Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kukan zuci kurum takeyi kasan uwa da 'ya sai Allah tadannene kurum Dan tasamu ta lallashi Marmy da marwa anty zubaida ce tayi qarfin halin fad'in:


"Wlh tallahi nayi rantsuwa da sarkin dayake riqe da Raina aduk ranar da mubash ya shugo hannunmu ko mintu 2 bazai qaraba sai kotu taraba auren qanwata da Mubash sai yasan wlh ya tab'a y'ar gata sai yayi danasanin shiga rayuwar Aymanah wlh da hannuna sai nazama silan tab'arb'arewa mubash da duk kafatanin mutane masu kalan halinsa!


Karku manta anty zubaida lawyer ce maizaman kanta!

Anty ameena ta d'ago ta kalla anty zubaida Wanda tun sanda tasoma magana kowa a d'akin ke kallanta yaah Hydar ne kurum tunda aka shugo falan yake tsugunne da kansa Dan shi kad'ai yasan halin da yake shiga ciki muddin yatuno da halin da Aymanah ke ciki!


Anty ameenan tace:

"Zubaida karki damu in Sha Allah Allah ma da kansa zai fanshema Aymanah haqqinta Kuma aikin asiri baya tasiri nasan duk inda Aymanah take asirin da akamata ya karye in Sha Allah zata dawo garemu very soon!


Ya Salim yace;

"Hakane maman uku mudai mucigaba da aduaa in Sha Allah Aymanah will be with us very soon Kuma wajibine mubash ya rabu da ita Kota halin yayane!

Wani kalan kasalallan numfashi yapendo Azma ta saukar tausayin Aymanah ne fal ranta kaf cikin'ya'yan qaninta tabbas tasan Aymanah ce mafi soyuwaa azuqatan kowa Dan yarinya ce Mai shiga Rai sosai gata da sanyin zuciya Aymanah duk inda ake naiman cikakkiyar 'ya Mai tarbiya inkasama Aymanah ka godema Allah murmushin yaqe yapendo Azma tayi sannan tace:

"Aduaa zamucigaba dayi in Sha allahu zata bayyana garemu very soon! Sai kuma Marwa inaso tadawo Abuja da Zama Kuma zan sa a dawo Dake base na Abuja Dan zuwanki kano bare bari Kina maida hankali ba! Allah bayyana Mana Aymanah!


A tare kowa ya amsa afalan da ameen ya Allah!


Nan kowa ya soma Shirin tafiya su anty zuby ne da ameenah da salima kurum zasu Bari gbe su koma, Marwa kuwa yapendo say masu aikinta da suka taho tare tayi suka kwashe kayan Marwan Nan wajajen qarfe 3 suka wuce airport jirginsu ya d'aga zuwa abuja.


Runtsa idanuna nayi Dan duk zatona a wuyana mubash yasaka wannan wuqan Jin shuru Kuma sai saukan mumfashinsa ke sauka a fuskana ya sani bud'e idanuna a hankali na saukesa akan fuskansa tsaki yaja sannan ya sauko Ashe kwanceni yayi daga bishiyar wata kalan hamdala nayi danjina nayi wasai Kai d'aure Abu Mai raima bala'ine!


D'aki ya wuce Niko nayi tsaye Ina tunanin mafita da zan d'aukanma kaina!


Shurun da yajine ban shugo d'akinba ya sashi kwalamun Kira;

"Keee ko tsayuwan ne har yanzun Bai ishekiba ?!"

Baigaama Ida maganar bama na dire a cikin d'akin wani kalan kallo ya bini da shi sannan ya miqe ya damqoni wunchulani yayi akan gado daga Nan ya soma romancing d'ina nidai kuka kurum na fashemai dashi araina sai bankomai Allah ya Isa nakeyi banyi aune ba naji ya zarce Yana biyama kansa buqata danko Ni ba Sam bana shaawan mubash Sam ya ficemun arai ji nayi yau tamkar itace ranar farko Dana miqa kaina ga mubash d'in wata azaba ce ke ratsa ilahirin kafatanin jikina ihu da cizo nashiga Mai harda yaqushi yanzun Kam Allah ya Isa kwando kwando naruqa Mai Kuma da qarfi nasan Sarai Yana ji Amman mugun ko saurarona bayayi!

