Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganin infection *


Ingantaccen maganin basir


Ingantaccen maganin gyaran nono


Ingantaccen maganin gyaran hips


Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake


Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah


Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.


Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.


Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.


Akwai zallan hadi na amarya


Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.


Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽


Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu 🤐
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐


Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽


Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌


Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉


Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
*_📲Typing_*.






*_🪁ƊINYAR MAKAHO...!🪁_*
_(Ta nuna a hannunsa)🍀_










_*UMMU MAHER(MISS GREEN ce)🍀*_




_*AREWA BOOK👉🏼*_


ƊINYAR MAKAHO:: https://arewabooks.com/book?id=6387a8e97dd221ff54205a4f






*GAWURTATTU 5🔥*
------------------------




P. 3&4




. . . . . ..ina komawa aji na tarar da Hadiza har tazo ita da wasu ƙawaye na,harara ta tayi sannan ta ce"oh ta ya sayyadi bada kanki asare kije gida kice ya faɗi".


Murmushi nayi na zauna ba tare dana ce komai ba.don daman ni ba mutum ce me yawan surutu ba,muna cikin hakan ya sayyadi ya shigo ajinmu ya yi mana ƙari.


Sosai nake kallonsa saboda yadda yace wai rayuwarsa tafi tawa muni,ni abin har mamaki yake bani?gashi dai ahaka Allah ya hore masa komai daidai gwargwado,ga mahaifiyarsa ga mahaifinsa ga ƙannensa kuma suna zaune lafiya klau,to banu wanda zaiyi tunanin aƙwai wata a ƙasa.










*_FRANCE🇫🇷🇫🇷_*


_State paris_


. . . . .ƙwance yake akan faffaɗan gadonsa wanda ya yi matuƙar haɗuwa,sosai yake bacci cikin wani kyakkyawan blanket ɗinsa,me laushi da kuma santsi baccinsa yake hankali ƙwance tamkar dai ba shida wata damuwa.


Wayarsa dake silent itace ke ta faman ruri alamar tana buƙatar taimako,tun farkawarsa ta farko yaji ƙarar wayar amman sai yaƙi ɗauka ya yi niyyar cigaba da bacci amman sai ya miƙe cikin fushi ya ɗauki wayar.

Ba tare daya duba waye ba ya ce"wani igiot ɗinne yake damuna"?.


Ya faɗi hakan cikin da ɗaga murya,shiru akayi daga cen ɓangaren ba tare da anyi magana ba,ya samu damar ɓalle bottle ɗin rigarsa kamar wanda zai yi faɗa,ya yi tsaki ya ajje wayar ya cigaba da masifarsa.

Ya shige banɗaki yana maganarsa,babu ruwansa da addu'ah ya shige haɗaɗɗan koman wankansa ya zauna aciki,ya ɗauki remote ya kunna tv ɗin dake manne ajikin kyakkyawan banɗakin,yadda kasan baza a bar duniya ba haka banɗakin yake.


Hmm wasu na cen suna fama da talauci,abinda zasuci ma yana damunsu tamkar dai Noor baiwar Allah,wasu kuma banɗakin ma tamkar babu agidan saboda langa langa za'a saka arufeshi don dai a samu wajen yin ɗahara,amman wasu sai kaga ban ɗakin tamkar ɗaki tsabar haɗuwa.


Ya Allah ka rufa mana asiri duniya da lahira amin.




Har bacci ya fara ɗaukesa ya tuna cewar yana da meeting aɗakin shugaban ƙasa,don haka ya tashi ya yi wanka,ya fito ya zauna gaban mirror tamkar wata mace.
Ya fara shafa wani lotion me mugun ƙamshi da sanyaya zuciya,Ya ɗakko cort fara da wandonta ma fari ƙal,ƴat cikin kuma baƙa ya ɗaura agogonsa me matuƙar tsada,wanda ya yi mugun toomuch da kayansa,ya taje ƙwantaccen gashin kansa tamkar na larabawa ko indiawa.




YARIMA yazeed kenan,mahaifiyarsa asalinta balarabiya ce wacce ta gaji sarauta agurin mahaifinta sarkin Masar suna da ƙarfin Sarauta da kuma mulki sosai.


Su biyune ƴaƴansa Gimbiya Zulaihat da kuma Umar Farouk,Tayi aure da mahaifin Yazeed shekara ashirin da tara kenan,ayanzu Yazeed yana da shekara ashirin da 27.


Kyakkyawane sosai Yazeed,mahaifinsa ɗan asalin Nigeria ne Kuma anan ya girma,ɗan sarautane gaba da baya kuma ayanzu shine sarki.


Kada kuga na ɓoye sunan garin da kuma sunan Masarautar nayi haka ne saboda labarin gaske ne,kuma komai yana son sirri.




Yarima Yazeed shi kaɗai ne namiji awajen mahaifinsa,sauran duk matane su goma sha ɗaya ne mata,su uku ne awajen mahaifiyarsa,daga shi dai ƙannensa ƴan biyu.


Yazeed irin yaran nanne sangartattu waɗanda duk abinda sukayi dai dai ne,hakan ya samo asaline ga mahaifinsa don yana masifar son Yazeed ɗin.


Mahaifiyar Yazeed babu ruwanta,a kullum tana nuna masa hanyar dai dai sai dai sam Yazeed baya ɗauka,baya jin magana ko kaɗan gashi yaro ƙarami amman abinda zaiyi wani babban ma bazaiyi ba.


Ga shegen miskilanci,da girman kai ba da kowa yake magana ba sai wanda yaga dama,kuma ba kowacce magana yakeyi ba,zaiyi wuya kaga yayi magana ya ƙara maimata ta,haka yake ƙannensa ƴan biyu suna matuƙar jin tsoronsa,don ma bai fiya zama a Nigeria ba kullum yana ƙasashen waje musamman ma Ƙasar France.


Don yana da kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da shugaban ƙasar France ɗin,Don Yarima Yazeed Allah ya yi masa basira da fikira,tun yana yaro yake masifar son zane zane,na gidaje dogaye da kuma maras tsayi,kai bai tsaya anan ba har zane zanen gadaje na titi masu matuƙar kyau da ƙawa.


Wanda ko su kansu turawan basu iya wannan aikin ba,Tun da Iyayen Yarima sukaga inda fikirarsa take shikkenan suka mayar da hankalinsu akan ta yaya zasuyi don suga ya cika burinsa na zama me tsara zanen gine gine.


To daya ke abin na masu dashi ne,sai ga Yarima ya cika burinsa don iyayensa sun bashi gudunmawa sosai.


Suka kaishi France acen yaje yayi karatunsa kaf,tun daga Primary,secondary,high institution,duk acen yaje yayi bai cika zuwa ba sai dole.iyayensa ke ziyartarsa don wani lokacin ma Gimbiya Zulaihat ita ce ke zuwa ta yi hutu wajen Yarima Yazeed sai tafi wata ɗaya tana cen.




To fa aɗan wannan zaman ne Mahaifiyar Yazeed ta gano wasu abubuwa dan gane da halayyar ɗan na ta.


Idan ya fice tun safe bazai dawo ba sai ƙarfe sha biyu na dare,bayan ta tambayesa bai ɓoye mata komai ba yace yaje Club ne.


Sosai hankalin Fulani Zulaihat ya tashi,ta rasa inda zata saka rayuwarta,bata taɓa tunanin irin rayuwar da ɗan ta yake ba.
Ashe yana cen wata uwa duniya yana aikata saɓon Allah,Ta nuna masa ɓacin ranta sosai.


Shi kuma Yazeed ya kasance me gudun ɓacin ran iyayensa musanma ma mahaifiyarsa don yana matuƙar ƙaunarta sosai,Har zuciyarsa ya nuna mata insha Allah ya daina zuwa.


Taji daɗi sosai da sosai,don tasan tunda yace ya daina to tabbas ya daina ɗin,don tafi kowa sanin ɗan nata yana matuƙar jin maganarta tare kuma da yi mata biyayya.


Ta baro ƙasar france cike da kewar ɗanta,tare kuma da jin daɗin jin maganarta da yayi,Tasan sarai Yazeed baya ƙarya ko zaka kashesa to tabbas gaskiyar nan zai faɗa komai ɗacinta,gashi baya shakkar kowa idan ba ita mahaifiyarsa ba,shiyasa akullum take me yi masa addu'a akan Allah yasa ya zama me sauƙaƙƙen hali.








