Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

warin HQ sannan yana matse mace, ya gyara ta, sai dai ba a so in ba kamar yanzu da aka haihu ba a cika amfani da shi shi da bagaruwa, baya2 ake son amfani da su, dan kar su yi illa ma wajen, kuma ana son in ana amfani da su a yawaita cin fruits da veges da kuma shan zuma mai kyau da zamzam, dan su zama sun saukar da ni'ima a HQ yanda ba zata bushe ba) bayan sun gama ne ya fito kenan Nafee ta dawo daga makaranta, shigowa tai da gudun ta, sakamakoj kukan bby da ta jiyo, ai suna ido biyu da Juwairah ta kwasa da gudu ta isa wajen ta ta rungume tana murna, " sannu matar Yayah Allah ya qara maki lfy ya raya mana abinda muka samu" " Ameen Nafee sannu da dawowa" " to malama sake ta haka taji da kanta" sakin ta tai amma bakin ya qi rufuwa kamar gonar audiga, gani tai ya dakko zanin haihuwar ya aje mahaifar a cikin leda zai wanke zanin, maza tai ta karbe, "Yah Jabeer barmun na wanke ni ban komai ba ai" " A'a sis basshi yanzu kk dawo skul bana son ki wahal da kanki, kayan jini ne ke kuma baki son su dan haka zanyi, beside ni ya kamata nayi, tinda ina kusa, ta yi me wuyar da ta haifo man the queen of beauties, shiga ki ga inda ake kyau barakallah" ai ko tini ya kwadaita mata gani yarinyat da gudu tai dakin, tana isa ta zube gwaraf gaban Innar mu, ta gyara yarinyar ta sha kwalli, tai matuqar kyau, idon ta bude fes kamar haihuwar sati, cikin zumudi ta amshe ta, tana mata addu'a Juwairah ce ta shigo da sallama daki tai ta na tasbihi ga Allah tana matuqar godiya daya sauke ta lfy, Mama Bilki ta sha addu'a yau a bakin Juwairah, ta gefen idon ta ta hango tsantsar kyau irin na yarinyar, " ikon Allah ke nan yanzu da wanne ido zani gida na kalli Mama da Abba, wai ni ce yau na haihu" shafa cikin ta tai da yai mata babba kamar bata haihu ba ga nankarwa da taji yayi, murmushi tai ta qara gode Allah, nan da nan ta hau shiri, man kade ta dauka ta shafe cikin da shi sosai ta murqe shi, dama ya sha gashi wajen Yah Jabeer, don jinin ya samu fita, bayan ta gama murje cikin ne ta kwalama Nafee kira dan ta zo ta daure mata cikin, zuwa tai ko ta tamke mata shi, tsam, ya koma kamar ba ta haihu ba, kayan ta ta saka atamfa riga da zani ya mata kyau sosai, kalar atamfar akwai pink da red a jiki, geshe jikin ta tai da turarika masu dadi ta fito, lokacin Jabeer ya gama komai yai wanka shima ya shigo, sannu tai masa da adduar Allah ya saka mai da alkairi, yai murmushi yace" is my duty love, so ki daina damun kan ki," murmushi tai mai da tasan yana biyan komai a wajen Yayan nata, kada kai yai alamar zamu hadu ne, kina tsokana ta ko, daki yaje ya shorya ya fito ya same su dika a zaune, gyaran murya yai ya kalli Abban su ya gaida shi, dan yana shiryawa ya shigo, yai ma harinya addua, Nafee na ta masu tsiya shi da Innar mu, miqa mai ita Abban su yai shima ya mata addua, sannan ya fadi sunan da za a ana kiran ta da shi, wato Hafsat sunan Innar mu kenan, Innar mu har kukan dadi tai, sannan yace ma Juwairah "sai ku nema mata sunan ku na yan gayu da na san dole sai kun saka mata," Nafee ce ta kalli Juwairah tace" matar yaya sai ki bamu suna" Juwairah tinani tai sannan tace" Na