Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

keso kuma yake sonki Dan Allah !


Wannan shine taimakona akanki Aymanah! Amman hakan bazai kasance ba Saida yardarki dakuma cire son komawa gun iyayenki abinda zakisa aranki shine cimma burinki dakuma d'aukan fansa Kuma kisa a ranki koba yauba zaki koma ga iyayenki!"


Habeebty ta ida maganar tana sake dafa kafad'una had'i da saukar da numfashi!


Tabbas maganaganunta sun shigeni Kuma sun gamsar Dani Kuma ilahirin gab'o6in jikina da gangar jikina sun yarda sun amince da wannan batu na wannan baiwar Allahn Mai hangen nesa maikuma tsantsan imani yooto inba Mai imani bace ai bazatayi tunanin taimaka mun haka ba! Tabbas Allah yasan dalilinsa na maida akalan rayuwata zuwa garesu Dan haka nikuma *Aymanah mubin* inna cika 'yar halas Bazan bijirema rahmar Allah ba dakuma taimakon wa'innan bayin Allan dabazan ta6a iya manta tarin Alkairinsu a gareni ba!


Da wannan tunanin na numfasa had'i da sake wani qasaitaciyar a jiyan zuciya nace:

"Anty Fahimnah tabbas maganganunki sun shigeni Kuma sunyi matuqar tasiri agareni Kuma nayi naam dawannan zancen naki nagode ma Allah da ya maida akalan rayuwata zuwa gareku banida bakin godema ubangijina dakuma ku tabbas shi Ubangiji rahmar saa ba ragagga bace lallai Allah baya jarabta bawan sa da kowani kalan Jarabawa face ya tanadar Masa wani rahamammiyar saka mako Wanda da ace bawa tun farko zaisan wannan sakamakon dake jiransa bayan ya iya cinye jarabawar tasa da wlh kowani bawa a duniya a kowacce sallolinsa sai ya roqa Allah daya jarabcesa Dan kawai yasama wannan sakamakon da Allah ke tanadarma dukkanin bayinsa dasuka cinye jarabawar daya saukar agaresu!


Lallai Allah ba azalumi bane shi Mai qaunar bayinsane kaicho da wa'inda suke gudun rahmar Allah inda inya jarabcesu suke qin cinye wannan Jarabtar!

Allah kabamu iko da falalar bautamaka kai kad'ai kakuma Sanyamu mutuwa acikin addininka!


(Ameen ya Allah Aymanah)🀲


Murmshi anty Fahimnah tayi tana maijin wani kalan qaunata acikin zuciyarta tareda San qara taimakamun!



*********************


Masu karatu zance maku wannan shine mafarin Soma rayuwata cikin nutsuwa da tsabta aqasar daba tawaba! A qasar daban tab'a mafarkin zuwaba!


Yanzun a qalla nasama kimanin watanni 3 a qasar burki nafaso!


A wannan watannin abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda muguwar shaquwar data shiga tsakanina da dangin Dr Saad shaquwace da Inka ganni a cikinsu bazaka iya banbace cewa niba kowa bace a gidan ba sosai mutanen kirkin Nan ke qaunata da Kuma tattalina ko wannensu son farantamun yake da d'ebemun kewar tunanin dangina!

Dukda shaquwar tawa tafi zafi sosai ga Anty Fahimnah (habeebty) da Kuma mijinta Dr Saad su d'in na daban ne a zuqatana Dan har yakaiga mun chanzama junayenmu sunan da muke Kiran juna Dr Saad Yana kirana da *better half* nikuma nakierasa da *best* Dan Kam sunan namu yaci ace hakan muke Dan Babu Abu nawa danake 6oye Masa Kuma Shima Babu wasu damuwansa da baya gayamun hakan yasa sunan namu yayi qamari inda Habeebtyn sa kuwa kekkyawar matarsa Mai tsabtaccen hali ciki da waje ! Soyayyan Dr Saad da habeebty soyayyace Wanda aka shimfid'e sa cikin so da fahimtar juna abinda na lura da wannan ma aurantan shine sun yarda da junansu matuqar yarduwa shiyasa shaquwata da Dr Saad bai ta6a 6atama Habeebty Rai ba Soyayyarsu nikam har shaawa take ban Dan duk mafarkaina irin wannan soyayyar naso shimfid'awa agidan aurena!