NOOR POV






. . . . .a tare muka taho da Hadiza,muna tafiya muna hira sai ta ce"wai Don Allah Noor in tambayeki?".


Murmushi nayi sannan na ce"ina jinki"?.




"Yauwa don Allah wai aƙwai wani abune a tsakaninki da Ya sayyadi?".


Ɗan murmushi nayi sannan na ce"ikon Allah me kika gani?".


Murmushi tayi sannan ta ce"Noor kenan wallahi ni nasan aƙwai wani abu,idan ka kalli idon ya sayyadi zaka ga sonki ne ƙarara acikin zuciyarsa,kawai dai kina ɓoyewa ne ke da shi,baƙwasan mu ƴan baƙin ciku mu sani".


"Hhh kai gaskiya Hadiza kina da fassara wallahi,ni fa nace miki babu komai tsakanina dashi,ke kin sani Hadiza bani da wata aminiya kaf faɗin duniyar nan daya wuce ke,sai kuma Hafsa ƙawata ta boko,amman da aƙwai wata alaƙa da ke ce zaki fara sani,don banga amfanin ɓoye miki ba don kinga kema bakya ɓoyemin komai na ki".






"Hmm to Allah dai ya tabbatar da alkhairi, don idan ke baki ga abinda na gani ba,to ni na gani wallahi don ke daman Haka kike Noor,sai dai wai wani ya hango miki wani yana sonki amman ke sai ki kasa ganewa".


Murmushi kawai nayi don nasan,halin Hadixa aƙwai jan magana shiyasa ma nayi shiru,don ni ba mutum ce me musu ba maganar ma ba kowacce nake yi ba musamman idan abu bai shafe ni ba.


Hadiza ta ce"Noor ina son muyi wata magana dake,amman wallahi ina tsoron gaya miki don ban san yadda zaki ɗauko maganar ba".


Dafa kafaɗarta na yi sannan na ce"to Hadiza faɗi mana kinga na kusa zuwa gida,kuma nasan hankalin Umma yana kai na yanzu,don haka ki faɗi maganar taki inji"?.


Janyo ni tayi wani lungu,sannan ta zauna akan wani dandamali,hawaye na fitowa ta cikin idaniyarta sannan ta ce"Noor kaf duniyar nan ayanzu banida wanda ya kaiki Noor,saboda ke ɗin me hankalice da kuma sanin ya kamata,tun da nake dake baki taɓa bani gurguwar shawara ba,nasan kuma ayanzu ma bazaki bani shawara marar kyau ba."


Ta faɗi hakan hawaye na cigaba da ƙwaranyowa daga ƙwarmin idaniyarta.




Shiru nayi ina kallonta,sai naji duk tausayinta ya kama ni sosai,na matso kusa da ita na saka hannayena,na share mata hawayen da suka ɓata mata idanu,sannan na juyo da ita tana fuskantar fuskata muka haɗa idanu sosai sannan na ce.


"Hadiza wai bana hanaki faɗar cewa ni kaɗai ce dake aduniya ba?Allahn daya halicceki yafi kowa sonki da kuma ƙaunarki,tunda dai shine ya halicceki baya ga haka ma ga iyayenki duk araye".?




"Hmm Noor kenan kina bani mamaki wallahi?sau nawa muke wannan maganar dake?ke kanki kinfi kowa sanin iyaye na dukansu basa sona balle kuma ƙaunata,Mahaifiyata tun ina shekara biyar suka rabu ita da mahaifina,tun daga wannan lokacin rayuwata ta shiga matsanancin hali,don har yau dana ke baki wannan labarin,mahaifiyata bata taɓa nemana ba wai tana da wata ƴa,shima mahaifina dai dai da rana ɗaya bai taɓa cemin wai ga inda mahaifiyata take ba?tunda mahaifina ya yi aure ya auri Baba Hanne shikken ni na zama tamkar wata banza,don dani da banza duk ɗaya muke awajen mahaifina,babu ruwanshi da yadda nake gudanar da rayuwata,Wannan matsalar dana ke ciki Noor zata iya sanadiyyar rasa rayuwata.. . . ."




Sai ta fashe da kuka me ƙarfi.








kallonta nayi sannan na ɗago haɓarta akan tafin hannuna sannan na ce"haba Hadiza na sanki fa da haƙuri,don Allah ki daina saka damuwa aranki,ki zamo me haƙuri da addu'ah akoda yaushe,kamar yadda Ya sayyadi ya faɗamin ɗazu,mu ɗan adam muna yin kuskure wani lokacin,bamu fiya yadda da ƙaddara ba kuma alhali yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin shika shikan musulunci."


Na faɗi hakan ina kallonta.


Kukanta ta cigaba dayi sannan ta kamo hannuwa na duka biyu ta ɗora akan ƙirjinta ta fashe da kuka sannan ta ce.




"Hmm Noor halinda nake ciki duk yafi wannan Noor,idan na baki labarin abinda yake damuna sai kin girgiza ainun,sai kinyi mamakin abinda ke faruwa."


Kallonta nayi sannan na ce"haba Hadiza sai ja min rai kike kuma kinsan umma na gida tana jira na,don Allah Ki faɗamin kinsan bana son ganinki cikin damuwa".


"Noor ƙanin Matar Babana ke son lalatamin Rayuwata".


Sosai na waro idanuwa na duka a waje,tsoro duk ya kamani na kasa cewa komai saboda firgici da kuma mamakin jin hakan.




A hankali ta miƙe jikinta duk yayi sanyi sannan ta ce"Hmm Noor daman nasan zakiyi mamaki sosai,yau kusan ƙwana biyu kenan dana je gidansa ya nemeni da wannan mummunar maganar,Noor nayi mamaki kuma na tsorata sosai,ashe dukkanin hidimar da yake min ashe so yake ya fanshe abinsa."?


Ta kalleni tana hawaye.


Nima hawayen nake sosai sannan na ce"Haba Hadiza kinsan da wannan maganar amman kuma kikayi shiru kamar babu abinda ke damunki"?.


"Hmm Noor kenan,to yaya zanyi da rayuwata?wa nake dashi da zangayawa?so kike na gayawa yayarsa ƙaninta na nemana?ko kuwa so kike na faɗawa Baba na?wannene acikinsu zai yarda dani"?Noor na faɗa miki ne don ki sani kuma ki tayani da addu'ah".






"insha Allah Hadiza zan tayaki da addu'ah,kuma babu abinda zai sameki sai ikon Allah,Amman Hadiza kin faɗawa Baba Hassana kuwa"?.


"Ban faɗa mata ba Noor na rasa ta yadda zanyi in faɗa mata,don ba ƙaramin firgitani yayi ba akan cewa duk wanda na faɗawa to na zama gawa,kema na faɗa miki ne don zuciyata ta samu salama,yanzu dana faɗa miki na rage jin raɗaɗin dana keji".


"Kuka na fashe dashi sannan na ce"Hadiza me yasa xakiji tsoronsa?don yace miki zaki xama gawa?Shi daba Allah ba?Allah ne kawai yake da rai da kuma mutuwa,babu wani bawa daya isa ya kashe wata rai face da hukuncin ubangiji,don haka kada kiji tsoro ki faɗa mata Allah zai kawo mana sauƙi insha Allah,idan kuma bazaki iya faɗa mata ba to ni zanje in sameta in faɗa mata,sai a haɗashi da hukuma don idan ba haka ba,zai lalata miki rayuwarki ƙarshe kuma kiyi nadamar yin shirun."


Da sauri Hadiza ta rufemin baki sannan ta ce"Noor ki rufamin asiri don Allah,mutumin nan yana da kuɗi ba kaɗan ba koda an haɗashi da hukuma bazai kamu ba".


Saurin cire hannunta nayi daga bakina na yarfeshi gefe sannan na nuna ta cikin fushi na ce"yafi ƙarfin Allah ne?wallahi Hadiza ki tashi ki farka idan ba haka ba,zai lalata miki rayuwarki abanza da hofi,ƙarshe yace bai ma sanki ba kinga wa gari ya waya"?.








Fashewa tayi da kuka sannan ta rungumeni ta fashe da kuka me ƙarfi.


Rungume ta nayi sannan na fara shafa bayanta a hankali tamkar ƙaramar yarinya,har ta tsagaita da kukan na ta nima har yanzu kukan nake na tausayin ƙawar tawa,wato duk rayuwar da kake ciki sai kaga wani ya fika.


"Noor ki tafi gida kin bar Umma ita kaɗai,kuma bana so ki ɓoyewa Umma wannan maganar,saboda nasan Umma aƙwai ibada,kuma bayan haka ma Umma tamkar uwa na ɗauke ta,nasan zata taya ni da kai kuka wajen ubangiji."




Sallama mukayi da ita,ta kama hanyar gidansu tana tafiya tamkar wacce ƙwai ya fashewa aciki.


Nima duk jikina babu daɗi,ga matsalar dana ke ciki ga ta aminyata Hadiza,abin ya damu ƙwalƙwakwata ina ta tafiya ina sauri-sauri don inzo gida in kalli sanyin idaniya ta wato mahaifiyata,duk baƙin cikin dana ke ciki idan na kalli mahaifiyata ina jin sauƙin raɗaɗi sosai.







Na tsallaka titi na farko na taho don tsallaka na biyu sai naji. ..




da gudu Drivern ya fito daga cikin motar yayo kai na,ganin har jini ya fara ɓata wajen dana ke shima ogan nasa da sauri ya fito,yayo kai na farar cort ɗinsa ta jiƙe da jini ya ɗagani cak.da sauri suka shiga cikin motar duk hankalinsu a tashe.




General hospital suka nufa,wato aminu kano teaching hospital taimakon gaggawa aka fara bani,aka shiga dani emergency don bani taimakon gaggawa.




Zagaye kawai saurayin yake don duk hankalinsa ya tashi sosai,Wayarsa ce ta fara ruri amman bai iya ɗaga wayar ba saboda tashin hankali,tunda yaka bai taɓa buge ko da ɓera ba balle kuma mutum.


Ganin kiran ya yi yawa ne yasa ya ɗaga,daga cen ɓangaren aka fara magana.




"Haba Ahmad baka saba kaiwa haka ba?lafiya kuma har yanzu baka dawo ba"?.


"Hajiya wallahi yau ina cikin matsanancin tension ne,na shiga cikin wani hali sosai wata yarinya na buge yanzu".


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".




"Ahmad wani asibiti ne?".


Faɗa mata sunan asibitin ya yi sannan ya ajje wayar,ya zauna ya kalli rigarsa wacce duk jini ya ɓatata,hankalinsa ya ƙara tashi sosai yana addu'ar Allah yasa kada ta mutu don ta zubar da jini sosai.




Ba'a fi minti talatin ba sai ga Mahaifiyar Ahmad,duk itama hankalinta a matuƙar tashe.


Ta kalli rigar Ahmad ɗin wacce duk jini ya ɓatata,tsoro ya kamata sosai ta ce"sannu Ahmad me ya akayi hakan ta faru"?.


"Hmm Hajiya ƙaddara,da kuma rabon sai na fito daman sai da kika ce kada na fito amman yanayin aikina yasa babu yadda zanyi dole dai sai na fito hakan ta faru."


Kusan minti talatin sannan likitocin suka fito,da sauri Ahmad ya ƙarasa kusa dasu yana tambayarsu ya jikin na ta.?


Likitan ya ce"kai ne ka buge ta?".


"Eh nine na buge ta,gama ɗan sandan da muka taho dashi".




Likitan ya kalli ɗan sandan sannan ya ce"ok ka biyoni office".


Yana faɗar hakan Ahmad yabi bayansa don yaji abinda likitan zaice,gabansa sai faɗuwa yake kamar zai faɗo ƙasa.
itama Hajiyar Ahmad ɗin binsu tayi don hankalinta ya kasa ƙwanciya,yadda taga jini ajikin Ahmad to ta tabbatar da cewa wannan yarinyar idan bata mutu ba,to tabbas tasha wuya sosai.




To acen ɓangaren kuma,mahaifiyar Noor na cen duk hankalinta ya gama tashi,gashi ita ba ƙafa ba balle ta tafi nemanta.


Ta rasa yadda za tayi,daman tana da alwalarta ta yi sallarta a zaune,ta ɗaga hannayenta sama tana kuka tana roƙar ubangiji.


"Ya Allah kaga xuciyata,kaf duniyar nan daga kai sai manzonmu muhammad(S.A.W)dasahabbansa da kuma matayensu,sai ƴata Noor kaf duniyar nan bayansu sai ƴata,ina masifar sonta har cikin ƙoƙon xuciyata,Noor shekararta Shida a ciki na,ba shekara ɗaya ba har shekara shida,haka nasha wuya na haifeta ya Allah duk inda take Allah ka karemin ita da karewarka,sannan Allah ka tsaremin ita da tsarewar ka,ba wayo na ko dabara ta ba,Allah na tabbatar da ka amshi roƙo na,Ya Allah kai ne kace mu roƙeka zaka amsa mana,to Ya Allah na kawo kuka na gare ka akan rashin dawowar ƴa ta gida,Allah ka tsaremin ita Amin ya Allah".


Dai dai nan ta shafa,tana shafawa taga an ɗaga labulen ɗakinta..ta hango hasken fitilar nefa a tsakar gida,wacce ita babu wannan gatan a ɗakinta,tunda ta lalace shikkenan yau kusan shekara biyu kenan tun sanda ta fara wannan ciwon.


"Ke!".


Sai lokacin ta gane wanda ya ɗaga mata labule,Mahaifin Noor ne tsaye sai harararta yake kamar zau dake ta.


Ta daure daga wani mugun haushinsa da take ji ta ce.




"Ina yini Baban ya. . . ."


Da sauri ya dakatar da i'ta da faɗin"ke Fatima kiyi a sannu fa,rashin mutuncin da kikeyi dake da ƴarki ya fara i'sata,ya za'ayi yarinya ta fita tun rana amman har yanzu kusan ƙarfe takwas na dare bata dawo ba?ko daman haka kika koya mata?don taje yawon karuwanci ta samo miki abinda zakiyi ƙarya?don dai nasan badon yunwa ko don wani abuba,don dai kinsan gidana ba gidan yunwa bane".?


Sosai take kuka hawaye ya wanke mata fuskarta,ta tsani cin mutuncin Isma'il sam be sam mutuncin ɗan adam ba,shiyasa san bata fiya shiga hulɗarsa ba,musamman ma yanzu da ba tada lafiya.


"Ba dake nake ba?kinyi min shiru munafuka sai ana magana kiyi wani wuƙi wuƙi da idanuwa na rashin gaskiya ko?to bari kiji idan na ƙara auna minti talatin bata dawo ba,to sai ranki ya yi mummunan ɓaci,don sai kin fita kin bar min gida na".




Sosai gabanta yayi wani irin mugun bugawa,Fatima ta dafe ƙirjinta wasu hawaye masu mugun zafi suna ƙwaranyowa daga ƙwarmin idanuwanta.


Lallai rashin imani irin na Isma'il ya yi yawa,yanzu ayadda take ɗinnan idan ya kore ta ina zata je?idan ya kore ta dawa zata haɗu,mutane nagari ko akasin haka?.


Inna Saude tana ganin shigowar mijinta ta ɗaure fuska ta yo da ɗaurinta gaban goshi sannan ta ce"oh amman Isma'il kana bani mamaki?yanzu da kaje tattaunawa kukayi ko me?baka kore ta ɗin ba?shine ka dawo min nan kana wani hura hanci?".


"Ai na bata nan da wasu mintina,wallahi indai bata dawo ba korarta zanyi daga gidana don daman wallahi ta isheni,mata kamar wata musaka ita ba ƙafa ba ita ba wata mamora ba.?"






***********


Suna zama likitan ya ce"yauwa daman na kiraka ne saboda inyi maka bayanin komai,wannan yarinyar ta zubar da jini sosai,ta yadda dole ne sai anyi mata ƙarin jini,don ma jininta me ƙarfi ne sosai da an rasa rayuwarta baki ɗaya,amman Allah ya taƙaita karaya ɗaya ce a ƙafarta sai kuma ƙarin jini da za'ayi mata Leda huɗu sai wasu magunguna da zan rubuta mata yanzu."


