Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta daka yar daddawa kadan dan ba isasshen maggi to daddawar zata taimaka abincin yai dadi , nan da nan ta kammala ta fada wanka , (Hikima r gyara daki kenan a wajen mace kan ta fita, in kk gyara gidan ki tsaf in da hali ma ki girki kan ku fita, da kin dawo to wanka zaki ki zauna ki huta, ba ruwan ki da zama cikin qazanta, da kuma taraddadin aiki a gaban ki) tana fitowa daga wanka Jabeer ya dawo, fita tai ta amshi ledar hannun shi ta ajiye sukai barka da dawo war su yanda suka saba, sannan ta ja shi bayi, sabon wanka ta sake domin cewa yai bata fita ba sai ya sake mata, tana dariyar gano wayon shi da tai tace" to shikenan ka gama nima sai na maka naka muje muci abinci dan na gaji yau da wuri zan kwanta" " tab yarinya ku daina zancen vacci ma in zaki bari" yana yi yana matsa cinyoyin ta da yake wankewa, yar qara tai ta shagwaba ta fada jikin shi, tana goga cinyar ta a jikin shi," Yah Jabeer akwai zafi fa" yanda tai maganar a saitin kunnen shi wani abu yaji har tsakiyar kanshi da qafat shi, janye ta yai ya kiqa mata soson" yi sauri ki wanke ni, nima ba zan iya jira ba, dariya tai ta amsa tana mai wankan cikin wani salon da ya amshe soson ya aje gefe ni dai ganin halin da yake neman jefasu yasa ji fecewa πŸ˜±πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ




BY HAERMEEBRAERH




This page is for u our missing Sawwama Qawwama, i and all ur fans ,tum hari yaad aa rahi hoo, we wish u will be back soon dearπŸ˜₯❀











Darene yanzu a cikin garin Abuja, a wani hotel da su Alh Salihu suka maqale wa, tare da 'yan matan su da bazan iya tantancewa arna ne ko musulmai ba, wata naji an kira da 'yar Gwal, daga nan na gane hausawa ne, amsawa tai ta juya, dayar ta mata nuni da ido, murmushi naga sun sakamr ma juna, " mene ne naga kuna wani dariya kamar wasu wadan da suka cinci damin kudi a qasa?" Inji Alhj Kallah kenan da ya ga sanda sukai hakan," 'Yar gwal ce ta hau cinyar Alhj Salihu tana wani karairaya tana shafa shi" Alhaji na kudi muke so, gaba daya qawayen mu sun wucemu a komai, bayan muna tare da ku, gaskiya zai zama abin kunya ace ko motar hawa bamu da ita" tana magana tana kai bakin ta jikin nashi, wani irin nunfashi Alh ya fitar da bai san yana ruqe da shi ba," Haba 'Yar gwal yanzu dan wannan shine kuke wani abu kamar baqi, ai in kuna son abu kamar umarni zaku bamu kuga an cika, dan haka,..... kan ya qarasa kamar jira suke suji zaa biya masu biqatar su, suka miqe tsaye suka ja su daga clube din dake cikin hotel din zuwa dakunan hotel din , tin a hanya suke romancing din su, naje leqawa sukai slamming qofar a fuskataπŸ˜₯ haka nai baya na koma gidan Suwaiba naga wainar tmda take toyawa.