saka mata Abrar( mao tsoron Allah)" " Oh ni Hansai yanzu ina ni ina iya fadan Abras" dariya suka kwashe har Abba, Abban ne yace" haba Innar su, yanzu Abrah dinne zai gagare ki?" Haba me zasui in ba dariya ba dan shima ya kwafsa, gyaran murya Jabeer yai ya fara magana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa tare da son sanar da su abin farin cikin da ya same su yace" Abba Innar mu Juwaireren Mama and my little sis Nafeesa, ina mai farin cikin sanar damu ci gaban da ya same mu, a yau kuma a dazu dana dawo na zo da labari me dadi na samun aikin da nai, a NNPC na can Abuja in da suka ban gida dake kusa da gidan man da zan aiki, a unguwar Jabi, harda mota, sin dauken a matsayin Manager na wajen gaba daya, sanan kuma bangaren kasuwanci na yau na biya ta kasuwa, Saifullahi dana kan bari ya min jiran wajen in bana nan ya dakkon kudade masu tarin yawa, da kuma wasu jakunkunan da na saro ba su iso ba daga malaysia , to a yau suka iso, har wasu yan kasuwan sun sara, shine ya ban kudin da suka kai dubu dari biyu da talatin cif a hannuna, nan take na bashi talatin din nayo gida da sauran" juye2 ya farayi yaga ina ya wurga ledar da yazo da ita, dubawa yai ya hango ta can hanyar shigowa inda ya yar ya iso wajen matat shi mai naquda, kasa kudin yai kashi biyu, sannan ya qara kasa kashi daya biyu, miqawa Abban shi yai kashi daya, sai kuma ya dauki dubu goma ya ba Nafeesa sauran dubu arba'in ya bawa Innar mu, yace gashi su sa mai albarka," lallai wannan yarinya ta zama mabudin alkairi a gidannan, muna ma Allah godiya, nayi murna da farin ciki sosai najin wannan abun alkairi daya same mu, Allah ya taya ka ruqo da gaskiya da amana, Allah ya qaro maka arziqi mai yawa mai albarka," amsawa sukai gaba daya da " Ameen" Innar mu kukan dadi take tin da aka fara maganar, dan bata taba tunanin riqe kudi rabin wannan bama dan tasan ba ta dasu bata kowa ba ajiya, yau gata da su kuma nata, ai sai murna, ta kasa magana sai kukan dadi take na daukakar da Allah yai wa danta a lokaci daya" Innar mu ki bar kuka addu'a da albarkae ki Yah Jabeer ya roqa" Juwairah ce ta fadi haka a lokacin da ta ke kurbar shayin da Nafee ta hada mata mai kauri da dumi, share hawayen ta tai tace" Jabeeru ba abinda zance sai dai nace Allah ya qara maka albarka ninkin ba ninkin akan wadda ya maka, ina alfahari da kai a matsayin ka na dana, Allah ya karen kai daga sharrin maqiya" amsawa sukai dikka, Nafeema ba a barta a baya ba wajen taya murna da godiya balle mai jego kuma, kiran sallah je ya karade wajen tare da duhun da ya bayyana hakan ya nuna masu cewar magrib ta yi, miqewa sukai bayan sun gabatar da addua, sukai alwala mazan suka tafi sallah matan sukai a gida, bayan ya dawo ne ya dakko kaza a akurkin su, ya yanka biyu, ya kaiwa Innar mu, Nafeesa ce tace ni zanyi dan nasan yanda take son ta, dauka tai ta koma bangaren Juwairah ta dakko ridin da suka daka tare , sa madarar shanun dake aje a randar sanyi, dakko kayan qamshin da suka niqo harda minannas a ciki ta gyara kayan miya ta zuba wannan kayayyakin amma banda madarar, sai da farfesun ya dahu sosai sannan ta zuva madarar shanun, tana tafasa daya biyu ta sauke ta