Zan iya cewa a ranar fyad'e mubash yamun ba shi ya barni ba har sai da aka Kira assalatu Kai mubash tantirin mugune bayida imani Kona secn d'aya azuciyan sa nayi kuka harna gode Allah a haka yamiqe ya barni Ina disgar kuka da kyar na miqe Dan tsarkaka jikina!


*****************


Marwa Kam suna Isa Abuja straight d'akinmu ta nufa Dan dama d'aki guda muke dashi a gidan nida Marwa inmunzo hutu ko kayanmu bama zuwa dashi Dan munada wasu anan jitayi yau d'akin duk yamata wayam memories d'in abubuwan damukeyi lokacin inmunzo taruqa tunawa hawaye sai zirya yakeyi a kumatunta a daidai Nan Kuma taqarasa wajen bedside drower ta d'auka wani frame d'in hoto damukayi mu biyu munsa Kaya iri d'aya hannunta riqe da wani plastic frame da Mubash ya aikomin lokacin nikuma inaso na kwata aka dauke mu hoto murmushi ne ya sub'uce Mata hawaye na Mata zirya a kumatu rungume hoton tayi tazauna a gefen gadon ta fashe da kuka tana Kiran sunana a hankali!



Abinda mubash ya tsira dashi kenan yanzun kullum saiya kusanceni inyagama ya tsallakeni wani zubin Kuma yaruqamun habaici Wai ban iya gamsar da mutum ba Babu abinda na iya naji tsoron ranar da zai karyani agidanan Niko azuciyana nace ai gwara Kar na iya gamsar fa fasiqi maqiyin Annabi Mai fuska biyu!


Yau na tashi duk jikina ciwo wani kalan zazzabi ne ya rufeni amai nakeyi tartilan hakan da Mubash yaganine yasashi d'aukata yakaini asibity zance munyi tafiyan kimanin awa biyu kafun muka fito acikin jejin damuke ciki hawayene kurum ke zirya a fuskana yau qaddaran rayuwa nice takawo cikin wannan jejen Kai Allah kabani saan cinye wannan jarabawar tawa Allah kakuma sanyamun imani azuciyana!


Koda muka Isa asibityn gwajin farko aka tabbatar Mana da Ina d'auke da juna biyu na wata biyu da sati uku Kennan Inada ciki tun muna Nigeria? Shine tambayar Dana ma kaina wani kalan baqin cikine ya ziyarceni yau nice da cikin fasiqi mazinaci nice zan Haifa d'ana ko 'yata da uba fasiqi shin in yarana sun girma sun tadda d'abi'ar mahaifinsu shin zasu yafemun zab'in uban Dana masu kuwa? Shin zasu yarda da ba a San
Raina na aura ubansu ba? Dawani idanun 'ya'yana zasu kalleni duniya ta nunasu tace masu ubansu mazinaci ne fasiqi? Innalillahi wa'inna ilahirajiun ya Allah Kaine sarkin da Babu kamarka Kaine ubangijin aljanu da mutane dabbobi ya Allah Kaine zaka iya bama Abu umarni ya aikata Nan take ya Allah nasan kasan dalilin tsaramun rayuwata a haka nasan baka iya jarabtar bawa da abinda bazai iya d'auka ba Allah na roqeka kabani ikon iya cin wannan jarabawar tawa Allah na roqeka!

Kallona kurum likitan keyi da kyar yace "madam lafiya kike ta kuka ?ko bakiji abinda nace maki kina d'auke dashi bane?"

D'agoda raunannun idanuna nayi na kallesa sannan na cije bakina nace:

"Dr naji abinda kace saidai wannan abinda kace d'in amaimakon yakawo farinciki a fuskana da zuciyana sai akasin hakan tafaru wannan cikin dakace Ina d'auke dashi Babu abinda yasan yamun face baqin ciki da qunar zuciya Kuma da danasani zuciyana da ruhina amaimakon Suma cikin danake d'auke dashi tarba da amanna sai akasamu akasin hakan Babu abinda zuciyana da ruhina suka tsana sama da wannan cikin saidai ba cikin na tsana ba abinda zan gayama abinda kecikin cikin nake kyama!๐Ÿ˜ญ


Shuru likita yamun Yana kallona kurum danshi nama Gama kwancemai notikan kansa yagaza sanin inda maganata tadosa a hankali yace:

"Baiwar Allah keko kinsan abinda kike fad'i kuwa?

Wani kalan murmushin kuka nayi nace:

"Likita nasani nasan abinda nake fad'a Sarai!"

