Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kuka dafe da kanta,
matso ta yayi cikin sanyi yace.
"Meenal meke faruwa?."
Kai ta d'ago cikin zunda k'ollah tace.
"Hamma Haiydar."
Sai kuma tayi shiru
cikin k'arin macewar jiki ya kalleta dan duk duniya mutum biyu ke ki ranshi da Haiydar Abban shi sai Ammin shi da ta guje shi sai yanzu kuma da yaji Meenal na ki ranshi da sunan.

Murya a sanyaye yace.
"Meenal me kike so? meke damun ki?."

Cikin kuka tace .
"Kai na Hamma Haiydar kaina zai fashe."

Ido ya tsurawa goshin nata tare kama lips d'inshi na k'asa yana tsotsa .

Jin taci gaba da kukan yasa ya d'an sunkuyo kanta hannushi na hagu yasa ya tallabe k'eyarta sannan ya d'aura tafin hannun shi na dama kan goshin nata ya danne tare da fara murza wurin,
cikin azaba da gigita ta rik'o hannayen shi tare da sakin kuka mai cin rai tanayi tana janye hannayen shi,
shi kuwa k'ara dirza wurin daya kumburan yakeyi dan ya samu ya bace,
cikin sakin k'ara da k'arfi ta sank'alo wuyanshi tare da komawa baya zata k'wace kanta ,
aiko cikin rashin kuzari ta fizgo General sai gashi ya fad'o kant........





By
*Garkuwar Fulani*
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 2⃣5⃣to2⃣6⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Tabbas wannan babu shakka (MOH ALLAH WUJI FURD'ATA, MOH ALLAH HOKKI B'URI MOH BABA HOKKI)*






Pml
Kanta cikin wani irin sanyin jiki da jini ya mirgina gefe tare da konciya rigin gine kanshi na kallon saman d'akin yayin da k'afafun shi kuwa ke reto a kasan gadon hannu shi d'aya kuma yana kan cikin ta,
so yake ya d'auke hannushi daga kanta amman ya kasa kuzarin shi duk ya tafi dan dama tun sanyin safiyar yake jin kasala ba abin da ke aiki a jikin shi sai zuciyar sa dake harbawa idon shi ya lumshe cikin sauke ajiyan zuciya daga nan ya kasa ko motsi mai k'arfi ,
a cikin ranshi kuwa sam bawai jin dad'in wannan yana yin yakeba gaba d'aya ya resa me kemai dad'i.

Ita kuwa Meenal shiru tayi tare dasa hannu ta rufe kan goshin nata zuwa kan idon ta sai hawaye dake bin fuskar ta sam ita bata san hannushi na kanta ba dan zafin da kanta ke mata shiyafi komai a gareta hawayen take zubdawa tare da fara sheshahekan kukan.

A hankali ya fara jin sautin kukan ta mai sanyi wanda sai in mutum ya kasa kunne zaiji,
shiru yayi tare da murza yatsatsa ma nunuyiya da babbar yatsarsa a hankali ya fara jin kuzari idonun shi yake son bud'ewa amman sunyi mishi nauyi dole ya k'ara lumshe idon cikin sauk'e ajiyar zuciya sannan ya tattaro sauran kuza rinshi ya mirgino ya juyo ya konta gefe d'aya yayin da fuskar sa ke fuskantar ta,
cikin k'arfin hali ya bud'e idon a hankali sannan ya tsura mata idon yana kallon ta,
ganin kukan take tayi,
cikin sanyi yasa hannun shi ya jawo nata ta mirgino ta fuskan toshi suna kallon juna har hancin General na tab'a goshin ta ,
cikin sanyi ya bud'i baki tare da cewa.
"Meehnarl."
Ido ta bud'e tare da tsurawa bakin shi ido,
shi kuwa gashin giran ta yake kallo jin bata amsaba yaci gaba da cewa.
"Meenarl kiyi hak'uri ki daure kinji ko murza miki wurin zanyi in kin daure na murza shi sau d'aya dai zai b'ace gacan magungunan ki nasha dana shafa insha Allah zai bari kinji ko?."

Rau-rau tayi da ido cikin zubda k'ollah ta tura baki tare da cewa.
"Hamma Haiydar zafi nake jifa"

Numfashin ya sauk'e tare da cewa.
"zan miki a hankali kinji ko."

