Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, normal common girl Allah yajarabeka da so Muhammad” wani kalan mugun kallo Mandawari yamai yace “and so”? Olusay yace “dan haka kadena jan aji slide into her dm and respond to all her messages and confess your feelings Bro koba hakaba guys” duka yan team nasu sukace “hakane” daya daga cikinsu mai suna Obi yace “I can’t wait to see babe din da Man keso yanda yakema mata wulakancin nan I know she must be the most beautiful girl on earth” dan tsaki Mandawari yayi yace “you guys should stay away from me and my business” yay maganan yana cire nashi rigan ya chanza kayanshi zuwa normal Riga da wando black yadauki wani big jacket yadaura akan kayan dan sanyi akeyi a Greece thank God yau zasu koma nigeria, yana gama shiryawa aka shigo akace bus nasu is ready fita duk sukayi koda sukakai bus din shida yasaba zama da Olusay yau bai zauna wajenshi ba baya yawuce yazauna abinshi Olusay baicemai komiba.



Airport suka wuce business class aka biamusu dayake shida Olusay ne zasu Nigeria sauran kowa yay garinsu, saida jirgin sannan ya kwanta wayanshi yabude yashiga chat dm din Lujain yana dubawa tun 2019 tafara turamai messages har zuwa yanzu dasuke 2022 amman baitaba amsata daidai dasau dayaba, fitowa yayi yashiga Fred dinta yana duba hotunan ta, 5 pictures ne kawai tai posting, daga wanda tasaka scchool uniform sai wanda take itada Gwaggo, sai wanda tayi ranan salla da Ya Samira, saikuma wanda tayi ita kadai tayi bala’in kyau a hotunan duka pink lips dinta ya tsare da idanu kaman tasaka pink janbaki, fitowa yayi yawuce wani blog a instagram yakara bude video ta na sex video nan da yanzu zai iya cewa yakalla yakai sau 20, saikuma ahankali yafito yashiga video da blog din still sukai posting na debunking news din cewa mutumin mijinta ne ga shaida daga wajen iyayensu, jazur idanunshi sukayi har jijiyoyin kanshi suka fito kashe wayan yayi ya runtse idanu ahankali murya chan kasa yace “you are mine Lujain! You love only me! You belong to me”…
*****


Har aka tashi daga makarantan tana aji, da kyar wuraren 1 ma tafita shima cafeteria officials nasu ne sukazo suka kirata kan tazo ta amshi lunch haka taje lafiyayyen abinci aka bata da drink harda kaza ga student awajen babu ma mai kallonta haka taci tadawo aji, malaman sai nan nan da ita suke yan ajinma namata magana itane ma bata amsasu da kyau kawai duktabi ta tsargu, 4 daidai aka gama musu special lesson din aka tashi kowa yashiga daukan jakanshi banda ita dake zaune inda take saida kowa yagama fita yarage ita kadai a ajin yasa tashiga hada books nata ajaka tamaida komi saikuma tai shiru tana kallon jakan yau kwana hudu kenan bataji muryan yan gidansu ba, bata gansu ba, koda su Baba dasu Mama dasu Ya Abida basu damu da ita ba Gwaggo fa? Yanzu Gwaggo barata nemeta ba, daman da gaske takosa takadata daga gidansu shikenan batada kowa, wannan wani kalan rayuwa ne da rana daya kawai tajefa kanta? Jitake kaman tadawo da hannun agogo baya ta chanza duka abinda yafaru ranan, babu wani abu datakejin dadinshi arayuwanta, ita batada waya, ita gidan nan babu wanda zai yarda yabata wayanshi balle takira Gwaggo ma, ita school dakomima baya mata dadi yanzu sabida batada Mama ne saisa abu haka ke damunta? Inda Mamanta na raye tasan barata wahala hakaba tunda gashi yanzu ma Gwaggo batasonta kaman Mama wasu kalan hawaye masu zafine sukazo mata tundaga