Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai bansan kokin maida Lulu kishiyarki bane amman tsakani ga Allah kemafa dazu kin shigo nabaki Kazan nan sannan kinci na wajen uwarki yanzu na jikata ne baraki bari taci ba” turo baki Abida tayi tace “ai nima jikankice” ihu Gwaggo tayi tace “daman nace ke ba jikata bace ni Safara’u amman ai wannan bata da uwa keko ga uwarki chan awaje tana aiki sai shegen bakin zuciya” daure fuska Abida tayi tamike zata fita Lujain tadauki katon cinya tace “uhm” juyowa Abida tayi ganin Lujain nabata tazo ta amsa tajuya bako godiya Gwaggo tace “kobaki gode ba Allah dai yabata lada kinga banbancin rainona da rainon uwarki ko, diyata akwai kirki da farar zuciya kuko zukatanku uwa an shafa bakin fenti irin na gyatumarku” daidai nan Lujain ta tashi tana gaytsa ahankali Gwaggo takalli abincin dudda bata cinye komi ba amman tarage sosai tawuce tashiga bedroom nasu kayan makarantan tacire tashiga bayi wanka tayi tafito daure da towel tasa hijabi tai salla sannan tafito falo ganin bataga Gwaggo ba yasa tadauko jakanta taciro wayan Ya Samira ta kunna wayan batai komiba amman screen din ya tsage faduwa gabanta yayi ahankali ta tashi tana rike da wayan tafito da towel din nan tawuce side dinsu bataga Mama awaje ba hakan yasa yasan tana kitchen dakinsu Ya Samira tashiga tana zuwa ta ijiye mata wayan akan kayanta sannan tafito tadawo daki Gwagho da fitowa ta daga nan daki kenan tace “barakizo kihuta ba kinsan anjima kadan zaku islamiya ko
EPISODE 9️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/


Bayan one week!
Yau Saturday kasancewa jiya Zainab ta tafi dan mijinta yadawo yasa jama’an gidan suka ragu, kowa na gidan nanan Abdallah ne kawai bayanan danshi both asabar da lahadi duka yanada lectures.
Zaune yake a falo yana sanye da jallabiya fara mai kyau hannunshi rikeda wani cup na shayi mai kyau yana kallon Hajiya da Mustapa dawani abokinshi Haruna shima soja ne yau kuma yashigo Abuja sai hira suke da Hajiya suna dariya shi iyakanshi yay murmushi aka tambayeshi eh ko a’a idan dasabo harsun saba da halin nan nashi, idan baka sansu bama zaka dauka shine bako su Musty sune yaran Hajiya, shayin yakai bakinshi ya kurma daidai wayanshi kiran IPhone 14 pro max dake aljihun gaban farin jallabiyan shi na kara ahankali ya ijiye mug din kan coffee table dake gabanshi yaciro wayan ganin messege ne from an unknown number yasa gently yabude.
“You have 24hrs to pay sum of 100 million in cash dakuma papers na company na Imran ceramic inba hakaba we will release your sex tape ma duniya, in 24hrs time zamuyi contacting naka ta hanyar fadamaka inda zakakai komi ka ijiye”.
Abee kyar ya tsaida idanunshi kan messege din daya karanta kusan sau hudu. “Hey hey Imran!” Firgigit dayago kanshi ganin Mustafa akanshi da Haruna sai Hajiya duk suna kallonshi, ganin idanunshi yasa Mustapa yace “lafiya dai ko me kake dubawa haka”? Mustapa yay maganan yana kokarin karanta abinda ke screen nashi da sauri yay locking wayan yana mikewa tsaye yace “time for asir ko let’s go” atare dukansu suka fice suna hira Haruna yakalli wani babban gym dayaga ana fito da tsofaffin kayan workout din ciki ana saka sabo yace “anya kuwa Musty komu sojoji zamu nunama Imran training kuwa”? Dasauri Mustafa yace “inafa bakaga saisa baya tsufa ba look at him please kaman Yayan Abdallah” wani mugun kallo Abee yamai yace “kadaina maidani yaro I don’t appreciate that” Musty shima mugun kallo yamai yace “kayi zuciya kai tsufa to” daidai sun kawo masallaci.
