Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dameni da masifar kallo,na lura Ahmad bai kula dashi ba sai dai ni duk ɗagowar da zanyi sai na haɗa ido dashi.


Saurayi ne kyakkyawa dashi,yana sanye cikin kayan sport.


Na juyar da fuska ta don bana son yawan kallo,amman sai naga tamkar ma shi hakan yafi mai don yafi samun damar kallon na wa.
Hmm tun daga kan jirgin jiki na ya yi wani irin mugun sanyi,saboda yadda garin yake da wani irin masifar kyau.gaskiya garin larabawa na sara masa adukkanin ƙasashe.


Kai tsaye wani gida aka kaimu,gidan me bala'in kyau ni dai kawai kusan ƙamewa na yi saboda tsoron gidan.


Haka dai muka shiga gidan,duk jikina asanyaye Umma ma da kanta na lura jikinta duk ya yi sanyi.


Muna shiga wani balaraben mutum yazo ya tare mu,na yi ta mamaki to wannan asibitine ko kuwa gida ne?.


Haka dai na daure na muka gaisa dasu.


Ahmad suka fita shi da mutumin,sai ga wata mata ta sakko daga bene ita kuma ganinta kasan bahaushiya ce,tana riƙe da hannun ƴar ta ƙarama wacce ke kama da wannan baturen daya fita,babu abinda ya banbantasu jinsi ne kawai ya banbantasu ita mace shi kuma namiji.


Da fara'arta ta ƙaraso tana mana barka sa zuwa cikin yaren Hausa,na yi mamakinta sosai duk da ba abin mamaki bane tunda kana ganinta kasan bahaushiya ce.


Matar tana da kirki sosai me suna Anty Sumayya,ƴarta kuma Basma sunanta ita ƴar asalin Nigeria ce,mijinta kuma balarabe ne mukayi ta hira da ita bayan an kaimu ɗakinmu me masifar kyau.
Su Ahmad basu daɗe ba sai gasu sun dawo.





*******


washe gari Ahmad ya koma Nigeria,bayan yayi mana bayani sosai wai ashe shi wannan balaraben babban malamine,kuma sunyi magana akan ciwon Umman shine yake faɗa masa matsalar Umma na ba ta asibiti bace,saboda duba da yadda matsalar take ashe kuwa asirinne don ƙwananmu uku ya fara bata magani,sai ga Umma na amai baƙi ƙirin,ranar duk jikina ya yi mugun yin sanyi ranar umma babu abinda taci sai ruwan zamzam da dabino.


Washe gari kuwa aka fara bata na shafawa,ana shafa mata sau uku arana ranar da muka cika ƙwana uku na yi wani mugun gani,don Umma na barci ni kuma na fito daga banɗaki na hango wani abu baƙi ƙirin ya fito ta jikinta.
Sosai na maƙale ajikin ƙofar banɗakin,ina kiran sunan Allah har na ɗanji sauƙin tsoron dana keji sannan na shigi cikin ɗakin.


Na ƙwanta a kusa da Umma na,ina ta tufa mata duk addu'ar da tazo baki na.


Na kasa barci sai juyi kawai nake,sai daga baya barci ɓarawo ya sace ni.


Sosai nake jin ihu kuma kamar muryar mahaifiyata,tana ihun kamar na murna tare da godiya ga ubangiji.


Buɗe idanuwa na nayi a hankali,tun kafin in gama buɗe idon na wa na hango abinda yasa na tashi da gudu ina ce wa.


"Umma ke ce kuwa?".


Umma ta rungumeni tana kuka tana ce wa"ni ce Noor Allah ya bani lafiya yanzu na koma kamar kowa".


Sosai na fashe da kukan murna,Umma na ce wa"haba Noor ba kuka za kiyi ba,murna ta kamata kiyi nima ina tashi sai naji jijiyoyin da suka riƙe na jiki na tamkar an saka noti an buɗe su."
Ranar ko baccin kirki ma bamuyi ba,Ammi ma bata yi barci ba wato Sumayya haka ƴaƴanta ke ce mata,ashe tana da yaranta ƴan mata biyu sai samari biyu suna ƙasar America suna karatu.


Mutuniyar kirki ce sosai,kuma aɗan zaman nan dana yi da ita,ya ƙara wayar min da kai sosai hatta man da nake shafawa na dabanne me matuƙar kyau da kuma tsada,haka ma Umma ta duk da ba tada lafiya ana shafa mata mayuka masu kyau,daman ga Umma na da kyakkyawan jiki,sai ta yi kyau tayi ƙiba sosai musamman ma yanzu da take da ƙafafunta sai dai in tsaya ina kallon Umma na ina murmushi,don irin jikin Umma na jiki ne me kyau,kuma idan mace na da irin wannan jikin za kiga ba ta tsufa da wuri.


Sai ta koma kamar ƴar budurwa,ƴar shekara 18 ko 20.


Washe gari Ahmad yazo ƙasar Masar,Ammi ta umarceni da shiga kitchen wai in girkawa ango na abinci da kai na,murmushi na yi ina me jin kunyarta na shige kitchen ɗin,tana koyamin wasu abubuwan abincinsu na Masar da kuma na Nigeria.


Ɗan zaman da nayi da ita ta koyamin abinci na sosai,da yake ba ni da wahalar ganewa sai gashi na gane ɗin kuwa don ko ayanzu na koyi abincin Masar da kuma na Nigeria yafi kala goma goma.


Ina jikin Umma na ina mata shagwaɓar wai ta ɗakkomin kayan da zan saka.murmushi tayi sannan ta ce"Hmm Allah sarki Noor ki godewa Allah da har kike da kayan da zaki saka ma,da har sai kin zauna kina zaɓen kayan da zaki saka,ni dai babu abinda zance da wannan yaron Ahmad sai dai Allah ubangiji ya saka masa da alkhairi."


Na kalle ta na ce"Umma wallahi wannan ciwon naki asiri ne,don wallahi aranar da zaki samu lafiya wani abu baƙi na gani ya fito ta jikinki."


Ɗan murmushi Umma tayi sannan ta ce"Noor kenan ke yarinya ce kuma har yanzu baki san komai arayuwa ba,wacce tayi min asirin ma zan iya nuna ta kuma sanda ma tayi abin na ganta,sai dai Allah bai bani ikon yi mata magana ba har ta aiwatar da abinda za ta aiwatar ɗin."


Da sauri na tashi zanyi magana,sai mukaji sallamar Ammi take faɗamin ai Ahmad yazo yana falonta.
Ai da sauri na tashi zan tafi wajen Ahmad ɗin,Umma na ta yimin dariya tana mamakin irin soyayyar da nake yi wa Ahmad.



Kunya ce ta kamani bayan na shiga falon,na kallesa a hankali yadda naga ya ƙara wani irin kyau,sajensa sai wani shining yake yasha jallabiya me mugun kyau da tsada irinta larabawa amman ba fara ba,ruwan golden haka take ta yi masa kyau sosai ya saka tabaron idonsa me kalar haske don kana hango cikin idonsa.


Murmushi ya yi yana kallona,yana ƙarajin wani irin son yarinyar na burgesa,don yana masifar son yaga mace me kunya ba maras kunya ba.


Sheik yana falon azaune,haka naji matarsa na faɗa masa kyakkyawan balarabe me ƙwarjini da haiba.


Na ƙarasa na tsugunna har ƙasa ina gaishesa,ya ɓata rai yana cewa"haba Noor ki daina tsugunna min kinji?har ma kina saka guiwowinki a ƙasa?ki daina haka kinji"?.ce war ya sheik duk sai naji kunya ta kamani.


Ina sanye cikin doguwar riga arabian gown,wacce tayi masifar yimin kyau ɗaya daga cikin wacce Ammi ta bani ne wato matar ya sheik.


Mu biyu aka bari afalon,Ahmad sai kallona yake wai na yi kyau sosai kamar an canja ni.


Sai dai kawai inyi murmushi,sosai Ahmad ya yi murna da sosai da samun lafiyar Umma,anan ne ma yake faɗamin wai har ya kai gaisuwa gidanmu,Babana ya ce wai sai an saka rana awajen.dom haka yanzu an saka ranar aurenmu da Ahmad wata biyar masu zuwa.


Sosai na dinga yi masa shagwaɓa har da kuka na,wai ni ban girma ba har yanzu ina 15 ban ƙarasa 16 bama.shi kuwa sai murmushi yake don shagwaɓa ta tana burgesa sosai.




*****


*Yarima Yaxeed*


. . . . . .ƙwana biyu kenan Fareeda ba ta nan,kuma bata gaya masa inda taje ɗin ba ya yi mamaki sosai don sai da ta yini ma da tafiya sannan ya san cewa ba ta nan ɗin,bayan da ya kunna CC camera ɗinsa ta gidan duka anan ne ya tabbatar da ce wa,Fareeda ba ta gidan abin ya basa mamaki sosai ya tambayi gate man suka ce masa ai ta fita da troley ɗinta tunda safe bayan ya fita.


Ya dawo kawai yana tunani to ko ta koma India ne?haka dai ya gama tunaninsa azuciyarsa ma ya ce ai gwara ta koma cen ɗin,don shi dai sam Fareeda bata cikin ransa ma don har mantawa ma yake da ɓurɓushinta.


Yana dawowa ya zauna a falo.daga shi sai doguwar rigar bacci pijamas,yana shan coffie yana kallon world news.


Ƙarar bell yaji kamar kada ya tashi sai kuma ya tashi,yana buɗewa ya tarar da ƙannensa Twins Afra da Afreen.


Afra ce me dauriya ta ƙarasa ta rungumesa tana ce wa"Bro munyi fushi da kai ko kaje ka taro mu".


Yaji daɗin zuwan ƙannensa sosai ya yi missing ɗinsu,amman saboda kada ya nuna hakan sai ya tsuke fuska,ga kuma kunyar kayan da ke jikinsa don shi arayuwarsa baya son takura ko kaɗan,ta surutu ko kuma ta yawan mutane,ya fi son yayi rayuwarsa privite babu me takura masa.
shigewarsa ɗaki ya yi,Afreen ta ce"you see ke ƴar shisshigi kinsan fa ce wa Bro baya son irin wannan amman kika wani rungumesa yanzu ai gashinan".


Afrah ta ce"to ina ruwanki?tsakanina da bro babu me shiga tsakaninmu,ƴar baƙin ciki kawai don kinga yafi sona akanki."


ɗan faɗansu suka fara wanda suka saba,ga troley ɗinsa na gefe suna ta cacar baki har Dai prince ya fito.


Tsawa ya daka musu yana ce wa"hyyyyyy!Parrot,ku yi min shiru shiyasa na ce wa Ammi kada kuzo min shine ta ce kunyi hankali ashe har yanzu kuna nan da halin Animal".


Sosai suka kama kawunansu,ya kallesu ya ce"zan tafi aiki za a kawo muku abinci".


Ya faɗi hakan a taƙaice ta fice ya barsu,ai yana fita ma suka cigaba da diramarsu abin dariya.


Ƙarshe kuma suka shirya abinsu kamar ma basu taɓa faɗa ba.


Da aka kawo musu abincin ƙin ci sukayi,sai suka tashi suka shiga kitchen suka dudduba kayan da yake madafar kusan aƙwai komai.


Tuni suka fara girkinsu,don ko da suna america su suke girkinsu da kansu,kuma wani girkin ma Ammi ke turo musu ta waya idan ta dafawa Mahaifinsu wato Sarki Abdussalam,da kanta take masa girki ba ƴan aiki take sakawa ba,kamar yadda wasu matan ke yi sai dai su saka ɗan aiki ya yi musu.
Shiyasa xa kaga wata matar babu abinda ta iya sai barci da son holewa,daga nan sai kiji me aiki ta yi wuf da megida.🫣


To ta fannin girki dai su Twins sun ƙware saboda mahaifiyarsu duk da basu wajenta bata barsu haka ba.




Suna girkin ma faɗansu sukeyi,ya daɗe da dawowa ya tsaya yana kallonsu kawai,idan yana ganin ƴan uwansa sai yaga kamar Ammi yake gani,yana masifar son ƙannensa sosai yana kuma son hira dasu amman shi sam baya son yawan magana ko wani surutu.






*GIDAN SARAUTA POV*




. . . . . . .Sarki Abdussalam ne ke xagaye a babban falonsa,kansa ya ɗauki mugun zafin da bai taɓayi ba,yana masifar son yaga ɗansa tilo akusa dashi,amman hakan ya faskara gashi masarautarsa na son ɗaukaka fiye da sauran masarauta,amman rashin ɗa namiji akusa dashi yana cutarsa sosai,don harkokinsa da dama yana son yaga ɗansa tun yana da rai ya koyi wasu abubuwan ammsn hakan ya faskara.


Bayan wannan kuma gashi takaddar da yake nema ya sameta aɗakin Sarauniya Xulaiha,sakamakon zazzaɓin da tayi jiya yaje sashenta duba ta to anan ne ya yi katari da wannan takaddar.


Sosai hankalinsa ya tashi,don ya yi mamakin samun hakan ta ɓangaren macen daya fi so yafi ƙauna,amman haka ta faru daga gare ta?tabbas ya yi mamakin hakan.


Yana cikin wannan halin sai ga Kilishi ta shigo cikin takunta na isa da taƙama,ta gaishesa sannan ta samu waje ta zauna da yake ranar ƙwananta ne.


Mace da wayo da dabara har sai da ta gano abinda ke damunsa,Sarki Abdussalam ya ƙara da ce wa"ina masifar son ganin Yarima akusa dani,amman na rasa me ƙasar France suke mai wanda mu bama yi masa.?"


Kilishi ta ɗanyi murmushi mugunta,amman bata bari ya gani ba ta ce"Hmm ni yanzu Me martaba idan nayi magana sai ya zama kamar na ɓata maka ne,ammsn maganar dana keso inyi ita kaɗaice za ta kawo warakar komai".
Ɗan kallonta Sarki ya yi don yana buƙatar shawara ayanzu,ya ce"uhm ina jinki Kilishi".


Ni daman abinda nake gani kawai shine ayi masa aure,ga ƴar ƙanwata Nasibat na sonshi,ga ƴar gidan Turaki ƙaninka duk suna sonshi me zai hana duk a haɗasu a aura masa,kaga duk abinsa idan yaga anyi masa aure har mata biyu dole ya dawo nan abadan".


"Good ideas gaskiya Kilishi kin kawo shawara."


Ya faɗi hakan yana ɗan shafa ƙwantaccen sajensa.




🫣🤫Ni Umma maher Yarima da mata biyu?anya kuwa xai yarda?to menens makomar Fareeda kuma?Uhm lallai aƙwai chaƙwalin chaƙwakiya nan gaba.
*Bayan sati ɗaya*




Noor pov




. . . . . .muna sauka a filin jirgi na dinga kallon ƙasata,na ɗan lumshe idanuwa na ina bin ko ina na airport ɗin,ina ɗan ƙwance kan kafaɗar Umma na ina kallonta,ina mamaki har yanzu ta yadda akayi Umma na ta samu lafiya?alokacin da zamu tafi tana abin tausayi yanzu kuma ta zama abar kallo,abar sha'awa don yadda tayi ƴar ƙiba ta murmure.


Ahmad na gefenmu yana kallona yana kashemin ido ɗaya,ɗan murmushi nayi ina ce wa Umma"kin ganshi ko"?.


Murmushi Umma tayi duk kunya ta isheta,tayi gaba ta barmu abaya.


Muna ƙarasowa na hango Hajiyar Ahmad da Umma suna rungume juna,na ƙarasa nima ina gaida Hajiya ta amsa tana murmushi tana sanyamin albarka.
Xaliha kuwa na gefe tana kallona irin kallon ƙasan nan,sai dai wannan kallon na yau daban yake da rannan don kallon mamaki take yimin da ƙasan idonta,ina tunanin ko ganin canjawar danayi ne yasa take yimin wannan kallon oho.?


Baki ɗaya suka rakomu gida,ko da muka shigo cikin gidan duk suna tsakar gida,Safara'u na ƙofar gida tana zance sosai abin ya bani mamaki don ganin wani lalataccen da suke tsaya dashi,wandonsa trea quater ga gashin nan har da kitso hmm rashin tarbiyya dai ƙarara.
Ko da mukazo wucewa binmu sukayi da kallo,musamman ma lalataccen saurayin Safara'u inda ya bini da ficificin idanuwansa yana kallo na kamar zai ɗakkoni.


Inna Saude kusan suman tsaye tayi tana kallon da mamaki sosai akan fuskarta,ita kuwa Inna Hafsatu sai ga ta har da kukanta wai Umma ta yafe mata.


Ranar Inna Saude har da zazzaɓi sai da tayi,mahaifina baya nan yayi tafiya ashe bayan tafiyarmu yaje ƙasar Niger ƙasarsa ta haihuwa,ƴan uwansa da mahaifansa duk suna cen.








*********




Ahmad bayan ya koma gida ya wuce wajen aiki don yana son ƙarasa wasu ayyukansa da bai ƙarasa.




"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."


Abinda Ahmad ya ce alokacin da yaga Noor da wasu mugayen ɗamammun kaya,ta yi ƙwalliya me tafiyar da hankali akan kyakkyawar fuskarta.


Tana ɗan zuƙar tabar sigari,tana rike da hannun wani saurayi fari kyakkyawa.


Kanta ko ɗanƙwali babu,kyakkyawan lallaisan gashinta awaje.


Tuni hankalin Ahmad ya yi mummunan tashi,idanuwansa sukayi wani irin mugun jajir tamkar an sanya garwashi acikinsu,wutar kishi na azalzalarsa ya kasa fitowa daga cikin motar sai jan zuciya ya ke,ya yinda yake jin wani sashe na zuciyarsa na masa zugi da ciwo,ya dafe saitin zuciyar tashi ƙwaƙwalwarsa cike da mamakin wannan abinda idaniyarsa ta gane masa.


Wai Noor ɗinsa ce haka?tare da wani ƙato?.


Da sauri ya ciro wayarsa ya fara ɗaukarsu hoto a irin motion ɗinda suke.


Ya ajje wayar yana gyara packing ɗin motarsa zai fito.


Ai sai yaga sai tashin ƙurar motarsu fuuuuu. . . . . .✍🏿





*******


Ya sayyadi bai san mun dawo ba,kai tsaye ya wuce gidansu Hadiza wai don yaji ko tana waya da ƙawarta?don yana masifar son jin muryar Noor.fushin da yayi da ita ƙwana biyu sai yaji wani irin mugun sonta da ƙaunarta duk ya shigesa,ga wani irin mugun haushin Ahmad da yake ji don gani yake tamkar Ahmad ɗin na son rabasa da muradin ransa wato Noor.


A ƙofar gidansu ya tsaya amman bai samu damar ƙarasawa ciki ba,gashi ya rasa yaron da zai tura don ma wani sa'in yana shiga gidansu Hadizan don yana koyawa ƙannenta karatu.


Don haka ya shiga a hankali sallama ɗauke a bakinsa,da yake ɗakin Hadiza na farko ya ɗsn hango hasken fitila,amman sai yake jiyo wani irin abu kamar ƙara ƙara kaɗan.


Sosai tsoro ya bayyana akan fuskarsa,ƙaddara na cewa ya buɗe aƙwai abinda ke faruwa.




Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.


Abinda ya ganine yasa shi yin gefe yana kiran sunan Allah,kansa na masa wani irin mugun juyawa hajijiya na son ɗibarsa. . . . . . .✍🏿






Hmm ikon Allah kome ya sayyadi ya gani oho?sai dai da alama abin ya girgiza ƙwaƙwalwarsa har da ta masu karatu.




Hmm cigaban duk sai a littafi na biyu,shin Yarima zai yarda ya auri mata har uku?




'Hmm shin Ahmad Noor ya gani ko ba ita bace?




'Shin waye Al'amin ɗin da ya koyawa Fatima shaye shaye?meye makomar rayuwarta?.




shin Ya sayyadi me ya gani?




amsoshinku duk suna littafi na biyu,ku biyo alƙalamina ni Ummu maher ta yadda zan ja alƙalamina wajen rubuta dukkanin amsoshinku.




Wannan littafin ya faru a gaske,don haka babu abinda na canja sai sunaye.




Kina son acigaba da wannan tafiyar dake?kuma ki amshi littafinki complete kina iya biyan kuɗinki tun yanzu naira ɗari uku kacal don more cigaba da karanta wannan daddaɗan littafin na wa.ga hanyar biyan kuɗin👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻💓




*Ga tsarin yanda biyan yake*


_Guda d'aya 300_


_Guda biyu 500_


_Guda Ukku 700_


_Guda hudu 800_


_Guda Biyar 1k_




Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.


0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK




Shaidar biya ta nan


0810 433 5144


Masu turo kati MTN ta wannan number.


0702 616 6536


Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.


0706 860 6171


Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu.




_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*




_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*




_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*


_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*


_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*






Miss green ce🫵🏾✍🏿🍀💓 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment