Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

falan sai tashin qamshi duk da yaah hydar falansa bai rabuwa da qamshi nayau Kam qamshin na dabanne hakan yasake tabbatar mun yaah Hydar yayi aure! Nidai sai faman nanata aduaa nake a xuciyana!

Daidai wani d'an d'aki muka tsaya nidai sai bin Marwa nake da kallo , murmusawa tayi sannan tace:

"Yauwa anan wacce ya mallakama zuciyarsa take "
Dam dam daaadam kakejin qirjina bud'e qofar tayi a hankali muka shiga Saidai d'akin da duhu tsinto muryan Marwa nayi tana fad'in:

"Aymany kulle idonki karki bud'e sai innace ki bud'e su"!


Nikam duk na qosa hakan yasani kulle idanuna har Saida Marwa tace:

"Oya bud'e"


A hankali nake bud'e idanun nawa har na saukesu Akan bangon d'akin dake hasko hotunan yariny'a da Bata fi shekara 4_5 a lokacin ba cigaba nayi da ware idanuna Dan tabbatar da Wanda nake gani d'in!

Nice fa😨Ni Aymanah hotunana nake gani suna haskowa tun Ina Yar kucilata tsayawa nai chak ina kallan hotunan dasuke ta hasko hotunana bankaiga qara tsinkewa da al'amarin ba Saida Naga hotunana tareda yaaah Hydar wasu Ina sa6alle a bayansa shikuma ya riqemun teddy muna dariya wasu Kuma Yana ban ice cream abaki hotunana dai kala kala !

"Bala'i dama Wai yaah Hydar Yana kulani lokacinda nake yarinya?Mai sa yaah Hydar sa hotunana a d'akin nan?!

Bankaiga samo amsan tambayar tawaba idanuna suka sauka akan wani qaton frame dake d'auke da zanen fuskata lokacin ina ga tym Dana kammala karatun law d'ina ne!

Kai tayaya yasan da hoton Nan aaa aima zanani akayi da sauri na Isa gurin Ina qarema hoton kallo tabbas wannan zanan mutum ne ya qeresa da basirar da Allah yamai nadai san yaah Hydar ba Arct ya karantaba nasandai lokacin yanada burin zama Mai Zane Zane sabida ya iya Zane Amman mahaifinsa ya hanasa !

Waigowa kurum nayi ina kallan Marwa kallan bangane komai ba!


Murmushi Marwa tayi sannan ta dafani tace:

"Hmm aymany ungo wannan"

Tamiqamun wani littafi Mai Kama da diary Mai kyawun gaske!

" Ki nutsu ki karanta Dan duk amsoshin tambayarki Yana cikin wannan littafin su zasu Baki amsan tambayar ki if Kika Gama karantawa nikuma zan maki qarin bayani!"


Daganan ta sany'a Kai tafita Niko nabita da kallo sororo nakalla littafin nakalla qofan da Marwa tabi!

Ganin ankusa fitowa masallaci yasani fitowa a d'akin da sauri nashiga part in yapendo na koma d'aki na Adana littafin sannan nayi salla nafito na iske kowa a falon qasa ana jirana!
Idon yaah Hydar qam akaina sunkuyar dakaina nayi kurum nara6a tagefe nazauna Abbansu Hydar ne yayi gyaran murya bayan yayi sallama da qara godia gasu Dr Saad yace :

"Aymanah munajinki shin Ina mijinki?"

D'agowa nayi karaf idanuna suka sauka Akan ya Hydar wani kalan murmushi yamun a hankali nima na mayar masa sannan namaida Kaina qasa nasoma wasa da zoben hannuna a hankali nasoma labartamasu tiryen tiryen abinda yafaru Dani Babu motsin da kakeji a falan Nan inba muryata ba kowa yayi tsit Yana saurarona tun ina jawabi Ina sharar kwalla hardai na 6arke da kuka Mai tsuma Rai Marwa ce da habeebty suka matso daf Dani suka rungumeni suma suka fashe da kuka aka rasa Mai lallashin mu tabbas kowa ya tausayamun a wajennan yaah Hydar duk iya jurewarsa Dan ganin hawayensa da yaketa 6oyewa Basu zuba ba Saida sukaci qarfinsa suka Soma zuba zuuu a kuncinsa!

Tsayawa fad'amaku kukan da dangina sukai Akan labarina 6ata lokacine Babu Wanda acikinsu bai zubarmun da hawaye ba musamman zubarmun dacikin da mubash yayi Saidai sunyi farincikin mutuwarsa Dan acewarsu anrage mugun iri!


