Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakane...............

nan na bashi dukkanin labarin Auran wahalan danayi da Mubash daga farko har iska kaina danayi a wannan asibityn!

Tabbas koban gayaba idanun dr Saad sun kad'a sunyi jajir tsananin tausayina suka baibayeshi a hankali ya furta:

"Kaico duniya Allah ya kyauta Allah kuma zai saka maki Aymanah mubash saiya qasqantu a duniyan nan dakuma lahira karki damu kicigabada haquri sabida Allah nacewa acikin littafinsa mai tsarki *Innallaha ma'assabirin* lallai Allah yana tareda masu haquri saboda haka kiyi haquri nikuma in sha allah zan taimaka maki har sai na maidaki gun iyayenki in sha Allah!

Murmushi nayi sannan nace:

"Likita ngde dason taimakamun da kakeson yi saidai muddin mubash na nan bazai barka ka taimakamun ba"

Murmushi yayi sannan yace:

"Hakane saidai mubash tunda yakawoki asibity har zuwa yanzun bai dawoba kinga ko zan iya taimaka maki ta hanyar.............

Nan likita saad ya zayyanomun tiryen tiryen yadda zai taimakamun ba tareda Mubash yayi zargin an taimaka mun na kub'uta a hannunsa ba!

Har cikin raina nayi na'am da wannan kalaman kuma nama likita saad godia sosai!
Chanzamun d'akin kwana likita Saad yasa akayi akamaidani private ward Chan sama d'akin yake sosai nasoma Jin dad'i a Raina na kusa komawa ga dangina kai Allah nagodema da ka aikomun da wannan bawa naka ya Allah kaid'in ubangijin taliqai ne maijin Kiran bayinsa garesa Allah nagodema !

Sai washegari mubash kaman Wanda ka wanchakala yazo asibityn office din Dr Saad yanufa kallo d'aya likita Saad yamai ya shedashi Dan haka cikin zuciyansa yaja wani siririn tsaki maganan da mubash yayine ya maido kallansa garesa:

"Amm likita Ina matata? Dan na duba d'akin da aka kaita Bata gurin"

Zaro glashin dake idanunsa Dr Saad yayi sannan ya kalla mubash din yace:

"Dama matarka ce?!

" Eh"

Mubash ya basa amsa ataqaice, d'an murmusawa likitan yayi sannan yace:

"Asha kana inane tun ranar daka kawota baka sake zuwaba sai yau haka?"

Kallansa mubash yayi sannan yace:

" Mushkila aka samu! "

D'an fuskan tausayi Dr Saad yayi sannan yace:

" Well inaso kasanyama ranka haquri kakuma San kowani bawa da tashi lokacin! "

Kallan likita kurum mubash keyi Yana qoqarin sakala maganganun nasa Dan yasamu ya fahimta inda zantukan likitan ya nufa Amman ganin bai fahimta komai ba yasashi cewa:

"Likita ban gane Mai kake cewa ba fa Sam!"

Ta6e baki Dr Saad yayi sannan ya Kuma sauya fuskansa zuwa na ban tausayi yace:

" Well we couldn't save her!"

Kallan uku saura kwata mubash yamasa Yana fad'in:.

" As in wat are u trying to say like this?"

Miqewa Dr Saad yayi ya zagayo inda mubash ke zaune sannan yadafa hannayensa saman kafad'un mubash d'in sannan yace:

"I mean kayi haquri dukkanin Mai Rai mamacine Allah ya amsa ran matarka tun aranar daka kawota munyi iya qoqarinmu Dan ganin munceto ranta Amman abin yaci tura cux ta zubda jini sosai mun nemeka sama da qasa Dan kabata jininka bakanan kafin aje anaimo jinin da zai yimata Allah ya amsa abarsa! Am sorry Allah jiqanta!

