Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zataje taga aunty Safiyya. (Safiyya tana matu'kar son Ayman shiyassa itama Ayman takeson ta sosai).

Hafiz yace "jeki gayama Momy'nku zakije" Ayman tace "to Abi" taje tataradda Safna na gyara gado malik yana wasa. Ayman tace "Momy muzamu gun aunty Safiyya" Safna tace "to adawo lafia agaida Ummi" Ayman tace "Momy bazaki gida aunty Safiyya ba?" Safna tace "namanta ne kigaidata itama" Ayman tayi daria ta fice.

Suka kama hanya. Ayman tace "Abi muje kasiyama Aunty Safiyya chocolate da sweet" Hafiz yace "ok zamuje ne" ta kyada kai . sukaje suka siyo kan suka huce gidan Ummi.

Da Safiyya sukai karo wadda take zaune tana karatun novels a online sai murmushi take. Aguje Ayman tazo gunta tana Aunty Safiyya tahaukan jikinta. Safiyya tace "aaa Ayman daga ina keda wa haka?" Ayman tace "Abi yakawoni gashi yace akawo miki" Safiyya tace "wow chocolate tnk" Ayman tayi murmushi. Safiyya tace ina Momy'nki da Abi din?" Ayman tace "bamuzo da Momy ba da Abi kawai nazo" Hafiz yayi sallama, Safiyya ta amsa tagaidashi, ya amsa fuska a sake. Yace "ina Ummi Safiyya?" Tace "Ummi tafita" yace "ok adawo lafia" Safiyya ta amsa da "amin". Amina ce ta fito sanye da wani mini sket da wata riga ta roba ta kameta sosai. Ta 'karaso falon ta gaida Hafiz dashi ko kallonta baiba ya amsa a ta'kaice batareda ya kalletaba. Tace " Ayman ko?" Tatambaya tana mai kallon Ayman dake kan cinyar Safiyya. Ayman tace "eh kefa?" Amina tadan bata fuska nan tace "Amina" Ayman tace "aunty Amina kenan sunanki" Amina yace "no sunana Momy kinji daga yau" Ayman ta dan sage kai irinna shagwababbu tace "a'a Momy'na ce kadai Momy ko Abi?"........

Kubiyoniiiiii✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻🏻

Pls kuyi hakuri wannan yayi kadan zuwa gobeπŸ‘πŸ»

Takun daiiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatttπŸ’…πŸ½

{ Luv u all sweet friend~d😘😍}
[10/23, 3:15 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~😘✍🏻
3⃣0⃣
Hafiz yadaga mata kai alamar "eh" Amina duk inda ranta yake ya bace ga kunyar data mata katutu, tashi tayi a kunyace tana nadiye tabarmar kunya a tsiwace tace "nikuwa momyn kice ko anki ko anso" tafice abinta. Hafiz yayi wani wawan tsaki acikin ransa wanda har Safiyya tajiyishi tace "ya Hafiz yanaga Amina ta rainakane yanzu?" Kallo yabi Safiyya dashi kan yace "sis bansan daliliba Ummi ta tsane Safna yanzu kwata-kwata batason ganinta a gidana" yagama maganar a tausaye. Safiyya tace "nikaina ya Hafiz yanzu gabaki daya abin Ummi ya isheni, watarana har tsoro takebani musamman ma zuwan Amina a gidannan nikaina Ummi bata kulani kamar yanda take kula Amina" Hafiz yanisa yace "sis wlhy Safna nason Ummi ina tausayawa Safna ga abinda kedamunta gameda IYAYEN ta gashi kuma Ummi tasakata a gaba" Safiyya tace "ya Hafiz nasan komai mizai hana kayi kokarin shiryata da iyayenta ba? Safna tamaka *Halacci* baidace musakamata da hakan ba" Hafiz yayi dan murmushi mai kama da kuka yace "nabi duk wata hanya na sasantasu ama iyayenta basubani damaba, har office nasame dadyn nabashi hakuri ama yace dani idan nasake tinkarassa da magana ta safna sai yayi k'arata a court" Safiyya tace "subhanallah! Ina tausayawa aunty Safna wlhy, kuma ya naji Ummi na sanarwa Momy'n su Amina akan auren ku dagaski ne ya Hafiz?" Hafiz ya furzar da iska yace "hakane sis Ummi ta cilastamin auren Amina kuma harda kalmar *BAKI* acikin maganar idan ban aure Amina ba" wani bakin cikine ya bayyana a fuskar Safiyya tace "dama nasan za'a rina ba banza ba. Ina tausayawa aunty Safna. *KISHIYA*! Ai wlhy ko ta karace bazanso akawoma aunty Safna ba bale wannan mai kama da karuwan bariki" hawayeni suka zubuma Safiyya tareda kara tsanar Amina. Hafiz yace "banida zabi ne nikaina banida burin auren mace sama da 1 bale Amina dana tsana tun tun. Shiyassa bana zuwa Abuja gidan baba Sa'idu".

Hafiz yajira dawowar Ummi sugaisa bata dawoba yadau Ayman dansu koma gida zuwa islamiya. Da wayo da komai suka rabu da Safiyya. Fitowa yayi yana rike da hannun Ayman suka nufe inda yayi parking, kamar karya bode marfin motar yaji kamar an tsikareshi a zuciya gabanshine yafadi yarik'e kirjinshi yana furta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

Ayman tace "Abi muje mana" tana jinjina hannunsa dake mak'ale da nata. Marfin motar ya bude yaja suka isa gida. Ayman sai surutu take zubawa acikin motar ama Hafiz ko saurarinta bayayi. Sai gabansa dake mummunan faduwa.

Safna ce kan kujera a falo tasha wanka wani hadaddin material ne dinkin yakamata. Malik yana zaune kan ruwan cikin ta yana kwasar dariya tanamai wasa. Hafiz ne yashigo rik'eda Ayman sukai sallama. Safna ta amsa tareda tashi daga kwancin datake suna hada ido Hafiz yaji kamar anfiddamai wani abu azuciyarsa atake tsanar Safna yakamashi! Jiyake kamar yahauta da duka. Safna namai sannu da zuwa hannu yadagamata alamar bayaso. Dakinsa kawai yanufa danshi bayamasun yaji muryar Safna idan tana magana jiyake kamar anamai ambaliyan ruwan zafi a zuciyarsa. Kirjinsa yadafe yanufe toilet yawatso ruwa yafito, atake shigarda Amina tafito da ita gidan Ummi tadawomai yana siffanta yanda yaganta dazun, wani azababbin sunta yaji ya shigesa one time.

Safna mamaki tayi yanda Hafiz yamata ita a iya saninta Hafiz bayason yaga bacin ranta bale shi yabata mata, toko dan tana fushi dashine? Ta tanmaye kanta. Ayman namata magana tace "Ayman jiki shirya driver najiranki kuje islamiyya" Ayman tace "to Momy" tafice .

Side din Hafiz tafice tattarad dashi yana kife kan lausanshin gadunsa yana murmushi ga alamu yanajin dadi. Abin yabawa Safna mamaki ita azatunta zata taraddashi yacika fal! Sallama tayi ba amsa, ta k
'Karasa kan gadun tazauna tace "kayi hakuri Hafiz na hukuntaka akan laifin da bakada hannu aciki, pls kayi hak-" keeee! Yafada tareda ciwa "tashi kifitanmin daga daki kafin na canza miki kamanni yanzu" yana huci. Safna ta tsorata sosai ganin fuskar Hafiz ba alamun wasa atattare da ita. 'Kasa takai tana "pls Hafiz kayi hakuri karka dau fushi dani dan Allah kasani Hafiz banida gata saikai adun-" Safnaaa! Banason ganinki a rayuwata banason jin kalamanki a tattare dani please safna kitaimakeni kifita rayuwata" ba abinda Safna take furtawa face Kalmar "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!" Har sau uku. Zatai magana Hafiz ya toshi kunnuwansa tareda nuna mata 'kofar fita. Haka Safna taja kafafunta tabar dakin.

Kwanaki sunja yau takama Hafiz ko ganin Safna batason yi ba abinda ke hadashi da Safna sai idan yashigo yataradda ita a falo, idan yahun bakinta zasu kwafe baya amsa maganarta duk abinda zai sa yahadu da Safna ko magana ko wani abu saidai yabaiwa Ayman yace takaiwa Momy'nta. Abin yana matu'kar ma Safna zafi sosai ama batada mafita sai addu'ar datake ba dare ba rana.

Allah sarki Safna😭 rayuwa ta juyeπŸ™† yau ba bakin tsiwaπŸ‘„
_Nimadai nafara tausayin SafnaπŸ˜ͺ kofa masu karatu_???????

To kubiyoni✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatttπŸ’…πŸ½

{ I realy miss u mom😭}
[10/23, 3:15 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~😘✍🏻
{3⃣1⃣}

πŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”Ή
√√√√ *MUN DAWO LABARI*√√√√
πŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”Έ
_Fatan kuna biye dani frnd~s_

Bayan sun kammala sallar safna ta musu mitar karatundu na islamiyya dama lesson teacher dinsu yana zuwa musu,,,,,, Ayman tace "Momy malam mai Qur'ani yace gobe duk wanda bai iyaba sai yasha kashi" Safna tace "to ki gyara na samu na miki bita kafin gobe" Ayman tace "koma yau a ajinmu nice kadai na iya, malaminmu yace wake koyamin nace Momy na" Safna tayi murmushi jin dadi tace "to sai kirage wannan surutun naki ko kyasamu ki hardace da huri" Ayman tace "Dagaske Momy zan hardace AL~Qur'ani kamar malam Nura?" Safna tace "sosai ma kuwa" malik yace "nifa Momy?" Tace "harda kai ma".

Karfe 9:30 su Ayman sukai bacci, Safna ta nufe dakinta domin kwanciya. Hafiz sai kusan 12:00pm yake dawowa gida yahuce dakinsa sai bacci. Duk wannan abin da akeyi baya hana Hafiz cin abincin Safna.

Yau takama Sunday kamar kullum Safna tashirya tsaf tareda yaranta bayan sunyi breakfast suna falo a zaune. Hafiz ne a dakinsa yana waya da Ummi " to ganinan zuwa Ummi" naji yafada yana mai saka shoe dinsa. A falo yasame su ko sallama bai musuba ya haura kan dinning yakwashe girki mai rai da motsi. Ayman ce taje gunsa tana gaidashi, ya amsa mata cikin fara'a tareda ciwa "kinyi naki break din ne?" Ayman tace "eh tun safe ma" Safna tazo kan dinning din ta zauna tace "Hafiz inaso muyi wata magana" Hafiz ko kallon ta baiyiba bale ya tankata takai 5mnt tana saurarin maganar sa amma shiru kakeji. Safna ta k'ara da cewa "dama ba wani abubane inaso kudi ne zanyi sayayya kayana na makeup sun kare kuma ba kudi a hanuna" nan ma shiru kakeji ba amsa. Safna tana jin zafin yanda takewa Hafiz magana baya iya maida mata.

Tashi yayi yadau jakarsa yanufe k'ofa Safna na magana ko waiwayota baiba ya fita. Su Ayman na biye dashi har suka isa parking space nan yaciro kudi a aljihunsa yabama Ayman yace "kikaiwa Momy'n ku" Ayman tace "to Abi a dawo lafia" ya amsa da "ameen" yaja motar yafice, su Ayman suka koma gidan.

Basu same Safna a falo ba sukai bedside can suka sameta tana hawayen bakin ciki. Ayman tace "Momy miyasa kike kuka ko dan Abi bai baki kudin bane?" Safna ta rungumota tace "a'a Ayman yajine yashigemin a ido" Ayman tace "gashi inji Abi yace akawo miki" Safna ta dubi kudin tai murmushin takaici azuciyarta tace "Hafiz ba kufinka nakeso ba, kai nakeso" malik ya ce "Momy mizaki sayamin" Safna tace "duk abinda kukeso 'ya'yana" suka hau murna suna tsalle.

Hafiz da fitarsa gidan Ummi yahaura a falo ya taraddasu suna breakfast. Ummi ya gaisa ta amsa fuska a sake ganin yanzu danta yanason abinda takeso. Ummi tace "son zumuyi break" tareda jamai kujera takusa da ita. Hafiz yace "Ummi a 'koshi nake" Ummi tace "a ina kai breakfast din" Hafiz yace "gida" Ummi ta hade girar sama data 'kasa tace "ok jirani yanzu" Safiyya ta gaisa dashi ya amsa a takaice, Amina ma haka tanadan jujjuya idano kamar mage. Hafiz ya amsa cikin fara'a.

Bayan sun kammala cin abincin kowa yafice dakinsa Hafiz yana biye da kallun Amina datake sanye da wata gown purple iya gwaiwa da dan karamin hannunta can dahe da kafadarta ga na fulaninta kamar zasu tashi sama dan cika. Ummi ta rufemai baki da ciwa "son kasaman a daki" yace "to" tareda tashi yabita. A can sukai maganar Ummi tace "kaga son yanzu saura 2week auren yakamata a fara shiri" Hafiz cikin jin dadi yace "hakane Ummi" Ummi tacigaba da ciwa "yanzu zakaje ka hadu lefe nanda kwana 4 saboda suma su Momy nan zasu tare sai angama bikin zasuzo jibi kaga yakamata suzo sutarad mun shirya komai" Hafiz yace "insha'allahu Ummi zanyi yanda kikeso" Ummi cikin jin dadi tace "yawwa son haka nakeson naji" yanzu sai kafara shiri, kagama a dakin dake kusaga naka za'abaiwa amarya kaga ita waccan bakar munafuka bazata takira kuba" Hafiz yace "hakane Ummi nima bansan daliliba banason ganin tama wallahi" Ummi tace "ai ba komai bane dalili asirin da sukaima ne itada iyayenta shine ya karye" Hafiz yace "to Ummi ni zan huce office zamuyi meeting" Ummi tace "to adawo lafia" Hafiz yafita yanufe office. Acikin mota yakira Mubarak yace "anjima zaka rakani super market zamuyi sayayya" Mubarak ya fashe da daria yace "Kardai kacemin Malik yasame 'kane" cikin zolaya. Hafiz yace "kai dan isaka kai kamata cikin ne" Mubarak ya'kara fashewa da daria ta mugunta yace "baniba wanda yasaba dai yayi" Hafiz yace "banza kawai" Mubarak yace "to mi zaka saya ne?" Hafiz yace "idan kuma ka kwantar da hankalinka zakasani" yakace wayar.

Safna tanaso taje super market tayo sayayya. Wayarta dauka ta danna no din Hafiz, har ta cinke bai daukaba tasake saiga na ukkun sa'annan yadauka batareda yayi magana ba. Safna tace "hello Hafiz" ba amsa itadai tasan andauka ama tayi maganar dunia ba'a amsaba. Shikuwa Hafiz daya dauka kan table ya ajiye wayar yanajiyo muryarta yayi banza yacigaba da rubuce-rubucensa. Ayman ce tabiyo malik akan ya dauke biro'n datake home work dashi. Kan Safna sukazo duka sukasameta tana "Hafiz! Hafiz!!!" Shiru Ayman ta amshe wayar tace "Abi" kira daya yadaga yace " Ayman " Ayman tace "Abi Momy na magana fa bakace komai ba" kansa ys sosa kamar a gabanta yace "ina aikine Ayman banason damuwa" Safna a sanyaye tace "kigayamai zamuje super market" Ayman tace "Abi zamuje super market amuna sayayya" gaban Hafiz ne yafadi. Yace "ok adawo lafia" yakashe wayar.

Hafiz yace "to yanzu idan muka hadu da ita a super market dinfa?" Saikuma a file ya furta " kuma ai super market din ba dayabace a garinnan tayu wadda zamuje ba ita zasujeba"..........

Kubiyoni✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatttπŸ’…πŸ½

{ luv u sweet mom}😘
[10/23, 3:15 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~😘✍🏻
{3⃣3⃣}

Gudu take cikin motar zuciyarta sai azalzala take can ta tuna da makarantar su Ayman gashi lukaci yaye 3:40 hanyar *Mabera* ta nufa batai parking ba sai *Namirah Islamic Academic* makarantar su Ayman kenan.a gate ta ajiye su suka nufe cikin makarantar tareda mata hannu. Ta kama hanyar Gidan 'kawarta sumee. (Sumee tayi aure bayan auren Safna har tanada yarinya khadijatul kubra wacce suke kira da kubra) gidan sumee ta yada zango horn takeyi kamar wacce aka biyo. Gateman din gidan ne yazo da gudunsa harda tuntube yake ya kware gate din. Kutsawa tayi cikin gidan taja wawan birki ko parking bata gamaba ta fito, ta haura ciki.

Sumee na zaune kan kujera tana wa Kubra tsifa tajiyo budin 'kofar juyowarta taga Safna a tsaye sai zubar da kwalla take! Sumee takai gabanta da sauri tana "Safna lafia? Miya faru kike kuka? Safna kuwa kanta tafada tana kuka mai ban tausayi, Sumee tace " kinga Safna kayamin miya faru?" Nanma Safna shiru tayi sai rera kukan datake. Sumee ta kaita bedroom ta zaunar da ita kan gado, har yanzu kukan take. Sai da tai kukan tagaji sa'anan ta dago takalle Sumee data zuba mata ido. Sumee tace "Safna kigayamin abinda ke damunki pls" Safna ta koshe komai tasanarw Sumee har forget dinta da Hafiz keyi cikin kwanakinnan. Sumee ta burta "Subhanallah! Safna Hafiz dai da Kansa?" Safna tace "wlh kuwa Sumee narasa dalili bale mafita, duk wata hala'ka dazata hadamu da Hafiz sai dai tabiyo ta gurin yar mu Ayman" Sumee tace "hmm Safna kinga abinda nake guje miki a gurin da namiji yau kinga anfanin *IYAYE* kinga kuma rashin bin umurnin mahaifa yau Safna kin ga *BAKIN IYAYE*'n danake guje miki tun baya Safn-" Safna ta katseta da wani kuka tace "tabbas Sumee na cuce kaina na zabe zama da Hafiz sama da *IYAYE* na lokaci ya 'koremin tabbas *BAKIN IYAYE* yayi tasiri a gare-" kukane yaci karfinta Sumee ta rungumuta tana lallashi tace "Safna lokaci bai 'kore miki ba tunda *IYAYE*'n ki sunada rai kina da sauran lokaci. Shawarata gareki kije kirokesu gafara Safna" Safna tana mai share hawayenta tace "Sumee iyayena basa bu'katar ganina saida suka gindayamin sharuda kafin ayi aurenmu nacewa kar na kuskura na taka gidan ko nazo gawo kukan mijina" Sumee taja wata ajiyar heart tace "Safna duk da hakan yakamata kije kinsan iyayenmu duk abinda mukai musu bazasu yi fushi damuba musamman *UWA* {Allah sarki uwa Allah shibarmu da soyayyarki Uwa. Ameen} idan kowa zai 'kiki Safna na tabbata mahaifiyarki bazata 'kikiba" Safna tace "Sumee ina tsoro ne shiyassa tun aure na har yau ban je gidan mu ba" Sumee tace "Gaskia Safna kin *Tabka babban muskure* Na rashin zuwanki gidanku" atakyaice Sumee tabawa Safna shawarware tareda kwanta mata da hankali. Batabar gidanba sai 6:00pm takama hanyar gidansu saboda ta kudiri niyar komai za'amata yau sai taje gidansu.

Hafiz dayaja mota bai tsayava sai gidan Ummi yakaimata kayan. Akwatina ne yasiyo set biyu anka zuba kayan abun dai ba'a magana. Ummi tayabawa kayan sosai taji dadi tace "Son kaya sunyi kyau sosai sai kayan da amarya zata saka a events zaka bada kudi a dinko sai kuma kudinta dazaka bata wadanda zatai lalura dasu" Hafiz yace "to Ummi nawane kudin?" Ummi tace 50k zasu isa" Hafiz yacire kudin yabata" yace zai huce gida yasan wasa ruwa yakwanta Ummi tace "ok badamuwa gobe yan Abuja zasu iso jirgin safe zasu shigo" Hafiz yace "Allah yakawosu lafia" Ummi ta amsa da "ameen" yafita.

Dakin Amina ya fice a zaune yataradda ita kan kujerat mirror sai zuba kwalliya take Indian dressing ne kejikinta. Bufin 'kofa tajiyo ta waigo taganshi a tsaye sai murmushi yake mata. Gaishe dashi tayi ya amsa a fara'ance yakarabo kusanta yazauna kan gado yace "kinyi kyau" cikin jindadi Amina tace "thinks" yace "dama nazo ne batun bikin kinga saura 1week nawa ke isarki kiyi hidamar bikin" Amina tadan tabe baki tace "dubu dari biyar ma zasu isa" murmushi kawai yayi yaciro kudin yabata yafita.

Gida yakoma a mamakinsa ba kowa a cikin gidan. Side dinshi yanufa yawatsa ruwa dinning yanufa yaci abincinsa yayi 'kat sa'annan yakoma side dinsa yana dan rubuce-rubucensa. Sai asannan yatuna da Mubarak daya baro a super market. Tsaki yaja yadauko wayarsa da take kan bedsheet yakira number Mubarak yamasa wajan 5 missed call bai dagaba daga karshe yagaji ya aje wayar tareda koma jan tsaki.

Shikuwa Mubarak bayan yayi waya gida da 10mnt saiga driver'n gidansu yazo yadauke shi suka nufe gida. Yana kwance kan gado ne yaga kiran Hafiz banza yayi da wayar har tagama rurin datake. Shima tsakin yaja afili a furta "dan iska waye banza dazaka barshi s titi daga baya kazo kadaman dakira".

Safna titin gidansu tahau bai sadata ko inaba sai gate din gidansu horn tayi mai gadi yabude ta kunna kai sai ciki. Dady yana zaune a wajen gidan yana shan iska cikin gate din ansaka runfa yana karatun nows a jarida, jin anyi horn ana kokarin shigowa da mota yasa yajuya akai dai-dai da Safna tajuyo wazai ganiiiiiiiiiiiiiiiπŸ˜³β“

Kubiyo ni danjin amsar✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatttπŸ’…πŸ½

{Luv u all sweet friends}
[10/23, 3:15 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~😘✍🏻
{3⃣2⃣}

Safna ce tafito tareda Ayman da malik suka nufe parkin space. Kasancewar Safna ta iya driven, wata hadaddar mota fara naga sun nufa, Safna taja suka fice daga gidan. Tafiya suke sunadan fira Ayman sai surutu take a motar. Ayman ce tace "momy muje inda muka ranar muka hadu da wata Aunty har ta bani chocolate" Safna tace "oh Ayman naso muje *Double 7* kawai" Ayman tace "pls momy muje can ko zan ga aunty ta ranar" tsaki Safna taja mtwsss! Dayake ance dake canne gun zamata ba" malik yace "Momy muje can pls" Safna ta hau titi batai parkin ba sai *Yusra super market* wanda yahadu iya haduwa. Parking tayi suka fito suka haura sama.

Hafiz ne da Mubarak cikin mota, Hafiz yace "wace super market din zamu je ne" Mubarak yace "wadda muka saba zuwa mana" Hafiz yace "kai ni yau naji duk banason zuwan can, kawai muje *Double 7* mana" Mubarak yace "Allah yanzu ancin masu hurin kaya masu kyau muje can" Hafiz yace "yau kaida super market dinka kamanta kanaji da *Double 7* Mubarak yace " Adaba" Hafiz yace "to bari muje kawai" afili ama azuciyarsa kamar ana dakamai ganga a cikin ta" Mubarak ne yakatsemai tinani da cewa "wai ma baka sanarmin mizakai acanba? Kuma wazakaima shopping" Hafiz yayi yar ajiyar heart yace "Aure zaniyi a wannan week din" Mubarak dake driven baisan randa yasaka birki ba yakalle Hafiz daya tsorata ganin Mubarak nason kashesu yace "Hafiz lafiyarka kuwa? Mi Safna tamane dazakai aure a wadannan shekarun?" Hafiz yadan kallai irin kallon ban waje, yace "aure nakeso nayi ku zaka hanani ne? Mubarak yace " haba Hafiz duk kwata-kwata yaushine kai auren fari dazaka koma wani sabon auren" Hafiz yace "kai banason shishshige a lamarina kuma aure ba fashi kasani a wannan week din" Mubarak yace "Wacece zaka aura ne" "Amina" yabashi amsar kai tsaye. Mubarak yace "Badai ta gidanku ba Hafiz" Hafiz yace "Kaiiiii ya isa hakan idan zaka min fatan alkhairi kamin idan kuma zaka cigaba da min wadannan banzayin maganganun to kaficemin a mota tun muna sheda juna" ya kauda kai. Mubarak yasan halin mazan nashi yace "ba haka nake nufiba kayi hakuri Allah yabada sa'a ina ma fatan alkhairi" Hafiz yace "anan zamu kwana ne ko sai sarkin zama ya iske mu?" Mubarak yace "mazahh zama dakai sai ni" yana mai jan motar suka dau hanya.....

Safna dasu Ayman sai yawo suke acikin super market din adauko wannan a dauko wancan. Saboda Hafiz yabasu kudi isassu. Malik ne ya ce"Momy baki sayamin ball ba" Safna tace "oh namanta wlhy malik but muje nadauko ma" suka koma wani lungu dake cike da kayan wasan yara.

Basui parking ba sai *Yusra super market* fitowa sukai a tare a dai-dai inda Safna tai parking da motatta shima nan yayi parking dintasa, bai kula da motar bama sam bale number motar kasan cewar motocin sunada number's. Cikin super market din suka haura.

Kaya suka fara kwasa kamar ba gobe. Safna bayan ta daukoma malik ball da wani doki mai kyau, Ayman tace itama asayamata teddy Safna ta dauko mata duk suna rungume da abinsu. Jiyowa sukai gun night gown zata sayama kanta. Ayman ce a gaba Safna na jeye da hannun malik dayan na jeye da basket dasukai mai uban lodi. Hafiz da Mubarak kuwa suna tsaye a hurin night gown suna kwasa. Mubarak ne yace "Kai Hafiz wannan amaryar kuwa zata sha kaya, wannan kayan hak-" dai-dai su Safna sun kawo hurin, Ayman ce ta watsa da gudu ta rungume Hafiz tana Abi " Hafiz dayake rice ta wata sleep gown maroon jin anrungume shi yasa yadago kai dan ganin ko wanene , wazai gani.......😳 Ayman datai mai wata wawuyar runguma. Hafiz baki na rawa yace "Ayman keda wa" tace "nida Momy mana" tafada tana mai juyuwa ta kalle Safna. Sai sannan Hafiz ya lura da Safna da tai mutuwar tsaye kasancewar taji maganar Mubarak sarai a kunnenta, sai dai neman gasgatawa da take but zuciyarta taki ta yarda, duk da dinbin sayayyar da tagani a basket tasan sarai ta macece gasu inner wears dinnan datagani. Hafiz duk da ya tsorata ama dayake namijin duniya ne sai ya faske sai kallun safna dayakeyi, ita kuma kallunsa takeyi tana kallun basket dinnan. Mubarak shumane kawai baiba a hurin sai gumin daya ketomasa.

Saboda bakin ciki Safna batasan randa taja hannun su malik ba suka bar wajan. Batareda ta idar da sayayyar ba ta fice. List din kudin akai mata ta biya ta fita. Inda tai parking motar ta takoma nanne talura da motar Hafiz da aka sakawa *H NA MAKKA 02* takara tabbatar da motar Hafiz ce, wani bakin ciki yakara lullubeta tashiga motar taja ta bar wurin duk motanin hurin kallunta ake yanda ta tada kura a hurin sai cika take. Wasu suce tayi iska ne da ita wasu suce kuma tayu rasuwa akai mata. Titi tahaura sai kwasar gudu take

Hafiz wayan cewa yayi duk da Mubarak ya gano tsintsar rashin gaskia a taredashi. Suma batareda sun kammala sayayyar ba suka fice. Bayan sun kama hanya ne Mubarak yace "Hafiz duk da bakaso a gayama gaskia a cikin wannan maganar sai dai kayi hakuri, ama a matsayina na amini a gareka zan gayama

Please Login or Register in order to submit comment