Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da cewa.
"Hamma Haiydar ni bana jin bacci."

Matseta ya kuma yi a jikin shi kamar maiyin rad'a yace.
"Lumshe idon ki,
ki rink'a fidda numfashin ki a hankali kisa kanki cikin k'irjin na,. sabida karki ga haske kiyi haka yanzu baccin zai zo kinji ko."

Bata kulashi ba,
shi kuwa bai kuma mata magana ba sai lumshe idon da yayi tare da jawo blanket ya rufe su.

Shiru kawai tayi tana mai shak'ar k'amshin turaren jikinshi,
cikin shak'ar k'amshin ne ta fara jin kasala jikin ta na sakewa a hankali ta lumshe idon lokaci d'aya bacci safe mai dad'in nan ya kwasheta,
shi kuwa yana jin tayi shiru a jikin shi yasa ya bud'e ido yana kallon ta fuskar ta ya tsurawa ido tare da tsanan ta buga war zuciyar shi,
a lokacin daya tuno yaran da ya had'u dasu a dai-dai k'ofar shiga part d'in Alhaji Ibrahim,
shiru yayi tare da karewa fuskar Meenalin kallo,
cikin sauri ya kuma rumtse idonshi yana tuno kamannin fuskar Rayhana,
a fili yace.
"Wannan wanne irin kama ne ?."
Tsaki yaja tare da cewa.
"Kamar tayi yawa duk da ana cewa ko wanne d'an adam yana da masu kamannin sa har 7,
gaskiya duk da haka kamar tayi yawa."

Yatsarsa yasa yana shafa gashin girarta cikin mamaki ko yanayin gashin girarsu iri d'aya hatta d'an bakin su iri d'aya,
shiru yayi tuno sautin muryar Rayhana tabbas sautin muryar ta sak irin sautin muryar da bazai mantaba duk da tsawon shekaru da yayi baiji muryar a zahiri ba tabbas sautin muryar ta irin ta Ammi ce tunda a koda yaushe yana mafarkin Ammin shi kuma yana jin muryar ta.

Ido ya kuma rumtsewa tuno fuskar Ramadan sai kuma yasa tafin hannushi yana shafa fuskar shi yana mai mamaki a sanyaye ya lumshe ido tare da sauk'e ajiyan zuciya a haka cikin tunanin bacci mai dad'i ya d'ebeshi suna ruggume da juna cikin shak'ar k'amshin juna...


Ita kuwa Mama da gari ya waye bayan sun gama lalalatan su ita da bokan ta ya had'a mata tuggun da take buk'a ya kuma shaida mata aiki ya kammalu daga yau Aliyu ya zamo Aliya bashi ba mace sai dai gani da ido zai zama dashi da logoni basu da babbanci ,
cikin rud'u shaidan da bacewar imani da mancewa Allah na nan ta yarda da maganar bokan nata ta kamo hanyar ta cikin happy ta dawo gida ita da Abdul suka rink'a had'a zalumci yayin da Nafeesat da ya Amir suke binsu da Addu'a da fatan shirya..


Rayuwa ta juya komai ya fara canzawa yayin da kwanaki sunja har ya koma makonni sun ja ,
Ramadan da Rayhana kuwa suna ta k'ok'arin had'uwa da d'an uwansu so sai dai basa son kowa ya sani kuma su a Kansu sun k'asa gano ina yake,
ganin bazai Ganeba gashi wata d'aya zasuyi su koma hakan yasa Ramadan ya yanke shawaran dole su nemi Captain Sani Wanda suke kira Hamma Sani sunyi shawara dashi a kan haka suka yanke shawaran k'iran shi yazo gida sunyi maganar ...


Shi kuwa General Aliyu a hankali rayuwa ta juya mai inda zuwa yanzu ya fara fahimtar akwai abin dake bibiyarsa zuwa yanzu kullum dare Aliyu kwana yake cikin azabben zazzab'i da sanyi da ciwon ciki da kasala mai tarin yawa da tsinke war zuciya da zaran anyi sallan insha wannan yanayin yake zuwa mishi shine bazai samu sa'idaba sai iskar asuba ta fara kad'a daga nan kuma kafin gari ya waye sai ya nemi ciwon ya rasa kab jikin sa sai yayi garau sai dai kuma dole sai yayita yin baccin rana haka yasa gaba d'aya yanzu bai fiye kwana a Jaji ba kuma yamma nayi zai dawo gida haka zasu kwana da Meenarl d'inshi cikin wahala shi baida lafiya ita kuwa tsoron yadda yake wahala da ruggume ta da yakeyi tsam yana rawan jiki shike hanata bacci a hankali ta fara jin tausayi yinshi na ratsata ta yadda take kwana mishi sannu da zubda k'ollah.....