Dagaske ainun mutawar Aymanah ta sosa zuciyar mubash sabida ji yayi tamkar a dalilinsane aymanan ta rasa ranta wani sabon soyayyarta ne lokaci d'aya ya dawomai ji yake inama Akan maida hannun agogo baya da tabbas zai maida yasoma rayuwar aure Mai dadi da Aymanah Amman is too late now abubuwan dayake mata kurum yaruqa tunowa mubash harda d'an kwallansa!

(Niko nace maida hawayen naka munafukiπŸ€¨πŸ˜’ai hawaye da kuka tartilan yanzun kasoma yinsu malam mubash save ur tears Dan nangaba karka naimesu karasa Dan sune zasu zaman Maka farin cikiπŸ˜’)

"


" Aymanah ki yafemun ki yafeni Allah jiqanki"😰

Yana maganar Yana share kwallan sa Dr Saad ko ta6e baki yakeyi aransa Yana fad'in:

"Mugu azalumi kurum ai Dana biyema da tun bayauba Aymanah ta rasun na gaske Wawa!"


Amman a fili sai ya tausasa harshensa Yace:

"Ayi haquri aduaa kurum take buqata ba kukaba"

" Hakane likita Amman Ina gawar nata yake? "

D'an ta6e baki Saad yayi sannan yace:

" Dake bamuganka tym din ba yasamu tunanin ko ba matarka bace taimakonta kayi yasamu maida gawanta mutuware Dan Nan ne kurum gawan nata will be save kafin anaimo danginta Amman tunda kazo zamu iya baka gawan nata sai muje kayi signing ka Kuma biya naira dubu tamanin na kulawa daakayi da ita na wannan lokacin"

Zaro idanu mubash yayi yace:

" 80k fa? "

Girar sama da qasa Dr Saad ya had'e Yana fad'in:

"Yadai haka price din yake waima Dan wannan 3days ne kurum!"

"Banida wannan kud'in yanzun Kuma bamuda kowa a Nan birki nafaso likita! "

" Ok ai zaka iya barin gawar har sai ranar daka samu adadin kud'in da tayi sai ka biya abaka gawar nata"

Wani dabara ne yafad'oma mubash Dan haka yace: axuciyansa:

" Ko na amsa gawan ma uban wa zan naimo sumata salla gwara tayi zamanta anan inyaso insun gaji da ajiyeta sa San yadda zasuyi da ita Dan nikam anjiman Nan ba gobe ba zan tattara na koma Nigeria!


Murmusawa yayi yace:

"Likita abarta anan d'in in yaso nasama kud'in saina zo na biya aban gawan"

Wani qayattacen murmushi Dr Saad yayi ganin cewa plan d'inshi yayi working yadda yakeso Kuma zai iya taimaka ma Aymanah kenan lumshe kyawawan idanunsa yayi sannan yace:

"Ok as u wish Allah kaimu ranar!"

"Ameen "..


Miqewa mubash yayi Yana ma likita Saad musabaha Yana cewa:

"Toh Dr sai ka gannin"

Murmusawa kurum Dr Saad yayi sannan yace:

" Alryt see you then! But bazaka ga gawan nata ba kan ka tafi?"


Waigowa mubash yayi yace:

" Will see her some other tym Allah jiqanta banson warin gawane Kuma kasan yadda mutuware yake da seant Mara dad'i"


Murmusawa ta gefen baki kurum Dr Saad yayi sannan yace: cikin ransa" better for u"

Amman a fili sai yace;

"Ok ok I get u! Bye then!"


Fita mubash d'in yayi ba tareda ya waiwayo likitan ba shiko likita Yana fita yaja dogon tsaki ya furta a fili:

"Very stupid human being da sannu zaka biya abinda kayi"


Daganan ya juya ga wani camera Yana fad'in:

" We are done pretty"


Niko wani kalan ajiyan zuciya nayi sannan na jinjinamai hannu alamun good job duk abinda suka tattauna Ina zaune Ina kallo a system dake jone da CCTV din office d'in Dr Saad !


Kulle system din nayi Ina furta Allah Alhmd................


