Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min d'an uwana ."

Shi kam General ya k'asa koda bud'e ido sai hawaye dake bin gefen idon shi yana d'iga ganin haka Rayhana tasa tafin hannun ta tana share mishi k'ollan,
shi kuwa Ramadan sai kallon fuskarsa yake yi,
Cikin kasalan da rawan jiki ya kamo hannun Ramadan ya jawoshi jikin shi tare da rugume shi murya can k'asa yace.
"Inah Ammi? Ramadan ina Ammi? ko ita bata son gani nah ta cireni a cikin yaran ta ko?."

Kai Ramadan ya rink'a juyawa cikin share mishi k'ollah yace.
"Hamma Aliyu Ammi tana sonka gari bai tab'a waye wa ba tare da ta tuna kaba rashin ka a kusa da ita shine nak'usun farin cikinta kullum in zata yi mana addu'a sai tayi maka kafin mu."

Haka Ramadan da Rayhana da Abba suka kwana dashi cikin tsantsar kulawa Captain Sani kuma yaja Abba da Daddy gefen yayi musu baya nin komai.

Aliyu kuwa koda Asuba ta kara to gaba d'aya tunanin shi ya koma kan Meenarl yayin da ko ido ya rumtse sai ya ganta a lokutan da take mak'ale mishi.


Cikin damuwan yayi sallan Asuba Rayhana kuwa kitchen ta shige had'a musu breakfast yayin da Nafeesat kuwa ta shigo ta taya ta sauran ayukan Abdul kuwa shida Ramadan tare suka wuce hospital dan samo magungunan Hamma Aliyun, Captain Sani ko duk inda Nafeesat tayi sai ya bita da ido yana d'an kad'an k'afa.


Forko ruwan Dr Ramadan ya k'ara wa General sannan suka rink'a bashi kula ta musamman shi kuwa gaba d'aya ya resa meke mishi dad'i a duniya duk da bawai ciwon yake ji ba amman yau har yanzu jikin shi a mace yake.



Meenarl kuwa yadda taga rana haka taga dare da zaran ta rumtse idonta sai taga Hamma Haiydar d'in ta cikin halin wahala ,
a d'akin Hajia Amina take dan Ummi na d'akin Abban ta.

Cikin kuka tace.
"Momy wallahi Hamma Haiydar bashida lafiya kullum baya bacci cikin wahala yake kwana ni dai wallahi ina jin tausa yinshi Hamma Jabeer ya kaini in dubashi."

Cikin kontar da hankali Hajia Amina ta matsota tare da cewa.
" takwarata kiyi shiru ki nitsu kinji ko yanzu kinga har k'arfe 4 tayi abinda ya dace kiyiwa Hamman ki Addu'a insha Allah zai samu
sauk'i yanzu jekiyi alwala kizo kiyi nafilfili tare da yi mishi Addu'a."

Ku kunsan Meenarl bata da musu haka yasa tabi shawarar da Momy ta bata.

Koda gari ya waye Meenarl ta k'asa samun sukuni ko abinci tak'i ci ita dai a kaita ta duba Hamma ta,
gashi su Ramadan har yanzu basu dawo ba.


Abu kamar wasa fa Meenarl tunda dare yayi ta fara zubda k'ollah tana bin Dr Jabeer tana cewa.
"Hamma Jabeer muje ka duba Hamma Haiydar wallahi bashi da lafiya baya baccin dare."

Sosai Dr yaji zafin yadda take kuka sosai akan Aliyu a ranshi yace yaushe ma kika sanshi.

A zahiri kuwa shiru yayi tare da tsura mata ido ganin k'ollah dake zuba a fuskarta cikin sanyi yace.
"Mu tafi in kaiki yanzu mu dawo." dan Dr Jabeer mutun ne mai hak'uri da sauk'in kai kuma yana matuk'ar son farin cikin Bodd'insu,
sai ya kuma kalli Ammi a hankali yace .
"Ammi muje tare mana."
kai ta girgiza cikin sanyi tace.
"Yaya Lawan yace kar naje sai sun jesu tukun."


Haka badan yaso ba suka tafi,
da taima kon Meenarl suka isa gidan,
yana yin Parking ta bud'e da sauri kai tsaye part ensu ta nufa shima Dr Jabeer binta a baya yayi.


Suna cike a parlour suna ta hira Ramadan yana yankewa Abba faratun shi,
Rayhana kuwa ta had'a mishi tea,
tana shiga Dr na binta a baya gaban Abba taje ta zauna
a hankali ta gaida shi tare da cewa .
"Abba Hamma Haiydar fa?."

"Yana wonka."
Abba yace tare da kallon Dr Jabeer dake gaida shi,
gaba d'aya kuma sai fuskar Dr ta canza ganin Meenarl ta shige cikin bedroom d'in...!


Ita kuwa tana shiga dai-dai lokacin General ya fito cikin toilet din daga shi sai towel dake d'aure a k'ugunshi,

Tana ganin shi tayi kanshi da sauri tare da cewa.
"Hamma Haiydar."
Shi kuwa ido ya lumshe jin yadda ta fad'a jikin shi ta rugume shi ajiyar zuciya ya sauk'e tare da manna ta da jikin shi gaba d'aya jikin sa sai b'ari yake cikin kewan juna ya tura Hanna yenshi cikin ...........!




By
*Garkuwar Fulani*
[8/18, 6:26 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

4⃣7⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡






*Mi noddi on Fulb'e mi hofni on Fulb'e fulfulde duna Fulb'e fulfulde funa Fulb'e*



Hannu shi d'aya ya tura tsaka ninsu cikin sauri ya kamo towel d'in k'ugunshi da ke k'oka'arin sincewa hannu d'aya kuma kanta yasa ya manna a k'irjin shi cikin sauk'e ajiyar zuciya ya lumshe ido tare da k'ara matsota jikin shi zuciyar shi na harbawa da sauri-sauri.

Ita kuwa Meenarl hannu tasa ta zagayo k'ugunshi tafin hannun ta ta wore tare da manna su a tsakiyar bayan shi cikin sanyi da tausayawa ta d'an d'ago kanta ta tsura mishi ida tare da tsuke bakinta ta d'an tura tare da karya wuya cikin kula tasa hannu ta d'aya a wuyan shi a hankali tace.
"Hamma Haiydar ya jikin ka? har yanzu yana maka ciwon ne?."

Ajiyan zuciya ya kuma sauk'ewa tare da karya wuyan shi ya matse hannu ta dake kan wuyan nashi cikin tsura mata ido da fuskar tausayawa kanshi da kanshi yana kallon ta har cikin ranshi yake jin zafin rabuwa da ita yana kuma tuhamar kanshi da jin zafin d'an indai yace bazai rabu da ita bama bayyi mata adalci ba,
sannan ya zaiyi da amanarta da Bappa ya bashi,
hannu shi dake rik'e da towel d'in k'ugun nashi ya d'an daga tare da kife hannun kan mararshi ,
har lau dai idanun shi na kan fuskarta matse marar tasa yayi tare da rumtse ido a hankali yace.
"Minalin Hamma Haiydar,
lafiya tayiwa Hamman ki tsad'a Minalin Hamma!
ciwo ya min illah! ciwo ya kama ni a inda ya zamar dani nida babu kad'an ne babban cinmu ,
Minali na na cutu,
na samu k'arin ciwo a kan damuwar da rayuwata ke ciki na rasa mahaifiya ta tun ina karami yanzu kuwa ciwo zai rabani da amanata."


Ita kam Meenarl tuni sai hawaye ke bin fuskar ta cikin raunin zuciya ta rink'a zubda k'ollah tana shafa mararshi inda ya kife hannun shi,
tana kuma kallon fuskar sa jin yadda wurin ya fara tauri da zafi yasa ta d'an matse wurin da d'an k'arfi.

Zillo General yayi cikin dauriya ya rik'e wurin a sunkuye ya isa bakin gado zama yayi cikin fidda numfashin wahala.

Matsoshi tayi cikin sanyi ta zauna gefen shi tare da cewa.
"Hamma kayi hak'uri muje asibiti."

Kai ya juya cikin cije lips ya koma ya konta a rigingine tare da yin mik'a yana mai rumtse idanun shi.
ita kuwa sai k'ollah ke bin fuskar ta,
tasa hannu tana shafa mishi kan marar tashi a hankali tana d'an danna wurin.

ido kawai ya tsura mata cikin sanyi ya jawo hannu ta kan jikinshi ya kontar da ita suna fuskarta juna murmushi k'arfin hali yayi tare da cewa.
"Minali Hamma,
Hamman kifa bashi da wani amfani a gareki banban cina da macecce kad'an ne ya rigada na gama mutuwa."

Ido ta zaro cikin tsoro tare da bud'e baki cikin kuka tace.
"A,a
a a Hamma Haiydar bazaka mutuba."

Sai kuma kawai ta fashi da kuka tanayi tana shafa sajen fuskar sa.

Lips enshi ya cije tare da mirgina ta ya kontar da ita kan pillow,
cikin sanyi ya yunk'ura yayi mata rumfa da k'irjin shi cikin sanyi yasa bakin shi kan fuskarta yana hura mata iska.

ita kuwa sai kukan take tana sheshshek'a k'asa-k'asa .
Idon shi ya tsura cikin nata a hankali ya manna bakin shi da nata harcenshi yasa ya rink'a lasar lips enta yana kallon fuskarta.
Shiru tayi tare da lumshe ido tasa hannu cikin suman kanshi.

Shi kuwa ganin yadda tayi shirun ne ya d'an yi murmushi a hankali ranshi ke fad'a mishi ,
"Meenarl matar lafiyeyyene."

A zahiri kuwa lips d'inta na k'asa ya d'an kamo tare da d'an cizawa.

Cikin duniyar nitsuwar da ta tafin taji zafin ya ratsata.

Cikin tsoro tayi zillo tare da tureshi tana yarfa hannu da zaro ido woje.

Shi kuwa General yadda tayi likimon da yadda ta zaro idon ne ya bashi dariya abinda General bai fiye yiba kenan.

Dariya ya rink'a yi a hankali tare da nunata dariya yake cikin danne mararshi dake mai ciwo a fili ta zaro idon shi kuwa abin ya bashi dariya da ta nitsu tanaso ya murjeta dataji sab'anin haka ta wani zoro ido.

Ita kuwa baki ta tura tare da kaimai bugu tana.
"Allah ko Hamma Haiydar sai na rama wallahi zan rama."

dariya ya kumayi cikin d'aga mata gira yace.
"Zo zo ki gani Minali."
tureshi tayi tare da matsoshi tana cewa.
"Maranka zan danna."

Kai ya juya cikin dariyar yace.
"Kashe Hammanki zakiyi ko."

Sai ya kuma nuna mata lips enshi yace.
"Zoki rama anan."
A hankali ta matsoshi tare da zama kan cinyarshi suna fuskantar juna,
lips enta tasa da nufin kamo nashi ta ciza ,
sai kuma tayi ajiyar zuciya tare da sakewa a jikinshi jin ya manne bak'in shi da nata ya zira harshensa cikin bakinta tare da d'aga mata gira d'aya alamar ki rama.
Ina shiru tayi tana jin yadda yake sauk'e mata kasala da salonshi..


A parlour kuwa Dr Jabeer mik'ewa yayi lokacin dayaji sautin dariya General cikin zafin abun ya kalli Ramadan da Captain Sani yace.
"Sani mu zamu tafi ."

Ramadan kuwa kallonshi yayi cikin girmamawa yace.
"Hamma Jabeer Ammi kam su Daddy sun hanata zuwa ko ? bazata zo taga halin da Hamma Haiydar ke cikiba."

Tsaki ya d'an ja k'asa-k'asa tare da cewa.
"Ba shine yake wannan dariyar ba? ko ciwon dariya yake yi?."

Shiru sukayi gaba d'aya d'an sun fahimci Hamma Jabeer a hatsale yake,
Ita kuwa Rayhana kallon shi tayi cikin had'a fuska tace.
"Hamma Jabeer inka koma ka cewa Ammi ni dai wallahi in bata zoba banzan koma Adamawa ba."

Harara ya cilla mata tare da cewa.
"Bodd'iiiii,
Bodd'iii".

Shi kam Abba ido ya zura musu.
shi kuwa Captain Sani hankali shi na kan Nafeesat yana nuna mata pic d'in Ammi a phone nashi.

A cikin bedroom d'in kuwa.
wani irin zafi da takaici ne ya tokari k'ahon zuciyar General jin muryan Dr Jabeer cikin sanyi ya zame bakin shi a cikin nata ,
cikin had'e fuska ya tsura mata ido a fili yake zaton yadda take mak'ale mishi haka take mak'alewa Dr Jabeer ko?,
a take sai zazzab'i ya fara rufeshi sai sanyi da ya fara ji cikin cushewar voice yace.
" Meenarl ke da waye kika zo?."
idonta a lumshe ta konto kanshi.

