Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakai Hameed kuma wlh azeem idan baka daina bibiyar rayuwata ba zan gudu ku nemeni ku rasa kowa ma ya huta




Fitowar Hajiya ne yasata tayi shiru da kukan da takeyi ganin a zaune yayi mugun qonawa Hajiya rai ta nunashi da hannu tace  tashi ka fita daga dakinnan dagowa yayi yace  amma Hajiya ya kamata ku tsaya ku fahimceni waini meyasa kullum ni me laifine bakwa yimin uzuri Hajiya kada idonki ya rufe kema kamar yanda na bloody ya rufe take caccakamin maganganu masu ciwo son ranta kuyimin adalci kafin yanke hukunci naji ni me laifine amma ku tsaya kuyi tunani da hankalina zan saki Umaimah har saki biyu wlh Hajiya ko maqiyina yasan inayiwa bloody son da bazan taba yiwa wata mace ba a duniya bazan iya rabuwa da itaba itace rayuwata Hajiya itace farin cikina




Wani murmushi Hajiya tayi me ciwo itafa ta fara tantamar hankalin dan nata saboda kalaman gaba daya babu hankali a cikinsu dauke yaron tayi daga jikinsa ta kama hanunsa tace  miqe ka tafi gdanka safiya ce yanzu matarka tanacan tana jiranka ka cika mata burinta tayi nasara ta rabaka da matarka me qaunarka domin Allah ga gidannan ku zauna ku kadai" tana fadin haka ta turashi waje ta rufe qofar.




Durqushewa yayi jikin qofar yana kiran sunan Umaimah sai yanzu yaji wasu zafafan hawaye sun zubo masa ya dade a gurin ganin babu wanda zai fito daga dakin yasashi miqewa jiri na dibansa ya fita ya fada motarsa yaci gaba da kukansa yana buga kansa da sitiyarin motar jin abin yake kamar almara wai shine ya saki Umaimah saki har biyu to me tayi masa meye ya hadasu yaushe ma yayi sakin kuma yaushe ya rubutashi kai ina bazai taba yarda ba wannan gonarsa akeson shiga ayi masa barna.




Daqyar ya iyajan motar ya nufi gdan abokinsa Yusuf dake asabar ce yana zuwa ya tarar dashi tsaye tare da megadi mamakine ya cika Yusuf saboda rabonsa da Hameed tun lkcn daya fada masa zai auri Salmah ya fito ya nuna masa bai amince ba so ko waya basayi kamar aikin asiri ya daina kulasa ko wayarsa ya daina dagawa.
Takawa Yusuf yayi har motar ya bude ya shiga yace  yadai mutumin yau amintakar ce ta motsa asirin ya sakeka kenan... hadiye mgnr yayi ganin yanda jikinsa yake bari haqoransa suna haduwa ya damqi hanun Yusuf yace  Yusuf wai su Daddy ne sukace wai nine na saki Umaimah da hanuna jiya da daddare har saki biyu yanzu shikanan bloodyna ta haramta gareni...."




A tsorace Yusuf ya dago yace  kamar ya wai akwai wanda ya isa yace ka saki matarka idan baka saketa bane?" Cikin fitar hayyaci yana qara dafe qahon zuciyarsa yace  ru...rubutu nane a jikin takardar amma wlh tallahi bansan yaushe na rubuta ba Yusuf nasani kai zaka gasqatani wlh inason matata bazan taba iya rubuta mata saki har biyu ba yama zaayi na saki Umaimah har saki biyu bayan nasan rabuwa ce ta qarsh...."




Bai iya qarasa mgnr ba saboda numfashinsa da ya fara sarqewa ya fara kokawa dashi tare da danna qirjinsa da sauri yace  kaini gda Yusuf maxa kaini gdana na mutu a dakin Umaimah Yusuf mutuwa zanyi...."



Yana fadin haka ya fara kakarin amai kafin kace meye wannan ya balle murfin motar ya fita ya durqushe a qasa ya fara sheqa aman jini tashin hankalin da Yusuf ya shiga ba kadan bane ya fito ya rirriqeshi yana jijjigashi yana cewa  dama saida na fada maka kada ka auri Salma bakai takeso ba farin cikinka takeson rabaka dashi kaqi ji yanzu ga irinta nan ta rabaka da matar da kakeso kuma Kai dama ba cikakkiyar lafiya ba idan ka mutu ai kowa ma ya huta saki kuma ya saku tunda harka ambata sunan Umaimah a takardar kuma ka dawo hayyacinka ka gani da idanunka Hameed da ace bayan kayi sakin baka dawo hayyacinka ba har kowa ya fahimci baa cikin hayyacinka kayi sakin ba da kana da damar dawo da matarka saboda babu alqalami akanka lkcn da baka cikin hayyacinka amma dawowarka cikin hayyacinka da wuri da kuma karbar takardar ka duba shine ya tabbatar da sakin Hameed Umaimah ta saku kuma ta haramta gareka harsai taje ta auri wani mijin yayi mu'amala ta aure da ita tukunna ta halatta gareka...."



Duk da azabar da yakeji a qirjinsa hakan bai hanashi daga masa hanu cikin azababban kishi ba yace  wlh aa ne babu namijin dazai shiga jikin Umaimah saidai dukkanmu mu mutu babu aure ka kaini gdana nace kada na mutu anan....." Yana mgnr yana qara qanqame qirjinsa kamashi yayi ya taimaka masa suka shiga motar yaja suka fita ya juyo yace  amma da asibiti muka fara zuwa" daga masa hanu yayi yace  bazani ba gda nakeson zuwa nafiso na mutu na huta meye amfanin rayuwata babu Umaimah" bai sake masa mgn ba saboda yasan tunda ya musa to bazaiyi ba horn yayi a qofar gdan suka shiga ya dauki biro da takarda ya rubuta rubutu kamar haka.




 _Qaddarar ki rabani da farin cikina ya hadani da baqar ashana irinki wlh baki isa kici gaba da zama dani ba ni Hameed na saki matsiyaciyar mace irinki Salma saki uku _



Yana gamawa ya bude motar ya fita da sauri a duqe yake tafiyar har ya shiga cikin bangaren Salma ya danna kai ya shiga qanwarta ya gani a parlourn baiko kula gaisuwar da takeyi masa ba ya shige dakinsa ya zare wata qatuwar belt a jikin wandonsa ya bude qofar ya nufi dakinta ya tarar da ita kwance ta baje gindi tanashan iska ya kawar dakansa tare da sanyawa dakin key ya fusgota daga gadon ya fara nada mata na jaki kamar mahaukaci tun tana ihu da dasasshiyar muryarta da kukan neman daukin daran jiya ya qarar da ita harta daina motsi bai daina jibgarta ba yayi mata fata² da jiki sannan ya cilla mata takardar yana haqi yace aje aci gaba da zawarci Hameed yafi qarfin ki la'anallahu




Bude qofar yayi yana budewa yaga uwarta a parlourn ko kulata baiyi ba ya fice jiri na dibansa ya nufi inda Yusuf yake jiransa a mota amma kafin ya qarasa ya yanke jiki ya fadi da sauri Yusuf da megadi suka nufoshi suka rufar masa Yusuf na danna masa qirjinsa yana kiran sunansa wayarsa ya zaro a kidime ya kira layin Daddy bugu daya aka daga yace  Daddy Hameed ne bashi da lfy muna gdanshi ka Kira likita akwai matsala"
Yusuf yana aje wayar suka kinkimeshi suka nufi bangaren Umaimah dashi suka kwantar dashi a parlour sai gumi yake hadawa zuciyarsa na bugawa da qarfi baafi minti ashirin ba Daddy ya shigo shida Dr Saleem wata Allah ya fara yimasa sannan suka fita dashi zuwa asibiti suna zuwa aka shiga dashi aka fara bashi taimakon gaggawa wannan karon bai shiga commer ba amma baisan inda kansa yakeba.......











*UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß*
[1/31, 2:24 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *GU*



























Gumu tayi gumu hankalin wannan family ya tashi wannan karon lamarin yafi qarfin fushi saidai addu'a saboda Hameed yana asibiti Umaimah ma tana asibiti har satin suna ya zagayo duk inda taso cirewa kanta damuwa da soyayya gami da tausayin halin da Abdulhameed yake ciki ta kasa saboda a jininta yake ji takeyi kamar ta cire ciwon ta mayar jikinta duk da a cikin qahon zuciyarta tanajin ciwon cin mutuncin da yayi Mata a daren da tafi buqatar taimakonsa da kusancinsa a daren ya yanke shawarar datse igiyoyin aurensu saida tayi sati biyu tana jinyar rabuwa da masoyinta a asibiti kadan ya rage itama zuciyar tata ta harbu amma jininta in yana kaiwa dubu ma to ya kai ga kuka babu dare babu rana tazama kamar zautacciya duk wata kalmar bakinta bloody ko ya jiki kace mata to amsarta bloody.




Hakan ba qaramin daga mawa su Hajiya hankali yayi ba kakace taga abin na Umaimah ya zama kamar tabuwar qwalwa hakan yasa tasa aka sauke mata qur'ani sannan akayo mata rubutun dangana aka rinqa bata tanasha satinta uku da haihuwa suka koma makaranta sabuwar motar da Hameed ya siya mata wacce yace itace gift dinta ta haihuwar Shuraif ita Daddy ya bata take zuwa makaranta da ita kamar yanda ya kafa mata doka har yanzu haka take bata fasa ba niqaf ne kawai bata sawa saboda dama a dole take sanya shi saboda farin cikinsa.




Saida yayi sati biyar a asibitin yana jinya sannan ya fara samun kansa shima da sunanta ya tashi a bakinsa Hajiya tana tausayawa dan nata tasan kafiyarsa shima da rubutun zatasa ayi masa saboda tasan akwai badaqala a gaba.
Haka suka koma gda dashi duk yawan gdajensa amma yaqi komawa ko daya daga ciki shima dakinsa tunna samartaka yasa Daddy dole saida ya gyara masa ya koma cikinsa sai lkcn ne Hajiya ta samu damar zuwa ta debowa Umaimah kayanta tsaf shikuma yasa gdan a kasuwa saboda ko gdan bazai qara zuwa ba balle ya tuna da baqar rayuwa da baqar ranar data riskesa a gdan ranar dabai taba tunanin zuwanta ba a rayuwar aurensa da Bloody dinsa.




Bincike yakeyi sosai akan sakin da ake iqirarin yayiwa Umaimah malamai sun bashi fatawa sosai inda kaso mafi rinjaye suka tafi akan ta saku saboda mgnrsu ta cewa lkcn da aka saukar da suratul dalaq manzon Allah ya sauqaqa sosai a cikin lamarina na saki harma yace idan mutum ya saki iyalinsa saki uku a kalma daya to zaa iya barinsa a saki daya idan yayi mata saki daya a baya kuma yazo yayi mata biyu to zaa iya barin biyun nan a daya a hada da wancan na farko ya zama biyu sannan idan mutum ya saki matarsa a cikin maye ko gushewar tunani to wannan sakin babushi.




So inda aka samu matsalar bayan wafatin ma'aiki (s a.w) sai abubuwa sukayi tsamari mutane suka rinqa wasa da aure sai mutum ya saki matarsa saki uku kuma yaje ya dawo da ita ko mutum yaje yasha giya ko wani abu me gusar da hankali yazo ya nadawa matarsa duka ya saketa idan ya dawo hayyacinsa ya koma ya dawo da ita wannan abu ya batawa Sayyadina Umar (R.A) rai zamanin khalifancinsa ya kira majalissar sahabbai aka sakewa dokar qwasqwarima saboda sauyawar zamani aka buga mata guduma akan cewa idan har mutum ya saki matarsa saki uku a kalma daya to ta saku sannan ko cikin gushewar tunani mutum yayi saki to matarsa ta saku sannan idan kayiwa mace saki daya sannan kazo zaka sake sakinta bayan kasan da daya a baya kuma ka furta mata biyu to ya zama uku saboda haka ta haramta gareka harsai tayi aure da tsarkakkakiyar niyyah ba niyar kisan wutaba kuma harsai mijin yayi mu'amalar aure da ita sannan tasu ta hadosu suka rabo to a lkcn ne ta halatta gareka sai ku sake daura aure fresh me igiya uku.




