Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miqawa Maha don ubanki uwaki ce Amarya ba ni ba masifa kuma nayi ni da baki na a gidan yarona kika zo kika sameni ba gidan ubanki ba bare ki gaya mun magana tangaɗaɗɗiya kawai tom ki gaji da garin nan har ki mutu in kinyi wasa sai na cewa ubanki abarki anan inga yacce zaki yi, wato ma dan lalacewa irin na Jamila gidan shisha ne ko shishu take barinku kuje oh Ni mairo naga rayuwan tangaɗi anan Insha Allahu Jamila zata zo ta sameni
Caɓ ni dai komawa gidanmu zanyi abuna Sannan ki zage ta ai ƴarki ce ba wanda ya haifa maki ita kunfi kusa atou ni me nawa
Yanzu dae cubulle dan baki da ta ido uwar taki kike cewa haka Allah ya shirya mana zuri'a, yanzu Shekara nawa ban ganku ba dudu yau kwanan ku nawa da zuwa inaji baku yi kwana biyu ba kice zaki tafi
Zaro ido Maha tayi tace "yo kin tsufa ba dole kice haka ba to bari kiji takwara munfi sati a garin nan mun kusa kwana goma ma inaga"
Kakus ta taɓe baki tace "to koma dai shekara ne ai cubulle mutum bazai guji nasa ba ni da nakeso abar mun ke tunda ke cubulle nace kinga hankalin mu zefi zama ɗaya abunmu ba mai jin tsakaninmu inasonki kina sona
Tura baki Maha tayi tana magana qasa-qasa
Mahreen ce ta shugo da sallama tare da ya Abdoul suna murmushi dukan su
Kakus ce tace "tom tattabaru gidan soyayya sannunku da zuwa damunmu muna hiranmu na soyayya ni da cubulle ta".
Dariya ya Abdoul ya saka wato dai yau shiri ake tsakanin kakus da cubun ta
"Shikkenan Hajiya Kakus in zuwan namu bai maki ba sai mu koma inda muka fito" inji Mahreen
Harara kakus ta mata sannu rasae wato kin qwacen miji ɗan cafanen da yakeman da ɗan goron da yake sayan mun kike son hanasa ko wai ku koma to ba in da zaku koma kaga zoka zauna angon amarya komi dozin nayi hiran da kai
Dariya suka sa dukansu wajan ban da Maha da murmushi kawai tayi
"Nikam ina habibu ne yayi? inji kakus
Ya habeeby ya futa ai kakus inaji yaje wajan abokanan sa anan barrack na garinnan
Ooh abunka da sojoji ba iyayen kalan dangi Kai da kake soja a kaduna me ya haɗaka da sojojin bauchi? habibu shishishigi shigilitu
Sai sannan Maha tayi dariya tace "Allah dai ya maki albarka takwaras daɗi na dake baki qyale kowa ba wato dai kalan dangi yaje yi".
Kallon ta Kakus tayi ta girgiza kai "cubulle ba dai iya dariyan mugun ta ba to wallahi yazo ya jiki ba ruwa na in yana lakaɗa maki duka ba ruwan mairo" ta faɗa tana karyan goron ta
Ya taɓa ni ya gani hayya sai kuma tayi qwafa
Hiran su suka cigaba da yi.



1 MONTH LETTER
(bayan wata ɗaya)

a haka rayuwa ke ta tafiya da daɗi babu daɗi har yau gashi watan shi guda cur a garin Abuja, yau ne kuma yake lissafi da shirin barin Abuja ko da su Ameerah basu so ba domin zaman ya isa haka lokaci na tafiya

Sanda ya gama shiryawa tsaff be ɗau kaya Ko ɗaya ba banda na jikin sa tunda baizo da kaya ba anan ya same su, fitowa yayi yaja qofan ɗakin ya nufin cikin gidan nasu
A palourn ya tsaya yayi sallama, amsa masa Ameerah tayi kamun nan ya qarisa shiga da ta masa izini
Kallonsa tayi tare da zaro ido yayana mai nake gani?
Ba dai kaceman ka shirya ba yayana sai kuma idonta ya kawo hawaye
Murmushi ya mata bece komi ba waje ya samu ya zauna
Daddyn Little ne shima ya fito ashirye ganin sa sai yayi murmushi yace "bros har ka gama ka fito ne? Ɗaga masa kai kawai yayi yana murmushi
Gashi har xaka koma baka faɗa mana komi akan ka ba bro ko wataran Allah zai qara haɗamu ko wani zumunci haka kaga ai zamu iya kai maka ziyara Insha Allahu ko wiffey
Murmusawa yayi ba qin faɗa maku nayi ba faɗan ne bance akwai amfani ba dan ina da nisa sosai Nima dalili ne ya kawo ni sai Allah ya qaddara haɗuwanmu
Ameera da idonta ke cike da hawaye tayi caraɓ tace "yayana nisanka doesn't matter, yacce dalili ya kawo ka sai kaga mu kuma sanadi ya kaimu in Allah ya hukunta hakan"
Kai de ka bamu address da kwatance kawai bros
Shikkenan karku damu
Yanzu dai banson ɓata lokaci tun da kunce akwai nisa bauchi da garin nan amma ba na faɗa maku ko kaɗan ne daga labarin inda na fito
So tunda ga waya we will be communicating Insha Allahu
nan ya basu ɗan taqaitaccen labarin daga in da ya fito
mamakine ya rufe su duka Ameera ce tace "Yayana yanzu daga Qatar dana sani kake dan Allah? Kazo Nigeria kawai dan neman magani lallai sannu da qoqari yayana"
Tom ai gwanda daka faɗa mana Ranan ai nace maka akwai family house namu a Bauchi sannan ina ji kakus na yawan cewa kakanmu malami ne yakan bada magani Kaga da ka bari munje can en may be ma ta gane maganin da kake nema basai kasha wahala ba, kaga mu qara ko da wata ɗaya ne kamun yasamu leave s wajan aiki sai muje dan bamu jima da dawowa ba wannan hatsarin ya faru
Murmushi yayi shi dai bece komi ba
Qanwata Kinga ba yanzu zaku shiga bauchi ba sannan ni ina da qidayayyen lokacin da ya kamata ace na koma
Kwanaki sun tafi sosai zan shiga bauchi in yaso ko daga baya zamu haɗu daku in kun samu shigowa kamun na koma in Allah yasa na dace kuma na samu na tafi sai dai Allah haɗa mu da alkairi
Sannan ina addu'an Allah ya sauqeki lafiya ya albarkaci duk abinda zaki haifa
Idon Ameera cike da kwalla ta shafa cikin ta da ya fara fitowa tace "Ameen ya Rabbi yaya AMJAD"
Murmushi Amjad yayi mata
Haka kaman karsu rabu suka yi sallama Ameerah har da yar kwallanta suka baro ta a gida dan Daddyn Little ne ya kaisa har motor pack ya sashi a Motorn Bauchi ya biya kuɗin motorn sannan ya basa wasu a hanunsa duk da ya nuna a'a
Jakan da tun ran da ya buge sa ya ajiye yaje motor ya ɗauko ya miqa masa bros ga jakan kayan ka nan sannan ya buɗe yasa masa kuɗin a ciki sun riga sunyi exchange na number. Sanda motornsu ya tashi kamun Daddyn Little ya ja nasa Motorn yabar tashan ya wuce wajan aiki
Amjad na zaune cikin Motorn suna tafiya shiru yayi dan ya fara jin kewan mutane masu halaccinnan dan baya tunanin azamanin da muke ciki ana samun mutane haka
Wasuma in sun buge mutum guduwa suke kamun ataru a kansu
"Allah ka datar damu, su kuma Allah saka masu da mafificin alkhaeryh".


Mahreen, Maha da kuma Soja sun dawo gida bayan satan nin da suka yi a bauchi, suka dawo cike da kewan mutan Bauchi da surutun kakar tasu
Umma taji daɗin ganin yaranta sosai sosai
Inda gefe ɗaya kuma da Umman da su Mahreen en duka ido suka zuba ganin ikon Allah yaushe Ummeyh kuma zata iso kullum ina hanya na kusa zuwa amma shiru
Mahreen ce in ta tashi qorafinta sai ta tura baki, tace "wa yasan ko jiddahn ya koma bangon duniya ne".
Tsakanin Maha da Little kuwa soyayyace ba kaɗan ba In ka gansu sai ka ranste itace uwarsa yacce yake maqale mata
Mahreen ke kwance a ɗakinsu tana aikin da ya same ta na waya
wayanne a maqale a kunnenta sai narkewa take "nide ya Abdoul ka dena bana so
Ta ɗayan ɓangaren ne naji ya Abdoul yace "nifa da gaske nake ba wasa ba zanwa su baba magana am eager to see you as my wife, I seriously need you by my side, Ina kallon wannan kyawawan idanuwanki masu tafiyar da tunanin mai kallonsu"
Lumshe idon tayi
Yace "and 1 thing kinsan me?
Tace "uhm uhmn yayana ban sani ba sai ka faɗa"
nifa in baki daina cemun yaya ba duk randa na kama bakinki hmmn
Turo bakin tayi kaman yana gabanta nide uhmn
Dariya yayi kaɗan kede kinji kunya ko tom shikkenan in zaki aje kunya agefe ki aje inba haka ba nifa baza'a qwareni ba bari kiji. I love you Queen
Muahhh! blowing mata kiss yayi ta wayan
saurin cire wayan tayi a kunnenta ta kashe tana murmushi ita dai ta rasa ya Abdoul wani iri ne ko kaɗan bai jin kunyan ta komi yaga dama faɗa mata yake
Rumgume fillow tayi inasonkaaa sosai nima yayana.
Maha ce zaune a palourn tana kallo
Litlle ya futo daga ɗakin soja yana bubbuga qafa yana anci boi na anci boi na (Aunty ball na)
Kallon sa tayi babyna ball naka a ina?
Nuna mata ɗakin soja yayi a akin unkui Tace mass "Ina uncle en
Kuma tom?
Fara buga qafa yayi unkui ayanan boi na aunci
Dafe kai tayi ba yacce ta iya haka ta tashi ɗaukansa tayi suka shiga ɗakin
Wow ɗakin tuzurun soja kenan komi na dakin white colour ne ɗakin ya haɗu iya haɗuwa ga tafkeken gadon da zai ɗauki mutum 4, tunda suka shiga sashin take qare ma palourn nasa kallo har suka shiga cikin ɗakin gaba ɗaya kaman ba'a Nigeria part nasa yake ba bare ace maka a cikin gidan Abba ka yarda dan ya haɗu iya haɗuwa san da ta gama santin sa dan bata taɓa shiga ba kamun ta wuce yin abinda ya kawo ta
Suna shiga ɗakin ya sauqe sa shi kuma ya nuna mata qasan gado wai yana ciki ball ɗin
Sunkuyawa tayi dan ta ɗauko masa har ta miqa hannu sai taji motsin an buɗe qofan bayi
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un shine abinda ta furta a zuciyanta dan tabbas tasan yau ta gama yawo little ya jaza mata dama wasan ɓoyel ɓoyel suke da marar kirkin nan yanzu gashi ta kawo kanta har ɗakin sa daɗin ya kashe ta ya ɓoye wuqan ko ya dakata har tayi laushi ba wanda ya sani bare ta karɓe ta tama rasa yacce zata yi
shi ko gogan naku ya fito wanka zuciyansa ɗaya 1 little ne kawai a ɗakin daga shi sai guntun towel white wanda be kai guiwansa ba faffaɗan qirjin sa a buɗe da kwantattun gashin da ruwa ya jiqa su(abinka da soja)
Wajan mirror ya wuce bai ko kalli Little dake tsaye gefen gado kaman mai jiran abu ba, yana share jikinsa kaman ance ya kalli can ai kuwa karaf ta cikin mirrow idonsu ya haɗe
Saurin rufe ido tayi tana duk addu'an da yazo mata a zuciyanta
shi kuwa haɗe fuska yayi daga baya kuma yayi murmushin mugunta
Tana nan wajan qasan gadon idonta a rufe a storace take sanda har ta qarisa futowa daga qasan gadon wajen qofa ta nufa da rarrafe wai dan kar ya ganta bata kai ga isa ba taji an riqeta
Juyowa tayi zata kwala ihu
Hanu yasa ya buge mata bakin
Dama wa yasa ki shigomun ɗaki? renin daki kamun har yakai haka ko
Bata ce ko qala ba ganin dai tana hannu idanuwan ga a rufe dan storo har jikin ta na rawa
Sake ta yayi yana faɗin "qaramar mara kunya fice mun a ɗaki kamun nayi ball dake ta yacce ko qashinki baza'a iya ɗaurawa ba idiot kawai"
Ai kuwa kaman jira take ya sake ta tana hamdala ta fita tana haqi da sauqe ajiyan zuciya yacce ya habeebu ya fusatan nan in yakaiman bugu 1 ai bani ba labarina amma Little ya jamun kwandon bala'ee
Hararan hanyan ɗakin sa tayi ta shige dakinsu da gudu tana ga kaman zai biyo ta
Little da ya samu Ball nasa dama palourn ya gudu yana yi dan inyayi a ɗakin unkui zai zana sa
Bayan fitan ta murmushi yayi yaci gaba da abun da yake yi hankalin da kwance ko bai dake ta ba dai yasan ta storita


Motorn su tafiya yake shi kuma da yake zaune a gaban motorn ya zubawa hanya ido, idon shi nakan hanyanne amma tunaninsa gaba daya yana gida Ummansa kawai yake misalta irin yanayin da take ciki gashi baisan taya za'a yi yayi magana dasu ba duk sunqi riqe waya daga ita har Abba
1 month basu yi magana ba bata kallesa ba sai yanzu ma yake jin haushin rashin riqe wayan da Umma da Abba suka yi
Shima kuma dama bawani damunsa wayan yayi ba shi yasa bai matsa masu ba dan bai tava kawowa zai yi irin wannan tafiyan har haka ya jima beji Umman sa ba
Tafiya suke tun da hansti har har sune basu isa bauchi ba sai can tsakiyan dare dan ma Allah ya taimake su driven bai yi zagaye ba kuma an gyara hanya
Sun shigo gari ga dare yayi gashi besan kowa ba
Gaba ɗaya ya rasa ya zeyi haka de wani bawan Allahn da suka zauna tare dashi a motorn suka wuce gidan sa suka kwana kamun da safe ya nemi abunda ya kawosa bauchi.


Zaune take gaban mai martaba kanta a qasa
Ibnateeyh yanzu kinsan in lissafina dai dai ne to yau saura wata 1da satanni bikin nan ko fatan kina sane?
Don haka za'a fara shirye-shiryen biki da komi sannan zanyi magana da mahaifin yaron
Insha Allahu ni ina ji a jikina ya kusa dawowa ma don haka kema ki fara shiri inaso gaba ɗaya ki daina fita yanzu kinji ba
"Insha Allahu Papa Allah taimaka" shine kawai abunda tace
ganin kaman bata yanayi me daɗi sai Mai martaba ya sallameta
Sannan ya aika da ɗan aike akan a faɗawa Abban Amjad yana nason ganinsa gobe in Allah ya kaimu

Umman Amjad ce zaune tayi tagumi tasa tuwo a gaba amma bata ko sa hanu ba shigowan Abba kenan daga wajan jin saqon qiran Sarki ya tarar da ita haka
Girgiza kai yayi bece komi ba
Zama yayi kusa da ita MARYAMA ki masa addu'a kinji Inshà Allah alkhaery ne ya riqe sa kinji
Sai hawaye a idonta sharrrrr ta cire hannu a abincin ma kuka nason qwace mata
Saurin share mata hawayen Abba yayi
Kul Maryama na haneki da mawa ɗanki kuka kibar zubar masa da hawaye dan hawayen uwa masifa ne akan ɗan ta ba mutuwa yayi ba tafiya ce kuma Insha Allah yana hanyan dawowa kinji ko mutuwa yayi ma tsakaninki dashi addu'a dan shine soyayyan ki gare sa
Adduah zamu masa yanzun ma kinji a haka ya lallaɓa ta da qyar ta yarda taci abinci
Nan ya fada mata yacce suka yi da ɗan saqon mai martaba
Sun kuyar da kai Umma tayi tace "Ni wallahi duk ji nayi ma da ban kawo shawaran ya shiga gasar nan ba tsakani da Allah na fara dana.." ta kasa qarisawa sakamakon kallon da Abba ya jefa mata
Wai ke Maryam mai yake damunki ne kam? Ja kike dashi akan hukuncin da Allah yayi akan ɗan ki? Kinsan zaki zo duniya? Ko kinsan zaki samu yaron? Mai yasa dan Allah ya qaddara abu akan yaronki kikeson butulce wa Allah ta hanyan nuna baki karɓi wannan qaddaran ba? Lokacin samun damuwan mu yayi tabbas in dai bazaki gyara kalaman ki ba, ki godewa Allah dan bakisan iya alkhaeryhn da yake cikin wannan qaddara ba ki ɗauki kanki ki kwatanta a matsayin da Sarauniya take ciki na rashin lafiya shekaru da shekaru in kece zakice haka? Tom inaso ki kasance mai yiwa Allah godiya dan yaronki kaman yanda Allah ya baki kyautan sa tom haka yake kyauta ga al'umman Annabi SAW kisa albarka a komi da ya shafi Amjad in dai kinason ki shirya da mahaliccinki akan kyautan da ya maki
"Kayi haquri Abban sa" shine abinda Umma ta faɗa tana share fuskan ta
Abba yace "ba ni zaki bawa haquri ba ki nemi yafiyar Ubangiji tun da wuri"
Astagfirullah ya Rabb Allah Alhamdulillahi Allah ka kare mun shi ka basa sa'an abinda yaje nema ka bamu ikon cinye ko wacce qaddara tamu
Yauwa Abban sa nikam ya za'a yi da maganan shirin bikin ne tom kaga fa ya kamata ace iyanzu ankai kayan tambaya da sauran su ya rage kayan Aure da sadaki to su masu sarautane Mu kuma Alhamdulillahi
Murmushi yayi ai tun ɗazu da wannan magana muke ai da yafi
Amma da kikace Alhmdlh kin gama zance shi wannan kalman yafi komi yanxu dai in Allah ya kaimu zuwa goben naje naji qiran akan mene ko ya ya ake ciki inyaso in na dawo mu kuma sai musan ya za'a yi mai ya kamata ayi ba
Musan ta ina zamu fara amma mudai Allah ya dawo mana da ɗanmu lafiya shine babba a wajan mu dasu duka
Da "Ameen" Umma ta amsa
ayyah jarumin Ummansa Ummanka na kewan ka nasan kaima duk inda kake kana kewata
Fatam Allah ya tsare mun kai ya haɗaka da mutane na gari Allah dawar dakai gida lafiya ya nuna mana wannan biki Alfarman fiyayyen halitta SAW.


Muje zuwa fan's ✍️

ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️


💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦

𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮

𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖

(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

_______________________________________________________________


🅿️ 51&52


💋💋 امى بتولة💋

**
𝙈𝙖𝙝𝙖
𝙄𝙨 𝙖𝙣 𝙖𝙧𝙖𝙗𝙞𝙘 𝙣𝙖𝙢𝙚 𝙬𝙝𝙞𝙘𝙝 𝙢𝙚𝙖𝙣𝙨
𝙆𝙞𝙣𝙙𝙣𝙚𝙨𝙨𝙨 & 𝙗𝙚𝙣𝙚𝙫𝙤𝙡𝙚𝙣𝙩
Maha is a name for ur baby girl's
**





Mahreen ce ta kalleta ganin ta shigo da gudu kuma tana waige sai tace "ke kuma daga ina Maha? Ke da waye wa kika stokano?
Maha tace "sai jero mun tambayoyi kike Ina ruwanki" ta wuce banɗaki tayo alwala tazo tai Salla
Da ta idar ta ninke darduma ta wuce tayi ɗakin Umma dan tana ga kaman zai iya biyo ta nan ɗin ma
Ita dai Mahreen ido ta zuba mata bata kuma cewa komi ba har ta fice a ɗakin taɓe baki tayi ta tashi itama ta ɗauro alwala
Assalamu'alaikum Ummata
Amsawa Umma tayi shigo mana ɗiyar Umma kuma surkan Ummanta
Turo baki tayi Umma kema xaki fara ko zan koma inda na fito Allah
Murmushi Umma tayi zo ki faɗamun waya taɓamun ke Autan Umman ta
Kan gadon Umma ta haye ta kwanta uhmn Umma nazo bacci a ɗakinki ne
Anya ba laifi kikai wa soja ba kika gudo doter?
Umma nidai bacci nazo yi banyi komi ba kuma ki tambayesa kiji
Tom ayi lafiya Auntan umma
Umma wayanta ta ɗauka ta qira layin Ameerah ya shiga har ya yanke ba'a ɗauka ba qara qira tayi haka ba'a ɗauka ba san da ta qira ana uku kamun aka ɗauka
Ameerah na ɗauka tace "afuwan Ummana"
Ina kika aje wayan kika je? Umma na mance wayan a ɗakine
Tom yayi kyau ya kuke?
muna lafiya Ummanmu
Ya mijinki ya baqonku?
Dukanmu lafiya lah Umma afuwan ban faɗa maki ba ai jiya ya tafi
Umma da yanayin faɗa tace "Ameera ya tafi kuma ban gane ya tafi ba?"
Umma yace abu zaije yi a bauchi tom tunda ya warke zai tafi
Ameerah ashe niba uwarki bace da baxaki faɗamun ba ko Abbanku amma de ya maki kyau daga ke har mijin naki
Umma Kashe wayanta tayi ranta a ɓace
Ameerah ce ta qirata ɗauka tayi tace "Yanzu kuma me kika qira kicemun?
Qasa tayi da murya kiyi haquri Ummata amma akwai phone number ensa a wajan Daddyn little
Shikkenan naji yanzu ina ya tafi? kwashe duk yacce suka yi da yayanta amjad en tayi ta faɗa ma Umma
Yanzu Ameerah rashin hankalinku da rashin tausayinku yakai haka dama mutum besan kowa ba tunda Allah ya haɗa ku ta sanadin hatsari ai seku temaka masa shima nan gaba sai kuga da ikon Allah ya temaka maku ko wa wani naku
Baisan kowa a Bauchi ba so kuke yaje yai ta tangariri agarin bauchi ko?
Nagode maku Ameera
Umma kiyi haquri Allah nace ya bari muzo tare yace a'a time nasa kaɗan ne
shikkenan yayi kyau Allah tsare sa ya basa sa'a
Haquri Ameera ta qara bawa Umma
Umma tace "Bakomi" sallama suka yi ta kashe wayan ta
Numbern Abba ta nemo ta qira
Ɗauka yayi "assalamualaikum hajiyata ya akayi ya gida"
Yallaɓoi kasan me yaranka suka yi
A'a sai kin faɗa maman yarana
Kwashe yacce suka yi da Ameerah tayi ta faɗa masa
Subhanallahi yanzu shi mijin nata biyewa shirmenta yayi? To shikenan Insha Allah zan qira mijin nata ya turoman numbern yaron in yaso sai na turawa Abdul ya kaisa gida ko ina fatan hakan yayi maki Hajiya ta
Allah qara girma yallaɓoi hakan yayi sosai ma, Allah shirya mana su sukuma Allah barmun kai
"Ameen hajiyata" Abba ya faɗa yana murmushi
Ɗan hiransu suka yi na masoya
Insha Allahu nima nan da kwan 2 zan dawo hajiyata dan nayi kewanki
Amma mai za'a ajiyemun haka aka damu na dawo?
"Kaima dai yallaɓoi ka sani dolema a tanadar maka abu mai daɗi koda kaman ruwan roba ne( faro)" Umma ta faɗa tana dariya
haba dai hajiyata wannan kam kice nai zamana nasha anan kawai sai dai ko acemun yar buduwar matata ta ajeman kanta
Zaka sani jin kunya yallaɓoi har da jikanne nake budurwa?
a'a nikam a wajena matata ƴar shawal-shawal

Please Login or Register in order to submit comment