Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinta na masu takaba ya shigo da sallamarsa Maliha da Shuraif sukayi tsalle suka rungumeshi Twince kuwa da suke koyon zama sai bangale masa baki sukeyi murmushi yayi me hade da kwallah yana tuna irin wulaqancin daya rinqa yiwa mahaifinsu lkcn da yana neman auren Umaimah ya sunkuya ya daukesu ya rungumesu a jikinsa wani kuka me qarfi ya kwace masa yayi saurin tashi daga gurin ya shige dakinsa da yaran ko gaisawa da Hajiya bai iya yi ba balle Umaimah tasaran zaiyi mata ta'aziyyar mijinta, itama batasan sanda mikin mutuwar D.S ya dawo Mata sabo.......







*UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß*
[2/3, 11:53 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *_GU_*






















Miqewa tayi ta shige dakinta ta kwanta tanajin haushi da tsanar duk wanda ya kasa yi mata gaisuwar rashin mijinta da takejin bazata mayar da kamarsa ba a duniya.
Shima ya jima yana kallon Nawwas da Nawwarah yana kuka yaran sai wasa sukeyi da gashin qirjinsa sunayi masa dariya kamar Nawwas da mahaifinsa har tayi yawa kamar dai shida Shuraif abubuwan da yayiwa D.S suna sake bijiro masa musamman haduwarsu ta qarshe lkcn mutuwar Nihal da Shurafah da yazo daukarta yana ganinsa yana miqa masa hanu ya bige hanunsa ya wucce hakan baisa yaji haushi ba washe gari ma daya dawo karba mawa Umaimah yajin daddawa lkcn da cikin yaran saida ya sake miqa masa hanu da yaqi bashi nasa kawai sai yaga ya share qwallah ya rungumeshi yace.




 Kada ka qullaceni a zuciyarka Yaya banine na rabaka da Umaimah ba qaddara ce kuma nima itace ta hadani da ita wlh da inada ikon halatta maka Umaimah tun kafin muyi aure zan halatta maka ita saboda nasani kaine Umaimah takeso kaima kuma ita kakeso amma Ina banida damar hakan abu dayane zai hanani dawo maka da Umaimah saboda ina burin rayuwarta ta samu farin ciki Hameed ka qaddara idan Umaimah rabonka ce zata dawo gareka amma bayan qasa ta rufe idona saboda a tsarin rayuwata mace ko cutar dani take indai bazata cutar da Umaimah ba zan rayu da ita balle Umaimah da kullum burinta farin cikina Hameed idan na mutu bana fatan kabar Umaimah ta auri wani bakai ba saboda Ina kishinta kuma nasan zaka riqemin dana saboda kanada imani kuma kanason uwarsu"




Yana fadin haka ya sakeshi ya shiga motarsa yaja yana daga masa hannu yanayi masa murmushinsa me tsayawa s zuciya  kyakkyawan namiji me kyakkyawan hali da sanyin zuciya ya mutu" ya fada yana rungume yaran a jikinsa yace  dole Umaimah tayi kuka saboda tayi rashin miji na qwarai amma nasani bazai fini sonta ba kuma zanyi iyakar qoqarina naga na bata farin ciki fiye da wanda yake burin bata zan riqe maka yayanka kamar nawa har qarshan numfashina Sulaiman Allah ya gafarts maka"




Yana mgnr yana kuka da shishi kamar qaramin yaro tunda yake baitabajin mutuwar data girgiza shi kamar ta Sulaiman ba ko mutuwar yayanss biyu batayi masa dukan mutuwar Sulaiman ba musamman idan ya kalli yaran sai yace  yanzu fah yanason rayuwa dasu Allah ya karbi rayuwarsa ko? Meyesa a duniya mutanen kirki basa dadewa?" Ya tambayi kansa tare da kwantar da yaran da sukayi bacci a gefensa ya ja blanket ya rufesu ya tashi ya dauro alwala yayi sallar Isha yayi shafa'i da wuturi yaci gaba da addu'a rabin addu'ar tasa ga Sulaiman ne yana kuka yana roqon Allah ya bashi hqr da kyawawan halaye da kyakkyawar mu'amala irinta Sulaiman.




