Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi uwa an biyota tazauna akan kujera daidai Mama tafito daga dakinta ganin Gwaggo taso tafirgita saikuma tace “lafiya Gwaggo da asuban nan” kallon banza tamata tace “lafiyan ce takawo haka” tabe baki Mama tayi tawuce tashiga kitchen abinta bata wani jima afalon ba saiga Babatareda Yayansu kafinma ya gaisheta hannu tamikamai tace “bani kudin sadakinta” dan kallonta yayi da mamaki yace “Gwaggo dama zan cika kudi ne namata kayan daki” cikeda daga murya tace “bakaji ance yanzu anan gidansu zasu zauna ba baa gama gidanshi ba lokacin daya gama gidanshi anemo wani kudin amata kayan daki” zama kawai Baba yayi yana kallon mahaifiyar tashi ganin haka yasa tace “ko baraka bani bane”? Ahankali yace “zan baki mana Gwaggo amman mezakiyi dahar dubu dari biyu gabadaya” cikeda ihu tace “yoo gyaran Amarya mana dudda ma babu wani lokaci mai tsawo yau kwana hudu yarage atafi da ita gidan mijinta amman dai abinda zanyi kenan” Mama dake tsaye cikin kitchen tanajinsu ahankali tace “fitinanniyan tsohuwa inama tamutu ahuta” kallon Yayan su Samira Baba yayi yace “jeka kawo kudaden nan adakina Auwal” tashi Auwal yayi yawuce dakin Baba baijimaba yafito da bandir na yan 1k guda biyu yakawoma Gwaggo yage takardan guda tayi sannan takalli Auwal din tace “kaine Babban jikana kaito ga dubu biyu sadaka kasama Auren kanwarka albarka” gudun fitina yasa yasa hannu yakarba yace “Allah basu zaman lpy” kwalama su Samira kira tayi tace “nasan kuna jina to kuzo nan” kaman munafukai suka fito suka gaida Baba da Gwaggo dake kallonsu tace “nasan kunsan kaddaran daya fada kan kanwarku Lujain, koma baku sani nasan farfesan uwar ku tariga ta fesa muku labarin daga tushe zuwa iri to yanzu dai Alhamdulillah Allah yabata miji nagari son kowa kin wanda yarasa da ake cewa bazata taba samin wanda zai sotaba da wannan kiban babu kalan gorin da baku mata ba to yanzu dai ga sa’an datayi dan haka nan sadakin tane zan muku sadakan dubu dai dai duk ku sanya mata albarka” dubu dai dai tazaro tabasu amsa sukayi kowannensu yace “Allah sanya alheri” tace Ameen, sannan takalli Baba tace “kake kallona kokaima nabaka ne” girgixamata kai yayi tace “bari naje namata abincin kari zan fita anjima, da daddare tarinka amai inhar naji jikinta da zafi zaka kaita asibiti” Gwaggo na maganan tana daga zaninta tana tura kudaden a cikin lalita tawuce tafita tana kaiwa dakin akan dadduma taga Lujain din tai salla takifa kanta akafa tana kuka hararanta Gwaggo tayi tace “aisaikiyi” kitchen tashiga tahau dumamata shinkafan jin kukan kuma taji takasa daurewa fitowa yayi tashiga uwardakan zama tayi agabanta tabuga tagumi tana kallonta tace “wai Lujain saikin kasheni tatas kinga bana numfashi zakiji dadi iyye? Yanzu mikikeso fadamin”? Ahankali batare data da go kanta daga kafanta ba tace “ni banason Auren nan ban isa aure ba kumani Mandawari nikeso” shiru Gwaggo tayi tana kallonta saikuma tace “kikace baki isa aure ba inace nannan Aisha har ajinku ta Islamiyya dake shekaru sha shidda tai aure har anko saida kika tasani agaba namata, su Zainab ma dake sha bakwai ba