Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kallonta yayi har xeyi magana sai bece komai ba ya fita.
A jikin Motorn da zasu fita ya samu little na jiran sa yasha jamfa murmushi yayi yace "looking gorgeous my son"
Tacuu Unkui.
motor suka shige sai masallacin juma'a


__
Abba ke shiryawa dan zuwa masallaci ransa a ษ“ace ganin ko yaushe in zai fita tana taya sa shiri amma tun jiya tafiyan yaron ta daga ta zauna sai tagumi.
Kallonta yayi yace "maryama wai yau kam baza'a taya ni shiryawa ba kuma ansani a gaba da tagumi da hawaye mai yake damunki ne?
Ko duk kewan ษ—an nakine tun ba'ayi nisa ba?
Ajiyan zuciya ta sauqe, ba kewansa ba Abban jarumin Umma Kawai Inaji a jikinane kaman wani abu ya samesa, numfasawa Abba yayi yace "A matsayinki na uwa kike masa fatan alkhairy kinji koh karki biye zuciya ko sheษ—an addu'a kawai ya isar maki kinji maman amadu.
Lumshe ido Umma tayi tana ajiyan zuciya Insha Allah
Kallonta yayi ya girgiza kai dan tabbas yasan **labarin gizo bai wuce na qoqi**

Allah bai manta damu ba marayamatou nah tabbas haihuwa rahamane Amma rashin haihuwa babban rahama ne ( Allah najin kunyan wanda be bawa haihuwa ba kwata-kwata ranan gobe qiyama)
Share hawayen tayi, ta tashi muje na raka ka ta amsa hulansa tana sa masa.



Hijab Ameera ta sanya ko da tagama shiryawa, Daddyn little dake jiran fitowan ta, tana shiga Motorn yaja suka kama hanyan Asibiti...




WA KUKE TUNANIN DADDYN LITTLE YA BUGE?
ME MAGANAN DA ABBA YAI WA UMMAN AMJAD YAKE NUFI?
INA LABARIN AMJAD?
duk amsoshin wannan tambayoyi namu mai sauqi ne mu dai cigaba da bibiyan wannan labari mai suna
๐Ÿ‘‡
ฦณAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh๐Ÿ•Š๏ธ


๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹

๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎuka:-
08146292652
๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ.
09161720046
๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐Ÿ˜!!!

# ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ
# ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š &
# ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š

๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ

๐˜ฝ๐™ฎ

๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™–

(๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorl)

ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค

_______________________________________________________________



*Godiya mutanen amana tabbas sai daku Allah saka da alkhairyh*
MATAR RASHEED marubuciyar (BAQAR IZAYA) ALLAH saka da alkhairy nagode da gudumawan ki sosai sosai
* Am speechless dear ALLAH saka ya temakemu baqi daya*
*My heartbeat( UKHTY) nagode da qwarin guiwank da kuma addu'a yar uwa rabin jiki ALLAH de ya bamu sa'a duka Fatahn alkhairy a garemu Allah albarkaci karatunmu ya albarkaci result*
SIR (ABUBAKAR SADEEQ) CEO LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION
*ina matuqar Godiya da jinjina gareka ba gudumawan da kake bayarwa a garemu Allah saka da alheri Allah qara ษ—aukaka*


๐Ÿ…ฟ๏ธ 39&40

๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹


Maganin da Abba ya tura masu sunji daษ—in aiki dashi dan kuwa Ammaan ta na samun sauqi sosai sosai ba kaman kwanaki ba
Mai martaba yasa a fara shirin bikin Gimbiya wata 3 da ฦดan kai ya rage, sannan ya fara tura gayyata wa sarakunan garuruwa daban daban.



