Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murya Bappa ya kumayi sannan ya kallesu baki d'ayansu tare da cewa.

"Lawan ana d'aura Aure da babu ne? ana d'aura Aure da wanda ba san inda take ba?."

Cikin goge zufa Barrister yace.
"A a tabbas ba,a d'aura auren da babu matar ,
Amman nima wallahi Ibrahim bai gaya minba sai kawai cemin yayi ya d'aura musu aure."

Cikin ilimi Bappa yaci gaba da cewa.
"A cikin rashin sani kukayi aure a kan Aure! toh cikin wadan nan auraki biyun wanene ya zauna wanda akayi da fari ko na biyu?."

Dr Jabeer kam tuni tabbayoyin Bappa ke tsinke mishi hanjin cikin shi sai ido yake bi Bappa da shi,
shi kuwa Aliyu jinsu kawai yake dan ya gama yanke hukun ci a ranshi shi dai Ammin shine zai tafi da ita.


Cikin sanyi Barrister yace.
"Na farin dai tunda shi na biyun kan na farin aka daura shi ."

Murmushi Bappa yayi tare da cewa.

" toh zab'i yana gun Amina ita zata zab'i wanda take so a cikin su dan haka shariya ta bata dama,
zancen gaskiya kuma Aliyu ni na aura mishi Amina Aure bisa koyarwan addinin mu ga sadakin Amina a hannuna ko sisi ban tab'aba,
kuma ko a wancan lokacin Aliyu bashi yace yana son Amina ba nine na rok'eshi dan sirar da mutun cin ta."

Sai ya kuma juyawa gun Aliyu yace.
"Dan haka Aliyu in baka sonta ka saketa ga sadakin ka sai a maida maka,
inko kana sonta saita zab'a a cikin Ku duk wanda tace bata sonshi sai a maida mishi sadakin shi ."

Gaba d'aya su yarda da maganar Bappa dan gaskiya ce.

Barrister ne ya kalli Meenarl cikin sanyin jiki yace.
"Meenarl wa kike so a cikin su in Aliyu kike so ki fad'i shima d'an uwanki ne."

Ita kam Meenarl sai kawai ta juya kan Dr Jabeer tana kallon shi ido cikin ido fuska cike da k'ollah ta k'asa magana sai kuka an kad'a an rawa tayi magana ta k'asa sai kallon Dr da takeyi tana kuka.

Shi kuwa Aliyu ba k'ara min hatsala yayi ba ganin yadda take kallon Dr Jabeer tana kuka cikin cije lips enshi yace.
"Ni banzan rabata da d'an uwanta ba dan nasan zafi da ciwon dake cin zuciyar wanda aka raba da d'an uwanshi dan haka ni zan barwa Jabeer ita ,
dan shiyafi cancanta da ita kuma shi ya tashi cikin farin ciki dan haka niko banzan zo rana tsaka na rabashi da farin cikin da ya rayu a cikiba ,
niko dama bansan menene farin ciki ko dad'in d'an uwa ba dan haka haka ni zan bar mishi ita."

General yana maganar ne da iya gaskiyar sa dan a can cikin ransa yana jin zafin yadda Minalinshi ke kallon Jabeer tana kuka shi kuma ko inda yake bata kallah ba a d'aya gefen zuciyar sa kuma yana tuna cewa shifa har yanzu lafiyarsa nada rauni.

Shi kuwa Dr Jabeer cikin tsantsar farin ciki da jin k'aunar General d'in yace.
"Nagode d'an uwana Allah ya bar zumunci da k'aunar juna."

Ita kuwa Meenarl zuciyar ta cushewa tayi sai wani irin sautin kuka ta saki cikin tsurawa Jabeer d'in ido.

General kuwa ganin duk sunyi shiru ne ya kara b'ata mishi rai a zuciyar shi yace.
"Ai dama su ba sona suke yiba."

Bappa kuwa ido ya tsurawa General dan ya gano Aliyu yaudaran kanshi yake yi.

Bappa ya bud'e baki zaiyi magana kenan Captain Sani ya shigo parlour cikin sanyi yace.
"Daddy ga Abban su Ramadan yazo tare da d'an uwan shi."

Cikin kula Alhaji Ibrahim yace.
"Maza je ka shigo dasu kace su iso."