Hango ta nai tana zaune ta baza kaji a gaba da fresh milk a gaba tana diba, hankalin ta kwance, tana danna wayar ta, bayan ta gama taje tai wanka tai brush, ta saka kayan hacci, amma sam bata jin bacci, komawa tai palon ta kunna kallo, tqna kallo tana duba lokaci, wannan rayuwa, ace miji ba zai dawo da wuri ba sai dare ya raba? Tashi tai ta dakko fruit salad data hada ta saka a fridge, ta zauna tana kallo tana sha, bayan ya qare ne, ta aje bowl din a gefe, dai hamma take tana miqa, duk ta gaji da zaman shirun, wayar ta taji tana ringing, miqa hannu tai ta dauka, "Saudat love" shine sunan da ya fito akan wayar, " Hey sis"
"Hey"
" ya kk, da yayan nawa?"
" muna lfy, Ya Alhjn ki?"
"Muna lfy"
"Dama kiran ki nai naji ko Baby na gidan ku, tsoro nake ji, gidannan ya min girma, duk dare sai naji kamar kirana ake," ta fafa cike da tsoro,
" Sis kiyi hakuri baya nan, nima zaman jiran mine nake, duk yanda akai suna tare, ki kwantar da hankalin ki ki mori abinda ya kawo ki, tin kan lokaci ya qure maki" amsawa tai da"to" sallama sukai suka kashe wayar Suwaiba ta tashi tai daki, bata jima da kwanciya ba, lokacin qarfe 2:45am ya shigo bakin shi duk warin giya, tsabar kwarewa da sukai ba sa layi, sai dai a gane ta idon su, da saurin fushin su,Suwaiba ce ta miqe ta nufe shi, " wai wannan wanne irin wulaqanci ne Sweethert, tinda nazo gidan nan i can't remember d last time we had xxx, amma da nai magana kace lokacin ban da lfy ne, yanzu danaji sauqi ka kasa sauke nauyin dake kan ka, amma kai da dikkan alamu har yanzu kayi auren ma wasu kk bi a waje, ga giyar da kk sha wadda ni ban san kai din dan giya bane, wannan ai iskanci ne" ta fada tana daga murya tana masifa" ni kk kira dan iska? Ni kk kira dan iska ko, ba dai ni kk cewa dan iska ba ? Yau zakiga iskanci ganin idon ki Suwaiba" miqewa yai ya janyo ta ya hau duka kamar an aiko shi, a haka ya cire mata kayan ya wurgar duk ya yaga su, aiki ya fara akan ta full time, and non stop, gaba daya jikin ta yai tsami ga duka , ga xxx din da ba tai niyya ba, kuka take tana" kai hakuri nice yar iskar ba kaiba, ba zan qara ba , ka taimaka min, ka duba auren soyayyar da mukai da kai" kwade bakin ta yai yace " auren soyayya ko auren kwadayi?auren kudi? Karki zaci ban san kr da uwar ki kwadayayyu bane da yan uwan ki? Ina sane da komai, ni ba qaramin mutum bane" qara wurgata gadon yai da take qoqarin guduwa ya kwanta a jikin ta, nan da nan bacci ya dauke shi, kuka take sosai jikin ta na ciwo, haka ta tashi ta ja jiki da kyar, ta tafi toilet, ruwan zafi ta hada mai zafi sosai, ta shiga, tana shiga tai qara dan azaba, a haka ta gasa jikin ta taji dadi sosai, nan da nan bacci ya fara diban ta a xaune a ruwan, fita tai taje ta saka wasu kayan ta koma daya dakin ta kwanta, ta rufa, nan da nan baccin wuya yai gaba da ita, da asubar fari Saudat ta kira ta a waya tana kuka, Ta sanar da ita irin cin mutuncin da Alhn ya mata itama, sata yai tai ta mai tausa, har wayewar gari, data fara gyangyadi ya zabga mata mari, ta dora daga inda ta tsaya, kuka sukai tayi, ba mai lallashin wani, itama Suwaiba labarin nata ta bata, sannan sukai akan gobe zasu hadu in mazajen sun fita, qoqarin shigowa ake ta