Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubu takwas a kowacce kaza daya zan samu ribar dari uku da hamsin da biyar kaga kenan inada million biyu da dubu dari takwas da arba'in sannan ina fitar da qwai guda million daya da rabi shikuma kifi duk wata ina fitar da conterner daya duk conterner ana samun ribar million uku da dubu dari bakwai da ashirin"



Murmushi Daddy ya fadada yace  kayy alhmdllh amma dai duk wannan ribace babu uwa a cikinta ko?" Daga kai yayi da sauri cikin qosawa da mgnr yace  kafin nayi lissafin riba saina fitar da uwa tukunna" dariya sosai Daddy yayi yace  kana samun million bakwai da kusan rabi a duk watan duniya kenan ko? Kayy naji dadi sosai" dakatar da dariyar yayi yace  am dubeni da kyau babana daga wannan watan inaso dole bisa umarnina idan ka hada kan kudadenka kazo ka kawomin million uku da dubu dari bakwai da hamsin wannan shine kason da zakake warewa na kula da lfyr Umaimah da cikin jikinta harsai ta haihu sannan a sake sabon lissafi tashi maza ka tafi gda dare yayi"







*UMMUH HAIRAN CE...
'<*
[1/20, 9:30 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'<: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-SIX*



Kallon Daddy yake da tsananin mamaki yace  amma Dad.... katseshi yayi da cewa zaka samin ciwon kai  ka tashi ka tafi gdanka nace dare yayi" yana fada masa haka ya shige dakinsa ya kullo itakam Hajiya dama ta dade da tashi a gurin ya jima yana saqawa da warwarewa kafin ya miqe a salube ya sauko daga upstairs din ya nufi dakin Umaiman ya murda ya shiga.



Kaka ya tarar a tsaye tana ninke kayanta kallonsa tayi da sauri tace  Lfy Umbamban meye ya kawokada darenan?"



Zubewa yayi a qasa ya ruqo hanunta idonsa na zubar da hawaye yace  kiyiwa girman Allah Kaka ki bani aron Baby inason yin mgn da ita.... daquwa ta watsa masa tace  qaniyarka umbamban ubanme zaka fada Mata wanda baka fads mata ba a tsayin shekara daya da kukayi kuna sheqe ayarku ta banason shirme da sakarci waima kay anya qlau kake kuwa?"




Miqewa yayi ya hau gadon ya birkito Umaiman dake bacci ya dora bakinsa saman nata tare da dora hanunsa daya a cikinta yanayi mata wata irin tafiyar tsutsa wadda yasan duk nauyin baccin da dakeyi idan yayi Mata saita tashi.



Miqa tayi ta banqaro masa boobs dinta yaja ajiyar zuciya tare da sanya hanunsa da sauri ya cafka yace  ohhhhh! Baby dadi..."
Bude idonta tayi da sauri ta sauke su cikin nasa lumshe idonsa yayi yana yamutsa boobs dinta, a matuqar zafafe ta tureshi ta miqe yayi saurin miqewa yabita Allah ya taimaketa qofar a bude take ta kuwa kwasa da gudu bayanta yabi yana qwala mata Kira kicibis din da sukayi da Hajiya ne ya sashi yin baya da sauri yana sosa qeya a kunyace yace  am... Hajiya Ina... Inason mgn da it...ita Baby... Kallonsa tayi tsaf tayi baya saboda ita kanta Hameed tsoro yake bata ganin yanda saitin uhum hum dinsa taga yanda take miqewa da sauri ta fuzgi hanun Umaiman ta cillata dakinta itama ta shiga ta datse qofar da key.



Shafa kansa yayi cikin tsananin feeling da jarabarsa tasashi tsokanowa kansa ya koma ya zauna a kujera yana mayar da numfashi.
Yafi 30 minutes a zaune a gurin kafin ya miqe ya fita ya shiga motarsa da Daddy ya basa key din ya tafi gda.




Yana zuwa ya fada saman gadon yana sauke numfashi tare da janyo pillow ya rungume qam a jikinsa kamar zai shigar dashi jikinsa zuciyarsa nayi masa wani tuquqi yanzun ta tuni Babynsa ce a rungume a qirjinsa amma su Daddy sun kasa fahimtarsa.




Hakanan ya kwana juyi ita kanta feeling ya yarda kwanciyar hankali ke kawota saboda gabadaya tunaninsa ya karkata yanda zai samu Babynsa ta dawo gareshi amma bai hango wata hanya ba.



Shi ji yakema da ace Daddy cewa yayi ya bashi duk abinda ya mallaka shikuma ya barshi da Babynsa da yafi masa sauqi fiye da wannan hukuncin rabasun daya dauka.
Daqyar ya it's tashi yayi sallah ya shirya ya nufi gdannasu babban tashin hankalinsa yanda Umaimah taqi daga wayarsa ko kadan qarshema yajita a kashe.



Yana zuwa gdan sama ya hau gurin Daddy suka gaisa babu wata alama ta bacin rai a tattare da Daddy itama Hajiyan yaga sauyi a fuskarta ba kamar jiya ba hakama Kaka amma gwanar tasa ko kallon tsiya bai samu a gurinta ba balle yasa ran samun na arziki duk hankalinsa yana kanta so yake ta dago idonta amma taqi har qafa ya rinqa turawa qasan table din yana zungurin qafarta amma ko gezau batayi ba qarshema miqewa tayi ta nufi dakinta zata shiga har takai bakin qofar yace.



 Am Baby ga motarki tazo jiya kije ki gani idan tayi miki I batayi ba sai a kawo miki wata" tana gama sauraronsa ta shige dakin ta datse qofar ta fada gadon tana sauke ajiyar zuciya quru kawai tayi ta shareshi saboda famfon da Hajiya ta kwana tanayi Mata akan halayyar da namiji ita kuwa ta hau ta zauna daram.




Haka lkc yayita tafiya kullum da sabuwar rigimar da Hameed za bullo da ita duk yanda yake tunanin samun sauqi a gurin Umaimah abin ya gagara kwata bata sakar masa fuska kayy yanzun takai ma ko a parlourn bata zama kuma kullum qofarta a garqame yabi takan qawarta Sa'ud amma abin yaci tura saboda ita kanta Sa'ud din yanzu Umaimah bata daga wayarta sai taga dama.
Tafi cikinta kullum qara girma yakeyi gashi har ya shiga wata na shidda ya fara fitowa sosai Daddy da Hajiya sun kasa sun tsare sun hanata fita ko qofar gda saboda sun lura batason cikin idan ta samu dama zata iya barar dashi.



Sadiya zama ya miqa a gda tunda suka rabu da Hameed bai qara waiwayarta ba gashi yaqi bata damar ganin yayanta ko sau daya suna gurin Hajiya Umaimah ke kula dasu kamar ita ta haifesu kullum basu da aiki sai shafa dan qaramin cikinta daya fara turawa suna cewa  aunty Uncle yace kin kusa ki haifa mana qani mune zamu rinqa rainonshi muna goyashi muna tafiya mkrnta dashi" itadai saidai tayi yaqe wanda akace yafi kuka ciwo saboda Allah ya sani tana cike da nadama da danasanin abubuwan da shaidan yasasu aikatawa a baya qashi tunda cikin ya shiga wata na bakwai take fama da rashin lfy ciwon ciki da ciwon mara sunje asibiti da Hajiya aka tabbatar musu da kwanciyar yarinyar ne ba daidai ba saboda haka tana buqatar kulawa sosai kallon Dr Saleem tayi tace  to amma Dr ya lfyr abinda ke cikinta?"



Murmushi yayi yace  lfyr baby qlau Hajiya amma dai a qara kulawa" da wannan kalamin suka dawo gda Hajiya tanajin so da qaunar cikin jikin Umaimah wanda tasani bata tabajin haka akan yayan Sadiya ba kodan Umaimah jininta ce oho.



Ita kuwa Umaimah a ranta ji takeyi dama ace cikin ya lalace idan taji motsin cikin ji takeyi kamar ta bigeshi daga jikinta haushi da tsanar Hameed na nunkuwa a zuciyarta saboda badan shiba da rayuwarta bata shiga wannan gararin ba.



A kuma wannan dan taqin ne Sadiya tayi aure saboda ta bibiyi Hameed yana wulaqanta ta harta gaji ta hqr ta saduda ta auri wani abokin aikinta me Mata biyu saboda takurawar da babanta yayi Mata akan cewa saidai tabar masa gda bazai iya zama da ita suna hada kafada da matansa ba kasancewar babanta matansa uku.
Hakanan ta auri Alh Salisu badon tanasonsa ba saidon gudun korar karen da babansu yakewa duk wata yarsa bazawara da taqi aure yazo kanta musamman ita da kowa yasan ita ta kashewa kanta aure da masifa da zafin kishinta da kuma qin karbar qaddara ga uwa uba rashin daukan miji a bakin komai.



*************************



Tun farkon dawowar Umaimah gda Hajiya tayima Daddy mgn akan cigaba da karatunta to lkcn semester tayi nisa saboda haka ya biya mata Jamb ta zana ya Allah ya taimaketa ta samu abinda ake buqata ta zauna jiran lkcn da zaa koma hutu saboda komai na mkrntar an gama mata Skyline University ce Daddy ya biya mata.



Tun cikinta nada wata bakwai Hajiya tayima Hameed mgnr siyayyar kayan haihuwa yace Mata shi ya gama siyan komai da ake buqata Aunty Zarah zata kawo.
A cikin satin Aunty Zarah ta kawo kayan daya gigita tunanin kowa Kaka kam sallallami ta hau yi tana cewa  wannan yaro wanne irin mahaukaci ne ina zaakai kayannan haka saikace wanda zaa haifama yaya goma



A haka kwanaki suka rinqa turawa ranar wata laraba da yamma Umaimah tana kitchen ita da Hajiya da titsetsan cikinta a gaba suna girki taji bayanta ya bada wata qara qass tare da riqewa tayi qasa da sauri tana dafe cikinta da bayanta tana fadin  way...yohhh uwata wayyoh ub...ana wayyoh Hajiya bay...ana cikina shikenan mutuwa tazo Hajiya ki yafeni>#......


*UMMUH HAIRAN CE...
'<*
[1/20, 3:00 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'<: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-SEVEN*




Kamota Hajiya tayi da sauri na hadata da jikinta tace  subhanallahi haihuwar tazo Umah bari mu tafi Asibiti" riqota tayi a jikinta suka fito parlourn inda Kaka take zaune tana duba jarida miqewa tayi da sauri daidai lkcn da Hameed din ya shigo parlourn ganin yanda Umaiman take yatsina ana rirriqeta ai baisan sanda yayi watsi da ledar shop din dake hanunsa ba ya nufi Umaiman da gudu ya ruqota Hajiya tace  yawwa maza sata a mota haihuwa ce..."



Ai bata I rufe bakinta ba ya sunkuceta yayi waje har yana tuntube yanakiran sunanta, sata yayi a sit din baya yashiga ya tada motar bai jira fitowar su Hajiyan ba saboda gani yake zata bata masa lkcn yaja motar a mugun guje ya fice daga gdan.



Suna fitowa sukaga tashin qurar motarsa suka shiga wata driver yaja suka rufa masa baya bai iya hqrn kaita asibitin nassarawan ba saboda nisansa yake gani daga unguwar tasu wani asibitin kudi ya nufa aka karbeta aka shiga da ita larbour room sai bayan an shiga da ita sannan su Hajiya suka qaraso Hajiya ce tabada katinta tare da fada musu matsalarta shikam gogan sai safa da marwa yake yana hada gumi kamar shine yake naqudar duk sanda ya juyo nishinta shima sai yayi kamar shine me haihuwar lamarin ba duk da halin tararrabin dasu Hajiya suke ciki basu kasa yimasa dariya ba amma shi ko a jikinsa bin likitocin kawai yakeyi da suketa kaiwa da komowa idan kuwa yajisu shiru ya rinqa leqe kenan ta window.



Cikin ikon Allah baa bata wani dogon lkc ba Allah ya sauki Umaimah lfy ta haifo kyakkyawar yarta mace me kama da ubanta da uwarta dake dama kamar tasu dayace kowanne ka kalla sai kace yarinyar tana kama dashi tsakanin Hameed din da Umaimah.



Kukan jaririyar ne ya ankarar dashi aikuwa tun kafin a bashi izinin shiga ya danna kai dakin ya hango Babyn tanata wutsil a hanun wata nurse ko takan Babyn baibi ba ya nufi inda Umaiman take ya tsugunna yace  wayyohhh Allah Babyn Uncle sannu kinsha wahala ko da wahala haihuwa ko? Ni nama yafe kawai wannan kadai ta ishemu



Wani kallo da takeyi masa ne yasashi miqewa a sanyaye ya matsa inda nurse din take riqe da Babyn take shiryata ya tsaya ya zubawa yarinyar ido kawai sai yaji wasu hawaye sun zubo masa Allah kenan duk cikin yayansa babu wacce take tsananin kama dashi kamar jaririyar ajiyar zuciya yayi ya miqa hanu ya karbeta daidai lkcn dasu Hajiya suka shigo dakin.
Da sauri Hajiya ta nufi Umaimah ta dagota ta nufi toilet din da taga wata nurse ta fito tace  akwai ruwan da zata gyara jikinta?"


Amsawa tayi da  eh nama hada mata gashi can a ciki" shiga sukayi Hajiyan ta gasa mata jikinta sannan suka fito ta zaunar da ita a gefen gadon dagyar saboda ta dunku kamar qwarya sai a lkcn Hajiya ta samu damar daukar jikar tata da taketa wawuran abinci ta zuba mata ido kamarta da ubanta lkcn yana jariri har tayi yawa.



Hakanan suka yini a asibitin Hameed yana liqe dasu suna zuwa Hajiya dakinta takai Umaimah tana mata sannu har yanzu tana maqale da jikarta saida ta bawa Umaimah abinci da tea tasha sannan ta dora mata babyn a cinyarta tayi murmushi tace  yarinya kyakkyawa amma kun bata mata nasaba saboda son zuciyarku"



Hameed ne ya dago ya kalleta ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace  muma ba muso hakan ba Hajiya komai yana faruwa ne bisa buwaya da ikon ubangiji ku daina zargina wlh ba haka nakeba rabon wannan yarinyar zatazo a hakane yasa kika takura saina saki matata a halin inasonta tanasona kuma mun riga mun zama abu daya bazata iya rayuwa babu niba nima bazan iya rayuwa babu ita ba Hajiya ku taimaka ku dawomin da matata tunda ta haifemin abinda ke cikinta"








*UMMUH HAIRAN CE...
'<*
[1/20, 7:57 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'<: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:




*PAGE THIRTY-EIGHT*




Miqewa Hajiya tayi ta zugewa Umaimah rigar jikinta ta sanya hanunta ta ciro nononta ta dago yarinyar ta sanya mata a bakinta yarinyar ta kama tana tsotsa ya zubawa nonon nata ido yanajin wani shauqi da feeling na bijiro masa da sauri ya miqe ya fita daga dakin don ya fahimci zamansa zai iya haifae da matsala ko wanne lkc zai iya kai hanunsa ya cafki nonon ya taya yartasa sha.



Gidansa ya nufa yayi wanka sannan ya fara sanar da abokan arzikin sa anyi masa haihuwa matarsa ta haihu harda hotunan da yayi da bebyn ya dora a status dinsa na WhatsApp da Facebook aikuwa ya samu addu'a sosai zama yayi dirshen yana kallon bebyn da yayima huduba da sunan Hajiyansa Zulaiha yana kallon hoton yana hawaye yana Istigifari nadama yake da zuciya me tsarki tabbas ya aminta so masifa ne saboda sone umul aba'isin faruwar komai tsakaninsa da qanwar tasa amma meye ya sabbaba hakan?  Hajiya ya fada a fili tare da cewa  itace taja mana komai amma yanzu laifina suke gani saboda nine mara gata



Wayarsa ya dauka a karo na ba adadi ya kira layin Umaimah amma a kashe yasani koda a kunne take ba dagawa zatayi ba saboda ta dade da ajiyeshi da rayuwarsa a gefe gashi shikuma sai yanzune ma yake qara gasqata cewa soyayyarta itace take sarrafa rayuwarsa komawa yayi ya kwanta a kujera ya zubawa hotonsu ido lkcn farin cikinsu nanan bai gusheba shi abin ar mamaki yake bashi yanda yake hangen tsantsar qiyayyarsa a idon Umaimah Umaimah da a baya yake sarrafata da zuciyarta yanda yake so.



Da wadannan tunane ya kwana da safe ya tashi ya shirya domin tafiya aiki saida ya fara zuwa yaga lfyr Umaimah da bebynsa daya laqabawa Shurafah sannan ya haura sama gurin Daddy daya dawo daga tafiya jiya da dare suka gaisa yayi masa barka kamar abin arziqi sannan yace.



 Alhmdllh babana Ina tayaka murnar samun qaruwar da kayi taya mace naji karar da kayiwa mahaifiyarku ka kyauta daka sanya sunanta wa baiwar Allan nan Shurafah so kamar yanda na fada maka lissafin da mukayi a baya zai canza ne bayan haihuwar Umaimah to alhmdllh ta sauka lfy saboda haka yanzu zabi biyu gareka kodai ka karbi yarka ka nemi wacce zata shayar maka da ita ko kuma ka rinqa biyan uwarta take shayar maka da ita"




Mamaki ne ya kusan kashe Hameed wannan fah shine tsugunu bata qareba ansai da biri ansai mage.
A sanyaye ya dago yace  amma Daddy na dauka cewa Umaimah koba itace ta haifi Shurafah ba ita me riqemin itace ta shayarmin da ita batare data nemi ko qwandala daga gurina ba...."


Daga masa hanu Daddy yayi yace  ai wai da take uwar tata shiyasa muka fada maka haka dama da ace ba ita ta haifaba ma aida mu da kanmu zamu bata ta shayar maka da ita saboda haka zabi ya rage naka idan ka yarda zaka rinqa biyane to wajibine duk wata ka kawo min 5 million na ciyarwa"



A matuqar mamakance ya dago yace  5 million fah Daddy me Shurafah zataci da har zata cinye 5 million a duk wata Daddy duk mutanen dake gdannan ma bazasuci 2 millions a wata ba balle jaririyar da aka haifa jiya?"



Shiru Daddy yayi ya dauki wayarsa ya fara latse bayan yan sakanni aka daga yace  kuzo dukkanku inason ganinku a parlourn sama" yana fadin haka ya kashe wayar yaci gaba da duba wayarsa yana murmushi irin nasu na manya,
Shigowa sukayi suka hada ido ita dashi gabanta ya fadi sosai saboda wani kyau da taga yayi mata duk da ramar da yayi.



Daqyar ta iya samun guri ta zauna saman tumtum saida Daddy ya gama dannensa yace  Hajiya bashi yarsa" dagowa sukayi da sauri musamman Umaimah da taji mgnr kamar dirar kwarankwatsa a kanta.
Miqawa Hameed yarinyar Hajiya tayi jikinta a sanyaye hanunsa na rawa ya karba yana cije lebe wasu hawaye masu zafi suka zubo masa ya kwantar da yarinyar da taketa sharar baccinta a cinyarsa ya dago ya kalli Daddy yace.



 Na yarda zan rinqa badawa Daddy ka taimakeni kabar yarinyar nan a gurin mahaifiyarta idan na tafi da ita bansan ya zanyi da ita ba ko kuma ka mayar mana da aurenmu mu raini yarinyar nan cikin kulawar da duk wani da me gata yake samu a gurin iyayensa.... daukeshi da mari Daddy yayi yace  zaka tashi ka barmin gurin nan da shegiyar yarka kosai naci mutuncinka"



Miqewa yayi a matuqar sanyaye ya matsa gaban Umaimah da take kallon Daddyn tana mamakin furucinsa kalmar shegiyar daya Kira Shurafah da ita tafi komai dukanta ya dora mata babyn a cinyarta cikin kuka me ban tausayi yace  Koda kowa na duniya zaiqi Shurafah bai kamata ta rasa gata biyu ba nawa da naki Umaimah ni namiji ne banida nonon dazan bawa Shurafah ta rayu dashi kada kibada qofar rabaki da yarki da qaddara ta qadarta mata zamowa me rangwamen gata duk da nasani a gurin gama garin mutane take me rangwamen gata amma a gurina me cikakken gatace saboda na yarda itadin qaddara tace Umaimah babu wanda ya isa yayi maka wannan kyautar bayan Allah kuma bakida tabbacin sake samun wani bayan ita ta yuwu ita kadaice rabon dake tsakanina dake karki manta Umaimah kinsani komai yana faruwa ne bisa buwayar buwayi gagara misali badon hakaba dasai kice ya zaayi muna matsayin ma'aurata mu samu yarda bata sunnah ba to wannan kadai ya isheki misali ganin damarsa ne hakan ta faru Umaimah na roqeki kada kibada qofar banzatar da rayuwar yarinyar da bataji ba bata gani ba laifi nawane naji ayimin hukunci a kankin kaina amma kada ya shafi Shurafah dan Allah Umaimah....."



Wata tsawa Daddy ya sake doka masa yace  wlh tallahi Hameed idan baka bacemin da yarinyar nan a gurin nan ba sainayi maka abinda baka taba tunani ba jikinsa har bari yake ya miqe ya dauki yarinyar ya rungume a qirjinsa yana wani kuka mecin zuciya ya juya ya kalli Daddy yace  hakan ma na gde daka bari aka raini cikinta a gidanka amma kasani Daddy wannan zata zama rana ta qarshe da zaka rasani nima zanbar maka gdanka kuma Shurafah zatabar maka gdanka bari na har abada"



Yana fadin haka ya juya zai fice Umaimah tayi saurin riqo qafarsa cikin kukan tashin hankalin abu biyu rabuwa da yarta qwaya daya tak a duniya tace   Ina neman alfarma daya Daddy baa matsayina na mahaifiyar Shurafah ba a matsayina na yar'uwar mahaifinta ta jini wacce zan iya fansar rayuwata da tasa ina neman izinin shayar masa da yarsa batare dako sisin sa ba Daddy na roqeka kayimin wannan alfarm....."



Daka mata tsawa Daddy yayi yace  wlh baki isaba Umaimah saidai ki tashi kibishi tunda kin zabi farin cikinsa akan nawa kin fifita darajarsa da matsayinsa akan nawa to kitashi maza ki hada kayanki kibisa bana buqatar ganin shegiyar yarinyar nan a gdannan" bata iyajin kalmarsa ta qarsheba ta toshe kunnenta tare da sakinsa ta fashe da wani gigitaccen kuka me firgita zuciyar me imani tanaji tana gani ya juyo ya kalleta shima yana kuka daidai lkcn yarinyar itama tasa kuka da alamun nono take buqata amma ya juya ya fice da sauri ta miqe tana hada hanya zata bishi Daddy ya ruqo hanunta ta kuma rushewa da kuka tace.



 Tun safe Daddy Shurafah batasha nono ba ka taimakeni kabarni nabata koda shine na qarshe da zatasha daga jikina......" Dauketa yayi da wani gigitaccen mari tayi qasa ta zube yaraf ta qara dora hanunta a kanta ta rushe da kuka tace  shikenan Daddy ka rabani da yata qwaya daya tak a duniya...." Miqewa ta sakeyi da gudu ta nufi window daidai lkcn da Hameed ya kwantar da yarinyar a kujerar me zaman banza ya shiga ya tashi motar a guje yabar gdan har lkcn kuka yakeyi.



Zamewa tayi ta zauna a qasa tama manta da dinki akayi Mata soyayyar da da mahaifi ta mantar da ita ciwon komai sai ciwon rabuwa da yarta, saboda tsabar kuka har muryarta ta dashe Daddy ya tsallake ta ya shige dakinsa inda ta miqe tana hada hanya ta fita daga dakin ta fara taka matattakalar benen amma bata iya sauka ba jiri ya debeta tayo qasa luuuuuu daga saman ji kake tim ta fado tsakiyar parlourn qasan kamar matacciya Hajiya dake zaune take gursheqen kuka ta taso da gudu hakan yayi daidai da fitowar Kaka dake baccin asara a daki......







*UMMUH HAIRAN CE...
'<*
[1/21, 9:52 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'<: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-NINE*



Da gudu sukayo kanta cikin tashin hankali Hajiya taja da baya tace  mun shiga uku Kaka jini ta bakinta da hancinta kinga wani yana fita ta qasanta zata mutu Kaka anya Adamu bashida mental problem kuwa yaraba uwa da yarta a daidai wannan lkcn da kowacce uwa tafi buqata da tausayin danta Kaka ina Hameed zaikai Shurafah yanzu idan Umaimah ta mutu akan wannan dalilin me Adamu zaice da ubangiji?"



Riqeta Kaka tayi tace  me..mekike cewa Zulaiha maza ku tafi Asibiti ina zuwa nima" tana fadin haka tayi sama da gudu gurin Daddy ta fara buga qofar kamar zata balleta fitowa yayi ya bude ta cukuikuiyeshi tace  ina ka bari Hameed ya tafi da yarinyar nan to wlh ka fita da gaggawa ka nemoshi ka karbowa Umaimah yarta kafin fushina ya hau kanka ku baku da hankali da tunani kullum baku da aiki sai yanke hukunci cikin fushi"



Tana fadin haka ta sake juyowa ko mayafi babu a jikinta ta fito waje ta tsari taxi ta sanar dashi inda zai sauketa suna tafiya tana cewa dashi ya qara gudu cikin saa tana zuwa qofar gdan nashi dake FRW Layout ta hangi motarsa da wata motar a qofar gdan ta cillawa driven 1k tayi ta fada cikin gdan a guje amma me sai ta rinqa jiyo wani kakari yana fitowa daga parlourn da sauri tasakai ciki idonta kan Shurafah ya fara sauka dake dauke hanun Sarah tanata kukan neman uwa shikuma yana kwance a qasa sai fitar da dafara yakeyi mijin Sarah yanata bashi taimakon gaggawa tare da danna masa.



Cikin tashin hankali Kaka tace  mun shiga uku mukam wannan wacce irin masifa ce ta nufomu ne" daidai lkcn Daddy ya shigo don cika umarninta.



Dafe bango yayi da sauri tare da furta  Innanillahi wa innah ilaihir raji'un" mantuwa daya Daddy yakeyi a rayuwarsa shine matsalar zuciyar da aka haifi dannasa Hameed da ita.
Da sauri ya qarasa inda yake kwance yana fitar da wani wahalallan numfashi ya rungumoshi yana jijjigashi yana cewa  Abdulhameed! Abdulhameed!! Abdulhameed!!! Babana ka tashi kada ka fada a bakin mala'iku kada muyi irin wannan rabuwar dakai kada ka mutu kabarni babana ba qinka nakeyi ba wlh inasonka"



Kuka yakeyi sosai kamar qaramin yaro yana girgiza dannasa Kaka itama tana kuka tace  Shikenan ai kun kashesu kun huta saura yar itama gatanan Adamu kasa wuqa ka yankata sai ayi jana'izarsu gabadaya su ukun kukuma ku rayuwa a duniyar ku dawwama

Please Login or Register in order to submit comment