Cikin zafi ya tureta tare da buga mata tsawa yace.
"Ke dawa kika zo?."

Ido ta tsura mishi baki na rawa tace.
"Hamma Jabeer nane fa."

Tureta ya kumayi tare da sauk'owa k'asa baki na rawa ya nunata da yatsa yace.
"Ehh ai nasan nakine ba sai kince min ke da Hamma Jabeer dinki bane,
nasan shi naki ne,
d'an haka tashi tashi ki bishi me ya kawoki gareni?."

Gaba d'aya ya juya fad'a yake har muryanshi na rawa kamar zaiyi kuka ga zafin zazzab'i yana zura rigarshi tare da cewa.
"Ni ban damu ba karki sake zuwa gareni Allah ne gatana ,
Ammi nama ta gujeni,
Meenarl kema ki tafi gun Jabeer,
karki sake zuwa gidan nan tunda iyayenki basa sona tun ina k'arami suka rabani da maifiya ta duk family naku bakwa sona,
Insha Allah zan shirya Na tafi Gembu zanje Membila zan koma wurin Bappa zanje na gaya mishi a manar daya bani tafi karfina zan taho dashi na nuna mishi inda kike."

Ita kam Meenarl kuka kawai take tana cewa.
"Hamma Haiydar ina zakaje?."

Tsawa ya buga mata tare da zaro key d'in motarsa,
yace.
"Ban sanina ki tashi kibi Jabeer din naki kije ya maida ki gun iyayen ki."

Parlour ya fito itama biyo shi tayi a baya suna fitow ya kalli Ramadan da Rayhana yace.
"Ramadan ku taso mu tafi."

Ba musu suka mik'e tare da cewa.
"Abba bari muje?."

Shima General Abban ya kalla tare da cewa.
"Abba zamu fita."

Shi kuwa Dr Jabeer hannun Meenarl ya kamo tare da cewa.
"Mu tafi a banza zaki tsaya kina kuka."

janta yayi ya fice.
shi
kuwa Captain Sani kallo yabi General dashi ganin yadda yake watsa mishi harara,
harce General ya juya cikin fillanci yace.
"Abba zamuje mu kwana a Jaji da kanne nah."

Murmushi Abba yayi tare da cewa.
"Toh saida safe kenan,
Amman ko zaku meda Rayhana gun Ammin ku ne,
shi kuwa Ramadan zai kula da kai."

Kai kawai ya gyad'a mai tare da ficewa.

Kai tsaye Jaji suka zo suna shiga cikin gidan nashi suka samu mai aikin a parlour ,
cikin mamaki suka kalli juna.
Shi kuwa General fuska a had'e ya kalleta tare da cewa.
"K'anne nane kin tsaya kina kallon su kije ki kawo musu abinci."
.
Kai Rayhana ta rink'a juyawa cikin tuhuma tace.
"Hamma Aliyu wannan kuma wacece? kuma me takeyi? A gidan nan."

Baki ya tab'e tare da cewa .
"Shara da jiran gidan take yi."

Harara Ramadan yayi mata tare da kallon yayan nashi yace.
"Gaskiya Hamma tabar gidan nan bai daceba ka zauna da ita."

Ido ya lumshe cikin sanyin zazzab'i yace.
"Toh ka salla meta tunda baka son zaman ta a nand'in."

Ido ta zaro cikin tsoron kar a rabata da aikinta zatayi magana
Ramadan yace.
"Kiyi hak'uri zaki bar gidan nan kam ki shirya da safe zan salla meki."
zata kuma yi magana General yace.
"Fita a daga nan gobe da safe zai salla mekin hakan da yace banson musu."

Haka ta fita ranta a bace tana jin zafin su ramadan.
Shi kuwa General ya biye musu ne d'an ya lura kamar zargin shi da ita su ke son d'arsuwan musu ,
sannan kuma yana son duk wani abinda zaiyi ya sasu Happy.