Bayan ya gama ya fita ya nufi kitchen domin dauko fresh milk sukayi clear da ido ido cikin ido amma sai ta dauke kai duk da ramar da tayi amma kyawunta yananan rabawa tayi ta gefensa ta wucce yabi bayanta da kallo bakinsa ya kulle ya kasa yi mata mgn gaisuwa yakeson yi mata amma ya kasa harta shige dakinta sannan ya juya kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya dauki madarar ya fita ya koma ya zauna gabansa na faduwa yana korar shaidan saboda yanda yake qawata nasa surar qanwar tasa bayan tana cikin halin takaba wanda ko kalma ta so baa so ta shiga tsakinsu hakan wani zunubi ne me girma.




Itama tana shiga ta kwanta badon tayi bacci ba saidon ta bawa zuciyarta hutu da tunanin mijinta Sulaiman daya kasa gogewa a ranta tanason taji yayanta a kusa da ita amma babu dama taso tambayar sa yaranta amma tana tsoron tujararsa don tasan ba mutunci ya cika ba bare yau da take ganinsa duk a firgice da haka dai bacci ya dauketa tunda ba sallah zatayi ba sai asuba ta tashi tayi wankan tsarki tayi sallah sannan ta gyara jikinta ta koma ta kwanta bata fito daga dakin ba sai goma saura ta fito sanye da hijjabin ta har qasa lkcn suna parlourn shida Hajiya da Daddy yanata tura twince din a motocinsu na wasa suna zagaya dakin sunata dariya shima yana tayasu qasan zuciyarsa cunkushe da tunanin ta inda zai fara da uwarsu don baiga alamun sauqi daga gareta ba ya lura tausayin ma nasa da takeji ya goge a idonta yanzj tsanarsa kawai yake hangowa a qwayar idonta zama tayi kusa da Hajiya tace.




 Morning Dad " murmushi yayi yace  Uwata tafi ta kowa kin tash lfy ya kayan lada" qasa tayi da kanta tace  alhmdllh" suka gaisa da Hajiya shima yazo ya zauna shine ya karya billen da cewa  qanwata ba fada meye ya kawo gaba?" Qasa tayi da idonta ya kumayin murmushi ya matsa ya zauna a kujerar dake kusa da ita yace  wlh ba laifina bane bansan Abu Nawwas ya rasu ba sai shekaran jiya Daddy yake fadamin kiyi hqr Allah ya jiqanshi ya gafarta masa Allah ya raya mana twins dinmu cikin imani"




Amsawa sukayi da amin ta daidai lkcn da Nawwas ya turo motarsa yazo ya riqeta ta dagoshi tana dariya tana cewa  Ehhh yarona bature na Ina kuka kwana ne yau Hajiya a gurinki suka kwana?" Dariya Hajiya tayi tace  aa nikam ai bana gayyar fitsari gurin ubansu suka kwana" yayi dariya yace  aikuwa nasha fitsari ta ko ina har gara Little ita nata da sauqi amma wannan fumfumgaron daya rinqa antaya min fitsari saida nayi zaton a swimming pool nake yasin" ba Hajiya da Daddy ba hatta Umaimah saida tayi dariya kyawawan haqoranta suka bayyana da yar siririyar wushiryarta dimples dinta suka lotsa sosai tuni Hameed ya shagala da kallonta rabonsa da ganin dariyar Umaimah haka tun tana gdansa shekara kusan biyu kenan da rabi.



Hajiya ce ta lura da inda hankalinsa yake ta dauki pillow ta jefeshi yayi firgigit ya dawo hayyacinsa yana sauke ajiyar zuciya ya miqe yace  a bawa twins abincinsu susha zasu rakani anguwa yana fadin haka ya shige dakinsa ya fada gadi yanajin wani farin ciki a ransa yaudai yaga dariyar Umaimatu wanka ya shiga ya fito ya shirya cikin qananun kaya ya taje kwantacciyar sumarsa data qara kwanciya chocolate din fatarsa tayi wani mugun kyau da haske ya zama fari ma zaace saboda hutun California.
Fitowa yayi ya tarar sai Umaimah kadai a parlourn tana riqe da qaramin qur'ani a hanunta ya jima yana kallonta kafin ta dago suka hada ido yace  ina yarana an shirya su?" Daga masa kai kawai tayi taci gaba da karatun ta baiji dadin yanda tayi masa ba amma haka ya danne ya nufi dakin da yake jiyo hayaniyar su ya daukosu suka fice.




Basu dawo gdan ba sai yamma liqis yana zuwa ya tarar da Hajiya Sa'adatu kakar twins da Nazir Sulaiman wanda suke tsananin kama da Sulaiman din suna zaune a parlourn Umaimah na gefe sunata hirarsu da Nazir yana bata lbrn aikin daya samu a Abuja ba qaramin faduwa gabansa yayi ba da ganin Nazir saboda tsananin kamarsa da Sulaiman har tayi yawa jiki kawai Sulaiman zai fishi da kuma shekaru.
Nazir yana ganinsa ya miqe ya miqa masa hanu ya karbi Nawwas da yaketa washe baki yace  oyoyo my son inata missing dinka long time aiki ya boyeni" yana mgn yana miqawa Hameed hannu shima ya miqa masa daqyar ya tsaya suka gaisa da Hajiya Sa'adatu yayi musu ta'aziyya ya shige daki yana kaiwa da komowa yana ayyanawa a ransa  dama Sulaiman yanada qani karfa qanin yace yanason zai auri Umaimah" gabansa ya sake bada wani rasss yace  aa ne bama zai yuwu ba wlh Umaimah tawace wannan karon da yardar Allah komawa yayi ya zauna zuciyarsa nayi masa zafi a fili yace  Allah kada ka qara jarabtata da rasa bloody a wannan karon Allah kafi kowa sanin halin da nake ciki ka qadarta min rabuwa da ita nace ka kasheni kaqi yanzun kuma ka sake rabani da ita Allah kada kayimin haka idan laifin dana aikata makane na tuba Allah astagfurullah ya Allah su Uncle manya>Ø#Ý
Kwanansa tara a garin Kano ya koma California.




Kwanci tashi babu wuya gurin lillahi yau litinin ta kama ranar da Umaimah ta gama takabarta takaba mai tsarki tayiwa Sulaiman ba irin takabar matan zamanin nan ba.
A washe garin ranar kuwa Hameed ya shigo garin cike da farin ciki amma me daga bakin get yayi turus ganin baquwar mota a gdan Umaimah ce tsaye sanye da hijjab dinta har qasa ita da Nazir ya kawo Mata wasu takardun filayen Sulaiman yana tsokanarta kan cewa taba dakai bori ya hau kawai ya taimaketa ya aureta tunda Sulaiman ya wullah takai masa duka tana dariya ya kauce tace  yaron nan ka rainani da yawa kalleni dakyau ka gani ni saarka ce?"




Suna dariya driven ya fito a mota ya bude masa shima ya fito ya zuba idonsa akanta idonsu ya sarqe da juna duk da nasa a cikin glass yake gabanta ya fadi sosai da taga ya nufosu ga mamakinta yana zuwa taga ya miqawa Nazir hanu sunyi musabiha ya cire glass din idonsa ya zuba idonsa akanta sosai yace  barka bloody sister".......







*UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß*
[2/3, 7:16 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *_GU_*





















Dagowa tayi ya sakar mata mayaudarin murmushinsa yace  muje inason ganawa dake" kawar da kanta tayi tace  kaje Ina zuwa" yanda tayi mgnr ba qaramin bata masa rai yayi ba amma tunda nema yakeyi sai kawai yayi gaba tabi bayansa da kallo tayi qwafa sukaci gaba da hirarsu da Nazir saida ta bata kusan awa guda sannan sukayi sallama ta nufi cikin gdan tun a qofa ta cire hijjab dinta tana cewa  gsky Hajiya weather din yau batada dadi ga zafi..."



Mgnr ce ta maqale a bakinta yanda taga ya zuba mata ido sun kada sunyi jawur ta kawar da kanta da sauri ta dauki Nawwarah ta nufi dakinta da sauri ta mayar ta kulle tana ajiyar zuciya koda yamma ma data fito yana zaune inda ta barshi da Nawwas a hannunsa Shuraif yanata zuba masa surutu amma hankalinsa baya kansu tazo ta giftashi sanye da wata riga fitted sheet iyakar qwaurinta ta hada gashinta ta daure gashin goshinta da yake gaf da hadewa da girarta ya kwanta luf cikakken qirjinta ya tsaya qam kamar bata taba shayarwa ba rigar ta kamata sosai ta fitar da qirarta da sheps dinta.



Allah ya sani badonshi tayi shigarba saboda yanayin zafin da ake cikine kawai ya raya mata tayi hakan kuma tanajin sha'awar sanya qananan kayan saboda rabonta dasu tun ana gobe Sulaiman zai rasu kitchen ta shiga domin dauko cake yabita da wani wahalallan kallo numfashinsa na shirin barin jikinsa yace  Tabarakallahu ahsanal kaliqin" yanajin wani irin yarr a jikinsa tsigar jikinsa tana tashi ya rasa meyasa yake mugun sha'awar Umaimah tunda yake baitabajin yanayin da yakeji akanta akan wata mace ba yana hasaso irin dadin dake qasanta har wani yawu ya hadiya ya miqe zaune tare da matse qafafunsa ya tashi da sauri ya shiga dakinsa ya riqe gabansa da hanunsa da qarfi yanajin wani feeling na bijiro masa ya dauki wani qwayar magani ya hadiya ya kora da ruwa saboda yanzu itace ta zame masa taimako gareshi donma shi kansa yasan a cikin lalurarsa kashi dari yanzu babu talatin tunda yakanyi sati gudama baiji sha'awar jima'i ta bijiro masa ba.



Ranar bai sake fitowa ba saida safe ya fito ya zauna a dinning ya fara break yana raba idon ganinta amma shiru can yaji murda handle dinta ya zubawa qofar ido ta fito cikin shigarta ta alfarma data qara fito da asalin kyawunta sanye take da wata yaluwar atamfa dinkin doguwar riga data baje sosai a ciki ta yafa blue din mayafi takalmi da jakarta duk blue sai wata siririyar sarqa data sanya a wuyanta ta gold wadda kyautar Sulaiman ta haihuwar twins kudin sarqar ya haura million biyu amma Idan ka ganta a ido zaka dauka batafi dari biyar ba saboda sirantarta ta zauna dass a wuyan Umaimah da zobunan sarqar suma sirara guda biyu sai agogonta shima gold kai iya haduwa ta hadu Hameed kusan qwarewa yayi saboda kallonta ta zuba masa ido ta cikin siririn glass din dake idonta shima ita yake kallo ta rungume Daddy tace  morning lovely" yayi kissing dinta yace  morning lovely daughter" ta sakeshi ta sake rungume Hajiya tace  ina fatan uwata abar faharina ta tashi lfy" dariya Hajiya tayi tace  qlau yar albarka yau sai skull kenan?"




