Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne da nasara da alama, rahama ce tayi caraɓ tace
"kar dai kuyi saurin yanke hukunci Kun manta wacece GIMBIYA d aalama da kuma iya faɗan t yaran sarakuna nawa ta gagaresu bare wannan ba ɗan kowa ba"
dariya bintalo da lubcy suka sanya harda tafawa, wai wa ya gaya maki abun daga kai ɗan wane ne? Abun baiwa ne rahama staya kisha kallo...

Sauran jama'an kuwa sai cewa suke "GIMBIYA" "GIMBIYA" "GIMBIYA" "GIMBIYA"
Sunansa da aka qira ya qara ɓatawa Gimbiya rai, sara ta kawo masa ta yacce ko taji masa ciwo ba ruwanta damuwan ta kawai ta kaisa qasa, fusatan da tayi hakan ya masa daɗi dan tana kawo sara da dukkan qarfinta ya shammace ta ya kauce, kamun ta farga sai jinta tayi a jikin mutum, yana qoqarin kai hanunsa ya kama abun fuskanta dan ya warware..
Wani zabura tayi tabar jikinsa zuciyanta na qara zafi, "har shi wa zai taɓa jikina? Waye shi da zai yi qoqarin kai hanunsa fuskana, lallai sai na nuna masa bai da wannan jarumtar kuma sai na masa hukuncin taɓa jikina" tagama saqa maganan ta a zuciyan ta, sai ta ɗago ta kalli idonsa, shima kallon ta yake idon su na haɗuwa ya sakar mata murmushi mai cike da ma'anoni da yawa wanda ko ita kanta bata iya fassara wa ba, kau da kai tayi ( Amma daga gani dai murmushin na mugunta ne).
Ihu jama'ar wannan wajan suka sanya , Sarki har da Murmusawa yayi ko ba komi yasan wataqil wannan ne mijin tilon ƴar tasa.
Umma ba abinda take sai murmushi cewa take "tabbas ina alfahari da kasancewa ta uwa ga wannan bawan Allah, Allah yai maka albarka jarumin Umma" Abba dake gefen ta shima murmushin yayi yace "Ameen maman Amjad"
Runguman nan fa ya sanyawa gimbiya jin wani iri ta stinci kanta a yanayin da bata san mai yake nufi ba, haka gogan naku ma. Duk wannan abinda suke ji bai hana su cigaba da fafatawa ba, fafatawan da yafi na farko armashi kasancewar Gimbiya na fusace shima Amjad da abun da ya taɓa masa rai, kai masa wani bugu tayi wanda garin ya kauce saura kaɗan ya fadi har dai sanda ya sa takobinsa ya tare shi yahanasa kai wa qasa, harta fara jin daɗin ta kai sa qasa sai kuma murna ya koma ciki ganin ya dawo ya tsaya da qafafunsa cak. Stiririn staki taja wanda dagani sai ita muka ji sa!
Ganin yana kallonta, hakan yasanya ta lumshe ido tabuɗe su akansa, sai idon nata yayi kaman mai jin bacci, kallon wannan idon da yanayin da ta sarrafa sa in bakada qarfin imani zaka mance ko hanyan garinku, takuwa ci nasara dan tabbas hakan ya haifar masa da qaruwan yanayin da yake ji wanda wannan yanayin haushin sa yake, wannan qaramar yarinya bata isa sashi jin wani abu ba.
Yi yayi kaman ya biye mata yacce take so, tana shammatan sa ta kawo sara, yayi caraɓ ya buge takobin nata da nasa wanda ya sanya duka tokubban nasu faɗuwa, ɗayan hanun sa ne ya fara warware abun fuskan nata
( ɗazu daya rungumeta bakin abun da tayi rolling a fuskan ya nemo) abun na fara warware wa ta ɗauke wuta gaba ɗaya, dai dai abun ya ciru duka tayi Suman wucen gadi, wanda hakan ya sanya qafanta ya kasa ɗaukan ta tayi baya luuuuuu zata faɗi. Hanun da ya sanya a bayanta dan taro ta kar ta faɗi, kaman wanda aka jonawa shocking haka tayi qasa shima ya bita, a samanta ya faɗo, fuskansu ya haɗe.
Wani qara da ihun da aka sanya da shewa ne ya fargar dashi mai yake shirin faruwa (jarumin umma ya mance da ummansa awajan, wani abu sae mace).
Gimbiya Mehwish gaba ɗaya ta qarisa sumewa,
Sarki da sauran jama'a kowa kallo kawai yake yayin da gefen Umma inbanda murmushi ba abunda take yi, mai martaba gaba ɗaya yafi kowa jin farinciki a zuciyansa ganin dai wanda yake kyautatawa zaton ya lashe gasar.
Har zai yunqura ya miqe sai kuma kaman an sanya shi ya rasa meya jashi Kawai ya sumbaci qaramin bakinta mai ɗauke da pink lips nata da tunda ya janye abun fuskan nata bakin kawai yake kallo.
Sumbatan da ya mata ne yayi nasaran farfaɗo da ita daga wannan suman da tayi, tana buɗe idonta sai ya haɗe da nasa, tashuwa yayi ba tareda neman shawaranta ba ya kama hanunta ya tayar da ita. Haushin da take ciki qaruwa yayi ya linku Ji take kaman ta sare masa kai ta huta, Mutuwan jikin da ya same ta kuma ya tafi.
Duk ɗauka cin jama'an dake wannan fili kuwa sai faman kulle ido suke suna qara buɗewa dan tabbatar da wannan mutum ce agabansu ba aljana ba. Hatta mai martaba sai yake ganin kaman ansauya masa ita.
Umma da ke zaune miqewa tayi tana kabbara da hamdala faɗi take "Allahu Akbar Allah Alhamdulillahi Allah yasa kyawun ki har halinki haka yake Alhmdlh"
Shima Amjad kaman kar yabar kallonta yake ji, amma sai ya basar ya fita a filin lokacin ne nasamu daman kallon fuskan GIMBIYA MEHWISH..
Fara ce irin fari mai ɗaukan idon nan bazaka ce yellow ba bazaka ce ja ba, tana da dogon hanci siriri fiye da hasashe dogon hancinta da madedecin bakinta waɗanda suka yi dai-dai da round face nata, idanuwanta manya ne dara-dara, farin idon ta tsabar farin sa har kaman kwantaccen hawaye blue blue a ciki sai qwayan idon nata wanda yake blue blue shima ba har can ba, a maimakon yawanci na wasu da ya kasance baqi, kyakkyawa ce ta ajin qarshe zayyano kyau da haɗuwa irin na wannan Gimbiya zamu kammala labari a zayyano kyawun ta kawai.

"𝙈𝙖𝙨𝙝𝙖 A𝙡𝙡𝙖𝙝" "𝙈𝙖𝙨𝙝𝙖 A𝙡𝙡𝙖𝙝" "𝙢𝙖𝙨𝙝𝙖 A𝙡𝙡𝙖𝙝"
𝙁𝙖𝙩𝙖𝙗𝙖𝙧𝙖𝙠𝙝𝙖𝙡𝙡𝙖𝙝𝙪 𝙖𝙝𝙨𝙖𝙣𝙪𝙡 𝙠𝙝𝙖𝙡𝙚𝙚𝙦!!

<~Ni harira bazan iya zayyano kyawun wannan baiwar Allah ba. Dan ta haɗu har ta gaji da haɗuwa fiye da tunani, da ace mutum ke halittan kansa tom tabbas wannan zamuce ta so kanta. Amma Ubangiji ke halittan komai da kowa yacce yaso kuma Yacce yaga dama.
Masha Allahu starki da yabo da godiya da kuma jinjina su tabbata ga Ubangijin dake halitta komai yacce yaso wanda yai halittu daban daban, Allah qarawa annabi daraja SAW~>

Hancinta dogo har kan bakinta, daga gashin da suka kwanta a gaban goshin ta da kuma sajenta zaka gane cewa tanada stawon gashi. Da mayafin nata ya zame duka gashin nata da ta nannaɗa shi bayyana yayi ya sauqo har gadon bayanta, baqiqqirin gashin nata ga kuma laushi daga gani.
Abun yafawan nata ta ɗauka taja ta yafa ta rufe har fuskanta amma ba kaman da farko ba, dan ajikinta take jin yacce idanun mutane ke yawo ajikinta, idanuwan ta har kwalla ya cika dan batason yawan kallo.
Hadimanta ne suka yi saurin xuwa suka yafa mata alkyabba, dokin da yake na hawanta akazo dashi wajan ta hau, dokin ya ɗau hanya.

Sarkine ya tashi fuskansa cike da fara'a kana ganin sa kasan yana cikin farin ciki!
jawabi ya fara kaman haka
"kaman yacce na faɗa tun farko zan baiwa duk wanda yaci nasaran buɗe fuskan Gimbiya Auran ta Insha Allahu, sannan zan basa kaso 1 cikin kashi 4 na dukiya na, Auran kuma zai kasance nan da wata huɗu 4 in Allah ya yarda"
Shewa wajan ya ɗauka da tafi masu taya Amjad farinciki nayi masu jin haushin sa na ji, Umma dan farin ciki ta kasa yin komai kawai bin komai da ake yi da ido take haka ɓangaren Abba ma sosai yake taya ɗan nasa murnan wannan gasa da yaci.
Mai martaba ya buqaci da a bawa Amjad abun magana ko yana da abun da zai ce.
Har inda yake zaune aka miqa abun maganan gare sa da girmamawa.
Karɓan Miche yayi (abun magana) ya miqe staye, gaisuwa yayi cikin girmamawa zuwa ga mai martaba, sannan da sauran jama'a manyan baqi na qasashe daban-daban da kuma na qasan Qatar da sauran mutanen wannan Masarautan. Ya qara da godiya ga Allah da ya basa ikon nasara.
"Ina mai matuqar Godiya ranka shidaɗe Mai martaba, ma amsa batun aure hannu bibbiyu Insha Allahu, amma ina mai neman afuwa a maganan da zanyi, ba wai ina nufin maida hanun kyauta baya ba Allah ja kwananka, Nagode sosai amma maganan dukiya amun afuwa da aikin gafara na yafe Allah saka da alheri ya kuma saka da Aljanna."

Ba Sarki kaɗai ba kowa dake wajan cike da mamaki suke kallon sa, suna qara buɗe kunnen su dan su tabbatar da gaske ne abinda suke ji, Abba dai bai yi mamaki ba dan sarai yasan halin ɗan nasa, haka Umman sa murmushi kawai tayi wanda ke ɗauke da ma'anoni da yawa, albarka kawai take sawa ɗan nata. dama tun can damuwanta ɗan ta yayi aure bawai kuɗi ba, kuma tasan ko anbasa bazai amsa ba.
Wannan abu da Amjad ya faɗa ya qara sanya Sarki cikin kogin farin ciki dan tabbas ko ba'a faɗa masa ba yanzu yasan ƴar sa tasamu miji Insha Allahu kuma ko bayan ransa yasan wannan bawan Allah zai riqe wannan gari cikin Amana, ba qaramin qara burge Mai martaba Amjad yayi ba.
Mai martaba yace "maganan dukiya alqawari ne acikin sharruɗan gasa amma duk da haka ba komi Allah ya maku albarka duka Allah nuna mana lokacin bikin da rai da lafiya, sannan zaka iya fara zuwa wajan gimbiya dan qara dedeta kanku kamun ranan biki. Baqin mu na nesa da kusa muna matuqar Godiya da halartar wannan taro da kuka yi ina mai roqon Allah subhanahu wata'ala da ya maidaku qasashen ku, garuruwanku, da gidajen ku lafiya."
Sarkin shela ne yaci gaba da jawabi da kuma godiya ga jama'a. Da kuma qara gayyatan su zuwa ɗaurin auren Gimbiya da yariman gobe inshà Allahu nan da wata huɗu.
Manyan baqi da sauran jama'a sai taya sa murna suke suna tayasa godiya.
Cike da farin ciki sarki ya haye dokin sa suka yi hanyan fada shi da fadawan sa, da sauran manyan baqi waɗan da ba ƴan garin ba.
Ƴammatan wajan kuwa waɗan da suke crushing akan Amjad sai suka fara jin kishin Gimbiya, dan tunda suka qyallare ido suka gansa duk yawanci su suka qyasa, sauran kuma dama suna kallon sa wani bin a kasuwa.
"Alhamdulillahi ni bintalo addu'a ta ta karɓu, Allah ka gani ina taya wannan bayi naka farinciki dan tabbas sun dace da juna Allah ka kare su daga sharrin masu sharri" bintalo ta faɗa hannun ta a sama!
Rahama tace "kai amma dai bintalo aiki ya ganki sai kace qannin ubanki ne shi lallai sannunki"
eh anji imma ba qanin ubana ba ai ɗan uwa nane musulmi, kuma dai dan kiji shi Hassada ba hali mai kyau bane ko kafuran zamanin Annabi SAW haddasa suka masa dan tabbas sun san shi Annabi ne, dan haka ina rabaki da abinda Annabi ya hanemu da yi, Ni dai alhamdulillahi har raina ina taya su duka farinciki both Gimbiya da Yarima Amjad insha Allahu, nan da wata huɗu kuwa har da ankon biki zamuyi, ko ba haka ba lubcy? Ah sosaima bintalo insha Allahu zamuyi anko Allah nuna mana da rai da lafiya. Rahama ko qala bata qara cewa ba tayi gaba, bintalo bin ta suka yi dan su wuce gida duka.
A hankali a hankali ake ta wastewa a filin kowa na kama gaban sa
Umma da Abba sun lelleqa basuga ɗan nasu ba, báko shakka sun san gida ya tafi dan haka suma suka kama hanyan komawa gida.
Fili ya waste shall kaman ba'a yi taro a wajan ba kowa ya koma gidan sa.