yatsun kafanta kawai kife kanta tayi akan kafafunta tafashe da kuka sosai Abee yadade tsaye gaban ajin yana kallon yanda takife kanta kan kafanta tana kuka sannan yadanyi gyaran murya da sauri tadago jajayen idanunta, ganin Abee yasa dasauri tashare hawayen da bayan hannu ta mike tsaye ahankali tareda daukan jakanta ahankali ta goya sannan tafara tafiya kanta akasa ta taho gaban kofan, baice mata komiba yayi gaba hakan yasa tabishi abaya har zuwa waje, mota yashiga itama tabude gaba tashiga tazauna har lokacin idanunta jazur, harzai tada mota saikuma yajuyo yakalleta bayabo ba fallasa yace “why are you crying”? Dan juyowa tayi takalleshi yanda ya tsareta da idanu saitaji takasa mai karya lips nata har rawa suke tace “kewan yan gidanmu nake…...” Wani kukan ne yazo mata dasauri takife kanta kan jakan makarantan da akabata a school tafashe da kuka sosai cikin kuka tace “babu wanda ya nemeni cikinsu da Baba da Mama, dasu Ya Samira harma Gwaggo basu nemeni ba sun kawoni gidanku I am all alone babu wanda ke sona, kowa haushina yakeji, I am so scared mutane su ganni kar adinga nunani babu abinda kemini dadi, I just wish inama zan mutu maybe namaga Mamana achan naji dadi, babu wanda ke sona har Gwaggo na” tunda tafara maganan kallonta yake tabashi tausayi sosai inda Kausar dinshi ne fa in this situation, “wayace miki Gwaggon ki bata sonki” dago kanta tayi dasauri da rinannun idanunta takalleshi dauke kanshi yayi yakunna key tareda tada motan yaja motan sukabar wajen, saida suka shiga titi ahankali tace “inda tana sona dabatamin auren nan ba ni inada wanda nakeso” dan kallonta yayi saikuma yadauke kai yakalli titi kusan 3min babu wanda yace komi acikin motan kaman daga sama yace “shi kike kallo rannan abayi”? Gyadamai kai tayi dasauri tana goge hawayen kan fuskanta da bayan hannu tace “eh sunanshi Muhammad Mandawari, ni shinakeso na aura” yana kallon hanya yace “kinfadama Babanki” gyadamai kai tayi tace “eh yasani” ahankali Abee yace “to mesa basu aura miki shi ba”? Dan rage murya tayi looking so sad tace “ai baitaba amsa messages dina a instagram bane ba” batare da Abee yakalleta ba yace “do you have phone”? Girgizamai kai tayi tace “a’a da wayan Ya Samira nabude instagram nai following dinshi rannan dana fara ganinshi a tV dakin Gwaggo yana buga kwallo” “kinason kwallo”? Abee yay maganan yana kallon titi, ahankali tace “eh inason kallon kwallo kuma inason Mandawari sosai, nasan inda yau zan ganshi all my problems will be gone zaije wajen Baba yace shine zai aureni bakaiba sai ka sakeni amini aure dashi natafi wajenshi muyi zamanmu” daidainan sukakai gaban wani saloon yakashe motan yadan kalleta ganin tana kallonshi kaman tasami tV da manyan idanunta masu kala dana mage yasa yadauke kai wayanshi yadauka duk tana kallonshi komi nashi anatse yakeyi baitaba mata dogon magana ba sai yau kuma kaman magic sai yan maganganun sukasa ta manta da bakin cikin datakeyi, ijiye wayan yayi yajuyo yakalleta jin alamun ana kallonshi dasauri tadauke kai tana wasa da yatsunta, dauke kai shima yayi daidai nan Anty Binta tafito daga saloon din tazo bangaren Lujain tabude tace “Iyye yan makaranta oyoyo” murmushi Lujain tayi, Anty Binta tace “ke baki gajiya da kuka ne look at your eyes fito muje to a gyara miki gashin nan dabaki iya tajewa da kanki a kitsashi, kawo jakan nan nasa abaya Ya Imran yawuce miki dashi gida” fitowa tayi tamaida jakan baya itakuma Anty binta tazagayo ta bangaren Ya Imran tace “Yaya bamu ATM card dinka zandan yima Lujain siyayyan kaya dasauran yan kananun abubuwa na mata da batadashi” wani dan iskan kallo yamata sannan yadauki ATM card nashi yabata yace “6701 is the pin” murmushi Anty Binta tayi tace “thanks Big bro” jan motanshi yayi yawuce itakuma Anty Binta yakama hannun Lujain databi motan nashi da kallo suka wuce ciki.EPISODE 2️⃣6️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/



Shuku Anty Binta tasa akamata mai bala’in kyau, mai style yan kanana nan da nan tayi kaman ba itaba, tasa aka wanke mata kumbunan kafa da hannu Anty Binta sai kallon yatsunta take both nakafa da hannu sunada bala’in kyau gasu so chubby sannan yatsun farare dogaye, mace mai ni’ima kana iya ganewa daga yatsunta both na kafa da hannu, bakaramin addu’a take kan Ya Imran yafara son yarinyar nan ba dan Lujain is a gift from Allah, kyautanta Allah yamai bayan wahalan rayuwan dayayi, 13yrs ba mata sai zaman kadaici da bautan Allah saisa Allah yabashi Lujain cus babu abinda Lujain batadashi gatada shiga rai, bala’in shiga rai, daga zuwanta saloon din nan harsun fara sonta, mai saloon din harda cema Anty Binta tanason sister nan nata tamata influencing saloon din nan adauki pictures nata zata biyata da kyau, saida tanuna musu matan aure ne mijinta bazai yarda ba sukabar zancen.

Biyan kudi sukayi sannan suka fito wani babban super market sukaje jakunkuna Anty Binta tasaya mata da takalma masu kyau da yankune da agogo, bracelets irin na yanmata dinnan, da kayan sawa english wears masu kyau sosai su sexy gowns, shorts, shirts, jeans dan sotake tadinga sawa Ya Imran yasoma dawowa hayyacinshi, takara mata abayoyi, da turaruka, harzasu fito tace “Anty su Chocolate” wajen chocholate sukaje sai alokacin Lujain tafara deban chocholates dasu biscuits dabama tasan dasu aduniya ba ita Anty abin dariya ma yabata tace “ai saisa kike kiba sweet tooth ni mutafi” biyan kudi sukayi aka kaimusu kayan mota sannan suka tafi bayan magrib suka shigo anguwan Anty Binta ke tuki gidan dake kusada nasu sukaga an bude ana shiga da sababbin furnitures Anty Binta tace “kowaye yasai gidansu Maman Adam oho” kallon gidan Lujain tayi dayake abude sai gyare gyare ake har fenti anyi, Anty Binta dake tuki tana kallon gidan tace “Maman Adam makotan mune sunada kirki gidansu ne amman sun saida sabida mijin zai koma US yasami aiki a chan” daidai anbude musu gate suka shiga cikin gidan, parking tayi suka fito zare hijab din school Lujain tayi tadauki ledan chocholate dinta tayi gaba mai gadi natayasu daukan sauran kayan sallama tayi tashigo falon ahankali daga Hajiya sai Musty da Abee afalo Musty ne ma yadago shi daga masallaci dabai shigo gidan ba sai bayan isha’i, kallo daya Abee yamata yadauke kai Hajiya tace “yan makaranta an dawo” Gyadamata kai tayi batare data karasa wajen ba tace “ina wuni” sannan takalli Musty ahankali tace “ina wuni” murmushi yamata yace “lpy lau” Hajiya tace “aiko kitson yay kyau mekika riko mana a leda” ledan takalla for the first time dan murmushi tayi tace “chocholate dina ne” dan dariya Hajiya tayi tace “sabida bakiso kibani ne kike cewa chocholate dinki ne ai shikenan jekisha Lujain” akunyace tadan sunnar da kanta kasa kaman mai koyon magana tace “Allah ni zan baki Hajiya” shi kanshi Musty dan murmushi yayi jin yanda tai maganan Hajiya tace “to nagode Allah amfana