.*Real pure moment of life writers*



😭 *AURAN WAHALA KOH SAKI*?πŸ™†πŸ»πŸ“πŸ˜­


*by Ayshkhair*



☺ *Jinjina Agareku Ayshkhair novels da Romantic writers fans tnx so much for the love huuun*😍


_Bazan manta dakuba kud'in na musamman ne Ayshkhair naji daku_:

*Maleeka*
*Hauwee*
*Temmah marafa*
*Maman inteesar*
Inayinku thanks uπŸ’™


*Page 41_42*


Kulle system d'in danayi da mintuna 2 Dr Saad ya shugo d'akin fuskansa d'auke da murmushin dake haddasa Mai matsanacin kyawuu nikam badan wani abuba danace Yana mun kama sak da yaah hydar sai dai yaah hydar yad'an fisa tsayi da qiba ne kurum Amman suna yanayi Kam sosai maganar sace tamaidani duniyar tunanin da nakeyi numfasawa nayi nace:

"Naam"

QuriYamun da manyan idanunsa nawasu secns sannan ya janye idanun nasa akan nawa Yana Mai lumshe su a hankali yace:

"Tunanin Mai kikeyi?"

"Babu komai" 😊

Na mayarmai a taqaice:

"Ok kishirya zuwa gbe zaa sallameki sai mukoma gida ko? "πŸ˜„

Ya ida maganar Yana wani kalan murmusawa Nima murmusawan na mayar Mai kurum miqewa yayi ya fita ni Kuma na zame na kwanta had'i da lumshe idanuna na fad'a duniyan tunani!

A daa in wani yacemun ni Aymanah zan tsince rayuwata a yadda nake yanzun Dana musamai Kuma nace maqiyina ne Amman ayanzun nake qara yarda da cewa wlh mutum mutum ne kurum ran ne kurum abin tinqahon mu Amman inba haka ba bamuda iko da komai a rayuwar mu sai yadda Allah ya tsara Mana Kuma babu wani bawa da ya wuce Allah ya jarabcesa wlh koshi wayene ko yafi qaruna kud'i ko yafi fir'auna sarauta yooo ko K'arunan ma da ragowan kud'insa kowa a duniya ke fatali da shi Allah ya jarabcesa bare mu! Allah sa dai mucika da kyau da Imani kurum Allah Kuma yasa dukkaninmu dake fuskantan wani jarabawa a rayuwannan Allah yabamu ikon cinyewa ya Kuma bamu ikon iya jurewa!

(Ameen AymanahπŸ˜ŠπŸ™πŸΏ)

Da wannan tunanin bacci b'arawo yazo ya saceni sau biyu Dr Saad nazuwa Yana dubani Amman Yana iske ban farka ba gashi lokacin tafiyan sa gida yayi Dan haka yasa wata nurse ta kula Dani takuma tabbatar naci abincin da ya siyomun nakuma Sha magani tace Mai in Sha Allah zatayi ya wuce Yana mata godia!



Washe gari sai misalin 9:30 Dr Saad yazo kasan tuwan yau d'in takasance weekend so baida duty yau ya sashi d'an baccin gajia Mai tsayi har kusan 9:30 kan yazo asibityn dubani!


Nidai tun safe nake zullumin tunanin irin rayuwar da zansoma Kuma a gidan su Dr Saad d'in ban Kuma San dalilin da yasa naji zuciyata ta kwanta dashi Dr Saad d'in ma'ana inaji bazai cutar daniba taimakona zai yi tsakaninsa da Allah!

Sallamansa ce ta katsemun tunanin nawa amsawa nayi had'i da d'ago Kaina na tsaidasu akan fuskansa:

"Fatabarakallahu ahsanal kaliqin"

Shi naji zuciyata na furtawa a hankli saman la66ana ma suna Taya futarda maganar Amman a hankali tayadda kowanda yake kusa Dani baizama lallai ya jiyo abinda nake fad'in ba!