" Hmmm toh kinsan abinda kike fad'i shine kike gayan maganganu irin haka?$hin cikin dake jikinki bana sunnah bane ?shin bakida aurene?


"Inada aure kuma cikin sunnah nake d'auke dashi hasalima uban cikin ka aika ya qarbo magungunan da ka rubuta!


Likita zaiyi magana Kennan mubash ya turo Kai Dan haka saiyayi shuru Amman kana ganin fuskansa zaka hango fal tambayoyi qarasowa mubash yayi ya zauna yace likita na amso magun gunan Amman Mai test d'in yanuna ke damunta?


Waigowa nayi na kellesa na wanchakalamai mugun kallo sannan naji likita naacewa:

"Well sakamako ya nuna tana d'auke da juna biyu na wata biyu da sati uku"

Mubash ji yayi maganar kaman saukar aradu!

" wat?!

Ya miqe tsaye Yana wani had'a Rai kaikace Allah Bai tab'a saukar da annuri a fuskansaba jinayi Yana cewa:

"No wannan bazai tab'a sab'uba it can't be ban shirya haihuwa ba infact I hate children natsana yara na tsanesu!

Bansan sadda na bankomai harara ba cikin ko inkula nace:

"Bakason Yara shine Kai aka haifeka?!and kaima yadda ka tsana cikin dake jikina hakannan Nima natsana cikin saidai Ni ba d'an natsana ba uban d'an natsana...Kuma Ina Allah wadai dazan had'a zuriya da fasiqi mazi..............


Wani bahagon Marin da yawankeni da shine ya hanani qarasa maganata had'i da had'iyar sauran maganar tsaban maruwan danayi har wani kalan stars nake kallo da sauri nadafa fuskana na fashe da kukan tausayi!


Shiko Dr mutuwan zaune yayi kansa yakuma qullewa Kai wannan mutane akwai lauje cikin nad'i a rayuwansu maganar da mubash yayi ne da Kuma abinda yafurta ya mugun razanani ya Kuma razana likitan har rige rigen miqewa mukayi nida likitan a tare muka furta:

"What..........!




๐Ÿ˜Ÿkaiko mubash Mai ka fad'i haka da ya razana Aymanah da likita? ๐Ÿค”!

Amsan Yana next page in Sha Allah โ˜บ
[6/25, 09:18] Other Line 9ja: ยฎeal pure moment of life writers



๐Ÿ˜ญ AURAN WAHALA KOH SAKI?!๐Ÿ“๐Ÿ˜ญ๐Ÿ™†๐Ÿผ



By Ayshkhairโœจ

Page 37&38

Harara ya banko mana duk mu biyun nida likita sannan yace cikin muryan fad'a;

"Kaman yadda kunnuwanku suka jiyo maku"

Hawayene Shar ke sauka a fuskana Kai wannan wani kalan rayuwa ce wani kalan masifa da bala'i ne ya kunnuma rayuwata?Mai na aikata nake fuskantan rayuwa irin haka?Kai ya Allah badan niba badan halina ba ya Raheem ka kalleni da idon rahma ka waiwayoni ya Allah ka kawomin d'auki; maganan da likita yayi ne ya d'an maidoni duniyar tunanin da na fad'a:

"Kana Koda hankali malam?shin kasan Mai bakinka ke furtawa kuwa? abortion fa kace tareda cire Mata wobm?mahaifatar fa?shin Anya malam kanada karatun addini kuwa?infact kasan hukuncin duk Wanda yayi kisan Kai a addini ko?in ka kashe mutum kaima kasheka zaayi tohm malam inbakason haihuwan Nan maikaika Auran baiwar Allahn da bataji Bata ganiba? Wlh ya.........

Mtseeeeeww

Tsakin da Mubash yayine ya katse likitan ya maida idanu kurum Yana kallon mubash in :

"Likita infa bazaka zubarda cikin nan ba kurum ka gayamun naga dai bakaine kurum likita a nahiyan Nan ba! "

" Bazan cireba Kuma in Sha Allah cire cikin Nan da zakayi a cikin matarka shine silar daqular kowani farin ciki a rayuwar ka zaka rasa farin ciki har illa ma Sha Allah in Sha Allah karubuta ka ajiye Ni Dr fahim nace ma haka"

Daga Nan likitan baijira Mai mubash in zai ce ba ya d'au wani file a hannunsa ya fice a office d'in ranshi a matuqar jagule:

Tsaki mubash ya ruqa yi a jere nikam na Riga da na ma sadakar kwalkwalwana da ruhina sun Gaza tunanin komai Kuma sun Gaza aikata komai hakan ne yasa nadawo mutum mutumi kurum!

Da qarfin gaske ya fisgo hannuna har Ina bigewa da tebur in office in Jana kurum yakeyi kaman raqumi da akala har zuwa mota inda ya wuntsilar Dani bayan mota ya rufe ya shugo ya tada motar ya barbad'e asibityn da qura mutane sai kallon mamaki kurum suke binmu da shi!


******************

Yau satin Marwa daya a abuja chif ba laifi tad'an rage damuwa sabida skul data Fara zuwa gashi Yapendo na yawan d'auke Mata kewa. Yauma kaman kullum bayan ta dawo lectures tana zaune a falan Yapendo tana Kallan wani series a televista saidai a zahiri zaka aza Kallan take Amman a bad'ini zuciyanta fal tunanin Aymanah ne Allah kad'ai yasan inda mugun Nan yaakai Aymanah gashi tasan Aymanah da shegen tsanyin ran bala'i tasan duk inda muke mubash na Nan na quntatamun!

"Marwa! Marwa!!"

Firgit Marwan ta waiwayo tana kallan Mai Kiran nata quri da Ido Yapendo tamata sannan ta numfasa ta zagayo ta zauna kusa da marwa had'i da kamo hannunta tace:

"Marwaty tunani ba naki bane aduaa shi ya kamace Yar uwarki pls kirage wannan tunanin Dan Allah karkisama kanki wani cutar pls! So kike in Aymanah ta dawo ta taddaki kin fad'a cikin wani Hali hunnn?!

Da sauri Marwa ta girgiza Kai a lokaci guda Kuma tana furta "aa" da sauri

"Yauwa good girl so inbakison hakan ya faru kidaina sama kanki tunani kinji marwaty?"

Gyad'a Kai tayi alamar ta gamsu bazata sake ba murmushi Yapendo tamata sannan tace:

"Kinga yau Hydar zai dawo pls jeki sashenshi ki gyaramai kinji Bai son masu aiki na gyaramai gashi nikuma zan fita zuwa asibity!

Murmushi Marwa tayi sannan tace:

"Tohm yapendon mu Bari naje Amman ai bazaki dad'e ba Zaki dawo ko? "

" Yes my dear check up zani kurum kafun azahar zan dawo babana ma yace after zhur jirginsu zai sauko"

Murmushi Marwa tayi sannan tace:

" Allah maidosu lfy"

Diga Nan ta miqe ta nufi part d'in Hydar!

Zata iya cewa yau shine karonta na 3 tunda take zuwa gidan yapendo ta shiga sashen Hydar d'in Dan bakoda YauShe yake gidaba sai ya jera watanni ma baizo ba sabida yanayin aikin shi Dan haka sashen qullum a kulle yake saidai a shiga a gyara a rufe Kuma ko ya nanan ma ba kasafai yake Bari ana shugo Masa ba sabida wani dalili nashi.Girgiza Kai kurum Marwa tayi tana Mai tunanin irin rayuwar da zatayi da wannan murd'ad'an yayan nasu insunyi aure! Itadai har ga Allah Aymanah Tama yaah Hydar kwad'ayin aure sabida tsaban da cewan da sukayi dalili kuwa shine Aymanah tanada matuqar sanyin Rai kuma tana da sauqin Kai irintane kurum zasu iya Zama a inuwa d'aya da masu kalan Hali irin na yaah Hydar hot tempers marasa fara'a Sam! Amman ya satayi qaddara ta riga fata sai dai adu'a kurum Dan itakam batajin zata iya jure zaman aure da yaah Hydar duk da tasani shid'in ba qaramin namiji bane every girls dream husband Amman wani zubin zuciyan mutum ya kamata ka ruqa lura ba Wai halittaba na fuska Kona jiki!