-----
bayan soja sun dawo masallaci wajan Umma ya nufa
Zaune take akan darduma tana jan carbi, ganin Autan nata sai ta shafa addu'an ta ajiye carbin. Zaunawa yayi a qasan ษ—akin ya naษ—e qafa ya zuba mata ido bai ce komai ba
Umma tace "ya akayi habeebyn Umma fatan an dawo lafiya?"
Lafiya lau Alhamdulillahi Umma.
Naษ—e darduman tayi ta cire himar duk yana zaune awajan bai tashi ba.
Kallonsa tayi da murmushi Autan Umma yau kuma nono zakasha ne?
Yace "uhmn Umma a'a na barwa wani Autan in kin haifa yasha"
Dariya kawai Umma ta sa haba dai Auta ai an rufe qofa kuma daga kai yanzu kam sai dai ku aifamun kai da Maha
ฦŠaure fuska yayi yace "Umma ni kar ma ki fara wannan magana".
Zaunawa tayi a bakin gadon ta tana murmushi tace "zo ka faษ—amun wa ya taษ“amun kai to"
Mastowa yayi ya ษ—aura kansa a cinyan Umman sa. Yace "Ummana me ya same ki? ฦŠazu na ganki wani iri Mai ya faru?"
Lumshe ido tayi! har cikin ranta tana jin qaunar yaranta sosai take son Auta shiษ—in kaman a tare zuciyarsu ke bugawa duk in abu ya dameta sai yaji a jikinsa kuma masa qarya bai da amfani, shafa kansa tayi bakomi Autan Umma, kawai Daddyn little ne yayi hastari ya buge wani bawan Allah shine sosai naji wani iri kaman wani nawa aka buge.
Ayya Umma tom ayi masa addu'a Allah ya basa lafiya amma kibar sa damuwa a ranki please!
Nan dai Umma ta sake ranta ganin ษ—an nata ya damu shima suka cigaba da hiran su ta ษ—a da uwa


^^^ ๐˜”๐˜ฆ๐˜ฉ๐˜ธ๐˜ช๐˜ด๐˜ฉ ๐˜ช๐˜ด ๐˜ข ๐™ฅ๐™š๐™ง๐™จ๐™ž๐™–๐™ฃ ๐˜ฏ๐˜ข๐˜ฎ๐˜ฆ ๐˜ฎ๐˜ฆ๐˜ข๐˜ฏ๐˜ด
๐™ข๐™ค๐™ค๐™ฃ &๐™—๐™š๐™–๐™ช๐™ฉ๐™ž๐™›๐™ช๐™ก
๐™ต๐š˜๐š› ๐š๐š‘๐š˜๐šœ๐šŽ ๐š๐š‘๐šŠ๐š ๐šŠ๐šœ๐š”๐šŽ ๐š๐š˜๐š› ๐š’๐š ๐š–๐šŽ๐šŠ๐š—๐š’๐š—๐š
๐˜๐˜ด ๐˜ฏ๐˜ฐ๐˜ต ๐˜ช๐˜ด๐˜ญ๐˜ข๐˜ฎ๐˜ช๐˜ค ๐˜ฏ๐˜ข๐˜ฎ๐˜ฆ ๐˜ฃ๐˜ถ๐˜ต ๐˜ช๐˜ต๐˜ด ๐˜ข ๐˜ฑ๐˜ฆ๐˜ณ๐˜ด๐˜ช๐˜ข๐˜ฏ ( ๐˜ฑ๐˜ข๐˜ฌ๐˜ช๐˜ด๐˜ต๐˜ข๐˜ฏ)
๐˜ˆ๐˜ฏ๐˜ฅ Islamically ๐˜บ๐˜ฐ๐˜ถ ๐˜ค๐˜ข๐˜ฏ ๐˜ถ๐˜ด๐˜ฆ ๐˜ต๐˜ฉ๐˜ฆ ๐˜ฏ๐˜ข๐˜ฎ๐˜ฆ ๐˜ช๐˜ง ๐˜บ๐˜ฐ๐˜ถ ๐˜ธ๐˜ช๐˜ด๐˜ฉ so
๐˜›๐˜ฐ ๐˜ฏ๐˜ข๐˜ฎ๐˜ฆ๐˜ฅ ๐˜ถ๐˜ณ ๐˜ฃ๐˜ข๐˜ฃ๐˜บ girl ^^^




Suna isowa asibitin direct office na abokin sa suka wuce sai suka tarar bayanan wata nurse ce tayi directing nasu zuwa ษ—akin da aka kwantar da mara lafiyan, Sun same sa anmasa dreesing na ciwon da yajin yana bacci.
Zama Ameerah tayi a kujeran dake gaban gadon ta zuba tagumi, suna zaune haka sai ga likitan ya shigo.
Musabaha suka yi yace masa "freind kasame ni office" ya gaisa da Ameera ya juya yabar ษ—akin.
"Ba naje na dawo" ya cewa Ameera ya fice yabi bayan likitan Ita kuwa Ameera gaba ษ—aya tayi nisa wajan tunani batama san fitan mijin nata ba.
Tura qofan office en yayi ya shiga da sallama ya samu kujera ya zauna.
likitan yace masa "freind ba wani mastala sosai bane kar ka ษ—aga hankalin ka stautsayi ne Allah ya riga ya aiko sai fatan Allah kiyaye na gaba kawai, ya ษ—an samu rauni a qafansa sai kuma kansa daya ษ—an bugu
Buguwar Insha Allahu ba komi, amma bari ya farka mugani
Magungunan da ake buqata da komi za'a yi duk abinda ya dace sannan karka damu da yawan zuwa za'a kula dashi sosai. Nauyayyar Ajiyan zuciya ya sauke ya miqe ya bawa likitan hanu suka qara musabaha yace "freind i have no word ta thanks You Allah saka da Aljanna" murmushi likitan yayi yace "you're always welcome Angon mairo" Hararan sa Daddyn little yayi ya fice a office en.
zaune ya samu Ameerah a inda ya barta, Sallama yayi ta amsa tana tambayan sa fatan lafiya ba matsalan komi?
Yace "lafiya Insha Allah"
To Allah yasa yace "Ameen".
Har yamma suna asibitin amma bai farka ba, tattarawa suka yi suka baro asibiti bayan Daddyn little ya gama settling na komai ya biya.

Abba ne zaune da Umma da Maha da Mahreen
Abba yace "nikam gobe ne tafiyan yaran nan bauchi ko?
Mahreen tayi carab tace "eh Insha Allah Abbanmu zamuje muga tsofuwan da taqi mutuwa sai masifa (dan qwalonta Abba yayi๐Ÿ–)
Gidanku doter kun renamun Uwa ko tom zan saษ“a maku
Dariya Maha tayi qyalesu Abba sun renamun namesy basu san albarkacinta suke ciba
"Yauwa yar kirki faษ—a masu dai" inji Abba yana murmushi. Allah ya kaimu goben lafiya nima zani Abuja wani aiki in Allah ya yarda
"Allah ya yarda Abba" suka haษ—a baki wajan cewa, Tashuwa kowa yayi dan yaje ya kwanta ganin dare yayi.

Soja ne da little a ษ—aki da alama wani aikin yake yi a system nasa ganin yacce gaba ษ—aya hankalinsa ke kan system ษ—in, little keta masa qiriniya da abun ya ishesa sai ya aje system ษ—in a gefe ya miqe, ษ—aukansa yayi yace "muje na kaika Umma"
ฦata fuska little yayi a'a unkui aje ba cede akaini wajan aunci ma'a
Badon yaso ba haka ya ษ—aukosa suka nufi ษ—akin su Maha.

Yana qwanqwasa qofan, Maha ce ta tashi ta buษ—e tana waye ne kuma?
Kallonshi tayi daga sama har qasa ta murguda baki
Little ya miqo mata hanu ancii ci auken, washe baki tayi ayoyo my boy.
Karษ“ansa tayi bata ce komi ba ta kulle qofan juyawa yayi yana auna irin renin da Maha ke shumfiษ—a masa tabbas akwai ranan da zai seta mata qwaqwalwan kanta dai-dai gwargwado.


***Bawan Allah shine bai farka ba sai wajan qarfe 2 na dare, da salati a bakin sa ya buษ—e ido.
Tashuwa yayi yana dafe kansa da yaji ya masa nauyi ga kuma matsanancin ciwo da yake masa kaman zai fashe
Nurse dake tare da shi qara masa alluran bacci tayi ganin yacce yake dafe kan baya ko son mostasa, a haka baccin ya qara ษ—aukansa.



^^^ ๐™ˆ๐™–๐™๐™ง๐™š๐™š๐™ฃ is an arabic name means, ๐™—๐™š๐™–๐™ช๐™ฉ๐™ž๐™›๐™ช๐™ก, ๐™ง๐™–๐™™๐™ž๐™–๐™ฃ๐™ฉ, ๐™ข๐™ค๐™ค๐™ฃ-๐™ก๐™ž๐™ ๐™š
Its an arabic name that means beautiful ^^^


**Gimbiya Mehwish ce zaune suna hira da Ammaan ta kasancewan jikin nata dama-dama tun da suka fara aiki da abun da Abba ya turo masu ta farfaษ—o kuma takan iya zama da kanta tayi magana sannan ciwon baya tashuwa sosai sai dai ba qafa har yanzu.
Labari Gimbiya ke bata tana bata fura mai sanyi, Ammaa har da dariyan labarin da ฦดar tata ke bata, Mai martaba ne ya shigo ya same su a haka da farinciki fal ransa har fuskan sa ya qaraso cikin ษ—akin
Sarauniya Meera da fara'a tace "Marhababika ya zaujee" murmushi yayi wa laki ya imra'atee
Tashuwa Mehwish tayi ta masu sai da safe
Mai martaba ne ya tsayar da ita "Gimbiya yaron nan yayi tafiya naji ko? Eh papa
Tom shikkenan in yayi inaso kisamu lokaci ki kai saqon sa gidan su
Tace "Insha Allah papa zan kai
Tom Allah maki albarka mu kwana lafiya da "Ameen" ta amsa fuskanta ta rufe as usual takama hanyan nata ษ“angaren.
Bayan fitan Gimbiya, Sarauniya ta kalli mai martaba tace "zaujeee nikam ya labarin Auran ibnateey?"
Mai martaba ya kwashe labarin duk abunda akayi ya faษ—a mata.
Cike da farinciki tayi hamdala ga Ubangiji kasan me zaujee wallahi tun banyi ido biyu da wannan bawan Allahn ba naji yayimun a surki ya kwanta a raina tabbas ya cancanci zama mijin ฦณAR SARKI.
azamanin nan da muke ciki abawa mutum kuษ—i yace a'a gaskiya da kamar wuya


To ina dalili Kuษ—i abunso
Masu gidan rana
Iya kuษ—in ka iya shagalinka
Barikinka aljihunka>


Sai dai bansan mai yasa kake biyewa shirmen Gimbiya ba zaujee
Cuta da Magani na Allah ne mai yasa ka goyi bayanta ta tura bawan Allah wata duniya can?
Murmushin manya mai martaba yayi yace "Sarauniya Meerah amma dai a labarin da na baki na yaronnan a faษ—a mai kaman wasa ya ษ—auke abun fuskan ษ—iyarki na gadon nan shi kike tunanin bazai iya ba? Zai iya imra'atee na yarda da jarumtan wannan yaro sannan ษ—an baiwa ne, Aure kaman yacce nace nan da wata 3 inshร  Allahu".
To Allah nuna mana Mai martaba Angon Meerah.
Murmushi yayi har ransa yanajin daษ—in ganin yacce masoyiyar tasa ta samu lafiya
Hira suka cigaba da yi tsakaninsu na masoya.

^^^ Tabbas soyayya baya tsufa bai bar tsohoba bare yaro inda yarda da juna da kuma haquri da juna da kuma ganin mutuncin juna, soyayyah nanan har a mutu
Shiyasa kome zaka yi ka ginashi dan Allah kayisa dan Allah bare kuma Aure
Waษ—anda a cikinmu suke da Aure Allah qara haษ—a kawunanmu da zaman lafiya da soyayya da zuri'a ษ—ayyaba tsakaninmu da mazajenmu
Waษ—anda basu da Allah ya kawo nagari alfarman Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ^^^



_____
washe gari da sassafe ko wajan aiki daddyn little bai je ba, bayan Ameera ta gama haษ—a masu abin kari shiryawa suka yi suka ษ—au hanyan asibiti.

Sun isa asibiti lafiya, shigansu ษ—akin da majinyacin yake yayi dai-dai da farkawansa, ganin ya farka Ameera farinciki kaman tayi ya!
Buษ—e idon sa yayi a hankali sai dai yanzu baijin ciwon kan sosai dan haka lumshe ido yayi ya maida kansa ya kwanta.
Doctor ne ya shigo ษ—akin ya dudduba abunda zai duba yayi hamdalah ganin komi yazo masu da sauqi ciwon kan nasa baija masa loosing memory ba yacce suka zata.
Duk abinda ake yana jinsu amma bai buษ—e ido ba, gaba ษ—aya wani iri yake ji shi da yake so a sati 1 ya gama ya koma sai kuma ga qaddara ya samesa.
Likitan ya duba komi Alhmdlh sai dai matsalan ciwan qafansa da zai iya kai kwana 10 zuwa 8 kamun ya warke yaji daษ—in tafiya sosai, yana gama masu bayani yace Allah "Allah qara sauqi ya kiyaye na gaba" sai ya fice a ษ—akin dan zuwa duba sauran majinyatan.

Likita na fita kusan a tare suka masto wajan gadon da yake kwance, Daddyn little yace "bawan Allah kayi haquri katashi ka wasta ruwa ka samu kaci abinci kayi sallah".
Jin an ambaci sallah sai zuciyarsa ta tsinke da ya tuna tun jiya da safe rabon sa da yayi sallah, yunqurawa yayi zai tashi sai ya kasa sakamakon qafansa da ke da rauni.
Daddyn Little hannun sa ya miqo masa ya temaka masa ya tashi, har toilet ya rakasa kamun ya fita ya tsaya a waje dan ya jira sa.
brush da maclean da suka kawo masa yayi amfani dashi ya lallaษ“a ya wanke jikin sa da dabara, ledan da ya ajiye masa a toilet ษ—in ya jawo ya buษ—e wani milk jallabiya ne mai hula da short a ciki, cirosu yayi ya saka.

{dogon namiji shine namiji kuma mijin aure gajeren namiji kan chager ne
Bafa ni naceba nima ji nayi ana cewa shine nima nace bari na ษ—an ษ—ana loll}

bayan ya gama sawa alwala ya ษ—auro ya futo a toilet en yana ษ—ingisawa da sauri Daddyn Little yace "bro bazaka qirani ba nazo na taimaka ma karka fama qafan ka" murmushi kawai yayi baice wa Daddyn little komai ba.
Ameerah ta shumfiษ—a masa darduma, Daddyn Little yace "bawan Allah kaci abinci sai kayi sallahn ko"
Lumshe ido kawai yayi bece komi ba yanzu ma sannan bai mosta akan darduman ba, ganin yayi shiru sai Ameera gaba ษ—aya ta rikice kar dai fa kurma ne ko baya magana Allah sarki sai idonta ya tara kwalla tayi saurin gogewa tace "yayana ko zaka yi sallan kamun ka karya?
Lumshe ido yayi ya jinjina kai alamun hakan ya masa, ba musu Daddyn Little ya masa nuni da alqibla Shi kuma ya tada kabbara a zaune ya fara sallan sa.
Bayan ya idar sosai ya jima yana addu'a kamun ya shafa ya zauna awajan shiru yana tuna Umman sa
tambayansa tayi yayana ruwan zafi da mai zaka ci? Tayi maganan tana kallon sa da tunanin wataqila kurma ne baya magana kawai tana jiran ya mata sing
Lumshe ido yayi kaman bai son yin maganan (asalim halin miskilancinsa ya mosta) da qyar ya buษ—e bakin sa a hankali ya mosta bakin yace "ruwan zafi kawai".
mamakine ya cika Ameera har da mijin nata wai dama yana magana caษ“.
Haษ—a masa komi tayi ta ajiye a gabansa, ruwan zafin kaษ—an kawai yasha bai ko kalli sauran abubuwan ba bare asa ran zai kai baki da sunan ci, gaba ษ—aya abincin Ummansa yake son ci.
magani ya amsa yasha sannan ya jingina da jikin gadon.
haษ—a kwanukan tayi ta maida basket ษ—in da suka zo dashi ta koma ta zauna itama, Daddyn Little ne ya tambaye sa ya jikin naka bawan Allah? Kai kawai ya kaษ—a fuskan sa a sake
Maida Kallonta tayi kan mijin nata, husby ko zaka samu ka wuce wajan aikin ni ka barni anan in ka taso aikin sai ka biyo muje gida na haษ—o masa abincin rana ba?
Ba tare da ya Musa mata ba yace "shikkenan wiffey zan wuce in Abba ma ya shigo yau ษ—in zamu taho tare You should take care, bro Allah qara sauwaqa sai na dawo" ya faษ—a yana ficewa a ษ—akin.
Baibi ko takan abokin nasa ba ya kama hanya dan yaje ya shirya gudun kar ya makara.

Bayan ya fita Ameera tashuwa tayi da kanta ta gyara masa gadon bata jira ma'aikatan asibitin ba, da ta gana tace masa "kana buqatan wani abune yayana? Girgiza kai kawai yayi.
murmushi tayi ita dae har ga Allah tana jin tausayinsa sannan ji take kaman ษ—an uwantane sannan tunda take bata taษ“a ganin mutum mai kyau irin sa ba kaman ba ษ—an Nigeria ba.
Suna zaune haka shiru sai ga qiran Umma, amsa qiran tayi suka gaisa take tambayan ta ya mai jiki? Mai jiki da sauqi sosai Umma gamunan ma muna asibiti. Umma tace "Daddyn little fa? Ta amsa mata shikam ya tafi wajan aiki Umma, ba nabawa mara lafiyan waya ku gaisa Umma.
Miqa masa tayi, yayana ga Ummanmu ku gaisa, amsan wayan yayi ya kara a kunnen sa.
Assalamu'alaikum yarona ya kake?
Jin muryanta ya sanya shi jin wani sanyi na mamaye ilahirin jikin sa bai san daliliba kuma kaman ancire masa ciwon kan, Yacce ta qirasa da yarona ba qaramin daษ—i yayi masa ba yaji wani nistuwa a ransa! Qara lumshe ido yayi yace "lafiya qalau Umma"
daษ—i taji har da ษ—an murmushinta Allah qara sauqi yarona, Allah qara afuwa, Allah maku albarka ya kiyaye na gaba Insha Allah anjuma babanku zai zo ya duba ku.
Bai qara cewa komi ba, yace nagode ya miqawa Ameerah wayan
Amsa tayi tai waje suka cigaba da waya da Umma.......



Fatahn alkhaeryh gareku kowa da kowa cikin girgin dazai zo langeria โœˆ๏ธ๐Ÿ˜‚


ฦณAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh๐Ÿ•Š๏ธ


๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹

๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎuka:-
08146292652
๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ.
09161720046
๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐Ÿ˜

# ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ
# ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š &
# ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š

ourmman batoolerh ceeeeโœ๏ธ
Taku har kullum........

๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ

๐˜ฝ๐™ฎ

๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™–

(๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorl)

ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค

_______________________________________________________________

*Na sadaukar da wannan shafi gareka MIJINA abun alfaharina ABU BATOORL ina godiya da gudumawanka da kuma qwarin guiwanka gareni wajan ganin labarin nan ya tafi yacce ya kamata godiya ta musamman daga matarka hareeyh- Mrs big barbieyh*


๐Ÿ…ฟ๏ธ 41&42


๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹




Mahreen ce ta fito sanye da riga da siket na atamfa wanda ya amshi jikin ta sai mayafin ta dake riqe a hannun ta da handbag nata, can sai ga Maha ta fito da ษ—an trolleyn da za suyi tafiyan dashi itama sanye take da dark-arsh abaya wanda ya amsheta sosai.
Duk suna tsaye a palourn ko akwatin ba'a fitar ba sakamakon Little da yasasu gaba yana kuka shi sai yabi auntyn sa, Umma tace "Angon granny zaka tafi ka barni ni ษ—aya? yana kuka yana magana nide gilani anbi aunci na an jauna anan ba.
Dariya Maha ta sanya yanzu Umma abarsa mu tafi mana yace baya zama dake ana soyayyan dole ne
Yanzu ke doter sai ku tafi duka ku barni ni kaษ—ai ga Abban ku ma tafiyan zai yi, Ummata tom kiga fa yana kuka kishirya kawai muje tare kar abarki ke ษ—aya.
Hararanta Umma tayi gidan kuma abarwa waye in na biku?
Lallaษ“asa da dabara aka yi suka samu yayi shiru lokacin soja ya fito shima a shiryen sa sanye da jamfa.
Umma sai binsu da ido kawai take tana hamdala a zuciyan ta ganin yacce yaran nata suka sha kyau, in ta kalli soja ta kalli Maha sai tace Ameen ya Rabbi.
Abbane ya fito shima ya gama shiryawa dan wuce wa Abuja
Gaba ษ—aya suka yi waje.
Nan umma jitai kaman ta bisu su tafi duka amma ba dama dan in ba dole ba bata so abar gida ba kowa sai masu gadi da mai aiki
Duk suka shiga Motor as usual Maha ta shige gaba abinta ta zauna ko a jikinta, Mahar kuwa dama ita ba gwanar fitina bace shigewa baya tayi tana fidda wayanta tana dannawa
Umma da Auta suka raka Abba wajan nasa motor suka masa Allah tsare hanya driver yaja motorn bayan Abba ya masu bye bye shima akan su kula da hanya sosai, Kuma Insha Allah zebi wajan su Ameerah ya dubo mara lafiyan. Airport Abba suka nufa tare da wani guard nasa da zae kaisa sai ya dawo da motorn.
Auta ya shiga mazaunin driver suka ษ—agawa Umma hannu yaja motorn suka ษ—auki hanyan bauchi da motor zasu sakamakon Maha tacewa Abba ita bata

Please Login or Register in order to submit comment