Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki jima da fitowa ba?,me kika koma yi a ciki ko wutar nepa babu?" Gabanta ya fadi saboda tasan halin inna sarai,tana matuqar qoqari wajen kiyayewa duk wani abu da zaisa inna ta zargi akwai wata a qasa amma a banza,mutum ce ita me mugun kula da kuma tsantseni

"Inna kayana na fito dasu na manta zan gyara na barsu a waje" ta fada cikin marairaicewa

"Saiki wuce ki debo masa abincin" ta sake maimaitawa tana miqe qafafunta da sukeso su fara mata ciwo,dama kwana biyun daurewa kawai takeyi

"Zan fara watsa ruwa,kamar nan da minti ashirin sai a kawomin"

"To shikenan....,idan zaki hada masa ga kwadon xogale can ragowar na malam da yayi buda baki dashi saiki hada masa dashi" da to ta amsa tana nufar kitchen,saidai ranta a bace yake sosai,kawai saboda amin din innan ta sakata a gaba take mata fada,yadda innar ke nuna masa kula da tattalinsa koda yaushe ko ya sadiqu bata yi masa haka,abincinma sai an wani hada masa kulli yaumin kamar wani magidanci,rana dai daine zai shiga kitchen ya dauko da kansa yaci.

Tunda take dashi bata taba ganin aibun hakan ba sai yau,sai yau da zuciyarta ta karkata zuwa wani hanya daban ba wadda a baya take kai ba.

Kwata kwata bata qaunar su kebe da amin din baki daya,wannan shine babban dalilin da haduwarsu cikin gidan ma ta haramatata,saboda batason ya sake dauko.mata magana makamanciyar wadda yayi mata a rannan,shurunsa da rashin nemanta da baiyi ba shima a kwanakin ya sauqaqa mata dukkan wani tsoro da kuma zulumi nata,koda bata buda baki tayi magana ba tana kyautata zaton ya zuwa yanzu ya gane inda ta dosa.

Tana hada abincin tana mita qasan ranta,fuskarta a hade,hakanan bakinta yana ta motsawa,tasan yayi hakkanne kawai don ya samu damar magana da ita,kuma batajin zata sake bashi wannan damar.

Data gama hadawar saita koma daki dauko hijabinta,hasken wayarta dake alamta shigowat saqinnin bassam ya zaunar da ita,ta saki murmushi sanda ta fara bin saqonnin nasa,saita manta da aikin da zatayi ta shiga maida masa amsa.

Ya jima tsaye gaban mudubi gana sharce kansa yana kuma duban fuskarsa,kwanyarsa na masa bitar tarin maganganun dake cunkushe daga zuciyarsa zuwa bakinsa,mamakin yadda komai yake qoqarin sauyawa cikin qanqanin lokaci yakeyi.


Cikin jallabiyya ya shirya bayan ya feshe jikinsa da turarensa kamar yadda ya saba,hatta da boxer na ciki bai tsira ba,sai ya koma saman kujerar dakin ya zauna yana duba lokaci,tayi delay sosai,amma sai ya bata uzuri,kamar hadda hali da dabi'ansa yake,mutum ne shi mai yawan bada uzuri,zaiyi wuya karon farko ya kamaka da laifi,sai ya dora hannunsa saman sumarsa da har yanzu danshin ruwan dake jikinta bai bushe ba,yana shafata a hankali daga gaba zuwa baya,yana jin yadda damuwa ke sandar jiki da zuciyarsa.

Wayarsa ya maida gefe ya ajjiye yana furzar sa zazzafar iska daga bakinsa sanda yayi kiran layinta yaji busy,wani abu ya tsaya masa a maqoshi ya kuma tokare masa maqogaro,a hankali yaci gaba da shafar sumarsa yana lallashin kansa da kansa,sai ya lumshe idanunsa yana sake fitar da iska mai tsaho wai ko zata rage masa nauyin da yakeji cikin qirjinsa.


Kiran wayarsa da akayi shi ya dauke masa hankali,ya kuma zuqe yawan mintunan data dauka bata kawo masa abincin ba.