Wasu ƴan rubuce rubuce ya yi sannan ya ɗago ya ce"yauwa to waɗan nan magungunan zaka sayo,sannsn maganar jini kuma siya zakuyi ko zaku bayar?".


Da sauri Ahmad ya ce"zan bada Leda ɗaya sai in siya guda uku ɗin".


Hajiyarsa ta ce"kai Ahmad ka siya mana?meye dalilin da za a ɗibar maka jini kuma kaima kasan ba kada lafiya"?.


"Babu komai Hajiya a ɗiba ai taimako ne,shi taimako ana yinsa ne don taimako don gyara lahirarka".




Ba don ran Hajiya yaso ba ta haƙura kawai,ta bar zancen don yanzu ba lokacin da za'a zauna ana musu bane.




8:00pm Dai dai lokacin Ya sayyadi ya sauka akan lifan ɗinsa,ya tsaya aƙofar gidan ya kasa shiga,ya samu wani yaro ya aikasa gidan ya ce.




"Kai idan ka shiga kace wai Noor tazo inji ya Sayyadinsu".


yaron ya ce"to".


Daman ɗakin Mahaifiyar Noor ne a farko,don haka kana shigowa da ɗakinta zaka fara cin karo.yaron ya shiga ɗakin ya ce"wai inji ya sayyadinsu Noor wai tazo".


Da ɗan sauri Umman Noor ta ɗago hawaye duk ya gama wanke mata fuskarta,ta ce"kai kace wai haryanzu bata dawo daga makaranta ba,nima nemanta nake yanzu."


Tana faɗar hakan ta fashe da kuka me tsanani.




Yaron yana fita ya ce"wai ance har yanxu bata dawo daga makaranta ba, mamanta ma nemanta take".




Sosai gabansa ya yi mugun faɗuwa,ya kalli yaron sosai kamar yaga hoto,ya rasa wani irin tunani zaiyi to ita Noor a ina ta tsaya ne?.


Wata dabara ce ta faɗo masa ya hau mashinsa ɗinsa,bai tsaya ko ina ba sai gidansu Hadiza don yasan duk inda Noor take to Hadiza ta sani.




Allah ya taimakesa ya sameta a ƙofar gidansu,da alama aikenta akayi ya sauka ya ƙarasa ya ƙwala mata kira don yaga ta kusa shiga gida.


Cikin tsoro ta juyo ta ce.




"a'ah ya sayyadi lfy kuwa na ganka haka"?.


"Ina fa lafiya Hadiza?ƙwarki aka nema aka rasa,shine naxo don inji ko kinsan inda take?tunda nasan aminiyarki ce kuma tare kuke tahowa".


Tunda ya fara maganar ta tsaresa da manyan idanuwanta,ta dafe ƙirjinta tana cewa"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga ɗaka ban fito ba..ɗaxu fa tare muka rabu,ta tafi gida nima na tafi wallahi tun daga nan ban ƙara sanin inda tayi ba".


Ta faɗi hakan tana fashewa da kuka sosai,jin ihunta yayi yawa ne yasa ya sayyadi ya ce"ke Hadiza shiga gida,ba kuka zakiyi ba addu'ah zakiyi".shima cikin dakiya ya faɗi hakan don bai san yana mugun son Noor ba sai yanzu.


Yanzu ta ina zai fara nemanta,ya share hawayen fuskarsa da handcachep ɗin hannunsa,sannan ya hau machine ɗinsa yabi hanyar gidansu Noor.


Ya tsallaka titi na farko ya tsallaka na biyu,sai wani tunani ya faɗi masa,ya sauka daga kan machine ɗin nasa ya gaisa da wasu samari daya gani sannan ya ce.


"Don Allah bayin Allah ɗazu bakuga wata yarinya ƴar fara ba?sanye cikin uniform ɗin makarantar islamiyya tana da ɗan matsakaicin tsayi."?


Wani daga cikinsu ya ce"haba mlm mufa tun safe muke wajen nan,tamkar masu jiran taimako nan ce majalissarmu sai dare muke tashi,kuma mutane da yawa suna zuwa wucewa,wasu mu kallesu

Please Login or Register in order to submit comment