danne wayar ta kwanta tai lamo kamar me bacci, qarasa shigowa yai ya zauna kuda da ita, " Haba my Suwai hakuri zaki, ke ma kin san in rai na y baci bana son a cika tambaya ta musamman maganganu na rainin wayo, auren kudi kikai kuma ga kudin nan, to meye na damuna sai na maki wani abun?" Kuka take ta gefen ido bata ce komai ba, janta yai jikin shi yana shafata, take ta fara saukr ajiyar zuciya tana hamma, don bacci take ji sosai, kiss ya mata ya maida ta ya kwantar yace shi zai fita, daga mai kawai tai ta koma ta lumshe ido, bayan ya fita ne tai baccin awa uku ta tashi tai wanka , ta hada abin karyawa mai rai da motsi da tea mai kauri ta ma manta jibgar da ta sha, taci tai nak abinta, Wayar ta ce tai ringing ta amsa da " ku barta ta shigo qanwa ta ce" ta kashe, Wajen kamar minti 5 Saudat ta shigo, cikin shiga ta alfarma, ga wata arniyar mota da ta zo da ita driver na tuqata, ta ci gold ko ta ina hannu da qafa da kunne, dan harda sarqar qafa suke daurawa, isa tai itama kusa da sister din ta akan dinning table ta ja plate ta zuba chips da kwai da farfesun naman kan rago, sai tea da ta hada itama mai kauri ta hau sha, sai da ta gama sannan ta yada kai baya ta zame kadan daga kujerar tace" Sis ina cikin tashin hankali wanda da dikkan alama kema haka ne, dan ga jikin ki ya nuna, dubi fuskata" ta fada tana mai nuna mata fuskar ta da tai jawur ta kumbura, sai rufewa tai da mayafi da ta shigo," ga zaman yunwa da nai dan jiya kwata2 kasa cin komai nai"
" yar uwa bari kiji, ki cire komai a ranki shawarar da zan bamu shine mu cire rai a son sai sun zama mutanen kirki, tin da dai ba halin su bane, mu zauna mu mori dukiyar da muka zo Abuja domin ta, mu xama manyan hajiyoyi,mu bawa maqiyan mu kunya, dan ni kam kin ganni nan, in ba jiya dana sha jibga ba, bana wasa da abin ci ko wani nau'i na jin dadi, sannan kuma da kk ganni nan haqqina na aure in daga yau ya ce ya daina ban ba zan damu ba, domin kuwa akwai hanyoyi da dama da zan iya maganin matsala ta, wanda na san kema kin dan su ba sai na tsaya bayani ba, i hope ba zasui gangancin turamu wannan stage din ba, zasu na daure wa ko once in a while ne suna biya mana buqatun mu, to kinga ba mu da matsala da bin matan su ko kuma wani abu mai kama da shan giya, sun dade ba suyi baπŸ™„ dan ba zan qara yarda a taba lafiya ta ba, an gama daga jiya" " kaiiiii yar uwa wannan shawara tayi wallahi" tafawa sukai suka koma palo duka debo dambun nama da juice suka dawo palo suka kunna kallo, sunayi suna hira qarshe waya suka dauka, suka hau kiran Goggo Sarai, suna waya, a lokacin suna tsakar gida dikkan su, Mama Bilki, Abban su Juwairah, Ammar, da ita kanta Goggon, wanki Mama Bilki keyi na kayan Abban su da na Ammar, ita kuma tana girki, wanda ta dade da dena cin abincin gidan sai dai tai nata, su kuma suci nasu, hakan da tai yada Abban sun ya samu ragi daga dawainiya, shiyasa ma wataran suke samun abinda suke aikawa Juwairah dan Mama ta kula da rayuwar da take ciki a zuwan da tai sau daya, amma da ta tambaye ta, qeqasa qasa tai tace ita lfy lau komai yake tafiya masu, addua tai mata kawai amma tasan akwai wata a qasa, cikin firgici ta daga kai daga tinanin ta sakamakon......

...............
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ




BY HAERMEEBRAERH







Hey guys i am sorry yesterday i fogot to number the page, it suppose to be page 10 and this is page 11. Thanx me love u XoXo.




Page 11:







Wata qara da Goggo Sarai ta sake da sunan dariya, dan kawai ta ja hankulan su,"Hahhhhaaaaa kaiiii amma naji dadin haduwar ku gaba daya tare, ikon Allah ana can ana cin amarci sai yau aka samu haduwa kenan, to ya masu gidan? Ya rayuwar hutu da jin dadi?"
"Lfy qalaou Goggo, ina Abba?"
" Hmmmm ga shi can wajen waccan sallamammiyar matar tashi da ta shanye shi"
" Bashi mu gaisa kar yace bamu neme shi ba"
" Aiko bada wayata ba ehe ku kira shi a yar rakani kashin shi kawai"
Tana fada tana hura hanci tana turo dankwali gaba irin na fitsararrun matan nan? Kada kai Abban nasu yai yace" Allah ya kyauta" murguda baki tai kamar wata qaramar yarinya, irin na rashin kunyar nan,( dan kunsan murguda bakin ma kala2 ne, akwai sexy murguda baki mai daukan hankalin oga, yaji dole sai ya kai nashi bakin a naki sabida yanayin yanda kikai yi shi da salon jan hankali, sannan akwai na rashin kunya kamar na Goggo sarai dai) miqewa yai da niyyar fita sai wayar shi ta hau ringing, dagawa yai da sallama, su Suwaiba ne, gaida shi sukai kamar ba sa so ya amsa tare da tambayar su gidajen su," hhhhhh Abba do u really have to ask ? We ar fyn, komai normal kamar dai yanda ka sani Abba mazajen mu masu kudi ne, so ina ganin ai bamu da wata matsala mu"
" Suwaiba ni mahaifin ku ne ba zan gaji da maku nasiha akan ku bi duniya a sannu ba, yau in kaine gibe ba kai bane, dukiya da abinda ke cikin duniyar nan ba komai bake face rudin shaidan ga wanda ya mai da su abin bauta, kuji tsoron Allah a lamarin ku, Hello ! Hello..... shiru yaji ashe sun dade ma da kashe wayar tin da ya fara wa'azi suna ta surutan yanzu zai takura masu, mamaki je cike da zuciyar shi, " yarannan ni suka kashewa waya?" " Abban su kai hakuri komai zai daidai ta da qarfin addu'ar da zaka dinga wa iyalan ka, Allah zai shirya maka su inshaa Allahu, adduar iyaye amsasshiya ce a wajen Allah, Allah ya shirya mana zuria" " hmmmmm Ameen Gimbiya ta Allah ya albarkace ki da zuriar mu duka" dadi ne ya kamata mara musaltuwa a duk sanda ya mata wannan adduar" Ameen a bin sona" murmushi sukai, nan da nan yaji baqin cikin shi ya tafi, ruwan wankan da ta saka mai yaje ya shiga yai wankan shi, ita kuma ta fara qoqarin dora madu abinci.( magidan ta ku na qoqarin yi wa matan ku godiya da addua musamman ta nema masu albarka a wajen Allah, in albarkar nan ta wanzu a garesu ta shafe ku, da xuriar ku kenan, mata ku dinga dukkan abinda kk san zai faranta masu rai sui maku adduar, soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa).










Nafeesa ce ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atampa, tayi kyau sosai ta taho bangaren su Juwairah" matar Yayah ya naga baki shirya ba kin saka dan guntun wando da vest an faka gashi gefe?" " Nafeesa kenan ina ga alama kin manta yau Yaya da wuri zai dawo sannan yau ranar dana ware domin gyaran lambu na ne ko? Ga girki da zan da wasu aikace2n, kuma sanin kan ki ne ni fa yawon shiga nan shiga can dinnan ba son shi nake ba, shike kawo mace ta daina kula da iyalan ta da gida tana qarewa a titi" " hakane kam gaskiya, ni dai zan tafi gidan Shamsiyya na gaida ta, dan na mata alkawarin zani yau din, na zaci zamu tare ne tinda naga ke kin dade baki je ba, sai na dawo to" " to ki dawo lfy, ina gaida ta da yaran" fita tai ta tafi, ta je gidan Shamsiyya inda ita shamsiyyar yaran ta biyu mace da namiji, Farha da farhan, goyo take tana goyon macen , gaba daya gidannan sai a hankali, komai da kan shi yake zama, bai da muhalli, shiga tai palo ta zauna da sauri ta miqe tana duba skirt din ta daya jiqe, hannu ta kai hancin ta taji wani mugun xarnin fitsari, da sauri ta kauda kanta ta fita tsakar gidan,ruea ta sa ta wanke hannnun ta saka a skirt dinta tana masifa" ni gaskiya shiyasa bana son zuwa wajen ku shamsiyya, ga gida har gida Allah ya hore maki amma sai uwar qazanta, duba dan Allah daga zuwa na xauna akan fitsari , ko da Juwaira bata haihu ba na san.abin da ba za a taba samun ta da shi ba kenan, yanzu haka saboda gyaran gidan ta da kula da haqqin mijin ta yasa taqi biyo ni, Juwairah nada lokutan yin komai, tinda ba za a hadu ace kullum zaka hada kowanne aiki kayi ba zaka gajiya, sai wanda suka zama aikin yau da gobe, dan Allah ki gyara, dan yana daya daga abinda yasa Baban Farhan yake neman aure duk.da ya fada maki amma kinqi gyarawa" kaiiii hajiya bala'i daga zuwa.sai wannan dogon karatu? To dan Allah ya kuke so nayi? Ga aikin gida gana miji gana 'ya'ya" sai ta fara hawaye wai ita a dole komai ya mata yawa, kama hannun ta Nafeesa tai suka koma palon ta zaunar da ita a kujera, sai da ta laluba wata taji ba jiqa ta zauna ta fiskance ta, " qawata ni ba wai ina maki fada dan ranki ya baci bane" " to dan meye? Saboda kowa ya tsane ni sai a dinga ce min qazama ? Kalmar qazama fa na da ciwo tsakani da Allah" majina ta sharba tana gige hancin da zanin ta, " to yanzu kingq hakan da kikai ni ba zan yi shi ba, da na goge majina da zani gwara na je na wanke hancin, ai in kk ji ance qazama akwai kalmar tsafta kuma ko? To ni so nake ki cire kalmar da kowa ke kiran ki da shi na qazan ta ki mai da shi mai tsafta, yanzu ki fa duba kiga Mama Bilki, kullum kk dhiga wajen ta kinga dai ta tsufa ko, amma tsabar qamshi da tsafta bazaki so barin wajen ba, come to think of it ba fa ta da kudi da wadata kamar ki? Dan Allah ki gyara ki rage son jiki,son kallo da karancr2n nan na zamani har sai kin gama komai sannan ki dauka ki fara,ina fatan wannan ya zama na qarshe da wani zai baki shawara ko za a zage ki akan tsafta, in baki gyara ba Abban Farhan yace maki zai qara aure kuma ya fara nema in kk gyara nasan bari zai dan matsalar shi dake kenan ba wani abu ba" " Na gode qawata, ba wanda ya taba zaunar da ni ya min bayanin ya shige ni" " ba godiya a tsakanin mu" murmushi sukaiwa juna shamsiyya ta miqe ta fara tattara kayan wajen data loda a kujera, nan da nan Nafeesa ta taya ta suka gyara gidan ya dau hake da qamshi, girki sukai mai rai da lfy kala2, wajejen la'asar Nafeesa ta bar gidan cike da tsaraba daga wajen shamsiyya, a ranar ta sha wanka da gaye, Abban Farhan daya dawo ya sha mamaki amma bai nuna ba, sai ya nuna mata matuqar jin dadin shi, dakuma yabawar shi tashi yai yaje dakin shi yace " ina xuwa" wata sarqace ta gold mai kyau ya zagaya ta bayan ta ya daura mata suna kallon madubi, dan harda koyawa yaranta baccin wuri sai da Nafeesa ta koya mata, godiya tai ta masa shima yana godiya, ba a jima ba taji zancen aure ya rushe, sai dai ya sanar da ita cewar" Baby ki kwantar da hankalin ki dan ni ba mai ra a yin mata biyu bane ko sama, tsaftar ki da rashin tsaftar ki in ni me ra ayi ne ba zata hana min yin aure ba, na fada maki ne dama dan ki gyara mu more ratuwar auren mu yan da ya kamata" taji dadi sosai inda ta qudurta ma ranta xama mace mai tsafta ta bugawa a jarida, yan dakowa ya mata tambarin qazan ta sai an buga mata na tsafta in Allah ya yarda. Ni ko na ce to Allah ya yarda ya shiryemu mu gane tsafta na da kaso mafi tsoka a rayuwar aure.