Wannan kalma ta sai Umaimah ta auri wani har ya kwanta da ita sannan zata halatta gareshi tana mugun dukan zuciyarsa yakanji dama ya mutu ya huta da ganin wannan baqar rana dalilin yasashi dawowa gdan dalilin ya qudurce a ransa bazaiyi aure ba itama bazatayi ba saidai su qare rayuwarsu a haka.
Abu daya da yake cin zuciyarsa yanda Umaiman tayi watsi da duk wani abu daya shafeshi so tari idan bashine yayi mata mgn a gdan ba itadai bai isa ta daga kai ta kalleshi ba yana yawan kiran wayarta amma bata dagawa har layi ya canza musamman saboda ita amma daya kirata tana dagawa taji muryarsa tace  hello bloody ya akayi Allah yasa dai lfy?"




Ajiyar zuciya yaja yace  ki taimaka ki fito come pound din gdannan inason ganinki don Allah" murmushi kawai tayi ta kashe wayarta bata fito ba kuma bata sake daga wayar tasa ba ransa yayi matuqar baci amma bashi da yanda zaiyi saboda baya iya fushi da lamarinta wani azabbaben so yakeyi mata wanda yake neman turashi lahira bai shirya ba haka lkc yayita tafiya tafi² har watanni takwas suka shude kullum cikin dagewa a karatunta take inda shi kuma Hameed ya mayar da azumin nafila abokinsa saboda lalurarsa tafi qarfin yace zai rinqayin na litinin da alhamis Hajiya tanajin dadin yanda Umaiman take tsarewa Hameed gida saboda tasan yanda yake rawar qafa akan duk abinda ya shafeta idan ta bashi fuska taasa zasu tafka ta lura basu zama inuwa daya daya shigo parlourn ita kuma zata tashi tabarshi da yayansa hudu Nihal Maliha Shurafah da Shuraif Maliha itace me wayo tunda a qallah yanzu ta doshi shekara takwas itace take cewa uban nasu  Uncle naga Aunty tana fushi dakai kuma kun dawo gdannan dukkanku kuma jiya naga wani yazo gurin Aunty ta fita suna hira har suna dariya" tashin hankali wata uwar zabura da yayi ya fara qwalawa Hajiya kira Hajiya ta fito daga kitchen tana cewa  waikai wanne irin mutum ne kaine diba nan duk yayanka ne amma kaqi hankali ubanme zaka bani kake dokamin kira haka?"




Duban Hajiya yayi da idonsa da suka canza kala saboda bala'in yace  wato Hajiya yarinyar nan har kin barta ta fara kawo mana qartin banza gdannan ko to wlh bazai yuwu ba karyata zanyi na balla banza kuma naci uban duk wanda ya qara zuwa gdannan da sunan yazo gurinta haba Hajiya wannan ai cin fuska ne da wulaqanci ansan dai ina gdannan koma meke faruwa zanji baba megadi yasha fadamin yaga wani ya tuqota ya kawota gda ko yacemin yaga wani yazo gurinta to nida kashedi ne nayi muku wlh Allah hauka zanyi a gdannan ga duk wanda ya qara zuwa yayimin sallama da mata shima megadin bari naje wlh ya qara barin wani dan iskan ya shigo gdannan a bakin aikin sa