Shugowa falan da tayine yasata tsagaita tunaninta Kallan falan kurum takeyi tana furta "wow" a k'asan maqoshinta lallai falan Nan ya had'u sai take ganima tamkar duk gidan sashen yaah Hydar yafi kyau hoton sa dake manne a saqo da lungunan falan ta ruqa kallo har ta idasa shiga d'akinsa nanma ya had'u sosai gyara tasoma dukda d'akin bawani qura tayi ba bayan ta Gama tashiga bayi ta wanke ta feshe ko Ina da turaruka masu d'adi tana gamawa tafito da niyyan fita Amman hango wani d'aki a wajen corridor da zai sadaka da dining area ne ya sata d'an tsayawa kaman ta wuce sai Kuma tayi tunanin shiga ta gyara Shima straight taje da niyyan bud'a d'akin Sai dai taji shi a datse har tasoma tafiya sai ta hango key a saqale a wajen kofan hakan yasata d'auka had'i da bud'e qofan qamshin turaren da ya bigi hancinta a lokaci guda ne yasata saurin juyowa Dan tabbatar da abinda hancinta suka jiyo Mata!
Ganin bakowa ne a bayan nata yasata d'an mamaki tana Kuma furta qamshin turaren Aymanah" qarasa shugowa d'akin tayi sai dai d'akin da duhu yake hakan nema ya d'an tsoratata gashi kuma qamshin turaren Aymanah sai dad'a yawaita yakeyi a cikin d'akin Kai kace tamkar tana kusa dakaine tana fesa turaren Dan tabbas wannan qamshin turaren datake shaqa tabbas tasan bamai irin qamshin sai Aymanah to Mai qamshin ta keyi a d'akin Nan! A hankali tasoma Kiran sunana waiko Ina d'akin ne๐Ÿ˜†!

Jin shuru yasata soma laluban inda zata kunna wuta da kyar ta samu saidai tana kunnawa wani blue haske ne yasoma bayyana a hankali Kuma kunna wani tayi nanma orange light ne ke fitowa a hankali Nan ta cigaba da kunna wutan har kala biyar a hankali d'akin ya baibaye da haske saidai hasken na bayyana wani hotuna ke moving a saitin bangon d'akin d'ago kai Marwa tayi tasoma qarema hotunan dake haskowa A d'akin da kallo a hankali take kallo bayan taga hotunan sun qarene yasata Kuma waiwayowa tana qarema maka makan frames d'in dake d'akin kallo hotunane kurum take gani wasu daka gani kasan mutum ne ya zauna ya qera hotunan da dukkanin basiran da Allah ya Bashi Saida ta Gama Kallan hotunan tsaf sannan tayi wani kalan kayataccen murmushi tana furta " wow ma Sha Allah yaah Hydar Kennan in ka gansa tamkar bazai aikata hakaba tamkar baisan Mai ake nufi da kalman LOVE ba! "๐Ÿ˜ผ๐Ÿ˜น

Wani d'an littafi ta hango saman wani table dake cike da hotuna irin pices d'inan duk birjik a saman table in kujeran table in ta jany'o ta zauna ta na Kallan hotunan tana yalwataccen murmushi sannan takai hannunta ta kunna wani lanta da shi ne zaka iya karanta littafin dake kan table in kasan tuwan yanayin wutan d'akin yake in mix colours bayan ta kunna ta bud'e littafin ta Karan ta heading din "my PA diary life" shine rubuce akan littafin kaman karta karanta Amman abinda tagani a next page in yasata Zama ta karanta littafin Nan tsaf daga farko har sai da in da taga ya ajiye pen d'insa alaman Yana cigaba da rubutawa ne mamaki ne fal ran Marwa ita mamakin da takeyi shine dama Wai yaaah Hydar ya iya. Soyayya haka tohm itakam tunda AllH ya halicceta ko a film da Novel Bata tab'a cin Karo da zazzafayen kalamomin soyayya masu sanya natsuwa da shauqi ga Wanda aka furtasu mawa ba kaman Wanda taga yaah hydar ta zauna ya tsaraba murmushi kurum takeyi tana fad'in ayyah Yaaah Hydar Kai d'in u are slow poinsion green snake under green grass!

Jin kaman idar da sallan azahar d'in da akayine yasata saurin miqewa ta rufo d'akin tafito da sauri ta rufe sashin takoma part din yapendo ranta fal farin ciki da Kuma mamaki!

****************


Rayuwan qunci da uquba Babu irin wa'inda bana Sha wajen mubash kullum Yana kan bakansa akan Kota halin mainene sai ya zubar mun da ciki sannan Kuma sai yasa an juyamun mahaifata nadai qala ban cemai saidai binsa da Ido kurum Dan abin NASA ya girmama tunanina kawai abinda nasama Raina yanzun shine nasan Allah nasane Dani Kuma shi ya tsaramun hakan a rayuwata Kuma nasan shi zai magancemun Dan haka kullum cikin aduaa kurum nake Allah daurani Akan mubash!