Har suka idar da salla sex tape na ranshi to kodai bashi za’a turama sakon ba sukai mistake amman kuma sun kira sunan company shi, gida suka koma daidai an gama lafiyayyen tuwon shinkafa da miyan kubewa da kifi yana zaune akan kujera wayanshi yakara kara ahankali yabude wayan video yaga an turamai babu wani rubutu tareda video, 5 secs video ne hakan yasa yabude tareda maida karan to mute shiya gani a video abayi yana tafiya yana kokarin kwance belt zaije bayin nan just 5secs yakare shiru yayi bayan video yakare he don’t really know what to think wannan ranan dahar yay using that general restroom was ranan da yan makarantan nan sukazo to where is the sex yan second dayayi abayin nan ne sex? waye a company shi yamai wannan video? Blocking number yayi sannan yay deleting message din gabadaya dan baiga amfanin abin ba though abin ya tsayamai arai dan shi yasan baiyi wani abu mara kyau ba.
“Are you eating ko mu cinye mubarka”? Musty yay maganan yana kallon Abee, Hajiya tace “ahap wannan aishi da abinci makiya ne baci zaiba kuci abunku ku manta dashi” mikewa yayi dagakan kujera yace “kuci I will eat later ina zuwa” yana maganan yay stairs duk suka bishi da kallo, dakinshi yawuce zama yayi akan gado yay shiru sai chan yay dialing number chief head of security na company shi ringing daya yadauka yace “Sir” anatse yace “Mr James I need you to email me the CCTV footage of on 23rd right away” cikeda girmamawa yace “yes sir” tashi yayi yawuce wajen desktop nashi ya zauna tareda kunna desktop din ya bude email nashi daidai video yashigo budewa yayi sunada yawa danna kowani department daban department da office nashi yake yabude yay fast forwarding zuwa daidai lokacin dayaje bayi saikuma yadawo baya daga lokacin daya fito daga office nashi yana waya har zuwa yazo corridor nan saiga yarinyar tazo da gudu ta bangaje shi alokacin yaga wani ma’aikacin shi da bazai ma iya tuna sunanshi ba but yasan yana cikin Human Resources team nashi, zama yayi yana kallon komi harzuwa sanda mutumin yaje wajen bayi a corridor bayi akwai cctv but babu acikin bayi daidai inda mutumin yafito da wayanshi yasa acikin bayi yay lumshe idanunshi yayi yay shiru meyama yaron nan da yakeso yabatamai suna daidai nan aka turo kofan dakinshi aka shigo dasauri ya kashe desktop din ganin Mustapha da Haruna, Musty dake kallonshi trying to read something from his face yace “are you okay kuwa Imran” key dinshi na mota dake kan desk din yadauka yace “I need to go to office now something came up” ta gefensu yabi yafice yabarsu nan tsaye Haruna yace “what is this saying ma?….Hali zanen dutse ko” tabe baki Musty yayi yace “ai murdadden halin Imran bazai taba chanzawaba tun yana yaro” zama sukayi, Haruna yace “Musty yafijin maganan ka wai har yanzu bazai aureba Kodai yanada matsala ne irin I mean medical one din nan” dan dariya Musty yayi yace “lafiyanshi kalau wlh” Haruna yace “to tayaya yay surviving 13yrs ba mata ni gashi yanzu inada mata biyu na uku ma nake neman yi yanzu dan sunmin kadan, nakasa gane yaya yake surviving” tabe baki Musty yayi yace “ohon mishi idan yazo katambaye shi, ni tashi muje mu buga ball jikina yamin nauyi sabida yan kwana biyun nan damukai ban motsa jiki ba” Haruna yace “yaushe za’a gama aikin gidan naku ne kadau matanka kutafi” murmushi yayi yace “cikin this week yau suke fenti ma dazu nida Imran munje gidan” suna hira suka fice daga gidan bayan sun gayama Hajiya zasu dawo suyi dinner tace to su kawo mata inibi.


Zama yayi acikin office nashi bayan yaciro file din Human Recourse team nashi kowanne ga sunanshi da passport da information nashi awajen akan yaron ya tsaya sunanshi Abdulganiyu Olaniyi Asiwaju Razak bayerabe ne from Osun state aikin nan ne yadawo dashi Abuja this is his second year a company shi, shiru yayi yana kallon hoton yaron, saikuma ahankali yashiga daukan number shi yay dialing yaji akashe ajiyan zuciya yasauke ya maida paper ya ijiye yay shiru kana ganinshi kasan tunani yake yana nan cikin office shi kadai har magrib jin ana kiran salla yasa yatashi yakulle office yafito tareda masu gadinshi sukai salla yajasu jam’i suna idarwa kyautan kudi yamusu har mota suka rakashi suna godiya yawuce yatafi tsayawa yayi wajen masu saida fruits siyan dayawa yayi aka samai a boot harzai wuce saiga mai saida ribbon Muna yatuna batada wani gashi but yanason ribbon most time yakan tsokaneta da aukin siyan ribbon amman babu gashin dazata kama dashi kiran mai ribbon din yayi yace “kawo” dasauri mutumin yazo kafinma mutumin yay magana Abee yace “nawane duka”? Washe baki yayi yace “duka nan kayan 4,500 ne” 5k yaciro ya kirga yabashi godiya mutumin yashiga yi yaciro komi yahada yabashi karba yayi yaja motanshi yawuce.


Saida yafara tsayawa yay isha’i a masallacin anguwansu sannan yafito yawuce gida bayan ya dauki su Hamza da Abdallah daya gani amadallacin yana parking ribbon din kadai yadauka yaba Hamza key yace “ku kwashe fruits kukai ciki” yawuce babu kowa a falo hakan yasa yawuce sama ahankali yay sallama tareda bude kofan dakin Kausar tana zaune sanye da dogon rigan atampan ta mai kyau rubutu takeyi tadage ganin Abee yasa ta yarda biron ta tashi da sauri tace “Abee dana dawo daga kitso bakanan” tai maganan tana tafiya wajenshi dan yana tsaye gaban dakin, ganin yana kallon kitson da aka mata yasa tawashe baki tace “kitson yay kyau Abee” gyadamata kai yayi yace “sosai” ledan hannunshi yabata dasauri ta karba tace “meka siyamin Abee” ganin ribbons dayawa daban daban wani kalan ihu tayi ta rungumeshi tana tsalle tace “Abee thank you” dan murmushi yayi yace “saken kije kicigaba da assignment dinki, kinci abinci”? Gyadamai kai tayi tana kallon ribbons dinta hankalinta yay nisa awajen, fita yayi daga dakin zuwa nashi.


Wanka yayi shayi kawai Hajiya ta aikamai dan tasan yanda dare tayi bazaici abinci ba, zama yayi yanashan shayin yana tunani na farko babu anything like sex dayayi so wanan ma is off list, nabiyu this so called guy dake blackmailing nashi employee nashi ne and when something happen that has to do with employee naka you need to handle it with lots of precaution, he will try his number again tommorow yaga how things goes.


Washegari yay dialing number still akashe ganin har yamma still babu komi yasa ya tattara komi ya watsar dan in the first place yasan babu wani sex video ballema har ayi leaking nashi a online.


Yau monday as usual bayan breakfast kowa yakama gabanshi Abdallah tareda Kausar suka tafi school dan lecturer su nasafe yace baida lpy bazai zoba, Hamza ya sauke yara yawuce shima Abee yashirya cikin wani Italian suit black dayamai kyau bana wasaba hannunshi daure da rolex, yana kaiwa company abinda yafarayi was yashiga office na HR amman seat na guy din empty bai zuwa wucewa office nashi yayi dan yanada ayyuka dayawa dazaiyi.



Wuraren 10 aka fita break kowa na ajinsu SS2A yafita banda ita dake zaune tafito da duka abubuwan da Gwaggo tazuba mata a jaka tanaci one by one, tana cikin cin egg and chips princess tashigo class din da ita da Lily dawasu maza guda biyu rike da goran drinks a hannunsu kallo daya tamusu tadauke kai ganin sun dumfarota tacigaba da cin abincinta gabanta na faduwa ganinsu su kusan shidda amman bata nunaba Princess na karasowa gabanta batai wata wata ba duka kayayyakin abincinta tawani barar dasu dayasa Lujain tamike tsaye dasauri tana kallon Princess da some much anger tace “mehaka princess”? Wani mugun kallo princess tamata tanuna kanta tace “kinganni Miss Chubby, kinga Lily we can proudly say eh munji muna chokes dasauran su but I can assure you this muba yan iska bane, our vaginity is intact unlike you dakin saba har kin iya moan” wani kallan kallo Lujain tamusu tace “me akace miki nayi I don’t understand ni kike kira da yar iska”? Wani murmushi princess tayi Lily ta tofar da miyau agefe tace “you disgust me Lujain you look so innocent babu wanda zai miki kallon karuwa sabida yanda kika kware a pretending” Lujain zatai magana Princess tace “kola play the video for her” dasauri Lujain takalli Kola dake danna wayanshi yana chewing cingum abaki kaman dan daudu saiga muryan Lujain tace “wayyooooo, Hmmm, Hmmm, hmmmm” hmmm hmmm din was repeating babu kakkautawa da karan buga kofa babu wani baligi mai hankali da zaiji da bazaice Iskanci akeba, Kola da abokinshi sukahau dariya Kola yace “Ashedai Fatty bombom tasan dadi kizo muyi dake I promise zan saya miki 5 shawarma da chocolates goma expensive ones ba irin na yan 500 din nan da kike zuwa dashi school ba” dukansu sukahau dariya princess tace “karuwa kawai mai gindin roba” baki Lujain tabude zatai magana kawai taji saukan drinks masu sanyi ana tsiyaya mata akai har zuwa jikinta princess tace “bari mu miki wankan tsarki da drinks” daidai nan Principal tashigo class din dakusan all the school teachers biyeda ita abaya.
EPISODE 🔟


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Zaro idanu Principal tayi ganin yanda suka watsa mata drinks sun mata wanka sun bata mata jiki gabaki daya tace “what in God’s name is this Kola and co?” Da sauri duk suka wurgad da gorunan kasa, Principal tace “to disciplinary office now!” dasauri suka fita sannan takalli Lujain wani irin kallo da Lujain takasa fassarawa koname tace “come with me” ahankali ta tsugunna ta dauki jakanta dake tsiyaya da drink ta kakkabe jikinta tabi bayan principal faran safan kafanta har tusan ruwa yake sabida yanda drinks suka jikashi teachers nasu na kallonta wani kalan kallo tawucesu ahankali suka rufamata baya suna fitowa taga student an taruuuu kawai kallonta akeyi kaman yau aka fara ganinta a school din aka wuce da ita saikuma chan taji student na murmuring “God forbid, ewwww wasu na cewa na karuwa” har zuwa office na principal suka shiga principal ta zauna akan wani kujera tanuna mata wani waje teachers kuma suka fita, anatse principal din na kallonta tace “a ina kikasan Alhaji Imran”? Zaro idanu tayi tace “na’am waye Alhaji Imran”? Dan to be honest bamata gane kan maganan ba, ahankali Principal tace “mai company ceramic, at first da aka fara fadamini awaya I thought maybe forcing naki yayi he took advantage of you but after watching the video…….” Principal tai shiru daga gani kasan maganan namata nauyi tace “after watching the video I understood komi yafaru ne with your consent dan is so obvious, ni baran wani iya cewa komiba dan you have your rights as an adult data wuce 18yrs you are 19, keba minor bace, all I will say is have this” tamika mata wani takarda ahankali Lujain tasa hannu takarba ganin letter na susupension yasa dasauri takalli principal din, Principal tace “I believe guardians naki are on their way right now tun dazu muka kirasu wata tsohuwa da farko damuka kira mukaji, hakan yasa muka dauki second number wanda yacemana shine mahaifinki yana hanya” shiru Lujain tayi kawai tana kallon letter ita she don’t even know what’s happening.


Suna parking Gwaggo data gama rudewa tace “Ya ubangiji kasa ba ciwon yarinyar nan bane yatashi ba Wanan damai makarantan takirani gabaki daya” fitowa Baba yayi tareda Mama dasukai gaba daidai lokacin wayan Baba yahau ringing anatse yace “eh muna makarantan yanzu, tom saikun karaso” dasauri Gwaggo tace “waye?” Ahankali yace “Abdulhadi da Yusufa ne” fashewa da kuka Gwaggo tayi tace “kafadamin gaskiya kodai Lujain dina tamutu ne wanan dahar ka kira kannenka suzo nan iyye kafadamin gaskiya” ja idanun Baba sukayi yakalli Mama yace “kujirani anan bari na shiga” Gwaggo na kuka sosai tace “wlh kafanka kafana kaida matanka damai makarantan kunki fadamin abinda ke faruwa saikuma kuhanani shiga wlh saina shiga” dan jim Baba yayi yana kallonta saikuma yace “muje” dasauri Gwaggo tabishi tana goge hawayenta da bakin zaninta data warware har zuwa principal office suka shiga, ganin Lujain zaune nata kallon takardan da aka bata yasa ta taho dagudu tana shafa fuskanta tana bude mata idanu tabude bakinta tana kallon da duba harshenta danta gane ko rashin lafiya take tace “Alhamdulillah babu abinda yasameki yarnan Iyyee Alhamdulillah wayyo Allah zuciyata kubani ruwa Insha” dasauri principal tabata ruwan gora budewa Gwaggo tayi ta kwankwade tass sannan ta zauna Baba batare daya kalli Lujain ba yace “gamu principal” ahankali tace “ba babanki takardan Lujain” ahankali Lujain tamikama Baba takardan fuskanta yakalla da jikinta daya baci da drinks da jakanta dahar lokacin na diddigan ruwa sannan yasa hannunshi ya amsa ya karanta yakalli principal din harzaiyi magana saikuma yatashi tareda kama hannun Lujain yace “muje” tashi principal din tayi tace “kuyakuri sir bazan iya barin yarinyar ku tacigaba da karatu anan makarantan nan ba she is a bad influence zata batamini sauran dalibai kuya kuri babu abinda zan iya” sai alokacin Baba yakalleta yace “akwai abubuwa da yawa da zaki iya na farko shine kare hakkinta jibi yanda akama y’ata wanka da drinks sabida kunga batada kani ko Yaya amakaranta kobaki koreta bama nixan cireta daga makarantan, inaso kisan abu daya, akwai Allah! Sannan zai wanke mini diyata agaban kowa muna nan zakusan you all have wronged her” yaja hannun Lujain dasauri suka fita tashi Gwaggo tayi tana kallon Mama tace “ke Maman su Samira me akace tayi ne kifadamin” chak Mama ta tsaya kaman jira take tace “yarinyan dakike mana tunkaho da ita kina fifitata kan nawa yaran video dinta dawani kato dasukaje excursion akafaninshi na yawo a yanar gizo suna fasikanci sun shiga bayi yana dugurguzanta diyarki na ihun dadi” wani kalan zaro idanu Gwaggo tayi tace “mene shairin kine dai ko” wayanta Mama taciro anan office an principal takunnama Gwaggo video tundaga lokaci da Abee ke kokarin kwance belt har zuwa lokacin daya shiga bayi ga muryan Lujain nan dako amarfi tasani tai ihu wayyooo saikuma uhmmm Uhmm uhmmm saikuma chan aka nuno Laujain tafito corridor tana gyara riganta tajuya dasauri ta tafi tunda Gwaggo take bata tabajin tashin hankali hakaba baya tayi zata sume dasauri Mama ta tarota tace “ni kada ki sumemin yace dagangan na nuna miki inason kashemai uwa mutafi” takama hannun Gwaggo tanaja suka fita awaje taga duka yaranta da Yusuf da Abdulhadi dukansu suna sanye da manyan kaya sai Yayanta sunyi jugum suna kallon Lujain da idanunta sunyi ja ganin Gwaggo tafito anriketa yasa tai wajen Gwaggo da sauri saiga hawaye, zaunawa Gwaggo tayi akasa tana zaunar da Lujain bata damu da yan makaranta ba tanuna kanta tace “Lulu tun kina cikin kwalban asibiti nake rainanki nasanki ciki da bai nasan halinki tsaf amman bansan ki da Iskanci ba kifadamin gaskiya meyamiki kike ihu” zaro idanu tayi dukta rude tace “waye? Wani ihu Gwaggo”? Wani kalan fizgota Baba yayi cikin ihu kaman zai mareta yace “ranan dakukaje excursion me mutumin nan yamiki abayi kike ihu”? Jikinta har rawa yake ganin Baba na shirin dukanta tafashe da kuka tace “wlh babu komi Baba” Baba Abdulhadi yace “to ubanme aka miki kike ihu”? Cikin kuka sosai tace “Baffa wlh naje bayi na kalli video wan nan dan kwallon Mandawari ne awaya” kusan dukansu atare sukace “a ina kika sami waya”? Cikin kuka sosai tace “wajen Ya Samira na ara bayan nabiyata da kudin asusu na” Baba yace “saime yafaru”? Cikin kuka sosai tace “ina zaune kan masai nasa earpiece a kunne kawai naga mutum yashigo yana kokarin cire wando” dukansu sukace “Meya miki kike ihu” jikinta har bari yake tana haki tace “wlh babu abinda yamin tsoro naji nadauka aljani ne saisa nadinga ihu na manne jikin kofa shine yamin ihu yace nafita nace ban iya bude kofaba shine yace na matsa yabudemin na fice yay min ball da jaka da wayan Ya Samira harta fashe na kawasa na tafi shikenan” kaman jira Mama take tace “wlh wlh karya kike ke yanzu ki kalli tsabaragen idanun Babanki da Baffan ki kina karya, kifadi gaskiya tun yaushe kika fara iskanci eh? Daman naga gabobin jikinki sai kara habbaka suke waya koyamiki? Wayake matseki? A ina kika sanshi dahar kuka hadu abayi yaushe kika dawo Yar iska mayyan maza Lujain”? Wani kalan fashewa da kuka sosai Lujain tayi tama kasa magana sabida yanda kukan yafi karfinta jin maganganun Mama, tashi Gwaggo tayi tana kakkabe jikinta takalli Baba tace “ku kaini kampanin yanzun nan” kallonta sukayi duka cikeda bala’i tace “ku kaini kampanin nan Kona tare abin hawa nakai kaina, koya mata wani abu kobai mataba bai isa tasanadin shi a batamin sunan diya ba a yanar gizo duniya tagama ganinta, wlh wlh yau sai anyita an kare” Baffa Abdulhadi yakalli Baba yace “Baba dole dama muje muganshi idan ma za’a kai kara hukuma ne asan nayi kumuje” Ahankali Baba yabude motarshi suna suka bude tasu aka shiga har akakai company nan kuka Lujain takeyi sai yanzu tagane abinda yasa su Princess suka kirata har karuwa dudda bata kallo video ba suna kaiwa company reporters dasuka gani agaban kampanin sunfi hamsin saukowa akayi Gwaggo takama hannunta suka wuce ciki ganin ana musu hoto mayafin jikinta tayaye tayafama Lujain dake kuka tarike hannunta sukai wajen shiga taresu security yayi Gwaggo da idanunta sukai jajir tace “na rantse maka da ubangiji zan tube nai dambe dakai awajen nan kace bazamu shiga ba, dan ubanka Mudi da Uwarka Safara’u idan akai kokarin batama jikanka suna bazakayi abinda yafi haka ba budemin kofa kona fasa” girgiza mata kai yayi yace “Mama Oga yace ba shiga ba fita bakiga yan jarida sun cika nan ba” cikin ihu Gwaggo tace “yo ina ruwana shi yasan Meyayi ai” jin yanda Gwaggo ke ihu Hamza da idanunshi sukai jajir yazo wajen daga ciki ganin student din makarantan nan da aka lullube da mayafi tana kuka sosai from yanda jikinta ke bari ga wayanda ke tareda ita dazai iya cewa iyayenta ne yasa ahankali yace “kushigo” bude musu kofa akayi Gwaggo taja hannun Lujain suka shiga ciki, waje yanuna musu awajen yace “ku zauna bari naje na sanar” cikin ihu Gwaggo da idanubta sun juya tace “nabaka minti biyu” stairs yayi karo yaci da Ibro da shima idanunshi sunyi jajir yana kallon su Gwaggo da yarinyan dake sanye da uniform da aka lullube da gyale ahankali Hamza yace “I think is the girls family ka kira Uncle Musty” gyadamai kai yayi yace “yama iso he’s trying to come inside” daidai lokacin wayanshi yahau ringing dasauri Hamza yace “Hajiya ko” gyadamai kai yayi ahankali, hawaye ne yakawo idanun Hamza dan he’s a very soft person yace “kana tunanin tasani” gyadamai kai yayi yace “kaima kasan that’s the only answer to yanda taketa kiranmu tun dazu clean those tears if our workers saw that kanason suyi tunanin Ya Imran zai iya aikata abin ne” girgixamai kai tayi daidai lokacin Musty na sanye da kayan sojoji da Haruna dakuma wani babban abokinsu police man su uku suka taho ganinsu yasa Musty yace “calm down you all Ya Imran din”? Ahankali Ibro yace “yana office working as if nothing is happening amman nasan deep down he’s hurting bama wanan ba Uncle Musty I believe the girl’s parent are here gasuchan” yanunasu ahankali Uncle yace “Innalillahi wa innailaihi raji’un! Allahumma ajirni fi musibati” yakalli hannu da police man yace “kuje ku kutaho dasu lemme see him” yana maganan yawuce sama su Hamza suka bishi ahankali yabude kofan office din Abee, kallo daya Abee yamai yacigaba da aikin dayakeyi bazaka iya gane takamaiman reaction dake kan fuskanshi ba karasawa gaban table din Musty yayi ahankali yace “the girl’s parents are here” chack ya tsayar da typing din dayakeyi batare daya kalli Musty ba, anatse Musty yace “nace su Harun su taho dasu nan we need to speak to them and show them, but maisa baka fadamin komi ba eh Imran” dago idanunshi Abee yayi yama Musty wani kallo yace “me kake so nagaya maka takamaimai nace maka wani anonymous number sent me a text demanding 100M and this company’s document koyay

Please Login or Register in order to submit comment