Amman Ina all my dreams a shattered mubash ya d'auke wannan mafarkan nawa Kuma ya kwace wannan farincikin nawa!


Fatana Allah yaban wani Mai sona Dan Allah dukda inanan Ina dakon soyayyar yaah Hydar a Raina nasan yanzunkam yaci ace sunyi aure da marwa qilanma tanada rabo a tareda ita! Wannan tunanin kansa naji rauni acikin zuciyata Kuma yakansa nayi saurin danne mahaukacin son da zuciyata keson yima Yaah Hydar d'in mutumin daya tsaneni da bakinsa yasha fad'amun haka!


Oh ni Kuma haka tawa zuciyar ke kamun son Wanda bai dace tasoba!
Son da nake ma yaah Hydar Anty Fahimnah wacce nake Kira da *Yar uwa love* ita
Kuma tana kirana *Masoyiya* sosai shaquwa yake tsakanina da wa'innan bayin Allan!

Hakan yasa nabaiwa Habeebty Labarin son danake ma yaah Hydar takan cemun:

"Masoyiya komun kyawun d'a namiji dole sai ya ga wata yaji Yana sonta nikam Ina gani yaah Hydar ba tsananki bane yayi sonkine yasa yake maki hakan Dan yadda Kika ban lbrnsa kamar mutum ne Mara San raini hakan ne nake gani yasa bai nuna maki son da yake maki danke d'in cikin qanensa qaramace! Karki damu in Allah yayi mijinkine ko ba Marwa ya aura ba! Allah zai kawo wani hany'an maidoku ma aurata! "


Wannan zancen natama yakan sauqaqamun tunani!


A watanni uku zuwa hud'un danayi a wannan qasar komai ya faru sosai ciki harda komawata makaranta da nayi mota har biyu Dr Saad da matarsa suka ban nikam Banda bakin gode masu Sam gashi mahaifin Dr Saad wato shugaban qasar Burki nafaso Shima Yana matuqar qaunata Dan har securities yake had'ani dasu inzani skul akan idanunsa nake komai Kuma su maidoni dukda wani zubin Nike tuqa Kaina har skul in !


A Kuma wannan watannin sosai mukeda labarin mubash ni har mamakin Yar uwa love nke (habeebty) Dan yadda tazaqe ta naimo mubash Dan nikam Saida ta tabbatar komai ya daidaita snnan ta sanarmun Kuma ta nunamun shi mubash in a system inta Dan yanzun haka Yana qasar Cameroon ne! Inda ya had'u da wata yarinya suka Soma soyayya har iyayenta sun amince dashi hakan ba qaramin tayarmun da hankali yayiba Amman Yar uwa love tace karna damu zata wargaza Shirin nasa bazaici galaban auran wannan ba Kuma a sannu zata Soma cusama rayuwarsa tagargura dabazai iya fidda kansa a ciki ba sai ta cusa Mai baqin ciki da abinda zai kassara rayuwarsa! Dan wa'innan mutanen da mubash keson auran 'yarsu su d'inma sunada wani babban manufa ason shugowan mubash in cikinsu Wanda sainan gaba zaisan dalilin nasu!



Oh oh mubash🀣Allah ya sadai ba gidan en yankankai kashiga badai! πŸƒπŸ½β€β™€πŸ₯Ί


Kai Habeebty daban take acikin mutane ko maza tsoronta suke inta shirgo wani tarko wlh ka rantse wani hamshaqin 'yan zamannin kakanninmu ne ke sarrafo bayanai haka ko shugabn qasa watau surukinta inzaiyi shawara da ita yake Soma yi Dan samun nagartattun shawara!