Bayan Juwairah ta gama komai ta yi wanka ta kwanta tana hutawa, tasbihi take ta yi ga Allah bacci ya dauke ta, tafiyar tsutsa yake mata a qafar ta ta farka idon ta na qara lumshewa, juyi tai ta cusa kanta a cinyar shi ta ci gaba da baccin ta, a hankali ya janye ta dan ya kula a gajiyae take, yaje ya cire kayan shi ya aje inda take aje masu kayan wanki bayan ya ninke, ya tafi wanka dan har da ruwan wanka ta aje mai, bayan yai wanka ne yaga kamar bata ci abinci ba ya shirya ya zo ya qara tashin ta sai magagi take bacci ne sosai a idon ta a haka ya daga ta ya zubo abincin yana bata yana ci duk abinnan da ake idon ta rufe yake, " Yah Jabeer ka dawo?" " Eh na dawo princess" " Sannu da xuwa" "yawwa, meke damun ki ne yau?" " bacci nake ji na gaji ne sosai, ga jiri danake ji, tin shekaran jiya kuma sai naji cikina na ciwo, kamar ana min motsi a ciki" har yanzu ta qi bude idon," Subhanallahi, gobe zamu asiniti mu ga likita dan shiyasa kk ji kwanaki ina ce maki sai naga kamar baki da lfy, abinda ke kwantar min da hankaki kawai ganin yanda jikin ki ba wani damuwa sai kyau da kk qarawa ma, nan din ki har wani kyalli suke" hannun shi ya kai saman rigar ta yana shafawa, a hankali ta janye hannun shi ta juya baya ta ci gaba da baccin ta, wani yawu ya hadiya, ganin yanda hips din ta suma suka ciko sosai kamar sui magana, tashi yai ya maida plate din ya wanke bakin shi da hannu ya rufe ko ina ya dawo" princess ko dai fushi kk ban dawo da wuri ba yanda na saba? Shi ne kk share ni kk son yin bacci?" Shiru yaji, matsawa yai jikin ya ya janyo ta, bacci yaga tana yi sosai, bai so haka ba, gaba daya ta rikita shi, amma haka ya hakura dan yasan ba halin ta bane kyale shi koda tana cikin fushi ne, ja masu abin rufa yai yai masu addua ya shafa masu, suka kwanta........
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ



BY HAERMEEBRAERH

Alhamdu lilLAAH ala kulli halin, naji sauqi sisters na gode da kulawa, Allah ya barmu tare da alkhairi mara yankewa. ME LOVE U XOXO❀


Page 12:





Da asuba ta tashi ta duba taga har ya fita masjid, addu'ar tashi daga bacci tai " "Alhamdu lilLAAHi alladhi ahyani ba'ada maa amatani wa ilaikannushour" sannan ta sakko daga gadon ta je tai alwala ta dawo ta gabatar da raka'atanil fajr tai sallar subh,tai azkar din safiya, tana idarwa tai azkar din ta, tana gama wa wanka taje tayi ta sake yin brush, gaban madubi ta zo ta warware kitson da tai da yamma, guda biyu akan ta sakamakon ba ta son kitso sosai kuma shima Yah Jabeer din nata yafi son tana mai adon gashin haka ba tare da ta kitse ba( yana da kyau mace ta iya yin kitso biyu irin na indiawan nan da muke gani ana raba kai biyu a kwantar gefe da gefe a dame shi a kitse sai yai matuqar kyau in ke mai santsin gashi ce ma zakiga har sheqi yake da dare ake wannan kitson bayan kin gama wa oga kwalliya, ma'anar yin wannan kitson na farko dai zaki bacci ba tare da kanki yai buyaya ba, kinyi muni, da safe zaki tashi kan ki tsaf da shi, bai barbaje ba, sannan kuma in ma kun samu kusantar juna da me gida kin yi wanka kanki ba zai na lalacewa ba nan da nan kiji mata suna kai yasha ruwa gashi na.zubewa, akwai fa'ida sosai akan yin hakan da sai kin fara zaki gano su da kan ki) da sauri take yin komai ba son jiki, dan ba ta son sai ya dawo ne zatai wadannan abubuwan, ya na dawo wa daga masjid ya tsaya wajen Innar mu su gaisa, kamar kullum, riqe shi tai d surutai na ba gaira ba dalili, daga baya ne ta fara tura mai saqon dake ranta a wayon ce" Allah sarki Juwairah yarin yar nan akwai hakuri, kaga fa yanzu wata na wajen.shida kenan.da auren ku, qawayen ta sun haihu amma ita ko batan wata bata taba yi ba, amma bata damu ba, ko dake

Please Login or Register in order to submit comment