Ta gyada kai ta dagawa Hameed hanun tace  Hi brother" tana fadin haka ta juya ta fara tafiya da sauri tace  nayi let Hajiya bazan samu karyawa a gdannan ba Allah yasa ma Hassan ya wankemin motar ji tayi yace  jirani nazo na kaiki tayi kamar batajishi ba Daddy ne yace  bakiji ba yayanki yana miki mgn uwata" tsayawa tayi cike da takaici ya miqe ya nufi dakinsa ya dauko mukullin da wayoyinsa ya fito suka jera suka fito abin gwanin sha'awa ya bude mata ta shiga shima ya shiga yaja suka fita daga gdan suka dauki hanya a hankali yake tafiya cike da nishadi ya sanya waqar R-kelly yana sauraro zuciyarsa na raya masa yayi mata mgn amma girman kai da izzah irin tasa ya hanashi waishi jira yake tayi masa mgn haka har suka isa harabar mkrntar yayi parking a wani guri me yalwar bishiyoyi da furanni ya kalleta sosai yace  qarfe nawa zaku fito?" Batare da tunanin komai ba tace masa  hudu" tana bude qofar ya ruqo hanunta yace  ki kula da kanki zan dawo na daukeki" bata bashi amsa ba sai fita da tayi ta nufi Hall din nasu yabi bayanta da kallo tun kafin ta ida shiga suka hadu da Prof Khair wani balaraban Qatar ne da yazo Reasech a skul din kusan tare tasanshi da D.S yana ganinta ya tsaya yanayi mata murmushi itama murmushin tayi ta qarasa suka gaisa sosai ya tambayeta yara tace suna qlau yaci gaba da janta da hira har suka isa Hall din ta shiga shikuma ya wucce apartment din da yake duk wannan abun akan idon Hameed ya hadiya sosai  wato har larabawa take kulawa" ya fada yana bawa motar tasa wuta ya juya ya fice ya nufi sabon gdan da yake ginawa a Ribadu road Hameed kwai dan wawuya duk gdajansa hudu ya siyar idan baku manta ba yana da gda a Nassarawa G.R.A inda Sadiya ta zauna sannan yanada wanda ya ginawa Umaimah a Zingeru road sannan wanda ya siya Mata a Farawa layout sukayi zaman daduro still wanda ya gina na qarshe me part biyu da suka zauna ita da Salma amma duka ya tattara ya siyar ya zuba kudin a gidan gonarsa sai yanzu da akace masa mijinta ya rasu yazo yasai wani katafaran floot a Ribadu road ya wawaki gini na uban ubansun ya fara batare da iyayensa ma sun sani ba saidai ya turowa Yusuf kudin shikuma ya bawa yan kwangila aikuwa aikin yana tafiya sosai duk da bashi da burin idan sunyi aure su zauna anan California zai tafi da ita tayi master da PhD dinta acan in yaso idan wani Abu ya tashi sunzo sake sauka anan.



Yaje ya yini sur a gurin aikin ginin qarshe uku da rabi ya koma makarantarsu yana zuwa ya kirata tana ganin kiran taqi dagawa Saudat Alfah ta kalleta tace  ba wayarki ake kiraba" tabe baki tayi tace  itace mana niyyar dagawa ne banyi ba" daukar wayar Saudat tayi har yanzu sunan sa haka yake  Bloody" tayi murmushi tace  Allah sarki masoyan asali Umaimah jinki kawai nakeyi wlh bazaki taba iya rabuwa da Hameed ba kada ki wahalar da shari'a ki bada kai kawai bori ya hau dama rabon twins ne ya rabaku kuma rabon wasu da bamusan adadinsu ba ya kashe D.S saboda haka kiyi hqr kawai ki rungumi qaddara wlh a duk duniya baki da masoyi saman Hameed"




Daga mata hanu tayi ta miqe tace  inma kwangila ya baki to kice masa nafi qarfinsa yanzu idona yayi budewar da bazan iya hqr da mulkin kama karyarsa da son kansa ba nariga na shaqi iskar yanci D.S ya nunamin yancina ya bayyana min cewa zaman aure ba zaman bauta bane zamane na yanci kuma rayuwace me dadi a cikinsa inason Hameed nasani shidin wani bangare ne na rayuwata amma bazan iya sake rayuwar aure dashi ba keni auren ma gaba daya ya ficemin a kaina bana sha'awar sake aure a rayuwata wlh" miqewa Saudat tayi suka jero suka fito tana tafe tana rangaji kamar bishiyar gamji harta qaraso inda ta hangi motarsa sukayi sallama da Saudat ya bude mata ta shiga yaja suka tafi yanajin kishinta a ransa baisan sanda yace.