πŸ˜„masu karatu inkun ganni yanzun Ina gani bazaku gane Aymanar taku ba! Dan irin murjewar datayi Aymanah taqara wani sihirtaccen kyau da Kuma haske haskenta gani gani zakasan Yana shimfid'e da kwanciyan hankali da Kuma hutu yooo toh kullum cikin Ac da kwanciyan hankali take ciki fatanta ya darje ainihin kyawun ta da Kuma Wanda ta qara suka bayyana ga wani d'an qiba data qara Kai Aymanah dai ta koma so ma Sha Allah! Fatan Allah ya ma rayuwarta albarka ya Kuma kawo mata qarshen da muwarta ameen!


***********************

*_Bayan shekara 4 da rabi_*


Zaune yake acikin makeken office d'inshi cikin kujerar office d'insa yake zaune hannunsa riqe da wata frame na hoto Mai kyawun gaske Dan frame in da silver golds aka qerasa cikinsa hoton wata kekkyawar budurwa ce wacce akalla acikin hoton zata Kai kimanin shekaru 16 haka!


Qaremasa kallo nayi Ina Maison gasgatama idanuna ko shid'inne ko Mai Kama dashine Wai?! πŸ€”................ ✍🏼





πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€........kuda post Kuma sai.......... 🀣🀭maman janar tamun data eheeeπŸ€£πŸ‘―πŸΌtakora Kuma datan masu kud'i nakeyi daga 5k zuwa sama hakaπŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸ€£


*Real pure moment of life writers*

😭 *AURAN WAHALA KOH SAKI?!*πŸ˜­πŸ“πŸ™†πŸ»


*_by Ayshkhair_*☺


*_page 45&46_*




Kallan tsaf natsaya Mai Dan tabbatar da shid'in ne dai dagasken kekkyawan namijine ajin farko Wanda dukkanin halittun namiji sun bayyana gawan Nan bawa na Allah so ma Sha Allah a wa'innan shekarun ya chanza sosai inda many'ace da quruciyar sa tasoma bazama ajikinsa sosai hutu ke shimfid'e a fatansa daketa kyalli kman azurfa! *_Aliyu Hydar Abdallah_* kenan d'an hajia Azma da seneta Abdallah jika Kuma ga Daadadi(kakarmu) matashi maiji da jini ajikinsa kud'i sun zauna Mai tareda kwanciyan hankali saidai kukansa d'aya watau 6atar abar qaunarsa "Aymanah". Hydar aqalla yanzun zaikai kimanin shekaru 35 a duniya Amman Inka gansa zaka rantse baikai 30 bama sabida kyawun halittarsa da maiduka ya wadatar agaresa!


Maganan da yasoma yine yasani matsowa daf dashi Dan son Jin abinda yake furtawa!


"Aymani _swanty_ I always feel your presence inaji ajikina kinanan dawowa gareni and I promise I will love u till the end of my life sannan zan nuna maki tsantsan soyayya agareki Bazan sake barin ego d'ina yahanani nuna maki Sona agareki na yake nurul ala nooor! Come back to me safe and soon _swantyna_!"

Da haka ya sumbace hoton hannun nasa sannan ya ajiye hoton akan tebur d'insa Yana sake ma hoton tsadaddar murmushi Yana shafa hoton daya ajiye akan tebur in Yana furta!

"Let hubbi get back to work swanty na" 😍

Ya ida maganar had'i da sumbatar hoton Yana sakin lallausan ajiyen zuciya Kuma Yana Mai jany'o system d'insa yasoma daddanna system d'in da yake ciki!


Yana cikin hakan ne yaji bugun qofa batareda ya juyoba yabada izinin shugowa sectary nasace tashugo tace:

"Sir kana da baqo"

D'an kallanta yayi Dan bai expecting kowani baqo Dan haka yace:

" Ok let him in"

"Ok sir!"

Tafita Bata jimaba ta Kuma kwankwasawa Saida aka Bata izini sannan tashugo tareda baqon sannan tafice kayansa!


Yanda Ya miqe Yana Mai kallan baqon NASA had'i da sakin murmushi Wanda har jerin fararan haqoransa ke bayyana yasa na gamsu da shi baqon yanada wani babban matasayi agun Hydar rungume juna sukai sannan suka saki juna suna Mai farincikin ganin junansu!


Yaah Hydar ne cikin muryar mamaki yace:

"Guy wat a surprise shine ko d'an waya babu saidai kurum naganka"

Murmusawa baqon yayi Yana d'an tafiya har ya zauna acikin kujerun da ke cikin offishin Yana fad'in:

" Ai ramawa nayi nima haka inzakazo wajena baka gayamun saidai kurum naganka ai" 🀨

Ya ida maganar Wanda yasa Hydar fashewa da kuka Yana qarasowa Dan yazauna da haka ya zauna kan kujeransa Yana juyi Yana kallan baqon NASA sannan yace:

"Bravo Friend tohm ka kyauta keep it up ! Nima zan ramane ai🀨Ina matars da F boy?!


Murmusawa Baqon yayi sannan yace;

"Ali Hydar habeebty tana qalau she send her gaisuwa F boi Kuma gbe nakeson zuwa maiduguri nagansa sai mukoma tare tunda sunyi hutun skul! ".

" Wow Kace zanga boy d'ina"


Ya ida maganar Yana miqewa Yana nufan fridge Dan kawo Masa lemun kwalba!


"Eh fake daddynsa ba baka zuwa Mai gashi Kuna qasa d'aya! "


Dariya Hydar yayi sannan ya juyo Yana miqa Mai juice in da ya tsiyayamai acikin cup Yana fad'in:.
"Hhhhhhhh zauna Nan kaji sai kaga ingaje ya nuna baisanka ba saini!


Ajiye cup in daya d'an zuqa juice d'in baqon yayi sannan yace;


"Aikai saidai a hankali"


Dariya yayi kurum sannan yace:

"Mr Man Ina _swantyna_?" 🀨

Hydar ya ida maganar Yana Mai d'agamai girar sama dariya sosai yayi baqon sannan ya kalla Hydar yace:


"Wai Mai kakecine nabaka nazuba Mr Man!"
.ya ida maganar Yana jany'o frame d'in hoton dake kan Decks d'in Yana murmusawa Yana fad'in:


"Habawa lover boy bazaka yi imagining yadda _swantynka_ tadawo ba ai tafi haka kyau ninkin baninkin"🀣


Ya ida maganar Yana dariya:

" Habadai SaadπŸ€”! Really? This so amazing hope dai kazomun da pics d'inta wlh na qagara ta kammala karatun Nan nata tadawo garemu I really really need her Dr plsss ! "


Dariya Dr Saad yayi sannan yace :


" Relax Aymanar ka is in good health Kuma sauran mata 6months kurum ta kammala karatunta only 6momths so ka qara haquri akan wa'inda kayi a shekarun baya! So that all shall go well nawan!


Murmusawa Hydar yayi sannan yace:


"Hakane Abokina banida bakin yimaka godia kaida mommyn Fa'eez (Habeebty)da su Ammah saidai Allah yasaka maku da alheri kurum! U guys deserve jannah thank u so much friend nagode da taimakona dakai dakuma taimakon Aymanata dakai!


In Sha Allah zan cigaba da tausasa Raina har sai sadda Aymanah ta dawo garemu Kuma zan cigabda nunama iyayenmu banida masaniyan inda take har yanzun thank Saad ! "


Murmusawa Dr Saad yayi sannan yace':

" Wat are frnz for naaa?Babu godia Akan abinda yazama wajibi Aymanah qanwa take agareni nima! "

Daga haka Dr Saad yasoma labartamai wasu labarukan da bai samu yasanar Masa in details ta system ko wayaba!