Idon ta d'an d'ago ta kalleshi cikin tsoro da d'an zare ido tace.
"A hankali sosai fa?."
lumshe idon yayi tare da d'aga mata gira d'aya.

kai ta juya tare da tsuke bakin ta tace.
"A a ni ka amsa min da baki."

Yunk'uri yayi ya zauna tsakiyar gadon tare da nad'e k'afafun shi yana fuskar tarta yasa hannu ya kamo hannun ta d'aya ya jawo ta zaune itama ta nad'e nata k'afan ya zama suna fuskantar juna kusa da kusa cikin muryar da tafi kama da mai yin rad'a yace.
"Ehh a hankali zan miki,
Amman kar na fara ki fara kuka ko ki tureni kisa nima na fad'i na fasa kaina."

Cikin d'an tsoron dai tace toh .
"Da hannu d'aya zakayi kar tare min kaina da d'aya hannun."

Fuskar ta ya d'an kala a fizge sannan yace .
"Toh matso."

Matso shi tayi har guiwar ta tana gogan nashi sai kuma tana yarfa hannu alamun tsoro.

Shi kuwa mamaki yake irin wannan raki da tsoro ga shegen mita duk ita d'aya,
hannushi ya d'ago zai kai kan goshin nata ,
ita kuwa sai kawai ta sa hannu ta kamo hannun nashi yasunta tasa cikin tafin hannushi ta matse tana.
"Wayyo zafi wallahi tsoro nake ji."

Shi kam General Aliyu shiru yayi tare da tsurawa hanna yensu dake had'e wurin d'aya ido ko k'eftawa ya kasa sai kallon ta yake yadda ta dage tana murza mai tafin hannushi,
ganin yayi shiru yana kallon hannun ta yasa tayi k'asa da kanta cikin sanyi ta zare yatsunta daga nashi hannun,
sai ta d'an d'ago kan ta tura mishi tare da cewa.
"Ayyah Hamma Haiydar a hankali fa."
Gira d'aya ya sake d'aga mata sannan ya d'ago hannushi ya manna kan goshin nata ,
ido ta lumshe tare da yarfa hannu tana.
"Shiishhhh wayyohhh."

Cikin sanyi da sanyin tafin hannun nashi ya fara goga k'ulun goshin nata,
ita kuwa tuni sai hawaye da shan yaji take sai shishita takeyi ,
jin yana murzawa da d'an k'arfi sai kawai tasa hannayenta ta rarumo cinyoyin shi ta rink'a damk'ewa da yamutsa shi tamkar mai yi mishi tausa,
Sai ta matse cinyar sa tace.
"Hahhhhhhyi shihhhhh wahhyi Hamma Haiydar zafi."
Shi kuwa sai sauk'e ajiyar zuciya yake yana ce mata.
"Oh sorry Minali kiyi hak'uri daure kinji ko? saura kad'an."

Kuka ta kara saki jin k'ara murza wurin yake sai ta fara fizge kanta tana yin baya,
shiko ganin haka yasa shi d'ago hannushi ya tallabe k'eyanta dan ya murza wurin da kyau,
ita kuwa jin haka yasa ta k'ara matse cinyoyin shi cikin zafi da kuka tana .
"Wayyo Hamma Haiydar zafi."

Bai kula taba sai murza wurin yake,
Cikin zafin tayi yunk'uri ta afka kanshi cikin k'irjin shi tasa kanta sannan tasa hannu ta zagaye k'ugunshi ta k'amshin k'am jikin ta sai kuma ta saki kuka .

Shiko General wani irin numfashin ya furzar tare da rumtse idonshi sannan ya gyara zaman shi tare da sa hannushi a kan bayan ta yana shafawa a hankali cikin yanayin lallashi tare da cewa.
"Gud gerl sannu ko Meenarl kinyi k'ok'arin sannu kiyi shiru ya isa bazan k'ara murza wurin ba ya b'ace kinji ko."

Ita kam shiru kawai tayi tana jin kan goshin ta yana zut-zut lafewa tayi a jikin shi,
shi kuwa shiru yayi ba tare da tuna komai ba.