Yau jumma tun da yamma General ya dawo gida a parlour ya zauna jiki a mace dan yaune ya gano wata matsalar dake jikin shi hakan ya sashi cikin rud'ani,
yana kwancen Meenarl ta shigo parlour kai tsaye gaban shi taje ta zauna kan carpet ido suka tsurawa juna cikin kula da tausayi tace.
"Hamma Haiydar yaushe ka dawo?."

Shiru yayi tare da kallon yadda take ma shi maga cikin tausayi yawa da kulawa,
abinda bai tab'a samuba,
ba wanda yasan halin da yake rayuwa a cikin in dare yayi sai ita shiyasa gaba d'aya yanzu tausayawa kanshi yake.

K'ara matsoshi tayi cikin sanyin murya tace.
"Hamma baka da lafiya ko?."

Ido kawai ya tsura mata,
ita kuwa ido tab da k'ollah tasa hannu kan wuyan shi cikin rawan murya tace.
"Hamma yamma tayi ko? har zazzab'i ya fara zuwa?."
Shiru baiyi magana ba sai kanshi yasa ya matse hannun ta a kan wuyan nashi .

Ita kuwa cikin zubda k'ollah tace.
"Hamma Aliyu kamin magana mana."

Ido ya tsura mata cikin tsuke fuska yace.
"Ina kika je? bana hanani fita ba?."

Kai ta lok'k'osa cikin sanyi tace.
"Kayi hak'uri Hamma naje gun Anty Aysha ne."

Shiru yayi sannan ya mik'e ya zauna tare da zaro hankicif d'inshi ya mik'a mata yace.
"Share hawaye ki ni lafiya ta lau,
bari ma inje masallaci,
ki tafasa min tea kafin in dawo."

Toh tace tare da binshi da ido har ya fice sannan itama ta shiga bedroom din nasu tayi sallan..


9:23 pm General ne zaune kan carpet d'in dake gaban gadon nasu sai rawan sanyi yake tare da damk'e cikin shi yana mai jujjuya kai,
ita kuwa durk'ushi take a gabanshi tana zubda k'ollah cikin rawan murya tana.
"Isa Hamma Haiydar sannu ."

Kai ya gyad'a mata cikin dauriya yace .
"Meenarl jeki rufe k'ofar parlour ki kashe wutan da fanka kizo ki konta."

"Toh" tace tare da mik'ewa taje ta rufe k'ofar tare da kashe komai sannan ta shigo ta sameshi ya had'a kanshi da jikin gadon gaba d'aya jikin shi sai rawa yake,
da sauri taje kusa dashi cikin tausayawa tace.
"Hamma Haiydar ni kam bari inje in gayawa Abba inya so sai mu tafi asibiti."

Kai ya juya mata cikin furzar da numfashin yace.
"A a Meenarl barshi kinga yayi bacci kar mu tayarmai da hankali kinga yana da hawan jini."

Hannu tasa ta share hawayen ta tare da jawo blanket zata rufe mishi jiki ganin yadda yake karkarwa,
hannun ta ya rik'e cikin cije lips enshi yace.
"Bari Meenarl ai yau da sauk'i ki hau kan gadon ki kwanta nima yanzu zan hau in kwonta."

Baki ta bud'e a hankali tace.
" toh tashi ka hau."

Murmushi k'arfin hali yayi tare da yunk'ura zai mik'e rik'e da hanna yenta dai-dai lokacin da sunkuyo d'in wani irin.....



