Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A sannan ji yayi babu abinda yake da buqata banda yaga iman a gabansa ya tambayeta abinda ke faruwa,yana da burin idan ta tashi amsa masa ta amsa da cewa wasa take,ba da gaske take ba. Ba tare da la'akari ko kuma duba da cewa dare ya fara yi ba ya miqe da hanzar ya nufi qofar fita,yana so ya sadu da ainihin cikin gidan.

Garam sukayi karo da sadiq dake shirin shigowa da ledar balangun da ya tafi siyo musu,saboda dukkanins mutane ne masu son cin dadi a bakunansu,hakan bai basu matsala ba,saboda kowannensu neman kudi yake tuquru

"Haba mana master......saurin me kake?,gani na dawo,wajen ne akwai layi,kasan ya iya gashi" ja baya yayi yana duban sadiqun da yake mulmula goshinsa,wanda shi sam bai ma damu da nasa goshin da ya buge ba,saboda rudanin da yake ciki,gaba daya ma ya manta wai sadiq din ya tafi siyo musu nama.

Idanu sosai sadiqu ya zuba masa yana masa wani baqon kallo

"Amin.....lafiya kuwa?,wani abu ya faru ne bayan na fita?" Qafafunsa dake a mace kamar lawashin da yasha rana ya fara janyewa da baya da baya,bayan hankalinsa a sannan yakai kan agogo,ya kuma tabbatar bazai iya shiga cikin gidan a yanzu ba,sabosa bai taba shiga din ba idan ba wani abu bane ya taso

"Babu komai" ya amsa ma sadiqu yana zubewa gefan katifarsa,tare da yin hobbasa na ganin ya saisaita mood na fuskarshi

"Koda naji" sadiqun ya fada yana cire takalmansa ya dorasu saman abinda suke dora takalma dake bakin qofar dakin sannan ya shigo,ya bude musu naman yana bawa amin din labarai kamar yadda suka saba duk dare kafin su kwanta.

Idan yace yana gane abu daya da sadiqun ke fada to tabbas ya zabga qarya

"Ya baka cine?,wai anya lafiya kake kuwa?" Kalmar da sadiqun yace dashi kenan yana rutsashi da ido,abinda yayi silar daya ringa miqa hannu ya a zaqular naman yana hadiyewa ba tare da ya tsaya cikakkiyar taunawa ba bare ya gane wanne irin taste gareshi,haka ya dinga tsaya masa a maqoshi kamar wanda ke cusa dan wake,abinda yayi sanadiyyar qwarewarsa kenan yahau tari,wanda ya sarqafeshi sosai,sai da yasha ruwan sanyin da sadiqu ya bashi sannan ya lafa,da wannan ya fake yaje ya kwanta,saboda qirjinsa da ya dauki zafi,sadiq yace may be ko ulcer dinsa ce ta motsa kuma.

Tunda ya kwanta idanuwansa a rufe suke gam,ko qwaqwaran motsi baya qaunar yaji a kusa dashi bare magana ko surutu,lokaci bayan lokaci yana bude idanunsa ya sauke ga agogo,yana qididdigar mintunan da suke gabansu kafin wayewar gari.

Zuciya da tunaninsa sunkai sun komo,ya kuma rasa a wanne bigire zai ajjiye tunani da zuciyarsa,karafkiya qaryata juna da sa'insa babu kalar wadda ba'a samu ba tsakanin sashe biyu na zuciyar dake qirjinsa,wata zuciyar na rinjayar da qaryar cewa ba iman bace,haka ba zata faru ba,yayin da wara zuciyar ke tabbatar masa da iman dince,saidai ta aikata komai ne bisa rashin sani,koma meye ya riga ya yankewa kansa hukunci kawo qarshen komai,koma meye zai faru ya faru,qirjinsa bashi da qarfin daukar zuciyar da zata rasa iman haka cikin sauqi,saima ya korewa kansa wannan tunanin da yake kallonsa a baqi kuma mummunar fata cikin rayuwarsa.


