Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

ο»ΏπŸ”₯πŸ”₯ *_KUFAN WUTA_* πŸ”₯πŸ”₯


Free page 01

*TAFIYA DA GWANI ME DADI*

*ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu sababbin tsararru kuma zafafan labaransu guda biyar kamar yadda aka saba*

RAYUWAR MACE
rano

NOOR ALB
Mamuhghee

MASARAUTA
miss xoxo

BAK'AR INUWA
Billyn Abdul

KUFAN WUTA
Huguma

Zaku samu gaba daya labaran akan naira

1k kacal
2_400
3_500
4_700

*Zaku saka kudin ta wannan account din*

1487616276
BILKISU IBRAHIM MUSA
ACCESS BANK

*SAI KU TURAWA WANNAN NUMBER SHAIDAR BIYANKU*

09032345899

*KATIN MTN KUMA*

09166221261

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
_MUJE ZUWA_πŸƒπŸΎβ€β™€οΈπŸƒπŸΎβ€β™€οΈπŸƒπŸΎβ€β™€οΈπŸƒπŸΎβ€β™€οΈπŸƒπŸΎβ€β™€οΈπŸƒπŸΎβ€β™€οΈ






Dogon layi ne sosai kamar irin na kowacce unguwa ta masu matsakaicin qarfi,hagu da dama na layin gida jene a jere na masu matsakaiciyar rayuwa,wadanda basu cika mugun kyau ba,kamar yadda kuma basuyi lalacewa da rashin kyan gani ba,duk da cewa wani gidan yafi wani kyau,kamar yadda kowa da irin yadda ubangiji S W T ya tsara masa matakin rayuwar da zai wanzu a kai.

Yawancin gidajen plate ne masu soraye,masu ginin benen daga cikinsu 'yan qalilan ne,haka nan gaban gidajen akwai kwata wadda tabi ta kowanne qofar gida,saidai kuma a rufe take da slap,duk da cewa zakaga daya biyu na wani gurbi da babu slap din,gurbin dake nuni da cewa cirewa yayi ko karyewa,ko kuma an tsigeshi ne bisa qarfi da da yaji,da kuma qiriniya irin ta yara,wanda bisa dukkan alamu ma slap din an hada taro da sisi ne daga mazauna layin an ginashi.

Daga can tsakiyar qarshen layin,wanda zaka iya karya kwana ta shiga dakai wani layin daban,dandazon yarane a tsaye carko carko sunata hargowa,idan daga nesa ka taho,zaka iya hangen yadda qura take tashi a wajen,alamu dake nuna cewa fada ake sosai a wajen.

Idan ka duba tsakiyar wajen sosai,yara ne guda biyu,wadanda gaba dayansu ba zasu zarta shekara goma ba gaba dayansu,'yar baqar dirarriyar yarinyar nata qoqarin kada abokiyar fadan nata,wadda idan kayi mata kallon farko ba zaka zaci zata iya dambe haka da abokiyar fadan nata ba,kasancewar bata kai wancar garin jiki ba,fara ce ba sol ba,kana iya hangen doguwar sumar kanta me santsi yadda ta debi qasa da yashi na wajen,sakamakon cirewar danwakalin kanta,baya ga hijabinta data ci damar dashi tun daga sanda za'a fara fadan.

"Iman.....iman.....ga malam nan" wata yarinya ta qaraso wajen bayan taja birki tana haki,da alama daga wani sashen ta kwaso gudunta ta kuma tuqe a nan.

Sarai iman din ta jita,saita qara himma da hanzarin ganin ta yar da rahama kafin malam din ya qaraso,ta tabbatar matuqar bata gama ba ya qaraso fadan yazo qarshe,hakanan kuma babu makawa itace me laifi a wajen malam din,koda kuwa ta fisu gaskiya.