jeki cire kayan makarantan saikizo kici abinci” Gyadamata kai tayi tawuce sama, tana shiga dakinta taga jakan school nata an ajiyemata waje daya, bayi tawuce tacire kayan school nata tareda jefawa a washing machine sanan tai wanka da ruwan zafi tafito daidai Anty Binta na shigowa dakin rikeda manyan ledojin kayanta Maman Aneesarh ma natayata dan kallon Lujain din Maman Aneesarh tayi yanda kitson yamata kyau tace “Ya school”? Ahankali Lujain tace “lafiya lau ina wannan baby”? Murmushi Maman Aneesarh tayi tace “tayi bacci” sannan tawuce tafita daga dakin, Anty Binta saida tajera mata kayan tass dan ita bata salla sannan tawuce tafita itakuma tana idarwa zama tayi kan gado tabude ledan chocholate nata tashiga sha saida tasha daban daban kusan guda 7 sannan ta tashi tasakeyo alwala tafito tahau kan dadduma tana salla shigowa Anty Binta tayi ta ijiye mata abinci a kula tana idarwa taci batawani ci dayawa ba sabida yanda tasha chocholate din nan hawa gado tayi ko 3min batayiba sai bacci danta gaji.


Wuraren 2:30 tabude idanunta ahankali sabida shegen yunwan datakeji, dakin da hasken wuta hakan yasa ahankali ta tashi zaune sauka tayi daga kan gado tabude kulan abincinta dabata ci jiya da daddare ba, yatsine fuska tayi danji tayi batasoncin abincin tamaida tarufe ledan chocholate nata ta dauka tabude ciro chocholate guda uku tayi sannan tabude jakan school nata tafito da books dinta tana duba abinda aka musu tanaci saida tacinye tass sannan ta tashi ahankali tasake hawa gadon nan da nan bacci yay awon gaba da ita.

4:30 Abee yafito saida yatada kowa sannan yakoma dakinta knocking yayi tareda bude kofan ahankali ledojin chocholate daban daban kusan 10 dayagani akasa yasa yakalleta tana kwance kan gado tadan rufa tana bacci ta peacefully, katon ledan chocholate din yakalla dahar ya rage yawa sannan daganan inda ya tsaya yace “Ke! Kee!” Firgigit tabude idanunta ahankali tareda dan turo baki saikuma chan kaman wacce ta tuna abu bude idanubta tayi tass ganin Abee ne ba Gwaggo ba yasa dasauri tamike tsaye tawuce bayi Abee yajuya yafice.

Wuraren 7:00 tabude kofan dakinta ahankali tafito ta shirya tsaf cikin kayan makarantan dasuka mata mugun kyau tagoya jakanta abaya hannunta rikeda farin hijab din dabata sakaba tanabin saman da kallo daidai Abee ya hayo sama kallo daya yamata yadauke kai itakuma ta tsaya chak inda take takasa koda motsi saida yakaraso daidai inda take yace “today should be the last time dazan ganki a falo babu hula ko lullubi” yana maganan yawuce dan turobaki tayi tasaka hijabin sannan tawuce tasauka kasa saida tafara gaida Hajiya sannan tai breakfast sosai taci abincinta baruwanta tashi tayi Hajiya tace “ina zaki Imrana dazai saukeki baima fitoba” ahankali tace “zan zauna awaje ne inga rana” murmushi Hajiya tayi tace “tom jeki” wucewa tayi tabude kofa tafita waje Kausar tabita da harara ahankali take kallon ko’ina na tsakar gidan tana kallon yanda gardener dinsu ke zubama flowes ruwa, juyawa tayi tayi wajen gate nasu tabude karamin gate din kadan tana leken waje batasan mesaba hakanan taji kaman wani abu na janta zuwa wajene ahankali tasa kafanta tafita waje wani sanyi taji yashigeta ahankali tadaga kanta tana kalle kalle titin estate din shiru babu motoci dan duka duka yanzu is 7:15, jitayi kaman ana kallonta ahankali yasa ahankali tajuyo da kanta takalli gidan dake kusada nasu chak taji numfashinta ya tsaya.


Mandawari tagani yana tsaye gaban gate nasu sanye dawani rigan jersey na Liverpool dark blue dawani farin short bathroom slippers ne a kafanshi hannunshi rikeda iPhone 14 dayakai kunnenshi da alamu waya yake amman idanunshi kyar akan na Lujain dabai taba tunani zai gani ba dan duka duka ko 20min baiyi da zuwa duba aikin da akeyi agidan ba.

Wani kalan sauke numfashinta Lujain tayi takai hannayenta dasauri ta goge idanunta dan tanaso takara gasgata ba gizo idanunta kemata ba Mandawari take gani yanzu haka agabanta jingine dawata mota black yana waya, ganin still shine yasa taji gabanta nawani irin mugun gudu takasa koda motsi, kusan 2minutes sukayi tana kallonshi yana kallonta yana waya sannan yazare wayan daga kunne awulakance yamata alamu da hannu datazo nan, nuna kanta tayi tace “ni?” Gyadamata kai yayi batare dayace eh ba, gabanta nafaduwa sosai tafara tafiya ahankali takarasa gabanshi ta tsaya tana kallonshi, cikin sigan yanga yace “why are you looking at me like that kinsanni ne”? Wani kalan lumshe idanu tayi tabude ga muryanshi nan sak wanda takeji idan yana live video batare daya kyafta ko idanu ba tana kallonshi tace “nasanka” tsareta yayi da idanu hakan yasa tace “you are Mandawari, kana buga kwallo, kai player Liverpool ne, sannan kana bugama Nigeria, ina following naka a IG, my name is Lujain and I am your biggest fan” takarashe maganan tana gasping breath tana wani kalan kallonshi kaman zata hadiye shi da idanu, dan yatsine fuska yayi yadau wayanshi yadan daddana batare daya kalleta ba yace “my biggest fan can’t be this ugly” dasauri takalleshi looking confuse, janye wayan dayake dannawa yayi daga fuskanshi sannan yakalleta awulakance yanunata da wayan dake hannunshi daga sama har kasa yace “I mean look at you, you are so soo fat, I don’t think ko mai cikin 5 months takaiki katon teba, so please excuse me go and loose weight saiki dawo kimin magana” yay maganan tareda juyawa yabude kofan motanshi ya shige tareda jan motan da gudu yawuce yabar anguwan daidai hawaye na zubomata sharrrr, “ana kiranki” taji muryan Kausar hakan yasa tajuya da sauri hada idanu sukayi da Kausar, Kausar zata juya takoma ciki dasauri Lujain tace “Kausar” hakan yasa Kausar ta tsaya tana kallonta karasawa wajenta Lujain tayida sauri, bakin Lujain har rawa yake cikeda wani kalan damuwa tace “Kausar dan Allah kifadamin gaskiya, please inada kiba”? Tsayawa Kusar tayi tana kallon fuskanta ganin yanda idanunta sun cicciko da hawaye ga damuwa karara afuskanta yasa tace “ke baki sani bane kike tambayana” juyawa Kausar tayi zata wuce dasauri Lujain tarike mata hannu tace “dan Allah kifadamini gaskiya nasan you don’t like me so you will tell me the truth” dan shiru Kausar tayi yanda taga she really wants to know yasa tace “eh kinada kiba Lujain” kaman jira Lujain take hawayen idanunta ne suka zubo dan zaro idanu Kausar tayi tana kallonta tace “Waike lafiyanki kalau kodai kinada aljanu ne” sakin hannun Kausar tayi daidai lokacin Abee yabude kofa yafito Kausar tayi wajenshi tace “Abee waje taje tana kuka” dan kallonta yayi yanda take tsaye awajen gate takai hannunta kan fuskanta tana sharewa kawai yawuce wajen motanshi hakan yasa Lujain ta taho tashiga motan Abee yaja motan suka tafi harsuka kai school baice mata komiba sauka tayi tashiga ciki yabita da kallo kafin yatada motan yawuce shima.