A haka har zuwa d'an wani lokacin sannan ya janye jikin shi tare da tureta gefe ya mik'e ya nufi parlour ba tare daya juyo ya kalleta ba.
ita kuwa madubin jikin kan gadon ta juya tana kallon fuskar ta,
murmushi tayi cikin goge k'ollan fuskarta taji dadi kumburin ya b'ace.


Shi kuwa yana fitawo parlour da niyar zai kira Captain Sani yazo ya ai keshi ya samowa wanna yarinyar abin da zata ci,
yana fitowa parlour ya samu kulolin abinci da filas wanda Anty Aysha ta
kawo,
kan kujera ya koma ya zauna cikin tsuke fuska da d'an d'aga murya yace.
"Meenarl ."
shiru bata amsaba,

"Meenal" ya kuma kira a karo na biyu.

Tana jinshi ta mik'e da sauri ta fito parlour,
cikin sanyi tazo gaban shi ta d'an zauna gefe,
fuska ya kuma tsukewa sannan yace.
"Zauna kici abinci."
Shiru tayi tare da sunkuyar da kai ,
A d'an fusace ya tura mata kulolin sannan yace.
"Kici nace ko."

Ganin yadda ya murtuk'e fuska yasa ta jawo filas d'in cikin sanyi ta zuba d'an ruwan tea a cup sannan tasa a baki tana d'an sha a hankali,
har tashanye sannan ta ajiye cup d'in tana kallon idon shi,
shiko ledan maganin ta ya jawo sannan ya b'alli d'aya ya mik'a mata,
ba musu ta karb'a tare da tsiyayo tea d'in ta had'iye maganin a haka yayi ta bata da k'waya d'ad'd'aya tana had'iye maganin da tea ,
shi kuwa mamaki yake yadda take shan tea kamar ruwa duk da dai na yanzu kam shan dolene.

Mik'ewa yayi rik'e da wani d'an farin roba gabanta yazo tsuguna sannan ya bud'e robar ya lakato maganin ya rink'a shafa mata a goshin nata,
yana gamawa ya mik'e tare da cewa .
"Zo ki konta kiyi bacci."

Baki ta d'an tura sannan tace.
"Toh"

Haka kamar dole ta konta ,
shi kuwa wonka yaje yayi sannan ya fito parlour ya kimtsa ya fito tsab cikin bedroom d'in ya koma gaban mirror ya tsaya tare da fesa turare,
har ya juya zai fita sai kuma ya dawo bakin gadon cikin tsurawa fuskar ta ido,
baccinta take cikin takurewa wurin d'aya kamar maijin sanyi,
kai kawai ya girgiza sannan ya jawo blanket ya rufeta,
ya juya ya fita.

Parlour Mama ya nufa cikin tsuke fuska sallama yayi tare da tsayuwa bakin k'ofar,
cikin tsana ziryan a idon Mama ta kalli ya Amir da ya amsawa sallaman General d'in ,
shi kuwa Abdul rumtse idonshi yayi cikin jin tsanar d'an uwan nashi wanda a halin yanzu baida burin daya wuce daukar fansa .

Shi kuwa a tsaye ya mik'awa ya Amir hannu suka gaisa sannan ya kalli Mama fuska a d'an yamutse yace.
"Ya Abdul da jiki."

"Ban saniba mugun d'an gidan mugaye wallahi a jutyi zuwa rafi dai tabbas wata ran tulu zai fashe wallahi tabbas akwai ranar nadama."

Baki ya tab'e sannan ya juya ya fita.

Yana fita ya Amir ya mik'e yabi bayan shi suka fitoh tare suna fita ya kira Captain Sani akan zasu biya gidan Alhaji Ibrahim su karb'i pictures d'in yarshi da aka sace d'in su rik'e dan pictures d'in zasu tai maka daga nan kuma zasu wuce Jaji.

Suna shiga gidan Alhaji Ibrahim Captain Sani yana gaba General yana binshi a baya,
a dai-dai bakin k'ofar General yaci karo da.....