Ana haka watarana mubash ya dawo yaban wani juice yace na kwankwad'e ba musu na amsa na shanye dan Sam bana Masa musu ko tijara yanzun komai yace nayi kafun ya Gama magana ma zan Fara aikatawa Dan mu rabu lfy Dan jikina Kar ya gayamun ga laulayin ciki ga duka Dan ba qaramin aikinsa bane yamun d'an Karan duka ko agefen kwalansa!


Bayan Shan wannan juice d'in dakimanin mintuna uku naji cikina na murdawa tamkar ana yaqin biyafra aciki tun Ina jurewa Ina botsarewa har hakan ta faskara ihu da salati da jerama Allah kirari kurum nasoma yi Jin ihu na yasashi fitowa daga toilet da sauri ya kamoni yana mun sannu Yana fad'in:
Daure ko? Daure yanzun Nan cikin zai fita ki rage Jin azaba !.

Ina nikam banma San yanayiba tsabaragen azaban danake Sha kalmatul shahada nasoma karantowa Dan jin yadda nayi a lokaci d'aya cikin nawa ya birkicemun jinake tamkar Raina ake cirewa jini ne yasoma liliyowa ta qasana ahankali chan Kuma sai ya b'arke tamkar panpo Kallan mubash kurum nayi ya daka tsallan murna yana furta "yes! Yes! Wlh shegen ya zube yes!

Sannu ko sorry "innalillahi wa'inna ilahirajiun kurum naketa furtawa a hankali idanuna sai kakkafewa sukeyi yanzun mubash zubdamun da cikin Nan yayi? Koda bana qaunar ubansa Ina qaunar d'ana Dan bansan iya Kwan da Allah ya rubutamun zan kyank'e she ba adoran qasa shisa ma tunsanda mubash yace zai zubda cikin na shiga xullumi d'ana Dana samu a sanadin aure yau shine ake cema shege yafita! Kai Allah gani gareka!

A hankali nake ta furta kalmn shahada idanuna na rufewa a hankali har suka rufe gaba d'aya bakina ma a hankali yasoma daina furta komai a hankali bakin nawa Shima ya daina motsawa nakoma na sulale a qasa shiko mubash Bina kurum da idanu yakeyi Yana furta:

"No ai an tabbatarmun bazaki mutu ba cikin ne kurum zai fita oya kitashi"

Shuru ban amsa Mai ba hakan yasashi jijjigani Amman Aymanah batada alaman motsi hakan yasashi saurin wawurarta yasata a mota yayi hanyar asibity da ita suna shiga likitoci suka amsheta akayi emergency room da be!*Real pure momment of life writers*


๐Ÿ˜ญ *AURAN WAHALA KOH SAKI*๐Ÿ™†๐Ÿ“๐Ÿ˜ญ


By " *AYSHKHAIR*"


Page 39&40


Likitocin sukai kimanin awa 1 akan Aymanah!

Likitane ya fito dan yay magana da Mubash dan Aymanah na buqatan jini saboda jinin datayi loosing dayawa! Koda likitan ya fito sai bai iske Mubash ba gashi any momment frm now inhar baasamu ansamata qarin jinin ba zata iya rasa ranta!

Da sauri wata nurse tafito daga d'akin tana kwala sunan likita kallanta yayi da sauri yace: "what!"

Cikin haki nurse in kecewa:

"Dr she needs oxgyn"

Da sauri likitan ya shiga d'akin yadda ya tarar numfashin Aymanah nasama taqasa tamkar ana cire mata rai yayi mugun firgita likitocin d'akin kallan machine din dake nuna heart beaten nata sukayi sukaga yana 0.3 tabbas yana kai 0.0 zata rasa ranta da sauri likitocin suka d'au oxgyn na mannawa a qirji dan saurin ceto ranta shikuma dr saad yayi saurin zuwa lab yaduba blood group din Aymanah da sauri yaje ya d'au leda biyu na jini ya zo ya maqala mata a duka hanna yenta biyu da kyar numfashinta yasoma tafiya in 0.7 alaman jinin yasoma shiga jikinta wani sanyayyan ajiyan zuciya likitocin suka sauke suna fur Thank God! Saida suka tabbatar komai na tafiya normal sannan suka fito Dr saad ya wuce office nashi ya zauna sai faman tunanin wani kalan maganine Aymanah tasha na abortion haka da har yake shirin salwantar da rayuwanta!