Saidai bata kai ga cimma burin nata ba taji tsawar malam din a kanta

Dattijon mutum,wanda a qalla shekarunsa sun tasamma hamsin,sanye da fararen kaya qal,riga 'yar ciki da wando,sai babbar riga malum malum,kansa sanye da farin rawani,hannunsa dauke da buzu daya nade wani abu a ciki,daya hannun nasa kuma yana riqene da baqar leda
"Ke hajaru,kinci gidanku!,saketa nace" Ya fada cikin kaushin murya idanunsa duka bisa yarinyar.

Tunkude rahama hajar iman tayi,ta duqa tana kwasar takalmanta da dankwalinta da suka turbude cikin qasa,ranta a bace na rashin samun damar tumurmusa rahama da batayi ba,dai dai lokacin malam ya waiwaya ga yaran yana musu fada,tare da kora kowa zuwa gida,bayan ya bude ledar hannunsa ya fidda alewa ya rarraba musu.

"Muje gida ke kuma,'yar qaniya" ya fada yana tasa qeyar iman zuwa gida,suna tafe yana mata sababi har suka isa qofar daya daga cikin gidajen dake jere a layin.

Tun daga qofar gidan zaka karanci cewa gida ne na makaranta,ma'ana gidan da ake karantar da almajirai,saboda babbar rumfar kwanon da tabarmi dake malale saman simintin dake qasan rumfar kwanon,tun daga malalen simintin,tabarmin dake shimfide din zuwa qasar dake gaban gidan a share wajen yake fesss,kai kace lomar tuwo zata fadi ka duqa ka dauka abarka kaci saboda tsabar tsabta.

Da hanzari almajiran dake zaune a wajen,wadanda basufi biyar ba suka miqe
"Sannu da zuwa malam" duka suka furta,daya daga cikinsu ya matso yana niyyar karbar ledar hannun malam din,sai ya dakatar dashi

"Yi zamanka habu....inasu haladu?" Ya jefa tambayar ga daya daga cikin mazauna wajen,wanda ya fisu girma da wayo

"Basu dawo ba tukunna,amma nasan suna hanya" kai malam din ya jinjina

"Shikenan,ku fara shirin sallar magariba,duk wanda ya dawo kada ya fita,inason ganinku gaba dayanku"

"To malam" suka amsa masa cikin girmamawa,saiya juya ya saka kai zuwa soron gidan.


Faffadan tsakar gida ne mayalwaci sosai,wanda ke dauke da bishiyar mangwaro da babu kamarta a unguwar,wata iriyar bishiya da Allah ya sanyawa albarka,me yawan fidda 'ya'ya masu dadin gaske da kusan kowa yake amfana da ita.

Dakuna biyu ne daga hannun damanka wanda suke falle daya da kuma rumfa da uwar daki,sai wasu da suke kalloka kana shigowa gidan,suma rumfa da uwar daka ne gaba dayansu,baya ga wani babban dakin falle daya dake a soron gidan.

Gab da soron gidan anan rijiyar gidan take,ma'abociyar ruwa me kyau da sanyi,wanda koda da rani ne nata qafewa,anan kusan duka 'yan unguwar ke diban ruwa idan aka shiga yanayi na rani wanda ake yawan samun qafewar rijiyoyi da kuma janyewar ruwan famfo,bandakinsu na daga can wani dan sakaye sai kitchen dake taqi kadan daga dakunansu.

Yadda qofar gidan da sorayenshi suke qal haka cikin gidan yake,komai a killace cikin tsafta a kuma muhallinsa.

Daga qofar kitchen din wata farar macace zaune saman kujera 'yar tsugono,sanye da wata jar atamfa data qara ma haskenta kyau,duka duka matar shekarunta na haihuwa zasuyi arba'in,saidai da alama ita din ma'abociyar tsafta ce da ado.

Kwando ne a gabanta wanda ke cike da alayyahu tana tsinkewa,baya ga albasa data gama yankanta tuntuni,cikin sauri sauri take aikin,da alama bata saba kaiwa dare kamar haka bata gama abincin dare ba.

Sau daya tak ta daga kai ta kalli iman wadda fa shigo tana gursheqen kuka,tabi takalmanta da ta riqo a hannu saboda tsinkewar da yayi,saita maida kanta taci gaba da aikinta,kamar ma batasan da wanzuwarta ba,abinda ya sake tunzura iman din,tayi zaman 'yan bori a waje tana aje takalman nata a gefe,tare da sake bude muryarta tana sakin kukanta.

Ko dagawa ta sake kallon iman batayi ba,saboda irin wannan koke koken da rigimar ta banza da wofi ba yau ne farau ba a wajenta,kusan kowa na gidan yasan da zaman wannan,har zuwa sanda malam yayi sallama ya shigo,sai tayi qoqarin rage sautin kukan nata,ta hau zazzare idanu.

Da malam din ya kalleta dariya ta bashi,amma saiya danne,ya maida kansa ga matarsa safiya da ake kira da inna,wanna tuni ta miqe tana masa sannu da zuwa,bayan ta ajjiye aikin da takeyi ta qaraso ta rusuna ta karbi ledar hannunsa.

"Yanzu ke hajaru.....bakya jin fada kenan ko?" Malam din ya fada yana kama kunnensa da hannu daya

"Sau nawa zan hanaki fada da yara?,.....ina cewa ko sati ba'ayi ba kukayi fada da asama'u....naja miki kunne,shine har kin manta?" Tsuru tsuru tayi tana raba idanu,tsoron yadda malam keta fiddo mata manyan idanunsa irin nata ya shigeta,takan jima har ma ta manta kafin malam yasa hannunsa ya daketa,duk ranar da ya daketa din kuwa lallai ba shakka ta qureshi ne.....kuma fa zata ji a jikinta

"Daga yau bazan sake miki magana ba,amma zan saki a mari idan baki wasa ba" ya qarashe maganar yana sakin kunnen nasa.

Inna da tuni ta koma bisa aikinta tana saurarensu,haushi sosai yake cikata kan yadda malam din bai iya zagewa ya daki iman sosai kamar yadda takeso,saida yakan gaya mata cewa,duka baya tarbiyya,kuma bashi ke gyara yaro ba,saidai ya batashi,nasiha da kuma nusarwa sune suka kamata.

Sannu da gida yayi mata kamar yadda ya saba,yana tambayarta kowa lafiya,ta amsa masa da lpy qalau,wannan kusan dabi'arsa ce,mutum ne shi managarci,wanda yake matuqar kula da iyalinsa dama buqatunsu,bakin gwagwadon ikonsa,abinci abinsha da suttura duka bai yarda sunfi qarfin iyalinsa ba,komai qanqantar abu ya daukewa gidansa,saidai duk da haka bai hana inna sana'a ba,saboda sanin muhimmancinta ga diya mace.

Gangarawa malam yayi ya daura alwala,ya maida rawaninsa yana shaidawa innar zai sake fita,bazai shigo ba sai an idar da sallar isha'i

"A dawo lafiya,Allah ya tsare" tasan ya fadi hakanne don kada ta damu da rashin gamaabincinta akan kari,shi yasa ya fita ya bata sarari don ta samu ta kammala a nutse.

Fitar malam din kamar dama jira hajar take ta sake bude baki da sabon babin kuka,abunda ya qule inna sosai,tayita qoqarin danne zuciyarta don kada ta kaiwa hajar din hannu,amma ko alamun sassauta kukan hajar batayi ba,abinda ya dinga tunzura inna kenan,taji babu makawa saita jibgi hajar din sannan zataji sassauci,don haka ta saki dambun data gama hadawa tana maidashi madambaci hawa na biyu,ta miqe a fusace.

Malam na gyara hannunsa daga qofar fita daga gidan,yana magana da wani babban dalibinsa sahabi,ya daga kansa a hankali sanda ya fara jiyo muryoyinsu,duk kuwa da cewa basu kai ga qarasowa inda yake ba,amma kuma har zuciyarsa ta tafi inda suke.

Su dinne kuwa,matasan yara su biyu ne tafe,suna jere da juna,dukkaninsu shekarunsu basu wuce sha bakwai ba,yanayin fuska da kuma yadda suke tafe cikin raha zai iya sawa mutum yace 'yan biyu ne,saidai kuma kamanni da sukayi matuqar shan bambam a tsakaninsu zaisa ka gane ba twins din bane.

Matashin farko ya dara dan uwansa fari da haske da kuma tsaho kadan,wanda idan baka da lura ma babu lallai ka gane hakan,yana da zagayayyar fuska da madaidaicin hanci mai tudu,siraran labba masu kyau da kwantaccen gashin gira,duk da cewa akwai sauran shekaru masu tarin yawa a gabansa.....amma kuma sai gashi saje ya fara fito masa sosai,alamun dake nuni da cewa mutum ne me yawan gargasa,don sumar kansa ma kawai ta nuna alamun hakan.

Wani irin idanu gareshi kamar na mai jin bacci,saidai idan kuma ya budesu sosai xaka fahimci manya ne suna da girmansu,duk da bai gama girmansa ba,amma kuma zaka fahimci shi din dogo ne,ya fito daga jinsin yaren da sukafi alaqa da fulani,yana sanye da riga t,shirt me kwala mai gajeran hannu,sai wani wandon jeans wanda ya danyi fari kadan,qila saboda yawan morarsa da yakeyi ne,saidai kana kallon jikinsa kasan gwani ne wajen tsafta,domin kuwa.....duk da wuni da yayi wajen aikinsa,hakan baisa koda karin gugarsa ya bace ba bare akai ga yin dauda,muhammad al'ameen kenan.

Saurayi na biyu shima farine,don har yafi dan uwansa fari,hakanan shima ba baya bane wajen kyau duk da cewa shima shekarun nasa basu gama bayyana komai ba,abu gudan da ya sake bambanta su....yafi dan uwan nasa garin jiki,shi kuma shadda ce a jikinsa,duk da cewa ba wata ta azo a gani bace ba,amma shima fes yake,saidai hannunsa da yayi baqi,sabida aikin gyaran mota da yake koya a wani garage,umarul farouq kenan wanda ake kira da faruku.

A ladabce dukkaninsu suka qarasa daura da malam,suna masa barka da yamma,fuskarsa fadade da fara'a,zuciyarsa kuma cike da alfahari dasu yake amsa musu da

"Yawwa.....ya wajen aikin?"
"Alhmdlh" suka amsa masa a kusan tare

"To ma sha Allah" sai suka miqe suka nufi cikin gidan,wanda al'adarsu ce kowacce rana,idan suka dawo gida lokaci irin wannan,basa shiga dakinsu dake soron,wanda shi suke fara tararwa,har sai sun shiga sun yiwa innar sannu da gida sun shaida mata dawowarsu.

A fusace inna ta ciri wayar radio dinta dake a gefanta,wadda ko awa biyu ba'ayi da kawota daga gyara ba,aikin da ya kacame mata yasa bata samu tashi ba bare ta miqa ta daki,sai tayi kan iman cikin fushi tana fadin

"Bari na dakeki da kyau.....sai kiyi kukan me dalili"

"don Allah innarmu" kalmar data ratsa kunnensa kenan,abinda ya sanyata tsaiwa cak daka dukan iman da tayi niyyar yi,ko da bata juya ba tasan waye,ba yau ta fara jin hakan daga bakinsa ba,matuqar yana gidan,matuqar kuma yana kusa baya yarda da adaketan,ya gwammace ya horata ta sassauqar hanya,amma baya qaunar a daga hannu a daketa.

Kafin innar ta gama miqewa tsaye daga durquson dukan da tayi shirin mata....tuni har ita iman din ta miqe da hanzari,ta kuma falla da gudu tayi inda alameen din yake tsaye.

Kafin ta iso ya duqa,ya kuma yiwa jikinsa garkuwa da hannyensa,saboda yasan tana zuwa din jikinsa zafa fada da shagwabar nan tata,abinda ya jima da yi mata shamaki da aikatashi,saboda yadda a kullum take qara girma,shekarunta suna daduwa.

Ilai kuwa tana zuwa abinda ta shirya yi kenan,saidai ya sanya hannayensa ya riqe nata hannuwan,ta sakar masa kuka,cikin sigar lallashi ya fara magana

"Ya isa haka.....ya isa,karki bari aga hawayenki mana" yana maganar ne tare da sanya gefan dankwalinta yana goge mata fuskarta,sannan ya miqe daha durquson da yayi ya kama hannunta suna takawa zuwa tsakar gidan.

Tsaki yaji daga bayansa,ya kuma san ba kowa bane illa sadiqu,wanda ya tabbatar da cewa zuciyarsa yayi matuqar kaiwa nesa,da kuma kara da yayi masa yau,banda haka tabbas ya sani....da tuni ya jima da kai hannu jikin iman din,kamar yadda ya saba duk sanda wani abu irin haka ta faru.

Yana riqe da hannunta har suka qarasa inda inna ke tsaye daura da qofar kitchen,ya russuna yana fadin

"Barka da gida inna" yana kuma ajjiye mata daya daga cikin baqaqen ledoji guda biyun da ya shigo dasu

"Barka kadai aminu,ya wajen aikin?"

"Alhmdlh inna"

"Ma sha Allah,Allah ya qara albarka" ta fada tana ajjiye kallonta kan Ledar da ya ajjiye ya tura gaban innar
"Alhamdulillah inna" ya amsa mata,saidai hankalinsa yana kan iman,wadda har yanzu take kumburi

"Me iman tayi inna?" Lamin ya maida dubansa ga innar bayan ya dauke idanunsa daga kan iman

Sai da innan ta tabe bakinta sannan ta ja ledar ta fara budawa kafin ta bashi amsa,amsar da tasan koda ta bashin babu abinda zai sauya zani

"Fada dai fada dai ita da yara,fadan da kuma kai da kanka sai da ka rabashi amma malam ya ganta da yaran bata haqura ba,ita ba za'a gaya mata ba taji kenan?".

Kansa ya juyar ga iman,wadda ta sake tale baki tana shirin fara wani sabon kukan

"Me yasa iman?,ina cewa ni da malam duka mun raba wannan fadan ko?" Cikin muryar dake nuni da cewa tana gab da sake sakin wani sabon kukan tace
"To ba sune ba.....da na fito sai su fara tsokanata....bayan kuma ni ban kula su ba.....wai idona irin na mage" qaramin murmushin da ya sake qawata fuskarshi ya sake,yana kuma duban qwayar idanun da take magana a kai,tabbas qwayar idanun nata dama eye lashes dinta ba irin na kowa bane,wannan yasa yara da yawa suke tsokanarta,abinda ita kuma ta tsana kenan,yake kuma yawan hadata fada da yaran,tasha sanya kuka kan a cire mata idanun a sauya mata wasu,duk saboda yadda yaran suke tsokanarta,ko kallonta inna batayi,alameen dinne yake tsayawa ya lalace bata haquri da lallaminta,tare da qoqarin yi mata bayanin cewa ba ciwo bane.


Cikin nutsuwa ya tattara hankalinsa a kanta

"Sau nawa zaance ki daina damuwa uhmm?,dukanmu muna son ganinki haka,kuma ke me kyau ce,bakiga duka kin fisu kyau bane?ke ta dabance kinji?,ki daina damuwa da abinda zasu fada" murmushi ta saka kamar kowanne lokaci idan ya yarrasheta irin haka,sai ta gyada kai tana murmushi,abinda ya sanya dimple dinta na hagu da dama lobawa,sai shima ya biye mata wajen sakin murmushin

"aminu.....an kira salla,ka tashi kayi buda baki ka rabu da wanann sakaryar" cewar inna,tana turo jug na ruwan sanyi data jefawa qanqara gabansa,waiwayowa yayi ya dauki ruwan kana ya miqe yana duban iman

"Zanje sallah na dawo...."
"Ina tsarabata?" Ta fada a shagwabe tana langwabe wuya tun kafin ya qarasa maganar da yakeyi,murmushi ya sakamar mata,shi kansa yana yaba rigima irin na iman,shi yasa babu wanda suke shiri dashi kaf gidan saishi kadai,sai kuma malam wani zubin

"Zan taho miki da ita" ya amsa mata yana shirin daga qafarsa

"Qaniyarki....ke me yasa kullum bakya hankali?"

"Idan na iso wajen saina balla mata dan yatsa,laifinsa da yake biye mata" saddiqu daya gama daura alwalarsa a bakin famfo ya fada bayan ya zubda ruwan kuskure bakin da ya guntsa,yana warware dogon hannun rigarsa tare da jefawa iman din harara kamar idanunsa zasu zazzago qasa

"Amma dai ina cewa ba da kai take ba ko?,to ba ruwanka" alamin ya fada yana watsawa saddiqun nashi idanuwan,sanda yazo gab da shi zai fice daga gidan,xuwa qofar gidan don miqawa malam kofin ruwan sanyi suyi buda bakin tare,kamar yadda suka saba,kusan dukansu suna azumin litinin da alhamis,hatta da iman qaramarsu ta fara,yau dinne kawai ya zamana shi da malam ne kawai suka samu damar yi,saddiqu yayi zazzabi na kwana biyu,bai jima da warwarewa ba,abinda ya hanashi yi kenan,ita kuma inna uzuri irin namu na mata,sai kuma iman wadda tun safe al'amin ya daure mata qarqashi kan cewa yau akwai rana,tasha ruwa abinta,ta bari sai ranar alhamis tayi,inna tayita mita har ta haqura ta sanya musu idanu,idan da sabo ta saba da wannan dabi'ar ta al'amin da iman,bama ita ba,duk wanda ya rayu dasu koda na 'yan kwanaki ne sai ya fuskanci haka.

_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

+234 818 401 7452

*Tasted and trusted*πŸ‘πŸ½πŸ‘πŸ½https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b


*FREE PAGE 02*


_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

+234 818 401 7452

*Tasted and trusted*πŸ‘πŸ½πŸ‘πŸ½
_____________________________

Basu shigo gidan ba su duka sai bayan sallar isha'i,saboda suna tsayawa daukan karatu wajen malam cikin almajiransa,hannunsa riqe da baqar leda wadda taketa maiqo dauke da awara me zafi da tasha cabbage da yaji mai uban yawa.

Dai dai lokacin da iman din ke zaune gefan tabarma tare da innarmu wadda ke lazumi bayan ta gama tata sallar,abincinta na gefe bata tabashi ba,innar tana ankare da ita amma bata kulata ba,iman din irin yaran nan ne da ko kadan basa qaunar abinci,wani lokaci har sai innar ta ajjiye madoki kusa da ita sannan zata ci abincin,wannan dalilin yasa bata da kumari ko kadan,kusan duka sa'anninta sun fita girman jiki.

Tana jin sallamar alamin ta miqe daga shirin kwanciyar da takeyi,ya qaraso gefanta ya zauna yana ajjiye mata ledar awarar,fuskarta a wadace da murmushi ta janyo ledar ta fara budawa tana cewa

"Na gode yaya alamin" shima murmushi kawai yayi ba tare daya amsa ba,suka bita da kallo sanda ta miqe zuwa kitchen,da alama plate din da zata juye awarar take nema.


Kusan lokaci daya suka dauke idanunsu shi da inna,sai innar ta ajjiyr carbin hannunta gefan daddumarta tana cewa

"Zauna aminu" sabule slippers din qafarsa yayi,ya zauna daga gefa,cikin yanayi na nutsuwa

"Me yasΓ  koda yaushe saidai ka yita biyewa shirmenta?,ta yaya ku da kuke nema ya kasance koda yaushe baka da aiki sai batar mata daa kudi?,yanzu meye laaifin daambu da bazata ci ba,saidai awara?" Murmushi ya saki kawai,sannan a nutse yace

"Inna mu din mune dolen imaan,mu ya kamata ace munyi mata daman,idan bamuyi mata ba waye zaiyi mata,kuma bata roqan kowa a waje saimu da muke yayyenta,kuma ma amfanin neman kenan inna,iman ba wani abu take tambaya ba da ya wuce dan abun marmari" kai kawai innar ta raausayar,dama tasan zaa rina indai lamin ne,wannaan ba shine karo na farko da magana irin wannan ta ratsa tsakaninsu ba,ta rasa wacce irin qauna da kulawa ce wannan da yakewa imaan din,duk da cewa sun kyautata masa matuqa da gaske,kyautatawar da duniya ma ta shaida da hakan,amma kulawar da iman ke samu daga gareshi ta musamman ce.

Koda ta matsa wajen ganin cewa ta hanashi,ko kuma ya rage tasan bata bakinta ne kawai,lamin din bazai sauya ba,a nata hasashen da ganin kamar ya kamata ya rage din,tunda ko babu komai akwai yayarsa dake aure a qauyensu,wadda wasu nauye nauye nata dana yaranta duka ya daukesu bisa wuyansa,kasancewarsa yaro jan gwarxo,mai himma qoqari da kuma neman na kansa,komai dadi komai wuya,kuma komai rintsi,kwata kwata baisan wata kalma ta lalaci,son jiki ko kuma qyuya da ganda ba,dukkan wani aiki da zai samar masa da kudi na halak yana tallafarsa,ya kuma karbeshi hannu bibbiyu yayi,babu girman kai babu ha'inci ko son jiki.

"Shikenan,Allah yayi muku jagora,yasa albarka a nemanku"

"Ameen inna...ameen" ya fada yana jin dadin addu'arta,uwa ce me yawan addu'a ga 'ya'yanta,kome qanqatar alkhairi idan sukayi,bakinta baya gajiyawa da yi musu addu'a dare da rana.

Duk sanda tayi masa addu'ar sai yaji dadi qwarai da gaske qasan ransa,ya rasa mahaifiyarsa tun hankali bai fara riskarsa ba,sai gashi Allah ya musanya masa da wata makwafinta a sanda baiyi zato ko tsammani ba,a lokacin da ya dauke haso ya kuma debe tsammani daga samun dukkan wani tattali kulawa ko kuma jin dadi,cikin tausayi da kuma jin qai na ubangiji ya hadashi da wasu kwafin na iyayensa.

Daga inda take zaune take binsu da kallo,sanda ya karbi awarar da kansa ya juye cikin farantin robar da iman din ta dauko,sannan ya zauna yana gutsutsura mata da daya da daya yana miqa mata tana ci suna hira,kallo daya xakayi musu ka tabbatar da cewa lallai akwai shaquwa me girma a tsakaninsu.

Lumshe idanunta inna tayi,bahaushe yayi gaskiya da yake cewa
"Da da da dukiya babu wanda yasan me morarsu sai Allah" ta Sauke idanunta tana tuna ranar farko da suka fara sanin lamin,ya kuma shigo rayuwarsu ya zama daya daga cikin iyalan gidan.


Malam ibrahim khalili shine cikakken sunansa,haifaffen garin maiduguri,cikakken babarbare wanda ya fito daga gida na ilimi da karatu,asalin gidansu malam khalili gida ne na malamai,da suka gaji karatu tun daga kakanninsu,malam khalili yana daya daga cikin yara uku da suka gaji mahaifinsu,duk kuwa da cewa su biyu rak mahaifiyarsu ta haifa Allah yayi mata rasuwa.

Khalili ya tashi da son karatu da kuma nema tuquru,wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya yabar maiduguri,ya shiga duniya neman karatun qur'ani dama na addini haiqan,daga gari zuwa gari,har ma wasu qasashen da muke maqwabtaka dasu.

Sosai karatu ya daukewa khalili hankali,bai samu yin aure da wuri ba,har zuwa sanda ubangiji ya nufeshi da zuwa qasar niger.



Please Login or Register in order to submit comment