadai yasan iyakar shi," to ya kamata mu ma muje Shopping, akwai wasu abubuwan danake so mu siyo yau" ta fada tana kashe masu ido, Saudat ce ta diro da sauri ta dage hannaye sama tana murna" Yeeeeehhhhh shopping" " u always act like a kid Saudat," inji Salma, pilon kusa da ita ta wurga mata, " eh din anyi,my husband always treat me like one," ta qarasa tana murguda baki, dariya suka saka, Juwairah tace" yeh u ar always his baby" " and u ar more like baby to me than she is always my love" juyawa tai taga Jabeer ya shigo cikin qananan kaya, tare da mijin Saudat, tsallen murna Juwairah ta daka taje ta rungume shi,wanda dama yana fada hannun shi is open, rungume ta yai kamar su kadai ne a wajen,gyaran murya mijin Saudat yau yace,babban Yaya muje ki, tinda shi wancan Baban yaran ya debe su muma mu kai su shopping din kawai, kallin juna sukai matan, ba haka suka so ba, akwai dan abubuwan su na mata da suka so kwasa, amma ba damuwa sun taya su zaba ma, dakko hijaban su sukai,Juwairah har da Niqab Yah Jabeer yake sata sakawa, haka suka fita, gwanin sha'awa, waya sukai ma mijin Salma ya same su a Sahad dake can ABJ din, aiko Salma da tana jin ta out of place sai murn,sa riya sukai mata, a can suka hadu da yaran da mijin Salma siyayya sukai sosai kafin kowa ya nufi gidan shi, Suwaiba gidan Jabeer zata kwana kafin wase gari mijin ta yazo su tafi.






Arziqi ya wadata a zuri'ar gidan Abba Baballiya, gidan kuma 'YAN ABUJA, albarkar Allah ta sauka masu, ko ta ina,inda a tsakanin Jabeer da yake dan su da surukan su, kowa qoqarin yi ma iyayen abun da zasuji dadi suke, an canja fasalin gidajen iyayen daga na qasa zuwa na cement, da kayan alatu kala2, ga shaguna da suka bude masu, na saida kayan masarufi suka saka amintattun yara suke kula da wajen, shiko Yah Jabeer kasuwancin shi yana nan da kamfanin jakunkuna na AF2 dake malaysia, abun ba a cewa. Komai sai godiyar Allah,makaranta mazajen dika ke tinanin maida iyalan nasu nan kusa su ci gaba da neman ilimi har sai sun ce ya ishe su, Suwaiba nonoless tin bata son saka bra din acuci maza irin ta Cutie har ta fara, mijin ta ya masu gini a unguwar Kabuga, qaton gida, yanzu harkar gwanjo ta bude sosai, Talle arziqi ba laifi, ana nan an zama manyan ustazai masu ma wasu wa'azi musamman da basu misali da rayuwar su, Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su, na rashin haihuwa, ba sa damuwa a ransu ko adan, tin ana zuga mijin ta yai aure har an gaji, domin soyayyar su suke sha, da shaquwa ga fahimtat juna dake tsakanin su.



Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya.


*Masoya novel na 'YAN ABUJA ku dakace ni gobe domin jin wasu bayanai da sharhi da zan akan wannan novel da inshaa Allah nake saka ran zai amfanar kuma zakuji dadin shi da yardae Allah, ina roqon ku da kuma fatan duk abinda na fada daidai kuma kuka san abin koyi ne da ku qoqarta saka wa a ayyukan ku, sannan wanda nai kuskure ku yafe ni akai, ina jiran gyaran ku akai daga yau zuwa gobe inshaa Allah na gode. Me love u XoXo❀*
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ



BY HAERMEEBRAERH


*Assalamu alaikum Jama aree bandi raabe am, yidibee novel 'YAN ABUJA, mido yetta on masin,beyeddi on holli am haa dow defteream, mido yeela ko end jangi pat end habdai end naftira bemai koo na pat ba end habda ko sedda on, mido usa mido yetta on walama bana fulbe haa on woni fu ha duniya do miyetti, walama bana yare IBRA, end doo woondi inshaa Allah, mido yidimon*❀


*Ina kuma riqon duk wanda Allah yasa ta fara bin wannan novel daga farko ko ta riski wannan page din koda bata bi daga farko ba ta daure ta karanta wataqila ta samu koda abu daya ne mai amfani a ciki*


Page 36:



Zan yi sharhi ne akan wannan novel namu na yan abuja, inna gama nawa wataqila ba zai yu na fidda komai ba ina son kuma makaranta ku fiddo man da naku hakan zai sa naji dadi maybe gaba na sake mana wani novel dinπŸ˜‰


1- da farko dai gaba daya a kuma dungule nai magana akan iyaye da tarbiyya ne, yanda iyaye in Allah ya basu yara ya zasu saka su akan hanya mai kyau wace tarbiyya zasu basu, me yaka mata su saka masu a zuqatan sh saboda gudun kar su tashi ba akan tarbiyya mai kyau ba.

2- sannan nai magana akan kwadayi, mahaifiyar su Suwai nonoless ta taso da su akan kwadaryi sa burin zuwa inda ba lallai ne arziqin su na can ba, unlike Juwairah da suka raina ta akan auren Yah Jabeer.


3- Ana son mace ta zama mai tarbiyya mai kyau, wadda ko ina ta shiga za ai sha'awar ta da halayen ta in bata nan ai kewar ta, ki iya zama da kowa da kyakkyawar mu'amalat, ki kasance wadda ko minti daya miji yai baku tare zaiji damuwa da tashin hankali, da duk wanda kk tare da shi ma.

4- Ana son mace ta zama mai tattali mai dabara in ba wannan a gida ta san ya zata hada wancan ya bada outcome mai kyau mai dadi, yanda ba mai gane ma rashi ne ya jawo hakan, sannan ta zama tana qoqarin dasa kowacce hanyar da zata kawo masu sauqi a gidan ta, kamar yanda Juwairah tai lambu a cikin gidan ta.

5- Mace mai rufawa mijin ta asiri a kowanne lokaci abar so ce ga kowa, ba namiji ma kadai ba ga kowa.

6- Mace ki zamo mai tsari, ya zamana kina da lokutan yin abubuwa, in kina haka za a same ki mai tsafta, baki kwaba

Please Login or Register in order to submit comment