Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A canne ya hadu da fatima buzuwa,tana zuwa daukan karatu makarantar wani abokinsa,yarinya ce a sannan me qwazo da kuma hazaqa,don lokacin ma ta kusa kammala haddar qur'ani,tana izifi na hamsin da biyar,tun daga baqara take rubutawa a allo ta haddace sannan ta wanke a sake yi mata qari,ta samu tarbiyya me kyau da kuma kulawa,duk da cewa mahaifinta ya rasu,amma mahaifiyarta batayi sakaci da tarbiyyarta ba,saboda ita daya Allah ya basu.

Lokaci daya soyayya da shaquwa ta shiga tsakaninsu,suka fahimci juna da kyau,manya suka shiga maganar aka tsaida maganar aure,ba dadewa suka angwance,ya kuma daukota ya taho da ita garin kano,inda anan ya bude tsangayarsa shima,yana karbar almajirai daga kowanne gari ko qasa.

Almajirancin makarantar malam khalili ba kamar sauran almjirci bane da muke gani ayanzu,wada aka watsar da duk wani mutunci da kuma kimarta a yanzu,yara suke wahala da sunan neman ilimin alqur'ani me girma,wanda sam hakan bashi da tushe bare asali sam cikin addininmu.

Dukka yaron da zai karba sai ya kasance makusancinsa ne ya kawoshi,zaa rubuta adreshinka da lambar wayar wanda ya kawoka,sunan gari dana qauyenka da kuma inda za'a iya samunka,sanna bai yarda a kawo masa yaro babu haka ziqau ba babu abinda zaici,abun kwanciya da kuma kayan baqatun yau da kullum,saboda shi din bai yarda da fita bara a makarantarsa ba,karatu aka kawo yaran shi sukeyi,yakan baka zabi idan ka soma hankali,kana da sha'awar karatun boko?,idan kana dashi zai shaidawa iyayenka ya sanyaka a makaranta,idan baka buqata kuma zaka kama sana'a ne,don bai yarda da zama babu sana'ar yi ba,saidai kowacce sana'a kake kana yinta ne bisa sanya idanunsa da kulawarsa,da kuma tabbatar da cewa sana'ar da kakeyi din bata sabawa addini da kuma al'ada ba.

Wannan dalilin ya sanya makarantarsa ta kasance mai tsari,mutane da dama sukeso kawo yaransu karatu nan wajensa,saidai duk shekara akwai adadin da yake dauka,idan suka cika kuma baya sake dauka sai wata shekarar.

Zamansa da fatima wani irin zama ne me matuqar dadi da kuma ban sha'awa,khalili wani irin mutum ne managarci,mai halaye da kuma dabi'u masu kyau,tsayyen akan harkar gidansa da kuma sauke nauyin iyalinsa,idan kaga fatima zakayi tsammanin tana auren wani me halin ne,saidai ko daya,tsabar kula da take samu ne da kuma tsaiwar mijinta wajen sauke nauyinta,babu abinda ta nema ta rasa,tana matuqar jin dadin xama dashi,kamar yadda shima yake yaba mata,yake kuma matuqar jin dadin xama daa ita,saaboda ita din macace ta gari,mai tarin biyayyawa mijinta,wadda tasan dai dai ta kuma san akasin hakan,bai taba cewa tayi ta musa ba,kamar yadda bai taba cewa ta bari taqi ji ba,Shi yasa shima yake qaunarta,da kuma qoqarin ganin ya hidimta mata iyakar iyawarsa,bata nema komai ta rasa ba cikin gidanta,cikin wannan yanayin,shekara biyu da aurensa Allah ya albarkaceta da samun haihuwar santalelen da namiji,aka sanya masa abubakar saddiq.

Daga kan saddiq tayita haife haife suna mutuwa wato WABI,makusanta da wasu cikin dangi sukayita so malam khalili ya qara aure,amma yace sam baiga dalili ba,yanajin dadin zama da matarsa,bai nema komai ya rasa ba,idanma ta hahuwa ce,kana iya haifar yaro guda daya amma ya zame maka me albarka fiye da masu tarin yaran,indai yana da rabo a haihuwa zata qara,ita kanta a sannan ta bashi dama amma yace bazaiyi ba,Cikin ikon Allah kuma sai Allah ya basu haihuwar hajar iman,haihuwar da duka fidda rai da ita,zuwan iman a daidai wannan lokacin ya janyo mata soyayya mai tarin yawa,saboda tazo a sanda basu zata ba,ta kuma zo a dai dai lokacin da suke marmari da buqatar qaramin yaron cikin gidan.

Shekarar iman daya a duniya da watanni biyar lamin ya shigo rayuwar cikin gidan a lokacin.

Yadda jama'a keta yabawa malam khalili kan yadda makaranta da kuma dalibansa suke a tsare ya sanya malaman wasu tsangayun dake unguwarsu da kuma wasu unguwannin suka shiga adawa da kuma takun saqa dashi,suke kuma matuqar jin haushinsa,ganin cewa ya fita daban da sauran malaman tsangayu,babu bautarwa ko azabatarwa ga dalibansa,kamar yadda bai yadda ya zama cima zaune me matacciyar zuciya ba,sai abinda iyayen yara suka dauko suka bashi,aah,shima kamar kowa,duk sanda ya tashi dalibansa shima yana tafiya neman kudinsa,ya dawo kuma lokacin da aka kusa sake zama ci gaba da karatu,komai nasu na tafiya a tsare ne,kana ganin dalibansa da yadda yake tafi da komai dole ya baka sha'awa.

Daren wata jumma'a ne,tana zaune tsakar gidanta daya kasance sai ita daya,sai hajar dake kwance a gefe saman wani abun shinfidarta me hade da katifa maras tudu,duk kuwa da cewa akwai motsin almajirai da hayaniyarsu daga qofar gida amma cikin gidan ba kowa,saboda babu wanda ke shigarwa malam gidansa gaba gadi don suna almajiransa,idan kaga yaro cikin gidan,to qaramine wanda shekarunsa basu wuce wanda shari'a ta wanzar da hani na shigarsa gidajen matan aure ba,tana da mai mata aike da maiyi mata wanki ana biyansa duk a cikinsu,bai yarda suyi mata aiki ba tare daya biyasu ba,saboda yace su din mutane ne suma kamar kowa.

A hankali hayaniyar tasu ta fara raguwa,da alama an gama rabon abincin dare ne,wanda ake auna cikin abincin kowa a hada,manya a cikinsu su dafa a rabawa kowa,a wani gida da suke zaune wanda yake daura da gidan malam din,gida ne da wani bawan Allah ya bayar kyauta su dinga kwana,hankalinta bai wajen sosai,yana can ga tunanin abinda ya tsaida malam da din bai dawo yadda ya saba ba,shi da saddiqu da yayi masa rakiya.


"Taho a hankali....riqeshi sadiqu" ta jiyo maganar malam din tun daga soro,abinda yasa ta ajjiye allon da take rubuta fasayakfika humullah ta maida hankalinta ga qofar shigowa gidan.

Malam dinne da sadiqu da wani dan farin yaro da bata sanshi ba,ta miqe tana masa sannu da xuwa,ya amsa hankalinsa yana kan yaron

"Maza dora ruwan zafi innar saddiqu" malam din ya fada yana tsugunnawa a gaban yaron,yana yage ragowar rigar jikinsa,da hanzarinta ta koma madafa,ta hada ragowar itacen data gama girki ta kunna ta dora masa ruwan,sannan ta dawo tsakar gidan,inda malam ke tsugunne gaban yaron yana masa sannu,sadiq na tsaye a saman kanshi yana kallonsu.

Kujera 'yar tsuguno ta jawo ta zauna,idanunta akan yaron da yake cikin hali na galabaita ta yiwa malam sannu da zuwa

"Yauwa binta" ya amsa da alamun rashi na a bace ne

"Ki duba maganin zafi don Allah idan akwai,idan ruwan yayi zafi ki juye sadiqu ya tayashi gasa jikinsa,bari naje na dawo" daga haka malam din ya miqe ya fita.