*Kuyi hak'uri da wannan sisters ina kuma k'ara Baku hak'uri rashin ganin nolen d'inna da zakuyi gobe zuwa jibi hakan zaifarune sakamakon zanyi tafiya Adamawa Yola 2 Gombe ina Neman Addu'arku fatan Allah ya kaini lafiya ya maidoni lafiya*



By
*Garkuwar Fulani*
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 3⃣1⃣ to3⃣2⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Wannan shafi sadaukar wane gareki k'anwata ta gari har kullum kina raina Ummee Garkuwa 😍😘*



Pml
yace.
"Ammi kin san abin da muka gani kuwa jiya da hantsi?."

Murmushi tayi cikin kula tare da maida hankalin ta kan d'an nata gudan jinin ta mai sata farin cikin mai share mata k'ollah a duk sanda suka koranyo a fuskar ta mai cike da tunani da bagen wani abun da ta rasa.

Kai ta jinjina tare da cewa.
"Me kuka gani Ramadan har ya rud'aku haka?."

Ido ya tsura mata tare da yana yin mamaki yace.
"Ammi jiya ba munje gidan uncle Ibrahim duba jikin shiba?."

kai ta gyad'a mishi tare da cewa.
"Ehh."

Matsota ya kuma yi tare da rik'o hannun ta cikin shak'uwa da mahaifiyar tasu yace.
"Ammi jiya a gidan uncle ni da Rayhana mun had'u da wani Soja a dai-dai k'ofar shiga part d'in uncle Ammi kin ga yadda Sojan nan yake kuwa?."

Ido ta tsura mashi tare da girgiza kai cikin son jin k'arshen maganar.

Cikin muryar mamaki yace.
"Ammi dana ganshi zuciya ta tayi ta bugawa tsikar jikina gaba d'aya ya rink'a tashi idona sai rawa suke a kan kaman nin fuskar sa hankali na kuwa ya tashi Ammi."

Rik'o hannunshi tayi cikin tsoro kar d'an nata yayi gamo ne tace.
"Ramadan me ka gani a fuskar sa? shi mutun ne ko aljan?."

Kai ya jinjina tare da sauk'e ajiyar zuciya a hankali yace.
"Ammi ina da tabbacin mutun ne shi,
Ammi kamannin fuskar Sojan nan ya bani mamaki da tsoro,
Ammi komai fa na fuskarsa da halittarsa irin nawa ne,
Ammi hatta farin mu irin d'aya ni dashi Ammi hatta k'wayar ida nunshi irin nawa ne,
Ammi hatta sajen dake fuskar sa irin nawa ne ,
Ammi wallahi ko yatsun hannushi irin nawa ne,
Ammi kamata da wancan Sojan yayi yawa har takai kamar da nakeyi dashi wallahi ko Rayhana da muke tagwaye bamuyi irin wannan kamar ba,
Ammi tsawo kawai da d'an k'iba ya fini alamun ya d'an girma ni a haife,
Ammi wallahi kwana nayi ina mafarkin shi yana kuka yana k'iran sunan ki yadda muke kiran ki Ammi shima haka yayi ta k'iran cikin mafar kina,
Ammi shi kad'ai na gani a mafarkin yana rayuwar kad'aici ba wanda ke kusa dashi dake nuna mai k'auna ko kulawa sai wata budurwa ita kuma tayi nesa dashi sai wani haske da yake tsaka ninsu sai kuma na haggo wani duhu a hannun wata mata tana turawa cikin hasken daga gefen shi kuma Hamma Jabeer ne yana jan hannun wannan budurwa."

Sai hawaye cur-cur a fuskar sa murya na rawa ya kifa kanshi jikin gadon ,
wanda Rayhana ke konce tana jin duk abinda suke fad'a tuni itama sai kuka take yi sun had'a kai wuri d'aya suna kuka a hankalin.

Ita kuwa Ammi bugawar zuciyar tane ta tsananta,
lokaci d'aya hankalin ta da tunanin ta suka koma kan d'anta Aliyu Haiydar wanda ta rebu dashi tun yana d'an shekara bud'u,
a badiri kullum Ammi Aliyu na cikin ranta dashi take kwana dashi take tashi tana son d'anta tana son ta kasance dashi ta bashi kulawa da tarbiya wacce ko wanne d'an yake samu gun mahaifiyarsa,
amman ina haka bata samuba dan fushin da iyayen ta sukayi.