suna zana jarabawan gama sakandire aka musu aure ba kema inda rashin lafiya yabarki kinfara makaranta da wuri da yanzu kin tsufa da gama sakandire, kawayenki kadai yan layin nan dasukai aure sunkai hudu yanzu da akazo kanki ne zakice baki isa aureba, shikuma Mandawarin yasan ki? Yasan dake? Yamasan sunanki? Ke yarnan ki kiyayi kanki da auran calamburuti ina gayamiki barinma Mandawarin nan mai kamada shaidanu har kitso yakema gashin kanshi” sosai take kuka still bata dago kanta ba tace “wlh shiba shaidani bane Gwaggo yanada kirki, yana bada taimako har gidan marayu yake zuwa, yarabama guraguma keke” Haba Gwaggo takama tace “to akace miki shi kadaine mai kirkin duniya” tai maganan tanajan hanci jin kauri natashi tace “nashigesu wannan yarinya tasa na babbaka abinci” tai maganan tana fita daga kitchen da sauri kashe rishon tayi dan arisho take girki tadawo zama tayi kusada Lujain din ahankali tadagota tace “haba Yar jikata Yar lukutata Yar bulbul Yar kyakkyawa yimin murmushi ingani” ashagwabe hawaye na gangarowa daga idanubta tamakema Gwaggo kafada irin baratayiba, washe baki Gwaggo tayi tace “naji to zan miki abinda kikeso” dasauri tace “zaki raba Auren ki nema mini Mandawari”? Gyadamata kai Gwaggo tayi wani kalan murmushi tayi dayasa dimples dinta suka lotsa tai bala’in kyau tawani rungume Gwaggo Gwaggo na dariya tace “to jekiyi wanka nima fita zanyi amman bari nafara hada abincin ki” tashi tayi tawuce bayi tsaf Gwaggo tahada mata abincin kari da shayi wani green towel ta daura tazo ta zauna tafaraci Gwaggo tadauki mayafi tace “tonatafi kiyi zamanki adaki kada kije konan da chan kinji” gyadama Gwaggo kai tayi.
Tun safen nan sai wuraren 4 na yamma Gwaggo ta dawo da buhu buhu na itace da saiwowi saikuma zabi kaji da tantabaru da aka hadesu aka kullemusu kafafu, wasu yara takira tasa suka yanka mata aka gyara tafito dasu karfi da yaji sukazo suna aiki Gwaggo tun tana yarinya tayi gadon iya hada magunguna lafiyayyun tsumi tayi anan tsakar gida akan ittace daya hada da zuma da mazankwaila babu suga ko digi, sai farfesun su zabin datayi na magungunan hada su Samira tayi da Lujain din duk sukaci sannan tashiga hada farfesun jijjibi wasu magunguna kuma ta shanyasu, sai wajajen shadaya suka gama komi su Samira suka koma dakinsu itada Lujain suka koma dakinsu tsumi tazuba cikin kofi tabama Lujain tasha sannan tahada mata wani ruwan zafin wasu itace data dafa, Lujain dake zaune tana kallon cartoon a falo tanashan tsumin kadan kadan tace “Gwaggo wai magungunan menene” batare da Gwaggo takalleta ba tana saka farfesun daban daban datayi dasuka jera a robobi a dankareren freezer ta tace “shawara tamiki yawa baki gankiba Saura kadan kizama zabiya tsabagen haskenki” yatsine fuska tayi tana gyara daurin towel dake jikinta tun Gwaggo namata mitan tawul harta barta dan bata taba ganin mutumin daya tsani kayaba irin Lujain.
Gwaggo bata kara mata maganan auren ba sai uban magungunan datake loda mata na safe daban na rana daban na dare daban, ita dakeson yogurt saida Gwaggo tasa tasani yogurt sabida yanda take zubamata garin magana a yogurt din daban daban.
****

Yau Friday tun ranan Monday bayan an daura auren nan dasuna shigowa gidan Abee yawuce dakinshi dagudu rabon kowa dayaganshi ko masallaci baya fita, Ya kulle dakinshi baya karban abinci yanda za’a kawo abinci a ijiye gaban dakin haka zaa dawo adauka, shigowa gidan Musty yayi afalo ya zauna yana kallon yanda Hajiya dakowa yay jugum ahankali yace “har yanzu bai fitoba Hajiya”? Wani kalan ijiyan zuciya Hajiya ta sauke tace “ai inhar ciwon nan yatashi saikuma yanda tayu, har yanzu likitan nashi”? Ahankali Musty yace “gashinan zuwa Ibraheem yadaukoshi daga airport” shiru dakin yasakeyi babu wanda keda walwala Kausar da Abdallah yakalla sun bashi tausayi yauma basuje makaranta ba, jin karan gate yasa Musty yaleka yace “Alhamdulillah gasunan” Dr na shigowa falon baima tsaya gaidasu ba yace “give me his room key” ciro key Hajiya tayi daga Yar purse na hannunta yawuce sama kowa na zaune akasa, kusan 30min yayi aciki sannan yasauko kowa tashi tsaye yayi yana jiran abinda zaice dan murmushi Dr yayi yace “ku kwantar da hankalinku he is fine” ajiyan zuciya kowa yayi, Mustafa dake kallonshi yace “Dr maisa yake kulle kanshi yaki fitowa duk yanda Imran yakaiga son bautan Allah jam’i baya wuceshi zakaga hatta masallacin baya fita yaje, yaranshi dayakeso baya yarda yagansu baya ganin kowa, why is it like that”? Ahankali Dr yace “kasan patient nawa aka rasa to PTSD post traumatic stress disorder? I applaud Imran bakaramin jarumi bane mai kwazoba he’s fighting it with all of his strength, PTSD nakama mutum ne Idan mutum yay experiencing a shocking event, mutuwan matarshi, yanda akai hanging nata sun harbeta a goshi, aka kashe yaranshi in cold blood shine abinda yasa PTSD yakamashi, symptoms nashi shine magrine, da mutum ya tsani kanshi yayita bama kanshi laifi akan abinda yafaru, mutum yay isolating kanshi daga mutane kaman yanda yake yanzu dasauransu irinsu rashin yawanyin magana, gashinan gashinan ne, for 13yrs I’ve been managing him da little medication su Anti depression dakuma psychotherapy, yana zuwa har office dina he talks to me I talk him out of all the guilt the experience dakomi dayake feeling, for a long time now kusan shekara daya kenan baitasomai ba sai ranan Monday din nan shima sabida wannan dan he’s traumatized sabida kazafin da akamai aka kuma yada aduniya yanar gizo, saikuma this sudden Marraige, Auren nan dan gani yake he’s betraying his late wife, yanzu dai I assure you komi yazo karahe, Hajiya inason kije kiyi magana dashi but before then dukku zazzauna inason magana daku gabaki daya” zama dukansu sukayi shima Doctor yazauna yace “all abinda patient na PTSD ke bukata is love and support from close family nasu and friend, ku nunamai kuna sonshi he means a lot to you, sannan kununamai ku bama kusan yana ciwo ba koyanada wani ciwoba duk randa yabude kofan nan dakanshi yafito kuyi mu’amala dashi kaman bakumasan yashiga daki ya kulle kanshi na kusan kwana biyarba baci basha kungane”? Dasauri kowa yace “eh” Dr yace “sannan karkumai kuka, don’t show him pity rather show them love, idan yaga kuna nunamai pity kunamai kuka zaiyi worsen condition nashine dan he will feel yana causing muku pain, karku nunamai kowani abu instaed ma zai iya idan yafito kuce mai babu kaza kaza kaza agida, Abee inada assignment kaza kaza kungane engage him in something life moves on” yakalli Hajiya yace “idan kinje dakin nan ba danki mai lafiya ke magana ba, ba Imran dinki zakigani ba, this one is Imran mara lafiya, PTSD mess with brain Hajiya, so no matter mezaiyi don’t show weakness kokuma kiyi kuka agabanshi, as his mother handle him kaman jariri tell me kinasonshi he’s your everything, sannan idan kin shiga dakin daidai da hasken screen na wayanki kada kisake ki kunna bayason haske bayason hayaniya bayason kuka at this time cus all of that nakara tunamai da traumatic experience na lokacin memory nadawo mishi fresh, idan tadade adakin ku aikamata da abinci kar wanda yashiga dakin abakin kofa zaku ajiye kutafi, babu abinci acikinshi sannan he’s dehydrated, ga weakness kungane” atare duk sukace to, Hajiya share hawayen fuskanta tayi tass sannan tawuce sama, Dr yabi kowa na dakin dasukai jugum da kallo yace “he is fine nan da 24hrs that’s idan yamakai kenan ya warware” yay maganan yana bama Ibraheem prescription sheet yace “he needs this drugs now kuje kusayo” tashi Musty yayi yakarbi takardan a hannun Ibro yace “bari naje nasayo kai Ibro drop Dr at home tunda ba mota a hannunshi” suka fita tare.