Duk yadda malam din yace tayi haka tayin,ya gasa jikinsa da kyau,sauran ta sakashi ya shiga bayi yayi wanka dashi,cikin kayan sadiqun ta zabo wasu ta bashi ya sanya,don xasuyi kai daya dashi,yana gamawa ta zuba masa abinci,ta koma ta dauki iman data tashi ta fara rigima ta fara bata nono,daga inda take din tana kallon yadda sadiqu ya sanyashi a gaba yana kallo,tun dazun shima zuciyarsa a karye take fuskarshi ta nuna hakan.

Malam ne yayi sallama,ya qarasa gaban yaron yana duban yaron daya ambata da lamin,ya bashi paracetamol din daya shigo dashi da kuma ruwan tea me zafi a leda,yace idan ya gama yasha yasha maganin,sai saddiqu ya kaishi daki ya kwanta.

https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b


Da ษ—umi-ษ—uminsa๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*๐Ÿ”ฅ
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*๐Ÿ’ฅ
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*๐Ÿ’…
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*๐Ÿ’ช
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*โคโ€๐Ÿ”ฅ
_Mamuhgee_



Guda 1๐Ÿ‘‰300
Guda 2๐Ÿ‘‰400
Guda 3๐Ÿ‘‰500
Guda 4๐Ÿ‘‰700
Guda 5๐Ÿ‘‰1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya๐Ÿ‘‡๐Ÿผ

*_09032345899_*


*KATIN MTN*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

09166221261


*_TEAM ZAFAFABIYAR๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ_*

_____________________


*KUFAN WUTA*๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ษ—ina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿค๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป_


*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ษ—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ษ—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taษ“a *Sign Up* shikenan an buษ—e account a ArewaBooks๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ˜‚.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taษ“a zata buษ—e maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buษ—e account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haษ—a ฦ™arfi da ฦ™arfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ษ—an uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buษ—e App... ฦŠin domin cigabanmu da jin daษ—inmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ฦ˜ARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ษ—in nan๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜๐Ÿฅฐ๐Ÿ˜๐Ÿ˜Š_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu๐Ÿ˜ญ๐Ÿ™๐Ÿป_*03


https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b


๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ

*ZAFAFA BIYARRRRR*


*_INGANCIN LABARAI_*

*_FASAHA NUTSUWA DA IYA SARRAFA ALQALAMI_*

*_TSARI DA TSANTSAGWARON HIKIMA_*

*_SOYAYYA MAI RATSA ZUKATA DA NARKAR DA ZUCIYA_*

*_JIGON LABARAI DA YASHA BAMBAM DA NA SAURA MAI SANYA ZUCIYA MAMAKI DA TUNANI_*

*_YIN LINQAYA CIKIN DUNIYAR LABARI KAJI KAMAR DAKAI AKEYI DA GASKE NE_*

*DUKA SAI CIKIN GAMAYYAR LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

*_ADADE ANAYI SAI GASKIYA_*

*_HIKIMA KASHIN KWANCE_*

*ABOKAN HIRA NE GA WANDA KE CIKIN KADAICI!*

*ABOKAN TAFIYA GA WANDA KE CIKIN NISHADI*

*WARWARAR MATSALA GAME NEMAN MAFITA*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*๐Ÿ”ฅ
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*๐Ÿ’ฅ
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*๐Ÿ’…
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*๐Ÿ’ช
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*โคโ€๐Ÿ”ฅ
_Mamuhgee_



Guda 1๐Ÿ‘‰300
Guda 2๐Ÿ‘‰400
Guda 3๐Ÿ‘‰500
Guda 4๐Ÿ‘‰700
Guda 5๐Ÿ‘‰1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya๐Ÿ‘‡๐Ÿผ

*_09032345899_*


*KATIN MTN*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

09166221261


*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
______________________________


Ajjiye iman inna tayi sannan ta nufi daki,ta dauko babbar tabarmar malam din da yakan zauna a kai ta shimfida masa,sannan ta gabatar masa da abinci da ruwan wanke hannu,ta zauna nesa kadan dashi tana ci gaba da shayar da iman wadda ke rigima saboda bata qoshi ba,ta sakeyi masa sannu da xuwa

"Yauwa sannu binta,ya hidima ya gida"