"Toh" Captain yace tare da juyawa ya taho da su.

Bappa kuwa haka kawai yake jin wani irin farin ciki mara adadi Inna kuwa da Ummi mahaifiyar Meenarl sai zuk'atan su ke harbawa da sauri-sauri.

Shi kuwa General Captain Sani ya watsawa harara dan ya naga shine yayi shishshigin kawo Abban shi gidan,
Ramadan kuwa sai murmushi yakeyi.


Suna shigowa parlon Captain Sani ne a gaba sai Abba dake binshi a baya.

Inna ce ta mik'e tsaye cikin tsananin mamaki da d'an rud'ewa gaba d'aya jikin ta sai rawa yake yi cikin firgici ta nuna Abban Aliyu baki na rawa tace.
" *WAZIRI* Kaine nake gani ko kamace? Bappa waziri juyo ka gani ga waziri da Usmanu."

Cikin sauri Bappa ya juya tare da sauk'e k'wayan idanun shi kan fuskokin ya ranshi da suka bace masu dere d'aya yau kimanin shekara 38 kenan."

Bappa kam ba abinda yake cewa sai.
"Alhamhadullih ala kulli halin,
Allah na godema da wannan rahawa da kayi min na godewa Allah daya bani aron rai da damar sake sa yarana a k'wayan idanuna."

Abban Aliyu da Daddyn Nafeesat kuwa,
gaba d'aya jikin su rawa yake kamar mazari kai tsaye gaban Bappa suka durk'ushe kamar yara kuka sosai sukayi cikin kewar iyayen sun.

Inna kuwa gani take kamar mafarki takeyi shi yasa ta matsosu tare da rik'e Hanna yensu tana.
"Alhamhadullih Abubakar Usman nagode wa Allah ."

Barrister Lawan ne yayi magana cikin rud'ewa yace.
"Bappa su waye wad'an nan din a gareka ? ka sansu ne?."

Aliyu ma kai ya jinjina cikin zubawa Bappa ido.


Ajiyan zuciya Bappa ya sauk'e tare da nuna Abban Aliyu da Daddyn Nafeesat yace.
"Lawan wadan nan da kake gani yaranane na jinina nine mahaifinmu su
Inna waziri itace uwarsu mahaifiyar su wannan mai kama da Aliyun shine d'anta Wazirin da kukeji ina kiranta dashi ,
wadan nan sune yayun Aysha mahaifiyar Bodd'i ,
yayunta uwa d'aya uba d'aya ,
sun bar rigarmu ne a wani deren munwayi gari babusu ba labarin su munyi nema har muka kareya daga bisani muka fauwalawa Allah tare da saka ran watarana zamu gana,
lokacin da suka bar gida Aysha tana k'arama ,
ashe Aliyu jika nane ban sanina."


Wannan abin al'ajibin ya saka farin ciki a zuk'atan su baki d'ayansu. "

Ummi da Ammi kam sai murmushi sukayi..

Sun zauna sun tattauna sosai sannan daga bisani .
Bappa yace .
"Toh a maida auren Abban Aliyu da Ammi."

Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim ne suka kalli juna cikin son nemawa k'anwarsu enci sukace.
"Bappa bamuk'i maganar kaba amman a bari sai gobe in munyi shawara."

Kai Aliyu ya dago tare da zuba musu ido zuciyar shi cike da tsanar su,
ya za'ayi ana son maida auren Ammin shi sukuma suna dojewa.

Cikin hatsala ya mik'e su Aliyun a goshi yace.
"Ni na bar muku y'arku,
Inma nine bakwaso a cikin zuciyar ku,
sannan yadda kuke ganin zaku hana Ammi na komawa gidan Abba na toh,
Shima yana iya d'auke mahaifiyar Meenarl tunda k'anwar sace,
sannan kuma zamu dauke Ramadan da Rayhana tunda yaran shine ,
ni kuwa a karan kaina ni Aliyu zan dauke Ammi na tunda mahaifiya tace,
Ku Kurik'e zuciyar ku muma mu rik'e tamu zuciyar."

Yana kaiwa nan ya fice yana cewa,
"kuyi tunani da kyau."

Yana fita ya figi motarsa yayi gida.