EPISODE 1️⃣3️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Parking yayi awajen parking nacikin gidan, yakai kusan 5min zaune acikin motan ya jinginar da kanshi tareda lumshe idanu sannan yatashi yabude kofan motan yafito ahankali da Maigadin yafaracin karo da shima idanunshi yay ja sai kallon Abee yake kaman yauya fara ganinshi, dauke kanshi Abee yayi, laptop dinshi ya dauka yamaida kofan motan yarufe sannan yay cikin gidan da sallama chan kasa yabude kofan Babban falonsu yashiga kowa na zaune falon harda Zainab dayasan takoma gidanta kaman gidan da akai mutuwa duk suna kallonshi ga Hajiya ita tabuga tagumi itama kallonshi take, ahankali yace “ina wuni Hajiya” batare daya jira amsanta ba yawuce stairs dasaurinshi dan baimason wani magana yana zuwa yabude dakinshi yashiga ciki, zama yayi ahankali bakin kujeranshi yacire takalminshi da safan kafanshi kafin yatashi yamike tsaye ahankali yake tafiya zuwa bakin gado gently ya kwanta akan gadon tareda fuzar da ajiyan zuciya ya lumshe ido ahankali yanajin kaman zazzabi na neman kamashi, knocking kofarshi da akayi yasa ya runtse idanunshi da karfi yabudesu ahankali batare dayay magana ba, muryan Kausar yaji ahankali tace “Abee” tashi zaune yayi da sauri yakalli kofan anatse yace “come in” bude kofan dakin akayi Kausar yagani tareda Abdallah idanunsu sunyi jaa suna tsaye gaban dakin duk suna kallonshi dawasu kalan disturbing eyes, wani abu yaji ya tsayamai azuciya amman yadaure batare da wani abu yanuna akan fuskanshi yace “kushigo” Kausar tafara shigowa da gudu tana zuwa batai wata wata ba kneeling tayi akasan gaban gadon gabanshi kawai tafada jikinshi tasa kanta akirjin ta rungumeshi ta kulle hannayenta ta bayanshi ta kankameshi sosai tawani kalan fashe da kuka duk duniyan nan batada abinda takeso kaman babanta, ahankali Abdallah da Abee ke kallo yanajin yanda Kausar ke kuka ajikinshi yakaraso wajen shima zama yayi akusa da mahaifin nashi agefen gado gently yadaura kanshi kan kafadan Babanshi batare dayace komiba, saukan dumin hawayenshi Abee yaji kan kafadarshi tunda abin nan yafaru sai yanzu ne Abee yaji kawai he’s completely heartbroken sabida yanda yaranshi suke kuka ajikinshi, Kausar ita wannan daman ta iya kuka but Abdallah rabon dayaga kukan Abdallah tunda mahaifiyarshi da yayyinshi suka rasu, shiru yayi jikinshi yayi wani kalan sanyi baimasan wane zai lallasa cikinsu ba, baisan mezai gayamusu ba, all he knows is yau shine reason behind his children tears, kusan 10min kuka suke ajikinshi hakan yasa yasauke ijiyan zuciya Abdallah yafara dago kanshi da hannunshi yace “mehaka kakeyi Abdallah Men don’t cry” dago fuskan Kausar yayi daga jikinshi dake kuka sosai hannunshi yakai yasharemata hawaye yadanyi murmushi tareda jan mata hanci yace “kinsan bansan kuka ko” girgizamai kai tayi cikin wani kalan sheshekan kuka tace “mekamusu akeson abata maka suna Abee, me Babana yamusu? Why you Abee”? Kifa kanta tayi akan kafanshi tahau kuka sosai gwanin ban tausayi, dagota Abee yayi idanunshi sunyi ja yakalleta dan murmushi yakakalo yakalli Abdallah dake kallonshi yama rasa abinda zaice musu kawai rungumesu duka yayi akirjinshi duk suka kankameshi kaman yanda he was holding them so tight, bayansu ya bubbuga anatse calmly trying to soothe them yace “everything is going to be fine I promise” yay shiru jin haryanzu hawayen su na zuba ajikinsu yace “if you two wants to break me kucigaba da kukan nan” kaman yabasu pills din tsayarda kukan sukayi hakan yasa yadago kansu murmushi yamusu yahada hannayensu biyu yakai bakinshi yamusu peck ahankali yace “you two are Abee’s strength if you break I break, so I want you to be my strength not my weakness kunji, everything is going to be fine I promise” gyadamai kai sukayi ahankali, murmushi yayi yaciro handkerchief a aljihunshi fuskan Abdallah yafara gogewa tass sannan yashare na Kausar shima tass ahankali yace “jeki kawomin abinci I am hungry” dasauri ta tashi tana gyadamai kai tafice daga dakin hakan yasa Abee yakalli Abdallah yace “mesa zaka biyema Kausar kuyita kuka idan tanayi bakasan kaine zaka lallasheta ba”? Gydama Abee kai yayi, Abee yay shiru yana kallonshi saikuma chan yace “how many lectures kai missing yau?” Ahankali yace “all” cikeda rashin nuna jin dadi Abee yace “kar hakan yasake faruwa” gyadamai kai Abdallah yayi daidai Kausar takawo abinci fried rice a tray da flask na shayin shi zama yayi ahankali akasa sannan yakalli Abdallah dake kan gado yace “sauko” debo abincin yayi yakai bakin Abdallah yace “haa” dan yasan dukansu biyun basuci abinci ba tsaf yay feeding nasu yasha shayi sannan yasa suka tafi shikuma yashiga bayi dan yay wanka yayi shirin zuwa masallaci magrib.


Shiryawa yayi cikin wani sky blue soft yadi mai kyau dinkin jumper da wandonshi iya idon sahu, hula yasaka sai uban kanshi yake yazura takalmi yafito daga daki afalo yaga su Hajiya da sauran yaran Hamza Abdallah da Ibro na ganinshi suka mike dan zuwa masallaci yakalli su Binta yace “salat” ahankali tace “eh duk yanzu zamu tashi Yaya” suka wuce suka fita, saida akayi isha’i yazauna yakarasa addu’o’in shi mikewa yayi zai tashi Baba Liman yace “Imrana biyoni” ahankali Abee yabi bayan Baba Liman daya daukeshi amatsayin uba har zuwa waje gaban wata Babban jeep da kallo daya yamata yasan motan Musty ne, bayan motan yabudemai yajuya yana kallonshi yace “shiga” dan jimm yayi ganin Musty da Harun ne agaban , Baba Liman yace “koban isa bane Imrana” babu musu yataho ahankali yashiga bayan motan Liman yashiga sannan yarufo kofan motan Musty yaja motan.



Suna kaiwa kofar gidan da Gwaggo tamusu kwatance ga mamakinshi motan Ibro da Abdul yagani akofar gidan, Hajiya, Anty Binta, sai Hamza da Ibro duk suna tsaitsaye da alamu su kawai ake jira, kofa Baba Liman yabude yafito yakalli Abee dake zaune yace “fito” ahankali Abee yafito daidai Baba yabude gate yafito sabida sallama da akace anayi dashi daman suna expecting nasu hakan yasa yagaisa da kowa yace “bismillan ku”.


Falon Baba aka kaisu duk aka zazzauna kujerun ciki basu dauki kowa ba hakan yasa duk suka zazzauna akasa daga Hajiya sai Baba Liman ne akan kujera da Gwaggo datake zaune har yanzu kayan dazu ne ajikinta sai Mama da Baba, su Samira na dakinsu duk sun zauna jingine da kofa dan suji ne za’ace, yanda Gwaggo kebin kowa da kallo kasan daidai take da kowa Baba na shirin magana tadagamai hannu tace “dakata Malam ai ba kai kabasu adreshin gidan nan bako dan haka wajena sukazo” Takalli Musty tace “kun yarda da sharadin nawa”? kafin Musty yay magana Baba Liman yay gyaran murya hakan yasa akai shiru adakin taron yabude da addu’a sannan yace “na farko dai nine ke matsayin mahaifi ga dukan yaran nan, marigayi mahaifinsu babban abokinane, dukanmu munzo nan ne mukara jajantawa sannan mubaku hakuri kan abinda yafaru wanan abin kaddaran, sannan na tunatar damu cewa mu musulmaine hakkine akanmu na murufawa juna asiri, sannan kusani cewa abin nan dayafaru tun kafin dukanmu nan muzo duniya aka rubuta hakan zai faru a Lawhun Mahfuz dan haka” yakalli Hajiya da ahankali tace “nine mahaifiyar Imrana, amatsayina na mahaifiyarshi na yarda da zancen Auren nan!” Wani kalan dagokai Abee yayi yakalli Hajiya dan baitaba sanin abinda suka yankeba kenan shifa yadauka sunzo ayi sulhu sunada hakuri ne but what is it yake fadi haka wani kalan rawa hannuwanshi suka fara gently Musty yadaura hannunshi saman hannayenshi dake rawa yarike hakan yasa yadago ifanunshi yakalli Musty da idanu yamai alamu da karyay magana ya kunyata iyayenshi, ahankali Hajiya tace “Imrana soja ne, yanadaga cikin manyan sojojin da Nigeria ta tura su yaki yan kungiyan bamaiyi dasuka addabi Nigeria dasaka bamabamai shekaru 13 kenan dasuka wuce, shine sojan dayaci nasaran kashe asalin Ogansu gabaki daya hakan yajawo mishi makiya har akazo har gidanshi aka kashemai mata da yara biyu sauran yara biyun ma da baa kasheba dan yaranshi hudu Allah ya tsirar dasu ne sabida sunzo gidana su kwana, tun lokacin bai kara aure ba, d’ana kamili ne adali kuma yarone da amana dayarike addininshi da gaskiya, ni nasan Imrana bazai tabayin abinda aka ce yayi ba amman tunda haka kaddaran tajuyo wayemu dazamuja da ikon Allah mun yarda adaura Auren Allah yasa hakane mafi alkhairi” washe baki Gwaggo tayi tace “Alhamdulillah Alhamdulillah” takalli Baba dake kallonta tace “ka tsareni da idanu waye zai rikemana diya amana inba mutum haka daya samu kyakkyawan shaida ba takanas takano wannan tsohon limamun yabiyoshi harnan shima yamishi shaidan kirki, dazu nan nan su Abdulhadi damuka bincike suka dawo suka ce duka yan anguwansu sun bada shaidan kirki idan baka aurama jikata mutum hakaba kamili Babba mai hankali wazaka auramawa Iyyee” Ahankali Baba yakalli Baba Liman yace “bismillah Liman adaura” wani kalan mugun ciwon kai Abee yaji yanaji idanunshi namai wasu kalan duhu Misty yarikeshi gam batare da kowa yay noticing ba, agabanshi yana zaune yana kallon kowa aka daura aure tsakaninshi da Lujain akan sadaki dubu dari biyu da friends dinshi Musty Harun da Abdul suka biya take yanke in cash, Gwaggo tace “jedakina Hadi ka kwaso goro” dasauri Hajiya tace “Muma muntaho dashi tashi ku kwaso Hamza da Ibro” tashi sukayi nan da nan suka fara shigo da carton carton na goro da sweet ana kawowa falon Abee na mamakin lokacin da duk aka sayo abubuwa haka but yasan aikin Hajiya dasu Musty ne shiru kowa na dakin yayi banda Gwaggo data tashi tana bare kwalin sweet da Goro tana kakkasawa kana ganinta kasan ita kadaine ke farinciki da wannan auren.