a lokacin da Abban Aliyu ya saketa,
ya kuma karb'e d'anshi haka yasa Babban yayan ta mahaifin Captain Sani da Dr Jabeer ya d'auke ta daga garin Kaduna ya koma da ita Adamawa Yola inda yake aikin sa cikin gidan shi ya ware mata part nata ita da mahaifiyarsu,
ya rink'a kula dasu da duk wani dawaini yarsu,
Karin konciyar hankali linsu matar sa Hajia Asma'u mahaifiyar su Dr Jabeer da Captain wacce suke kiranta Nenne ,
macece mai mutunci da sanin ya kamata ta d'auki dangin mijinta kamar denggin ta ,
ta taimakawa mijinta wurin kula da y'ar uwarshi da mahaifiyarsu du-du yaran Nenne 2 ne Dr Jabeer sai Captain Sani ,
amman ganin d'an uwanshi bai tab'a haihuba wato (Alhaji Ibrahim mai dala),
sai ya d'auki d'anshi na biyu Captain Sani kenan ya bawa k'anin shi,
daga nanne Captain Sani ya koma Kaduna da zama.

Ita kuwa Ammi bayan fitan ta gidan Abba da wata d'aya ciki ya bayyana inda take laulayi kamar zata rasa ranta,
cikin kulawa d'an uwanta Barrister Lawan mai dala ya kaita Asibiti gojin forko aka gano tana d'auke da cikin wata 3 a jikin ta,
Ammi tayi farin ciki dan ita a zaton ta ko dan albarka cikin yayunta da mijinta zasu gyara auren ta koma kan d'an ta gudan jininta,
haka kuwa sukayi Alhaji Ibrahim yaje ya samu Abba da batun cikin,
amman da yake a wancan lokacin asirin da Mama tayi ya kama shi yana aiki a kanshi shiyasa,
fir Abba yak'i yace shi wannan cikin ba nashi bane can suje su nemi uban cikin dake jikin ta,
shi ba ruwan shi ,
wannan kalma ta cewa ciki ba nashiba yasa Barrister Lawa fushi mai tsanani Wanda daga nan ya yanke duk wata alak'a da zata had'a Ammi da gidan Abba hatta kadunan Barrister ya hana Ammi zuwa kota-kota,
Ammi kam da tajin maganar tayi kuka kamar ranta zai fita sana din wannan abin ta samu hawan jin,
inda mahaifi yarta da Jabeer suka zama abokan zaman ta Jabeer yana son Ammi a ranshi fiye da zaton d'an adam Jabeer jin Ammi yake tamkar ita ta haifeshi domin komai a part nasu yake yi Ammi kemai duk abinda Uwa keyiwa d'anta Ammi ce abokiyar shawaran sa itama shine abokin shawaranta tasha zama ta bashi labarin Haiydar shima Jabeer sai yayi ta kuka yana son d'an uwan shi kuma shine kad'ai yasan yadda Ammi ke shiga damuwar rashin d'an nata, yayin da Kaka ke basu kulawa gaba d'ayan su,
bayan watanni 6 Ammi ta haifi yan tagwayen ta inda Ramadan ya fito mai kama da Aliyu sak da sak ,
ita kuwa y'a macen sun rasa dawa take kama ba abin da ta dauko na kowa a zuriyarsu sai muryar tace kad'ai irin ta Ammi da zaran ta bud'u baki tayi magana toh sautin muryar Ammi sak.

Haka yara suka tashi cikin gata da kulawa da tattalinsu da ake a cewar Alhaji Ibrahim su yaran basuma ishesu ba bare a wulak'an ta musu y'ar uwa a banza su zasu rik'esu har iya rai da mutuwa,
ita kuwa Ammi tun daga nan bata kuma yin aure ba aceqarta zata kula da yaranta,
Dr Jabeer da Ramadan da Rayhana sun tashi gida d'aya d'aki d'aya gaban Ammi ta musu tarbiya mai kyau sun tashi cikin k'aunar juna da shak'uwa.