Ramadan kam tare ya kwana da General a kan gadon shi yayin da Rayhana ke d'aya d'akin ,
shi kuwa General mamaki yake d'an ciwon shi tun juya yake reguwa d'an jiyama bai mishi kamar na kullum ba bugu da k'ari kuma da asuba yana jin wani yanayi da ke bashi mamaki,
sai kuma gashi yau kam zazzab'i ne ma kawai ke damun shi,
a d'aya sashin zuciyar shi kuwa,
Meenarl yake son yak'i cewa haka ya kwana cikin tunani ,
da k'udirin washe gari zai wuce Taraba d'an gaba d'aya hankalin shi ya koma wurin Bappa .

Haka kuwa. Akayi da asuban fari ya shirya tsab shida k'annen shi , sannan suka sallami mai aikin suka ja gidan suka rufe,
sannan
suka d'auki hanyar Taraba Rayhana da Ramadan zuciyar su k'al da farin ciki dan suna matukar kaunan wannan garin.


Captain Sani kuwa suna fita ya kalli Abba cikin tank'waushe k'afafun yayi k'asa da kanshi tare da cewa.
"Abba Hamma Haiydar ya rasa farin ciki da kulawar mahaifiya tun yana k'arami,
hakan tasa ya rayu kamar maraya ko yaushe fuskarsa cike take da maraici,
hak'ik'a nasan iyayena basu kyauta ba ,
Amman baya ta wuce yanzu mu gyara gaba,
Abba ka maida auren Ammi ka dawo da itakan 'ya'yan ta,
wannan ne kawai zamuyi musa farin ciki a zuciyar. Hamma Haiydar a dawo da Ammin shi kusa dashi."

Kai kawai Abba ke gyad'a wa cikin gamsuwa da shawarar Captain ya kuma yarda da shawarar ,
sannan yace.
"Insha Allah gobe zan gayawa d'an uwana kuma jibi ko gata zamuyi shiri muje gidan ku,
zanje na nemi gafarar Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim da Fatima ta dawo kan yaran ta."

Sosai Captain yaji dad'i dan yana son ya bawa General mamaki ,
ya kuma yi niyar dawo mar da farin cikin sa AMMIN shi.

ITA KUWA Meenarl tunda suka dawo ta k'asa ta tsare so take tayi fushi da Hamma Haiydar d'in nata amman tausayin shi nacin zuciyar ta,
Abban ta da Barrister da Dr Jabeer kuwa abinyana damun su Ammi kuwa tunda Meenarl ta gaya mata halinda General ke rayuwar in dere yayi ,
ta dage tuk'uru tanayiwa d'an ta addu'a da nema mishi sauk'i da kariyar ubangiji kuka take tana kai kukanta gun mahaliccin mu tana kuka tana yiwa d'an ta addu,a.


Tafiya mabud'in ilimi General Aliyu kam tuni yabar jihar haduna ya nausa Taraba ,
A cikin *Mayo balwa* sukayi sallan magariba sannan sukaci gaba da tafiya,
gudu Aliyu yake kamar zai fire d'an so yake a yau dinnan su isa rigarsu Bappa tuk'in yake da sauri a lokacin da suke cikin Membila dan zuwa yanzu mararsa da zazzab'i ga sanyin ciwon da yake ji d'in ga sanyin garin Mambila tuni ya fara karkarwa,
ganin haka yasa Ramadan ya karb'i tuk'in dai-dai lokacin da suke za gayawa bayan dutsen mambila d'in.

9:47 pm dai-dai Ramadan yayi parking a k'ofar gidan Bappa cikin rawan sanyi ya kalli General dake ta karkarwa yana damk'e da mararshi.

Rayhana kuwa kai tsaye cikin gida ta nufa tana zuwa,
Bappa na ganin ta ya mik'e cikin tsantsar farin ciki ya mik'e tare da yin woje yana cewa.

"Muta nen Kaduna kai sannun ku da hanya wannan tafi yan deren cikin deren kuka shigo wannan lardi Allah ya k'ara karewa."

"Amin" tace.
tare da zauma a gefen Inna dake ta faman yi mata sannan .


Bappa kuwa yana fita ya nufi inda motarsu ke tsaye cikin mamaki ya kalli Ramadan tare da haska wanda ke koncen yana rawan sanyi.

cikin firgici da kad'uwa da mamaki da farin farin ciki yace.
"Aliyuuuu,
Alhamhadullih Aliyuuu dama nasan tabbas! tabbas wata rana zaka dawo wannan rigar tamu."

Sai kuma ya kalli Ramadan cikin kad'uwa yace.
"Ramadan meya sameshi ? kama shi mu shiga cikin gida."


Bayan sun kontar dashi kan katifar Bappa Ramadan ya d'ebo magungunan shi zai bashi .

Cikin fahimta Bappa ya matse matar tashi kai ya juya cikin sanyi yace.

"Ramadan ciwon Aliyu bana asibiti bane wannan ciwon kura'ani ne da add'a maganin shi."

K'ara damk'o wurin Bappa yayi tare da matsewa da k'arfi.

cikin wani irin.....



*Allah Yau da k'er nayi typing d'inga*



By
*GARKUWAR FULANI*
[8/18, 8:58 PM] β€ͺ+234 813 799 9565‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

4⃣9⃣to5⃣0⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*Wannan shafi d'uggu ruggum d'in shi nakine ke kad'ai Khaleesat Haiydar Allah bar zumunci da k'aunah ina al'fahari dake, MI YID'I MASIN KHALEESAT*



Dr Jabeer shima yayi parking,
Ido Aliyu ya tsurawa motar Dr Jabeer d'in cikin takaici,
Meenarl ya haggo zaune a gefen Jabeer daga dukkan alamu tare suka fita kuma yanzu sunka dawo tsaki ya jaa cikin murtuk'e fuska yayi shiru yana matse siteri,
Bappa kuwa da Inna da Rayhana shiru sukayi dan basu san me yasa shi jan tsaki ba kuma ya tsuke fuska ya k'i ya bud'e musu motar,
Shiko Ramadan shima kallon motarsu Meenarl d'in yake tare da son fitowa dan sauri yake yayiwa Meenarl albishir da zuwan su Bappa.

Ita kuwa Meenarl shiru tayi tana kallon Hamma Jabeer d'in nata da ya rik'o hannun ta yana murza yan yatsunta cikin wani salon ya k'ara juyowa gareta suna fuskar tar juna cikin sanyi yace.
"Bodd'i na ina sonki inason kasan cewa tare da ke inason farin cikin ki,
me yasa kike k'untatawa kanki akan Aliyu ai da ya damu dake yadda kika damu dashi da bazai iya korarki ba,
Bodd'i nifa d'an uwan kine na jini ki dawo da zuciyar ki gareni zan soki zan kula dake zan riritaki."


Shiru tayi fuskar ta na cike da k'ollah tace.
"Hamma Jabeer,
Ni ina tausayawa Hamma Haiydar bashi da lafiya kullum dere baya bacci kuma ba mai taimaka mishi sai ni."

Sai hawaye shar-shar a fuskarta tana juya kai.

Shiru Dr Jabeer yayi zuciyar shi cike da k'aunar ta yasa hannu ya tallabe hab'arta k'ara matsota yayi tare dasa hannun shi ya share mata k'ollah.


Shi kuwa General da k'arfi ya rumtse idanun shi cikin k'ara matse siterin yana mai juya kai.

Ganin haka yasa Ramadan dannan pin d'in bud'e motar sannan ya bud'e ya fito tare da bud'e wa su Bappa da Inna suma suka fito,
shima kainshi a sunkuye ya bud'e ya fito cikin tsuke fuska.

Suna fitowa ,
Meenarl ta wore ido cikin tsananin mamaki da farin ciki cikin sauri ta fito tare da yin gudu tana zuwa ta rugume Inna cikin kewar juna Inna ta rugumeta Bappa kam sai murmushi.

Ita kuwa Meenarl sai hawayen farin ciki,
sai ta kuma sake Innar tayi cikin gida da gudu tana.
"Ummi! Ummi ina kike ? Ummi ga Bappa na da Inna ya Ramadan ya kawo minsu."

Su kuwa bin bayan ta sukayi suna dariya a babban parlour suka tarar da mutanen gidan baki d'aya,
cikin farin ciki da k'aunar juna suka gaggaisa.

Shiru Bappa yayi ganin Aliyu bai shigo ba cikin kula ya kalli Ramadan dake gefen Ammin su yace.
"Kai Ramadan ina Aliyu ."

"Yana woje yace shi bazai shigoba tunda masu gidan basa so."

Cikin girma Bappa yace.
"Shima ai nan gidan sune."

Sai kuma ya mik'e ya fita yana zuwa kai hannun shi ya kamo yayi cikin gida dashi suna shiga parlour.

Ammi da ta zubawa k'ofar shigan ido tana ganin shi ta rink'a sauk'e ajiyar zuciya tare da tsura mishi ida wasu hawaye masu zafi suka kwaranyo mata cikin rawan murya tace.
"Haiydar."

Shi kuwa General Kanshi a sunkuye yabi Bappa dake rik'e da hannu shi ,
gaban Ammin yaje ya ajiye shi sannan ya zauna gefen shi cikin kula yace.
"Aliyu ga mahaifiyar ka gata a kusa da kai gata a gaban ka."

Shiru Aliyu yayi tare da tsurawa yatsun k'afafun ta idanu lokacin d'aya yaji wani irin karayan zuciya gaba d'aya sai yaji zuciyar shi ta raunata.

Ita kuwa Ammi hannu tasa ta jawo kanshi ta d'aura kan cinyarta yayinda kan Ramadan yake kan d'aya cinyar Rayhana kuwa ta rakub'e a jikinta,
cikin sanyi ta d'aura hannun ta kan tsakiyar kan Aliyu baki na rawa tace.
"Aliyu Haiydar ina sonka d'ana ina tunako ako wacce rana ban tab'a yin sallah na idar ba tare da nayi maka Addu'a ba Ammin ka tana sonka kaine farin ciki na
Nagode wa Allah daya kare min kai."

Shi kam General manna kanshi yayi da jikin Ammin kamar mai tsoron kar a saceta a hankali yaji hawaye masu zafi irin hawaye da yake ji a duk randa bagen mahaifiyar shi ya dame shi,
ita kam Ammi fad'ar farin cikin ta bazai yiwu ba,
General kuwa zuciyar shi cike da k'aunar mahaifiyar shi a d'aya gefen kuwa har cikin ranshi yake jin zafi da haushin yayun mahaifiyar tashi dan su suka mishi Katanga da ita tun yana k'arami suka mai dashi marayan dole.

Bappa ne ya gyara zama cikin halin girma ya kalli Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim sannan ya kalli mahaifi yarsu a hankali yace.

"Wannan shine babban kuskuren da mutanen mu sukayi a wanna zamanin, aiki da zuciya fushi da tunzura a duk inda aka samu saki ya gifta a tsakanin ma'aurata,
mata kin forko da za d'auka shine hak'uri sai kuma a duba darajan Aure sannan a koma a duba makomar yaran dake tsakanin dan gujewa aikin dana sani,
babu wani riba cikin yin fushi dan anyi saki a reba uwa da d'an ta domin ko a shariyance yara suna gefen uwane har sai sun shekara 7 yanzu kai Lawan ribar me ka samu daka reba y'ar uwarka da d'anta kalli hawaye dake bin fuskar ta,
kalli illar rebesun da kukayi yasa Aliyu ya rayuda Bodd'i tsawon lokacin Amman baisan y'ar uwarsa bace itama bata sani ba,
kuna ne manta a can gefen bakusan tana kusa da kuba."

Shiru sukayi baki d'ayansu dan tabbas gaskiya Bappa ke gaya musu,
gaba d'aya zuk'atan su sun cika da nadama,
Barrister kuwa har cikin ranshi yake jin kunyar y'ar uwarshi.

Haka Bappa yayi ta musu nasiha da fad'a da nuna musu illar yin fushi dan an saki y'ar uwarka kace zaka rebata da yaran ta.


Gaba d'aya sun maida hankali kan Bappa shi kuwa cikin girma ya sake gyara zama tare da yin gyaran murya yace.

"Ibrahim wai ka d'aura auren Aminatu da Jabeer."

Cikin sunkuyar da kai Alhaji Ibrahim yace.
"Ehh Bappa na d'aura musu Aure ."

"Yaushe ka d'aura musu auren?."

"Bayan munje Membila lokacin da kukace an saceta toh damuka dawone da wata 1 na d'aura musu auren tunda shi Jabeer yana sonta."

Kai Bappa ya jinjina cikin kafeshi da ido yace.
"A lokacin kana da yak'inin Aminatu tana rayene? a lokacin kana da yak'inin zata dawo ne?
kasan inda take a wanna lokacin ne?.

Ajiyar zuciya Alhaji Ibrahim ya sauk'e tare da jin saurin tabbayoyin Bappa sai kai kawai yake gyad'a wa tare da cewa.
" a a,
bani da sanin wannan Bappa."

Gyaran

Please Login or Register in order to submit comment