Dan gyaran murya Abdul yayi yakalli Gwaggo yace “Kaka mu bangaren police muna bukatan video da statement naku dazaku bayar amatsayin shaida cewa sudin mata da miji ne sabida duniya tagani hakan zai siliencing kowa kafin ayi tracking yaron shima muna kan hakan” dasauri Gwaggo ta ijiye kwalin tace “to fara dani” kunna video yayi yace “Kaka waye Imarana” washe baki tace “mijin jikata ne, jikata matarshi ce” yama su Baba dasu Baffa sannan yama Hajiya tace “Lujain Matar d’ana ne” saida yagama sannan yay murmushi yamaida wayan aljihu yazauna dakin aka karayin shiru anatse Liman yace “Alhamdulillah yanzu an daura aure Imrana Lujain matarka ce yanzu sai magana tagaba aahhh yaushe zata tare”? Gamgam Musty yarike hannun Abee dayaji na rawa sosai, Baba na shirin magana Gwaggo tace “zakudan bamu kwanaki mudan shirya, tunda yau litinin ranan asabar idan Allah yakaimu mahaifinta dakanshi zai kaita dakinta ko”? Gyadamata kai Baba yayi yace “in sha Allah” Gwaggo tai murmushi tace “yanzu ma dan tai bacci ne dana turota ta gaisheku tunda nake bantaba ganin Lulu tai irin kukan datayi yauba har muka dawo gida har magrib kuka yarinyar nan take Allah dai yasaka muku dagakai Imrana har Matar taka Lujain, kutashi kutafi gida shima yaje yahuta Allah kadai yasan yanda zuciyanshi ke tafarfasa Dan mutum kamili dashi wani gantalalle chan Ya batamaka suna ana kiranka da fasiki, Allah ubangiji ya saka muku yakuma bimuku hakkin ku, yanzu fa anxama daya zamu hadu mu kare mutunci yaranmu ne murufa musu asiri, kai dan nan idan akwai wani video dakakeso nayi kuma kazo zan maka In har hakan zai kawo saukin lamarin nan” dan murmushi Abdul yayi, Baba Liman yatashi hakan yasa Gwaggo da kowa na dakin suka tashi gaggaisawa akayi Gwaggo da Hajiya sukai sallama sannnan har waje suka rakasu suka tafi.
EPISODE 1️⃣4️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Gwaggo kotakan su Baba batabi ba bangarenta takoma tana shiga tamaida kofan dakinta tarufe tasaka sakata ta ijiye kwalin sweet da goron data shigo dashi akasa sannan tawuce uwardakan tana kallon fuskan Lujain dake kwance kan gado daure dawani farin towel kanta babu dankwali idanunta sun kumbura sosai da fuskanta ma, karasawa gaban gadon Gwaggo tayi tazauna ahankali tana kallon fuskanta murya chan kasa tace “bantaba sanin kankanin abu na faruwa ba dazai kawo wani rayuwanka wanda hakan yake kaman aya agareka ne sai akanki Lulu, ninafi kowa sanin yanda kikeson wannan gantalallen dan kwallon Mandawari, yau agabana kika fasa zunzurutun asusunki kika kaima wanan kuran kudin Samira dan kawai ta aramiki waya ki kalli dan daudun mesaka hakorin makka, ni tsabagen yanda nama tsani yaron da kullum kike nunamini awaya idan yana magana zan ma iya zanashi da pencil naganshi, ranan sabida shi bokon ma bakiso zuwa ba dan kada yazo baki kalli video ba amman Allah bless yasa kikaje makarantan, jibidai yanda nida idona da muna kallon video naga bayin dakiketa nema akasa ki shiga baki ganiba domin Allah ya daukemiki idanun awajen so yake kije sama kihadu da Imrana, kikaje saman kika bangajeshi kika bata mishi kaya da fanta amman fuskanki nakan waya shaidanin nan kike kallo kika wuce bayi nafi kowa sanin yanda kike neman waje shiru ki natsu duk sanda zaki kalli Mandawari dan ko ni nan idan zaki kalla uwardaka kike shigewa ko nazo ina kwalamiki kira shiru kike ki kyaleni” shiru Gwaggo tayi sannan ahankali tace “Allah ne ya aiko miki Imrana diyata, shima kuma Allah ne ya aikamishi ke rayuwanshi saikuma Allah yakaddara cewa ba

Please Login or Register in order to submit comment