Dai dai lokacin da iman din take can kwance saman tata katifar a zahiri,a badini kuma tayi matuqar yin nutso kuma me zurfi cikin kogin qaunar bassam,wanda ta ara masa daqiqa masu dama yana sake karanta mata yadda qaunarta ta tashi zuciyarsa a aiki,irin girma da kuma matsayin da take dashi,abinda ya sake sawa taji kanta ya fasu,alfahari da samun bassam da kuma soyayyarsa ta shigeta,ta bude masa tata soyayar sosai wadda ta narkar da ilahirin zuciyar bassam,ya kuma dauka mata alqawura masu matuqar nauyi a mizani,girma kima da kuma martaba cikin duniyar soyayya,wanda daga qarshe sukayi tarayya kan alqawari guda,duk rintsi.....duk wuya.....suna tare,babu gudu kuma babu ja da baya,dukkan wanda ya sauka daga kai ko kuma ya sauya,la'ana da kuma hukuncin cin amana yahau kansa.

Wannan kusan itace hira mafi dadi da sukayi da bassam a wajenta tsahon tarayyarsu,domin kuwa ko bayan ya sauke wayar sun rabu kasa runtsawa tayi,murmushin dake kan fuskarta cikun duhun dakin yaqi barin fuskarta,hirarraki muryarsa da gwala gwalan kalamansa sukaqi barin qirji da zuciyarta,ta dinga tariyarsu tana jin wani dadi qauna da shauqi yana sake kamata,zuciyarta jaririyar zuciya ce,wadda ta fara soyayya ta zahiri a karon farko,don haka komai baqo ya kasance mata,sai daga bisani fa samu baccin yayi awon gaba da ita,cike da mafarkan bassam,wanda a ciki har ya zama miji a gareta.


Kwata kwata baccin da yayi tsahon daren dukansa bai wuce na awanni uku ba,suma din a tsitstsinke,a kunnuwansa akayi kiran asubahi,yayi alwala suka fice masallaci tare da sadiqu,wanda hakan al'adarsu ce,kuma acan suke tadda malam.

Miqewa sadiqu yayi ya dubeshi bayan an idar da sallar,wasuma har syn fara watsewa

"Nikam yauma idan zaman azkar dinkan nan zakayi saidai mu hadu a gida,don wallahi jiya kwata kwata bacci bai isheni ba" ya fada yana miqa

"Shikenan,saina taho" ya amsa masa yana sake maida kansa qasa,don bayason sadiq din ya fahimci bai samu bacci ba.

Yana kallon sadiq ta qasan idanunsa har ya fice,hakanan yaji bazai iya komawa cikin gidan ba,ya kintata wani lokaci ne da zai cimma iman,duk da cewa yau tana da makaranta alhamis ce.

Cikin wani nishadi da walwala take zuba kunu da awarar data soya cikin cup da plate don taci ya wuce makaranta,ta gama shirinta tsaf,kana duban fuakarta zakasan wani nishadi takeji,bassam ya raya darenta ya kuma qawata mata safiyarta da kyakkyawan saqon barka da safiya.

Ta juyo zata fito kenan yayi sallama bakin qofar kitchen din,idanunsu suka shiga cikin na juna,sai ta hangi baqon yanayi tattare dashi,saidai bata kawo komai ba cikin ranta ta zarce da gaisheshi,ya amsa mata yana nazarinta

"Akwai ruwan dumi?" Ya tambayeta yana jingina da qofar kitchen kamar yadda ya saba,tsaiwarsa kwnan duk sanda zai karba ruwan,duk da yawanci a gajiye yake shigowa dama saboda exercise da yakeyi,sabanin yau,da babu execise din da ya iya fita,saidai zuciyarsa a jigace take qwarai,wanda hakan yayi tasiri har zuwa gangar jikinsa,ya matsu ya kuma damu ya fidda abinda yake zuciyarsa da ransa komai da komai ma ya huta

"Yaaya...gashi" ya tsinci muryarta tana masa magana,da alama tun daxu ta zuba ta miqa masa,sai ya karba ya fara kurba a hankali,bayan ya matsa mata hanya

"Idan kin gama ki dauko litattafanki ina jiranki" har tadan dakata sai kuma ta amsa da to tayi gaba,kasancewar ta saba lokaci lokaci yakan rakata,koda ba har makaranta ba to xai kaita bakin titi,saidai a kwanakin nan abun yaja baya.


