Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka barwa Allah komai tare dasa Ulama'u suci gaba da addu'a akan Allah ya bayyanata yasa tana hanu na gari.




Tafiya tanata miqawa har antafi shekara da batan Umaiman inda a bangarenta da Yayanta abin baacewa komai farko abin nasu yaso ya basu matsala saboda duk yanda takai da jarabarta Hameed yaci uwar babanta daga bayane yake dura mata wasu qwayoyi su kwana suna cinye junansu maimakon rama sai wata qiba da tayi tayi kyau sosai ta murje ta zama babbar mace baqaramin kulawa Hameed yake bataba komai yagani ya siyowa babynsa ya kawo mata komai tace tanaso jikinsa na rawa zaiyi mata.



Zamanta da Sa'ud da Aunty Sarah maqociyarta ya qara mata wayewar kai saboda itama Sarah akwai ilimin sanin da namiji ga Sa'ud da ita kuma kudinta yake qarewa wajen siyan maganin mata wani tabawa Umaimah tasha taje su kwana suna gwatso.
Sosai Hameed yake amfani da hikimomi da dabaru wajan qauracewa samuwar cikin Umaimah amma duk da haka saida Allah ya nuna masa bashi da wayo shekararsu daya da wata biyu ta fara wani zazzabi me zafin gaske cikin dare yaji tana karkarwa da azamarsa ya tashi ya rinqa yimata daburu ya danna mata jikinta da ruwan sanyi sannan ya qara shigar da ita jikinsa daqyar suka iya kaiwa safiya ya dauketa suka nufi asibiti hankalinsa duk a tashe yake suna zuwa aka karbeta aka dubata likitan ya tabbatar masa tanada shigar ciki wata biyu da sati uku.......



Babu kunya Hameed ya daga hanu yana godewa Allah ya shiga dakin da take kwance ya ruqo hanunta yana murzawa cikin nasa yana murmushi yace  babyn Uncle congrats dinmu mun samu qaruwa zamu haifawa Hajiya dan soyayya kuma dole ta goyashi tayi masa rawa jikanta ne naso kaucewa hakan amma Allah bai nufaba duk da haka nayi farin ciki sosai zan kula da kayana harsai ya taka duniya shima
Tunda ya fara mgnr ta zuba masa idanunta da suka qanqance saboda azabar zafin zazzabin da takeji hawaye ne suka biyo kuncinta a sanyaye tace  aa nidai Uncle don Allah kayi hqr a zubar dashi nikam bazan iya haihuwar sheg...." Saurin rufe mata baki yayi yace  kul Umaimah kada ki batamin farin cikina gsky shege shine wanda bashi da galihu wanda akayi cikinsa a titi kuma wanda baasan asalin wanda yake da alhakin yin cikinsa amma ke kinsani cikina ne kuma inason kayana sannan dan asaline dan dangi saboda haka kadaki qara sheganta min da gsky zamu samu matsala babba dake






*UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß*
[1/18, 3:48 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-THREE*





Miqewa tayi tanayi masa wani mugun kallo amma ta kasa ce masa komai sai yanzun ne ta fara nadama da danasanin biyewa zuciyarta da rudin shaidan suka kasance cikin wannan baqar rayuwa ita da Uncle dinta da gaske fah yanzun ba cikin sunnah ne a cikinta ba ko?
Ta tambayi kanta tare da dagowa ta kalleshi suka hada ido idanuntakesi suka fara zubar da hawaye bakinta take motsawa da alamun so take tayi mgn ta amma ta kasa.