Alhaji Ibrahim kuwa duk sanda zaije Taraba Gembu Duba yarshi Amina yakan biya cikin Yola ya d'auki d'an yayan nashi wato Jabeer suke tare,
toh shi Jabeer daga nan yasan Meenal haka kuwa yasa kullum k'arshen sati sai ya shirya yaje Yola to Membila yaje ya duba k'anwar shi Ammi ma da su Ramadan da Barrister da Nenne tare da Kaka duk suna zuwa su kaiwa Meenal ziyara,
a haka shak'uwa mai tarin yawa ta shiga tsaka ninsu ,
shiko Captain Sani kasan cewarsa a makaran tar sojoji yake da yanayin karatu shi da aikin shi yasa bai tab'a zuwa canba ko sau d'aya,
Sannan Abba kuwa yana sakin Ammi Mama ta kuma mishi asirin da dole zaman Kaduna yafi k'arfin shi saida ya k'aura ya koma Katsina yana Katsina ya karisa ginin gidan da suke ciki a yanzu suka k'aura suka koma can yayin da Aliyu ya tare a part d'in Abba shi yana rayuwa shi d'aya a haka ya girma komai na karatu Abban na mishi,
toh sana din k'auran nasu yasa Alhaji Ibrahim bai kuma ganin Aliyu ba bare da ya girma Alhaji Ibrahim bazai gane shi ba kuma shi Alhaji bai tab'a zuwa gidan su Aliyun ba dan in yaje kam zai had'u da Daddy toh dole zai gane Aliyu .....


Toh yanzu sanadin B'atan Meenal yasa Alhaji Ibrahim ciwon zuciya da hawan jini,
shine fa Barrister Lawan ya shirya da iyalanshi kab da Kaka mahaifiyar su da Ammi dasu Rayhana da Nenne duk suka zo Kadunan duba Alhaji Ibrahim d'in da jikin yayin da suka sauk'a a gidan Barrister Lawan d'in dake nan cikin kaduna,
toh su Ramadan sun zo sun gaida Uncle Ibrahim d'inne sun fito zasu koma suka had'u da General...


*Mu koma kan labarin*

ajiyar zuciya Ammi ta sauk'e tare da zubar k'ollah tana mai kama hannun Ramadan da Rayhana da
Ramadan kuka kawai suke yi cikin kukan Ramadan yace.
"Ammi nasan fa akwai abinda kuke b'oye mana nida Rayhana Ammi na fara zargin mahaifimu na raye,
Ammi wannan sojan d'an uwanmu ne duk yadda akayi mun had'a jini dashi."

Cikin kuka sosai Ammi ta basu labarin abin da ya faru shekaru 26 da suka wuce ta kuma d'ora da cewa.
"Ramadan ina ji a jikina Sojan nan d'an uwanku ne yayan ku Haiydar ne shine yayanku Uwa d'aya uba d'aya,
Amman ko kunce zakuje yan uwana zasu ha naku dan sun rik'e mahaifin ku a ransu."

Hannu Ramadan yasa ya rik'o nata cikin share k'ollan fuskarsa yace.
"Ammi mu dai Abba mahaifin mune bamu da wani uba daya fishi kuma mu ya watsar da mugun furucin ,
mu kuwa nida Rayhana mun yafewa mahaifin mu muna kuma son uban mu zamu kuma nemoshi muna son d'an uwanmu zamu je gareshi zamu raba shi da zaman kad'aici zamu sashi happy a rayuwar sa dan haka karki gayawa su Uncle komai akan zamu nemi Abban mu,
bamuga laifin su Uncle ba dan dole suji zafin abin da akayi miki a matsayi su na yayunki."

Kai Ammi ta jinjina cikin zubda k'ollah tace .
"Rayhana kinji abinda Ramadan yace kuma kema kina bayan shi?."

Kai Rayhana ta jinjina cikin kuka sosai tace.
"Ammi inason Abba na in ason in ganshi ina son Hamma Haiydar naji tausayin Hamma Haiydar ya rayuwa tamkar maraya alhalin iyayenshi na raye,
haba ashe shiyasa fuskar Hamma Haiydar ba fara'a baida sakewa ashe cikin kuncin rashin Uwa da uba yake rayuwa ba d'an Uwa ba y'ar Uwa a kusa dashi ina son d'an uwana Ammi."

Cikin kuka Ammi ta dafa Kansu tare da cewa.
" Allah ya muku albarka rabbi ya kaddara saduwar ku da mahaifin Ku na amince kuje gareshi."

Murmushi Ramadan yayi tare da mik'awa Rayhana hannu,
ta d'ora nata hannun kan nashi,
cikin yana yin jinjina ni yarsu,
itama Ammi murmushi tayi a ranta koba komai farin cikin ta zai dawowa gareta d'anta abin al'fahari ta Aliyu Haiydar..