Yana gama fadamin haka ya fice fuuuu kamar zai kifa riqe haba Hajiya tayi tace  wata sabuwa inji dan caca to uwarka zatayi maka a gdan da zakace baza azo gurinta ba zakuwa kaci kan uwarka wlh Hameed dani kake zance kama godewa Allah Umaimah najin kunyarka ni bantaba ganin yarinya me yakanar Umaimah ba ko baqo tayi da zarar taga yamma tayi zata sallameshi idan nace meyasa tace babu komai bayan nasan saboda Kaine"
Yana fita kuwa yayi katari Dr Sulaiman ya kawota daga mkrnta malaminsu ne tunda ya qyalla yaganta ya dauki so da kulawar duniya ya dora mata da farko Shuraif yakeja a jikinsa saidaga baya daya bincika yaji sun rabu da mijinta sannan ya fara fito mata da ainihin buqatarsa gareta da farko taqi sai daga baya Saudat ta rinqa tausarta tana fada mata shima kyakkyawa ne gashi fari gashi da gani babu tambaya naira ta zauna masa to daqyar dai ya samu ta saki jiki dashi suka fara gudanar da soyayyarsu amma qasan zuciyarta danqare dason dan'uwanta wanda bazata iya gogeshi a mind dinta ba don tasha kiran Dr Sulaiman da Hameed saidai yayi murmushi kawai yace  sweet Allah yasa kisoni koda rabin son da kike yiwa Hameed ne sweet wlh inasonki fiye da tunaninki na fada miki bantaba soyayya ba saboda tsoron mata nakeji sai a kanki"



To yauma zancen da yake mata kenan tayi dariya ta lakace masa hanci tace  sai kuma ka fara da bazawara me yara biyu.... dora hanunsa yayi a saman lips dinta ya kashe mata ido yace  banason ji idan yayanki goma inasonki kuma zan rayu dake zan baki soyayya madara kuma nasani nima zaki soni irin son da kikeyiwa abu Shurafah koma fiy...." Aslm alaikum sukaji anyi musu sallama gabanta yayi mugun faduwa da sauri Sulaiman ya dubeshi yayi murmushi tare da shafa sumarsa ta fullanin asali yace  amin wslm" ya miqa masa hanu amma sai ya noqe ya kalleta da jajayen idanunsa ka cafketa da qarfi yace  dama abinda kikeyi a makarantar kenan idan kinje irin wadannan yan iskan kike kulawa to karatun ma kin daina" yana fadin haka ya figeta ya cillata parlour ya juyo shidai Sulaiman yana tsaye cike da mamaki  dama wannan shine yayannata da take cewa dashi tanajin tsoron yazo gda kada yagansa?" Ya tambayi kansa kafin ya samo amsa yaji muryarsa yana cewa  kada ka qara biyomin qanwa gda wlh zan daureka harsai igiya tayi rara" wuccewa yayi Sulaiman yayi saurin binsa yace  kayi hqr Yaya wlh bada wasa nake ba auran Umaimah zanyi....









*UMMUH HAIRAN CE...*
'<Øûß
[1/31, 5:48 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *GU*






























Wani abune yaji ya caki zuciyarsa ya juyo da sauri yace  aure kuma wa zaka aura habadai wlh tun lkc be qure maka ba ka kama gabanka Umaimah ba matarka bace nayi mata miji" tsayawa Sulaiman yayi sororo har Hameed ya shige parlourn yana zuwa ya fara dukan dakin na Umaimah yana cewa  aure fah yace Umaimah aure? Wlh qarya yakeyi ya aureki" Daddy dake zaune ya miqe ya haye sama.
Ita kuwa tanajinsa taqi budewa muryar Hajiya taji tanayi masa mgnr ya juya ya fara sababi yana cewa ai duk ke kika daure mata gindin tacimin mutunci harni wani zai tara yacemin wai auren matata zaiyi wlh bazai yuwu ba kasheni kukeso kuyi" Hajiya ce ta haushi da bala'in da yafi nasa dole yayi qus sai zafin zuciya da sharar hawaye da yakeyi.




