Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisuwa dake da mutanen grp dinki nagode da kulawa*

Wai ya hashim mesa ya suhailat bata zuwa gida ne tun auren ku

An tabo inda ke mata susa
Ya gyara zama yace oho mata
Haba dai
Wai ya suhailat?
Hawayen ta ne ya zubo tace ni ban san ya zan yi ba da rayuwata laifi ne nayi shi kuma ya wuce amma kowa yaki ya yafe mani ni kaina ma gaji da zaman kadaici

Ta ko ina ban fita ba kowani yake ki akan avunda ya wuce ko kofar gida fa bana fita balle naje gida abba ya ki ni mama ma ta kini da ya hashim ya nuna musu cewa shima ya koma kamar da komai normal muna lafiya dashi ai da ba haka ba kusan wattani biyar da yin abu daya ki musu magana kila sa hakura shi kuma ku masa huduba ya maida komai ba komai ba aure an riga an yi shi duk wani hukunci da ya kamata a min amun shi zuwa yanzu ta karasa fada tana kuka.

Se nanah taji tausayin ta ya kamata ta karyar da wuya tace haba ya hashim mesa haka? Ni na yi tunanin an wuce gurin ka manta baya

Hmm ke ni kar ki dame ni ai ganin ki yasa ta iya magana ba dan haka ba ai bata isa ba amma ta wani fannin gwara ta fadi sirrin dake ran ta kinga nima naji

To ai tace ayi hakuri
In naki fa
Allah baka hakuri yaya amma mugunta ba kyau ka taimaka ka gyara kar Allah ya kama ka tana mace ta hakura balle kai

Hararta yayi yace kar ki fadan isllamiyya man ai na san da hakkin aure ni in tambaye ki zaki fada min gaskiya?

Meze hana?
Kina son ya alee?
Tayi jim se kuma ta kyabe fuska tace ina son sa man ai dan'uwan na ne ai

Karya kike ya fada ya hauro kaman ze dakeya yayi mici mici da idon sa

Tayi masa dariyan da yasan na me shi kam

Tace naji rigima dan baka son matar ka ni se naki mijina?

Koda ban san ya alee ai tunda mun yi aure yazan yi umarnin iyaye dole mu bishi kuma dole mu cika iyakoki da dokokin hakkin aure koda kuwa bama so dan zama ne bana kare ba sede wani ikon Allahn

Wallahi xan mareki mara kunya
Ai gaskiya ce kuma ta zama dole na fade ta koda kuwa ba ka so

Ke kuma ya suhailat kiyi kokarin zama mace kiyi kokarin son ya hashim in baki so shi ba taya zaku xauna lafiya

Kaima ya hashim try and love her respect her.

Harara ya kuma buga mata se kuma ya mike kai kamal zo muje ka rakani unguwa wannan yarinyar ta fara wa'azi ni kuma bana bukata tunda ita ma karya take ma zuciyan ta

Hhh ya hashim kasan me?
Se kin fada ya amsa mata yana mikewa

Ni xan ma ya alee komai
Kasan dame dame?
Mtsw se anjima in mun dawo kwa tafi .
Ta raka shi da dariya kasa kasa.

Suhailat ta ce zaki iya ma ya aliyu komai bayan ....

Eh ta katse ta
Zan ma ya alee komai zan basa kulawa, zan masa girki, zan masa wanki, zan masa guga,zan masa biyayya,komai na rayuwan aure zan masa amma bazan taba son shi ba


Kallo ta bita dashi irn kallon kin yi kokari dan abu ne me wuya ki kasa son ya aleeyu dan ya aliyu namiji ne kaman yadda yake fada ya aleeyu ya isa kuma ya cancanta a so shi koda kuwa baki so ba ko da yake kowa da nasa assumtion din.

Ya suhailat ki gyara zamantakewar auren ki da yaya dan yana bukata kuma kina bukata na gani a idan sa kin san dai dukgidan mu ba wanda ze fada min waye ya hashim bayan maman su

All the rest nice dan kusan dukkan lokacin sa nawa ne tare muke yin komai dashi olwaya mina tare kema kin sani kina da labari!

Haka ne to mezan yi ?

Kece ko da abun yi kuma u ve to do it
Zan yi masu mama magana insha Allah zaki ga canji ta ko ina zaki shiga ko ina a dangi kamar da kawai u ve to be strong

Nanah nagode miki
Uhnn ta ce mata sanna ta bata rai
Me kumw kika canja face?

Kawai in na tuna kece sanadi se raina ya baci amma yazan dake after oll ke yar'uwata ce yazan yi

Kin sa ba karatun ba kuma masoyan anyi switching

Kin sa komai yayi upside down

Ayi hakuri nanah a yafe ni nayi azanci na sani kuma ina dana sani yanzu ki yafe min

Ta wuce
Bara na dora abinci
Ki barshi zan yi
No baki da lafiya ai barshi zan dora
To

Amma nanah kin ga yadda kika canjs kuwa?
Haba dai kowa haka yake fada

Ni kuma normal nake
Kin yi haske sosai kuma kin kara kiba

Dariya tayi

Ta shiga kitchen din tana girkin suna hira da ya suhailat din

Ya aleen ko ya dawo?
Ina fa ni mantawa nake da rayuwan sa fa

Haba dai
Eh man me ruwa na dashi yayi ta zama can nima nayi ta zamana yafi min dadi ni na san muguntan sa.

Ai shi kennan

😍 fans weekend mubarak.
*#teamfatimaaliyu*
[20:08, 27/08/2017] khairee muhammad sani: *NANA FATIMA*
*gajeran labari*
*lurve story*
*na khairat up*
*15*
*dedicated to fatima iaa*


Da magrib kamal suka dawo bayan sun yi sallah sun ci abinci tare gaba dayan su cikin plate daya babba kaman ba abunda ya faru ko ya hadasu dazun bayan isha suka dau haramar komawa gida.

Ya kamal muje ta gidan baffa

Yin me?
Zumunci man
Kai nanah na gaji wallahi Allah

Kai ya kamal
Ki bari gobe zan kai ki da yamma da kaina
Gobe zani makaranta

Ohh to da daddaren se muje
To

Salamu alaikum
Wa'alaikum salam
Sai yanzu
Wallahi umma mun sha hira
Ai kun kyauta
Seki zauna ki huta
To umma dan ko na gaji
Seda safe
Allah ya tashe mu lafya
Amin.

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

Aliyu zaune shi da wasu suna tattaunawa game da aikin da suke yi kusan hour din su biyu a cikin dakin sannan suka gama

Be wani zauna ba peter ya fito da wayan sa a hannu ya kame yace sir!

What?
Mail
Uhm ok keep it
Ya ajiye masa wayan ya juya bayan ya sara masa hulan sa ya cire yace hashh

Ya kuna ac din sannan ya dau wayan nasa mail din da ya gani ya dan sa shi ya murmusa sannan yayi reply

Wata tsohuwan budurwan sa ce tun a school can cyprus ta nanne masa taki yinaure shi ne yau ta tuna dashi take fada masa zata zo nigeria nan bada jimawa gun dangin maman ta dakw su a ghana suke kuma zata sauka ne a gidan su

Sunan ta nusaiba (nusy)

Ya ajiye wayan ya shiga wanka yana fitowa ya kira abban shi suka dadde suna hira nan ya sanar masa cewa ana kewarsa nan gida ya kamata ya dawo ya ko assureing din sa ya kusan dawowa.


Kwanaki na ja wattani na ja har seda aliyu yayi wata takwas da yan sattika be dawo ba balle ya waiwayi matarsa

Inna nata fada harda wai a tura ta can garin ya karata amma baza a hana yarinya zaman lafiya ba

Sede nanah ta kyabe fuska tace kan ki ake ji inna.

Suhaila ma tayi amfani da shawarar nanah har ta dawo da martabar ta cikin dangi kuma suna zaune lafiya da mijjn ta in ka gansu bazaka ce auren dole aka musu ba dan mugun kulawa da suke bawa juna duk wata rashin kunya ta daina yin ta tayi ma kanta karatun ta nustsu tana da shigar ciki wata biyu da sati uku yanzun.

Suna zaune a tsakar gida dan an kawo lefen hafsi da khaadja ana ta raha

mama tace wai nike nanah zo nan

Ta mike ta koma kusa da ita
Gani mama

Kina ganin likita kuwa?
Uhm uhm meya faru lafiyata kalau fa

Ai na sani amma ke asiya baki mata zancen zuwa awo ba ?

Awo kuma name?
Mama me kike cewa ?