*_LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.


*_TEAM ZAFAFABIYAR_*18

Jerawa yayi da ita kafada da kafada sanda suke takawa a hankali,idanunsa qur saman hanya,zuciyarsa na taraddadi da fargabar abubuwan da zayaji.

Satar kallonsa ta sakeyi a karo na barkatai,ganin sun nufi hanyar makarantar tasu kai tsaye ba tare da ya tsaidan mata da abun hawa ba

"Yaya,a qafa zumuje?,ka manta?,kawai dan nisa fa?,naga munbi ta layin nan" lokaci ya kalla a hankali kafin ya sauke hannunsa ya kuma sake rage speed na tafiyar,ya zaro wayar dake aljihun hagunsa ya miqawa iman idanunsa cikin nata

"Karbi ki dubamin" cikin rashin fahimta ta miqa hannu ta karba wayar,ta kuma bude kamar yadda ya umarceta.

Abinda ta gani din shi ya birkita kwanyarta cikin sakanni,duk da tasan da wanzuwarsa,amma bata tsammaci yaci gaba da wanzuwa cikin wayar ba,take rudewa suka bayyanar mata,saidai tayi qoqarin bawa kanta dakiya da qwarin gwiwa,tunda babu wani na sabo ko rashin tarbiyya kaf cikin charts dinsu,bugu da qari ma tana jin lokaci yayi da zata bayyanawa duniya bassam dinta

"Waye wannan?" Amin ya fada yana kallon wayar kafin ya maida dubansa ga fuskar iman. Har cikin ranta taji tambayar kamar tazo mata a dai dai,don saboda dama ya amin dinne kawai take tunanin zatayi maganar dashi,ya kuma fuskanceta har ya kai zancan gaban malam,to saidai shima duk sanda ta yunqura zata yi masa maganar sai taji ya mata wani mugun kwarjini,amma yanzun komai zaizo da sauqi.

Sunne kai tayi irin na alamun jin kunya

"Saurayina ne ya amin"ta fada tana rufe fuskarta da tafin hannu.

Hasbunallahu wa ni'imal wakil,ita yayi qoqarin zuqowa saga mafitar maganarsa zuwa saman harshensa,sannan yayi azamar dafe wata bishiya da tafiyarsu ta ratso dasu ta gefanta don neman agajin tsaiwa sa qafafunsa.

Kasancewar sautin addu'ar tashi bai samu fitowa ba illa maqalewa da yayi saman harshensa.......wannan ya sanya sam batasan me yake faruwa ba,cikin wani irin tashin hankali yaci gaba da kallon iman duk da fuskarta a rufe take da hannunta

"Iman......ina alqawarin da kika yimin ba zakiyi soyayya da kowa ba?,ina alqawarin da kika yimin na bani damar zabar miki miji na gari?" Yanayinta ya sauya kadan cikin boyayyar fuskarts,duk da bata kalli tasa fuskar ba amma ta fuskanci sauyun sauti sosai fiye dana dazu

"Yaaya.....kayi haquri,na saba maka wannan alqawarin,amma shima ina da tabbacin irin mijin da kakeson zabarmin dinne,kuma zaka yaba da zabina yaya,ya shiga rayuwarta ne katsam" qara dafe bishiyar yayi da kyau saboda jin jiri na dibansa da yayi,babu sauran kwana kwana ko boye boye

"Iman......nine mijin da na yi miki tanadi,ni ya amin dinki nine mijin dana zaba na kuma killace kaina saboda ke,iman.....ni amin nike sonki iman,zuciyata ta girma da sonki ta kuma rayu da sonki tsahon shekaru masu yawa". Kamar wadda aka jibgawa wani abu a saman kanta haka taji,ta yaye fuskarta da sauri da kuma hanzari don tana da buqatar tabbatarwa kanta ba shirin film akeyi a wajen ba,tana son ta gani da gaske ya amin ne?,kuma ba wasa yake mata ba?.