"Alhmdlhi" ta fada tana dan murmushi,duk data saba da irin wannan kulawar tashi,amma duk sanda ya tambaya din hakan yana mata dadi,saboda tasan cewa mata da yawa ne suke neman hakan basu samu ba

"Wannan yaron da kike gani sunansa lamin,na tsinceshi ne a can unguwar da naje nida saddiqu dubiyar abokina,abinda ya bani mamaki yaro qarami yashe gaban famfon tuqa tuqa,jikinsa duka tabo na duka,yasha ruwa yanata amansa,wadda ina tsammanin babu komai ne a cikinsa,yayimin kama da almajiri don haka na matsa kusa dashi,sai daya dan rage aman na tambayeshi sunansa da kuma inda yake,yamin bayani,ashe almajirin makarantar malam dan lami ne,sai na tuna kwanaki uku da suka wuce tabbas naji ana neman wasu cikin daliban,na tambayeshi me yakeyi to a nan,kansa tsaye ya shaida min guduwa yayi,na masa fada na kuma nemi dalilin da yasa yabar makarantarsu,shi baya jin tsoron wani abun kada ya sameshi,a yadda na fahimta tsoron malamin da makarantar yafi tsoro akan duk abinda zai sameshi,abun takaicin kudi malamin yake sanya musu duk ran laraba,kowa sai ya kawo wadan nan kudaden,idan kuma ba haka ba,zai ma yaro duka mai tsananin da zai gwammace koma ta yayane ya samo ya kawo masa,to shi kusan duk sati sai an dakeshi,saboda baya iya kawo komai,don yace bazai iya yadda sauran sukeyi ba,don cikinsu harda masu sata don kawai su kawo,lamarin ya dagamin hankali,na daukeshi na maidashi gaban malamin,duk da inajin tausayinsa,amma babu gatan da xanyi masa da ya wuce hakan,saidai abun mamaki abun takaici kuma abun haushi,sanda naje ga malamin,tunda ya tambayi waye ni ya fara yimin wani kallo,nasa ma'anar kallon,tunda sarai nasan waye malam dan lami,yana daga cikin masu adawa da tsarina,amma ni hakan bai dameni ba,burina da fatana shine kowa ya gyara,tun kafin nakai ga cewa komai ya soma dakawa lamin tsawa,tare da jifansa da miyagun sunaye da kuma kalamai,ya kuma fara hanqoran neman manya cikin dalibansa su dauke lamin su saka masa shi a mari,abinda bai jima da fita daga ciki ba,a nan na nuna masa nima ainihin xafina,na hana kowa yaxo wajen ya taba yaron,a nan malam dan lami ya tada husumar cewa dalibinsa ne,kuma babu wanda ya isa ya hanashi yi masa duk hukuncin da yaga dama,tunda a hannunsa aka danqashi,indai kuwa bazai hukunta laminu ba,saidai yabar masa makarantarsa,ya koreshi,ya kori yaron ba tare daya tsaya yaji meye zance ba,bai tsaya yaji me yaron shima zaice ba,bai kuma sanar da magabatansa ba bare susan ina yaronsu ya koma"

"Na fuskanci tijara yake ji,don haka bance komai ba na tattaro al'aminu,na wuce dashi chemist saboda yanayin ciwuka da raunin dake jikinsa na tabon bulalai da duka da kuma mari daya dade a qafarsa ya zame masa ciwo. A hanya nake tambayarsa wayeshi da kuma qauyensu,ya shaidamin shi din dan birnin kudu ne,mahaifiyarsa ta jima da rasuwa tun yana qarami,yayarsa da ita ta riqeshi har zuwa sanda ya tasa,mijin yayar yace bazai iya daukar nauyinsa ba saboda shima bashi da komai,yayarsa bata da yadda zata riqeshi saboda shi da itan duka marayu ne,hakan ya sanya mijin yayar ya kawoshi bara,ya damqa shi a hannun malam dan lami,tunda kuma ya tafi bai waiwayoshi ba,duk da cewa bai wani jima a makarantar ba,azaba ba wacce bai gani a waie malamin ba,don kusan karatun ma dana tuntuba ba wani mai yawa bane,azabar da suke sha tafi karatun yawa,wanna dalilin ya sanya na yanke shawarar kawoshi makarantata yayi karatu,zuwa sanda zai warware kuma mu nemi ita 'yar uwar tasa ko mijinta mu gaya masa inda yake a yanzu".