EPISODE 2️⃣7️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Ranan har aka tashi daga school tarasa abinda kemata dadi koda taje lunch takasa cin abinci sosai, 4 suka tashi tadauki jakanta tafito daga ajinsu tundaga nesa tahango Abee tsaye jikin motanshi yana sanye da suit nashi black yasaka wasu bakin glass a idanunshi wayanshi akan kunne yana magana ahankali take tafiya harta karaso inda yake tasauke kanta kasa tana wasa da yatsunta murya chan kasa tace “ina yini” wani kalan kallo yamata sannan yashiga cikin motan itama zagawa tayi tashiga yatada motan suka tafi, tunda suka shiga estates nasu take kallon gidan Mandawari dataga gate din arufe horn Abee yayi aka bude musu gate suka shiga cikin gidan parking yayi tareda kashe motan dan juyowa tayi ta kalleshi daidai shima yadan kalleta ganin bata bude kofa tafita ba, sauke kanta tayi kasa tashiga wasa da yatsunta kaman yabude kofa yafice abinshi saikuma yace “me kike bukata”? Dan dago kanta tayi takalleshi ganin ita yake kallo yasa ahankali tasauke kanta kasa tana wasa da cute white chubby fingers dinta dakenan gyare tsaf murya chan kasa kaman batason abinda zata fadi tace “dama….dama…..” saikuma tai shiru batasan tayaya zata tambayeshi kudiba, dan dago kanta tayi ganin kallonta yake yasa tadauke kanta dasauri tace “I…..don’t have any money Uncle……” taidan shiru realizing this is the first time take kiranshi kumama wai Uncle abin yamata wani banbaran abaki, dan kallonshi tayi kadan suka hada idanu dan lankwashe kai tayi kaman wata macijiya murya chan kasa tace “kuma…..kuma magani nakeson in saya” kallonta yake kyar batare dayace komiba, dan dago kanta tayi suka hada ido murya chan kasa tace “uhmmm….maganin rage ki…kiba” dan lumshe idanu yayi yakalleta sannan yace “a ina ake saida maganin”? Dan kallonshi tayi kana ganin kwayan idanunta kasan batasani ba, ahankali tace “nima bansani ba amman ai za’a samu a kasuwa” wani kalan kallo dayamata yasa tamaida nata idanun kasa yace “kintaba ganin yaran gidanmu sunje kasuwa?” Girgixamai kai tayi, ahankali yace “kin taba zuwa kasuwa?” Sake girgixamai kai tayi tace “amman Gwaggo na na zuwa tana sayo magunguna da yawa nasan zan samu nima innaje” tunda take maganan yake kallonta yace “did anybody told you kinada kiba a school ne”? Sake girgixamai kai tayi tace “a’a” ahankali yace “maisa kikeson kisha maganin rage kiba”? Batasan mesaba hakanan taji takasa fadamai karya ahankali tace “Mandawari bayason mace mai kiba” yadade yana kallonta harsaida tadago kanta takalleshi dan gajeren tsaki yayi yace “yabaki maganin rage kiban to” yay maganan yana yunkurin tashi dasauri tace “namishi magana”? Dan tsayawa yayi saikuma yajuyo yakalleta yace “I told you zaki iya kome kikaga dama I don’t consider you my wife and you are not my wife, dazaran this whole thing yalafa aka kamo yaron zan rabu dake” wani kalan murmushi tayi daya lobar mata da dimples nata tace “thank you Uncle” tai maganan tana bude kofa tafito tawuce ciki tana tafiya ahankali yadan bitada kallo.


Hajiya kadaine a falo da Maman Aneesarh ahankali tace “ina yinin ku” murmushi Hajiya tayi tace “sannu da zuwa” Aneesarh data gani taduka tadauka tana murmushi tace “zomuje dakina” murmushi Mamanta tayi tace “wanan saita batamiki daki wlh da barna” murmushi tayi tace “dan Allah kibarni natafi da ita Allah ina sonta” Maman Aneesarh tace “shikenan kuje” wucewa sukayi sama Abee yashigo shima gaida Hajiya yayi, Hajiya tace “sannu da zuwa Imrana” ahankali Maman Aneesarh tace “sannu da zuwa Yaya” Gyadamata kai yayi yawuce sama, Maman Aneesarh takalli Hajiya tace “Hajiya Ya Imrana is so nice towards this girl” Hajiya tace “Imrana has always being nice to kowa, banbancin Babba mai hankali kenan da kananun yara samari, Lujain is just like Kausar kozai wulakantata bazai iyaba dan kaman diyar cikinshi ne bazai iya imagining wani ya wulakanta mai Kausar ba, nasan Imran dina dudda bayason Auren nan bazai taba cutar da ita kokuma yaga abin cutarwa yabari ya cutarda ita ba” Maman Aneesa tace “saisa yasata a makaranta mai tsada ko su Kausar ba makarantan turawan nan sukayi ba” Hajiya tace “inba irin makarantan nan ba awanne za’a sata yarinyar da fuskanta ya zagaye yanar gizo so kike kullum adinga dukanta ta tsani makaranta gabaki daya taki fita” ahankali Maman Aneesarh tace “Hajiya ni tausayi yarinyar ke bani koda zamuso zamansu da Ya Imran tayaya zata fara kula da Ya Imran? Babu abinda ta iya wannan saidai shi yakula da ita ai” Hajiya tace “daga next week duk idan tadawo daga makaranta zan dinga sata tana shigowa kitchen kuna koyamata abu daya biyu haka harta kware” kallonta Maman Aneesarh tayi tace “Mama kinason auren su ne?” Hararanta Hajiya tayi tace “kin isheni da tambaya amman abu daya zan fadamiki babu Babba dazai cemiki yanason mutuwan aure duk Auren da aka daura fatanmu shine yadaure har abada, idan zamansu tare Alkhairi ne Allah yahada kansu kullum shine addu’a na”.
***



Olusay ke tuki suka shigo estate din, horn yayi gaban gidan gateman yabude musu suka shiga ciki Olusay yace “wow gidan yay kyau wlh Man” yadan kalleshi ganin yana cikin IG, karasa parking yayi ganin Mandawari baima saniba yasa gently yakai hannunshi yadaura akan shoulder nashi hakan yasa dasauri Mandawari yakalleshi yace “ohh harmun shigo”? Olusay yace “kanachan kana kallon hoton stalker naka yaza’ayi kasani” kallonshi Mandawari yayi, ahankali Olusay yace “can I talk to you Man I am serious”? Dan yatsine fuska yayi yana cire sitbelt yace “what”? Dan jim Olusay yayi dan baisan how he’s going to take the magana ba ahankali yace “first of all Muhammad I don’t know your reason na sayan gida right next to gidan da stalker dinka ke aure, nabiyu you saw everything mezakayi da matan aure yarinyar data Riga tayi aure? Thirdly kasan your Mom bazata taba bari ka auri yarinyar that went viral online hakaba, and nahudu kariga kayi loosing chance dinka da bakin wulakanci for the past how many years yarinyar nan namaka magana wulakancinka yahanaka kulata sai yanzu bayan an mata aure ne zaka fara sonta what’s all this Man? Mezakayi da wannan yarinyan kanada thousands of mata har yan film dake sonka sai wannan da aka mata unfortunate Marraige din nan zaka wani fara so” shiru Mandawari yayi saikuma chan yace “you want an honest answer?” Gyadamai kai Olusay yayi ahankali yace “I buy this house triple amount na gidan nan because of the girl dan wasu harsun sayi gidan nakara kudade, sannan kai kanka you just call the marriage unfortunate one kawai anyishine dan ayi blocking mutane from saying shit

Please Login or Register in order to submit comment