WANI kyau yayi sosai kodan ban tab'a ganinsa cikin kayan gida bane that y Amman Kam yayi kyau ainun Sanya yake cikin kaftan inda akama d'inkin rigar in 3qter size kayan jikin nasa brown ne yayi matuqar amsan jikinsa hulan kansa da takalmin kansa duk brown sai fidda wani ni'imtaccen qamshi Mai sany'aya zuciya yakeyi kwarai wannan mutumin Allah yayi halitta ajikinsa shikam inbai godema Allah ba bazai qimai biyayyaba da bauta masaba!


Ashe har ya matso gab Dani banma luraba nafada duniyanan tunani:

"Aymanah!"

Yafad'i sunan nawa acikin husky voice d'insa firgit na kallesa nace:

"Naam"

Zama yayi d'an nesa Dani yad'an nazarceni kafun ya bud'e baki yace


"Yajikin naki?"

"Da sauqi sosai"

"Babu dai inda yake maki ciwo ko? "

Gyad'amai Kai kurum nayi sannan nace:

" Babu nagod sosai da taimakona"

Murmushin gefan baki kurum yayi sannan yace:

"Allah qara sauqi ga wannan kije kishirya sai kizo mutafi gida su habeebty na jiranki! "


Murmusawa nayi nacemai tohm a Raina Kuma ina fad'in sukam Nan kowani suna sakama mutum suke yanzun haka qilan yarsa ce habeebtn ko qanwarsa ko kakarsa ko mahaifiyarsa miqewa yayi ya fita nikuma na shiga ban d'akin na tsaftace jikina Dan har yanzun ban gama bleeding ba yana mun a hankali dai ledan da yaban na bud'e wani dogon riga kamar abaya ce aciki pink colour da d'an kwalinsa da Kuma takalmi murmushi nayi sannan nasaka kayan Aiko Nan yamun d'as saidai ramar danayine kurum yad'ansa wuyan yamun yawa kad'an kallan Kaina nayi a madubi kayan sunmun kyau ba laifi Amman Kam nayi duhu sosai manyan idanuna duk sun fad'a kaman bani Aymanah ba!


Nan dai nashirya nafito ganinsa nayi zaune Yana latsa waya tsayawa nayi a qofar bayin kurum ina wasa da yatsun hannuna kaman ance yad'ago ya Taras Ina tsaye Ina wasa da yatsuna murmusawa yayi yace muje ko miqewa yayi sannan yasoma tafiya nikuma nabi bayansa har muka fito far fajiyan asibityn:



Wajen parking lots muka nufa wani dalleliyar motar dake fake ita kad'ai awani side naga ya nufa Dan haka nabi bayansa nima Danna key in yayi motar ta bud'e zagayowa yayi ya bud'emun sannan yacemun Bismillah shiga nayi ya rufemun sannan ya zagayo Shima ya shiga yatada motar!

Lallai Koda motar kawai na barku masu karatu yaci ace kusan Dr Saad hamshaqin Mai kud'ine!


Tafiya mukeyi bamai cema komai qala har mukai tafiyan kimanin mintuna 25mins gaskiya qasar birki nafaso akwai kyau Niko a mafarkima ban tab'a tunanin zuwa Nan ba Amman yau qaddarar rayuwa takawoni!


Wani had'ad'an layi naga munshiga Wanda layin tunfarkonsa har qarshensa da wuya ka iske Mara kyawu da fasali a wani makeken gate naga ya tsaya Yana danna horn gaskiya duk jerin gidajen dake wajennan wannan gidan yafi kyau da tsaruwa bangama shagalta da gidanba Saida muka shugo farfajian gida tab ai wannan ita ake Kira aljannar duniya tsayawa tsaramaku fasaltuwan gidan da kyawun gidan sai yasama mujima ban gama Baku labarin rayuwata ba!

Nabarku ku qiyasta dakanku!


Wajen parking lots muka tsaya wajenma kurum abin kallone Saida ya kashe motar sannan ya kallane yace:

"We are home!"


Murmusawa nayi kurum shikuma yafito ya bud'emun a hankali nasakala qafata nafito had'i da furta Bismillah!!