Kai inna ta gyada idanunta na kan lamin,zuciyarta cike da tausayinsa,tunda malam yake kawo almajirai bata taba ganin yaron da taji ya kwanta mata ba kamar lamin din,a dan awannin da yayi dasu wanda bai wuce awa daya da rabi ba,ta fuskanci nutsuwar dake tattare da yaron,komai nashi a hankali yakeyi cikin nutsuwa

"Allah ya rufa asiri,ya gyara mana xukatanmu" shine abinda inna ta fada,suka kuma fara rayuwa da lamin din,wanda cikin kwanaki biyu ya sake da sadiqu,wani irin sabo sukayi sosai dashi,saika zaci sun dade tare.

Tun farko dama aminu din bai soma kwana cikin almajirai ba,cikin dakin saddiqu suke kwana,hakanan hatta da suttura ta saddiqun yake sanyawa,kafin daga bisani malam ya bayar da kudi inna ta samo musu gwanjo masu kyau shida saddiq din,sosai sadiq ke murnar samun dan uwa,lokaci kadan lamin ya shiga jiki da zukatan su inna,saboda yarone haziqi,duk wani aiki da saddiq keyiwa inna da malam alamin din ya daukeshi,sai malam da inna na hanashi suna raba musu kowa ya dauki nasa.

Kusan tare sukayi rainon iman da inna,idan inna tana aiki tofa iman tana hannunsa,yayita tiri tiri da ita kenan,tun tana masa qyuya har ya zamana duk cikin gidan babu wanda take yarda dashi Kamar yadda take yarda da alamin,wani lokaci idan aiki ya kacamema innan idan ya dauki iman sai tayi da gaske ta korashi makaranta sannan zai tafi,sannu a hankali sai sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu,baya son kukanta,baya son abinda zai taba iman din,da a daki iman din gwara a dakeshi,koda malam ya sanyasu makaranta sai ya zamana sai ya fara kai iman sannan shi zai wuce,koda kuwa shi xaya makara,kudin break dinsa kuwa badai yaci a cikinsa ba,komai ya gani shi zai kwasowa iman din ya kawo mata,idan kaga yadda yake matan sai ka rantse da Allah ciki daya suka fito.

Kamanni ne kawai zasu tona asiri,saboda kowa a cikinsu kamanninsa daban,hasken fata ne kawai ya hadasu,tun iman na qarama ta fita daban,tana da kyan fuska qwarai da kuma yalwar suma,wadda ta gajeta daga wajen inna.

'yar lele iman take a wajen alamin tun tana da qananun shekaru,zai iya hana cikinsa ya bata,duk abinda tace tana so to matuqar yana dashi sai ya bata,idan babu kuwa zai nema mata,abinda yasa ya tashi kenan da zuciyar nema,zama da madaukin kanwa inji hausawa sukace shike kawo farin kai,tun saddiqu bashi da ra'ayi har zama da lamin ya sanya ya zama mai neman na kanshi kamar alamin din.

Kusan duk kudin daya samu wajen nemansa fiye da rabinsa siyawa iman wannan ne siya mata wancan,tun bata isa ado ba yake mata siyayyar kayan kwalliya da qyale qyale,tun malam da inna na fada,har suka fahimci a jininsa yake kulawa da iman,bazai iya dainawa ba,dole suka haqura suka sanya masa idanu,saidai innan tayi masa fada da kuma dabarar ya dinga aje wani abu saboda yayarsa,wadda a yanzu shekaru ke sake jaa nauyi na dada hawa kanta,tana kuma da buqatar taimako ko yaya ne.