Barrister Lawan kuwa shiru yayi yana tunanin a zahiri fa Aliyu zai iya tsanarsu ya dauki gaba dasu ,
tuno hakan yasa shi yarda a take a wurin aka d'aura auren Ammi da Abba ,
Barrister yayi haka ne dan Samar da fahimta,
sannan batun Meenarl kuwa,
Sukace tunda shida bak'in shi yace ya hakura shike nan.


A ranar Abban Aliyu ya dauki matarshi da iyayenshi da su Ramadan ya koma dasu cikin gidan shi.

Gidan su Aliyu ya cika da farin ciki da wolwola sai dai sam Aliyu baya sake wa da Ammin shi.

Meenarl kuwa tunda General ya fita take ta kuka DR Jabeer yayi iya yinshi tak'i sai cewa take.
"Hamma Haiydar bashi da lafiya wallahi inajin tausayin shi."

Captain Sani ne ya kalli d'an uwanshi cikin sanyi yace.
"Hamma Jabeer wallahi tausayin shine jigon so da zaran tausayin ya zauna toh akwai so maitarin yawa,
inka yarda ka meyarwa Hamma Haiydar matarsa shi take tausayawa ni nasan irin zaman da su kayi."

Washe gari da dare
Wannan magana ta Captain ita tasa Dr Jabeer karaya ganin tun jiya take kuka tak'i ko cin abinci haka ta wuni har zuwa yanzu na d'arfe 9 na dare gaba d'aya ta tsanan ta damuwan ,
hakan yasa Dr ya yankewa kanshi hukunci yanzu zai kaita gun Aliyu shi zai hakura da ita zai bar mishi ita,
ko dan hadisin nan da ya horemu da mu sowa yan uwanmu abin da zamu sowa kanmu.

Haka yasa ya kalleta cikin sanyi yace.
"Muje en kaiki."

Haka kuwa ta biyoshi suka taho gidan su General d'in.


Shi kuwa General a dai-dai lokacin ya sallami Ammin shi ya fito da nufin wucewa cikin Jaji.

A bak'in get ya tsaya ganin motar Dr Jabeer na shigowa,
fitowa yayi ganin Dr Jabeer d'in ya fito rik'e da hannun Meenarl kai tsaye gaban General d'in ya tsaya cikin sanyi ya kamo hannun Meenarl ya had'a dana Aliyu cikin karfin guiwa da zuciya yace.
"D'an uwana ga matar ka ni na bar maka ita har a bada dan na gane cewa a kanka Meenarl tasan so."

Shiru General yayi cikin mutuwan jiki ya k'asa ko magana,
Shi kuwa Dr sai murmushi yayi tare da cewa.
"Fatana zaka bani auren Rayhana."
Shima Aliyu sai murmushi yayi,
tare da cewa "uhummm."

Daga nan shikam Dr Jabeer ya shige cikin gida gun goggonshi Ammi,

Shi kuwa General hannun Meenarl yajawo tare da cewa.
"Minalin Hamma Haiydar zomu tafi Jaji a can zamu kwana."

Sai kuma ya jawota jikin shi tare manna...



By
*Garkuwar Fulani*


[8/26, 8:11 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

5⃣1⃣to5⃣2⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



*Wannan shafi naki ne ke kad'an Fiddausi sodangi Allah ya bar zumunci*








*Hak'ik'a mai sonka shike kawo maka goron gayyata da nufin kaje muhallin sa tare da baka kulawa da karramawa ta mussam man tabbas nasan kuna k'aunata k'uggiyoyin da kuka nemi da na kasance a cikin ku , ku sani bazan mantaku ba kuma har kullum a duk inda nake kuna raina Garkuwar Fulani takuce kamar yadda kuke nawa INA k'aunarku 😍😘🀝🀝 ina al'fahari daku ina kuma mai kyau tata zaton zakuyi min uzurin da kekyawan fahimta na rashin karb'ar goron gayyatar ku gareni. ina k'aunarku inamai al'fahari daku 😍😘🀝*


Manna ta a k'irjin shi yana sauk'e ayijar zuciya,
ita kuwa Meenarl tureshi tayi tare da janye jikinta daga gareshi cikin had'e fuska ta tura bak'in tare da juyawa tayi bak'in gate d'in da nufin zata fita gidan.