kaima Juwairah guda dayar dan dama dayar can ta batwa Innar mu ta dafa wa kowa a gidan a ci wannan ta mai jego ce, godiya ta mata Jabeer na shigowa ya zauna zai saka hannu, Nafee ta riqe" A'a Yah ga tamu can wajen Innar mu wannan nata ne, ita fa ta haihu ba kai ba, sannan na zuba mata maganin basir a wannan ka jira tamu" dariya yai sosai har yana kama ciki," yarinya zaki bayani ne kice kawai Nafeesa na hada maki kayan da zaki warke da wuri ki dawo na dora daga inda na tsaya ne kawai, banqi ba in an hanani ci saboda ita ta haihu tai wahala ya kamata taci tai qat amma batub ace wani basir in haka ne ai na fita bair nifa namiji ne" dariya sukai dika. Wajen jaririyar yaje ya dauke ta yana kallon ta yana mata wasa, wanj farinciki yake ji, nan take ya hau mata hotuna, yana gamawa ya danna kiran Abban su Suwaiba, lokacin duk suna tare har Goggo Sarai, duk da ba wani sake mata kowa yai ba amma sun rage gudun ta, sallama yai ya sanar da shi haihuwar, cike da murna kowa ke amsar wayar suna gaisawa, amma Juwairah sam taqi karbar wayar wai kunya take ji, dariya suke ta maya Suwaiba tace sai gobe zasu zo, dik da mamakin dake zuwatan Jabeer Juwairah Da Nafee bai hana su suma sakewa da ita aita hirarn ba, bayan sun gana ne Juwairah ta dauki pilon da aka kawo mata dan ta zauna ta jefawa Jabeer, tana.buga qafa cike da shagwaba" ni baka fadan zaka kira su ba kawai sai dai naji kana waya, kuma wai Abbana ka fadawa na haihu, wayyo ni Allah da wanne idon zan kalle su?" " da idon da kk kallen a daki ki ka kuren su kina lumshe su a daka lokacin inaa....." bata san sanda ta miqe da sauri ta damqe bakin shi ba, tana kallon inda Nafeesa take cike da kunya , duka ta kai mai mai zafi a qirji,ya ko yi qara, Nafeesa ce ta fita tana ta dariya" Yah Jabeer Allah mun bata" ta tashi daga jikin shi zata tashi, saurin kamo ta yai tana tirjewa" A'a faaaa ba zan iya da shagwabar nan ba bayan kin san ke ba lafiya gare ki ba, ki hakuri dan Allah ba zan sake ba kinji" kama kunnen shi yai alamun ban hakuri,murguda baki yai ta tashi ta shige daki ta dau jaririyat dake kuka ta fiddo nono zata bata, ga shi ya qura mata ido qurrrr, tura mai tai gaba "ni wannan kallon ya ishen, tinda ka gama naka turn din this is hers pls let her enjoy ita" ta qarasa tana murguda dan bakin ta, sakama bbyn nono tai a baki taji wata azabar zafi na tsotso, janyewa zatai amma jabeer ya hana ta ta hanyat kai bakin shi nata, rasa wanne zata dauka tai, zafin bada Nonon ko kuma kiss din da take karba????





Makaranta ku zaba mata daya...... lols😂😂😂
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA. 💅🏼





BY HAERMEEBRAERH




Page 29:





Alhj kallane ya kalli Alhj salihu yace, " kai nifa ba qungiyar da zan bari, haba me akai da maza inji karuwa, har yanzu fa da quriciyar mu, ko hamsin bamu rufa ba, akwai sauran rayuwa gaba na tuba" " hmmmm Kalla knan kai abokina ne mun taso tare dakai, iyayen mu da yan uwan mu mun bada su ta wannan harka, kana ganin zunubin bai isa haka ba? Tin da ba yanda za ai mu dawo da su? Ka duba fa in bamu tuba ba yanzu kowanne lokaci mutuwa na iya zuwa, ita bata sallama bare qwanqwasa qofa in......" " malam dakata, yqu in da abin da kazo kenan, i am very sorry to disappoint you, cos i am not ganna buy this shit, akan me ina tsaka da jin dadin rayuwa ta kace na koma rayuwar talauci, bayan kasan sharadin fita daga qunyiya mai da duk abinda ka mallaka ne daidai da allura ba a yarda ka aje ba, me na tanada wanda ba daga qungiya bane? Haka sidda madalaqan kasa na koma almajirin qarfi da yaji, kan kuma ka fita karka manta sai an yi asiran rufe maka tinanin ka na gidan Oga zaks da qungiya gaba daya wanda a kallah zai kai nan da sati uku, kai ka san dan mun riga da an bamu daukaka a qungiya ne yasa akai mana wannann alfarmar da qananan yan qungiya ne kashe ka za ai ko tinanin nan kai, ni dai ina nan kai kuma Allah ya taimaka ka fita lfy, amma ka sani sisina ba zan taimaka maka da shi ba in ka talauce, abotar mu na nan har yauma ta nade" baza babbar rigar shi yai.ya fice ya bar Alhj Salihu da tinani, wata zuciyar na kwadaita mai ci gaba da rayuwar hutu, daya ban garen na nuna mai illar hakan, in ya ci gaba da zama dan qungiya yakai soyayyar Suwaiba inaa? Kaiii daya rasa abar son shi gwara ya hakura da qungiyar nan Allah zai kawo mai wata hanyar, miqewa yai, yana miqewa wayar shi ta hau ringing, dubawa yai yaga kiran Alhj Kallah, tsaki yai kamar ba zai dauka ba, dan abin da ya mai dazu ya sosai ran shi sosai, amma sai yandaga yaji ko ya canja ra'yi ne zasu fita tare, yana dagawa yaji wata muryar daban da bai san ta waye ba" waye kai ina mai wayar?" " ranka ya dade mai wayar Allah ya mai cikawa yanzunnan ya samu hatsari wanda gaba daya kan shi ya fashe, sannann qafar shi ta dama ta karye" " innalillahi wa inna ilaihirra ji'un" kalmar da yake maimaitawa kenan, ya kashe wayar ya zauna, qarar message ne yashi, cikin tashin hanakali ya duba sai yaga address din inda Kalla yai hatsari aka turo mai, kamqr wanda aka ma allura haka ya miqe yana fadin" Allah na tuba ka yafeni, Allah ka gafarta min ni Salihu daga yau nai alqawarin tuba daga zunubaina na daina harkar nan ko zan rasa raina ne" kuka hake matuqa haka ya kai ga motar shi ya tada yai inda aka kwatanta masa, wayar shi ce ta qara ringing " Oga Zaks" shine abinda ya gani, tsaki yai ya daga" Salihu kaji abinda wani ta fadan? Kana ina yanzu haka, da gaske ne Kalla ya mutu?" " nima ban sani ba sai na isa wajen na gani, ka oashe na kusa isa ga mutane can dai an taru.a wajen sosai" kashe wayar yai ya qarasa, yanda ya ga abokin nashi take ya yanke jiki ya fadi, wasu je a gefe suka taimaka mai da ruwa ya farfado, yai wajen shi a guje yana kuka, riqe shi mutanen wajen sukai suna bashi hakuri, umarni ya basu akan su taimaka mai su daga gawar akai masallaci mafi kusa a mai wanka a binne, kawai dan basu da kowa, haka ko akai , waya ya zaro ya sanar da Oga zaks, jikin Oga zaks yai sanyi amma dake zuciyar ta dake ko kuka bai ba, sai dai ma kawai ya mai taaziyya ne kawai yace in an kai shi yaje yana son ganin shi, kashe wayat shi yai yace" ba dole ma na fita ba, ai ko ba komai Kalla yai wa qungiya hidima, ya cancanci azo kan gawar shi a mai addua amma wai in an kai shi na je, ko baka ce ba zaka ganni kuwa" share hawayen shi yai shima yabi bayan yan tsiratun mutanen da suka gama rife Kalla a makwancin shi na gaskiya,mota ya fada yai gidan shi, tattaro duk wata dukiya tashi yai, yaje ya dakko ATM cards din shi, da makullan motar shi, da takaddun filaye da gidajen shi kamfani da komai ya zuba a motar, ya sa kai, bai zame ko ina ba sai qofar gidan Oga Zaks, yana isa a ka ya tsaya ma Oga Zaks , " ya haka Salihu, zaka zo ka tsayan akai kamar wani sanda" " miqa mai komai yao da suke a wani akwati, ya ce" Oga ina son barin qungiya ba dan komai ba sai dan ina son na koma tsaftatacciyar rayuwa, abinda ya faru da Kalla ya qaran son barin qungiya" take ya kwarorowa Oga Zaks duk abinda ya faru da Kalla da shi kafin hatsarin da yai, nqn danan jikin Oga Zaks ya dau rawa, qaton cikin nan kamar ana buga ganga haka yake qara, maganganun sun shige shi sosai, " To salihu ba za ai haka ba ka fita kai daya, yau kuma a yanzu zan tara mutanen mu, na sanar da su, wanda yaga zai fita ya biyo mu dan nima fita zan, wanda yaga zai zauna ga waje, amma zan so yanda ni ne na assasa wannan qungiya na rusa ta, dan ko na tafi zunubin xai bini" wani dadi ne ya lillibe Salihu dan bai zaci hakan ba, ya zaci zai sha wahala kafin ya amince mai, waya yasa ya kira mutanen su,kusan awa biyu sika dauka kan kowa ya hallara, ganin fuskar Salihu da ta sha kuka ya badu mamaki, nan take ko Oga Zaks ya fara zayyana masu komai, cikin qanqanin lokaci wasu da dama suka aje makaman yaqin su, wasu kuwa suna ganin ai su akwai sauran lokacin tuba,tsawar da Oga Zaks ya daka masu ce ta dawo dasu daga cece kucen da suke ta yi" na yake hukunci wannan qungiya rushe ta zan, wanda ya sake kafata shi ya sani, amma ni kam na gama , dan haka daga gobe zan rushe ta, tsakanina da dodo ko kashe ni yai na kubuta da ikon Allah, fatana Allah ya gafarta min, ya ba wa wadan da na zalinta ikon yafe man a filin qiyama" sai ga Oga Zaks na kukan nadama, basu rufe baki ba suka ji gidan na wani irin qara, mai firgitarwa, haba mana xo kuga gudu, kowa na gudun ceton rai, Salihu ne ya ke qoqarin taimaka wa Oga zaks su gudu, amma ya dakatar da shi" Salihu kai ta kan ka kawai, ni nasan tawa ta qare, da wannan uban tumbin nawa kk tsammanin samun gudu a gareni? Ka dube ni fa ka gani nayi ka bakwai, ka barni kawai, abin da na aikata zan girba, i am willing to give my life for urs, coz i started everything, i think it has to end with me, just go, run for ur lyf, and pls don't forget to pray for me, ask Allah to have mercy on me" tura Salihu yai da qatfi a daidai lokacin da wani qaton baqin zaki ya fito daga wani baqin daki, yayo kansu, Salihu diba yai da gudu ya bar wajen, Oga Zaks salati kawai yake, ya cika wando da fitsari shataf, tsoro da tashin hankali ya ganshi qarara, tinawa yai ashe haka wadanda suke ba dodon suke ji kan su mutu, take yaji qirjin shi na wani mugun bugu, cafka zakin nan ya kaiwa wuyan shi ya hau cinye shi, Oga Zaks kam an tafu inda Kalla ya tafi, Salihu kuwa gudu yake kamar me , mota ya gani da makulli jiki me ita wataqila tsabar tsorata ne ya hana shi ci gaba da tada ta, dan harda takalmi qafa daya a ciki, da alamar danshi a sit din, maybe fitsarin shima ya sake🤔 take Salihu ya tada motar ya debi hanyanyat kano.