"To ba damuwa,bari zan kira idan na duba" amsar da ya bayar kenan sanda yaji motsinta,da kuma sallamarta a bakin qofa cikin zazzaqar muryarta,ya bata izinin shigowa yana qoqarin sanya wayarsa a silent,wanda kafin ya gama ya daga kansa harta ajjiye abincin ta juya

"Iman" ya qwala mata kira,ta waiwayo tana jin ba dadi a zuciyarta kan tsaidatan da yayi

"Zo ki zauna......magana zamuyi"

"Yanzu zan dawo" ta amsa masa a taqaice,saiya gyada kai lumsassun idanunsa suna zube saman fuskarta,yana ganin sauyi muraran daga iman dinsa zuwa wata iman din ta daban,ta juya da hanzarinta ta fice,cikin ranta tana jin saidai suyi maganar da wata amma ba ita iman din ba.

Amma kuma tana saka qafarta a tsakar gida inna dake fitowa daga daki ambaci sunanta

"Wai wanne irin baqin hali kika koyo imani?,wannan zobon da kika ajjiye ya gama hada sanyinsa babu mesha ba zaki kai masa ba,bawan Allah azumi yakai fa?" Kamar zata dora hannu aka ta zunduma ihu haka ta dauki jug din zobon ta nufi soron dashi,bata taba jin inama tana da qanne ba irin yau,da babu shakka saidai fa ta tura daya daga cikinsu ta samu ta dawo,domin har a jikinta tana jin bassam nacan yana jiranta,haka fa tura qofar dakin ranta a bace sallamarta a ciki,daidai sannan nepa suka kawo wuta,hasken farin qwan lantarkin dake dakin ya mamaye ko ina,ya kuma taimakawa ameen qwarai wajen ganin yanayin fuskar iman din.

Can nesa ta samu ta zauna bayan ta dire masa jug din,kanta a qasa kamar wata surukarta tace gani.

Baiko motsa ba sabda tayi maganar,sai kafeta da yayi da lumsassun idanunsa na wasu daqiqu,sannan ya miqe cikin nutsuwar nan tasa,ya taka a hankali ya rage tazarar dake tsakaninsu,a hankali ya zame saman carfet ya zauna saitinta,ta yadda zasu iya ganin juna yadda ya dace.

Dakakkiyar muryarsan nan me cike da amo na mazantaka ta fara fita,yau din cikin wani irin yanayi na sany da laushi,duk da cewa dama can ita iman din wannan amon ta saba ji daga gareshi,bai fiya kausasa mata a magana ba

"Iman.....a duniya idan akwai wanda zai fadi halayyata bayan inna da yayata to kece ta ukunsu,banajin ko sadiqu ya sanni yadda kika sanni" sai ya sanyi shuru yana sauke numfashi gami daci gaba da kallonta sannan ya dora

"Kwanaki biyar da suka shude,munyi magana dake.....na bayyana miki komai,saidai kuma har yau na kasa karantar me wannan iman din take nufi?,ina ta fuskanta?,ina ta sa gaba?iman baki sona ne?,ko ya amin din naki bai miki ba?,idan banyi miki ba iman ki fito ki gaya min,saboda ni ba baqonki bane......"ga fada maganar cike da qwarim gwiwar samun akasin abinda zuciyarsa ke raya masa,saida amsar da iman din ta bashi tayi matuqa girgizashi,ta motsa masa zuciyarsa fiye da yadda ya zata ko kuma ya tsammata......amsar da bai taba kawowa koda cikin mafarkansa zai jita daga bakin iman din ba,bai taba zaton zata iya furtata ba


"kayi haquri ya amin........bassam nakeso" ta amsa masa,tamkar dama jira take a bata wannan damar.

Dukkan wata jijiya dake kai saqo jini da kuma iska a jikinsa zuwa muhallansu sai da ta tafi hutu na sakanni,kafin ya samu nasarar zuqo numfashinsa,bayan ya tabbatar numfashin ya koma saman qirjinsa yadda ya dace,sai ya fara kokwanton duniyar zahiri ce ko ta mafarki,saboda haka yayi qarfin halin motsawa kadan

"Iman.....sake maimatawa naji". Yayi maganar sautin muryarsa na fidda wani amo wanda zai alamtawa mai sauraron da kunnensa da kuma qirjinsa ya cika da hikima cewa lallai akwai wani abu mai tsananin nauyi da yake shirin danne zuciyar da wannan sautin ya fito daga gangar jikinta......
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment