Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaka nema awaje na in kasa ba ka shi,in dai Noor ce na baka ita amman yana da kyau ka tuntuɓi mahaifinta duk abinda ya ce to ni bani da ja akan hakan,sannan kuma ka nemi amincewar Noor idan har ta amince maka to tabbas Noor ta zama ta ka".


Ɗan murmushin jin daɗi ya yi,don yasan indai ta ɓangaren Noor ne ba shida matsala don tuni har sun ƙulla alaƙarsu a ɓoye don haka ba kowa ne yasan da hakan ba.


Ahmad ya ce"Umma na gode sosai da kulawa Allah ubangiji ya ƙara miki lafiya,kuma insha Allah zan gayawa Hajiyata da kuma ƙanin mahaifina duk yadda mukayi,daga bisani sai aturo nan wajen Baba ayi maganar".


Ɗan murmushin jin daɗi Umma ta yi,don bata shakku ko kaɗan akan Ahmad don tasan ba zai taɓa cutar mata da Noor ɗinta ba ko da kuwa bayan ranta ne.


Bayan sunyi sallama da umma yana fitowa yaga Noor a bakin ƙofar ɗakin,ita da wata mata sai hira suke abin ya bashi mamaki sosai don bai ɗauka Noor ta iya labari haka ba.


Daga bayanta taji ana magana Ahmad ya ce"to sannu uwar surutu aku me magana"?.


Da sauri Noor ta yi ɗaki tana dariya cike da kunyarsa.





Bayan Ahmad ya koma gida ya faɗawa Hajiyarsa duk halin da ake ciki,Hajiyarsa ta ce"kai masha Allah naji daɗi sosai da wannan maganar da kazo min da ita,yarinyar arziƙi me son mutane haka ma mahafiyarta Allah dai yasa muga wannan rana".


"Amin".


Ahmad ya ce yana fito da wata dalleliyar sabuwar waya dal aƙwalinta,ya ce"Hajiyata wannan wayar ta yi kyau kuwa"?.


Murmushi ta yi sannan ta ce"kai amman ta yi kyau wallahi,kamar shigen wayar da ka siyowa Zaliha ko"?.


Murmushi ya yi sannan ya ce"eh Umma duk iri ɗaya ce wayar kawai dai design ne ba ɗaya ba,Daman Noor nake son bawa wannan wayar kinga yanzu zasuyi wannan tafiyar kuma kinga idan babu waya babu yadda za ayi mu dinga gaisawa,duk da farko tare zamuje amman inason yau ba sai gobe ba zan tambayi mahaifinta akan wannan tafiyar don inji me zai ce"?.


Hajiya ta ce"eh haka ne Ahmad yana da kyau ka tambaya ɗin ka ga sai muji ko?"




Har wajen sana'ar mahaifina Ahmad yaje,wato sana'ar zamam majalissa wacce ke gefen layinmu don mahaifina baya sana ar komai yanzu sai dai sana'ar zaman majalissa.


Ko daya samesa shi kaɗai ne awajen,babu kowa masu sana'a duk dun tafi ƴan malaman makaranta ma duk sun tafi,sai mahaifina shi kaɗai ne ba shida sana'ar kansa.


Kai tsaye ya amsawa Ahmad buƙatar daya zo da ita,sannan ya ce"kawai ya turo don ganin kuɗi tingis a hannunsa don rabonda ya riƙe wasu kuɗi masu kauri tun zamanin kasuwancinsa.


Kai tsaye yana dawowa gida ɗakin Saude ya nufa.


Fatima ƴar wajen Inna Hafsatu na ganin aljihun Babansu acike ta yi wuf ta faɗa ɗakin mahaifiyarta,wadda ta sameta tana ƙwaɗawa ƙannenta tuwo da manja da yaji.


Jikin Fatima na tsuma ta fara maganar kamar haka.


"Inna wallahi ki tashi ma ki bar wannan ƙwaɗon,ga Baba cen na ga ya shigo ya yi ɗakin Inna Saude da sauri kuma wallahi kamar kuɗi na gano maƙudai".


Banza tayi da Fatima daman yanxu suka gama faɗa wai akan taƙi ɗaukar talla,wai ita yanzu ta girma don haka ba za tayi talla ba.


Ganin mahaifiyarta tayi shiru yasa ta ce"to shikkenan Inna wallahi Inna Saude ita kaɗai zata cinye kuɗin,don kinsanta da haɗama da baba kere da kuma cin rabon mutane."


Jin hakan yasa Inna Hafsatu juyowa sannan ta tashi ta fita,kai tsaye ta laɓe a labulen ɗakin sai taji Inna Saude na ce wa.


"A'i kuwa wallahi ko zanyi yawo tsirara bazan bari wannan yarinyar tayi aure tabar ƴaƴa na wata ƙwaila da ita,kuma naga har yanzu ko sha shida bata rufe ba,gani da ƴaƴa ye masu shekara talatin waɗanda ke gaba na muna jerawa,yo ba gwara yazo in masa gwanjon wata a cikinsu ba?to wallahi tun wuri ma ka gaya masa baza ka basa ƴarka ba,yazo nan gasu nan ya zaɓa ko ƴaƴan Hafsatu ban yarda ya zaɓi wasu ciki ba,don ita na ta tana samu ta aurar dasu ko da kuwa a ƙauye ne amman ni nawa a ƙauyen ma sun kasa shiga kamar waɗanda aka yiwa asiri ko kuma baki".?


Shiru mahaifina ya yi,tamkar wata uwarsa haka yake nutsuwa idan tana magana ko uwarsa dake Niger Lanta baya mata biyayya kamar yadda yakewa Saude.


Warce kuɗin hannun Mijin na ta tayi sannan ta ce"bani kuɗin nan bazan bar maka su a hannunka ba,kaje ka rabawa ƴan zaman majalissa ba bani su aƙwai abinyi akansu,saura kuma ka gayawa Hafsatu don babu ubanda zai ci kuɗinnan sai ni da ƴaƴa na."


Ta fai hakan tana irga kuɗin,dubu hamsin ne cif cif tana ayyanawa aranta wannan kuɗin,kyauta ma ya bawa mijinta ina ga kuɗin aure ma?ai wallahi baxa ta yarda ya auri Noor ba,don tasan idan ya aure ta ai ta huta ita da uwarta wacce ta tsana kamar mutuwarta,tabbas da za'a bata bindiga to kai tsaye sai ta kashe Fatima wato mahaifiyar Noor don yadda ta yi mata muguwar tsana.








Da gudu Inna Hafsatu ta shige ɗakin,ta wafto kuɗin da sauri tana watsa mata wasu ta ƙwashi rabonta sannan ta ce"wallahi ke dai Saude kinyi asarar rayuwarki,ko da yake daman bakin uwa na kanki sai dai ace Allah ya shiryar dake,kuma baki isa ki hana auren Noor da wannan yaron ba,muguwa kawai me baƙar aniya insha Allah ƙarshenki ba zaiyi kyau ba."


Tana faɗar hakan ta fice don ta ɗibi rabonta,abinda ta ɗauka ma yafi dubu ashirin don sun tasamma dubu talatin.


A'i kuwa Inna Saude sai ta haukace tana zage zage,tayo hanyar ɗakin Inna Hafsatu wai za ta amshi kuɗinta.




Inna Hafsatu irin ƙarfafan matan nanne don haka ta ce"wallahi tallahi kika shigomin ɗaki wallahi sai na karyaki na karya banza".


Inna Saude kuwa irin matan nanne sirara babu tsayi babu ƙiba saboda sabar saka masifa aransu sai kiga duk sun zama abin tausayi.


Zagi dai Inna Hafsatu ta sashi,don har uwarta dake kabari sai da ta zaga akan kuɗin da ta ɗauke mata.


Amman fa sai dai xagin babu kataɓus,don sunsha dambe ita da Inna Hafsatu kuma tasan halinta ba tada imani ko kaɗan,don tsaf za ta zaune akanta daman ga ta duk ƙashi.




Hmm mata mu gane wani abu guda ɗaya,ba wai cin abinci ke sa ƙiba ba wallahi ƙwanciyar hankaline,idan har kila zamo masifaffiya jarababbiya wallahi bazaki taɓa yin ƙiba ba sai dai ki yi ta tsotsewa ki zama taɓarya a shiga ɗaura miki zani.


Ranar dai anyi ruwan masifa agidan Mlm Isma'il,sau biyu Inna Saude na neman ta faɗa ɗakin Inna Hafsatu wai sai ta ɗakko kuɗinta,ita kuma Inna Hafsatu sai ta biyo ta da gudu,ta falfala da gudun tsiya ta ɓuya bayan Mlm Isma'il,don duk abinda suke yana kallonsu don shi ba mutum ne me faɗa ba,sai kuma abin ya haɗu da asiri sai ya zama Salamatu don kome zasuyi a gabansa bai iya magana sai dai ya yi tagumi yana kallonsu,ko kuma ya yi gaba abinsa zuwa zaman banza majalisa.
******


washe gari aka sallamemu daga asibiti,Ahmad yazo yau ma ya yi kyaunsa cikin farin yadin boyel me masifar kyau,irin me ɗan sharashara ɗinnan me adon siga siga kana ganinsa kasn me tsada ne don ba kowa zai sa irinsa.


Fatarsa ta ƙwanta sosai alamar tana samun gyara yadda ya kamata.

Kuma kafin yazo Umma ta yi min bayanin komai,kunya ta isheni na tabbatar lallai Ahmd ba shida kunya ashe har ya samu Umma da maganar?shiyasa ko da yazo yanzu na hau ɓoye fuska ta saboda nasan abin ai da kunya.


Sabuwar waya fil ya bani me masifar kyau,sosai nake juyata a hannuna saboda mamakin wai yau ni ce da waya haka?wacce ko a mafarki ban taɓa tunanin samunta ba?.


Da kansa ya zauna ya fara koyamin komai duk yadda zanyi.


Umma ma ta taya ni gode masa,da kansa ya ɗakkomu ya dawo damu gida ya tsaya ya siyi mana kayan abinci sosai komai sai da ya siya mana,muna ta yi mai godiya don Ahmad mutunne me mutunci.
A ƙofar gida muka tarar da majalisar su Babanmu,na kalleshi sosai ya ƙara zuƙewa sai fari da hanci da kuma idanuwa.


Azuciyata na ce"Hmm tashin hankali ma a'i ba zai bar mutum ya yi ƙiba ba,don Babanmu yana cikin wani hali sosai sai dai ayimai fatan samun lfy.


Ace ƴar ka ta ƙwanta a sibiti amman ka kasa zuwa ko da duba ta?a'i ko da matanka basu je ba a'i kai kaje ko?.


Har ƙasa na tsugunna na gaishesu sannan ni da Ahmad muka riƙo Umma muka shigo da ita gidan.


Mahaifina sai kallonmu yake tamkar wasu baƙi,kai tsaye muka shiga gidan,ɗakin mahaifiyata a hangame kamar ma sun shiga ɗakin,don gashinan duk an bincika kayan ɗakin.


Rai na ya sosu sosai,na kawar da kai don ko gaishe dasu Inna Saude dake tsakar gida banyi ba,don da alama ba a zaman lfy agidan don na ga kowa harkarsa yake,Ita Inna Hafsatu tana zaune da ƴaƴanta suna tsince shinkafa,ita kuma Inna Saude sun ƙure Radio suna jin garaya ita dasu Halima da Aisha guzumayen ƴaƴanta.


Don Halima shekararta talatin da biyu,ita kuma Aisha talatin cif cif sai dai kullum kaga sun tara taron yara ƴan iska,don ba auren ke kawosu ba zuwa suke don su ƙwashi rabonsu suyi gaba.


Aishar ce ma ta kula da shigowarmu don ni kaɗaice yanzu Ahmad iya soro ya tsaya,na goyo Umma na abaya har zuwa ɗakinta,sai kuwa Aishar ta ce.


"Inye ikon Allah,Ah lallai kin ƙaro wulaƙanci ƴar nan?au yanzu ko sallama babu haka zaki shigo mana gida da wata guzumar uwarki me mataccen jiki ashine zaki shigo mana gida?saboda yanzu kina ganin kanki ɗaya da kowa tunda me kuɗi na sonki?".


Ban kula ta ba,har sai dana dangana da ɗakin namu,na ƙwantar da Umma a hankali na ɗan karkaɗe wajen sannan na fito zuwa wajen Ahmad wanda ke soro.


Kallon gidanmu kawai yake har rufin ɗakin,yana mamakin yadda akayi gida ƙato gashi har yana son faɗuwa?ina zuwa na kallesa ina murmushi sannan na ce"yaya lafiya kuwa"?.


Murmushi ya yi sannan ya ce"a'ah babu komai wallahi ya Umman?".


Na ce"lafiyarta klau".


Hannu ya saka acikin aljihunsa ya ciro wata farar ta kadda,wacce ke manne ba zaka gane abinda ke cikinta ba?.


Ya miƙomin na amsa ina ɗan dubawa.


"Aishatu Noor ki kaiwa Umma kice inji ni,kuma tafiyarmu dai kin san jibi ne?don haka sai a fara shiri ko?munyi maganar da Baba."


Nan dai muka cigaba da ƴar hira,ban wani daɗe ba na dawo na yiwa Umma murmushi sannan na fara gyara ɗakin,na gyara ɗakin tsaf tsaf don daman ɗakin babu komai siminti ne kawai sai wata ƴar yaloluwar katifa don itama katifar wan Umma ne ya bata ta gidansa da ta lalace don da ita muke ɗan maneji".





A ranar Umma ta takuramin sai dana je gidansu,ma'ana gidan da aka riƙeta don bawan Allahn daya tsinceta Allah ya yi masa rasuwa sai matarsa yanzu kuma ra ɗan tsufa,sai dai har yanzu ba ta son Umma na ko kaɗan,Umma ke matsamin zuwa wajenta amman na tsani zuwa tunda ba ta son Umma na.


Kai tsaye gidan na ta na yi,gida an gyarasa ya yu tsaf tunda yanzu ɗanta ya yi kuɗi,amman sam baya taimakawa Umma na ɗan kuɗin daya ke biya na makaranta kullum naje sai an gama cin zarafina sannan za'a bani shi,Allah sarki duniya zumuncin yanzu ya yi ƙaranci sai kaga ɗan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya amman baya taimakonka sai dai ƴaƴansu da kuma matayensu.


A babban falonta na samesu ita da jikokinta,amman ƴan ƙananan tana haɗa musu kayansu da alama ma gida zasu koma.?


Ko dana gaisheta bata amsa ba,balle ma ta ɗago idanuwanta ta kalleni sai naji duk rai na ya ɓaci.


Amman sai na tuno da nasihar da Umma ke yimin a kullum,musamman ma idan za ta aikoni gudan nasu takan cemin,Noor ita rayuwarnan haƙuri akeyi ko Allahn daya haliccemu haƙuri yake damu,badon haƙuri ba da tuni an taɓar damu saboda yawan saɓon da muke dashi.


Kai tsaye na fara gaya mata abinda ya kawoni,akan tafiyarmu ƙasar Masar da zamuyi.



Sai alokacin ta ɗago idanu tana kallona sosai har taso ma ta ɗan bani tsoro. . . . . .✍🏿
Sai naji tana ce wa"ke ni sa'ar wasanki ce da zaki dinga gaya min zancen banza?uban wa uwar taki take dashi da zai kaita har Masar"?.


Bance mata komai na tashi tsaye,sai ta bini da kallo don ganin irin ƴar ƙibar dana yi da kuma ƙara kyau.


Sannan hijabin dana saka cikin hijaban da Ahmad ya siyomin ne,masu kyau tana ta ƙaremin kallo sannan na ce"Gaskiya ne ba tada kowa amman tana da Allah."


Ina faɗar hakan na fito abina zuwa gidansu Zainab,daga nan kuma inje gidansu Hadiza.


Ina shiga gidan na su na yi ta sallama naji babu kowa,sai na hango ɗakin Fatima a buɗe don haka na ƙara sautin sallama ta ina shiga cikin ɗakin.


Sosai na zaro ido na tsoro ina salati tare da ɗaga hannaye na zuwa kai na ina kuka. . . . . . .✍🏿




*Hmm kome Noor ta gani Oho sai a next page zamuji abinda ya faru?*.




#Miss green ce#🫵🏾✍🏿🍀








*Bazan ga ƙaunar da kuke nunamin ba,har sai kun taya ni da share da kuma comments me ratsa zuciya,ina alfahari da masoyana aduk inda kuke.*




Masu yimin copy na littafi,kuna ɗorawa amadadin ku kukayi,babu komai bazanyi Allah ya ida ba,sai dai in gode muku don na san duk cikin love ne,amman aji tsoron Allah🙏🏼🙏🏼🙏🏼.


_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*




_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*




_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*


_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*


_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*


*Ga tsarin yanda biyan yake*


_Guda d'aya 300_


_Guda biyu 500_


_Guda Ukku 700_


_Guda hudu 800_


_Guda Biyar 1k_




Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.


0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK




Shaidar biya ta nan


0810 433 5144


Masu turo kati MTN ta wannan number.


0702 616 6536


Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.


0706 860 6171


Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu.




*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...


Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.


Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?


"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.


08179523215




*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.


*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽


*ingantaccen maganin infection *


Ingantaccen maganin basir


Ingantaccen maganin gyaran nono


Ingantaccen maganin gyaran hips


Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake


Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah


Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.


Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.


Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.


Akwai zallan hadi na amarya


Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.


Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽


Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu 🤐
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐


Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽


Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌


Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉


Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.




*_📲Typing_*.






*_🪁ƊINYAR MAKAHO...!🪁_*
_(Ta nuna a hannunsa)🍀_










_*UMMU MAHER(MISS GREEN ce)🍀*_


_AREWA BOOK👉🏼_
ƊINYAR MAKAHO:: https://arewabooks.com/book?id=6387a8e97dd221ff54205a4f






*GAWURTATTU 5🔥*
------------------------





P. 19&20




.............."Fatima me ya sameki haka?innalillahi wa inna ilaihi raji'un".na faɗi hakan ina kuka na ƙarasa kusa da Fatiman na rungume ta kamar zan komar da ita cikin cikina.


Ina kuka na fara ce wa"shaye shaye Fatima?waye ya koya miki?me yasa kika lalata rayuwarki"?.duk alokaci ɗaya nake mata wannab tambayoyin?amman nasan baza ta amsamin ba?tunda baki ɗaya tasha ta bugu.


Da ƙer Fatimar ta fara magana tana ce wa"wa. . .wa. . .wa. . .wallahiiii Al'amin ne ya koya min,kuma kinsan ni inasonshi don haka bazanƙi bin umarninsa ba".da sauri na saka hannu a baki na kukana yana cigaba da ƙarfi.


"Fatima wani Al'amin ɗin?Al'amin Saraki dai da aka rabaki dashi ashe baki rabu dashi ba?haba Fatima me yasa kike son zama marajin maganane?meye amfanin cigaba da hulɗa da Al'amin yaronda bai ganin kan kowa da gashi amman ke dashi kike hulɗa?don Allah Fatima ki rufawa kanki asiri kada ya ɓata miki rayuwarki".


Kallona tayi da idanuwanta wanda ya kaɗa ya yu jawur,sannan ta fara magana kamar haka.


"No. .No. . .Noor ki tayani da addu'ah bazan iya rabuwa dashi ba,zan iya rabuwa da kowa saboda dashi don Allah Fatima kada ki faɗawa Ummana,yanzu kinga ta yi tafiya Baba kuma sai dare zai dawo shiyasa na ƙwaye yanzu kafin ya dawo".


Kuka na fashe mata dashi,don yanzu Fatima ta xama abin tausayi,Al'amin da Fatima ta tsaneshi ada ko kallonsa ba ta sonyi?tun tana ficiciyarta yake bibiyarta amman bai taɓa samun albarka ma ayi masa magana ba?kamar aikin asiri?.


Ni kaɗai nake ta faɗa azuciyata,na kasa fitowa daga gidan har sai da bacci ya ɗauketa,na lulluɓe ta sannan na tarkata ƙwalaben na juye su a leda sannan na fito na rufe musu gidan.


Kai tsaye gidansu Hadiza na wuce,na saka ƙwalaben acikin rami dake hanyar gidansu Hadiza,har yanzu zuciyata babu daɗi,wayo ita rayuwa haka take?kuma kowa da irin ƙaddararsa lallai Fatima tana cikin jarrabawa me girma.


A tsakar gida ta samu Hadiza tana tulun uban kayan wanke wanke,Inna Lami ba ta nan don haka na taya ta wanke wanken,ta kalleni sannan ta ce"Allah Noor kina cikin damuwa amman kinƙi Faɗamin,bayan tafiyar da zakuyi aƙwai abinda yake damunki ko?".


Sunkuyar da kaina nayi,ina tunanin faɗa mata a halin dana tsinci Fatima,duk da nasan wacece Hadiza ba tada maganar ma da har za ta faɗawa wani sannan na ce.


"Hadiza Fatima ta tana cikin wani hali,shaye shaye na same ta tana yi kuma duk a silar Al'amin Sarki?."


Hadiza ta saka salati sannan ta ce"Noor Al'amin so yake sai ya lalata Fatima sannan zaiji daɗi?shi wai don ubansa yana da kuɗi sai ya dinga abinda yake so?,wai me yasa yanzu mutane suka mayar da kuɗi kamar ado ne?sai kiga mutum wai don yana da kuɗi yana abinda ransa ke so?kamar yanzu ni Noor ƙanin Inna Lami dake son lalatamin rayuwata,addu'ar dana dage yi da ita ƙwana biyu shiyasa ko gidan nan baya zuwa".


Rai na ne naji ya yi ɗanyi min sanyi sannan na ce"A'i gwara dama ya daina zuwa don wannan ba ƙaramar annoba bace acikin Al'umma ba".


Haka dai mukayi ta hirarmu har na fito daga cikin gidan.


Washe gari da asubar fari muka tashi,don Ahmad ya ce min bazamu tafi da kaya ko ɗaya ba.


Sai dai wani tashin hankalin da muka faɗa wai Baba na ya ce bazamu je ba.


Sosai hankalina ya tashi,Inna Saude na ta yin Murna don har da yu mana habaici ni da Umma na.


Na rushe da kuka me mugun ƙarfi,Umma na rarrashi na itama tana kuka a haka har Ahmad yazo ya samemu.


Sosai shima hankalinsa ya tashi,har sai da ya kira Hajiyarsa awaya taxo sannan aka kashe case ɗin,bayan ta cikasu da kuɗi don ta gane mutanen sunfi gane yaren kuɗi akan yaren Nasiha.




Ai kuwa sai ga mahaifina har da adawo lafiya,su Inna Saude har soro aka biyomu ana mana adawo lafiya,ni abin ma dariya ya bani mutane babu tsoron Allah?sai tsoron kuɗi?.


Har filin jirgi Hajiyar Ahmad ta biyomu ita da Zaliha.sai dai ni abinda yake bani mamaki da wannan Xalihar bai wuce yadda take min wani irin kallo ba?kamar dai ta sannine awani zamani daya shuɗe,kuma a wannan zamanin babu rabuwar arziƙi acikinsa don kallon ƙasan idon ya yi yawa.


Sai dai nima ban wani damu ba,tunda Hajiyar Ahmad ɗin na so na,shima Ahmad ɗin na nuna sona da kuma ƙauna ta.to kuma banga abinda zai dagulamin ƙwalwa ta ba.


Sosai naji tsoron jirgi,don kuwa ko afili ban taɓa ganin jirgi ba sai dai a tv itama sai dai in gani a gidan wasu ba dai a namu gidan ba.


Jikina har wani kakkarwa yake saboda tsoro.Ahmad ne akusa dani ya kalleni sosai sannan ya ce"kada kiji tsoro kinji?babu komai acikin jirgi sai alkhairi don haka kada ma kiji wani tsoron komai babu abinda zai faru insha Allah,kuma Insha Allah Ummanmu da ƙafarta za ta dawo kada ki damu."


Ɗan murmushi na yi sai kuma na saki jikina,na kalli Umma wacce aka saka mata wani abu don tare ta,sai na hango hawaye akan fuskarta itama tana kallona amman kuma tana ɗan murmushi.




Tunda muka shiga wani

Please Login or Register in order to submit comment