Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sonki bafa Aliyu hydar Zaki aura ba wannan masoyinki zabinki Zaki aura fa, Dan Haka kiyi gaggawan cire wannan tunanin dan shedan ne da bayason ganin kin raya sunnan manzon rahma ke cusa maki wannan raayi ki miqe muje ga kankana da cocumber namaki blending muje nasa maki Madara Kisha sannan kishika ga ruwan turarukanki najira kizo kiyi wanka kinji ko"

Gyad'mata kai kurum nayi sannan na fito muka wuce falo fridge ta bud'e sannan taciro bowl din kankana da cocumber datayi tasamun Madara peak gwangwani biyu tajuya sannan ta kawomin tace:

"Oya yimaza ki shany'e "

Ba musu na amsa nasoma Sha lumshe idanu nayi nashanye kayana tas Dan abin baa bawa yaro Mai kwiya! Marwa ce ta shugo hannunta riqe da Faty tana cune baki tana fad'in:

"Marmy gaskiya yaran Nan ana kammala biki zasu tattara sukoma da uwarsu Yara sai shegen jaraba!

Ido Marmy ta bita dashi sannan tace:

"Kajimun Yar Nan toh saukomun da jika kafin ki fadar da ita , Sha nake kece kemana rainansu? Da har zakice sukoma toh Babu inda zasu sunanan har su riqe 'ya'yan ki"

Dariya na yi sannan na miqe naje na shiga wanka yanzun Kam turare yazauna daram dam ajikina yadda kasan kamfanin turare innazauna a wuri na miqe sai turaren yafi minti 30 Bai bar wajenba ! Bayan nayi wankan nafito nayi hayaqi da wasu turarukan Dan yau zaa kawo wacce zatamun dilka da sauran gyaran jiki!
Ina gamawa Marmy ta miqomun gumba tace naci iya cina amsa nayi nasoma ci , nidai wannan Sha da cin sunfara isata😒kullum aikin kenan ko Mai anfanin su oho? Maman mu ce ta shugo hannunta riqe da wani qaramin farin roba ta miqa mun tace innagama cin wannan shima naci, tohm kawai nace sannan nan na amsa na bud'e na d'and'ana abun balaifi yanada dad'i daga ji da Madara aka had'a.



Yau bikina yakama saura sati d'aya kacal Wanda izuwa wannan lokacin yayyunmu Mata harsun soma zuwa anty ameenah ce kawai Bata zoba sai ranar kamu zatazo Dan ana bikin qanwan mijinta, Ina kwance akan ciny'an Marmy tana mun nasiha Akan aure sai Marwa tashugo fuskanta d'auke da murmushi ta kalleni tace:

"Amaryar mubash! Guess what?!

Kallonta nayi nace:

"Mai faru?

Dariya tayi tace:

" Wlh ga mubash chan da abokan sa sunzo suna d'akin baqi"

Tab'e baki nayi Wanda daga Marwa har Marmy Saida sukayi mamakin hakan daga wajena dan Sunsan baqaramin dad'i zanjiba ganin karsu d'agoni yasa nad'an saki murmushi nace:

"Sannunsu da zuwa "

D'aga nan ban Kuma cewa komai ba! Naqara kwantar dakaina Akan ciny'an Marmy wacce tasake baki sangangan ita da marwa suna kallona, Marmy dai dataga Banda niyyan tashi yasa tace:

"Autan mamanta lafuya kuwa? Kinji ance mubash yazo Amman shine bazaki miqe kije ba?