Shi kuwa Aliyu yana shiga bedroom d'in lokacin daya bi bayan Meenal jikin durowa ya tsare ta cikin had'e fuska yace.
"Ke me kike ta min kallon munafurci kina wani zaro ido kamar mayya."

Shiru tayi cikin kallon shi a tsorace tana mai girgiza mishi kai tare da cewa.
"Mayyahh."

Fuska ya kuma tsukewa tare dasa hannu kan....

By
*Garkuwar Fulani*
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 3⃣4⃣ to3⃣5⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



*Dedicated 2 Amina Aminu ( Meenah parrot)*


Yaji wani irin azababben ciwon ciki,
gaba d'aya jikin shi ya rink'a b'ari kar-kar dole ya zame tare da damk'e mararshi,
ita ma Meenarl komawa tayi ta zauna tare da jingina da jikin gado cikin rawar murya da tausayawa ido na zubda k'ollah ta rink'a cemai.
"Sannu Hamma Haiydar Allah ya baka lafiya ehsa Hamma am."

Shi kam Aliyu zamewa yayi ya konta kan cinyoyin ta tare da tura kanshi cikin fatar cikin ta sannan yasa hannu duka biyu ya zagoyo k'ugunta tare da rumtse ido sai karkarwar da yakeyi gaba d'aya ya dunk'ule a jikin ta,
ita ma cikin tausayawan ta ruggumo shi da kyau tare dasa hannun ta tana shafa wuyan shi zuwa kafad'an shi tana kuka tana mishi sannu,
hannun ta na rawa ta tura hannun kan marar tasa cikin mamaki da tsoron ta zaro ido tare da cewa.
"Hamma Haiydar ji mararka kamar wuta ga tauri kamar dutsen."

Shi kam kanshi kawai yake turawa cikin jikin ta kamar yaro k'arami a cinyar mahaifi yarshi,
hannu tasa kan marar tashi ta d'aura a hankali sannan tasa yatsunta ta rink'a murza marar tashi a hankali tare da sunku yowa tana karan ta addu'oin tana mishi tofi a kai tare da murza marar tana danna wurin tare da murza wurin da taji yayi tauri da zafin.

Shi kuwa General
K'ara K'ak'k'ame ta yayi tare da murza kanshi cikin jikin ta yana wani irin numshi da k'arfi sai mutstsu kata yake yi tare da yin magana cikin wahalcecciyar murya.
"Lahaulawala k'utah illabillahi aliyul azim wayyo Allah na wayyo jikina cikina Meenarl marata zata b'alle."

Sai kuma ya k'ara tura kanshi cikin jikin ta yana mai murza kan nashi,
murza kan nashi yake cikin wahala har saida ya b'alle boturan rigar jikin ta ya zamana gaba d'aya cikin ta da k'irjin ta suna woje haka ya rink'a tura kanshi yana murza kanshin a tsakiyar k'irjinta tare da k'wak'wume ta.

Ita kuwa murza marar tashi take tana mishi tofi tare da rugume shi,
a haka ya fara lafawa sai numshi yake sauk'ewa a hankali yana sauk'e ajiyan zuciya,
ido ya rink'a lumshewa yana d'an bud'ewa a hankali ya mirgina tare da gyara konciyar shi kan k'irjin ta.

Ita kuwa jikin gadon ta koma ta jingina tare da gyara konciyar shi a jikin ta sannan ta jawo blanket ta rufesu,
shi kam shiru yayi tare da lumshe idon shi a hankali bacci ya fara d'ibarshi,
ita kuwa ido ta tsura mai fuskarsa take kallo ganin yadda yayi wani irin kwarjini sai zufa dake tsatstsa fo mishi,
a haka ita bacci ya saceta.


