Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

laushi.

Ya sakankance sosai abinsa,yanata aikata mata da kallon da yake da tabbacin zai wuce kai tsaye zuwa cikin zuciyarta ne yayi masauki me kyau,koda bai furta komai a gareta ba,baya da fargaba saboda inna tace zata shiga tadan kwanta,malam kuwa yayi baqi a waje,wanda yasan yawanci idan sukazo sukan dauki awa biyu tare kafin su tafi,sadiq kuwa baida matsala dashi,shi ba baqonsa bane bare yaji kunyarsa.

Kusan tare suka gama komai da ita,sannan ya wuce dakinsu bayan ya sanyata ta saka masa ruwan wanka.


*HILTI UNISEX CHOCOLATE*

*_chocolate ce ta musamman daga qasar TURKEY_*

*_Maganin matsalarki hajiya keda mai gida cikin tsari babu yane yamen magunguna_*

*Ki tuntubi wannan number don k'arin bayani*

0818401745207

*_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI AMIN._*
__________________________________

_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_

_(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_

_SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_

_KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_

_AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_

_KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_

_WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_

Turaren wuta list*
Queens special
Kajiji mix
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous

*_DA SAURAN SU DA YAWA_*

*_Handles_*
*Instagram* @sakina_vendibles *Facebook*
@Sakina vendible *Tiktok*
@Sakina vendibles_


Tsaye take gaban mudubin nata tana karanto addu'o'i,bayan ta gama shirinta tsaf na tafiya makaranta don zana jarabawar placement,kamar kullum,tayi kyau cikin uniform din da a kullum idan ta saka zaka dauka ta sanyashi ne da nufin gayu ko ado,saidai sam ba haka bane,qirarta ce,haka Allah ya yita,fatarta na daukar kowanne irin nau'in dressing.

Lokaci daya gabanta ya dan fadi,ta kuma lumshe idanunta sanda ta jiyo muryar ya al'amin yana tambayar inna bata fito ba,wannan wani baqon yanayine da bata jima da tsintar kanta a ciki ba,a duk sanda zataji murya ko motsin ya al'amin din.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana wara idanunta da suka dauki mintuna a kulle sanda ta tsinci muryar inna tana kiranta,cikin yanayi na me kama da me alhini ko tsoron haduwa da ya al'amin din ta zura takalmanta half cover masu kyau,wanda al'ameen dinne ya siya mata,kamar yadda fiye da rabin komai nata da take amfani dashi na rayuwarta.

Dashi suka fara hada idanu sanda ta fito tsakar gidan,saita sauke idanunta daga kanshi da hanzari saboda yanayin kallon da ya jefeta dashi,wanda shi kansa baisan yayi ba,tayi masa kyau sosai yau din,duk da ya saba ganinta amma yau din kamar an qara mata girma da shekaru,itama cikin ranta take tadinshi,yayi wani kyau cikin shadda light blue daketa qyalli,bisa alamu sabuwa ce kar,yau ya fara sanyata,hakan kuma baya rasa nasaba da daurin auren dan abokin malam din da zashi,wanda malam dinne ya wakiltashi yaje,saboda a jiya shi ya wuce Niger,can dangin inna da akayi mata rasuwa zai musu gaisuwa.

Ko kadan bata zargi kanta kan yadda takejin sauyi da baqunta tattare da ya al'amin din ba,saboda ita kanta tana ganin kamar shima ya sauya,kallo da yanayin firarsu gaba daya ya canzata,bata saba jin nauyinsa ba idan suna hira a baya,tana hira dashi kamar yadda takeyi da ya sadiq,amma a yanzu tanajin akwai wani banbamci a tsakaninsa da ya sadiq din.

Tana qoqarin gaidashi inna ta fara mata fada

"Kinsan yana jiranki zaki shiga ki zauna....."
"Innaaa.....bansan lokaci yayi bafa....girkin nan shi ya cinyemin lokaci" ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba,boyayyen murmushi ya kubce masa,abun ya zame mata cikin jininta,ta saba maganarta a haka,abinda ke sake daukan hankalinsa dangane da ita kenan,duk da yana qoqarin boyewa da kuma dannewa
"kaima duk da kai aminu,da tafiyarka,tasan hanya ai,ta tafi da kanta"


Baice komai ba,yadan saki sassanyan murmushin nan nasa,sannan ya matsa inda ta hada komai nata ya sanya hannu ya dauka yana fadin

"Mun wuce inna,daga wajen daurin auren shago zan wuce"

"Ba zaka dawo ka karba abin karin naka ba" sumarsa irinta buzaye daketa qyalli ya shafa da hannunsa

"Ina da ayyuka da yawa ne inna.....akwai dinkin wata amarya da nake,nace mata tazo jibi ta karba,banaso tazo ban gama ba" kai inna ta gyada,ta sanshi da matuqar qoqari wajen cika alqawari,mutum ne shi kaifi daya,mai matuqar qoqarin ganin ya cika alqawari,sam bashi daga cikin jerin layin teloli

"Haka ne,to Alla ya dafa ya tsare mana ku,sai kun dawo"

"Ameen inna" suka amsa gaba dayansu,sannan ya sanya iman a gaba suka fice.


Cikin jikinta take jin kunya nauyi da kuma wani irin yanayi,yayin da shi kuma tunaninsa yayi nisa game da yadda zai tafiyar da koma a tsakaninsu bisa tsari da tsafta,tafiyar sai tazo da sabon salo,saboda ba haka ya saba rakata zana jarrabawa ba,sau biyu tana satar kallonsa,ya ganta sarai,amma sai yayi kamar bai ganta din ba,har zuwa sanda sukayi tsaye a bakin titi suna jiran abun hawa,daga layin cikin layin da yake facing dinsu,wata mata dake sanye da uniform fari da ash,wanda hakan ke alamta ma'akaciyar jinya ce wato (nurse) take tunkaro bakin titin,dukkaninsu sun ganta,har zuwa sanda ta iso titin daga daya tsallaken ta tsaya

"Kamar haka nakeson ganinki.....ina miki sha'awar karatun jinya,ina miki sha'awar ilimi me zurfi"muryar al'ameen wadda ta fara cika da amo na mazantaka a 'yan watannin nan ta ratsa kunnen iman din.

A hankali ta daga kanta ta sanya dubanta ga matar,tun ba yau ba dama ta sani wannan shine burin al'amin din a kanta,ta dade da haddace hakan,kusan kowa a gidan ya sani,don haka sau tari idan suna irin wannan hirar ma babu me ce musu uffan,tsakaninsu ne

"Kiyimin alqawarin zaki cikan wannan burin" cikin mamamki kalamansa ta daga idanu kamar zata klalleshi amma kuma ta kasa,saboda tuna yadda take ji,da kuma yadda idanuwansa ke mata nauyi yanzun a jiki da zuciya

"Bake da kula kowanne irin saurayi,bake ba soyayya" lafazin nasa ya ratsa ta tsakiyar tunaninta ya katse mata shi shi wani sauti mai taushi kuma qasa qasa.

Wata irin kunya ce ta dirarta mata,ire iren maganganunsa kenan da suke caza mata kai,da kuma sake sanyata jin kunya da nauyinsa,maganganun da a baya baya mata su,tadan sadda kanta qasa,qaramin murmushi yana qwace mata

"Eh,wannan ce hanya daya da zaki taimaki cikar wannan buri nawa,ki bari,idan lokaci yayi,ni zan zaba miki ɗanɗasheshen miji da zai dace dake" qarasa rufeta kunyar tayi,sai ta kare fuskarta da hannunta tana cewa

"Ni ban kula kowa ya al'ameen,kuma ma waye zai kulani nima?,dubeni fa?" Murmushi ne ya qwace masa sanda ya saka hannu yana tsayar musu da wata adaidaita sahu sannan ya bata amsa

"Kina da kyau imani....ke kyakkyawa cw ta ajin qarshe ko farko zance,irin kyan dake jan hankalin kowannw namiji....wanda ke ba zaki gane hakan ba,amma a taqaice,ke sarauniya ce" wanda tun daga ranar ta samu sunan queen daga wajen al'amin,sunan da ya koma kirata dashi lokaci lokaci,musamman idan ya zamana babu malam ko inna a wajen,don ta sadiq dama ya maidashi kamar wani kakansa,ba wai kunya ko nauyinsa yakeji ba,yayin da sunan ya tsayewa iman,yake kuma matuqar yi mata dadi,zuciyarta nata mata saqe saqe akan al'amin din,me yasa ya canza?,me yasa yanzu yake tsaye mata a rai?.

Cikin guntar karatun litattafan hausa data fara a boye ya samu amsoshi da dama,saidai kuma har yau bai furta mata ina sonki iman ba,to hakan meyake nufi?.

*******. ******. ********

Tun dazun data zauna a wajen hankalinta yake rabi da rabi,daya a wajen,daya kuma ya karkata kan jinkirin shigowar al'amin gidan yau,sau biyu tana tura almajiran gidansu suna gano mata rumfar karatu ko yana wajen malam sai ace mata baya nan,tunda ta gama ayyukanta tayi alwalar magariba ta shimfida musu tabarma ita da inna a nan wajen sukayi sallah take saka ran shigowarsa,amma shuru kakeji,gashi har qarfe tara na dare na haramar yi,har sadiq ya shigo yaci abincinsa ya sake fita.

Ta gwada kiransa ta wayar inna kuma sau uku ana ce mata a kashe wayar take,har inna dake jin radio ta rage sautinta tana jajjabin rashin shigowar tasa,wanda bata sauke ba sai ga sallamarsa.

Wani boyayyar ajiyar zuciya da batasan daga inda ta taho ba iman din ta sauke,shi dinma koda ya shigo idanuwansa suna kanta,ta miqe a kunyace a kuma nutse tana gyara daurin dankwalinta tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa tana yunqurin karbar ledojin hannunsa

"Yauwa Queen" ya furta qasa qasa yadda innar ba zata jiyo ba,saita saki murmushi tana dora kayan saman daddumar data tashi a kai,inda shi kuma ya qarasa yana zama a kai tare da yiwa inna barka da gida,ta miqe daga kwanciyar da take tana amsa masa tare da tambayarsa dadewar da yau yayi,har tana shirin tura sadiq ya dubosa.

Murmushi yayi yana jin dadin yadda har kullum inna ke nuna masa qauna da soyayya irinbya da da uwa

"Aiki ne yau ya riqeni inna,ban gama musu ba,kuma gobe zasu shigo da safe su karba,na katse ne na shiga kasuwa,shi yasa dinkin ya kaini har dare" jinjina kai inna tayi,tana sake jin qaunar al'ameen din cikin rai da zuciyarta,har kullum shi mutum ne dake sanya cika alqawari gaba da komai a rayuwarsa,ya tsani saba alqawari

"Sannu da qoqari,Allah yayi jagora"
"Ameen inna" .

Iman na daga kitchen tana qoqarin hado masa abincinsa tare da dora masa ruwan wanka take jiyo hirar tasu,ta hada komai a nutse a kuma tsaftace kamar yadda inna ta horar da ita ta fito dashi zuwa inda yake zaunen.

"Sannu da aiki autar inna" ya furta cikin kulawa,ta saki murmushi bayan ta duqa ta aje a gabansa

"Kinga bar abincin nan,zo kiga.....siyayyarki ta tafiya nasreen memorial academy" sosai maganar tayi mata ba zata,makarantar da inna ta kusa dukanta a kanta,saboda yadda ta nace ta kafe tanason makarantar,ita kuma inna ta haneta da zancanta,saboda private school ce da duk term ake biyan kusan dubu goma sha biyar,innan kuma tasan matsawar alamin din yaji tofa sai ya kaita,shi yasa ta sanyata a daki ta ja mata kunne,koda ta sanarwa malam murmushi yayi

"Bansan ko tabarar auta ke damu hajar ba,banda haka.....yaci ace wasu abubuwan zuwa yanzu tafara ragewa,yaron nan hidima da kuma bautar da yake mata ko ciki daya suka fito iyaka kenan,kinyi dai dai,taci gaba da zuwa ta gwamnatinta yadda ta saba,tunda ita takeyi tun tasowarta,kuma tana da basirar gane abubuwa,gashi lafiya lau komai ke tafiya"

Laqwas jikinta yayi sanyi sanda yake fiddo siyayyar da yayi mata yake kuma shaida mata sati me zuwa zata fara zuwa,an gama koma,idanunta suka ciko rau rau da qwalla tana satar kallon inna,tana tsoron kada tace itace ta tusashi gaba ka dole sai ya kaita,ko kuma ita ta gaya masa zabinta.

Ta bangaren innar ma jikinta sanyin yayi,wane irin yaro ne al'ameen din?,ta tabbatar yinin da yayi har dare a shago kudin wannan siyayyar ya hada ya kashewa iman din gaba daya,tabi kayan da ya zazzage din da kallo,litattafai ne tari guda, school bag,takalmi me kyau da 'yan makaranta,biruka da pencils,hatta da uniform din makarantar gashinan a dinke a goge sai sanyawa kawai.

Fada sosai inna ta rufe iman dashi,wannan karon harda al'amin din,kan me yasa zai dinga biyewa iman din da duk abinda tace tana so,ita din 'yar wace da bazata ci gaba da zuwa makarantar gwamnati ba,kamar yadda saura suke zuwa?.

Sosai yaji babu dadi saboda kukan da yaga iman din tanayi,saida inna ta soma sassauta fadan sannan ya mata magana cikin kwantar da kai,yana mata bayani zafa fahimta banbamcin karatun makarantun gwamnati da kuma da na kudi,tare da nuna mata shima yana sha'awar ya canza mata makaranta dama,bawai ita ta sakashi ba,ya dade yana wannan tanadin.

Saida inna ta tabbatar ba iman ce ta tursasashi ba sannan ta fara saukowa,saidai duk da haka bata bar mita ba

"Yanzu kai da kake da nauyin 'yar uwarka a ka,ga naka karatun,sanna kuma ka dauka duk wata lalurar iman ka rungume?" Murmushi kawai ya sake

"Ba komai inna,Allah zaiyi,mudai aci gaba da yi mana addu'a.....sannan don Allah inna karki sake cewa komai sadiq yaji" ya fada da sauri,saboda jin muryar sadiq din dake shigowa da sukayi,kuma yaga reaction na fuskar iman,yasan sadiq din dan hada waje ne,maimakon ya gyara saidai ma ya bata,saidai duk da hakan daya shigo shima sai daya tofa albarkacin bakinsa,magana dai bata mutu har shigowar malam,shine ya yayyafawa abun ruwa,ya sanya albarka a ciki,ya kuma ja kunnen iman,sannan ya kebe da al'amin din bayan kowa ya tashi ya basu waje.

"Yanzu kai malam al'ameen haka za'ayi dakai?" Cikin fargabar ko wani laifi ya yiwa malam ya daga kai ya dubeshi,malam din ya fahimci abinda ke yawo saman fuskarsa,sai ya saki murmushi

"Kai da zaka zama magidanci nan gaba,haka zaka zauna sai abinda takeso zakayi mata?,shifa namiji kullum so ake ya zama tsayayye,yana da kyau a dinga bawa mata dama kan raayi da zabinsu,amma kuma bafa akan komai ba,qarqashinka zata zauna nan gaba kadan,to dole tun yanzu ka dinga azata akan tsari da tafarkin da kakeso ta kasance akai" cikin hikima malam din ya dinga nusasheshi,daga bisani kuma suka fada hira,wanda wannan ba sabon abu bane dama tsakaninsa da malam din ba,sunawa juna kallo da da mahaifi ne.

Ya jima yana nazari kan maganganun malam,su suke ganin kamar yana biyar son ran iman dinne,wanda sam shi ba haka bane,duk abinda yakewa iman....tun kafin ya soma jinta da wani matsayi daban a cikin zuciyarsa kawo yau,yana mata ne saboda ta cancanta ta kuma dace yayi mata hakan,sau tari kuma zabu da ra'ayinsu ana samun arashi yana zuwa daya,iman din ta dabance cikin rai da rayuwarsa,duk da yana ganin abubuwa sosai tattare da ita,ita dinma kamar ta canza,amma nan gaba kadan zai qarasa bude mata komai,yana son yabi komai ne bisa tsari na hankali da dacewa,da wannan ya kwanta a ransa.

*ZAFAFA BIYAR 2022*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKANFARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA_

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.


*_TEAM ZAFAFABIYAR_*08

*_LITTAFIN KUDINE,ZAKI IYA TUNTUBAR WADAN NAN NUMBERS DIN DON SIYAN NAKI_*

09032345899
Ko kuma
09166221261
_______________________________


Misalin takwas da rabi na safiyar ranar litinin din,zaune take saman doguwae kujerar dake falon principal din nasreen memorial academy,tayi neat cikin shigar uniform din makarantar da shima ya karbeta fiye da makarantar data baro,idanunta sunyi narai narai tana kallon al'amin daya miqe yana sallama da principal din,bayan sun gama komai shi da sadiq sun damqata ga hannun hukumar makarantar,baqunta take ji sosai cikin wannan makarantar,tamkar yau ne rana ta farko data fara zuwa makaranta,al'ameen ya waiwayo a nutse ya sanya hannunsa a aljihun wandon lallausan yadin jikinsa da iya tsahon rigar ya tsaya a gwiwarsa,ya ciro 200 ya miqa mata

"Idan ba zaki iya komawa gida ba ki jirani na dawo,sai na maidake" hannu tasa tana amsa
"Zan iya yaaya" ta amsa mishi a tausashe,principal din yayi murmushi

"Wannan qanwar taka da alama kana ji da ita" ua fada cikin salon barkwanci,sai al'amin ya waiwaya ya dubeshi sannan ya saki murmushi

"Auta ce"
"Oh....i see" ya sake sakin murmushi ya musu sallama yabu bayan sadiq suka fice.

Tana zaune nan tana rarraba idanu,har principal din ya kira daya daga cikin masu goge goge dake aiki a makarantar,tayi masa kiran Assistant monitor din ss 1,ba jimawa ya dawo yace tana zuwa.

Ba'a rufa minti biyar ba tayi sallama,cikin nutsatsiyar muryarta,tana sanye da uniform irin na iman din,iman din ta bita da kallo,tana da haske saidai baikai nata ba,tana da madaidaicin kyau,a qiyasce shekarunsu zasuyi daya da ita

"Ga new student nan,ayi mata seat,sannan a shigar da sunanta cikin register"
"Okay sir" ta amsa a ladabce,sannan ta waiwaya zuwa sashenbda iman ke zaune.

Suna hada idanu ta sake mata murmushi,saita soma takawa zuwa inda take din tana dubanta,har yanzu kuma murmushin bai bar kan fuskarta ba,ta duqa ta dauki hand bag din iman din tana cewa

"Taso muje" saita miqe tana dan jan rigarta tabi bayan yarinyar.

Tare suka jera cikin yanayin baqunta,saita waiwayo ta sake sakar mata murmushi

"Sunana munira hasan......nice assistant monitor na ss 1,monitor dinmu namiji ne.....kefa,meye sunanki?"

"Hajar ibrahim khalil"
"Yadda kike da kyau haka sunanki yake da dadi" munira ta fada tana sakin murmushi gami da kallon iman.

Martanin murmushin iman din ta maida mata tana cewa

"Na gode" sukaci gaba da takawa,maganar muniran na maimituwa a ranta,sai ta sanya hannu ta shafi fuskarta a fakaice,an jima ana fadin ita me kyau ce,saidai ita bata taba ganin kyan ba a karan kanta,hakanan bata taba baiwa maganar wani muhimmanci ba.

Kai tsaye munira ta kutsa kai cikin ajin,wanda ya dauki shuru,kowa ya bada hankalinsa ga allon da malamin dake tsaye yaketa cikashi da rubutu daliban suna kwafa suna mayarwa zuwa ga litattafansu. Sallamarsu sai taja hankalin kowanne dalibi dama matashin malamin dake tsaye gaban allo,ta qarasa daura da malami tana cewa

"Sir,sabuwar daliba ce inji principal,yace a saka sunanta cikin register" kai ya gyada gami da cewa

"Okay"idanuwansa nakan fuskar iman,wadda ta fara jin wani iri,saboda yadda idanuwa sukayi mata caa na dalibai maza da mata,musamman ita da banda primary data yi da maza lokacin bata da wayo, junior dinta ajinau mata ne zalla,kasancewarta government school

"What is your name?" Malamin ya jefa mata tambayar da harshen nasara,cikin sassanyar muryarta data sake janyo mata idanuwa ta amsa masa,sai ya jawo register din kusa dashi ya rubuta sunan,sannan ya bawa munira umarnin tayi mata wajen zama.

Kai tsaye seat dinta ta matsa mata,saboda tsarin zaman duk seat daya mutum biyu yake dauka,da su biyu ne akai ita da qawarta,to bayan an shiga sabon term sai aka canzawa qawartata makaranta,hakan ya sanya take zaune ita daya,saboda ba da kowa ita din take jurar zaman ba.


Ranar farko a makaranta ga duk sabon dalibi rana ce dake cike da baqunta da rashin sabo,kusan hakan taso faruwa ga iman,saidai kuma kirkin munira ya hana hakan faruwa,saboda janta data dinga yi da hira,koda aka fita break tare sukayi break din,aka dawo suka zauna a seat dinsu,tana ta bata labaruka da suka danganci makarantar da yadda take,har zuwa lokacin da aka kada bell an tashi kenan,iman din ta saba jakarta tana nufi qofa bayan ta yiwa munira sallama.

A qafa ta fara takawa sabida tadan qara gaba inda babu cunkoson dalibai sosai,tana tsaka da tafiya taji muryar munira na kiranta,saita dakata ta kuma waiwayo suka hada ido,kowa ya sakarwa dan uwansa murmushi,ta dakaci muniran har ta qaraso inda take,suka jera sukaci gaba da tafiya tare,kafin daga bisani muniran tace

"Ya na ganki kina takawa a qafa?" Waiwayawa iman tayi tadan dubeta cike da mamakin tambayar tata,to ame takeson ganinta?,kamar taji tambayar da ta yiwa kanta sai ta dora
"Ko mai daukarki ne bazai samu zuwa ba?,ranar farko a makaranta kuwa ai bai kamata ya barki kiyi tracking ba". Sai yanzu ta fahimci zancanta,saita murmusa

"Dama can motar haya nake hawa,saidai wataran idan hanya ta biyo da yaa al'ameen ta qofar makarantarmu ya jirayeni mu koma gida tare" kai munira tadan jinjina,tana cike da mamaki,saboda kallon farko data yiwa iman,ta mata duba ne na yaran da suka fito gidan hutu,sam kyan qira da dirin da Allah ya bata tayi zubin gidan yaku bayi ba,ta tsammaci zata ga wata shimfidediyar mota tazo daukarta ne,saita aje tunanin nata tana tambayar iman din unguwar da take.

Sanda ta gaya mata idanu ta fiddo

"Ai bamu da nisa da juna,abun hawa daya zamu hau,tunda nima yau shuru ba'azo daukata ba" ta fada tana saka hannu tana tsayar musu da adaidaita sahu,suka masa bayani suka shige,iman din na qoqarin neman ragi kan kudin da ya gaya musun,amma sai taga muniran bata damu da price din da ya fada ba,don haka itama sai tayi shuru kawai.


Suna tafe muniran na jan iman da hira,a dan zamansu na awanni iman din ta fuskanci muniran kamar daga gidan masu dashi ta fito,koma ba haka ba to tabbas gidan data fito sunfi nasu wadata,tadan saki jiki kadan da ita tana biyewa hirar tata,har aka kawo inda muniran zata sauka,wanda daga nan zuwa gidansu iman baifi naira 20 ba kudin mota.

Kudin da ya buqata munira ta ciro ta biya musu,iman zata doje tayi gaba abinta bata tsaya ma sauraren qorafinta ba,mai adaidaita yaja sukayi gaba,cikin ranta kafin su qarasa gida tana ta yaba kirkin muniran da karamcinta,azamansu na wasu taqaitattun awanni.


A dan gajiye ta shiga gida,saboda akwai qaerin lokacin tashi kadan a wannan makarantar kan makarantar data baro.


Da sallama ta kutsa tsakar gidan nasu qarfe biyu da rabi da minti biyar,inna dake duqe tana baza masarar data wanke don ta samu tasha iska akai niqa ta dago tana amsa sallamartata,idanunta akanta,ta sabule jakar bayanta ta zauna saman kujera 'yar tsuguno tana dan goge zufar goshinta tare da yiwa inna sannu da gida

"Yauwa,an taso kenan?" Ta fada tana juyawa zuwa ga aikinta

"Wlh inna,duk na gaji,makarantar tafi waccan nisa"

"Ah to,aishi sa kai yafi bauta ciwo" tasan mita sarai inna zata dorar,don haka ta saki dariya kawai ta miqe tana daga jakarta

"Amma inna karatun da ake mana a waccar makarantar baiko kama qafar rabin na wannan makarantar ba"

"To Alla ya taimaka" ta amsa mata.

Kamar zatayi gaba sai kuma ta dakata

"Inna ya al'ameen bai dawo ba?"

"Tunda ya fita dai bai shigo ba" saita daga hannunta duban fuskar siririn agogon silver dake hannunta tana duba lokaci,wanda yau ta fara sakashi,kuma al'ameen dinne ya siya mata saboda makarantar

"Amma dai inna ba tuwo zakiyi ba"

"Zanyi ko zakiyi?" Kai ta gyada cikin salo na zaquwa da son jin amsar innar

"To zanyi inna"

"Bashi bane maqiyar tuwo.....dambu nakeso wai nayi" sai fuskar iman din ta dan saki,don ita gaba ce tsakaninta da tuwo,tunda taji batun dambu kuwa,tasan saboda malam da al'ameen za'ayishi,don haka tayi damarar zagewa tayishi yayi kyau yayi dadi ko don al'ameen din,tana matuqar jin dadin yadda yake yaba mata idan tayi girki,da yadda yake nuna jin dadinsa,koma bayan sadiq dake kusheta,wani lokaci har sai malam ya shiga sannan zai qyaleta,duk da shima yana yine kawai saboda tsokana,bawai don bata iya din ba,don ta fannin girki inna ta yarda da ita dari.bisa dari,tun tana da shekara takwas innar ta fara shiga madafa da ita,tana da shekara sha biyu kuwa ta sakar mata girkin,saidai ta

Please Login or Register in order to submit comment