Alamin shine kewa iman komai,itama duk abinda take da buqata alamin din take durafafa kanta tsaye,bata ko kallon sadiqu dan uwanta,saboda yana da zafi shi din,hakanan yanzu yanzu ba wani abu bane yakai mata bugu idan tayi ba dai dai ba,sabanin alamin.....wanda bashi da daukan zafi a kanta,hasalima yana tare duk wani abu da yasan xai bata ranta ko ya cutar da ita,idan tayi ba dai dai ba cikin ruwan sanyi zai nusasheta ya kuma gyara mata,tana kuma daukan maganarsa fiye data kowa cikin gidan.


Dinki dashi lamin yafi qwarewa,ya iya dinkin mata kamar masifa,har zuwa yanzu da yake kan shekara ta kusan goma sha shida,wannan yasa iman dake da shekaru goma sha daya cikin rayuwarta tun a sannan ta zama abun kallo,indai tayi kwalliya kowa sai ya yaba,tana da kyau sannan kuma alamin din yana fitar da ita da dinkuna sai kace wata qatuwar budurwa,don idan kaga dinkunan da take sanyawa saika tambaya waye yayi mata,sau tari idan yayi dinkuna ya samu kudi sosai,yakan je kasuwa ba tare daya gayawa kowa ba,ya samo mata atamfa falle bibbiyu masu sauqin kudi ya mata skert da riguna tsala tsala,saboda bata iya daura zani ba har yanzu,abinda yake hadata da inna kenan,kullum fama take amma har yanzu iman din bata iya ba,koda yaushe saidai ayi mata riga da skert ko kuma doguwar riga.

Idan kaga iman din saika dauka diyar wani ce,saboda bata rasa komai ba,kullum tsaf zaka ganta cikin suturu masu kyau.


Amin Abubakar haifaffen garin birnin kudu ne dake jahar jigawa,bafulatani ne uwa da uba,abinda yasa ya gaji kyau kenan shima tun quruciyarsa,tun shekarunsa basu fara nuna ba,yaro ne da tun a halittarsa Alla ya masa baiwa masu tarin yawa,yana da nutsuwa qwarai da gaske wadda ta hade masa da miskilanci,miskilancin da tun zamanin quruciya ya sanya ba kasafai zaka ganshi cikin wasanni irin na yara ba,yafi ganewa yana zaune daga gefe yana kallonsu,idan abu ya burgeshi ya saki murmushi kawai.

Kafin rasuwar mahaifiyarsa ya samu tarbiyya qwarai daga wajenta,wannan tasa ya zama wani na daban,idan yana wasu abubuwan saika dauka wani babba ne me shekaru.

Yadda malam da kuma inna suka riqeshi abune da bazai manta dashi kafatanin rayuwarsa ba,sun masa wani gini sun kuma zame masa garkuwa kuma ginshiqi cikin rayuwarsu,ya fahimci daga inna sadiq da kuma malam dukkaninsu suna qaunar iman,suna dannewa ne saboda yanayi irin na tarbiyya,shi kuma baiga abinda zaiyi ya faranta musu ba fiye da kula da abinda sukeso,hakan yasa ya sanyawa kansa bawa iman din dukkan kulawa,sannu sannu kuma sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu.

Wani lokaci har mantawa yakeyi,yakan kallo iman din a matsayin 'yar uwarsa ta jini,har sai idan wani abun ya gitta da zai sanya ya tuna cewa ba jininsa bace.


_shimfida kenan......muje zuwa_


_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

+234 818 401 7452

*Tasted and trusted*๐Ÿ‘๐Ÿฝ๐Ÿ‘๐Ÿฝ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ *KUFAN WUTA*๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ

NA

*HUGUMA*

Free page 04



*_MASOYA 'YAN QASAR NIJER,ZAKU TURA KATIN WAYA(AIRTEL/MOOV) TA WANNAN NUMBER_*

+22795166177




ย  ย ย  Zaune take saman kujera 'yar tsugunno,sanye da uniform na makarantar primary din da take zuwa,tana ta qoqarin daura takalmin sandal a qafarta,komai nata tsaf kuma fes,karin guga ya kama uniform din jikinta sosai,shaidar cewa suna samun kulawa yadda ya kamata,hatta da takalmin sandal din qafarta qyalli yake,kamar yadda farar safarta take qal kamar baa sakata.