Sosai Hydar yaji dad'i sannan yayi godia garesu Dan habeety ma yakan yawan kirashi tacemai "d'an uwa kodai aduaa kake ma _swanty_ ne dan Naga har son datake ma nason fin Wanda kake Mata fa! πŸ˜‰

Yakan cemata "qanwas Ina ai ko kaso rabi cikin sanda nakema masoyiyar ki baikai Wanda take munba kekam cigabada cusamata son nawa intadawo gareni kiga romiyo and julliet sai mun fiku zuba love keda mr Guy (Dr Saad)"


Takan Mai dariya tace" toh d'an uwa Allah nuna Mana wannan Rana lfy it will be the best day of my entire life Kam! "


Yanajin dad'in kalaman habeebtyn agaresu hakan Kuma yaqara Mata matsayi a zuciyarsa Kuma ako wacce salla tasa sai ya ma ilahirin dangin Dr Saad aduaa!

Da haka suka Gama tattaunaaawa har Dr Saad ya bashi hotunan Aymanah daya wanko masu kyau Hydar da kyar ya iya saita natsuwansa Dan mugun tafiyar da imaninsa da Aymanar tayi lallai dole yakasa son kowacce mace a duniyanan inba Aymanahba Yana Mata sonda baisan adadinsa ba wlh Allah dai ya mallakamasa ita kurum shine aduaarsa a kullum!


(Ameen Hydar din _swanty_🀣)


Da haka suka miqe Dan zuwa masallaci dakuma Dan zagaya gari!


"" "" "" "" "" "" "" "" "" "" "" "" "


Ragwaf tafad'a a bayan mamanmu tana magana cikin muryarta ta gwaranci:

"Granny! Granny! Kinga Mommy zata dakanπŸ˜ͺ!"

Daidai Nan Kuma mommyn Tata ta iso tana naimanta Dan ta qaramata bulalan tana hangota wajen mamanmu ta tsaya chak Dan tasan mamanmu ba barinta zatayi ta dake ta ba Dan hakan saita Nuno yarinyan da bulalan hannunta tace:

"L2l Ayni if nakamaki Zaki sanine!"

Ta qarasa maganar tana hararar yarinyan tana Mai juyawa Dan fita a falan Dan ba barinta marmy da mamanmu zasuyi ta bige 'yar ba Dan haka tasaman ma kanta salama tafita!

Hhhhhhhh Marwa Keenan iyaqin San rainiπŸ€¨πŸ‘―πŸΌ

Mamanmu ce ta kalla yarinyar Wanda sai a yanzun na qaremata kallo yarinyar sak kamarta da Marwa sosai kaman atsaga Kara an tsara suna Kama sosai saidai Kuma tana yanayi da Aymanah still yarinyar bazata wuce shekara 1 da rabiba Amman Inka ganta zaka zata takai 3yrs Dan irin jikinta tana magana rau sannan tana guduwa a ko Ina hakan yasa mahaifiyata yayeta!


Hmmmm _Aymanah Abdul'azeez_ Keenan wacce ake ma laqani da _l2l Aymahni_ 'ya ga _marwa mubin Aliyu lere_ da mahaifinta _abdul'azeeZ bukar_

Yanzun shekarun Marwa 2kenan da aure inda ta aura abun qaunarta abdool sosai suke son junansu lbrn faruwan aurensu senan gaba zan warware maku yadda auranta amaimakon yazamana Hydar ne mijin saiyakoma ga abdool d'inta a yanzun haka Marwa ta Gama bautar qasar ta Kuma tana aiki a wani company anan garin datake aure watau a garin Abuja a unguwar gwarinpa! Sosai Marwa ke qaunar 'yar sabida sunan Rabin ranta datake dashi watau 'yar uwarta Aymanah hakan da mijinta yagani yasa shi sama 'yar su sunan Aymanar Wanda ya matuqar yima dukkanin dangin su murna plot na gida har wajen 4 Hydar ya baiwa l2l Ayni Wanda shidakansa nema yasamata wannan laqanin watau l2l Ayni sosai Hydar ke qaunarta inda itama l2l Ayni ke matuqar qaunar uncle d'in nata Babu irin gatan dabai nuna Mata Dan in har ya shugo garin Abuja to lallai tabbas sai yaje dakansa har gidan Marwa ya d'au l2l aymani harsai zai koma gun aiki sannan yake maidata ga iyayenta!

Wannan Keenan!


Mamnmuce ta jany'o l2l Ayni ta zaunar Akan cinyarta sannan tace:

"L2l Ayni maikikama mommyn ki?"

Murya shagwa6e had'ida gwarancin harshe tasoma fad'in;.
" Granny Wai... Wai... Dan na fasa hoton secnd mommy shine tadakan! Kuma ai bada sanina na fasarba ko granny!?😟😫


Ta ida maganar cikin yanayin tausayin shagwa6a😟


Daria mamanmu tayi Dan tasan dama babban laifi Ayni tayi shisa Marwa tabiyota!


"Lalalala u are a good girl l2l cuz kin 6ata hoton secnd mommah d'inki Maza jeki baiwa mommy haquri"

Sauka l2l tayi tana fad'in " granny when will secnd mommy be with me? Ban ta6a kallonta ba😫!


Dariya mamamu tayi tace "soon oya go give Mama apology Maza!"


Da ihun murnarta ta ruga Dan Jin ance zataga 2nd mommy soon Dan haka taruga aguje tana kwala Kiran sunan "mommy" πŸ€£πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€!


Itako mamanmu d'an murmusawa tayi Dan tuno da gudan jininta watau wacce l2l Ayni ke Kira da secnd mommy Aymanah sosai yanzun mamanmu ke yawan tunanin yarta hakan yasa kullum saitayi sadaka tana roqon Allah maidota garesu lfy! Dahaka tanisa Dan zuwa duba marmy da ba lafy a asivity shinema dalilin zuwansu Marwa gomben!

*********************

*6months leta*


Repeat after me!

Shine kalamar da want babban lawyer daake jidashi yaturta ga wannan kekkyawan barrister dake agabansa Sany'e da kayan lauyoyi masu karatu zanso kuga yadda wannan uniform Yama Baiwar Allan Nan kyau Wanda Baku zato ga fuskanta sai fidda annuri yakeyi Jin yasoma gayamata abinda zata gayane yasani waiwayowa Dan yadda naji ta amsa sai ya burgeni matuqa cikin harshen turanci kman sarauniyar ingila:


*_I Aymanah Mubin Aliyu promise to be a trusful and truthful prosecutor lawyer! I Aymanah promise and vow to be a justice lawyer and to take decision and actions on all the Constitutions of the country before taking any case on my clients I vow to be obedient and good prosecutor to the constitution!"_


( *Ni Aymanah Mubin Aliyu nayi alqawarin zama amintacciya da Kuma maigaskiyar lawyer Mai Kare hakkin Wanda aka cuta*!

*_Ni Aymanah nayi alqawari Kuma nayi rantsuwa Alan zama lawyer Mai adalci and zan ruqa d'aukan mataki da Kuma raayi acikin Constitutions na qasa kafun na aiwatar da kowacce case Akan wa'inda nake karewa nayi alqawarin zama mailadabi da biyayya a continuation*)


Da haka tajany'e hannayenta Akan qur'anin Mai tsarki data rantse akai Wanda inhar Bata cika alqawuran data furta Akan qur'aninba zata gamu da fishin Allah yawancin shuwagabbinmu saikaga kafun a rantsar dasu saisun rantse da littafin Allah Amman dasun hau mulkin giyar mulki na d'ibarsu saikaga sunyi watsi da wannan alqawarin dasuka dauka Wanda wlh dasunsan hukuncin Wanda yayi rantsuwa da littafin Allah Kuma ya karya wlh da dukkanin alqawuran dasuka dauqa sai sun tabbatar sun cikasu sabida irin azabar da Allah ya tanadar ma masu sa6a alqawari bayan sun rantse da littafinsa shiyasa siyasa wlh 6attacen wasane is a dirty game a duniya dai zasuji dad'in mulkin Amman a lahira zasu yabasa Aya zaqi a ranar da Allah da kansa zaiyi magana da bayaninsa inda zaice:

*_limanil mulkul yaum? _*

(Wayene da mulki yau)?