4:27 Am , General ya d'an gyara konciyar shi dan a lokacin ne ya fara jin kuzari cikin baccin yake jin duk ciwon na tafiya juyawan da yayine ya tasheshi daga baccin cikin d'an sauran kasalan ya bud'e idanun shi,
shiru yayi yana mamaki ganin inda yake konce lumshe idon ya kumayi tare da sauk'e ajiyar zuciya fuska ya d'an dago tare da tsurawa tata fuskar ido bacci take cikin takurewa a jikin gadon sannan tasa hannu ta ruggume shi sannan hannun ta d'aya kuma ta tura kan mararshi ,
ido ya rumtse da k'arfi ganin kanshi na tsakiyar k'irjin ta ,
bud'e idon yayi tare da sake diresu kan k'irjin ta ,
shiru yayi ya zama tamkar soko ko wani gaulah so yake ya d'auke ida nunshi daga kan abin da yake ganin kuma ya kasa idon yake son lumshewa amman sai idanun sukayi mishi nauyi ba abinda yake ganin sai k'irjin nata,
tsikar jikin shi ne ya rink'a tashi tare da fuzgar numfashi hannun shi ya jawo da k'yer a nufin shi ya jawo rigarta da ta bud'u ta zame kad'an zai rufe k'irjin nata ,
amman yana d'ago hannun sai kasalar jikin shi ta rinja yeshi cikin kasalan ya dire hannun nashi kan k'irjin nata,
shiru yayi cikin tsinke war jinin jikin shi ya kara ruggume ta sannan ya murza hannushi kan abinda ke tafiya da tunanin shin ido ya tsurawa k'irjin yana kallon irin halittar da Allah yayi mata kanshi ya kuma murzawa cikin kasala ya rink'a murza kan nashi a tsakiyar k'irjin ta d'in yana gogar abin da ke sashi kuzari a haka ya fara jin kuzari shi na dawowa har ya samu ya mik'e zaune ido ya tsura mata ganin tana ta baccin ta sai kanta da take ta d'an juyawa .

Yana tashi zaune ya motsota cikin kauda kai yasa hannun ya jawo rigar tata yana manna mata botur d'in,
yana zuwa na saman jin inda yasa hannunshi ya juyo da sauri ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yasa hannun ya shafa k'irjin nata sannan ya manne botur d'in mik'ewa yayi ya tallabota sannan ya nufi kan gado da ita,
ita kuwa yana d'ago tan tasa hannu ta sank'alo wuyan shi tare da manna kanta a k'irjin shi.

Haurawa yayi kan gadon ya kontar da ita tare da gyara mata konci yar tata,
zai tashi zaune yaji ta sank'alo wuyan nashi haka tasa dole ya maida kanshi kan k'irjin ta,
ita kuwa sai kara shigewa jikinshi take tana tura mai k'irjin ta gaba d'aya ta birki tashi ya gaza gane wanne hali yake ciki ya k'asa babbance shi lafiyeyyene ko ma jinyaci ne yana dai jin wani irin yanayin kam a tare dashi,
yadda ta rik'e shin yasa ya maida kanshi kan k'irjin nata sannan yasa hannun yana mata wani irin salon shafa waishi a tunanin shi bacci yake son sata ita kuwa jin yadda yake shafa ta kamar a mafarki kuma tana jin yana sata cikin wani yanayin hakan yasa ta rink'a mik'a mai cike da kasala tana turo mishi k'irjin ta tare da nad'ewa a jikin shi ,
shi kam zuwa yanzu ya gaza gane a duniyar da yake yadai tsinci kanshi da murza yarinyar yana shafata da tsotse inda yake tsone mashi ido,
sarrafata yakeyi sosai sai nishi yakeyi yana jawota jikin shi kanshi ya tura kan k'irjin ta sannan ya manna bakinshi kan farin ganin shi cikin salon cikar zatin haibar ya rink'a mata wani irin abun da yasa ta cikin baccin ta rink'a kamo kanshi tana.
"Shihhhhh hahhhhh huhhhhm."

Shima tuni ya fara sauya salon fitar numfashi ,
ita kam sai shafa kanshi take yi jin yasa hannun kan cibiyarta yana mata tafiyar tsutsa yasa ta bud'e ido cikin sauri tare da janye jikin ta baki na rawa tace.
"Hamma Aliyu lokacin sallah yayi fa."
Shiko shiru yayi tare da yin rufda ciki k'irjin shi kuma na kan nata ya k'asa janye hannushi kan k'irjin nata sai wani irin kunya da yake ji shin me zaice mata kuma me yake mata haushin kanshi ya faraji yana jinta

Please Login or Register in order to submit comment