Ganin bamai bashi amsa ya sa shi cigaba da aikinsa ransa fal tunanin mubash inda yaje yabar Aymana acikin wannan halin!



Kwanan Aymanah d'aya a asibityn amman ko Alamar giftawar mubash babu a asibityn hakan ne yasa Dr saad tunanin qilan kawota kurum yayi dan ya taimaka mata or somtn lyk that!

Shugowan Dr Saad d'akin da shi da wata nurse yayi daidai da qarar machine din dake nuna gudun zuciyan aymanah yasoma bugawa a hankali a hankali da sauri likitan ya qaraso yana tab'a wasu wajen yana kuma mai kallan Aymanah dake sauke ajiyan zuciya da sauri da sauri qarasowa yayi daf da ita ya cire mata Oxygn d'in dake saqale a dogon hancinta dan tasamu tayi fast breath hannuntane yasoma motsi alaman tana farfad'owa sosai kallan jinin da aka qaramata yayi yaga ya qare wurwus kuma wannan jinin shine leda 5 kenan daaka qaramata!

A hankali Aymanah tasoma bud'e idanunta har ta waresu tsaf akan likita saad kallansa takeyi quri da idanu batako kyaftawa dan so take ta tuna mai ke faruwa a hankali komai ya soma dawomata sabo runtse idanunta tayi a hankali tana fad'in:

"Dan allah ku rabani da shi ....zai kashe ni da yarona......

Saida likita saad yakai kunnansa daidai la66anta sannan yajiyo abinda take fad'i hakan ya sashi mamakin kalamanta a hankali ya qarba alluran baccin dake hannun nurse sannan ya ma Aymanan dan tasamu ta yi bacci aiko yana mata bada jimawa ba ta soma bacci!

Kallanta likita saad yayi duk tausayin yarinyan yabi ya isheshi kallanta yakeyi kamar qanwarsa data rasu wajajen haihuwa runtsa idanunsa yayi sannan yace ma nurse din amaidani d'akin hutu nurse tace masa okey sir! Daga nan ya wuce office nashi dan duba wasu patience d'in!



Sai wajajen qarfe 4pm sannan na farfad'o ina qarema d'akin kallo bisa alama a asibity nake hakan ya tabbatar mun da maganin da Mubash yabani na zubda cikine shafa cikina nayi a hankali na furta:

"Kayi haquri d'ana Allah jiqanka kuma Allah zai saka maka in sha Allah gwara da Allah ya qaddara rashin zuwanka doron duniya hakan ba qaramin gata mahaliccinka ya maka ba sabida karka taso ka tarar da baqin azalumin mahaifinka! Allah zai saka mana!"

Diga haka kuka yasoma cin qarfina a hankali na shiga rairo kukan ina kiran sunan mamanmu da marmy da yayyena a haka likita saad ya shugo ya taddani da saurin sa ya qaraso yana fad'in;

"Subhanallahi baiwar Allah kukan fa namainene?keda zaki godema Allah ya barki da rayuwarki shine kuma kike kuka!

Kallan likitan nayi da kana ganinsa zakaga zallan kamanninsa da 'yan burki nafaso!

A hankali nace;

"Likita da mutuwan nayi dana fijin dad'i samada idan inada rai kuma igiyan aurena yanaga mugun miji!

Da mamaki likitan ya kalleni yace:

"Baiwar Allah keko maisaki furta wanga kalamai?"

Murmushin da yafi kuka ciwo nayi sannan nace:

" Wlh da mutuwa nayi nakoma ga mahaliccina dana fi kowa farin ciki a doran duniyan nan!

Kallona kurum likita yasoma yi yana mamakin wannan kalaman nawa chan ya nisa yace mun:

"Baiwar Allah niko kazaki iya gayamun maike damunki haka? Dakika zab'a kimutu sama da ki rayu?!"

Murmushi nayi dan ni kam bana shakkar gayama ko waye labarin quncin Auran danayi ! Murmusawa nakuma yi sannan nace:

"Lbarina yana da tsawo amman labarin yasoma kaman

Please Login or Register in order to submit comment