Guntun tsaki naja sannan nace:

"Marmy Dan Allah Mai zaimun Kuma!? Bacin ankusa kaimaini " 😒

Marwa wacce tsabaragen mamaki yasata kasa cewa komai da kyar ta kalleni tace:
"Tabdi kice akwai maqarqashiya Dan Allah kimiqe muje wlh da abokansa yazo fa"

" Nifa ba inda zani"

Marmy ta kalli Marwa sannan ta kalleni tace:

" Auta miqe kije injini nace Inna isadake kimiqe kije"

😩maraice fuska nayi Dan kawai Marmy tasan vazan iya tirjema maganan ta bane yasata fad'in haka yatsine fuskana nayi na miqe Ina turo baki nashiga d'aki Dan d'auko hijab Marwa da Marmy suka bini da idon mamaki har nafito nazumbula qaton hijab nayi gaba Marwa tabi bayana!
Marmy tabi bayana da ido tana mamakin wannan chanjin "yoo komadai Mai intadawo sai na tilastaki kingayamun"

Ta Ida maganar tana Mai miqewa Dan shiga kitchen ,

Marwa takama hannuna gudun Kar naqi shiga gurunsu mubash , a Haka har muka Isa cikin falan Marwa tayi sallama suka amsa muka shiga kaina aqasa wannan qamshin turarensa da yayi kusan kwanaki ajikina ne yadoki hancina Wanda hakan yasani saurin d'agowa mukayi Ido hud'u dashi Ras naji gabana ya fad'i ban San dalili ba ganinayi ya bankomun harara fuskan Nan tashi a tamk'e!


🙆🏼‍♀🙆🏼‍♀Ni shatu Wai any'a auran mubash da Aymanah zaiyi kuwa? Shin inma anyi zaman su zaiyi dad'i? Zaman doya da manja zasuyi ne? Karku manta sunan littafin Auren wahala ko saki? Muje dai zuwa in Sha Allah zan warware maku bindi har wutsiya🌚
[6/17, 8:30 PM] .: *_®eal pure moment of life writers_*


😰😭 *AUREN WAHALA KO SAKI?!*📝😭🙆🏼‍♀


( *_Story base on fictional writing📝_*)

*MALLAKAR AYSHKHAIR 💗*

WRITTEN BY AYSHKHAIR 💗

Page 15-16

Cikin mutuwan jiki muka gaishe su mubash Kam ma banza yayi damu abokansa suka soma jawabin zuwan su inda suka tambayemu nawa muke buqata Marwa kawai ke amsawa Niko nqzqmq mutum mutumi a d'akin har suka miqamata damun kud'i muka musu sallama nayi tafiyata ko kallon inda mubash yake banyiba fito wa nayi na wuce d'akin maman mu nayi kwanciyata na lumshe Ido Ina saqa da warwara.


Washe gari duk en uwa da abokan arziqi sun soma cika hajia Azma ma tazo zai kaffa kaffa takeyi Dani Dan kaf cikin yaran gidan tafisona duk da naqi d'anta hakan baisa ta qinaba Dan ko lokacin danake yarinya da aka yayeni gunta aka kaini yaye.


Ansoma event yau ya kasance ranar kamu in ka ganni yadda aka mun kwalliya nayi matuqar kyau Sam bazaka gane ni ba nayi kyau har nagaji qarfe uku akayi kamu aka gama qarfe 6 ranar jumma'a ka d'aura aurena da:

*Mubbashir Musa Adam dani Aymanah Mubin Aliyu Akan sadaki dubu 50*

Nidai bazance nayi farinciki ba Kuma bazan ce banyiba a qarfe 2 motocin zuwa d'aukan amarya suka zo Dan a chan kano zan zauna nayi kukan rabuwa da iyayena harna gode Allah anmun Nasiha iya nasiha , nan aka fito Dani lullub'e cikin alkebba ta har zaa shigar Dani mota mukaji ance:

"Kudakata"

Waigowa kowa yayi Dan ganin waye Jin shurun yayi yawa yasa ni d'agowa Ido biyu mukayi Wanda harsaida gabana yafad'i amman bansan dalilin hakan ba wani zuciyata tace qilan sabida kina tsoransa ne a hankali na furta:

"Yayah Hydar"

Sam bansan yazo bikin ba sabida ko gezau Banga yayi acikin gidan ba shin yaushe yazo? Maganar da yayi ne yasani kasa samo amsan maganar ji nayi yace:

"Marwa wuce muje ga motar da zaakaita"

Yama su nuni da wata dalleliyar motar Mai matuqar kyau gata baqa da baqin tint kallon mamaki nabishi da shi sabida a iya sanina tun tasowata bama jiyuwa da Yaya Hydar baisona Sam ko sadda aka had'a auran mu cewa yayi naje nace banaso Dan shi Yana da wacce yakeso maizaiyi da 'yar qarama yarinyan da ko qannensa sun girmeta!