Inda dukkanin basarake ko shugaba basuda damar amsa wannan maganar dan Babu sarki Babu shugaba adali kaman _alkareem Al gafur Al rahim ubangijin Adam da Musa ubangijin Aysha da muhd ubangijin fir'auna da qaruna ubangijin mala'eeku Kuma ubangijin shed'anu da aljanu Ubangiji kowani Abu Mai Rai da Mara Rai Wanda shike raya matacce acikin Mai Rai Kuma ya raya mairai acikin matacce ubangijin da inya nufeka da rahma Babu wani mahaluki adoron duniya ya haneka samun wannan rahmar ta Ubangiji Kuma Malaccin da idan ya aikama da masifa Babu Wanda ya Isa ya cirema shi face yayi izinin hakan Alrahim Mai qaunar bayinsa Wanda yake fushi har in bawan sa yaqi roqonsa Wanda mutane dayawa Allah Yana Jarabtar sune Dan su dawo garesa su naima buqata agunsa bawai Dan baya qaunarsu bace aa saidai Yana fushi idan baka roqansa Allah ka karamana qaunarka acikin rayukanmu ya Allah ka Kuma sa mu mutu masu Imani da shahada)

Da kansa zai bama kansa amsa Dan bamai iya basa amsa inda zaice : "lillahi wahidul qahhar" (Allah shi kad'ai keda ita)

Ameen ya Allah !


Qarasowa 'yar uwa love tareda Dr Saad sukai suna Tayani murna Dan ayaukam an rantsar Dani nazama lawyer cikakka Mai zaman kanta! Kai Allah abin godia hmmmm !

Wanda nagani tsaye ya hard'e hannayensa Yana wurgomun murmushi ne Mai Cike da so da qauna yasani saurin zaro idanu bakina na rawa ina furta "yaa.. yaaah Hydar!


Da sauri su Dr Saad suka juyo Dan San ganin Wanda nakira d'in Amman wayam basu gansaba hakan yasasu tambayata lfy Aina kikaga Hydar din cikin yanayi mmakin 6acewar sa a daqiqu Soma nunamasu da hannu inda nagansa Amman wayam Babu shiΒ‘

Dariya Yar uwa love tayi tana Mai Kama hannuna tana fad'in:

"Kayya swantyn Hydar masoyiyata zomu tafi hai babu wani Hydar anan shida yake Nigeria!

Kama hannuna tayi mukasoma barin wajen Niko nabita kman raqumi da akala Dan wlh nikam dagaske idanuna sun ganemun yaah Hydar d'in wlh nagansa to yaakayi Kuma ya 6ace kodai kawai Dan nayi mafarkinsa jia Akan yazomun taron murna ne yau nagansa mafarkin ya haskomun shi? Banda Mai ban amsa haka naruqa bin wajen da kallo har muka fita muka shiga mota Dr Saad ke tuqi habeebty na gaba Ina baya kmn ance na waiwayo kurum nagansa a bayan motar mu Yana dagamun hannu alaman bye bye da sauri nakuma kallonsa Dan banso kwakwalwata takuma cewa ba shi d'in bane da gaske kallan saman la66ansa nayi bisa alama sunana yafurta hakan yasani 6ullo da Kaina ta window ina furta "yaah Hydar........... ✍🏼


Real pure moment of life writers

😭 AURAN WAHALA KOH SAKI?!πŸ˜­πŸ“πŸ™†πŸ»


by Ayshkhair☺


page 47&48


Ban jira wani tambayan su Dr Saad kurum ba 6alla murfin motar na yi hany'ar inda naga Yaah Hydar yabi! Da mamaki suma suka fito suna kirana Amman Sam bana majinsu burina kurum nagan na Isa kun Yaah Hydar d'ina! Wani kalan fad'uwan gaba naji a lokacinda nariqe bayan rigar Yaah Hydar d'in lokaci guda Kuma hannuna yasoma 6ari Dan bansan irin tarbar da Yaah Hydar d'in zaimun ba ga mamakina Yana waigowa sainaga waninsa sa6anin shi Yaah Hydar d'in hakan yasani saurin jany'e hannuna akan rigar mutumin Wanda inma mafarki nakeba ta66as da ita Naga Yaah Hydar da shi tohm kodai kodai idona gizau takoma yi Akan Yaah Hydar d'in ko Kuma aljanine ke zuwan mun a siffarsa Dan ganin tsananin son shi da nakeyi? Tohm inba hakaba ai wlh da idona nagansa Yana dagamun hannu sannan Kuma yana mun murmushin da ba Koda yaushe yake yinsa ba Ohni Aymanah 'yar Mubin jikar Aliyu! Wata kaliyar rayuwa Kuma nakeson jefa Kaina?!