Ganin haka yasa General yin sassanyan numfashin tare da binta a baya cikin sanyin murya yace.
"Minalin Hamma Haiydar ,
fushi kikayi da Hamman ki ne?."

Shiru bata kula shi ba sai ci gaba da tafiyarta tayi tana zubda k'ollah.
Matsota ya kumayi cikin kula ya mik'a hannu da nufin jawota jikin shi ,
da sauri ta kauce tare da k'ara saurin tafiyar tata.
Shi kuwa General gabanta ya sha tare da tsura mata ido fuska a tsuke yace.
"Tun da bakya son ganina zoki koma gun Dr Jabeer ai shi kina son kasan cewa tare da shi."

Cikin fushi da kukan da ya kufce mata tare da ci gaba da tafi yar tace.
"Ehh zan tafi d'in nima zan tafi gidan mu shi ma Hamma Jabeer ai bayada zuciya ne ina jinka ai jiya kace ba ruwan ka da ni harda cewa su Abba su rik'e zuriyar su kuma ku rik'e taku dan haka nima bazan je gidan kuba."

Kamar wasa yaga tuk'uru tafiya take har ta fita harabar gidan ta mik'e kan titin tana tafi yar ta ga uguwar shiru kowa na cikin gidan shi sai haske da ya gauraye kan titin ganin haka yasa shi juyawa cikin gidan cikin motar shi ya shiga tare da jan motar a hankali ya fito tare da bin bayan ta.

Bappa dake cikin masallancin k'ofar gidan kuwa murmushi yayi tare da binsu da ido.

Shi kuwa tafiya yake a hankali har yaje gab da ita sai kuma ya tsaya tare da bud'e mata marfin motar ,
tsuke baki ta kumayi k'ollah na bin hab'arta sai tafiyarta take kamar ma bata ganshi ba.

Shi kuwa k'ara binta yayi a hankali har ya iso gefen ta sannan ya kuma bud'e mata motar,
nan ma juyawa tayi tare da tsuke baki ta tura shi ta d'anashi sama kamar k'arin kunama.
Shi kam General haka kawai yake jin shauk'in yana yin da suke cikin sai murmushi yake yi tare da shafa sajen shi.

Matsota ya kumayi da motar,
Amman sai ta kauce tayi gaba da sauri.

a hankali Meenarl ta fara juyo sautin kukan kare yana dumfaro inda take,
gaba d'aya sai ta kame jikin ta dan harga Allah tana da tsoron kare a rayuwar ta gashi titin uguwar shiru kamar ba mutane .
shi kuwa General binta ya kumayi tare da tsayuwa a gaban ta ya bud'e murfi tare da tsura mata ido cikin karya wuya.

Share shi tayi tare da d'aga k'afar ta taku d'aya tayi a nabiyun ta d'ago kanta cikin zare ido dan haggo karnu ka har guda 4 sun nufo kan titin da taken cikin gudu da haushi,
ido ta zaro tare da juyawa ta kalli Hamma Haiydar d'in nata,
ganin haik'an k'adaran kanta zasuyi yasa ta juyo cikin tsoro da fushi ta shige cikin motar tare da jawo marfin ta rufe gim.

Shi kam General kai ya sunkuyar tare da sauk'e ajiyan zuciya ya figi motar a guje,
tafiya yake kamar bai san da ita a cikin moton ba ,
ita kuwa tura baki tayi da had'a fuska ga yunwar dake k'wak'wular hanjin ta sai kawai tayi luf a jikin sit d'in tana zubda k'ollah.

a haka cikin lokacin kad'an suka isa cikin Jaji kai tsaye gidan shi ya nufa dasu.

Yana yin parking ya fito tare da yin mik'a sannan ya bud'e baya ya sunkuye tare da jawo laptop enshi sannan ya koma gaba ya dauko phones enshi,
sai kuma ya rufe k'ofofin tare da zaga yawa gunta bud'e motar yayi ba tare da yayi magana ba,
Ita ma shiru tayi sannan ta fito ,
tana fita ya rufe motar sannan ya mik'e ya nufi cikin gidan,
da fari kamar ta tsaya so sai kuma taga gaba d'aya harabar wurin cike yake da sojojin ,
hakan yasa ta bishi a baya,
a parlour ta riskeshi yana since igiyoyin takalmin shi,
ita kuwa sai ta koma gefen ta tsaya cikin fara kuka kasa-kasa dan harga Allah yunwa takeji,
Shi kuma yana cire takal man ya mik'e tare da balle beld'in k'ugunshi ,
ya zame wondon kakin dake jikin shi,
sai kuma ya fara balle boturan rigarshi,
yana gamawa ya zare rigar ya bar bocs da bes sannan ya had'e su a hannun shi ya wuce cikin bedroom.

Yana zuwa kai tsaye toilet ya shige cikin sauk'e ajiyan zuciya yayi wonkan shi pes tare da murje jikin shi da sabulai masu k'amshin gaske, towel ya d'aura a k'ugunshi tare da rataye d'an k'ara min towel d'in a kafad'an shi
yana fitowa gaban dressing mirror ya tsaya ,
hannu yasa ya rink'a murje jikin shi da mai tare da feshe duk sashin jikin shi da turaruka masu sanyin k'amshi da sanyaya zuciya gaba d'aya d'akin ya d'auki wani irin k'amshi da sanyin A,C.

Ita kuwa Meenarl zuwa yanzu ta gama iya dauri yarta sai kawai ta saki kuka mai k'arfi tare da yarfa hannu tana d'an dire k'afafun ta tare da cewa.
"Wayyo Allah na! wayyo Bappa na! ni dai wallahi yunwa nike ji kirjina ciwo wayyooo."

Kai General ya d'ago cikin tab'e baki ya ajiye rigar baccin sa d'aya zaro sannan ya fito parlour yana gyara d'aurin towel d'in dake kan k'ugun shi.

Yana zuwa gaban ta ya tsaya tare da Sa hannu ya jawota gare shi,
itako sai yarfa hannu take tana d'an dukan k'irjin shi tare da cewa.
"Ni dai ka maidani gun Ummi na wallahi ni gun Bappa na zaka kaini ni yunwa nikeji."

Fizgota jikin shi yayi da k'arfi sannan ya matsota a jikin shi cikin had'e fuska yace.
*"Meenarl* ki nitsu ki tsaya me kike so?."

Cikin kuka tace.
"Ni yunwa nake ji jiri nake ji k'irjina ciwo."

Kai ya juya tare da Jan tsaki a ranshi yace.
"Ba ga irinta nan ba RAMADAN YA KORE MIN MAI AIKI,
yanzu ya zanyi."

Ita kuwa jin yaja mata tsaki yasa ta tureshi ta koma kan kujera ta zauna taci gaba da kukan.

Ajiyar zuciya ya sauk'e tare da jawo phone enshi ,
Captain Garba ya kira tare da bashi umurnin ya somo mishi d'an abin da zaici.

Cikin k'ank'anin lokacin sai ga Captain Garba da aiken ogan nashi.

Yana karb'a ya juya tare da rufe k'ofar gaban ta yazo ya ajiye mata ledodin sannan ya mik'e tare da shigewa kitchen pilet da cup ya d'auko,
yana zuwa ya wore ledan wanda kaji ne a ciki wanda sunsha kayan had'i sai k'amshi yake tashi ,
kan pilet din ya baje mata shi sannan ya d'auki cop d'in ya tuttula mata juice mai sanyi,
sai ya tura mata su gaban ta cikin murtuk'e fuska yace.
"Sauk'o kici a cici kawai mai kukan yunwa."

Tura baki tayi tare da sauk'owa k'asa ta zauna cikin share k'ollah ta fara tsakuran naman gefe-gefe tana cin tana d'an shan juice d'in,
shi kuwa phones enshi da laptop nashi ya tattara zai mik'e kenan ta ture pilet d'in tare da mik'e wa tana tura baki tace.
"Hamma ya isheni wonka nake son yi kuma girjina yana min ciwo."

Pilet d'in ya kalla sannan ya d'ago kanshi tare da tab'e baki yace.
"Ai dama ba yunwar kike jiba mai jin yunwa harda kukan ne zai cakalkali abinci yace ya k'oshi."

A hankali tace.
"Zanyi wonka fa."

Juyawa yayi ya shige cikin bedroom yana.
"Toh zoki hau kaina kiyi wonkan!."

Kai ta kad'a tare da tattare pilet din ta kaisu kitchen sannan ta shige cikin bedroom d'in,
shi kuwa dama yana shiga kan gado ya haura tare da watsa laptop enshi da phones nashi a gefenshi shi kuma yayi rigingine ya had'e tafin Hanna yenshi yayi pillow dasu gaba d'aya k'irjin shi a woje sai towel dake k'ugunshi.

Ita kuwa tana shiga bata kalleshi bama ta shige toilet d'in cikin jin bacci ta zare doguwar rigar dake jikin ta sannan fesa wonkan ta,
sannan ta kalli. towel d'in dake wurin d'an k'ara mine gashi ita kuma bata son maida rigar da ta cire yanzu,
shiru tayi tare da jawo d'an bireziyar da ta cire wanda kab Momy ce take saya mata su duk da dai ita ba sakawa take yiba asalima yau ta fara sakawa dan ya bata sha'awa,
mak'alashi tayi da k'er sannan ta d'aura towel d'in kan k'irjin ta kai ta sunkuyar ganin bai kai guiwarta ba,
amman sai ta yi k'asa da kanta sannan ta fito ,
gaban mirror taje ta d'auki man shafawarshi ta shafe jikin ta sannan ta koma kan turaru kanshi ta rink'a feshesu a jikin ta tana lumshe ido,
shiru yayi yana kallon yadda take feshe turarukan fees,
saida taji kanshi ya isheta sannan ta je gaban shi a bak'in gadon cikin sanyin bacci da sanyin AC ta kalleshi tare da cewa.
"Bacci nake ji ina zan konta ?."

Lumshe ido yayi tare da nuna mata gefen shi.

Ita kuma sai tsuke baki tayi tare da cewa.
"Ni wurin nan ya min kad'an gashi duk ka ajiye tarka cen woyoyin ka."

Shiru yayi tare da bud'e idanun shi a hankali ya tsurawa fuskar ta ido,
sai ya kuma nuna mata kan k'irjin shi murya a kasalan ce yace.
"Tunda ke giwace uwar birgima zo ki hau kaina ki konta tunda nan duka bazai isheki ba."

Hannu ta fara yarfawa tana d'an buga k'afa tace.
"Ni dai bacci zanyi gashi k'irjin yana ciwo."

Haka ta rink'a mita har kusan 12 ganin hanashi bacci zatayi ya sashi mik'o hannu a hankali ya jawota jikin shi kan k'irjin shi ya kifata,
hannu yasa a tsakiyar bayan ta ya rink'a shafawa a hankali murya can k'asa yace.
"Dere yayi Minali kiyi baccin ki kinji ko."

Kanta ta rink'a juyawa tare da murza k'afafun ta a kan nashi har tana shirin zame mishi towel d'in jikin shi cikin jin bacci tace.
"Hamma kirjina wallahi kirjina ciwo yake min numfashi na yana tafiya."

"Dama kina da ciwon k'irjin ne?."

"A a ni Yau na fara jin ciwon."

Hannun shi ya cusa cikin towel d'in jikin nata a hankali ya cusa yatsun shi biyu ya kamo robar bireziyar nata sannan ya sake shi pet a bayan ta cikin rad'a yace.

"Yaushe kika fara saka wannan abun?."

"Yau ne nafa ta sakawa."

Ido ya lumshe sannan yace.

"Toh zan cireshi dan shine yake saki ciwon k'irjin."

Shiru tayi tana shak'an k'amshin jikinshi .

Shi kuma hannun shi ya saka tare da ture laptop nashi da iPhone nashi can gefen sannan ya murza k'afafun shi ya waresu,
ita kuma ta gyara konciyarta,
k'ara tallabeta yayi tare da had'e hanna yenshi duka biyu kan tsakiyan bayan ta sannan ya balle brzyar ,
a take Meenarl taji gaba d'aya ciwon girjin ya sake sai ji tayi kamar an kunceta .

Shi kuwa a hankali ya tura hannun shi a tsaka nin k'irjin su,
kamo jikin brzyar yayi tare da zaro shi ya fidda shi gefe,
ita kuwa jin zafin zarowan yasa ta d'an d'aga k'irjin ta sama.