Matsawa yayi ya ruqo hanunta ya dagota zai hadata da jikinsa tayi saurin janyewa tayi baya da sauri tana wani irin kuka me ban tausayi ta zube a qasa ta durqushe tana girgiza kai tana kuka me ciwo tana fadin  Astangafurullah wa'atubi ilaik astangafurullah ya Allah" yanda take kukanne yasashi komawa ya tsaya yana kallonta a hankali zuciyarsa tana tariyo masa abubuwa da yawa firgigit yayi kamar wanda aka tsikara ya dafe kansa yace  oh My gud Umaimah don Allah ki daina kukannan banaso akwai damuwa ko shima wannan din so kike ki zubarmin dashi" miqewa tayi jikinta na rawa ta matsa gabansa ta tsugunna tace  munyi kuskure babba Uncle Hameed tabbas muna cikin tabewa da fushin ubangiji waima ya akayi hakan ta faru dama ni Umaimah zan iya zaman zina meyasa muka zabawa rayuwarmu haka meyasa muka kasa yiwa kanmu da rayuwarmu da zuri'armu adalci Abdulhameed wannan wanne irin baqin tambari zamu yiwa zuri'ar Alh Abdulhameed Yauri Shuwa wanne irin mugun tabone Uncle cikin zina a jikina kuma naka Uncle wayyoh nikam na shiga ukuna Uncle dama a waje nayoshi idan har yana cikin qaddarata da nafi samun sauqi fiye da ace nakane...."



Sakin baki yayi yana kallonta da nazarin kalamanta towai me hakan yake nufi?
Sunkuyawa yayi ya dagota yace  fargar jaji mukeyi dagani harke Umaimah tabbas munyi kuskure amma laifin waye tsakanin mu da iyayenmu da suka kasa yi mana uzuri su fahimci kedin mahadina ce nima mahadinki ne nayi nadama da nadamarki Umaimah amma kuma inason cikina dake jikinki inason ki haifemin shi ki rainarmin shi Umaimah kada kicemin aa wannan abune daya zama dole akanki
Yana gama fadin hakan ya zaunar da ita saman gadon ya juya ya fita, ya jima sannan ya dawo shida likitan ya bata magunguna sannan yace zasu iya tafiya gda.



Miqewa tayi tayi gaba yabi bayanta da sauri yasha gabanta ya bude mata mota ta shiga shima ya shiga yaja suka tafi saida ya tsaya yayi mata siye siyan kwalam na masu juna biyu sannan suka wucce gdan tayi shigewarta daki ta fada gado tayita rera kukanta na nadama mara amfani wadda ake kira da ihu bayan hari ko fargar jaji.
Saida ya shiga kitchen ya dafa mata Indomie sannan yayi mata kunun cous-cous saboda ya lura a yan kwanakin nan tanason sa sosai sannan ya nufi dakin nata ya bude ya shiga ba qaramin faduwa gabansa yayi ba ganin yanda tayi flat a gadon taketa gursheqen kuka jiki a sanyaye ya ajiye kayan hanunsa ya nufeta ya zauna a gefen gadon ya janyota jikinsa tare da zubawa fuskarta ido yanajin kukan nata har cikin qofofin gashin jikinsa miqewa tayi zaune tana gyara rigar jikinta yace.



 Da ace zaki hqr ki daina kukannan dakin taimakeni kuma kin taimaki kanki sannan kin taimaki abinda ke cikinki Babyn Uncle nifa banga abin tada hankali a lamarin nan ba tunda ba kanmu aka fara ba kuma bazamu zama qarshe ba balle mu zama abin kwatance ko misali iyakadai ayi surutu na dan lkc ya wucce shikenan ya zama tarihi idan kika sawa kanki damuwa ke abin zai dama ni kinganni babu abinda ya dameni iyaka na barki da hawan jininki kuma dole ki haifemin na dauki abina nayi masa huduba na yanka masa rago kamar kowanne da"



Yana fadin haka ya dauko Indomie ya diba a cokali yakai mata bakinta tayi saurin kaucewa tace  bazanci ba Hameed bazanci ba ai dama nasan haka zakace baka da kaico nida na biyewa so da rudin zuciya har hakan ta faru tsakanin mu nice da kaico amma inaso ka sani kuma nayi maka albishir ni Umaimah bazan haifi shegeba wlh ko ba dade ko bajima saina zubar dashi yabi ruwa kamar yanda akayimin asarar halattatu ni zanyi asarar shegen cikinka da han...."



Wani wawan mari ya dauketa dashi daya sata saurin hadiye furucinta ta dafe gurin a gigice har mararta saida ta amsa ta dago kanta bakinta yana rawa hawaye yana malala a idonta tace  ni ka mara Abdulhameed akan na zagi wannan tsinannan ala qaqai din cikin naka to wlh saina maimata kuma bazan fasa fada ba saina zubar dashi saidai ka kasheni azzalumi kaw..."


Wata damqa yayi mata da tasa idanunta yowa waje ya janyota tare dayin qasa da kansa daidai fuskarta yana wani mugun huci yace  idan kika qara sheganta min da sainayi miki shegen duka" yana fadin haka ya cillata gadon ya bita ya danne ya fara wasa da ita kuka ta sake sakin masa mai gunji amma kota kanta baibi ba yaci gaba da bata wuta duk irin kukan da takeyi masa da magiya bai bar abinda yakeba saida ya bata kashi sosai ya tabbatar da ta karba a jikinta sannan ya dagata ya shiga bathroom ya sakarma kansa ruwa bayan ya fito ya juyo ya dubeta fuskarsa a hade yace.



 Tashi muje nayi miki wanka kizo kici abinci banason ki haifemin da da tamowa" rufe idonta tayi batare data tashin ba ya sake cewa kada ki bari na sake haurowa gadon nan kinsanni kinsan aikina fiye da kowa" miqewa tayi tana jiri bawai don taji mgnrsa ba saidon sanin rashin mutuncin sa idan tayi masa gardama yanzu zai dora daga inda ya tsaya.
Bathroom ta shiga tayi wankan tsarki ta fito yana zaune a saman carpet din dake gaban gadon yana susuta mata kunun da cokali tazo ta giftashi ta ta nufi wadroop din ta bude ta dauki baqar abaya tasa ta nufi qofar ta murda da nufin ficewa tabar masa dakin amma sai tajita a rufe da key.



Juyowa tayi ta dubeshi shima itan yake kallo yana murmushi ya taso ya ruqo hanunta ya mayar da ita gurin da ya tashi ya debi kunun a cokali yakai mata bakinta taqi karba murmushi yayi yace  ok bakiso ko? To bari nasha saina bawa dana ta inda ya shiga yasha" kafin ya rufe bakinsa ta dauki kofin ta fara shan kunun tana hawaye dariya yayi sosai bayan ya gama dariyar ya zuba mata lulu eyes dinsa yana qare mata kallo yanajin wani mugun so da qaunarta yana qara bijiro masa saida ta gama ya ballo magungunan ya bata tasha sannan yace taje ta kwanta.



Bata da zabin daya wucce kwanciyar saboda jikinta da yake mata mugun ciwo miqewa yayi ya bude qofar ya fice daga dakin kai tsaye gdansu ya nufa yana shiga gabansa ya fadi ganin Hajiya da Daddy da Hajiya Kaka a zaune a parlourn sunyi dako² Hajiya sai kaiwa da komowa takeyi tanajin muryarshi ta nufoshi gadan² ta daukeshi da wani gigitaccen mari da saida yasashi durqushewa sama gwiwarsa ya dago kansa a hankali ya kumajin wani marin ta wani bangaren ya sake rintse idonsa tare da budesu akan iyayen nasa da suke tsaye akansa.
Wata shaqa Daddy yayi masa cikin muryar tashin hankali yace  ashe kai mugune ban sani ba Hameed ashe kai bakada tunani baka da lissafi Hameed mu ka mayar abokan wasanka kenan ka mayar damu qananun mutane da bamusan abinda mukeyi ba dama Umaimah tana gurinka ka mayar da ita farkarka harda ciki kake mana wasa da tunani Hameed qanwarka ka mayar dadironka me mukayi maka da zafi haka da zaka saka mana da haka yanzu idan Umaimah yarinya ce ta gudu tabar gda kaima ashe yarone da zaka biye mata ku ware gefe guda ku rinqa aikata fajirci a doron qasa ni dama na dade ina zarginka Hameed saboda babu yanda zaayi a yanda kake ka iya zaman shekara harda watanni babu mace amma ka yaudaremu kuma ka munafurcemu ka cutar damu ka cutar da marainiyar Allah Hameed"..........








*UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß*
[1/18, 8:06 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-FOUR*



Hajiya ce tayi gefe ta zauna a qasa ta dafe kanta tana zubar da hawaye tana maimata kalmar innanillahi wa Innah ilaihir raji'un ta zubawa Hameed din ido mamaki takeyi na labarin da Dr Saleem ya sanar dasu ko a mafarki kuma ko a hasashe zuciyarta bata taba raya mata hakan ba ashe gaske ne baka bada shaida akan dan zamani komai zai iya, da wanine ya bata wannan labarin ba Dr Saleem ba kuma ko shidin dabai nuna musu shaidar bayyane ba ta hoto me motsi wato video da yayima Hameed din da Umaimah lkcn da suke qalubalantar junansu akan cikin ba da bazata taba amincewa Abdulhameed dinta zai aikata haka ba kuma tasani tabbas laifinta ne tunda dagashi har Umaimah sun tabbatar Mata dako an rabasu bazasu rabu ba yanzu gashi garin gyara tayi gagarumar barnar da zataci gaba da yado har qarshen zuri'arsu.



Maganar Kaka ce ta dakatar da ita daga tunanin da takeyi tace  banga laifin Hameed ba laifin Umaimah ne tunda ita mace ce yakamata ace tayi qoqarin kare kanta amma ita da kanta ta gudu daga gdannan saboda haka itace ta fara bashi qofa kuma bisa sahalewa da jagorancin ki Zulaiha da kinbi komai a hankali kamar yanda muka tsara tun farko duk da baa kawo wannan matakin nadama da fargar jajinba



Hawaye ne yakebin kuncin Hajiya ta miqe tana hada hanya ta zari mayafinta ta dubi Hameed tace  katashi ka kaini inda ka boyeta wawa kawai" bata jira abinda wani cikinsu zaice ba ta fita Daddy ne da Hajiya Kaka suka biyota sai Hameed da yake tafe kamar wanda kwai ya fashewa a ciki yana zazzare idonu kamar wanda aka tsayar hisabi>Ø#Ý



Shiga motar yayi gabansa yana faduwa ya tasheta Suma suka shiga yajata a hankali suke tafe babu wanda yake iya cewa da wani qala tsakaninsu kowa da abinda yake ayyanawa a ransa.


Shi Daddy mamaki nema ya cikashi da suka shigo unguwar ko a Ina Hameed din yasan unguwar koshi da yake ubansa jin sunan anguwar yake amma bai taba shigarta ba parking yayi a qofar gdan ya bude ya fita ya bude get din ya dawo ya shiga motar sosai Daddy yake binsa da kallon mamaki wato saboda tsabar bai yarda da kansa ba ko megadi baisa a gdanba suna shiga yayi parking a dan qaramin parking space din da baifi na mota biyu ba budewa sukayi duk suka fito zama yayi a cikin motar bashi da niyar fitowa saida Daddy ya doka masa tsawa ya fito simsim ya bude musu qofar parlourn suka shiga sun jima suna qarewa parlourn manyan hotunansa da Umaimah da sukayi da gani kasan suna cikin shauqin qaunar juna lkcn da sukayi hotunan su Hajiya ta zubamawa ido tana mamakin lamarin juyowa tayi ta watsa masa jajayen idanunta tace.