A hankali su Marwa suka Jani muka shiga motar ni kad'ai a baya sai Marwa tashiga gidan gaba inda yace sauran suje su shiga sauran motocin , Nan ya zagayo driver side yashiga yasoma tada motar d'agoda kaina nayi mukayi Ida biyu ta mirror fuskansa a tamk'e ya wurgomun harara saurin kauda kaina nayi a Raina nace:

"Dama nasan Yapendo Azma ce taba shi umarnin yakaini amman if not shikam danyin kansa bazai yiba , "

Nan yaja mota aka sa motar mu a tsakiya aka jera aka dosa kano abun gwanin ban shaawa tafiyan kurame mukashiga yi Gashi sai tuqi yakeyi a hankali tamqar Mai koyon tuqi en bayan mu Dake binmu sai horn sukeyi Masa Amma Sam ko tunanin qara gudu yaqi hakanan wasu suka ruqa yin reverse suna shiga gaban mu har aka barmu mune abaya! Marwa kuwa tsqban mamaki ya sata turomun text Wanda sai ayau na kunna wayar :

"Wai Dan Allah Mai wannan yaah Hydar d'in ke nufine Wai Aymanah? "

A hankali na turamta:

" Ohon mashi ke bakisanshi da mugunta bane? Inbaiso yin abuba aibayayi!,

Ina Gama turawa kaman an mintsileni nad'aga Ido na kalla mirror karaf nasauke idanuna akansa Ashe kallona yakeyi bankomun harara yayi da sauri na d'auke idanuna na d'an gyara zamana na kishingid'a a motar kafun kace Kobo har bacci yasaceni dama gani da gajiya ajiki Allah sama yau banida tsqrki da saidai mubash yakuma d'auramun wani sabon gajiyan, amman nasan duk da haka ba barina zaiyiba😒

Bacci ne sosai ya kamani itama Marwa baccin takeyi shiko yaah Hydar zubamun idanunsa yayi Yana ta kallon fuskana ko tunanin Mai yakeyi oho wasa wasa sai 6 muka Isa kano sauran Kam tun 5 suka Isa ana jiran amarya tazo mubash yaruqa kirana awaya danjin lfy amman inaaaa wayar tana silent Koda muka iso ita Marwa tafarka amman ni still baccina nakeyi abuna a hankali yayi parking sannan ya kashe motar ya kalle gefena yaga Ina bacci ya kalla Marwa yace kifita kice mun iso Aiko Nan tafita tashiga cikin gidana tasanar mun iso da sauri mubash ya fito ya doso motar mu yaah Hydar Wanda ya shagaltu da kallon fuskana baima ji lokacinda mubash ya bud'e motar ba gani kawai yayi mutum na kiciniyar d'aukan Aymanah da sauri ya kalla mubash Dan San ganin waye amman ganin mijinane yasashi kawar dakai mubash ko d'aukata chak yayi ya mannani da jikinsa Yana aukin sunbatan fuskana.


Shiko yaah Hydar runtse idanunsa yayi da qarfi yadanna giyar motar yamata wani wawan jaaa da gudu kamar Mai Shirin tashi sama ya fita a layin da sauri mubash ya waigo Wanda nima daidai Nan na farka Dan qarar motar ta firgitani a hankali nabi gefen da mubash ke kallo Naga qura Baja Baja kallona yayi kafun kace Mai mubash tuni ya cusa bakinsa cikin nawa Yana qika musu saqonnin dayafi qarfinsu........... 🌚


Late typing kuyi haquri 😩Kuma baku comments gaskiya zandaina wahalar dakaina in novel din baimuku ba baadole sai na daina dama sabida kunce naxigaba da rubutu yasa nacigaba amman daa na ajiye🌚🌚so iya comments iya adadin yawan page 💁🏻‍♀in kunason read more biyar gobe Naga comment Baja Baja yau kamar yadda nake ganin nasu Jawaheer😩


AYSHKHAIR"
[6/17, 8:30 PM] .: *_®eal pure moment of life writers_*


😰😭 *AUREN WAHALA KO SAKI?!*📝😭🙆🏼‍♀


( *_Story base on fictional writing📝_*)

*MALLAKAR AYSHKHAIR 💗*

WRITTEN BY AYSHKHAIR 💗

Page 17&18

Babu inda Mubash ya ajiyeni sai Akan gadon d'akina , yabi ya ratsa duk jamaan Dake cikin falan kowa sai tafi yake Mana abokan sayl kuwa cewa suke "easy man easy man" Bai kulasu ba Kuma baice masu uffan ba nidai idona a runtse yake nasan kuma yanzun mubash zai batamun kwalliyata gani nayi ya soma cire kayansa Amman ji dayayi ana buga qofan d'akin yasa shi dagatawa had'i da cewa:

"Wayene? " Shooter abeg ka hanzarta is already 7 fa har an fara tafiya dinner kufa ake jira in aka dawo ai shikenan"

Badan mubash yaso ba ya kyaleni muka miqe muka nufo falon duk har ansoma wucewa dinner Niko mubash yariqeni Kam a hannunsa tamkar zaa kwacemai ni, nikam sai qara bitar sunan daaka kirasa nakeyi *shooter*!

Nan akayi dinner 12aka tashi muka wuce in taqaice maku dai a daran munsha drama da mubash Dan yaqi Sam qawayena su kwana agida haka akaje aka Kama musu hotel Marwa Kam tacika tayi fam Niko tamkar nayi kuka Wai shin any'a ban d'ebo ruwan dafa kaina bakuwa?!


A daran Kuma muka kumayin kacha kacha sakamakon banida tsarki ai mubash tamkar ya zauce ji yake kaman ya rufeni da duka fad'i kawai yake:

"Mtswww Amman wlh bakida tunani Mai kyau ace sai kin daidaici ranar danakeson kusan tarki sai kidage kice bakida tsarki wlh wlh this enough nizaki rainama wayau inbakison auran tun farko aisai da karkiyi bawai kiyi kizo kina showing ma mutum attitude Wai banida tsarki mtsww wlh nidai navaki zuwa gobe da safe ko ya tafi ko bai tafiba , ko kinyi wanka ko bakiyi ba wlh sai nacimma burina wlh bazaiyu inzauna inzuba maki Ido ba mtswwww"

Daga haka ya miqe ya shige bayi Niko tunda yasoma maganar inbanda binsa da kallon mamaki Babu abinda nakeyi:

"Shin Wai wannan mubash ne Wanda nasani Mai qaunata? Wanda baison ganin b'acin Raina duk bama Haka ba ina karatun addininsa? Da har zai gindayamun sharud'a? Ni Gashi sainan da kwana 3 abinnan zai tafi oni Aymanah Naga takaina🙆🏼‍♀😭bansan lokacinda na fashe da kuka ba Ina mamaki da tunanin sabuwar rayuwan da zan yi a gidan mubash shin dad'i ko rad'ad'i?!

Bankai dabama kaina amsa ba naji yafito a bayin yarufe bayayin da qarfi ya wuce dressing mirror nikam kallonsa kurum nakeyi daga qarshe na miqe naje nasauya kaya nashiga nayi wanka nafito Naga har ya kwanta ya kashe wuta duk d'akin ya d'au duhu a hankali nasoma naiman inda ake kunna wuta Amman sai na tsinkayo muryansa Yana fad'in:

"Karki sake ki kunna mun wuta wlh inba hakaba ranki zaiyi munmunan b'aci acikin gidan Nan"

Daga haka ya Kuma gyara kwanciyansa yadda ban hango komai NASA inba bayanshi ba Niko wani kalan zazzafan yawu na had'iye a hankali nafurta:

"Waiyooo Mai ke Shirin faruwa da Aymanah? Anya Mubash ne kuwa Allah kasa mafarki nakeyi Dan nafarka naqaryata abun Nan dan wannan mubash banyarda zaiyi haka ba!

A haka danaga ba sarki sai Allah na lallab'a na kwanta Akan kujera daga ni sai d'aurin towel da kyar bacci ya saceni cike da tunanin su Marwa!

Washe gari kuwa tsaban gajiya , yasa ko Kiran sallan asuba ban jiba nikam ji nayi ana yayyafamun ruwan sany'i firgigit na miqe Ina raba idanuwa mubash nagani tsaye da goran ruwan faro Yana zubamun cikin fuskan tausayi nace:

"Yakai mijina angon Aymanah shin Mai Aymanah matarka ta aikata a gareka dahar kake fushi da ita a ranarta na farko na kasancewan tareda Kai a matsayin muharraminta?!

Muryan danamai had'ida fuskan tausayi Wanda yaga naqaramai kyau yaji tausayina ya dira a zuciyansa d'an murmusawa yayi sannan ya durqusa daidai fuskata har inajiyo futan lumfashinsa jinayi ya d'an dungulemun dogon hancina sannan yace:

"Angon Aymanah na fushi da amaryar sa dan baqonta yaqi barin Angon Aymanah raya daran sunnan manzon Allah "

Murmushi nayi sannan cikin low tone na kwantar da kaina Akan kafad'ar say Wanda dukkaninmu Saida wani baqon al'amari ya ziyar cemu a hankali nace:

"Angon Aymanah yayi haquri Dan Allah Dan Aymanah matarsa bata tab'a ganinsa cikin wannan yanayinba Kuma tayi alqawarin farantamai kafun baqonta yatafi Nanda kwana 2"

D'an murmusawa yayi yad'an mannamun peck sannan yace:

" Shikenan Matar mubash Amman abin nan yayi yatafi yabarni naji zuman Dake tattare da matar mubash shi kad'ai"

Murmushi nayi nace :in Sha Allah

Nan ya miqardani ya d'auke ni chak in bridal style yayi toilet Dani Wai shi zaimun wanka tun Ina noqewa Ina kulle fuska hardai nasake jiki Ina biyemai Dan Naga mubash a faninnan baida kuny'a😒a Haka muka ruqa wasa da ruwa shikuma daga ya latsa Nan najikina sai ya tsotsa nan ya sunbace chan hardai muka Gama muka fito ya rungumeni a jikinsa muka fito shi ya shafamun Mai ya shiryani Nima yasani Dole na shiryasa Nan muka ci ado cikin qananun Kaya munyi kyau gwanin ban sha'awa kallona mubash ya tsayayi ganin yadda kayan yayi matuqar fitting d'ina komai nawa yafito intact Babu wani makusa ajikina Dan Allah yamun baiwan sama da qasa a hankali yasoma lashe leb'e Yana fad'in
"My baby is bae.....



🤸🏽‍♀Manage pls
[6/17, 8:31 PM] .: *_®eal pure moment of life writers_*


😰😭 *AUREN WAHALA KO SAKI?!*📝😭🙆🏼‍♀


( *_Story base on fictional writing📝_*)

*MALLAKAR AYSHKHAIR 💗*

WRITTEN BY AYSHKHAIR 💗

19&20

Haka rayuwan auran mu ya cigaba da gudana nida mubash tun ranar muka shirya muka dawo normal yadda muke daaaa mubash na matuqar nunamun kulawa sai dai shi Sam Bai d'aukan irin wasa da miji d'innan sai yace Wai ai rainine Amman in buqatar sa ta tashi a Rana sai yayi sama da sau 5 hakannan nake daurewa Dan kawai na faranta Mai Rai yau auran mu Sati d'aya daidai niban ga kowa ya shugo gidana ba tunda nayi aure har yau iyayen shi ma ni Babu Wanda nagani yazo Koda cikin Yan uwan sane hakan ba qaramin d'aure mun Kai yakeyi ba Amman ba damar magana yau muna zaune kasan cewan yau weekends ne Ina zaune Akan kujera bayan nagama Yan aikace aikace na mubash kuma na kwance a ciny'ana Yana latsa waya ni Kuma na d'aura hannuna Akan gashin kansa daya cika kaman na daadaa Amman yasha gyara a hankali nake kwantar Mai da gashin waya tace tayi ruri d'aukan wayan nayi Dan tunda nazo gidan mubash ya amsa wayata ya bani Nokia Wai tunda nayi aure baiga anfanin babban waya a hannuna ba chatting daukemun hankali Wai zai yi inkasa bautan aure Nan ya cire mun sim Dina yasamun a qaramin Nokia nidai bance Mai qala ba illa tausayin kaina danakeyi Dan nasan na d'ebo ruwan dafa kaina a hankali naduba Mai kirana Marmy ce aibansa sadda wani kalan murmushi ya fisgeni ba da sauri na d'aga Ina:

"Hello Marmy Na ykk? Ya gida? Ya su Marwa?"

Murmushi marmy tayi sannan tace:

" Amaryan mubash Bata laifi Kota kashe masu gida , shin duk cikin dad'in auren ne yasaki kashe waya har tsawon sati d'aya Aymanah?

Murmushi kawai nayi sannan nace:

"Marmy kedai bari kawai"

"Aymanah daftan kina lfy Kuma mubash na kulan Mani dake Koh?

Satan kallon mubash nayi Wanda baida aiki sai chatting Yana murmushi a hankali nace:

"Eh wlh Marmy Wai Ina Marwa ne "?

"Marwa ta koma makaranta yau kefa Yaushe Zaki koma? "

Murmushi nayi sannan nace:

" Marmy soon , inq maman mu fa ?

" Tana lfy ta fita taje asibity check up"

" Allah sarki kigaisheta Dan Allah "

" Toh zataji kigaida mubash din anjima zqn kiraki"

" Tohm Marmy sai anjima nagode"

Nan mukayi sallama na datse Kiran na kalla mubash Wanda duk hankalinsa nakan waya saifaman murmushi yakeyi ko shidawa ke magana dake sashi murmushi ohon Masa a hankali nace:

"Angon Aymana, Marmy na gaidaka"

"Ok" kurum yace daga Nan baikuma tanka mun ba Nima nayi shuru Ina kallansa a hankali nace:

"Wai Yaushe zamuje gidansu hajiane kaga tun ranar da akayi bud'an Kai fa bamu sake zuwaba"

Tsaki yayi sannan yace:

" Bazan making qarya bafa Aymanah dangina basa sonki!

😨zaro Ido nayi har muryata na tseren fad'in:"basa Sona Kuma Mai na masu?"

Miqewa yayi daga kwanciyan dayayi a laps Dina sannan yasa hannunsa ya lakuta hancina yace:

"Yes basa sonki cuz bake sukayi niyyan na aura ba wata yar uwar mahaifiyata akeso na aura nikuma naqi nace sai ke shiyasafa bakiga sadda kukazo ma Baku wani sama tarba Mai kyau ba? So shiyasa Kuma Hajia tace karna sake na tab'a kawo mata ke gidan ta kowa Wai yayi zamansa anasa gidan Danni kad'ai ta haifa ba ke ba shiyasa ban kaikiba Kuma bakiga kowa yazo ba , yauwa kima shirya anjima da yamma abokaina zasu zo su 3 Kuma anan zasu kwana Dan Haka yau Zaki fara girki Dan ma nqgaji da siyan takeaway ai yau kinyi sati so kifara girki Kuma kiyi yayi dad'i bari yanzun zanfita nasiya kayan Miya tunda shine kawai Babu Naga duk kayan abinci iyayenki sunkawo ko? So kiyi yayi dadi Dan Allah"

Daga Nan ya miqe yana sakanmun murmushin da nakasa fassarashi, 😭ji kawai nayi hawaye na gangaromun a fuska maganganun mubash suka kAsa samun masauki a zuciyata Mai yake nuffi wai iyayensa basa Sona? Basa qaunatana uwar miji tamun iyaka dazuwa wajen ta ? Na shiga uku na lalace ni Aymanah😭maike Shirin faruwa Dani ne Wai innalillahi wa'inna ilahirajiun "

Da sauri nasoma share hawayena Jin motsin futowan shi da sauri na sadda kaina gudun karya gani jinayi yace na tafi sai nadawo "

Gyad'amai Kai kurum nayi tonowa danayi yamun gargad'i Akan inzai tafi basai namai rakiya ba inyi zamana kawai hakan ko nake Mai kullum inzai fita , aiko Yana fita kaman anbud'emun wani babin kukan , da kyar zuciyata ta lallashe ni tace:
Aymanah aure fa kikeyi aure Kuma ance bauta ce kobakya Jin dad'in auran ai bazaki qi kinaimo aljannarki ba Dan Haka kiyi haquri tunda ai ba zaman mamanshi kikeyi ba zaman shi kikeyi kinii Aymanah kiyi haquri ki sadda kanki aduk abinda zakiji Kuma zaki gani kinji?

A Haka nayi na'am da shawaran da zuciyata tabani hakan yasani miqewa na shiga d'akin mubash Dan gyarawa ko ina ya tarwatse yadda na lura mubash qazamine na qarshe saidai Yana gyaran jikinsa sosai Gashi ya iya d'aukan wankan dazai iya tafiya da imanin mutum Amman Kam inyacire kayan sai su kwana 3 baikaisu wanki ba Gashi kayan suta wari inya aske gashin private parts d'inshi kuwa a inda ya aske anan yake barinsu Kai abubuwan mubash day sai Allah watarana har kuka nakeyi Ina kulle hancina in Ina Masa gyaran d'aki yauma hakan ce tafaru bayan na gyara d'akin tas na wanke Mai bayi nafeshe d'akin da turaruka masu dad'i na kunna ac na kunna turaren wuta Nanda Nan d'akin ya d'au qamshi nafito na soma gyara falanma na kunna turaren wuta Mai dad'in gaske Wanda Marmy ce duk tasa aka had'omun su gyara nayi sosai Jin yace abokansa zasu zo chan naje kitchen na bud'e store Nan Naga kayan abinci maqil Wanda mahaifina yasa ka cikamana store da kayan abinci fridge na bud'e Naga Shima shike da Naman kaji da Shanu da rago harda kifi cat fish da sauransu.

Shugowa yayi ba tareda sallama ba hannunsa riqe da wani black leather qarami ni har ya tsoratani kallonsa nayi nace:

"Angon Aymanah sallaman fa?"

Qaramin tsaki yayi sannan yace:

" Opps sorry na manta gidan uztaza Aymanah nake banyi sallama ba afwan salamualaikum"

Dukda shi cikin gatse yayi maganan baihanani d'aukan maganan cikin wasa yayita ba hakan ne ma yasani yin murmushi Ina amsan leather hannun nasa miqamun yayi yace :

"Ayidai yayi dad'i zantafi zamu dawo tareda su bayan sallan magrib kiyi wanka kiyi kwalliya cikin qananun Kaya!

Da sauri na kallesa nace:

"Qananun Kaya Kuma?
D'agamun gira yayi 🤨 yace:

"Yes ko kinsama ciwon kunene?"

Kallon mamaki nabisa nace:

"Abokanka fa kace zasu zo Mai sa zansa qananun Kaya toh shikenan zan sa Amman zansa hijab! "

Kallan uku saura kwata yamun sannan yace:

"Ok kisa kiga yadda ranki zaiyi munmunan b'aci kina Abu tamkar baki waye ba Mai in abokan nawa sunzo Kuma sun ganki Sha nake Suma kaman ni suke awajenki tunda abokaina be yanzu invana Nan ai wani acikinsu Mai riqekine so Mai Dan sun ganki da qananun Kaya ko sindir nace kizo ne? Dawani Zaki fara kawomun qabli da ba'adi su matayensu da muke ganinsu da boomshorts su Mai Kika fisu? Mtseeeewww karkisa Dan Allah kinji"

Daga Haka ya fice ransa a matuqar b'ace Niko tsaban mamaki, taqaici, danasani, kaico ne duk sukabi suka turnuqeni jinake tamkar na d'aura hannuna a sama na fasa ihu wannan Abu damaiyayi kama ?

Shin Wai *Auran wahala* nayine? Nashiga uku Wai kowama inyayi aure haka yake fuskanta ko Kuma mubash ne. Kawai kemun hakan shin dama duk soyayyar a waje ake nuna shi kana shugowa daga ciki shikenan saidai aruqa muzguna ma? Allah gani gareka nidai bazan sab'ama ba wajen farantama mijina ba!

A Haka na juya hannuna riqe da ledar jikina duk amace nashiga kitchen bud'e ledar nayi had'i da zaro ido😨

Tattasai nagani irin Wanda ake siyarwa a cikin farin Leda na hamsin hamsin d'auri biyu Wanda aciki guda hud'une kawai aciki sai tarugu kulli d'aya albasa guda 2🙆🏼‍♀tabd'i abinda bansaba ganiba Dan nikam tun tasowata nasaba ganin buhuhunan kayan Miya a gidanmu bantaba ganin ansiyo na qulliba to Mai zan dafa masu Haka da wannan kayan miyan kad'an tabd'i jam nan adai haka nagyara nayi greating Dinshi nasoma kici kicin girki shida da rabi nagama komai:

Shinkafa fara namusu Wanda nasa Mai colour yazama yellow kaman fried rice sainayi stew da kaza dake inada tumatur na Leda da aka samun a store shi nacika sabida miyan tayi kauri dan duka tattasan najuye tarugu ne dai bansa dukaba sai namasu fruit salad da coconut juice na rufe NASA a fridge na fito na jera abincin a daining na wuce d'akina nayi wanka na d'aura alwala nafito na shafa Mai nasa hijab nayi salla namiqe Dan d'akan kayan da zan sa Amman sai nagani mubash ya fito mun dashi ya sa akan gado Riga da wandone d'amanmu Wanda ko a gabansa kuny'a sasu nakeyi barega abokai
A hankali na d'au kayan nqkai minti 10 Ina tunanin insa ko karnasa chan dai danaji horn din motar shi nayi sauri nasaka sannan na kalla kaina a madubi duk surata abud'e taf d'aura d'ankwali nayi nazauna akan gado na kulle fuskana da tafukan hannayena Ina mamakin maike damun mubash nee Wai ji kawai nayi ance:

"Wow" d'agowa nayi na kallesa sannan na kauda kaina qarasowa yayi ya miqar Dani yakaiki wajen madubi ya sakala kansa akan wuyata Yana sunsunan qamshin dake fita ajikina cewa yayi;

"Kingako yadda kikayi kyau baby tamkar hurul aini nasan abokaina sai sun maki kyauta sabida komai naki intact saidai d'ankwalin Nan dakikasa ya kwafsa maki nan ya cire

Please Login or Register in order to submit comment