Tana zaune a dakin wayarta tayi qara tana dagawa taga Dr sunan da tayi saved din number Sulaiman da ita ta daga tace  ina fatan ranka bai baci da abinda bloody yayi maka ba" gabansa ne ya fadi yace  bloody kuma wifey Hameed fah kenan?"
Ajiyar zuciya tayi tace  hakane shine mijina na farko shine Abu Shurafah Dr qaddara ce ta rabani dashi nasani yana Sona kuma yana kishina so wannan dalilin yasa nake boyeka gareshi saboda nasani bloody baya da juriya akan duk abinda ya shafeni nasan baqin kishinsa kuma nasan matsalarsa yanada matsalar heart attack shiyasa banason abinda zai taba lfyrsa ko banza yayana ne shine ya riqeni tun bayan mutuwar iyayena kuma uban yayana ne....




Numfashi yaja me qarfi yace  ya isa Umaimah pls ya isa haka don Allah ki gabatar dani a gdanku wlh da gaske nakeyi inason yin aure nagaji da kadaici sweet inason nima naga yayana abokaina daga me yaya biyu sai me uku nima yakamata ace yanzu inada iyalina wlh ko bakya sona zan hqr na rayu dake sweet please murmushi tayi tace  to yanzu ya kakeso ayi Dr? numfashi ya sauke yace  ki bani dama na shigo gdanku na gabatar da kaina iyayena suzo ayi mgnr aurenmu Allah ni idan son samuna ayi bikinmu da wuri saboda a matse nake sosai inason naji abinda akeji"




Ta bude baki zatayi mgn taji Hajiya na cewa  Baby kizo Daddynku yana kiranki" amsawa tayi da to ta miqe tace  afwan D.S zanje Daddy yana kirana" amsawa yayi da  babu matsala amma don Allah ki duba buqatata Ummuh Shurafah" ajiye wayar tayi ta dauki mayafinta ta yafa ta fito saida gabanta ya fadi ganinsa kwance a parlourn ta raba ta gefensa zata wucce ya riqo hanunta ta juyo da sauri ta zuba idonta cikin nasa ya miqe zaune ko riga babu a jikinsa ya janyota da qarfi ta fada jikinsa ya matseta a qirjinsa yana goga mata gashin qirjinsa yace  kasheni kikeson kiyi ko Umaimah saboda kinga inasonki shine har kika dauko wani banza kika kawosh..." Daga masa hanu tayi ta janye jikinta daga nasa ta hade rai sosai tace  banaso kada ka qara zagarmin mijin da zan aura Hameed duk yanda nake mutunta ka da baka haqqinka a matsayinka na yayana hakan baiyi maka ba saika shiga rayuwata to gaskiya banas.... bai barta ta ida fadi ba ya dora lips dinsa saman nata ya riqe qugunta sosai yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya qoqarin qwacewa take yaqi bata dama neman zura hanunsa yakeyi a rigarta ta qanqame jikinta ta saki kuka daidai lkcn Hajiya da Daddy suka sauko daga saman turus suka tsaya Hajiya tayi saurin rintse idonta ganin yanda suke kokawa bilhaqqi yana neman balle bottle din rigarta Daddy ne ya daka masa wata uwar tsawa hakanne yasashi dakatawa da abin da yake shirin aikatawa ya hada kansa da kujerar yana mayar da numfashi ita kuma ta miqe da gudu tana kuka ta qanqame Hajiya wani takaici ya cika zuciyar Hajiya tace.