 Ko babu halin nuna mana inda hamshaqiya mandiyar me wanke qafa da sosan qarfen takene">Ø#Ý>Ø#Ý
Ba Hameed ni kaina da ace naga alamun rahma a gurin Hajiya babu abinda zai hanani darawa amma Ina babu dama sumsum ya wucce ya murda jamlock din qofar ya bude ya shiga suka rufa masa baya tana nade cikin bargo tana sharar baccinta saboda magungunan daya bata kafin ya fita harda na bacci kallon kallo aka shigayi tsakanin Hajiya da Daddy da Kaka shikam gogan zuba mata ido yayi yanda take baccin da gani kasan bana dadi bane na wahala ne saboda shida kansa yasan tsakanin jiya da yau ba qaramin kashi ya bata ba ga zazzabin da take fama dashi.




Yama manta dasu Daddy a gurin ya haye gadon ya yaye blanket din data rufe jikinta dashi daga ita sai harp vest rabin qirjinta duk awaje yake hanunsa ya dora a saman cikinta yana sauke ajiyar zuciya tare da dora daya hanun a tudun boobs dinta da sauri Daddy ya kawar da idonsa tare da qwallah masa kira yayi firgigit ya dago tare da kallon iyayen nasa ya sosa kansa a kunyace yace.




 Oh sorry Daddy tashinta zanyi fah" Hajiya ce tace  dan ubanka haka ake tashin mutum a bacci wato gwada mana zakayi a gabanmu mugani ko zaka sauka a gadon kosan na dagargaza maka kai shashashan banza da baisan kansa ba" miqewa yayi a sanyaye ya koma gefe ta haye gadon ta fara tashin Umaiman shure² ta farayi tana qunquni tana cewa  nifa ka qyaleni banason takura wlh baccinma bazaka bar mutum yayi ba kai kullum baka da aiki sai jarrab....."



Dukan bakinta Hajiya tayi tace  kinci uwarki keda jarabar dan ubanki tashi nice dai da kika gudo kika baro saboda inason qwata miki yancinki shashashar banza" ai suman kwance Umaimah tayi saboda tsabar tsoro da firgici batasan sanda fitsarin da takeji tun dazu ya kwace mata ba don tasan yau kashinsu ya bushe daga ita har Uncle din nata>Ø#Ý>Ø#Ý>Ø#Ý



Finciko Hajiya tayi dan guntun fitsarin da take matsewa ya qarasa zubowa tayi baya luuuuuu zata fadi yayi wani kukan kura ya rungumeta yace  ke kada ki zubarmin da ciki wlh ranki baci zaiy...." Wani lafiyayyen naushi Daddy yayi masa a baki tare da fincike Umaiman daga hanunsa ta fada jikin Daddyn saboda nanne kawai take tunanin sauqi ta lafe a jikinsa ta saki kukan munafurci tana cewa  wlh Daddy bansan ya akayi hakan ta faru ba don Allah kada ku kasheni wlh bazan qaraba zanyi muku biyayya wayyoh Allah mamana wayyoh Abbana...."



Rufe mata baki Daddy yayi ya daka mata tsawa yace  zakiyimin bayani ne dan qaniyarki Hajiya ce ta bude wadroop ta zaro mata hijjab ta cillah mata tasa Daddyn ya figeta zai fita da ita Hameed ya riqeta da sauri yace  Daddy Ina zaka kaita?" Juyowo yayi ya watsa masa daquwa yajata shima ya kuma riqeta sai yanzu da yaga da gaske zaa rabasu sannan yaji zuciyarsa ta fara tafasa yace  amma Daddy kasan akwai shaquwa tsakanin mu ku barmin ita harta haihu don Allah ku barta na kula da dana batasonsa zata iya zubarmin dashi fah" finceke hanun nata Hajiya tayi Daddy yana riqe da ita a parlourn yaga mukullin motar daya kawosu ya dauka ya jefa Umaiman ciki Hajiya tashiga Kaka ce ta fito itama ta shiga yanabinta yana bata hqr akan ta fada musu su barsa da matarsa harsai ta haihu inyaso duk hukuncin da zasuyi sai suyi amma itadinma babu wani sauqi.