 Waye wanda kuka jera dashi dazu kuka shiga ciki dashi" batare da damuwar komai ba tace  abokin mijina ne" ya kalleta da sauri yace  abokin mijinki ince dai ba mijin naki bane?" Tabe baki tayi tace  ba abin mamaki bane idan kaji cewa ya zama mijin nawa ma..." wani uban birki daya taka shine yasata saurin dagowa tayi baya tayi gaba kawai saita fada jikinsa ya sauke wata ajiyar zuciya me qarfi yasa hanunsa ya maqaleta daga ita har shi sunajin wani irin yanayi a jikinsu janyewa tayi da sauri ta koma ta zauna ya sauke numfashi ya bude idanunsa akanta yace.




 Don Allah kiyi hqr da wasannan da kikeso muyi wahala zansha ki bani dama ta qarshe bloody idan har nayi wasa da ita kiyimin duk hukuncin da kikaga ya dace kada ki tausayamin amma yanzu ni abin tausayi ne a gurinki saboda zuciyata takasa hqr dake nayi iyakar qoqarina naga na cireki a raina amma na kasa nayiwa Daddy mgnr aurena dake tun jiya yace bazai miki dole ba sai abinda kikeso zaiyi miki har yana gargadina kada na takura miki"



Kallonsa tayi da wani irin salo na baka da wayo tace  aure kuma" dagowa yayi yace  Eh haka nace" dariya tayi sosai tace  tab kana ruwa iya wuya kuwa" daga haka bata kuma cewa komai ba shima baice ba yaja motar suka tafi gdan gonarsa yakaita yayi horn megadin ya bude ya shiga gurin ya girma sosai ya qawatu bangaren kaji daban na kifaye daban na gigs daban na shanun madara daban da bangaren tsuntsaye irinsu talo² dawisu da jimina abun dai baa cewa komai.
Wata qofa ya bude ya shiga ya tsaya yana jiranta amma sai yaga ta cake a waje ta tsuke fuska sosai ta yanda saida yaji gabansa ya fadi ta motsa dan qaramin bakinta tace  bance da Hajiya zan biyoka muzo nan ba saboda haka kazo ka mayar dani gda ko na fita na nemi abin hawa




Murmushi yayi ya fito ya janyo qofar ya rufe ya qarasa kusa da ita yace  kina tsoron kada nayi miki fyade ko? Hmn itadai batace komai ba suka koma suka shiga motar suka tafi gda suna zuwa ta bude zata fita ya ruqo hanunta ta juyo idonsu ya hadu tayi saurin janye nata yace  ki daina jamin aji Umaimah ni ba wanda zaki jawa aji bane ko yau kika amince min gobe zaa daura aurenmu so nakema naje nayi miki VISA saboda nagaji da zaman kadaici wlh kuma duk saboda kene bloody bazan iya zama da wata mace ba bayan ke idan har na rasaki to na hqr da aure har abada balle ma bazan rasaki ba wannan karon wancan ma qaddara ce ta rabamu kalaman nasa mugun qonanta zuciya sukeyi saboda haka ta fizge hanunta ta shiga cikin gdan a fusace.........







*UMMUH HAIRAN CE...*
'<Øûß
[2/4, 9:05 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *_GU_*


























Yanda Hajiya taga ta shigo gdanne yasata zuba mata ido sannu kawai tace mata ta bude qofar ta shiga daidai lkcn dashi kuma ya shigo gdan shima baiyiwa Hajiyan mgn ba ya shige dakinsa ya kwanta ya lura wahala zaisha sosai da Umaimah tunda ya fahimci babu digon tausayinsa a qwayar idonta amma duk da haka zai jure zai gwada tasa baiwar har ya cimma gaci.



Wayarsa ya dauka yayi short write ya tura mata tana zaune a bakin gado tana feeling din yayanta tana kallonsu saqon nasa ya shigo ta dauka ta bude
_Tunda na rasaki Umaimah mace ta fita a raina ki daina jin tsorona wlh ba Hameed din da bane nasamu lfy ki bani dama bloody banason komawa California batare dake ba banajin dadin rayuwa ni kadai bloody inason mu rayu tare yaranmu su rayu a cikin kulawar mu inason twins dina amana tace babansu ya bani su tun kafin a dora masa ajalinsa yayimin kyautarsu tun kafin suzo duniya ki aminci su rayu qarqashin kulawata_




Jikinta ba qaramin sanyi yayi da kalamansa ba wata kalma daya da D.S yayi mata ranar data haifi twince ta fado mata _ nayi farin ciki da haihuwar nan Sweet duk da inaji a jikina bazan rayu dasu ba amma banajin komai saboda Hameed yana raye_


To dama kalamansa abinda suke nufi kenan ajiyar numfashi tayi cikin sanyin jiki da sallamawa rayuwa farin ciki wata kalmar da yake yawan maimata mata ta dawo mata.



_ Umaimatu ina kishinki bana fatan ko Nazir qanina ya riqe hanunki mutum daya tak nake burin bayan bana numfashi ya zama replacing dina Sweet Hameed nake nufi da ace zan iya dana halatta masa ke ina raye amma bazan iyaba course_ _inasonki sonda idan na rayu babuke zan galabaita sweet zansha wahala fiye da wadda Hameed yakeyi saboda ke dalili ni qaramar zuciya ce dani bantaba shiga tashin hankali makamancin wannan ba kiyi hqr kada ki qullaceshi wlh ba laifinsa bane sharrin qaddara ce yanzun wacce ta zama sanadin rabakun tana ina? Tana asibitin mahaukata idan ba saaba ita da hankali har abada itama ki yafe mata duk da nasani Hameed bazai yafe mata ba saboda ta cutar dashi ita duniya qaramin gurine da zaka zo ka taka rawarka ka kauce wani ya taka Umaimah ki yarda da hakan_ _watarana _muma zamu kauce mu rabu rabuwa ta har abada rabuwar da bazaki sake ganina ba _




Wannan kalamai suna dukan zuciyarta dole tayi biyayya ga kalamansa wannan kamar wasiyya ce adali aqili managarcin mijinta ya bata miqewa tayi a sanyaye ta zaunar da yaran ta nufi bathroom taci kukanta me zuciya ta jima kafin ta daure ta miqe ta fito a zaune ta tarar dashi yana yiwa twince wasa ya dauki madara yana basu yana mitar anbar masa yara da yunwa bata kulashi ba ta fice daga dakin ta shiga kitchen ta zubo abinci ta zauna a dinning din tana juya cokalin Hajiya tana ankare dasu amma batace musu qalaba tanajin lkcn da Hameed din ya shiga dakin taso yi masa mgn amma ta lura duk a zauce yake wani abun ma baisan yanayi ba tarasa wanne irin so yakewa Umaimah kamar wanda tabawa ruwan nono yasha indai yana ganinta baya iya control mind dinsa har tausayinsa takeyi musamman wannan karon data lura kwata² baya gaban Umaimah.




Zama Hajiya tayi a parlourn tana zaune yazo ya wucceta hankalinsa nakan Umaimah yaje ya zauna a kujerar kusa da ita ya ajiye twince suka tafi harkarsu yasa hannunsa ya dago fuskarta yaga yanda hawaye kebin kuncinta gabansa ya fadi sosai ya sanya hanunsa ya fara share mata hawayen yana girgiza mata kai idanunsa nakanta yace  don Allah kiyi hqr wlh ban turo miki text din da nufin

Please Login or Register in order to submit comment