Ni'imtaccen iskane yasoma kad'a jikina ahankali muka jero muna barin harabar parking d'in kallan farfajian gidan nasoma yi na lura kowani lunguna da saqo na gidan d'auke yake damasu tsaro dake Sanye da black suit da black spectacles (glasses) hannanyensu riqeda bindiga hakan sai ya birgeni na Kuma lura ko Ina akwai. CCTV camera hakan yad'ansani shakku wani side muka nufa inda yake gaba Ina binsa a baya!


Har muka shugo hmmmm waiyoooo cikin gidankam baa magana Dan Babu abinda Babu sallama ce d'auke abakunan mu muka shugo ba tareda munsamu an amsamana ba shigowanan da muka idasa yi cikin falane yasani tabbatarwa da babu kowa a falan muna shugowa Dr Saad ya kalleni yacemun:

"U are welcome home Aymanah make ur self comfortable bari nakira su habeebty! "


Gyad'amai Kai nayi Ina Kuma Mai murmusawa Saida ya tabbatar nazauna sannan ya wuce ya haura saman upstairs dake cikin falan nikuma nabi falan da kallo!


Saukowan su nasoma ji hakan yasani snanin suna qarasowa kenan Kuma gyara zamana nayi na durqusar da Kaina qasa Ina kallan hannuna! Jinayi Ana cewa:

"Haa'a lale marhaban da Aymanar mu!"


Murmushine ya su6ucemun sannan na d'ago Kaina na saukesu Akan wacce taimaganar!

Ma Sha Allah wata kekkyawar budurwace wacce a qalla zata Kai kimanin shekaru 23 kekkyawace ajin farko doguwace tas Mai yalwataccen idanu da gashi Dan ta bazo gashin nata ne har wutsiyan kafad'unta tana Kuma sany'e da wani dogon riga Mai kyau murmushi nayi inda ta qaraso inda nake zaune ta zauna had'i da kamo hannayena!

Hakan yasani Dan Sadda Kaina Ina murmusawa diga gani tanada faraa dason mutane maganantane ya katseni inda take cewa:

"Aymanah ya jiki?"

Batareda na kalletaba nace:

"Da sauqi sosai wlh"


Zatayi magana kenan mukajuyo muryan Dr Saad yana fad'in

" Ohoo Amma kije kiganta tafi habeebtynki kyau faaa!"


Hakan ne yasa wacce kezaune Dani dariya tana miqewa tana fad'in:

"Amma shareshi kinji zoki ganta"

Nan suka qaraso nidai Kaina a qasa maganar wacce aka Kira da Amma naji tana cewa:

"Lale marhaban Dan 'yata d'ago ki kalleni"


Cikin yanayin kunya na d'an d'ago Kaina nakelleta ina sauko qasa Ina gaisheta Wanda hakan ya matuqar matA dad'i Dan ganin yadda na mutuntata:


"Aaaa zauna kinji miqe kizauna ma Sha Allah Ashe dai dagaske ansamo min wacce tafi habeebty kyau yau"


Murmusawa nayi dannikam ban magane wayene wannan habibtyn dasuke yawan kiraba: murmushi kurum nayi yajiki Amma tamun had'i dacewa Allah bani lfy Kuma nasake jikina taredasu tamkar Ina gida Saad yabamu lbrnki Kuma mun tausayamaki Allah bimiki haqqinki kinji"


Godia na mata sannan tace ba komai cemun tayi:


" Ni sunana Ruhaimah saidai 'yayana nacemun Amma wannan Kuma babban d'ana Saad sai wannan Kuma qanwarsa iftital"


Murmushi nayi kurum bance komai ba!


" Iftital kaita tayi wanka tahuta ko?"


Murmusawa iftital tayi had'i da kamo hannuna muka haura sama wani d'aki Mai kyawun gaske ta bud'e sannan tamun iso muka shiga sofa d'in dake falan ta nunamun tace zauna Bari na had'amaki ruwan wanka murmusawa nayi sannan tashiga bayin d'akin Bata jimaba tafito tana murmushi tace:

"Aymani shiga kiwatsa ruwan na had'amaki"


Cemata nayi nagode sannan namiqe nashiga kasan cewan na iya anfani da irin bayin yasa banyi qauyanciba Dan sak irin bayinmu Keenan najima Ina gasa jikina inda naji dad'i sosai sannan na wanke Kaina nafito d'aure da towel d'ayan towel d'in Kuma Ina tsana gashin Kaina Koda nafito sai na Taras ta fiddomun da kayan sawa hakan yasani murmushi shigowanta d'akinne ya sani d'agowa inamata murmushi itama murmushi tamun tace ayyah sorry nazo nuna maki mayukan shafawane"

" Laa ba damuwa"

Bavata amsa nunamun tayi sannan taban dryer tace nayi drying gashina! Nan tafita nikuma naje na shafa mayukan data nunamun had'i da drying Kaina!


Saida nagama sannan nasaka dogon rigar data bani Aiko nafito d'as Kai wankama da gyara jiki rahmane Dan harwani kalan sany'i nadaban nakeji ajikina dad'i koina jikina kemun rabonda nayi wanka da ruwan zafi Mai yawa da sabula masu qamshi haka tun Ina Nigeria!


Kallon Kaina kurum ba tsaya yi a mirror ba qarya nayi kyau dukda bawai namaida asalin kyawun da Allah yamun bane Amman nasan with tym komai zai dawo normal daga bayana naji Ana furta:

"Wow!"

Hakan yasani waigowa Ina mata murmushi itama ta mun tana fad'in:

"Wow Aymanah haka kike da kyau ai kinfi habeebty kyau da gaske"


Nikam zanso nasan wace wannan habeebtyn daake had'ani da ita komaisa oho!

Kama hannuna tayi tace muje family najiranki a dining"


Nan muka jera muka fito saidai barin side d'in gaba d'aya mukai wani side d'in nadabn muka nufa Wanda yafi wanchan nafarkon kyau da tsaruwa want babban dining area na hango dake d'auke da mutane kimanin 6 dukkansu kyawawa qarasowa mukai sannan na durqusa Ina gaidasu amsamin sukai Rai sake!

Iftital ta miqar Dani ta zaunar Dani a gefen ta nidai Kaina a qasa Amma ce tace masha Allah 'yata karya sai na gabatardake ga mutan gidan!


Hakan ko akayi muka Soma karyawa Babu abinda kake juyowa sai qaran fake da spoons!


Saida muka kammala sannan masu aiki in uniform suka shugo suka kwashe kayan Amma ce tayi gyaran murya sannan tace:


" Ma Sha allah nasan dukkaninku dai kusan lbrn Aymanah tunkan tazo Kuma kun tausaya mata matuqa gatanan yau kungata"

Murmusawa sukai dukkaninsu Amman tace:

" Aymanah d'ago kanki namaki bayaninsu"


D'agowa nayi a hankali Amma tasoma gayamun:

"Wanchan Dr Saad babban d'ana Mai bimasa Zainab tana aure a Uganda sai wanchan Habib sai Marmy co-wife d'ita itakeda habib da Zainab nikuma Saad da iftital"..

Murmusawa nayi sannan tace:

" Ga habeebty nan.!"


Da sauri na d'ago Kaina Dan ganin habeebtyn fatabarakallahu ahsanal kaliqin gaskiya ita kekkyawace wlh tsayawa fad'in asalin kyawunta wlh b'ata lokacine tanada kyau na lahaula kyawun nata har yaso fin qarfinta Niko waneni na had'a kyau da wannan Kai tanada kyau Kam dukda nasan da kyawuna nanan na daaa zamud'an goga wajen kyawun Amman a yanunkam itad'in sarauniyar kyawawace!


Magnanan Ammane ya maidoni tunanin danake :

"Habeebty ita Kuma............. ✍🏼


.*Real pure moment of life writers*



😭 *AURAN WAHALA KOH SAKI*?πŸ™†πŸ»πŸ“πŸ˜­


*By Ayshkhair*


*Page 43&44*


"Habeebty ita Kuma matar Saad ce! Itane Habeebtyn da muke Gaya maki"

Da mamaki nacigaba da kallan wannan kekkyawar halittar itace matar Dr Saad ba shakka Kam Dan sun matukar da cewa da juna ma Sha allah Ashe yanada mata Inka gansa bakacemai magidan ci ba sosai Habeebty ke sakarmun murmushi Wanda har dimples nata sai lotsewa sukeyi chanciki Wanda shi ke Kuma fidda matasanacin kyawunta hmmm wannan da zamannin annabi yusufa muke sai ace cikin jininsa tafito! Muryartane maikamada algayyata ya furta sunana:

"Aymanah yakike Yaya Kuma jikinki?"

Cikin Yar mamakin hausan datakeyi Dan duk azatona batajin hausa sai naji akasin hakan murmusawa nayi nace mata "da sauki sosai"

Fuska sake tace Allah qara lfy daganan tamiqe tazo inda nake ta riqe hannuna ta miqar Dani tana fad'in muje muje kihuta part Dina Zaki zauna"


Murmusawa kurum nayi Dr Saad naji Yana fad'in:


"Habeebty kinaso ki kwacema Amma itane ko?"


Cikin sigar hararar wasa tace: " Zawj ai Amman dakanta tace tabarmun ita! Muje Aymanah"

Daga haka tawaiga tana Jan hannuna har muka fice a part din su Amma namana Daria!


Tafiya Mai d'an Nisa da part din da muka fito mukayi Dan har d'an qaramin dogon titine ke shimfid'e a farfajiyan wajen inda shine yaraba part din gidan wani part muka dosa Wanda shi kana ganinsa kasan ginin gida guda ne sukutum gidan yayi mugun tsaruwa Shima baje yake da bodyguards marasa annuri dasakin fuska !


"Musa shiga straight falo muka shiga inda tsayawa fasalta kyawun falan 6ata lokacine wlh saidai kana shugowa falan hotunan Dr Saad da habeebty ne kurum zasu Soma Maka sallama hotunansune takowani lunguna da saqo acikin falan Wanda tsayawa gayan kyawun dasukai 6ata bakine da Kuma lokaci!


A falan muka yada zango inda ta zaunar Dani kusa da ita tana fad'in :

"Wash Allah na Kinga wlh yau nagaji sosai"


Murmusawa kurum namata sannan naji ta riqe hannayena ta sakasu a cikin nata sannan ta kalleni tana fad'in:


"Aymanah"

A hankali na furta "naam"

Murmusawa tayi sannan tace:

" Sannunki da zuwa gidan shugaban qasan burki nafaso ! Nidai sunana Fahimnah Farhan Fahad nidai ba er Nan burki nafaso bace ni Yar qasar Saudi Arabia ne saidai mamana er Nigeria ce a garin maiduguri take a Saudi aka haifeni nayi yarintata a Chan sannan Kuma na girma a Chan Dan inada shekaru;13 mahaifina yarasu Kuma nikad'ai suka mallaka hakan yasa muka dawo qasar Nigeria da zama inda anan na kammala girmana da Kuma karatuna inda aure ya maidoni Nan burki nafaso mun had'u da mijina a Saudi ne lokacinda nakai ma en uwan mahaifina ziyara Nan muka qulla soyyah wacce har takaimu ga aure inda ayanzun auranmu kimanin shekaru 4 Keenan d'an mu d'aya Fa'eez inda yake Chan Nigeria da mahaifiyata tun bayan yayesa danayi yakoma Chan saidai yakan zomana hutu! Habeebty shine sunan da dangin mijina suka laqamun ranar bud'an Kai na aurena hakan yasa sunan yabini har ma Fahimnah keson b'acewa! Lallai naji labarin rayuwarki da Kika baiwa mijina natayaki baqin ciki da Kuma tausayi lallai wanna jarabawace Allah ya had'aki dashi saidai yazuba ido yaga kozaki iya cinye jarabawarce ko aa Alhmd ked'in macece Mai qarfin hali dakuma Imani shiyasa Allah ya Soma sauqamaki Jarabtar dakike ciki Allah ya shigoda mijina Dani da danginsa cikin rayuwarki Dan mutaimakeki ne Kuma in Sha allah zamuyi iya bakin qoqarin mu Dan ganin mun taimakeki iya gwargwadon iyawar mu!


Allah ya qare tsaremu ameen! Lallai ni Fahimnah namaki alkawari zan taimakeki sosai inda harsai kin kifa babban tahiri akan mubbashir da kowani ahali masu halyayya irin nasu in Sha allah sai na taimaka maki kinbi hakkinki kin hukunta mubash in Sha Allah!


Saidai zan ce maki komawanki gida Nigeria bazai Yu yanzun ba!...


Tun da tasoma magana ban d'ago na kalleta ba sai yanzun Dan mamakin furucinta nidanasha ko sati Bazan yiba zaamaidani gun iyayena Kuma yanzun inji ana fad'in komawata ba yanzun ba hakan yasani kallanta da San Jin dalilin hakan?!

Numfashi ta sauke sannan tace:

"Yes Aymanah koma wanki not now and not soon! Dalilina na cewa haka kuwa shine to make u achieve wat u want to achieve tun kan kizo Nan na qudurci hakan a zuciyana har na gayama Zawj (Dr Saad) Kuma ya amince Dan Jin hujjojin nawa Wanda kema zan Gaya maki su a yanzun!


Aymanah koma wanki wajen iyayenki yanzun bai kamace kiba! Dalili kuwa shine ko kin koma wajensu a yanzun still bazasu sake sosai ba Dan akwai igiyan aura mubash akanki har 3 hakan ko zaisasu kasan cewa cikin baqin ciki Dan ko kin koma bazakisan inda mubash yake ba ko lbrn inda yake hakan zai saki zama da auransa akanki Kuma kikasa auruwa Wanda hakan bazai ma iyayenki dad'i ba!


Da wannan dalilin nakeso kizauna damu anan kikoma makaranta kisoma daga 2lvl afannin law dakika Soma karanta a Nigeria Wanda dashine Kuma Zaki iya fansar abinda mubash ya aikata a gareki Kuma dashi Zaki fanshe ran gudan jininki da mubash yayi silan kashewa ! Da wannan makamin aikin naki ne Kuma Zaki koma ga iyayenki inda zasuyi alfahari dake da Kuma godema Allah Akan b'atanki bai sa rayuwarki ta gur6ace ba! Illama wani kaso da ya kafa a rayuwarki Wanda ko en baya aka bama labarinki zasu ji qaunar zama jaruma kamarki inda nasan mutane dubunne zasuyi alfahari dake sannan Kuma zasu so suyi koyi da hali irin naki !


Nikuma namaki alqawari daga Rana irin tayau zan taimaka maki har sai mubash yadawo a tafukan hannayenmu yake yawo! Hummmm Aymanah nid'innan na karance criminology ne Dan haka nasan dukkanin wani hany'a da ya kamata nabi Dan damqo masu hali irin mubash Kar 6atansa yasa maki shakku Akan Bazan iya naimo saba!

Aa wlh ko baitul Mani mubash yake zan iya binciko inda yake Kuma yasoma yawo a tafin hannuna saidai kona naimosa kafun kigama karatunki Bazan damqashi garekiba harsai randa kikazama cikakkiyar lawyer a inda a ranar zan danqa maki mubash ke Kuma ki damqasa ga kotu kuyi sharia dake da shi inda itakuma zata hukunta sa daidai abinda ya aikata bama akanki kurum ba Akan duk wasu da Yama haka inda kotu zata amsan maki takardar sakinki a wajensa kekuma kin wanke qafarki a duk wani shirgi keda mubash inda Zaki cire dukkanin tunanin say ranki Zaki zama pure Aymanah bake ba mubash sannan Kuma ki koma gun danginki kizame masu tauraruwa daganan ki aura Wanda ranki

Please Login or Register in order to submit comment