Jan motar Daddy yayi a guje da sauri Hameed din yayi baya suka budeshi da qura yana ganin sun fita ya zube a gurin ya saki wani ihu yanata da qura kamar zararre.
Daqyar ya iya tashi ya shiga gdan ya fada saman kujera yana saqawa da kwancewa tabbas akwai buga March tsakaninsa dasu Daddy saboda shidai yasan bazai taba iya rayuwa babu Umaimah ba to waima wanne munafikin ne ya sanarwa su Hajiya Umaiman na gurinsa?........







*UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß*
[1/19, 9:39 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-FIVE*




Sukuwa su Daddy suna zuwa gdan Hajiya ta figi hanunta suka shiga ciki a parlour ta zaunar da ita itama ta zauna ta hada kai da gwiwa itako Umaimah banda kuka babu abinda takeyi haushi da takaici ne yasa Hajiya cewa.
 Tun yanzu kika fara kuka Umaimah me akayi da zakiyi kuka? ai baki fara kukaba sai lkcn da kuka fara girbar abinda kuka shuka sai lkcn da kika haife abinda ke cikinki ya girma ya tambayeki meyasa baki haifeshi da aureba meyasa kika bata masa nasaba lkcn ne zaki kukan da babu mai rarrashin ki lkcn ne zakiyi nadama mara amfani Umaimah..."



Fasali Hajiya taja kana ta dora da cewa  kin bani mamaki Umaimah koda yake babu abin mamaki cikin lamarinku duba da sakacin namune tun farko da ace mun riqeki a gurinmu mun tsaya kaida fata wajen tarbiyyarki da bamu bashi ke tun kina qarama ba da mun nuna miki cewa shidin ba kowa bane kuma duk da yake dan'uwanki amma akwai bambamci tsakaninku ke mace ce shi namiji ne da ace bamu barki kin saba dashi ba irin sabon daya zama matsala yanzu tsakaninku har kuke tunanin bazaku iya rayuwa babu juna ba nasan da bakiyi masa biyayya akan son kansa dason zuciyarsa ba kema da baki biyewa zuciyarki ba kin gudu har yasamu damar kama miki gda ya killaceki kunci gaba da mu'amalar aure bayan dukkanku babu jahili ya sauki kin sauke yasan fiqihu yasan hadisi kema kuma kinsani kunsan komai amma kuka take yau ga ribar soyayya nan a jikinki"



Daddy ne ya amshe da cewa  wai ma ni ya akayi har suka hadu kuma Ina cikin da kika bar gda dashi?" Kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita Daddy ne ya kuma daka mata tsawa yace  ba mgn nake miki bane sai kinji a jikinki?"
Cikin kuka da in...ina ta fara zayyane musu komai...
Mamaki da tsoro gami da al'ajabi ya cika zuqatansu koda wasa basu taba tunanin tun batan Umaiman Hameed ne yayi kidnapping nataba gashi tun ranar da abin ya faru tayi bari aura kuma ya riga ya furta kalmar sakin duk da bai qarasa ba amma ai sakin yasaku tunda saki yana faruwa ne ta hanyar furtawa koda baa qididdige adadi ba shikuma ya riga ya furta na sakeki saki day saboda haka saki ya saku.




Miqewa Daddy yayi ya haura samansa ya kwanta yana tunanin abinda ya dace yayi amma bai hango wata mafita ba.
Itama Hajiya miqewa tayi ta kama hanun Umaimah ta shiga da ita daki gurin Hajiya Kaka tace  kaka kisa ido akan sha'anin yaran nan ni tsoroma suke bani wlh" amshewa Kaka tayi da cewa  suke baki tsoro ko suke bani nikam lamarin Umaimah da Hameed ya girmi tunanina Allah dai ya kiyaye daba yakuma rufa mana asiri wannan abin kunya har ina niko a labarin tatsuniya irin tamu ta mutanen dauri ban tabajin wannan kwamacala ba to kodai suna tunanin da aure tsakaninsu ne?"