Shi kuwa General idanun shi ya rumtse da k'arfi dan k'ok'olwarshi bazata iya juran ganin k'irjin ta a hakaba.

Ita kuwa cikin jin kunya tayi sauri ta kife k'irjin ta a kan nashi k'irjin tare da lumshe ido.

Shi kam General wasu irin ajiyan zuciya ya rink'a direwa a jere a Jere gaba d'aya jikin shi ya rink'a tsuma ida nunshi suka k'asa bud'uwa ya koma tamkar makaho,
sai manneta da ya karayi a jikin shi k'irjin shi na duka tara-tara ba abinda yake fad'i sai.
"Meeenarrhl zaki kashe Hamman kifa."

Itama gaba d'aya jikin ta sai kerma yake ta k'asa magana dan kab tsikar jikin ta ya mike' tsaye sai yatsun ta ta cusa cikin suman kanshi tana murzawa.

A hankali General ya mirgina ta cikin rawan jiki ya tsurawa fuskar ta ido murya can ciki yace.
"Minalin Hamma ?."
Sai kuma yayi shiru yana sauk'e nannauyan numfashi.

Ita Kuwa mik'e wa tayi cikin rawan jiki ta zauna a tsakiyar gadon ,
shima tashi yayi ya durk'usa tare da jawota gare shi rugume ta yayi da k'arfi sannan ya d'ago fuskarta tare da lumshe ido ya manna lips enshi kan nata cikin wani yana yin ya rink'a sauk'e mata muguwar kasala sai sakewa tayi a jikin shi tare da rugume shi tana lumshe ido tare da murza k'afafun ta,
a haka har ta ture mishi laptop enshi,
Amman ina basuma san ya fad'in ba.

Jawota yayi suka konta sannan ya jawo blanket ya rufe su ,
ita kuwa hannu tasa tana tureshi jin yana kauce zatonta ,
sai kawai ta saki kuka cikin tsoro tace.
"Hammahh kayi hak'uri barni inyi bacci ka barni."

Jin haka ya sashi juyawa da k'arfi ya kifu tare dasa hannun shi d'aya ya rugume ta cikin wani yana yin yace.
"Nah.. Nha.. Nah bar ki kar kiyi kuka Meenarl tunda ba kya so na barki."

Haka suka kwana rugume da juna.

Da Asuba General ya mik'e cikin lumshe ido yaje yayi wonka tare da yin alwala,
masallaci ya wuce dan bin jam'i
shine bai dawo ba sai 7 dai-dai.

A parlour ya samu Meenarl konce kan 3 str fuska ya murtuk'e dan har cikin ranshi yake jin zafin abin da tayi mishi a daren jiya gani yake ko Dr take so.

Fuska a murtuk'e yayi kanta tare da...



By
*Garkuwar Fulani*
[8/26, 8:11 PM] πŸ’žIt's @lh@jiπŸ’ž: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

5⃣3⃣to5⃣4⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*Yebon goni ya zama dole hak'ik'a rigar mutunci kan sanya a zatawa mai sanyashi mutunci kinkai a yebi ki, mu matan arewa muna yebawa da halin ki da shigarki Namecy tawa AISHA LAWAN UMAR jarumar ma aikaci mai mutunci tauraruwar AREWA 24 Garkuwar Fulani ke mik'a sak'on jinjina a gareki🀝😍😘*



Sunku yowa kanta yayi pillow d'in da ta matse a k'irjin ta ya zare a hankali sannan ya d'an durk'usa murya can ciki yace.
"Meenarl a nan zakiyi baccin ai wuyan ki zaiyi ciwo."

Kai ta juya cikin jin dad'i baccin safiyar ga garin yayi lum alamun hadari ga iska mai dad'i ga kasan cewa cikin tsabta ceccen wuri mik'a ta d'an yi a hankali ta kai hannun ta kan,
fuskar shi sajen shi ta shafa a hankali,
Ido ya lumshe tare da sauk'e ajiyan zuciya shima hannun shi ya d'aura a kan goshin ta tare zubawa kirjin ido murya a raunane yace.
"Muje kan gado kiyi baccin anjima zan shiga cikin KD zan dauko miki kayan ki."

Ido a lumshe cikin muryar bacci tace.
"Uhmmm Hamma."

Matsota ya kuma yi

Please Login or Register in order to submit comment