ย  ย  ย ย  Wannan kusan duka aiki da horon lamin ne,idan baiyi mata da kansa ba,to ya riga ya koyar da ita,iman din akwai tsafta kamar yadda lamin din yake,bare ma kafin ta yiwa kanta wani abu sau daya yayi sau goma,wankinta da nashi duka suna wuyansa,kama daga uniform dinsu zuwa kayansu na zaman gida.

ย  ย  ย ย  Lamin din na tsugunne gefan kitchen yana shirya mata abinci a wani dan qaramin kwando me kyau,wanda shi da ita sukaje ta zaba ya siya mata,tana ta masa surutu yana biye mata,wanda duka akan jarrabawar common interence da zata zana ne a yau,inna na daga cikin kitchen din tana zubawa shi yana shiryawa har ya gama,dai dai sanda ta gama sanya safa da kuma warin takalmi daya,dayanne ya gagara,don haka lamin din ya qarasa wajen ya tsugunna ya kama takalmin yana daura mata,sannan ta miqe tana diban takardunta sabon pencil biro har ma da cleaner dasu sharpener da lamin din ya siya mata.

ย  ย  ย  ย ย  Suka miqe suna yiwa inna sallama,saboda lamin din ne zai kanta har can inda zasu zana jarabawar da kansa,daidai lokacin malam ya shigo

"A'ah,har kin gama shiryawa kenan,to ai Allah yasa motar bata tashi ta barki ba" malam ya fada yana danna wayarsa Tecno keypad dake hannunsa saboda yaga lokaci

"Dama ba tare zamu tafi ba,ya lamin ne zai kaini" iman ta fada tana duban malam

"A'ah,wanne irin sakarci ne wannan,ya ga motar makaranta zaki ce saidai laminu ya kaiki?,ki wuce ki shiga cikin 'yan uwanki dalibai ku tafi"

"Ai malam kada ma ka bata bakinka,babu yadda bayi dasu ba,tun jiya nake sababi,amma dole ne naja bakina na tsuke,saboda shine yake goya mata baya,wai kada ta shiga cikinsu uniform dinta ya cukurkude......sai kace tafi kowa" jin inna ta sako baki ya sanya iman ta fara narai narai da ido kamar me shirin sanya kuka tana duban lamin din,so take ya sanya baki,kada su malam su hanashi ya rakata.

ย  ย  ย ย  Zahiri ita tsoro takeji,saboda yadda taji wadanda suka gama primary wancan shekarar suke fadan wahalar jarabawar,duk da yadda lamin din ke qarfafa mata gwiwa tare da nuna mata cewa ba wani abu,suma sunyi fa,iya karatu tasan ta yishi,don a rana suna kwashe awanni masu yawa lamin din yana mata lesson,tana da matuqar qoqari da fahimta,saboda haka duk karatun da yake mata tana daukeshi,wannan dalilin ne yasa lamin din yaci burin tayi karatu mai zurfi,duk sa'ilin da suka zauna suna hira kuwa rabin maganarsa kenan,wannan abu yayi tasiri itama cikin ranta,bata da burin daya wuce ta ganta ta gama qaramar makaranta ta shiga jami'a,ta zama likita lawyer ko 'yar jarida,cikin ukun nan takeso ta zama daya.

"Malam kasan wannan shine karonta na farko da zata fita wani waje tayi jarrabawa irin wannan,rakatan kuma zai qara mata qwarin gwiwa,tunda makarantar basu hana ba malam ka bari na kaita" da qyar lamin yasha kansa ya barsu suka fice.

ย  ย  ย ย  A soron gidan ya dakata yana cewa

"Bari na tada sadiq ya rakani,tafiya bibbiyu tafi dadi"
"Yaaya,Allah bazaije ba koka tasheshi" iman ta fada tana jan tunga,sai ya waiwayo ya kalleta,taso bashi dariya yadda ta tsuke dan qaramin bakinta ta marairaice,ya fuskanci so ne batayi yaje din,don tabbas idan suka tafin tare bazai barta ta sake ba,duk kuskuren da tayi saiya taso mata da fada hantara ko kyara.

"Ina zuwa dai" ya fada yana saka kansa cikin dakinsu.

ย  ย  ย ย 

Please Login or Register in order to submit comment