*Kuyi hakurin da wannan sisters*

By
*Garkuwar Fulani*
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page 2⃣7⃣to2⃣8⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



*YELAN BANDIRAWO MA KHAIRUJI NUMIN BANDIRAWO MA KHAIRUJI WANNU BANDIRAWO MA DO'A KHAIRUJI, TOH ALLAH JAB'I A LARAI KHAIRUJI D'ER HABARUJI KHAIRU HAMAD'A BE BANDIRAWO MAD'A TO EN NUMI ENFU EN BANDIRAB'E*



Pml
Da wani dan saurayi wanda bazai wuce sa'an Abdul ba cikin wani irin yanayi yaron ya zubawa General ido tare da mamaki cike a ranshi,
shima General d'in kallon yaron ya d'an yi cikin mamakin wannan abu sosai yake mamaki bin yaro yayi da ido jin yadda yaron ke magana.
"Ayyah sannu ban lura da kaiba ne."
Ido ya runtse cikin son tantance kalan muryan yaron wanda gaba d'aya ya tsaya mai cikin rai,
ganin shiru su duk ba wanda ya kuma magana sai budurwar dake bayan d'an saurayin tayi magana cikin kallon General.
"Kayi hak'uri bandirawo."
sai ta kuma kallin Saurayin wanda ke bin General da ido kawai tace,
"Ramadan mu tafi kaga lokaci na tafiya fa."

Saurayin da ta Kira da Ramadan ko,
sai ajiyan zuciya ya sauke tare da yin murmushi ya shafa sajenshi sannan ya nuna fuskar General ya kuma nuna tasa fuskar,
sannan ya matsa gefe tare da jan hannun budurwar nan yace.
"Zo mu tafi Husaina ta."
Janta yayi suka fita ta gefen General ita kuwa sai yarfe hannu tayi tana cewa.
"Can tafi da yawar ka wallahi ka dena kirana Husaaina inba haka nima na rink'a cema Hassan d'in ka."
murmushi yayi tare da kamo hannun ta yace.
"Na bari y'ar biyu na babyn mu mai kyau nace dake Raihanan ki ko?."

Kai ta gyad'a mai tare da cewa.
"Harda wani cemin baby ka dai san awa d'aya ka bani ko?."
dariya yayi tare da kamo kafa d'anta yace.
"Na yarda amman dai na fiki tsawo,
mu tafi kawai B'iyaye na."

Haka suka tafi suna wasa suna raha cikin k'aunar juna da yawan surutu gashi daga surutun su har mun gano cewa y'an biyu ne su,
shi kam General tamkar an kafashi a wurin ne ya kasa shiga cikin gidan sai juyawa da yayi ya hard'e hannu a k'irji ya zuba musu ido har suka je bakin motarsu nan ma suka fara rigima ita Rayhana tace ita zata jasu shiko Ramadan yace sai dai shi,
ganin Rayhanan zata bata musu lokaci ya cilla mata key,
tare da cewa.
"Naci girma karb'i mu tafi."

Shi kam General ya kasa d'auke idonshi a kansu su duka biyu ita yarin in yar inya kalleta har tsikar jikin shi yake jin yana tashi.

Suma cikin Mamaki ganin yana yin General suka tafi.

Yana tsaye a wurin har Captain Sani ya fito tare da Dr Jabeer gaisawa sukayi tare da mik'awa General fayel na bincike kan b'atan Meenal din wanda aka yishi a jihar Taraba zuwa Yola 2 Gombe,
toh yanzu an mik'e binci ken a hannu General inda zai fara kafa jamin tsaro da binci ken daga jihar Jigawa zuwa Kano har ya gaggaro nan Kaduna yayin da aka bazai yan sand'an ciki kuma tako wanne sak'o na kasar na.

Karb'a fayel din yayi tare da cewa .
"Insha Allah zata dawo gareku cikin k'oshin lafiya,
yanzu tunda da hotu nanta zamu bada a kafafen yad'a labaru sannan za'a buga jarida da neman ta tare dasa kud'i mai tsoka ga duk wanda ya kawo labarin ta ."

Murmushi Dr Jabeer yayi cikin jin k'arfin guiwar,sannan sukayi sallama da juna.

Daga nan Captain Sani da General Aliyu suka wuce cikin Jaji ,
suna isa General ya ajiye fayel d'in a kan kujera sannan yace wa Captain Sani .
"Ga wannan ni zan d'an shiga zanyi bacci yanzu wani Abdulkarim zai zo,
yana zuwa ka bashi fayel d'in amman ka zaro pic d'aya a ciki ka ajiye sauran kuma ka had'a mai su."

"Toh " ya amsa mai cikin girmamawa,
sannan shi kuma ya wuce cikin bedroom d'in ya konta,
shima Captain Sani konciyar yayi a parlour.

