Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shaidawa mutanen gidan nasu Aliyu ya dawo,
Sani na gama parking ya fito su Garba ma duk suka firfito sauran sojojin dake biye dasu ma duk suka fito kab suka zo gaban General din nasu suna Sara mai tare da yimai sannu da zuwa.

Cikin murtuqe fuska ya d'aga musu hannu tare da murza yatsun sa yana kad'asu alamar su tafi kawai ganin haka yasa cikin bin umurni suka juya suka tafi kab d'insu sai Captain Sani daya ke binshi a baya.

Cikin gida kuwa
Kab suna tare a harabar babban parlon Aysha matar Ya Amir ce zaune a gefen Mama da keta surfa mata masifa sai Abdul d'an goyon bayanta da yake gefen ta yana cillawah Aysha harara cikin izzah yake cewa.
"Mama ai ita bata san zafin haihuwa bane shiyasa take mana iskancin da taga dama tunda tasan ni bancin tuwo ai sai ta dafa min abin da zanci."

Nafeesat ce ta kalleshi cikin tsoro tace .
"Ayyah Yaya Abdul Anty Aysha bata da lafiya fa."

Cikin yatsuna fuska yace.
"Ke kuma muna fuka waya kasa dake?."

Maman ne ta kai mata mari cikin fad'a tace.
"Ba nace ki dena as mana baki ba in muna maganar mu."

Shiru tayi tana kallon yadda Aysha ke zubda qollah shima ya Amir sai sunkuyar da kai yayi cikin tausayawa matar tasa.

Ga masu aiki ya kawo amman dole an maida matar sa y'ar aiki sam baza'a barsu su sake ba.

Suna cikin haka
General Aliyu Haiydar ya shigo cikin murtuqe fuska da manna baqin glass a fuskar sa dan ya tabbata Mama zata tare shi da baqar magana sanin haka yasa cikin cije lips enshi ya zaro bindi garshi ya d'aga sama ya danna kuna mar ya rinqa sakin harbi ba qaqqautawa gaba d'aya ya cika gidan da qara Captain Sani ma dake bayan shi sai hannu yasa ya kama kanshi tare da to she kunneshi.

Su kuwa su Mama gaba d'aya suka waste a guje parlon ya zama ba kowa ganin haka yasa cikin sauri da takun cikar zati ya komai farfajiyar gidan kai tsaye motar ya bud'e sannan ya rarumo hannun Bodd'i ya fizgota woje sannan ya jata sukayi cikin gidan,
shi kam captain sai sake baki yayi tare da binshi da ido.

Kai tsaye part enshi ya wuce da ita yana janta da qarfi suna shiga ya jata har cikin bedroom kan gado ya cillah ta sannan ya juyo da qarfin ya rufe qofar sai ya kuma dawo kan.........



By
*Garkuwar Fulani*
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 7⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Pure moment of life writers


*Na saudau kar da wannan shafi a gareku Salmab Fadeela Fashuna biebie deee Fadeela Lamid'o Firdaus ina al'fahari daku*


Tsayawa yayi a kanta cikin d'aure fuska ba fara'a ko kad'an ya kuma tab'e baki cikin fad'a da bada umurni yace.

"Ke kina jina ko."
Shiru tayi bata kula shiba sai kanta da ta sunkuyar tare da fidda numfashin tsoro da far gaba,
shurun nata ya qara tunzura shi cikin tsawa yace.
"Ke kina jina ina magana kin wani share ni ko ke kurma ce?."

A tsora ce ta d'an d'aga mai kai cikin zare ido da tsoro ta gyada mai kai alamar ehh tana jinshi .

Qara murtuke fuska yayi tare da zare mata ido cikin muryar fad'a yace.

"Kina jina ko wlh doka ce zan kafa ya miki ! kuma umarni ne ! Wlh kika kuskura kika sab'a abinda zance miki Wlh zaki gane kurenki ."

Sai ya kuma d'anyi shiru sannan ya qara tamke fuska yace.
"Kina jina ko?."
Kai ta gyad'a cikin sauri da tsoro .