"Are u okey?"!

Maganan sane yadawo Dani duniyar tunanin Dana fad'a da sauri nad'aga Ina kallon mutumin da ya kafeni da qananun idanunsa yasason Jin ba'asin riqe Masa bayan rigar danayi batareda nayi wani tunaniba ta kalla hannun nawa dake riqe da hannun rigarsa nayi saurin cire hannuna ina mamakin tohm ayaushe Kuma nariqe rigar hannunsa bacin Kuma bayan rigarsa na riqe? Ta6e baki nayi sannan nace:

"Am...am...am Dan Allah sorry it was a mistake perdone me!"


Girgiza Kai kurum yayi ya juyamun baya yasoma tafiya abinsa nikuma nabi siririn bayansa da kalloπŸ€” tohm ko uwar Mai nake kallo abayan NASA? Ohon mun wata zuciyar tace qilan fuskan Yaah Hydar kikeson yafito a bayan bankaiga wani tunanin ba naji an dafani sosai na juyo Ina qare Mata kallo nad'an saki wani lallausan ajiyan zuciya Ina kallan habeebty murmusawa tayi takama hannuna tajani har cikin mota inda *besty Saad* ke jiranmu dukamun bayan motar muka shiga nida habeebty sannan *besty* ya tada motar yabata wuta muka bar haraban *bar* d'in Saida mukai tafiya Mai d'an Nisa sannan 'yar uwa ta dafani takira sunana a hankali:


"Masoyiya"

A hankali nad'ago idanuna da tunda muka shiga motar band'ago na kalla kowaba! Kallanta nad'anyi duk fuskarta cikin damuwa hakan yad'an sani tunanin ban kyauta masu abinda nayi yanzun ba!

"Naam "

Kama hannuna tayi sannan tace:

"Kinason kikoma gida gun Yan uwanki ko? Masoyiya? "

D'an murmushi nayi sannan na kalleta nace:

" Aa 'yar uwa ai nasan zan koma"

Wani ajiyan zuciya tayi sannan ta kalla Dr Saad Wanda yake tuqi Amman dukkanin hankalinsa na akanmune ta mudubin mota yamata maagana da ido Ina gani itama ta mayarmai amsa ta wutsiyar ido sannan ta lumshe idanun nata ta bud'esu Akan nawa sannan tace:

"Hakane Masoyiya in Sha allah Zaki koma cikin watan da zamu shiga Dan in Sha allah zamu shiga shari'arki da mubash Nanda 2wks Dan nayi nasarar damqosa yanzun haka yadawo qasar birki nafaso akaro na biyu Wanda awannan karon rabuwarki dake dashine takawosa! "

Sany'any'an ajiyan zuciya nayi Danni yanzun ba mubash bane agabana Yaah Hydar ne dan komai nawa tunanina zantuqana komai na Yaah hydarne ban tunanin zan iya musany'a kalamai Dani da mubash Dan duk kalamaina sunaga Yaah Hydar ne Wanda zuciyata tayi naam aduk lokainda nagansa saina fallasamai sirrin zuciyata saidai inzai bigeni yayi gunduwa gunduwa Dani Amman Kam Yasin saina gayamai kozan sama zuciyata tarage wani abar a dangane dashi!


Amman Kuma inna tuna aurena dake Kan mubash sai Kuma naji inamai son sake ganin mubash in Dan kwantan takardata kota hany'ar qaqaniqaqa nasan ko kud'i nace zanbaiwa mubash Dan yaban takaddata zaiban tunda lashe money ne

Please Login or Register in order to submit comment