 Kin fara biye masa ko to wlh baku isa ku cusa mana baqin cikin da kuka qunsa mana a baya ba saboda haka Daddy yau dai ka ganshi da idonka wannan shaidanin yaron ko Umaimah bata bashi hadin kai ba ana kwana ana tashi saiya yaudareta balle itama qwaryar sama ce ke dukan ta qasa haline yazo daya harijan banza da wofi to wlh ki fito da miji kiyi aure duk kwartancinsa ai baya biki gdan mijinki ba ko kuka takeyi sosai tace  wlh Hajiya ba gurinsa nazo ba Kiran da kikace Daddy yanayi min shine ya fito dani shi kuma ya tsayar dani Daddy ne ya kamo hanunta yace  waye yazo gurinki dazu?"  malami nane Daddy  meye ya kawoshi ance ba zuwansa na farko kenan ba ko?" Dagakai tayi tace  eh zuwansa na uku kenan wai aurena yakeson yi" murmushi yayi yace  alhmdllh anzo gurin to ke ya kika gani kina son sa?"



Kallon Hameed tayi daya dago kansa da sauri ya zuba idonsa akanta yanason yaji me zatace sake maimaita tambayar Daddy yayi yana kallon Hameed din cikin in...ina tace  aa.. eh Daddy" murmushi yayi yace  amsa daya nakeso ki bani eh ko aa kawar da kanta tayi da sauri tace  eh Daddy tana fadin haka ta kwasa da gudu ta fada dakinta shima miqewa yayi da sauri yace  haba Daddy meye hakan wanne irin tanasonshi yanzu aura masa ita zakayi Daddy kada kuyimin haka ku bakwa kishina ne wlh duk ranar da kuka daurawa Umaimah aure da wani nama mutu na gama na kwanta da ita wani ya kwanta da ita..."



Bige masa baki Hajiya tayi tace  to ai matsalar tace tanasonshi saboda haka ka shafawa kanka lfy ka nemi mata ka aura ka huta da kwana kai daya kana fama da azumi kullum" Daddy ne yace  idan kin shiga kice da ita nace ta turomin shi gobe inason ganinsa" amsawa tayi da  karkaji komai Daddy Sulaiman mutumin kirki ne kullum yazo gurinta saiya aikomin da gaisuwa yanzu Umaimah zatayi aure me yanci" maganganun iyayen nasa mugun caccakar zuciyarsa sukeyi yaja qafa daqyar ya shige dakinsa ya fada saman gadon zuciyarsa na tafasa ya miqe da sauri ya dauki magungunansa yasha ya koma ya dauki wayarsa ya kira number Umaimah amma sai yaji user busy ya sake kira haka a qarshe dole ya hqr ya qyaleta.





A ranar da Daddy yace yanason ganin Sulaiman washe gari yazo suka zauna da Daddy sukayi mgn bai fada Mata yanda sukayi ba washegari Hajiya ta aiketa gdan Aunty Zarah a ranar magabatan Sulaiman sukazo gdansu suka kawo kudin aurenta dubu dari biyu da hamsin aka tsayar da lkcn biki wata daya masu zuwa washegari dake juma'a Hajiya ta cire Shuraif daga nono itadai batayi mgn ba kuma bata tambaya ba sai bayan kwana biyu Sulaiman yake tsegumta mata cewa an kawo kudin aurensu har anci kwanaki uku.
Batayi wani farin ciki ba sukayi sallama ta ajiye wayar hakanan Hajiya ta rinqa gyarata ta kowanne bangare gyaran jiki gyaran sama da qasa babu inda Hajiya bata yiwa gyara irin nasu na shuwa ba.



Shi kuwa Hameed tun ranar da aka kawo kudin auren Umaimah yake wani mugun zazzabi da ciwon qirji fushi yakeyi da Daddy sosai musamman da Daddy yace shine zai karbi waliccin auren Umaimah......







*UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß*
[2/1, 8:18 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'<Øûß: *_GU_*















Haka kwanaki sukayita tafiya rayuwa taqiwa masoyan dadi duk yanda Umaimah takeso ta watsar da lamarin Hameed ta kasa jinsa takeyi a cikin jininta ciwon da yakeyi yafi komai daga mata hankali musamman a yan kwanakin nan da abin nasa yaci tura ranar daya rage saura sati daya bikin Umaimah dangin Sulaiman suka kawo lefenta ya zuba mata kaya sosai babu harkar

Please Login or Register in order to submit comment