Cikin bada umurni yace.
"Kinga wannan d'aki toh kada ki yadda kada ki kuskura inga qafarki ko a parlon nanne bare kuma ta kai ga kin fita cikin gidan nan,
Wlh in kuwa kika yarda kika sab'a umarni nina wlh sai kin gommace kid'a da karatu,
sannan kada ki kuskura kice zakiyi wani abu da zai nuna akwai mutun a d'akin nan in kuwa kinqi zaki gane kuren ki."

Kai kawai take ta gyad'a mai tana numfashi sama-sama dan tsoro.

Shi kuwa ido kawai ya tsura mata sannan ya juya cikin rashin kula,
jikin Windows yaje ya rinqa zuge glass d'in yana rufewa sannan ya sassauqe labulayen ya juya ya kunna mata wuta sannan ya fice ba tare da ya kalli inda take ba.


A cikin gidan kuwa su Mama duk sun fito parlorn jin shiru qaran bindigar ya tsaya gaba d'aya sukayi cirko-cirko suna kallon Captain Sani da ya tsaya kamar dolo.

Mama ce ta kalleshi a yatsine cikin had'e fuska tace.
"Kai Sani wato uban gidan nakane yazo yana mana harbe-harbe a cikin gida kamar wani mahaukaci,
koda yake ba laifin shi bane mashayi kuma menene bazai aikata ba yaje ya gama d'ura giya yazo yana qoqarin hallkamu banza asararre ."

Nafeesat ce ta karya fuska cikin sanyi tace.
"Ya Sani ina Hamma Aliyu da gaske tare kuke?."

Abdul ne ya watsa mata harara cikin yatsin fuska yace.
"Can da Allah kauce banza kawai ji yadda kike wani damuwa dashi sai kace qanin ubanki ne shi."

A fad'ace Mama tace.
"Banza mashayi kawai yazo ya cika mana gida da yan iskan sojojin su mashaya ."

Cikin zage-zagen Abdul ya nufi part en nashi yana.
"Bari inje in sameshi wlh ya shiga hankalin shi."

Yana juyowa Aliyu dake tahowa ya d'aga mai hannu cikin tsawa yace.
"Kai dakata tsaya a wurin kar ka qara ko taku d'aya,
dan wlh duk maison kanshi da lfy kar ya kuskura yace zai zo iya kar part d'ina ko wacce ta tsaya matsa yinta daga yau kar wanda ya shiga hurumi na inba hakaba wlh zan iya yin komai ."

Baki Mama kam ta saki cikin qanqantar da ido irin na bala'i tace.
"Iyeh lallai ka isa yanzu kai ko ubanka ya isa yamin iyaka da wani wurin a gidan nan?."

Kai ya kad'a tare da cewa.
"Hmmmmm mutun ya goda mana ya gani Wlh"
Sannan ya juya gun cikin tsuke fuska yace,
Sani je ka kwaso kayan dake cikin motar ka kawo ."


Captain Sani kam juyawa yayi cikin bin umurni ya fara kwaso tsarabar da Bappa ya had'o musu yana shigar dasu har cikin part d'in Aliyun na sawa a fridge duk ya lodasu sannan wasu ko ya shiryasu a cikin kitchen d'in dake jikin parlour.

Shi kuwa Aliyu a babban parlon nasu ya zauna kan kujera tare da d'ora qafarsa d'aya kan d'aya yana d'an buga qafan ya kuma manna glass a fuskar sa ya murtuqe fuska tamau.

Mama ko sai kanne ido take tana juya kai da cije lebenta tana ta huci,
shi kuwa Abdul dama duk iskan cinsa yana shayin Aliyu dan baya mai wasa,
Ya Amir kuwa da Nafeesat murmushi sukeyi dan dama susan Aliyu sarai tarawa Mama yakeyi inya tashi baya sha yinta,
ita kuwa Aysha sai zame jiki tayi ta koma d'akin ta Daddy ko wanda shine mijin Mama kuma Baban ya Amir da Abdul sai Nafeesat kuma Yaya ne ga mahaifin Aliyu,
shima yana gefe yana hoggo yadda Aliyu ya tsare yau yana juyawa Matar tasa ido har ranshi yaji dad'i dan dama yana jin zafin abinda matar tasa take yiwa d'an,
d'an uwanshi sai dai ba yadda ya iya da masifar ta.