𝙆𝘼𝘿𝙐𝙉𝘼

Zaune suke a palourn har da Umma suna fira, Little dai na maqale da Maha. Ameera ce ta sauqo sanye take da mayafi, da alama zasu koma Abujan du yau ne.
Waje Ameera ta samu ta zauna jin hiran nasu sai ta kama dariya, duk sai suka zuba mata ido har dai Daddyn Little, mamaki suke dan su dai sun rasa me yasa ta dariyan.
Ummace tace " ke lafiyanki kuwa? Dariyan me kike?" dariya ta qara fashewa dashi "
Wallahi Lafiya ta lau Umma, kawai ina tunanin wannan irin zazzafar soyayyan dake tsakanin Habeeby da Maha ne, yafa kamata ayi gaggawan haɗasu a Aurar dasu in ba haka ba soyayyan zai fi haka, dubi fa yacce basa kunyan kowa ko a ina soyewa suke" ta faɗa tana dariya.
Haɗe rai Autan Umma yayi! Ita kuwa Maha turo baki tayi, tace "Ummata ki faɗawa aunty banaso, Ni mema zan yi dashi caɓɓ"
Ummace tayi murmushi tace "yi shiru abinki ki qyale ta ai kinfi qarfin sa, daughter na sai mai gida da motor da jirgin sama". Mai zasu yi a palourn in ba kwashewa da dariya ba, Mahreen har da kama ciki.

Daddyn little ne yasa baki, haba dai Umma ke da zaki ce tayi sa'a ma zata Auri soja ɗan fari kyakkyawa kuma Autan Abba, ai Umma kin sai dai Auta duk yana da abubuwan da kika lissafa. Mahreen ce tace "yauwá dai uncle faɗawa Umma ya habeeby kam in baice yafi qarfin wannan mara jin ba ita bata isa tace tafi qarfin shi ba ato"
Harara soja ya gallawa Ameera, in an rainani ma kece kika jamun, kuma ki kaita ki barota nikam bulale ta xanyi sai tayi jinya ta san halina.
Ameera qunshe dariyan bakinta tayi, Allah huci zuciyan angon Maryam sai ta kuma sa dariya!
Allah shiryaki Ameera yanzu zaki haɗa mun yara faɗa aka taɓamun yarinya akanki zan rama mata, maza tashi ki barman gida.
Tashuwa habeeb yayi ya nufi hanyan fita a palourn yana cewa "in kin gama haɗamun renin sai kuzo na kaiku airport en akwai inda zanje" ya faɗa ya fice a palourn.
Miqewa Daddyn Little yayi, Umma kina koranmu ba mu tafi muma, waje ya nufa yana murmushi! Ameera kam dariya take yi, tana cewa "Umma Autan kin nan ya renani ya rena inda na zauna ki koramu shima ya wani ce wai yana da inda zai je, inda zai je ya wuce hira cikin palourn Ummata wajan qanwaty Maha, Allah Umma yaronki yana ga kaman yanzu shine babba, baisan dai duk girman sa Ni auntyn sa bace" ta faɗa tana miqewa. Rataye jakanta tayi ta gyara mayafinta har yanzu murmushi ne a fuskan ta!
Murmushi kawai Umma tayi tace "duk kunfi kusa nice bare tsakanin ku ya rage maku Ni dai adaina takuranmun daughter".
dukansu miqewa suka yi suka nufi waje, sun samu habeeb da Daddyn Little already suna cikin motorn fitowan Ameera kawai suke jira. Har bakin motorn suka rako Ameera ta buɗe gidan baya ta shiga gefen mijin ta, ta zauna. Miqawa Little Hanu tayi my boy zo mu tafi, maqale kafaɗa Little yayi, ya qara qanqame Maha.
Kamun kowa ya ankare ko ya kula sai aka ga Maha da Little maqale a gaban Motor, Juyowa habeeb da ke zaune mazaunin driver yayi, ya kalleta yace "ki fitamun a motor ni ba sa'an yawo dake bane, hararan gefe Maha tayi, shide little bai san menene ba yace "unkui damu fika nida anci na" ya faɗa yana washe bakin sa
Habeeb ya buɗe baki zai yi magana Umma ta kallesu duka tace "kul ya isa kuje kawai Allah tsare hanya ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, su kuma Allah stare masu hanya" Suka ce Ameen Umma.
Jan Motorn yayi da gudun gaske suka fice a gidan, Umma da Mahreen na ɗaga masu hannu, bayan fitan su suma suka juya suka koma cikin gidan.
Komawa palourn Umma da Mahreen suka yi, Umma tace "daughter yaushe zakuje wajan Amarya? Umma zamuje wataqila nan da sati kamun nan mun huta, Muje muji rigiman kakus.
Dan qwalo Umma ta mata, kun raina mana uwa ko..
---
Har airport suka kai su Ameera, ganin jirgin nasu ba yanzu take zai tashi ba, sallama suka masu da addu'an Allah stare hanya ya kai su lafiya, Little har dashi a masu bye bye ba ruwan sa yana jikin Maha.
Bayan sun baro airport, juyowa habeeb yayi ya kalle ta yace "saura kuma naje dake wajan abokai na kimun fitsara agabansu mu koma gida jikinki ya faɗa maki." Turo baki tayi tace "haba dai yah habeebu Nifa ina da hankali, ba kaman sojoji ba. Su sojojin mene rashin hankalin nasu? Tun anan zaki fara kasa hali ko hmmn. Ina soja yaga hankali yah habeebu in zaka faɗi gaskiya, Haka dae suke ta rigiman su a motorn Little kam baccin sa yake sha ajikin mummyn sa Maha.
Direct eatery suka yi, saya masu icecream, shawarma da chocolate yayi, Maha dai ta kwashi tarkace don Little yana bacci.
Bayan sun fito wajan sayayyan nasu wuce wa wajan abokin nasa suka yi. Da suka isa fita yayi a motorn suna gaisawa da abokin. Man wannan ce amaryar tamu kenan, irin dacewa haka kallifa yaron sai yayi kaman naku. Hararansa yayi in kasan renani da yarinyar nan tayi bazaka ma haɗani da ita ba Man, kasan rashin jinta kuwa, ba inda zankai wannan yarinya qaramar.
Shikkenan aboki in baka ciki ni amun hanya kawai na shiga layin masu nema, dan tabbas tamun.
Hararansa yayi, ya ɓatar da maganan
Suka yi sallama ya shige motorn yaja, bai bari ko sunyi magana ba.

Gida suka koma ita kamma bacci tayi a motorn, ga little ma na baccin sa.
Kallonta yayi ga yarinya dai kyakkyawa da fuskan innocent girls amma rashin kunyanta ya fita shekaru.



-------------
Mai martaba sun koma fada ankai manyan baqi masauqi.
Ya umurce waziri da a aika aqira masa wannan yaro da yaci gasan, acikin baqin kamun su wuce gobe akwai masu buqatan haɗuwa dashi. Waziri yace "Tom shikkenan ranka shidaɗe, Allah ja kwanan mai martaba Allah gwada mana goben da rai da lafiya" da Ameen Sarkin ya amsa.

Gimbiya gaba ɗaya tun barowan ta wajan gasan jikin ta yake mace sai dai ta rasa dalili kwata kwata batajin haushi ko wani abun gatanan dai kawai, wanka tashiga a wajan wanka ta dirje bakinta har kaman zai ɗaye abinka da farin fata ga laɓɓan nata pink, ta dirje har kaman zata yi kuka dan ko ya ta rufe ido ganin kaman a lokacin ya sumbace take.
Gaba ɗaya ta rasa nustuwanta, qarshe haka ta fito toilet en ta kwanta ta zubawa saman ɗakin ido.
Tana cikin wannan halin jakadiya tayi sallama a qofan ɗakin nata, bargo taja ta rufe jikinta kamun ta amsa Sallaman, shigowa jakadiyan tayi kanta a qasa tace "ranki shidaɗe mai martaba ne yayi qiranki" tafaɗa tana qara qasa da kanta. Da Tom kawai Gimbiya ta amsa, jakadiyan ta tashi ta fice a ɗakin.
Tashuwa Gimbiya tayi ba dan taso ba ta shirya cikin dogon riga ta yafa veil nata har ta rufe fuskanta yacce ta saba kamun ya fito a ɗakin, a palourn ta ta samu jakadiyan da sauran hadiman ta, tana fitowa suna mata Barka da fitowa Gimbiya. Ko kallon su batayi ba bare su samu arziqin a amsa masu, tawuce tayi gaba hanyan da zai sada ta da sashen mai martaba ta nufa dan tasan yana can in dai ya qira ta haka baya wajan Ammaahn ta.

Da sallama ta shiga shashen mai martaba, kuyangu sai durqusawa suke suna gaida ta, ɗaga hannu kawai take musu ta wuce, ko da ta iso qofan palourn mai martaba kuyangun ta stayawa suka yi dan ba'a yarje masu shiga wannan palourn ba. Duk juyawa suka yi ta shige palourn, "Assalamualaikum" tayi sallama jin shiru ba'a amsa mata bane yasa ta tura qofan ta shiga ta samu waje ta zauna jiran fitowan mahaifin nata.
Tana zaune taji anyi sallama a qofan, amsawa tayi aka buɗe qofan aka shigo da mamaki ta ɗaga kanta dan taga waye ne???

Muje zuwa................



ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️


💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

💦💦💦💦💦💦💦💦

𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮

𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖

(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

_______________________________________________________________

🅿️ 33&34

💋💋 امى بتولة💋






Waziri ne ya shigo palourn, ganin waziri ne tayi mamaki amma sai bata ce komi ba. Gaida waziri tayi ya amsa mata da fara'a, yana mata sannu da gajiya, Murmushi tayi.
Waziri ya buɗe baki dan tambayan ta mai martaba sai suka jiyo sallaman sa, qarasa shigowa palourn nasa yayi ya samu waje ya zauna. Gimbiya dake durqushe a qasa ne tace "Barka da fitowa Papa" yauwá Gimbiya sannu da gajiya, amsawa tayi.
Waziri sauqa qasa yayi ya durqusa yana "Barka da fitowa
Mai martaba." amsawa Sarki yayi yace "Waziri lafiya kuwa?" Lafiya lau ranka shidaɗe ansanar da yaron saqon qiran da ka masa sannan kuma baqin nan wai in ba damuwa suna son magana da kai. Mai martaba yace "shikkenan a masu iso zuwa ɗayan palourn baqi, ina zuwa". Tashuwa waziri yayi yace "Tom a fito Lafiya Mai martaba" ya juya ya fice a palourn.
Duk zancen da Sarki da waziri keyi tana jin su sai dai kanta na qasa. San da waziri ya fita kamun ta ɗago ta gai da mahaifin nata, amsawa yayi cikin fara'a dan kana ganin fuskan mai martaba kasan yau cikin farin ciki yake.
"Gimbiya Mehwish ina mai tayaki murna a mastayina na mahaifin ki, nasan ko ban faɗa maki ba kema kinsan kinyi Sa'an abokin zama Insha Allahu, ko yau na faɗi na mutu Alhamdulillahi nasan wannan yaro zai riqeki ya riqe

Please Login or Register in order to submit comment