Saidai kuma.....kallon farko ta karanci zallar gaskiyar dake fitowa tun daga zuciyarsas shimfide saman fuskarsa muraran,abinda ya sake firgitata,ta danyi baya kadan tana jin tashin hankali yana rufto mata,ta yaya haka zata faru?,ta yaya zaice wai da sonta ya rayu?,me yasa bai gaya mata tun da can ba sai a yanzu data riga tayi alqawari da wani,data riga tayi nisan kiwo cikin duniyar soyayyar wani?,ta yaya zata gane yaren da yakeson koya mata bayan bashi ta iya ba?,meye yake shirin faruwa?.

"Ya ameen,da gaske kake?,nice fa iman dinka?"kai ya gyada mata yana kallon tsakiyar idanunta kai tsaye

"Na sani,iman dita ce,shi yasa nake gaya mata halin da zuciyata take ciki,ina sonki iman......burina kuma na aureki,in fact,malam ya jima da bani ke!" Maganarsa ta qarshe saura kadannta wargaza kwanyarta

"Me?!" Ta furta da wani sauti me kauri da amo

"Eh,malam ya bani ke tuntuni" ya fada yana gyada mata kai tare da tabbatar mata.

Kanta ta soma girgizawa,sam sam kwanyarta ba zata dauki wannan batun ba,wacce iriyar magana ce haka mara dadin saurare?,ta yaya zaizo mata da wannan maganar?,tsahon zamansu da rayuwar da sukayi a muhalli guda bai taba tunkararta da maganar ba sai yanzu?sai daidai wannan lokacin?.

Ci gaba tayi da gigixa kanta tana koma da baya,kafin ta juya cikin wani irin hanzari ta nufi hanyar gida,ya miqe da sauri yabi bayanta yana qwala mata kira,saidai ko waiwayawa batayi ba bare ta saurareshi,har ya fara rufa mata baya,sai kuma ya tsaya cak bayan ya yiwa kansa birki ya kuma gayawa kansa gaskiya kan bai kamata ya bita ba din,jama'a suna kallonsu,sannan kuma gida zata shiga a hakan,shigarsu tare cikin wannan yanayin su duka biyun bai kamata ba,kuma yana biye da ita,sai ya dawo a hankali cikin wata kasala da mutuwar jiki ta gaske,ya duqa ya dauki jakarta data sulale a wajen ya soma takawa a hankali shima zuwa hanyar gidan,kwanyarsa na juyawa,tunaninsa yana hautsinewa,yaya iman ta dauki maganar?,me ya sanyata firgicewa haka?,wadan nan sune tambayoyin da ya dinga maimaitawa kansa su wanda bashi da amsoshinsu.

A hanya komai kama kamar iman bai gani ba,hakan ya alamta masa ta jima da isa gida kenan?,wannan yasa daya dawo shima bai shiga gidan ba,dakinsu ya wuce kai tsaye,ya zame saman katifa yayi rub a ciki,bayajin akwai wani abu da zai iya tabukawa,saboa ya jin kamar qafafunsa ba zasu iya daukar gangar jikinsa ba.

Yadda batasan a gida ya wuni ba itama shima baisan tana kwance cikin dakinsu ba,dukkaninsu wani irin yini sukayi mai wahala qunci da kuma takura,tunanin dake qirjin kowannensu ya nauyayar masa,wani irin yanayi mara dadi na zulumi da kuma fargaba,fargabar data kasance mai tarin banbamci a tsakanin iman da ameen.

Sai magariba da ya shiga cikin gidan inna keta mamakin dama yana ciki?,saboda sadiqu nada aiki da yawa a ranar a garejinsu,abinda ya sanyashi fitar wuri sannan kuma har zuwa lokacin bai shigo ba

"Banajin dadi ne inna,kuma banaso na gaya miki nasan zakiyita damuwa ne" amsar daya bata kenan

"Ikon Allah,don iman bata jin dadine itama,nasan da dole zata bincikoka,nayi mamaki nima da banji motsinka ba ashe jikinne.....don Allah aminu ka daina zama da ciwo baka fada,babu kyau,a qalla ya kamata ko leqaka a dinga yi ko ana ganin yanayin jikin naka,baka zauna a daki kai kadai ba kamar babu kowa cikin gidan uhmmm"

"In sha Allah inna,kiyi haquri" ta amsa masa sa babu komai,yanayin sanyi da yanayinsa ya koma saita azashi da cewa don bayajin dadin jikinsa ne,daga bakin qofar dakin iman din ya tsaya yayi mata sannu saboda wanzuwar inna a wajen kada taga ya wuce,ya jiyota can qasa sosai ta amsa masa,sai ya sake wucewa zuwa dakinsu.

********. ****. ********

Munira ce rike gam da hannun iman din sanda suke zagayawa zuwa bayan ajujuwansu,bata sakar mata hannu ba sai da suka dangana saman wani dan tudu wanda asalinsa tarin qasa ne saboda jimawa a wajen ya koma kamar dutse.

"Tunda kika shigo na tabbatar ba lafiya ba,gashi jiya na dinga zura idanu an bani saqo na baki amma baki shigo ba" munira ta fada tana duban iman dake zaune ta rungume qafafuwanta a qirjinta.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke,a.hankali ta fara magana cikin sautin da sai ka dauka wani babban ciwo tayi

"Rayuwata na neman fadawa garari munira......na shiga rudani me zurfi daga jiya zuwa yau,irin wanda ban taba hasasowa ba" matse fuska munira tayi tare da sake tattara hankalinta waje daya

"Rudanin me?,me ya faru?rabuwa kukayi da bassam?" Kai ta girgiza

"Muna gab da rabuwarne wala'alla"

"Karki gayamin wannan mummunar kalmar mana iman,kina haukane?,bassam din zaki bari ya subuce miki?"

"Munira.....ya ameen ke sona" saita firfitar da idanu waje

"Yayannaki da kuke ciki daya?,wanne irin hauka ne wannan?"

"Ba ciki daya muke ba,riqonshi inna tayi,kuma almajirin malam ne,dalibinsa ne" sak munira ta tsaya tana kallon iman,tarin mamaki ne fal saman fuskarta,sai iman ta gyara zama ta gaya mata duk yadda akayi.

Fuska munira ta yatsina

"To don yana sonki shine me?,kawai saiki zauna a rabaki da wanda zuciyarki takeso?,wanda zai zama hutun rayuwa a gareki matuqar kika aureshi,karki manta,'yammatan wannan zamanin SHI SUKE BURI" Kai iman ta girgiza tana jin tashin hankali na sake ninkuwa cikin ranta

"Munira.....bakisan halin malam ba,na tabbatar baya magana ta tashi,kuma wallahi wallahi indai ya ameen ya tabbata yana sona malam ya sake fahimtar hakan babu wanda ya isa ya hanashi bashi ni duk duniya" murmushi munira ta saki,sai ta matso kusa da iman din sosai

"Kinga,ayi me baro baro kawai a wuce wajen......ki bude bakinki malama,karki cuci kanki,ki gayawa kowa kina son bassam,kuma shi kike da burin aura,ki gayawa ameen bassam kikeso kanki tsaye,idan kikace zaki tsaya kunya ko kara,to wallahi kina ji kina gani za'ayi babu ke,ni dama na dade ina zargin sonki yake,shi yasa ya tajura rahuwarki ya hanaki sakewa kamar kowacce diya,abu daya ne ya ciremin zargina da kika gayamin cewa yayanki ne.....amma Allah na tuba,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa,ki duba surarki da kyau....banda ma yiwa kai kasada me zaisa yace yana sonki a irin wannan lokacin da arziqi ya qwala muku kira?,me yake dashi da zai riqeki iman?,ina cewa makarantar da zaici gaba ma kokawa suke shi da ita da fafutukar ganin ya sameta,idan kika auri bassam.....bashi kansa ba,hatta da abokansa dana kusa dashi.....danginsa na qauye rankatakaf sun huta,amma shikenan saboda ya dankwafe rayuwarki sai yace wai yana sonki saboda cuta da mugunta,yana da kyau yana da kwarjini na daukar hankali,amma magana ta domin Allah bashi da sinadarin riqe mace kamarki.......da dinki zaici da ke?,koda karatun da bashi da tabbacin samunsa?ke rabu da gaibu fa ki kama dahir,kuma shima matuqar yana sonki ai zaiso ci gabanki ne,bawai ya aureki ku dankwafe waje daya babu ci gaba ba" ire iren maganganun munira kenan data ci gaba dayi,kamar zata ari baki.

Iman tana saurarenta tsaf,ita ba wannan bace damuwarta,babbar damuwarta soyayyar bassam da zuciyarta ta saba da ita,kuma batajin zata iya jurewa rasashi.

"Gashi inji bassam......,jiya ya aiko yaranshi ya kawo min da daddare saboda ya kikkiraki jiyan bai jiki ba,ya damu sosai,shi kansa yaron nasa idan kinga motar da yake hawa ko......hmmmm" tayi zancan sanda take fidda waya sabuwa dal tana miqa mata.

Wannan karon batayi musun karba ba,jiki a sanyaye ta amsa,saboda tana jin wannab shine lokaci mafi dacewa da su kasance tare da juna da bassam din.

Nan da nan labari wayar ya karade cikin qawaye da classmates dinta,tanajin mazan ajin suna fadan kudin wayar,mamaki ya kamata,ta jujjuya wayar a hannunta tana mamaki yadda mutum zai iya narka kudi kamar haka ya siya waya qwaya daya jal.19

Cikin jiki zuciya ruhi da kuma idanu ya tabbatar akwai matsala,irin matsalar da duk sanda zuciyarsa ta gaya masa akwaita yana qoqarin qaryata kansa da tunaninsa,komai da komai din na iman ya canza kuma ace ya janye daga muhalli da bigiren da ya santa ada,duk dacewa ba mazaunin gida bane shi.....amma kuma gaba daya iman din ta yiwa idaniyarsa qaura,ya daina ganinta,walau da safe koda dare,tamkar wasan buya ta tsiro dashi a tsakaninsu a tsanake,yasha ganin wucewarta wuf a duk sanda ta karanci motsinsa a waje ki tahowarsa izuwa wajen.

Iman din dake tiri tiri da dukkan wani abu da ya shafeshi a yanxu ba ita bace,iman din dako yaushe take shiga kokwanto da wasi wasi duk sanda wasu awanni suka shude bataji motsinsa ko gilmawarsa ba,dukka a yanzu sun kau,kwanaki biyar din da suka biyo bayan maganarsu bai sake sanyata a idanunsa ba,koda muryarta zai iya cewa baifi sau uku ya jiyota ba tsayin kwanakin.

Wata iriyar rayuwa yake a kwanakin wadda shi kansa baxaice ga inda ta dosa ba,saboda rashin gane ainihin abinda iman ke nufi,ina tasa gaba?,meye alqiblarta?, Duka bai sani ba,tarin damuwar dake danqare cikin zuciyarsa ta bayyana cikin ayyukansa na yau da kullum,ada idan gana dinka riga goma a wuni daya,a yanzu biyu yake iyayi,sauran duka tunani ya cinyeshi.

_wannan kenan_

K'arfe takwas na dare bayan kammala sallar isha'i ya shigo gidan,wanda direct daga masallaci gidan ya nufo,tunda dama can shi ba ma'abocin zaman majalissa bane,koda ya zauna din baya wuce minti goma zuwa ashirin zai sallama dasu ya wuto gida yaci gaba da sabgoginsa.


Sanda yake sanyo kai cikin gidan tare da sallama a bakisa yaga kamar wani abu ya gifta wuf zuwa daki,inna ta daga idanunta tabi iman da kallo wadda ita dince tayi hakan,cikin mamaki tana amsa sallamar amin din,ta fuskanci wasu sauye sauye sosai game da alaqar ameen din da iman,yau dinne kuma idanunta suka ganeta real,zuciyarta tadan tsinke kadan,tana fatan kada ubangiji ya sanya wata matsala ce ta afku tsakaninsu komai qanqantarta,don basa fatan hakan,saboda ko a jiya sun jima ita da malam suna tattauna batu akan aminu da iman din

"Barka da dare inna" amin ya fada cikin murmushin sannan me sanyi da akullum yake fuskantar innar dashi,fuskantar da da zai yiwa mahaifiyarsa cikin girmama a tarin ladabi.

Cikin nata salon kulawar da kuma nuna qauna ta sakar masa fara'a

"Yauwa aminullahi,sannu da qoqari,an samu shigowa?" Ta qarashe maganar tana tura masa kujerar tsuguno,sai ya zame ya zauna kan shimfidar abun sallar da iman ta tashi yanzu akai,ya zauna sosai akai ya tanqwashe qafafunsa yana gaidata kamar wanda ba tare suke gida daya ba.

Cikin kulawa ta amsa masa,sai 'yar hira ta shigo kan wajen aikin nasu,aduk sanda wata matsala ko ci gaba suka sameshi kam aikinsa,da ita yake shawara,da ita yake tattaunawa,su kashe su binne,inna takanji matsalarsa dari yayarsa dake jigawa bataji guda daya ba.

Duk wannan hirar fiye da rabin hankalin inna yana kan dakin iman,tana zuba idanu tare sa saka ran ganin fitowar iman,tana fara'a gamida nuna kulawa dayi masa sannu da zuwa,ta kuma debo abincinsa ta gabatar masa kamar yadda suka saba,sabanin haka shuru kakeji.

Hankalin inna ya dan daga kan,ranta kuma sosu,ta kasa jurewa sai data daga murya cikin sauti mai qarfi ta qwalawa iman din kira.

Kai tsaye kuwa kiran ya isa kunnuwan iman,wadda ke kwance rub da ciki kan katifarta,ta nutsa cikin duniyar chart da bassam,wanda har bata iya jin hirar dake gudana tsakanin inna da bassam dake zaune daga qofar dakinta.

Da hanzari ta danna wayar qasan pillow,tunda dama babu wanda yasan da zaman wayar,koda yaushe kuma a silent take,ta tashi da wani irin reaction na rashin gaskiya ta fito waje tana gyara daurin dankwalinta.

Tamkar batasan ya shigo gidan ba,tamkar ba dalilin shigowarsa yasa tabar tsakar gidan ba ta gaidashi,duba daya yayi mata yasan lallai mawuyacine abinda zuciyarsa keta gujewa ba shine ya afku ba,iman din dake marmarinsa a yau ita ke gaidashi babu wani doki babu komai,fara'a da ya santa da ita babu kaso casa'in cikin dari.

Da wani mugun bin qwaqwafi inna ke karantarsu gaba dayansu,saita danne tace da iman

"Wanne irin sakarcine wannan,ki wuce ki dauko masa abincinsa,kin kama kin wani qule daki?,haka kawai kin koyi nunqufurcin banza da wofi na zaman daka?,inacewa

Please Login or Register in order to submit comment