Hawaye Hajiya ta dauke tace  ba wannan tunanin bane Kaka dukkansu babu wanda baisan shari'a ba kuma ma wannan ai budaddiyar mas'ala ce ya saketa kafin yakai ga mayar da ita ita kuma tayi bari kinga aure ya warware gaba daya koda a ranar ya farfado yakeson mayar da matarsa sai ya sake biyan sadaki anyi siga an sake daurin aure to Kaka cikinsu waye baisan wannan ba ko wanda baije islamiyyah ba indai yana zuwa masallaci kuma yana zama cikin musulmi zaisan wannan ballesu da daidai gwargwado mun basu ilimi kawai tsagwaron rashin mutunci ne ba wani abu ba.



Tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin ita kuma Umaimah ta zauna a gefen gadon dafe da habarta har yanzu bata daina hawayen nadama da danasanin biyewa rudin zuciyarta takaita ta baro idan ta tuna cikin dake jikinta sai taji wani malolon baqin ciki da takaici ya tokare mata maqoshi.
Mugun haushi da tsanar Hameed takeji a ranta saboda tasani badon Shiba da komai baizo Mata a haka ba da wannan tunanin ta kwanta bawai don tayi bacci ba saidon kwanyarta ta huta amma ta kasa samun sauqin tananan kwance tana juyi wayarta tayi Ring ta dauka ta duba sunan Sa'ud ce mayarwa tayi ta ajiye saboda har Sa'ud din haushinta takeji don tasani da ace batazo ta dauketa daga gdan ba da abubuwan da suka faru duk basu faru ba tanajin wayar tana Ring amma taqi dagawa bayan kamar 2 minutes wani kiran ya shigo tana dubawa taga My Spirit sunan da tayi saved number Hameed da ita kenan.



Kawar dakai tayi tare da danna wayar a silent yayi kira yafi ashirin amma taqi dagawa hakan ba qaramin daga masa hankali yayi ba yinin ranar haka ta qarasa shi a daki kwance ko parlourn taqi fita tunaninta kawai yanda zatayi da cikin jikinta.
Da dare yazo gdan ya jima a parlourn babu kowa kasancewar yasan asabarce yasashi haurawa sama gurin Daddy a zaune ya tarar dasu shida Hajiya suna tattaunawa akan matsalar ya samu guri ya zauna yanata gada zuffa kallonsa Daddy yayi da fuskarsa ta rahma yace.



 Babana ya akayine Allah yasa dai lfy kazo kasamu gaba?" Sosa qeyarsa yayi cikin kunya yace  Daddy din Allah kuyi hqr kuskure ne nayishi abani dama ta qarshe bazan sake ba"
Kallonsa Daddy yayi yana murmushi yace  to yanzu ya kakeso ayi babana idan anyi maka afuwar?" Sake marairaice murya yayi yace  ku bani ita mu zauna harta haihu in yaso sai a mayar da aurenmu wlh babu abinda zai sake shiga tsakaninmu nayi muku wannan alqawarin"



Dagowa Hajiya tayi zatayi mgn Daddy ya daga Mata hannu ya dubi Hameed da kyau yace  yanzu kuma idan nace bazanyi ba kuma mene zai faru?" Dagowa yayi da sauri yace  ka taimakeni Daddy wlh inason cikina kada kuyi sakacin da zata zubarmin dashi Daddy shine na uku fah duk sauran sumbi ruwa shima kada ya salwanta plz nafison basu kulawa da kaina" dakatar dashi Daddy yayi yace  yanzunma Kaine zaka kula da abinka nawane ma albashinka?"



Dago kansa yayi ba tare da tunanin komai ba yace  dubu dari hudu da tamanin" murmushi Daddy yayi yace  kayy Masha Allah Nice salery sai kuma mene yake kawo maka kudi kuma ribar nawa kake samu a wata?" Murmushi yayi yace  ina harkar kiwon kaji da kifi a qallah duk wata ina fitar da kaji guda

Please Login or Register in order to submit comment