Ke baku taba lura ba kun bar yarinya a haka

To kin barmu cikin duhu halima meke faruwa ne

Inji inna talai
Maman ta kama salati amma kun bada ni in ita yarinya ce ai ku manya ne

menene wai?
Yarinya na zaune da abu a jikin ta bata da labari kuma baku da labari wasu irin iyaye ne ku?

Nanah ta zabura tace ina zaune da abu kuma? Nifa lafiyata kalau mama ta fada tana zuburar bakin ta kaman tayi kuka

Kalli jikin ta kafafunta sun kumbura
Ke nanah yaushe rabon ki da ganin al'ada?

Ta ma manta se yanzu ma ta tuna ta dadde bata ga period ba tun bayan bikin ta da wata daya.

Mama kusan wata takwas

Takwas inji mama!
Amma baki tambaya ba
Na dauka ba komai ai

To maza ki shirya gobe kuje a duba lafiyan abun cikin ki ayi miki awo

Inna talai ta cafke ikon Allah ni na dade ina wannan tunanin ganin canji a tatrare da ita sossai amma ban san cewa abun ya kai haka ba.

Cikin ya kwanta ba girma kwata kwata ita kuma sokuwa bata fuskanta

Da ihu da sauri tace na shiga uku *ciki kuma?*

Eh ciki fa
Subahanallahi
Wai me kuke cewa haka.

Ciki fa kuka ce mama ni nanah ciki ?
Tabdi jam
Ai se tayi luu ta koma ta fadi sumammiya

Kowa yayo kan ta ana kiran sunan ta.

*#teamnanafatima 😍*
[17:22, 28/08/2017] khairee muhammad sani: *NANA FATIMA*
*lurve story*
*Gajeran labari*
*Na khairat up*
*dedicated to fatima isah*
*16*

Daki suka maidata hankali a tashe matukar gaske

Yayafa mata ruwa aka yi farfadowa tayi tana bude ido ta fashe da kuka se kuma ta riko hannun inna talai tana shan majina ta sharce hawayen ta

Inna kice min ba haka bane ni ban da komai ko ? Inna kice ban da komai ni kinga ba son shi nake ba shi ya aleen

Inna tace me a ciki ai seki yi tayi.mara tunani kawai in kin ga dama ki hau sama ko fado kasa ki kashe kan ki da abun cikin naki me nawa a ciki

Ai kya fada mata inna wannan yarinyar ban san mesa bata da hali ba sam sam bata da mutunci

Suka fice daga dakin daga ita se mama halima a dakin ta ce ba a rayuwa a haka nanah ko da ba kya san mutum ai ba za ka nuna ba musaaman gaban yanuwan sa da mahaifiyarsa tana ji kina kin danta amma bata taba cewa komai ba seki mata kawaici kema ai ko

To ni mama ya kuke so nayi

Mamam ta gyara zaman ta sannan ta soma mata fda tana mata magana a hankali cikin nutsuwa har seda ta ga alamun ta hakura sannan ta fita.

Kuka ta fashe da shi ta kuma shafi cikin cikin nata cike da mammaki matuka dan bata taba zaton haka ba ko a mafarki.


Washe gari suka je asibiti aka tabbatar da ciki ne kuma dan wata takwas cif cif kuma lafiya babyn yake sede adduan Allah raba lafiya.

*bayan wata biyu*

Nanah na hango cikin riga doguwa tana zaunw tsakar gida ita da umman ta saura duk sun je bikin wata makotan su.

Abba ya shigo da kaya niki niki yana ajiyewa shi da ya majeed

Ya majeed kayan me ?
Wallahi nima ban sani ba nanah ni ai dan taya aiki ne

To

Seda ya gama ya zauna umma ta kawo masa ruwa ya sha sannan ta zauna kusa dashi majeed ma ya zauna dan jin karin bayani

Kun ga kaya ko?
Eh
Kayan haihuwan uwata ne
Nanah?
Eh
Da kayan sawa da na abinci komai na tanada

Lallai kana ji da uwanin nan inji ya majeed

Allah dai ya raba lafiya in ji umma
Amin

Kasa tayi da kanta taji hawayen dadi wanda ya kamata yayi bema san ana yi ba se shi Allah yamaka kaima abbana

Ta fada a ranta.

Adaren ranan suna hira nakuda ta kama ta karshen dauriya nanah tayi shi tana cicijewa

Umma tace lafiya nanah ko muje asibitin

Uhm uhm ni lau nake
Suka cigaba da hirar su

Ae gumi take ta ko inna
Inna talai tace nanah ko de muje naga kina gumi
Ah ah inna
In naji ciwo xan fada muku

Bara na shiga cikin daki bacci nake ji.

Mikewan da zata yi taji bayan ta ya rike takoma ta zauna tace wash wayyo Allah na

Umma !
Zan mutu
ki yafe min
Umma bsyana
Umma kuguna
Umma cikna!

Umm......se kuma ta koma salati tana cije lebban ta

Kanta suka yo gaba daya daki suka kaita daga inna talai se mama karama a dkin haihuwan

Kowa na waje amma hankali a tashe.

******* *****

Bayan wasu lokuta ta sauka lafiya santaleliyar budurwa jajir da ita masha Allah kubul kubul da ita

Bayan kowa ys amsa ana ganin ta kowa na tofa albarkacin bakin sa kowa kaman ya alee ta dauko

Bayan an gyara ta da babbyn ta umma ta bata kunu tasha suka kaita asibiti aka duba su kowa lafiya sannan suka dawo gida

Hafsi tace masha Allah babyn nan sak ya alee very cute da ita

Bata dai tanka musu ba ita kam balle tace a bata ita tasan wuyan data sha wajan haifo babyn nan banda ikon Allah waya isa? Babu

Ya majeed na kallon ya hashim daya rike yar yace waxe ce wannan yarinyar zatazo da kauri dubi fa cikin ba a ganin sa har ya girma ba dan mama ta toni asirin shi ba

Gaskiya kam amma yarinyar da jikin ta wallahi.

Amsa kigani zahra ya hashim ya fada
Ta dauke kai
Ya majeed ya dauka ya dora mata a hannu ita babyn ina ruwan ta eh da zaki shafa mata kiyayya

Ta dan hararshi nida nayi wahalan ta baku ce min sannu ba baku ce min muna kama ba se ta ita kuke

Aka sa mata dariya
Kaka tace ai jikin naki ne nanah.

Daukan babyn tayi tace masha Allah tubarkallah gaskiya yarinyan nan tayi hawayen dadi taji wannan babyn tawa ce daga jikina ta fito jini na ce alhamdulilahi Allah nagode ma da wannan kyautar me girma

Ban ita inji ya suhailat
Wow
Amma naji dadi Allah raya mana baby
Amin.

Allah raya mana new born baby!
*#teamfatimaaliyu*
[09:25, 29/08/2017] khairee muhammad sani: *NANA FATIMA*
*gajeran labari*
*Lurv story*
*Na khairat up*

*17*
*Dedicated to fatima isa*

Kowa santin babyn ya ke yi dan masha Allah tayi kyau sosaai

Gata jajjir
Kubul kubul da ita tubarkallah.

Sanda abba ya kira aliyu be same shi ba yasan kennan ya tafi yakin da zasu se kawai ya masa mail ya ajiye wayan ya masu adduan samun nasara a abunda suka je yi.

Nanah ko Allah ya dora mata son babyn kaman me wata sa'in ta kura mata ido ta mata kuri da ido wani sa'in kuma tayi ta mata magana
Sun sha wanka sossai gun inna talai ita da jaririyar

Ana gobe suna ana ta shirye shiryen suna suna tsakar gida ana ayyuka ana hira

Hashim ya shigo da kaya a hannun sa ya ajiye ya kalli naseer yace masa ka daure ragunan nan a waje

To

Ya zauna
Suhailat ta basa ruwa ya sha ya ce ban abinci in da akwai

To
Tuwo ne amma
Kawo kadan bada yawa ba

Ta kawo masa ta ajiye yana ci ya ce ku dinga masa addu'a sun dade suna fama ba ma a san taka mai mai inda suke ba yanzu kaman an far musu kaman abin yayi tsamari

Inna talai tace ai inaji masa wannan aiki Allah yakiyaye su dukkan su ys basu sa'a

Amin inna

To wane suna za a sa ma yarinyar

Ai ina ga a tambayi abba ko

Ai sunce kaine madadin sa ka fada

To inna a sa mata sunan mama man nasan ko shi haka zeyi tuanin a yi .
Allah raya mana nafisat
Amin.

Washe gari aka sa mata nafisat suhailat tace a dinga ce mata *amal*


Wasa wasa wata uku da tafiyan aliyu kuma daidai da girman amal

Ba labarin sa lokacin hankula sun tashi sossai da sossai ana tunanin ina ya aliyu saboda haka ma aka daga bikin hassan da hussain da hafsi da khadija har se an samu labarin sa.

Amma mutuniyar ko a jikin ta ita kawai seta tsinci kanta da jindadin rashin dawowan sa .

Nonon nanah ko ya karbe ta sosaai ta kuma yin kiba.

Abba yasa kullum se an yi sauka a gidan kuma ana karatu dan bayyanar aliyu.

Makarantarta ta cigaba da zuwa daukan karatu da kuma koyan dinki abinta bata da wata damuwa.

*bayan shekara biyu*

Mami
Uhm amal
Mami ni zani aunty suhailat
Uhm kije abba ya kai ki
Abba yace bai zuwa yana aiki
Hah abban?
Uhm abba
To abba kamal fa?
Shi baya nan ta fada kaman zatai kuka
To mezaki yi gun auntyn?
Ni gun fauzan zani muyi wasa
Kai kai gaskiya ya kamata a kai ki kam
Taso muje ki fadawa umma tasa a kai ki

Ta mike rke da hannun ta tana mata hira har suka je kofar dakin umma

Umma ga kishiyarki zata unguwa ki samu me kaita

Wannan me kama da ruwan hodan ina zata

Amal tace gun fauzan wasa

Hah bakin wasa
To ina abba majeed din naki
Wai yana aiki
Kai to abba kamal fa
Baya nan

To ki bari anjima in wani ya shigo se a kai ki

Ta zauna a kasa dirshan ta dinga kuka tana ihu

Nanah ta dinga mata dariya ita kam ta zauna sega hashimu ya shigo

Ys karasa inda take da sauri ya dagota ya dauketa waye ya taba min amal

Abba mami da umma ta fada tana kuka

ya harari nanah yace dan me ?

Saboda rigimar ta dai ni ina ruwq na

To me kike so
Ni gun fauzan
Yace to hau muje ya goyata ta soma dariya sukq tafi abinsu.

Umma tace badan hashim ba da sauram maxan gidan nan da bamu san ya zamuyi da amal ba wajan samun soyayyar uba mussaman hashim

Allah ya bayyana aliyu shi ya yaxo yaga kwansa a duniya

Amin nanah ta fada ta koma cikin dakin ta.

Hakika in tace bata damu ba da rashin aliyu tayi karya dan abun ya zama babba daga wata an koma shekara daga shekarq daya ya zama shekarq biyu lallai akwai matsala koda ba so a tsakanin su akwai zumunci da yanuwan taka ya kamata ta kuma dagewa da addua Allah bayyana mata aliyu kodan farin cikin amal da iyayyen su.

*************
Mami
Uhm
Mamai yaushe abba ze dawo?
Uhm ze dawo bada daddewa ba my amal

Mami wai abba soja
Eh
Mami me soja?
Suna tsare mu ne daga miyagun makiya
To su waye makiyan

Amal sleep dare
Aa mamai ni moon zan gani

Ai seki ta zama
Ta zame ta kwanta ta juya mata baya tana nazarin wasu abubuwa

Amal ta kwanta a bayan ta tace mami wai ya kaman abba na yake

Ta juya tana kallon ta yadda tayi tambaya kaman wata babba ba yar shekarw biyu ba

Amal abban ki kaman abba hashim

Hah ai naga hoton sa abbana me kyau ne da kayan yaki

Tayi murmushi amal yau hiran abban ki zamu yi ba bacci ko?

Uhm mami na
To baki isa ba ki koma can gun kakarki ni bacci zan yi

mami ke dai
Uhm amal bacci .

Ta dings mata tafiyan tsutsa a kafa tace hah amal mugunta ki bari zan rama fa

mami hira
Amal bacci
Mami hira
Amal bacci
Ta juyo tana mata cakulkuli
Ta dinga dariya mami na daina zan yi baccin mami sorryna

Ta ce oya ayi bacci ta mata addua ta tofa mata sannan ta rungumeta suka yi bacci
*#teamaliyufatima*
[11:10, 29/08/2017] khairee muhammad sani: *NANA FATIMA*
*gajeran labari*
*Lurv story*
*Na khairat up*

*Dedicated to fatima isa*
*18*

Amal! Amal!
Uhm abban
Kina ina yan mata na?
Ka nemo ni na buya
Ah lallai amal an wayo ko
Uhm uhm
Ai na ganki a bayan tv
Hah abba ai bazan fada ma ina bayan kujera ba

Ya sa dariya yana zagayawa nima ban san kina ina ba ya cafko ta
Hah wa na kama?

Ta dinga dariya abba ojoro
Ah amal ojoro

Umma ta shigo da shayi da kwai ta ajiye kan tebur

Amal muje ki ci naki abincin

Ai abba kazami shan shayi
Ya gutsri kwai yana dariya yace kai wannan yarinyar kaman ya aleeyu basa san shayi da kwai ji yanda take min da hanci wai kazami umma kwashi jikar ki ku je ta karya karta hana ni cin abinci

Suna dariya suka tafi falo

Doya aka soya mata fara da dankali ta zauna tana ci.

Wai umma baza ku yi bikin su ya hussain ba kuna ta jiran shi bayan ba wani labari

To ya kike so ayi biki aliyu baya nan ai bayi tunani be se uwarsa tace ba a damu ba da batan dan ta

Amma su kuma fa ana ta shiga rayuwan su ko

Ke de ba ruwanki ba maganar ki bace ba ko
Ai shi kennsn Allah ya kaimu
Amin.

********* *******

Baka san zumudin da nake ba bilal yau burina ze cika mun samu abunda muke so kaga wannan hoton

Wow
Na waye?
Na yata ne yar da na bari cikin jikin nanah gashi ta haifa min

Amma yanzu nasab tafi haka ni yanzu airport zan je nayi booking na tafi nasan suna can suna nemana sun dimauce shekara biyu fa da wattani ba waya ba sako ai an shiga hakkin su da yawa

Haka ne ina ga tare zamu je da kai su san cewa bada san ka hakan ta faru ba kaddara ce kuma kaima kaga ta kan ka nasan karfin addua ce ta cece mu daga wannan bala'i da muka shiga Allah ya kuma kiyayewa

Hmmm! Ban taba sanin cewa ina da jigon komawa gida ba amma kawai sanadin wannan yarinyar zan koma gida da kwarin gwiwa nima na zama uba duk da nanah bata cikim.tsarin rayuwata

Ina aliyu nanah ko ita ce tsarin rayuwan ka banda gulma fa

Hmm kai bazaka yarda ba ni ban iya sharing din abuna da wani ba

Wane irin sharing
Bazan iya son nanah ba saboda ina da kishi kuma nanah tayi soyayya da dan uwna hashim har yau nasan tana son sa kaga kau bazan iya sharing heart dins da wani ba ni nafi son abuna ya kasance abu na ni daya ba tare da kowa ba

Amma wannan ya wuce

Man kyale ni bara nayi wanka nayi packing kayana daga nan se nigeria to my family to my daughter my life!

Tare suka fita daga dakin kowa ya shiga nasa respective toilet din.

*******************

Tun safe gaban ta yake faduwa ta dinga innalillahi a ranta ko irin walwalar nan ba ta yi kaman na sauran lokuta har seda amal ta dawo tayi ta mata hira bata wani kulata da kuka amal ta fita daga dakin nanah

Yaya majeed ya dauketa yace me amal mesa kike kuka?

Ba mami na bace ina mata hira bata kula ni

Ai mamin ki yar kauye ce muje na siya miki sweet

Ta hade rai ni mami na ba an kauye bace ba yab gayu ce

To abun ds zaki min kennan

Ta ce uhm
Abbs muje sweet

To ni na fasa
Ta bata rai zats bare masa baki tasa kuka yace dan Allah ki tausaya min kar kiyi kukan nsn zan kai ki muje wannsn hawayen naki ai me tsada ne

To muje abba majeed
To *amal aliyu*

******************
Wajan karfe goma da rabi na dare wayan kamal na ringing dake suna kofar gida a zaune suna kan daddamu suna hira da flssk na tea a gaban su

mikewr da suka ga kamal yayi shi ya daga musu hankali meye

Ina zuwa
Daukan wayan yayi hannun sa na rawa

Ban ce kace komai ba ina airport silently ka taho ban san hayaniya nasan kuna cikin wannan hayaniyan.majjalisar ka zo yanzu.

To

Ya wuce kuma ina zaka?
Ina zuwa

Da gudu ya shiga mota yana gudu har yaje airport din

A kan kujera ya same shi a zaune shi da bilal ya wani daure fuska

Da sauri kamal ya shiga da gudu ya fada kan aliyu ya sa kuka

Aliyun yana murmshi yace wai ku

Please Login or Register in order to submit comment