Sin gama gyara gidan tsaf, sun ma iyayen nasu girki, wanka sukai, suka gyara jikin su, jikin Suwaiba duk ba kwari haka take jin faduwar gaba, Saudat kam ita in banda sharar dakin su ba abinda ta tsinana, komai kusan Salma da Suwaiba ne sukai, gaban ta sai tsananta bugawa yake, amma sai tai ta maimaita addu'o'i a bakin ta, haka itama Suwaiba, bayan sun shirya ne suka dauki hanyat gidan Juwairah me jego, sun isa daidai Jabeer ya fito riqe da towel din da yake gasa mata jiki musamman cikin ta da bayan ta da shi, kallo suka bi shi da shi , saka makon ganin Juwairah ta fito tana" Ni dai gaskiya a canja min me yin wanka, kai gaba daya kamar ba wankan ne ke kai ka.......... " maganar ta maqale dan ganin yayun nata na shigowa, niyyar ta ta koma bandakin dan juyawa tai tare da damqe bakin ta, zata shige, Saudat ce ta ruqo ta da sauri tana dariya," Me Yah Jabeer din ke maki? In kina son a canja maki mai wanka sai na dinga maki, amma ni sai ruwan ya tafasa sau uku sannan zan amfani da shi" zaro ido tai waje tace" A'a Adda Saudat a barmin Yah Jabeer din mu lallaba a hakan" dariya suka kwashe da shi, Jabeer yace" kuji yarinyar nan fa, wai zata lallaba a haka sai kace wani mugunyar nake mata" Nafee ce ta amshe da" Hmmmm Yah ai shiru kawai da wannan maganar amma ko dazu naji qarar ta" hararar ta yai yace " Suwaiba ku shiga ciki mana kuka tsaya a waje" shiga sukai har me jegon, Nafee ce ta miqe sakamakon kiran ta da Innar mu ke yi, zuwa tai ta bata wani kwanika biyuo ta kawo wa juwairah, amsa tai tai ta tafi bangaren juwairah, sallama tai ta shiga suna ta hira kowa na yava kyaun jaririyar da sunan ta" wannan suna na yan gayu anya kowa zai iya fada" cewar Salma, dariya Nafee tai da ta qarasa aje kwanon gaban Juwairah dake shafa man kade a cikin ta," ai jiya sai kun sha dariya dan daga Innar mu har Abban mu basu itmya fada ba" " ai ko wannan suna zan so jin shi a bakin Goggo" cewar suwaiba, dariya suka bushe da ita dikkan si sun san a kwai case dib fadan Abrar a bakin Goggo sarai, Juwairah ce ta gama shiryawa Suwaiba ta daure mata cikin ta, sannan Jabeer ya shigo dauke da plate da Spoon da cup sai tea spoon, gaishe shi sukai dika ya amsa tare da yi masa barkar qaruwar da aka samu, godiya yai ya isa gun kwanukan ya bude, farfesu ne na naman qaramar dabba, yasha kayan qamshi irin na jiya harda ridi, gefe kuma kabewa ce innar mu ta dafe ta tai laushi ta dame ta tai kamar kunu, sannan ta zuba maya madarar shanu mai matuqar yawa sai zuma, zuba mata yai a cup din ya zuba mata naman a plate, " oya maza taso ki ci ki shanye, dan bana son kina zama da yunwa" turo baki tai gaba, " ni fa na qoshi, dazu da asussuba na qarasa naman jiya saboda yunwar dana tashi da ita, yarinyat nan ci gare ta kamar Innar ta Salma" dariya suka dauka da dikkan su" ai ko baki isa qoshi ba da dan ragowar naman nan, in baki matso kin fara ci ba zan maki dura gaban su, dan dora ki cinya zan na maki irin na kwanaki" zaro ido tai waje sai gata a qasa ta saka pilo ta hade qafafun ta waje daya ta miqe su( haka ake so mai haihuwa tana zama, kai ko ba haihuwa ba a son zaman nan na ware qafa, kabewa da madarar shanu da xuma duk wadda ta hada ta zata bada labari bazan ce komai ba🙊) kaiwa baki tai ta fara ci dadin da ya ziyatce ta bata san sanda ta cinye ba ta shanye kabewar dika, " just like a gud gurl" kissing din gefen fuskar ta yai ya dauke kwanukan zai fitar Salma tai saurin karba, " haba yayah muna nan ai sai ka bar mana aikin in mun tafi ka ci gaba" muemushi yai ya sakar mata yace" ni bari naje.na shirya zan wuce Abuja yau zuwa qarasa shirye2n komawar mu bayan suna" anan ya sanar da su komai game da aikin da ya samu, murna suka taya shi , da fatan alkairi, fita yai yai wanka, ya dawo zai shirya Juwairah ce ta tashi taje, yna shiryawa suna.hira tana hada mai kaya a jaka, duk da hana tan da yau.sai da ta hada masa, bayan ya gama ne ya dauki Abrar ya mata addu'a yau kissing din ta ya hade bbyn da maman ya rungume, daidai ya sake ta yai gaba ne ya dawo" Af nayi mantuwa" " me ka manta honey?" Matsawa yai kusa da ita ya janyo ta jikin shi yana mata kallo qasa2," No no no u can't do this now pls, Adda Suwai ba is here, Adda saudat is here, and Salma too, pls kai hakuri har ka dawo,

Please Login or Register in order to submit comment