Shi kam General tunani ne goma da ashirin a ranshi ko ido ya rumtse fuskasu Rayhana da Ramadan yake gani kunne shi na ajiye mai sautin muryar yaran masu cike da k'aunar juna.

A d'aya sashin zuciyar sa kuwa Abdul yake tunowa tunda ya k'oneshin yaune kawai ya kuma fita ya bar Meenal a gidan ita kad'ai sai su Maman ido ya rumtse tuno hali irin na Mama zata iya yin komai akanta da d'anta dan imanin ta reggegene.

Ita kuwa Meenal tunda ya fita tana baccin ta ,
kamar a zahiri kamar a mafarkin ta rink'a ganin General d'in cikin wani irin hali da bata Ganeba kamar dai cikin wahala yake,
cikin d'an tsoro ta farka tana tashi ta fito parlour dan a tunanin ta yana nan tana fitawo parlour ta samu Abba a zaune,
a hankali ta k'arisa gefen shi ta zauna tare da gaida shi cikin kulawa ya amsa gamida cewa.
"Meenal ya jikin naki?."
kai ta d'an d'ago ta kalleshi cikin k'aunar Abban dan yana da mutunci komai zai mata cikin kula yake mata shi.
"Da sauk'i Abba yanzu kam ma banji zafin sosai."

"Masha Allah haka ake so Allah ya k'ara sauk'i ko."

"Amin ya rabbi ."
Tace dashi tare da yin murmushi,
haka Abba ya d'an yi ta janta da hira,
kuma ba laifi dama itama tana sakewa da Abban.

A d'akin Mama kuwa cikin jinjina kai ta kalli Abdul murya k'asa-k'asa tace.
"Abdul yanzu kai a burin ka me kake son ayiwa Aliyu dan d'aukar fansa.?."

Cikin cije lips enshi yace.
"Mama ni so nake a mishi shegen duka a karya Mashi hannayen da k'afafun shi ."

Ido ta kuma tsura mai tace.
" shike nan abin da kake so?."

kai ya gyad'a tare da cewa.
"Ehh."

Tsaki taja sannan ta mik'e tana safa da marwa cikin mugunta tace.
"Kai ai baka da hankali baka kuma san k'ofofin mugun taba sannan baka San cewa kowa da wurin da za abi naci nasara a kanshi,
ai Aliyu indai ta wurin duka ne har a badan da'iman ba zamu cin nasara a kanshi ba,
sannan ko munci nasara an karya shi wallahi ni ban huceba,
abin da yaso yayi maka Allah bai bashi sa'a ba ni zan masa badai akan mace yaso ya nak'asa min kai ba?."

Kai ya gyad'a cikin kallon yadda yake zama ba wondo sai jallabiya ajiyar zuciya ya sauk'e tare da yin hamdala a ranshi yana cewa.
"Mugun yaso ya maida ni mace ko mata maza amman Allah ya fishi gani garau da lafiya ta tamkar doki.

Yana cikin tunanin yaji Mama tana cewa .
" Toh ni yau d'in nan zanje gida boka mai gobe da nisa,
zan kashe kud'i ko nawa ne a maida Aliyu Mace ya tashi daga Aliyu ya koma Aliya zan Sa boka ya nak'asa mana shi ta yadda har a badan shi da Mace sai dai gani da ido ta yadda zai rayuwar da wannan yarinyar daya k'ona ka akanta sai dai ido kuma tunda sunce matar sa ce ita ba k'aruwa ba to shakka babu kai d'in,
nake so ka mai data karuwa ka zama tamkar mijin ta,
yayin da shiko Aliyu zan sa boka ya maida shi tamkar logoni ko tsuma,
shi da mace sai dai ya kalleta da ido ,
wannan Meenal din da yake gadi zata zama haramiyar sa,
wanna ne kad'ai zamuyi mu d'auki fansa ta yadda ko wanne wayewar gari Aliyu k'ara mutuwa zai keyi a tsaye,
shi zai koma mata maza
tunda a fad'an zahiri baza muci nasara ba toh na sunk'uru zamuyi mishi,
yadda na rab'a uwarsa da ubanshi haka zan rabashi da ko wacce y'a mace."

Ido Abdul ya zuba mata cikin murmushi farin ciki baki na rawa yace.
"Mama kin gama min komai wallahi."

Sai kuma ya d'anyi shiru sannan yace.

"Amman kar a hanashi Aure gaba d'aya in yaso adai rabashi da Meenal d'in kawai."

Zama tayi gefen shi cikin rashin imani tace.
"Dama ko Aliyu bayyi ma haka ba inason in hanashi aure inko ban hanashi auren ba toh zan hanashi haihuwa bare kuma yazo ya maka wannan abin."

Cikin mamaki yace.
"Toh Mama me ya miki?."

Jinjina kai tayi sannan tace .
"Na tsane shi ne,
sabida ai kasan dai gidan nan na Abban Aliyun ne ba gidan Daddyn ku bane? Toh tun kafin a haifi Aliyu naso in zubar da cikin sa yafi sau biyar ina bawa Ammin Aliyu maganin tana sha kai harda allura nasa an mata cikin dabara amman da yake wannan Aliyun taurin Kaine dashi kamar shaid'an tun yana cikin uwarsa shi gardama yake min wallahi sai cikin sa yak'i zubewa."

Cikin mamaki yace.
"Toh Mama meyasa kike son hana matar Abba haihuwa? tunda naga ita ba kishiyar ki bace?."

Tsaki taja tare da cewa.
"Kaima banza ne naga alama ka fara zama irin yayan ka Amir da k'anwar ka Nafeesat,
raguwar zuciya gareku ko toh,
abin da yasa nake tsoron kar matar Abban ta haihu sabida kar ya samu Magaji kaga in baida yaro da zaran ya mutu Daddy kune zai gajesa kaga d'en duk dukuyarshi ta zama tawa nida Ku y'ay'ana,
toh amman don jaraba da taurin kai saida wannan jarabebben d'an nasu Aliyu yazo duniya gashi ya fito d'an namiji ta yadda duk zai kwakwashe gadon,
toh shine yanzu banson Aliyu ya haihuwa tunda ko ubanshi ya mutu ya gaji dukiyar toh in baida y'ay'an dole kune zaku gajeshi daga nan dukiya ta zama tamu,
kaga dama shi Daddyn Ku ba abin da yake dashi yana nan kamar b'eran masallaci fak'aru alal larurati kawai."

Ido ya ware cikin jin hud'ubar shaid'aniyar uwarsa,
cikin zak'uwa yace. "toh Mama ya kikayi ki rab'a iyayen Hamma Aliyu?."

Murmushi tayi cikin yarda da kanta tace.
"Yanzu kan zan tafi gidan boka mai gobe da nisa dan ya fara min aiki a wannan rana sai gaba zan baka labarin yadda na rabasu a sauk'ak'e."

Ido ya zura mata tare da mik'ewa yana tafiyar yan kaciya yasa hannun ya d'an dago jallabiyar sa karta fameshi,
Ita kuwa mayafinta ta yafa sannan suka fito parlour anan ya tsaya itako ta wuce gidan bokan nata Wanda yake can cikin k'auyen Zaria kauyen ma a bayan garin.

Tana zuwa ta samu gidan a cike da mata anata bin layi gidan boka ya zama tamkar asibiti,
Itace bata samu shi gaba sai goshin maggariba tana shiga bokan ya kalleta cikin yin shu'umin dariya yace.
"Hajia zulai a gidan lallai mugunta ta motso."
Zatayi magana yayi maza yace.
"Kiyi shiru nasan meke tafe dake amman kinsan sharad'in aiki na dole yau nine matsayi mijin ki kuma kinsan abinda zamu aikata."

Kai ta jinjina tareda cewa.
"Ba dai buk'atata zata biya ba?."

Cikin zare ido yace .
"Sai dai in ban miki wonka ba."

Kai ta jinjina tare da cewa.
" na yarda"
Dariya yayi tare da cewa.
"Toh a wannan Daren zan tura aljana kasalau ta zuba mishi kasala da sanyi mai tsanani da zazzab'i ta yadda bazai iya yin nafilfilin daya saba yi da karatu k'ura'ani da azkar da yake duk sai ya kasa yi kafin mu samu nasara a kanshi."

*Wa iyazubillah ya Allah ka tsare mana imanin mu hak'ik'a wannan abu ya yawa ita a cikin matan wannan zamini*


Shi kuwa General bayan anyi sallan ishah ne ya koma kan 3str ya konta,
Captain Sani ne ya kalleshi cikin kula yace.
"Sir ya kamata mu koma cikin Kaduna ko?."
Kai ya jinjina tare da rumtse idonshi ,
can kuma sai ya mik'e tare da rarumo..

By
*Garkuwar Fulani*
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 3⃣3⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



*JOGU ALLAH BE ANNABIJO BE DEFTERE ALLAH LELDI ANNBIJO MEN BE MAI , TO ALLAH JAB'I TA JOGI D'ONI A HISAI DUNIYA BE LAHIRA*




Kan gashin ta saitin idanun nata cikin tsuke fuska yace.
"Inafa gaya maki ki daina yimin irin wannan kallon munafurcin inba haka ba sai na k'wak'wulo k'attin idanun naki masu kama dana jinnu- jinnu."

Shiru tayi cikin zubda k'ollah tare da zamewa k'asa ta tsuguna ta kifa kanta kan guiwowin ta,
ta saki kuka mai sanyin sauti.

Shiru yayi a tsaye a kanta ya kafeta da ido,
yana jin yadda take fidda sautin kukan nata,
tsaki ya ja cikin lumshe ido ya juya ya koma kan gadon jiki a mace cikin jin bacci,
dan deren jiya bai samu yayi bacci ba,
hakan yasa konciyar yayi tare da jan blanket ya rufe jikin shi,
yana kallon ta kamar wasa amman sai kukan take shi kuwa harga Allah ranshi na b'aci en yaji sautin kukan nata idon ya kuma bud'ewa tare da tsura mata su a kanta ,
kokaci d'aya kuma sai tausayin ta ya rufeshi tunda ya tabbata shine ya rebota da kowa nata shine sana din zuwan ta garin shine aka bawa amanar ta,
sannan a kanshi take kuka da zubda k'ollah,
jiki a mace ya mik'a mata hannu tare da bud'e baki a hankali yace.
"Meenarl "
shiru bata kulashi ba sai sautin kukan nata ido ya kuma lumshewa yace.
"Meenarl kina ji ina kiranki kinyi shiru bazaki amsa ba."

kai ta d'ago tare da zuba mai ido cikin zubda k'ollah,
shi kuwa hannu ya kuma mik'a mata tare da cewa.
"Taso ki taso kizo nan kinji ko?."
ya fad'a yana nuna bakin gadon cikin tsare ta da ido,
kai ta sunkuyar tare da mik'ewa a hankali ta matso bakin gadon murya na rawa tace.
"Gani."
Idon a lumshe yasa hannu ya kamo nata sannan ya jawota kan gadon ta zauna a bakin gadon,
shi kuwa ya mirgino ya juyo gareta yana kallon bayan ta jiki ba k'arfi ya k'ara matsota yana kallon fuskarta murya can k'asa yace,
"Juyo nan ki gani."
juyo wan tayi tare da kallon shi cikin tsoro tana mai murza yatsun ta,

Shi kuwa hannu yasa a kanta ya jawo d'an kwalinta
sai kuma yayi shiru yana kallon yadda gashin kanta ya zubo kan kafad'un ta,
ita kuwa cikin kalloshi kawai take cikin fidda numfashin da sauri-sauri ,
mik'a mata d'an kwalin yayi tare da cewa.
"Ki bar kukan ki share hawayen ki ."

Shiru tayi bata kulashi ba sai k'ollan dake zuba,
mik'a mata ya kuma yi tare da lumshe idon nashi dan baccin yake ji,
jin shiru bata karb'a ba yasashi mik'a hannushi tare da kamo nata cikin sanyi ya jawo ta kan pillow ya kontar da ita yana mai kallon fuskar ta,
ita kuwa sai janye jikin ta takeyi tana k'ok'arin tashi,
fuska ya tab'e tare da cewa .
"Kinitsu fa."
kukan ta kuma saki tare da cewa.
"Ni zan fita parlour zanje gun Abba."

Tsaki ya ja tare da jawo ta jikinshi ya sata cikin k'irjin shi ya matseta da hannu d'aya murya can k'asa yace.
"Bacci zamuyi dan jiya kema bakiyi bacci sosai ba."

Baki ta tsuke tare

Please Login or Register in order to submit comment