Sai da mukai kukan mu ma'ishi muryan Dr Saad ne ya maido hankulanmu gareshi:

"Tabbas a farko Dana taimaka ma aymanah bansantaba bankuma San komai nata ba Saidai bayan komawarta gidanmu da sati d'aya mukai magana da Abokina Hydar inda yake sanarmun 6atar qanwarsa harya turamun hotonta ganin farko nagane cewa Aymanah ne hakan yasa nama Aymanah hoto naturama Hydar Yana gani yazabura yakirani yace Aina naga Aymanah ? Dakyar na kwantarmai da hankali nabasa lbrn abinda yafaru tundaga Nan Hydar yace na riqe Aymanah harsai ta fita acikin quncin datake ciki Dan dawowanta Nigeria babu abinda zai Kuma jany'o Mata face damuwa Kuma hankulan iyayen mu bazai kwantaba Dan baasan inda mubash yake ba kuma gashi aurensa na akan Aymanah!

Da wannan muka Yankee hukuncin naimo mubash inda matata muka bama wannan damar kasan cewarta zaqaqura a fannin naimo Mai laifi hakanko akai tundaga Nan muka Soma binciki har Allah yasa muka gano mubash har Kuma Allah yasa Aymanah ta Gama karatunta lfy! Hydar kanzo jefi jefi qasar Yana ganin Aymanah Dan ko ranar graduation natama yazo Kuma wannan kyautar Dana Baki acikin box hydarne yaban nabaki shiyasa dakikazo mun akan Jin ba'asin boz in nace kije zan Gaya maki watarana! "


Hohoooo masu karatu ai wani saban kukane na Kuma 6arkewa da shi miqewa nai naje na rungume yaah Hydar qam Dan kobaace munba Kuma ko bai gayamun ba nasan wlh Yana Sona ER takardar dake cikin box d'innan ya tabbatar mun da haka qanqameshi nayi inata kuka inamai godia shiko rasa abinda zaimun yayi!

Nan yashiga bibbige bayana a hankali har Saida na tsagaita kukana d'agowa nayi na kallesa nace:

"Haqiqa yaah Hydar kaid'in Mai qauna tane tsakaninka da Allah! 😭ngde ngde Allah sakama da alkairi! "

Murmushi kurum yamun!

Masu karatu Bari na taqaita maku aranar dai aka tsaida maganar aurena Dani da yaah Hydar sati biyu masu zuwa Dan ayi dasu Amma Kuma zai tafi Cyprus Nanda wata d'aya yin wani course nashekara 2!

Yaah Hydar dakansa ya fidda maganan yanasona Kuma Yana so ya aureni kowa yayi murna musamman Ni masu karatu tsayawa fad'i maku murnar danai wlh 6ata lokacine!


Haka rayuwa tacigaba da gudanar Mana cikin Jin dad'i kowa sai shirye shiryen bikinmu yake Dan Babu Wanda ya koma gidansa sai angama biki!


Shaquwace ta musamman ta shiga tsakanin dangina dasu Dr Saad !

Qaunar junanmu nida habeebty sai gaba gaba yake iftital Kuma suka qulle da Aymanah !

Wata Mata a Chad aka d'ako na musamman take gyaramu duk mu hud'u Ni habeebty Marwa iftital Saidai Ni nawa na musamman ake!


Masu karatu babin shafin soyayya na musamman muka bud'e nida yaah Hydar dankam wlh har mamakinsa nake yadda yake shagwa6emun ya kainainayeni da zafafan kalmomin soyayya abin baa magana!


Komai akasamai Rana Dole sai yayi a yau jummaa aka d'aura auren *Aliyu Hydar Abubakar da Aymanah Mubin lere* Akan sadaki dubu 50

D'aurin aurene dayasama d'unbin jamaaa mayyan en kasuwa gwamnoni senotoci Kai har shugaban qasa Saida ya halicci wannan d'aurin aure!

Murna gun iyayena da yayyina da uban gayyan Yaah Hydar baacewa komai a ranar akayi dinner yaah Hydar ya kashe kud'i kaman baisan zafinsuba!

Komai ya qayatar a daran ranar kuma aka Kaini gidan mijina anan wuse2 agarin Abuja nayi kukan rabuwa da iyayena kaman barin qasar nai gaba d'aya!


A daran ranar Kam munsha soyayya nida mijina har baacewa komai mun biyama juna buqata cikin Jin dad'i duk da na sha baqar wahala gun yaah Hydar Kam Dan jinai tamkar aranar ake rabani da budurcina lalle yaah Hydar cikakken namijine Dan awannan daran Saida ya mantar Dani da duk wani damuwata !