Shiko General Aliyu Captain Sani na fitowa yace ya gama shigar da kayan ya miqe yaje ya rufe qofar parlour sannan ya zura key d'in a haljihu suka fice tare.

Ita kam Mama bala'i ta rinqa yi bayan ya fita ya Amir da Nafeesat ko kowa ya kama gaban sa,
itako da Abdul zama sukayi suna ta tubka da warwara ta yadda shima zasu cusguna mishi.

Shiko suna fita kai tsaye Jaji suka nufa suna zuwa ya wuce gidan shi ruwa ya watsa sannan yasa Esther yarin yar dake mai girki su shara da dai sauran su ta kawo mai abinci yad'an ci sannan ya shiga ya konta dan yin baccin gajiya.

Esther aiki takewa General Amman ita har ga Allah take sonshi a burin tako koda bai aureta ba sunyi zaman daduro shiyasa take bin duk hanyar da zata iya kasan tuwa dashi,
Shiko Aliyu ya rigada Allah ya tsare mai imanin shi da sauran jikin shi duk da kasan cewar sa soja kuma mata shi mai cikar zati.


A Gida kuwa
Tunda Aliyu yayiwa Mama kashedi da karta shigar mai part enshi har yana "a goda agani mana " gaba d'aya ta rasa yadda zatayi dan tsanar yaron ga Daddy kuma ko da ta kaimai qorafi mijin Hajia sai cewa yayin "in yazo weekend ki mai fad'a ."

Yau kwana 3 da dawo warsu Gembu Membila Bodd'i kam tunda Aliyu ya qinda ya mata doka ko bakin qofar parlour bata jeba duk da irin rayuwar kad'aici da takeji ga azabebbiyar yunwar da takeji gashi bata san yadda zatayi komai ba dan ko bayan gida sai a hankali da tab'e-tab'e ta gane har ta samu tayi wonka komai dana Aliyu tayi amfanin kama daga soson wanka da brunch har zuwa towel a haka sai dai tayi wankan ta d'aura towel en ta fito ta d'an goge jikin ta sannan ta meda kayan jikina tun Wanda tazo dashi,
tunda shi kad'ai ne kayanta gashi irin kayan nanne na Fulani farine wanda yasha aikin Zane da ulu red da light green sai yellow rigar y'ar qara mace ko cibiyar ta bata gama rufewa ba sai in ta d'aura zanin sama kad'an kanta ko a tsefe yake sai dai ta d'an tub keshi.

A haka tai ta rayuwa inda taji yau d'in yunwa na shirin hallakata gaba d'aya jikin ta sai bari yake ko tsayuwa gagararta takeyi kawai sai ta kama kuka.

Shi kuwa Aliyu a office enshi Captain Sani da yake kamar shine do garin sa ya shiga bayan ya sara mai cikin sanyi yace.
"Oga ya Meenal kwana biyu bamu leqata bafa."

A fili kauda kai yayi kamar bai ji ba a bad'iri kuwa
ido ya rumtse cikin mamaki ya akayi ya manta da ita shi wlh sam ya manta da itama.

Cikin sanyi Sanin ya kuma cewa .
"Oga tun da Yau ba wani aikin yi ya kamata mu leqa cikin Kaduna."

Kai ya jinjina mai sannan ya miqe tare da cewa.
" ba yanzu ba."

Shiru yayi shi kam Captain dan yasan Aliyu kaifi d'aya ne .

Da yamma liris goshin maggariba ya Amir da Sauran mutanen gidan suna tare a babban parlourn sun zuba ido suna ganin yadda Mama da Abdul suke ta kicini Yar b'allah qofar parlon Aliyu Mama ta dage sai cewa Abdul take.
"Wlh yau sai mun b'alla qofar mun shiga har cikin muga tsiyar da ya ajiye a cikin d'akin."

Shiko Abdul ya dage sai buga qofar yake ganin bazai bud'u a hakan ba yasa ya fito farfajiyar gidan ya d'auki qaton dutse yazo yanata bugawa wai shi zai ballah qofar bugu 2 ana 3 ya d'aga hannu zai buga kenan yaji .......


By
Garkuwar Fulani
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 8⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Pure moment of life writers

*Dedicated 2 Aishat A Muhammad & Ummyn Yusrah and Ummu yahya musa sisin mama & Sadnaf and Husna Abubakar Bauchi*

An kama hannu shi cikin tsoro ya zaro ido woje ganin Aliyu ne tsaye cikin murtuqe fuska ga woni irin cabke mai hannu da yayi ya riqe cikin matsar qashin hannun nashi lokaci d'aya yaji wani irin azaba na ratsa shi cikin in ina baki na rawa yace.
"Hamma Aliyu zaka karya min hannu fa ni ka sake ni ."

Bai kulashi ba sai qara damqe hannun yayi tare da soka yatsar sa tsakanin jijiyoyin hannun shi d'in.

Cikin jin zafi Abdul ya saki qara mai qarfi tare da sunku yawa yana cije hagoran sa a wahal ce yace.
"Wayyo Mama Hamma Ali zai karya min hannu Mama zai tsinka min jijiyar hannun."

Matsoshi tayi cikin isa ta d'ago hannu ta yarfa mai mari tare da cewa.
"D'an iska kawai a gabana zaka karya min hannun d'an nawa dan kai baka san dad'in d'aba sannan baka san yadda uwa ke son d'anta ba,
ai ko mutuwa tana jin kunyar uwa bare kai Aliyu."

Ihu Abdul ya kuma saki da qarfi har kamar zaiyi fitsari a jikin shi.

Jin qaran da ya kuma yine Maman ta leqa fuskar Aliyu da yayi jawur dan takaici bawai dan zafin marin da tayi maiba gaba d'aya idonshi sukayi jazir leben bakinshi sai rawa yake dan fushi hakan yasa ya had'e hannun shi da qarfi wanda har saida hannun Abdul yayi qaran targad'e .

Yana tabbatar da ya targa d'ashi ya yarfar da hannun shi cikin fuzgar magana yace.
"Next time in kayi gigin bud'e qofar nan karya ka zanyi."

Yana kaiwa nan ya bud'e qofar sannan ya shiga tare da cewa Captain Sani ya shigo.

Itako Mama kamar ta bishi ta cinye shi d'anye takeji bala'i take kamar ba gobe fad'a take ko numfashi bata ja .

Shi kuwa Abdul kan kujera ya koma ya zauna tare da tallabe hannun da hannun shi mai lafiyan yana maida numfashin wahala.

Su kuwa su Aliyu suna shiga a parlour ya zauna kan 3 str ya koma ya jingina kanshi tare da lumshe ido yana mai jin zafin kalaman Mama a kanshi ko yaushe bata binshi da kalma mai kyau sai baqin alkaba'i,
gefen shi Sani ya zauna riqe da goran Faro mai sanyi cikin fargaba ya miqa mai murya can qasa yace.
"Ser ga ruwan sanyi ko zaka Sha?."

Baiyi magana ba kuma bai bud'e idon shiba sai kad'a qafa da yakeyi .

Ganin haka yasa Sani yayi shiru sai shiga kitchen da yayi ya kunna gas ya d'an d'aura musu ruwan tea.

Har yanzu idon shi a lumshe yake a hankali ya farajin zuciyar sa tana d'an sanyi dan addu'a da yake tayi,
lokaci d'aya kuma ya fara jin sautin a hankali yaji sautin kukan ta na tashi daga cikin bedroom en sai shesheqa takeyi cikin rawan murya take ta kukan ido ya d'an bud'e sannan ya zurawa qofar d'akin ido zuciyar sa na tafasa.

A ranshi yake tuna cewa ,
Itace qarin matsalar sa ko ya zaiyi ne ma shi bai saniba .

A fili yace.
"Ni bansan ya ake kula da wani ba dan ban taba samun kulan ba nike kula da kaina sai gashi an had'ani da wata jarabar tsiya."

Shiru yayi yana sauraron ta,
har Sani ya fito da y'an cup guda biyu da ruwan tea mai kauri a ciki sai qamshin citta da kanamfari yake,
yana zuwa ya jawo Stol ya ajiye mai a gaban shi tare da cewa.
"Ga tea ."

Shiru baiyi magana ba har zuwa woni lokacin,
shi kam Sani bai kuma magana ba dan ya ga ogan nashi a sama yake .

Can dai ya miqe tare da cup d'in tea d'in a hankali yake takawa har zuwa cikin bedroom en ,
kan gado ya ganta konce rufda ciki tasa hannu biyu ta riqe cikin ta tana kuka murya can ciki tare da yin magana cikin kukan.

"Wayyo cikina wayyo Allah na wayyo Bappa na zan mutu yunwa zata kashe ni qirjina ciwo kaina ciwo."

Duk tana maganar ne cikin fillanci shi kuwa tsayuwa yayi dab da ita sannan ya d'aga kanshi sama tare da kawar da idon shi daga kanta murya a daqile yace.

"Ke ya isheni haka banson sakarcin banza ya zaki zauna kina mana ihun yunwa."

A take ta had'iye kukan nata sannan ta yunqura cikin rawan jiki ta zauna tana bari kar-kar.

Ba tare daya kalleta ba ya miqa mata cup din cikin bada umurni yace.
"Shanye ki ban cup d'in."

A yadda take jin yunwa kamar zata kasheta wai a bata abu a d'an cup d'in nan .

Tana cikin tunanin da qoqarin matsowa ya juyo kanta cikin wani irin cilla mata mugun kallo da yana yin zaki karba ko yaya.

Jiki na rawa ta karba sannan ta kafa kai ta rinqa zugan shi a hankali shiko sai zuba mata ido da yayi har ta shanye.

A take sai ga zufa ta keto mata tako ina lokaci d'aya kuma ta fara damqe cikin ta.

Ganin haka yasa ya fito da kofin kai tsaye kitchen ya nufa yana zuwa ya sake had'a mata tea mai kauri sannan ya dawo ya same ta sai riqe cikin take tana murqususu
cup d'in ya kuma miqa mata,
a wahal ce ta rinqa juya kai hawaye na bin fuskar ta cikin wahala tace.
"Cikina zan mutu."

Bai kula taba sai murtuqe fuska daya kuma yi dole ta karb'i cup d'in ta k'afa kai tana sha tana kallon yadda ya tsuke fuska kamar d'an zai mareta dole sai data shanye sannan ta ajiye .

aiko sai zufa take ta karyo mata dole ta zaune tana yiwa kanta fifita da hannun ta duk da A.C dake fesa sanyi.

Ido ya tsura mata tare da tab'e fuska murya a daqile yace.
"Ke ba'a wonka a garin kune?."

Murya na rawa tace .
"Anayi."

"Qazan tace ta hanaki yi ?."

"Nayi ."

"Toh wanna buhun zanin naki kuma na gadone ko?."

Zuwa yanzu hawaye ya jiqa mata gaban riga cikin tsoron yadda yake mata mgnan murya na rawa tace.
"Banida wani kayan."

Mitsss yaja d'an gajeren tsaki sannan ya juya gun y'ar madaidai ciyar durowar ya bud'e cikin durowar ya tsura ido har zuwa wani lokaci sannan ya zaroh wani 3qtr enshi wanda kuma kamar skin teit ne sannan ya zaro riga mai dogon hannu rigar farace qal wondon kuma read ne mai ratsin fari-fari,
gaban ta ya dawo cikin tsuke fuska ya miqa mata,
ita kuwa hannu tasa ta karba tana mamaki ya zatayi tasa wannan kayan ,
ganin ya tsare ta da ido yasa ta shiga toilet ta zare kayan jikin ta tasa wanda ya batan sannan ta fitoh tana ta d'aga hannu tana gyara hannun rigar don ya mata tsawo har yatsun ta hanna yen suka rufe sai fama take da rigar ga wuyan rigar ma ya mata yawa wondon ne dai ta samu yayi kib da qugun ta,
yana ganin ta fito shima ya fice kai tsaye masallaci suka wuce shida Sani dan maggariba tayi.

banya sunyi harda ishah Sani ya wuce Restaurant ya samo musu abinci sannan ya dawo,
a parlon suka ci tare da d'an yin kallo har zuwa 8:15 Pm Captain Sani ya kalli ogan nashi cikin sanyi yace,
" Oga bari inje in kwana a d'akin Abdul,
tunda yanzu nan kam ba fili."

bai kulashi ba har ya fita sannan shi kuma ya miqe cikin gajiya ya d'auki ledan abinci ya nufi cikin d'akin ,
a gaban ta ya dire mata ledan sannan ya juya yaje ya rufe qofar parlour ya dawo cikin d'akin kai tsaye ya nufi.......

By
Garkuwar Fulani
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 9⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Pure moment of life writers


*Dedication 2 Anty Fauzah & Neena Cool and Maryama Abdool & Momyn sultan*


Toilet ya shiga tare da maida qofar ya datse har ya fara zare rigar jikin sa sai ya lura towel nashi baya cikin toilet en ganin haka yasa ya mai da rigar sannan ya fito.

Kanshi a sun kuye ya tsaya tsakiyar d'akin shiru ya d'anyi na wani d'an lokaci sannan ya d'ago kai ya dudduba cikin d'akin bai gani ba .

Ita kuwa tunda ya ajiye mata ledan a gaban ta tana zaune ko motsi ba tayi ba sai wasa da yatsun ta da take yi tana ta nad'e hannun rigar da yamata yawan .

Murtuqe fuska yayi tare da daqile voice yace.
"Ke ."

Kai ta d'ago cikin tsoro ganin yadda ya had'e fuska, kuma yasa tai saurin yin qasa da kai.

Shiko cika tunxura shi tayi da takaici yana mata magana tana wani mai kallon hadarin kaji.

A kufule yace.
"Ba ke nakewa magana bako?."

Miqewa tayi cikin sanyi da tsoro tace.
"Me zanyi?."
Mitsss yaja tsaki tare da tsuke fuska yace.
"Can tafi ni me zan saki!
ina kika d'ura min towel na ? da kika samu a toilet?."

Sanin akwai abin da ta d'auka a toilet fine ne yasa ta gane me yake nema,
shi yasa cikin sand'a ta wuce gefen shi kan qofar bedroom d'in ta jawo towel d'in da ta shanya data fito wonka.

A hankali ta taka tazo gaban shi cikin sanyi ta miqa mai kanta a qasa.

Shi kuwa ganin yadda take tafiya da yadda ta wani tsaya kamar marigayin zakara,
shi yasa ya tsura mata ido ba tare daya karba ba,
jin shiru bai amshi towel d'in ba yasa ta d'ago kai ,
cikin sauri tai qasa da idon ta tana kallon enda yake kallon.

Wuyan rigar ta ya d'an kalla ganin wuyan ya mata yawa ga d'aya botur d'in ya bud'u ,
itako ganin inda yake kallo yasa ta matse towel d'in a qirjinta sannan ta cukui kuye wuyan rigar ta had'a tare da damqe shi da hannun ta d'aya sai ta kuma tsaya tana d'an zare ido irin na tsoro.

Shi ko General harara ya cilla mata tare da jan tsaki sannan ya komo towel d'in ya fizge ya juya ya shige toilet d'in yayi wonkan shi tsab.


Itako tunda ya shiga ta koma kan gadon ta zauna tare da yin tagumi fuska na zubda qollah sai numfashi take fizga cikin son yin kuka mai sauti sai dai kuma tsoron shi take ji.

Shiko yana fita ya bud'e durowar ya zaro blanket mai taushi da laushi sannan ya zare pillow ya juya ya koma parlour ya konta kan 3str ba tare da jimawa ba bacci yayi awon gaba dashi.

Itako ganin shiru-shuru ba motsin sa ga bacci data fara ji ga yunwa yasa ta zauna kan carpet d'in tsakiyar d'akin sannan ta jawo ledar ta samu ta d'an ci abin cin tana mai zubda qollah sannan ta d'an shan juice ta koma tayi konci yarta kan carpet d'in tana cike da kewan yan uwanta da ta kaicin a haka da ker tayi baccin.


Haka dai sukayi rayuwar kwana 2 tare a d'aki d'aya kuma tun randa ya tabba yeta towel bai kuma mata magana ba,
Sani ke musu hidi mar girki ko yaje Restaurant ya seyo musu in dere yayi Sani ya tafi d'akin Abdul mai targad'e ,
shiko General ya koma parlour itako tana daga ciki,
Mama kuwa da Abdul suna nan suna ta shirin shirya mai gadan zare.


Yau Sunday da yamma Sani da General sun gama shirin komawa cikin Jaji Sani kam har ya d'auki jakar laptop d'in ogan nashi zayi gaba,
ganin General na zaune dole Captain ya dawo ya zauna .

Sukayi gum har zuwa d'an woni lokacin sannan ya miqe cikin d'akin ya nufa a bakin qofa ya tsaya cikin murtuqe fuska da muryar miskilanci yace.

*"Meenal"*
Shiru bata amsa ba a kufule ya kuma cewa.
*"Meenahl* shiru bata amsa ba.

Cikin quluwa yace.
"Bororiya zaki zo ko na tafi?."

Jin haka yasa ta futo da sauri hannun ta na riqe da wuyan rigar ta jikin ta har rawa yake sai fidda numfashi tsoro take.

Juyawa yayi ya nufi kitchen,
itako sai ido ta zura mai,
jikin ta na d'an rawa, bayan ya shige cikin kitchen d'inne
Sani ne ya kalle ta cikin rad'a ganin Ogan a kufule yake yace mata.
"

"In kinji ya kiraki da Meenal ki amsa sannan kome kikeyi inya kiraki kizo yanzu maza bishi kitchen d'in."

Kai ta geda cikin sanyi tabi bayan shi.

A tseki yar kitchen d'in ta ganshi a tsaye sai ta rab'a gefen shi ta tsaya,

Murya a turnuqe yace.
"Kin iya girki ne?."
"ehh." ta bashi amsa a taqai ce

Tsaki ya d'an ja sannan yace.
"Ke ni sauri nake ki matso kiga yadda ake kunna gas d'in sanan ki san abinda zaki dafa kuma kiyi iya ciki ki."

Ido ya zaro mata tare da cewa.
" kina jina ko?."

Kai ta geda mai.

Harara ya watsa mata sannan yace.
"ai baki da bakin magana aikin banza cikin ki ko cikina."
A d'an firgice tace.
"Ina ji."
Tsaki yaja tare da nuna mata komai sannan ya qara da cewa.
"Wlh in kikayi garaje da barin gas a banzace,
zaki babbaka fuskar ki kuma wlh ni ko a jikina."

Toh kawai take ce mai a haka suka gama ya fito parlour tana biye dashi a baya suna zuwa ya cewa Captain Sani .
"Mu tafi."
suna fita yaja qofar ya rufe saurin da yake yasa ya manta bai murd'a key d'in ba

haka suka fita suka tafi.
A parlour suka tarar da Mama tare da Abdul tana d'uma mishi hannu qato dashi,
wucewa yayi kamar bai gansu ba a ranshi kuwa zafi yakeji shi bai tab'a samun irin wannan kulan ba shi ya rasa wannan gatan a rayuwar sa.

Suna fita daga cikin parlour General Aliyu yaji muryar....


By
Garkuwar Fulani
[8/18, 6:26

Please Login or Register in order to submit comment