Yaah Hydar sai faman samun albarka yake tamkar shine Wanda nafara miqama budurcina!


Sai bayan bikinmu da kwana3 su Masoyiya suka koma birki nafaso munsha kukan rabuwa da juna har baacewa komai!

Tafiyansu da sati muma muka takarkata muka koma qasar Cyprus inda muke cin amarcinmu son ranmu!

Tsantsan soyayyah da zaman lfy nida yaah hydar muka shimfid'a a wannan qasar kowa baya burin 6atama d'an uwansa Rai!


Nikam saiyanzun nasan dad'in aure wlh!

Mijina na qaunata har Ina Gaza sanin irin San da yakemun!

*******************

Bayan shekara 5

Aymanah ce kwance Akan qirjin yaah Hydar shikuma sai faman shafan bayanta yake Yana gayamata wasu kalamai a kunnuwanta itakuma tana dariya kiranta daakeyine yasata d'agowa!:

"Mommy mommy! Daddy"

Wasu kyawawan yara masu Kama da juna sak nagani Wanda bazasu wuce shekara 3ba suka nufo su Aymanah da gudu!

Miqewa nayi a jikin yaah Hydar Ina fad'in:

"Jinan, jannah maifaru"

Dariya sukai sukace "mommy anty maa tace yau zasuzo tareda su l2l ayni"

Dariya nayi na kalla yaah Hydar dake faman kallona Dan zamannan da mukai cemun yake yanada buqatata😂Niko naqi nace Masa su jinan sunanan
"halfme kallan fa?" 😆

D'an murgud'amun Baki yayi yace:

" Habubba Notting kurum kallan matana nakeyi"
.dariya nayi nakamo hannun 'ya'yana abin alfaharina wa'inda dagasu ban sake samun haihuwa ba kasancewan mahaifata data sama matsala Danko haihuwar ma sai operation akamun nagaza haihuwa dakaina tun matsalan zubar mun da cikin da mubash yamun!

'ya'yana duk Mata Jinan da jannah kyawawa masu Kama da Abbansu!


Kamosu nayi na rungumesu na kwanto a jikin mijina nace:

"Halfme haqiqa Ina godia ga Allah daya bani Kai a matsayin mijina uban 'ya'yana I love u with all my heart"

Sunbatar goshina yayi sannan yace:

" I love u more than love itself my Darling wife I love u and I will forever do Babu macen dazanso aduniyanan sama dake Allah barminke uwar 'ya'yana"


Tohm ameen romiyo ND julliet 😂"


Fad'in Marwa dake shugowa da 'ya'yanta su uku l2l ayni Jawad da inayah"

Miqewa en biyu sukai a guje suka rungumi juna suda en uwansu Niko dalloma Marwa harara nayi nace "sannu uwar uku Saidai ki Kira 'ya'yanki kisanar masu saki zo Amman bakisan da gayamunba😏"

" AAA hajia Mrs Hydar maida wuqar chaa nake wayanki nasoma Kira Kan nakira line line Amman kunanan Kuna zuba love Taya ma zakiji ringing din waya"🙄

Ta ida maganar tana ballomun harara yaah Hydar ne yace"iyye uwar uku matar tawa kike harara?"

Dariya mukai duk mu ukun Marwa taciro wayarta ta shiga camera tazo daidai inda muke tsaye nida yaah Hydar tace:

"Oyaa my babies kuzo kushiga muyi 🤳 selfie"

Nan su jinan suka rugo suka haye jikinmu muna dariya Marwa ta d'aukemu selfie 🤳🏽 Kuma cewa Tai!.

Yaah Hydar ka kalli Aymanah dariya yayi had'i da kallona itako Marwa ganin munyi kyau ta ce ma yaran oyaaa chiiiiiiiis Nan dukamun mukace"cheeees🤳🏽!


Tammata bilhamdulillah anan na kawo qarshen littafin Nan nawa *AURAN wahala Koh saki* kura Kuran dake ciki Ina Roqan Allah ya yafemun Ina Kuma fatan na isar da abinda nakeson isarwa a wannan littafin Allah sa muyi anfani dashi!


Godia ta musamman gareku makaranta littafin Nan da wa'inda suke bibiyata da wa'inda suka tsaya harsai na kammala sukaranta godia Mai tarin yawa Allah hadamun a aljannah nagode sosai godia tamusamman gareki *anty maimunaaah* ked'in ta musamman ce nagode da kulawarki gareni!


😂saikuma inkun sake jina a saban littafina 😂Amman saina huta sosaifaaa !

Ma'assalam!

*Ayshkhair 07061276995*

*The end*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment