Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*Mangoro road* wanda zasu kuma dukkansu shida yan uwansa uncle Usman da uncle Farouk gidan family house mai dauke da part 3 gidan ya tsaro tubar kallah,,,,,,,,,

Anyi shirye-sherye anzuba komai na bok'ata a gidan dana more rayuwa,,,,,,,su uncle Usman ne suka daukosu a airport,,,,suka huce a sabon gidansu Dady sai dadi yakeji ganin yanzu sun dawo huri daya shida yan uwansa *abin alfahrinsa* suma su uncle haka sukai murna sukai godia,,,,,,,,,,

Momy ce tsaye a gun dinning tana jera abinci,,,,sallama akai ta amsa cikin kulawa,,,,Faisal yazo dagudu ya rungome ta yana "wlcm momy I really miss u s mc dear" Momy ta murmusa tace "me 2 luvly son,,naga ka k'ara zama babba" Jabbar yace "badole ba Momy wannan gara ne dolensa ma yak'ara girma" Nafee tace "hmm Momy ya gida sannu da dawowa" Momy ta ce "yawwa sannu Nafee, yagida yajikin? Jabbar yagayamin bakijin dadi" Nafee tace "eh Momy ama da sauki sosai ma" Momy tace "to Allah yak'ara lafia, inda ce ba'a dakanmin yaro ba" Nafee tai daria tace "ba wanda yadakeshi Momy kitambaishi" Momy tace "hakane autan momy" Faisal yace "eh ai aunty Nafee ce bata barin yaya Jabbar yadakan" Momy tace "yawwa Nafee Allah kayimuku albarka ya saukeki lafia" Nafee cikin jin kunya tace "ameen Momy, ni zan shiga gurinsu Umma" Momy tace "Au dazuwanki ko ruwa bazaki shaba" Nafee tace "Momy zandawo nasha inaso naga Umma ne" tace "to agaidasu" Faisal yace "aunty Nafee zanbiki" tace "to autan Momy muje" Jabbar yace nima gani zuwa" kamal ne yashigo suka gaisa da Momy tatambaye Maryam yace "ai tare suke tana gun Ammi" Momy tace "yo ni naga yara kowa zaije gun mamarsa" Jabbar yayi daria yace "to ke mom ai ba ga 'ya'yanki sunzo ba" tace "suna ina yayan?" Kamal yace "gamu" Momy tace "a'a ni banaso nabarwa su haj hauwau da haj maimuna" duk sukasaka daria kamal yakama hannun Jabbar suka fita,,,,,,,.

Shekaru sunja yau idan kaga Safna bazaka shaidata ba ta rame sosai ga bakin da tayi,,,,,bata cikin kwanciyar hankali saboda Ummi ta sakata a gaba kullum bakin cikin datake ma Safna karuwa yake,,,,yanzu Safna ta daina zuwa gidan Ummi,,,,,,,,ga Safna Allah yabata saurin haihuwa Ayman nada shikara 1safna ta haife Abdul-malik wanda suke kira da Malik,,,,kuma dukkansu sunada babban jiki idan kagansu bazakace 'ya'yan shakara d'ai-d'ai bane saboda manyan jiki ne dasu,,,,,,,,,,,

Harkar Ummi sai k'aruwa take saboda Amina da momynta sai yahun bokaye suke dan Amina ta aure Hafiz,,,,,,,,, Ummi ce ke sallama kamar daga waje take magana,,,Safna ta tajiyu muryar Ummi nan hanjen cikinta suka fara shoky,,,,,,,,,,,

Fitowa tai da saurinta ta amsa sallama takai k'asa ta gaidata tace amsa a dak'ile,,,Safna tace "Ummi sannu dazuwa kizamna mana" Ummi ta kwalla mata tsawa tace "bazama nazoyiba bale kinunamin hurin zama nida gidan d'ana kin bi duk kin maganceshi sai abinda kikace to nasan duk wani makirci dakuke kullawa keda *Iyayen* nake,,,,kuma kisani nida d'ana mutu karraba munafukar banza" Safna nan hawaye suka kwararo mata tace "dan Allah Ummi kiyi hakuri" Ummi tace "yimin shiru kilinbabba mata" tana kainan Hafiz yashigo,,,,, jiki ba kware ya gaidata,,,,ta amsa a masifance,,,Hafiz yakalle safna datai kneel down sai zubar kwalla take!

Hafiz yace "Safna lafiya?" "Kasheta nayi kajiya yanzu ma a kabari take kajiya" Ummi ke fadar tareda wargamai harara, Hafiz yace "dan Allah Ummi kiyi hakuri Safna bataimiki komai ba ama kinbi kin tsaneta,,please Ummi kigaya min abinda Safna tamiki dan Allah" Ummi tace "ehh lallai Hafiz wato abin ya tabbata naganema idona wato dagaskene Safna da iyayen ta sun maganceka ko sun sadakar dakai ga boka ko? To kisani tajuya kan Safna da har iya yanzu tana zubar hawaye! Ta Allah ba takuba munafuka kawai yar matsiyata" Hafiz yace "Ummi kidaina wannan maganar mana ni Safna bata maganceniba kiyi hakuri" Ummi tace "shashasha kawai idan kagama kasaman gida inason magana dakai idan uwar taka ta ma izini" fuhhhhhhh! Ta huce. Safna ta tashe a guje ta shige dakinta ta banko kofar! Kan gado ta fada tana wane azababbin kuka, Hafiz ya biyuta yana buga k'ofar ama Safna bata budeba saima kukanta dayake jiyuwa a kasalance. Falon yakoma yazauna yabuga tagumi. Wayarsa ce tayi ring yazabura yadauko yaduba screen din yaga Mubarak yabayano a screen din wata ajiyar heart yayi shi atunaninsa Ummi ce, saida akakuma maimatu kiran kan ya daga. Can akace "hello Hafiz kana inane gamu munata jira kasanfa zamuje dauren aure'n nan kuma 2:30PM aka saka yanzu har 2:00 bakazoba" Nisawa Hafiz yayi tareda furzar da zazzafan iska yace "hakane Mubarak kuyi hakuri Ummi takirani" Mubarak yace "mikake nufi Hafiz? Waima yanaji muryarka ba dai-dai ba" Hafiz yace "bakomai kainane ke dan zafi kasan nayi aiki sosai a office yau wlhy" Mubarak yace "Allah yakoro sauki ama zakazo dan Allah? Wlhy Bashir yama hidima sosai ga aurenka yakamata kamai gaskia" Hafiz yace "zanje kiran Ummi daga can zan zo ama kada kujiran kawai kuje ni zan zo daga baya" "ok saika shigo kagaisa da Ummi" cewar Hafiz yakatse.

Dakinsa ya huce ya watsa ruwa tareda alwarla yafito. Motarsa yaja ya fice masallaci yai sallah kan ya ja burki gidan Ummi. Sallama yayi yauma kamar kullum Amina yatarad. Sallama ta amsa cikin ladabi da kisisina,, tace "ya Hafiz sannu da zuwa,,, ko kallonta Hafiz baiba ya fice abinsa fuskar nan kuwa tamke ba alamar fara'a kamar wani tsohon soja. Dakin Ummi yafice, a zaune yatarad da ita kan sallaya ta idarda sallah. Gaishe da ita yayi ta amsa batareda ta kalleba, yafi 5mnt bata kulasaba kan can tace " sai yanzu tabaka damar zuwa ne?" Hafiz yace "A'a Ummi sallah nayi kan nazo" "dayake kai ne ladanin masallacin ba" fadar Ummi da har ila yanzu kanta ma bata juyoba. Hafiz yayi shiru yana nazarin canzawar mahaifiyarsa dayasan batada wannan mumunan hali ama yanzu lokaci daya ta canza kamar kar Amina tazo gidann-" Ummi ta katseshi da cewa "amsa kirana kazoyi ko tunanin wancan munafukar matar ka?" Hafiz ya natsu huri daya yace "A'a Ummi" tace "to kanatsu kaji nagayama wata magana kuma banason musu ko musaya" Hafiz yace "to Ummi" tafara "Hafiz nasamama mata mai kirki da ladabi ba irin waccan ba ka auret-" Ummi aure kuma"? Hafiz yakatseta da tambaya. "Sosai kuwa aure kuma Amina zaka aura ko kaso ko karkas-" "Amina kuma Ummi wace Amina"? Ummi ta bogamai tsawa " karka sake tsaidani idan ina magana Hafiz wlhy inba hakaba nasassabama a gidannan! Kuma Amina zaka aura ta cikin gidannan yar k'anin mahaifinku, sa'annan wannan kalmar ita ake kira *Kalamu wahid* ba gudu ba jadabaya" kafin Hafiz yace wani abu ummi tace "tashi kaban huri" Hafiz da tune ya zurma k'oramar tunani sam bai jiyo Ummi ba, saida tak'ara mai-mai tawa a razane ya seto kansa yafara tafiya kamar wanda kwai yafashema a ciki, har yakai kofa yafita,,, Ummi ta buga dariya kamar ta yan tsibbo duk da itadin ma a rik'e take tace "Safna sai na fitarda d'ana daga tarkon ku matsiyatan banza masu bin bokaye" .

Afalo yaci karo da Amina sai yamutsa fuska take tana karai-raya. Hafiz afusace yafito tana mai magana wata harara ya bartso mata dani kana Manshat saida na tsorata (nazata dani yake danake biye dasu dan daukar rahoto) kai ta sosa ganin Safiyya a tsaye yasa taji kunya, Safiyya dana wani abu zata dauka a falo dan ita sam batason Amina musamman ma ayanzu da Ummi ta fifitata fiye da ita da ta haifa, wani littafi ta dauka a kan kujerat da Amina ke zaune batare da ta kalleta ba ta koma dakinta. Amina taja tsaki "mtwsk ai ke k'aramar kunamace saina gama da naman daki kannazo kanki ke" tawangala wata dariya mai cin ran mai saurare. Ummi tafito tace "Baby zi kisaman a daki zamuyi magana" Amina tace "to Ummi gani zuwa" (Amina tanada kirki ama na munafurci idan tanaso taci riba kanka to lokacin zakaga ladabi da biyayya ama idan batason komai dakai zatana bakantama ga walak'antar da alumma musamman ma talakawa. Ummi nasonta acewarta tafi 'ya'yanta ladabi shiyassa kullum tana mak'ale da ita awa gam)

Hafiz daga fitarshi motarsa yakoma yajata a hasale kamar namijin zaki yabar gidan. Tafiya yake kace biyoshi akai, da taimakon Allah ya isa gida lafia, dakinsa yahuce yakwanta sai wane nauyayyin bacci yayi gaba dashi.

Kubiyoniโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป

( *Ina mai baku hakuri makarantar wannan littafin darashin typing danayi kwanannan abubuwane sunkai yawa dan Allah kuyi hakuri ba lallai bane kullum ajini cuz inada abubuwa sosai a gabana nagode*)

Takun daii๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
Writer
๐Ÿ’Manshatt๐Ÿ’…๐Ÿฝ

(Luv u sweet frn~d's)๐Ÿ˜
[10/23, 3:15 PM] โ€ช+234 703 632 4075โ€ฌ: ๐Ÿ™†๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘„*BAKIN IYAYE*๐Ÿ‘„๐Ÿ™†๐Ÿ˜ญ
*Na*
~Mrs phareesy~๐Ÿ˜˜โœ๐Ÿป
2โƒฃ6โƒฃ
Hafiz kam shiga yayi akabashi yarinyar yagani tubar kalla,,,komai na Hafiz ta kwaso saidai ta dauko farin mamarta Safna,,,,,, karkuso kuga murna gun Hafiz,,,,,yamata duk abinda akewa jinjirin yaron idan yazo duniya ya duba jikin Safna,,,,,,,,

Waya yadauka yasanarwa su uncle Usman,,,,,sunyi murna sosai kuma sukace gasu zuwa yanzu,,,,,,nan take sukazo shida uncle Farouk sukaga Safna,,,,,,, waya sukawa su Dady dady kashe wayar ma yayi bayan yaji ciwa Safna CE ta haihu,,,,Momy ce tatsaya cewa Allah ya kyauta yaraya abinda anka haifa,,,,,,,,

Kwanan Safna 3 a asibitin sa'annan aka sallamesu,,,,bako kurar Ummi bata koma tako asibitin ba,,,,,,a gidan uncle Usman Safna ta zauna da yarta,,,.

Bayan sati yarinya taci sunan *Ayman* suna matuk'ar ji da yarinyar tasha kayan barka ba'a magana ita da mahaifiyarta ansha biki an ci ansha dangi da yan uwa duk anyi murnar haihuwar Safna,,,,,,,,

Itama Zainab Alh C,,, R,,, O ya barta taci gabada karatun ta har ta kammala scdry dinta kuma yasamam mata admission a jamiyar Dan fodio wato *Usmanu Danfodiyo university sokoto* inda take karatun *Science*

Har akagama shagul-gulan biki aka maida Safna dakinta Ummi bata zoba,,,,suma su Umma da Ammi sunyi mamaki rashin zuwan Ummi gidan har aka maida Safna,,,,koma komai aka aika daga gidan tamaida tace aisu ba matsiyata bane da arzikinsu akagansu,,,,,abin yawa Safna ciwo sosai har take tambayar Hafiz ko tawa Ummi laifine batazoba kuma Safiyya batazoba har anka maidata,,,,, sai dai kawai yace mata tayi hakuri bakomai bane,,,,,,batare da gamsuwa ba safna tabar maganar,,,,,,.

Yau Safna taceda Hafiz tanaso yakaita gidan Ummi taganta yace "to kishirya muje" tama *Ayman* wanka itama tai suka fito falo,, Hafiz yafito ya dauke Ayman suka tafi,,,,,,,,

Da isarsu gidan Ummi sallama sukai,,,ba kowa a falo sai Amina wacce take zaune ta daura daya kan daya tana taunar cingom sai chart takeyi,,,,,sallama suka koma yi still ba'a amsaba,,,suka shigo falon Hafiz yace "keeee bakyajin sallama ne ki wane share mutane" tace "au ya Hafiz banganka bane" yace "eh to ko bakiganni ba bazaki amsa sallamarba ko ba gidan musulmai bane?" Tace "sorry ya Hafiz" Safna datake tsaye tayi ajiyar zuciya tace "wannan kamar Amina A Mai makka" takalleta a walak'ance tace "eh nice ya ankayi?" Hafiz yace "kee wannan matata ce banason rashin mutunci" tayi dariya tace "laa ya Hafiz wannan ce Safna matarka?" Safiyya ce tafito tahango Safna tace "laa aunty Safna yanzu kuke tafe" Safna tace "eh wlhy sis ina Ummi?" Safiyya tace "tana ciki bari nakirata" Amina ta tashi tana wata rausaya tabar falon,,,,Hafiz sai tsaki yake,,shi arayuwarsa Amina batai masaba wlhy sbd batada rayuwar kwarai kanta rawa yake,,,,,..

Ummi tashigo yamutse da fuska tace "sai yanzu aka samu lokacin zuwa gurinmu?" Hafiz yace "ai Ummi basu jima da dawowa ba" Ummi tace "rofemin baki shashasha kawai" Safna na gaidata tai banza da ita Hafiz ne yace "Ummi ana gaidaki fa" tace "ina amsawa anzo lafia?" Nan jikin Safna yadau rawa tanata sak'e-sake a zuciyarta ko tayiwa Ummi wani laifine? Ummi tatashe ta koma side dinta Safiyya tana zaune tasan sa'ar da hawaye suka keto mataba ita dai tanason Safna wlhy kuma Ummi ba haka takeba yanzu duk ta koma hakan,,,,,Hafiz jiki ba kwari yace da Safna tashi muje"

A mota Safna sai kuka take tana cema Hafiz "Hafiz minaiwa Ummi ne take fushi dani wlhy akwai abinda namata take fushi dani Hafiz kagayamin pls nabata hakuri" Hafiz sai famar lallashin Safna yake akan tai hankuri bakomai bane,,,dakyar ta hakura ahaka suka isa gida kowa yanufe side dinsa da tunani fal a zuciyarsu,,,,,,

Da shigar Amina daki ta hau tsalle tana murna sbd tana labe taji duk abinda ya faru tsakanin Ummi da su Safna,,,,, kan gado ta fada tajawo wayar ta takira ring daya aka daga can naji ance "Daughter yakike?" A fangarin Amina tace "Momy na lafia klu nake" tace "ya dai fatar komai yana zuwa dai-dai"? Tace " sosai ma mom ai yanzu suka fita kinsan Allah mom wlhy ko kallun yarinyar bataiba" ta hau dariya,,a can bangarin tace "yawwa yarinya kirki ai hakan yayi dai-dai kuma komai daran-dadewa saikin aure Hafiz kinjiko" tace "to mom nagode fa" tace "yawwa my daughter, acigaba da gashi" tace "to mom bye" ta ajiye wayar takulla wata mahaukaciyar dariya tace "hmm dani kuke zancen ba Safna take ko wama? Allah saina fitar dake a gidan Hafiz sbd Hafiz nawane nikadai bawata banza dazatazo rana tsakiya takwacemin shi wai harda wata Ayman hmm.........

Kubiyo niiiii
~Uwar gidan phareesy~๐Ÿ˜œ

Takum;;;;;;;;

Writer

๐Ÿ’Manshattt๐Ÿ’…๐Ÿฝ

Luv u all frnzzzzz๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
[10/23, 3:15 PM] โ€ช+234 703 632 4075โ€ฌ: ๐Ÿ™†๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘„*BAKIN IYAYE*๐Ÿ‘„๐Ÿ™†๐Ÿ˜ญ
*Na*
~Mrs phareesy~๐Ÿ˜˜โœ๐Ÿป
2โƒฃ8โƒฃ
Safna kuwa bayan tasha kuka mai isarta tagaji dan kanta ta tashi,,,,kasancewar su Ayman na bacci yasa taji dadin cin kukan har ta k'oshi. Malik ne ya fara kuka a dakin su Ayman ta zo falo bataga Safna ba taje side dinta acan ta taradda ita tafito daga toilet tana shiri, daganin fuskar Safna yau ba walwala acikinta. Ayman tace "Momy Malik ya tashi yana kuka" Safna tace "to Ayman muje nai muku wanka" Ayman tace "Momy idan kikai muna wanka zaki kaimu gurin Aunty Safiyya ne?" Safna tayi murmushi mai kama da kuka tace "kinmanta yau fri?" Ayman tarufe baki tace "wai namanta fa Momy, bt gobe sat zaki kaimu nida Malik?" Safna tace "eh zankaiku, muje Malik na kuka kincika magana Ayman".

Fitowa sukai a tare A falo suka taradda Hafiz yasha wanka, yana dauke da Malik sai wasa yakemai. Kusa dashi tazo zata karbeshi Hafiz yarik'e hannunta yace " haba My beauty miye kuma na fushi ki kwantar da hankalinki mana" Safna ta kwace hannunta ta dauke malik batare da ta tankasaba tafice.

Dakinsu ta koma dashi ta mai wanka ta shiryashi tsaf, tayi kiran Ayman sai gashi sun shigo itada Hafiz yana dauke da ita. Ajiyeta yayi gaban Safna datasha mur, yajahuta a jikinsa yana "dan Allah My beauty karki hukuntane da abinda ba nine da laifiba kinsan Ummi tamiki ba niba haba Safna" Safna tayi k'okarin k'oce kanta daga jikin Hafiz ama inaaaa! Hafiz ya matseta sosai a jikinsa, Safna ko sai hawayen dake zubu mata (ita tasan tanason Hafiz ama ya ankayi take hukuntashi akan abinda tasan bashine da laifiba). Wayar Hafiz ce tai kuka shine dalilin sakin Safna yana lalubo wayar a aljuhunsa. Sai lukacin yatuna da daurin auren abokinsa Bashir, innalillahi! Ya furta a file yadaga wayar. Safna taja hannun Ayman suka nufe toilet, wanka tamata itama ta shiryata tsaf ta fesh
esu da turare, (kasancewar Safna macece mai tsafta batason kazamta ko kadan).

Daga wayar yayi yana mai bada hakuri can najiyo muryar angon yana cewa "haba Hafiz kafasan kune kawai abokanena miyassa zakamin haka?" Hafiz yace "wlhy Bashir kainane ke ciwo sosai shiyassa nadan kwanta ama gani zuwa yanzu" yace "ok Allah yakara lafia muna jira". Hafiz yafita yaja mota sai gidansu Bashir yayi parking. Hakuri yakara baima angon tareda mai fatan alkhairi. Mubarak yakallai a tsukane yace "ya dai baba ko uwar gidan ce ta hanaka fitowa?" Yana dariya, Hafiz ya jefamai harara yace "eh itadince ina ruwanka munafuki kawai" Bashir yafashe da dariya, Mubarak yace "kai jacan dawani baki kamar nabaka aro, sai wani tallar hauru kake kamar sabon ango" Hafiz ya tuntsure da daria yace "kamanta angone shi yau ne?" Yanayin tambayar ta tsokanace Mubarak yadinga daria Bashir yace "kaidai gayama ba ance kazo kai aure ba kak'i yau zakaga ta tsiyar" Hafiz yakalle Mubarak daya kusan sukewa kan daria yace "lallaima Bashir yo kaima ba'afakai ba fa kake ma Mubarak tsiya" Mubarak yace "tayani dai ganin hanya wai makaho yazo gulma" Bashir yace "to ku hana akawo ta din yau" Hafiz yace "idan kak'ara magana zanyi waya nace andaga kawo amaryar har zuwa next week" Bashir ya zaro ido waje yace "hmm da sunganni wlhy dakaina zan daukota nakawota gidana" Mubarak ya yi daria saida yarik'e ciki yace "Allah kayi raki my man" Hafiz yace "ba dole ba". Nan dai suka cigaba da cima juna zarafi har dare yayi aka dauko amarya sai gidan ango. Canma sun tsula tsiyar suna cimai rai akan ya ragar mata dan Allah a yau, ya wanka musu harara ya rufe gidan.

A fangarin Ummi kowa komai sai ci gaba yake dan ita kam jitake a jikinta kamar bazata same kwanciyar hankaliba muddun ba'ai auren ba, ji take kamar ana tsikararta da allura. Zaune suke itada Amina tana gayamata maganar aurensu itada Hafiz cikin satin nan, wata sassanyar ajiyar heart Amina tayi wacce saura kadan Ummi tajiyota, tace " to Ummi nagode kuma zanyi miki biyayya akan auren" Ummi tace "Allah kayi miki albarka " tace "ameen Ummi" tafita. Dakinta ta koma tadaka tsalle tareda dauko wayarta tai kiran momy, bayan sun gaisa Amina kema momy albishir cewa "sun take sa'a ta farko saura ta biyu" Momy ta rangata gu'da tareda cewa "dama nagayamin daughter bokannan yankan hu'ka ne" Amina tace "ai kuwa mom inama ace kinga wannan ba'ar uwar tasu yanda take zagwadi wai ita zata aura ma danta yar karki" momy ta yi daria tace "hmm bari kedai daughter zakisha mamaki, yanzu gobe zan koma hurin boka yakoma azamu akan wata turbar dan nasan Hafiz akwai taurin kan tsiya kamar ubansa" Amina tai daria tace "ai kedai mom bari bakiga wani kallo dayakemin ba na tsana" Momy tace "ai barshi mungama da uwar tasa saura shi shimadin abune mai sauki gobe zankoma gun boka yankan hu'ka yamana aiki" Amina ta dare tareda shewa tace "Think u mom bye".

Safna ce a falo itada Ayman da Malik. Ayman tana tunawa momy'n tasu zuwansu gun aunty Safiyya, Safna tace " bari Ayman gobe Abi zai kaiki kinji ko" Ayman tace "dagaske Momy" Safna ta gyada mata kai kawai. ( Ayman yarinya ce mai surutu sosai idan kana zaune da ita saika 'kosa da ita). Hafiz ne yayi sallama Ayman ta amsa tareda masa "oyoyo dady ina ice-cream?" Dagata sama yayi yace "kaiii Ayman ko fa hutawa banyiba kike maganar ice-cream" Ayman tayi daria tareda jawomai dan guntun gemin daya tara kanar an tsinke kara tace "Abi daga ina kake ne haka? Ko kaje gurin Aunty Safiyya ne?" Hafiz yace "a'a daga wani gu nake Ayman baki bacci bane?" Yana maganar yana kallun safna dataci wani mayen wanka. Safna da tun farin maganarsu bata tankasuba tace "idan kingama surutun ai sakizo muje ki kwanta" Ayman ta sagobe kafada tace "ni ni sai Abi yabani ice-cream sa'annan" Safna tace "bazaki baccin bane kenan?" Ayman ta turo baki. Hafiz sai kallo ne nasa. Safna tace "zakizo ne ko saina iskeki hurin na babballaki?" Hafiz yajawo ledar dake gabansa yaciro ice-cream yace "Ayman ga ice-cream dinki jeki kibi Momy'n ki kinji?" Ayman ta amshe ice-cream din tareda mannamai wani lafiyayyen kiss a kunce ta sauka a jikinsa tace "nagode Abi" tabi Safna suka shiga dakin. Kwantar dasu tayi tareda musu addu'a duk da Ayman tanada wayo sosai ga baki ta iya addu'ar shiga bacci, Safna takaramusu wata bayan Ayman tayi tashafamusu da Malik da tune yayi bacci takashe hutar dakin tareda rage Ac din dakin taja 'kofar.

Kubiyoni......โœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป

Takun dai๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
Writer
๐Ÿ’Manshattt๐Ÿ’…๐Ÿฝ

{ Luv u all sweet friend~s๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜}
[10/23, 3:15 PM] โ€ช+234 703 632 4075โ€ฌ: ๐Ÿ™†๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘„*BAKIN IYAYE*๐Ÿ‘„๐Ÿ™†๐Ÿ˜ญ
*Na*
~Mrs phareesy~๐Ÿ˜˜โœ๐Ÿป
2โƒฃ9โƒฃ
Da fitarta dakinta ta huce batareda ta koma kan Hafiz ba marfin kofar ta maida ta rufe. Hafiz ya bita koda ya isa 'kofar yajita a rufe gam! Wani haushi yakama sa ya boga 'kofar tareda fadin "Safna! Safna!! Kibude 'kofar mana pls karkimin hakan wlhy duk abinda kinkagani ba laifina bane Safna ki fahimtan mana" Safna kan gado ta fada tana kuka mai tsuma rai. Hafiz bayason yaga bacin ran Safna ko kadan bale kukanta. Yakai kusan 30mns yana abu daya daga baya ya hakura yaje dakinsa ya kwanta ga yunwa na damunsa ama baya iya cin komai saboda bacin rai. Yazo bacci kuma baya iyawa kalam Ummi kadai ke dawomai a kunne, shi a tinaninsa ma yaza'ai yagayawa Safna zai 'kara aure gaskia shi bazai iyaba. Da wadannan tinanin bacci yayi gaba da shi...

Safna kuwa ba itada bacci ba sai 12:00 tasamu ya dauketa bayan tasha mai isarta ta gyatsa. Sai kusan asuba ta farka tayi nafilfili kan aka lokacin sallah yayi ta yi tadawo ta kwanta kasancewar yau weekend. Basuda tashiba sai 10 Safna ta farka wanka tai tashiga kitchen bayan ta kammala breakfast taje dakinsu Ayman ta musu wanka tashirya su itama ta sake wani sabon wankan suka nufe dinning. Abinci ta zuba musu suka tsakiyar ci Hafiz yafito da shigarsa kammalalliya shima yanufe dinning saboda shima yunwarce ta tadashi. Sallama yamusu Safna ta amsa a ta'kaice batareda ta kallaiba tacigaba da bama malik a baki. Ayman ce tace "Abi barka da asuba?" Hafiz yace "barka dai Ayman kintashi lafia?" Ayman tace "lafia klu" zama yayi yana kallun Safna dako daga kanta bataima bale ta dubeshi fuskar ga tamke kamar Billy ta dau fushi. Lolz

Hafiz yace "ni baza'a bani abincin bane?" Ayman tace "Abi kazo ga indomie dina kaci" Hafiz yace "barshi kawai Ayman indomie ai saike ni abinda momy'nki taci shinake so" Ayman tace "momy kizubama Abi nasa mana yanajin yunwa" Hafiz yayi daria yace "kwarai kuwa Ayman kamar gabanki akai" Safna tagama ta 'koshi ta tashi abinta. Hafiz dayaga zata batamai lokaci yazuba abinsa ya'kosa sai da ya 'koshi ga Safna gwanace gun girki ko wani iri na zamani dana gar-gajiya ta iya ta huta shiyassa Hafiz baya iya cin abinci a waje sai na safna. ( garemu mata iya girki yanada very infortance a rayuwar mace saboda kokinma miji wani laifi wlhy a hurin cin abincin zai neme laifinki ya rasa saboda haka pls yan uwana mata mu koya karkiji kunya dan kar aga GP dinki yayi down wlhy ba wani GP kije kikowa gun 'kawarki ko yar uwarki koma makarantu na koyar da girka yanzu alhamdulillah kai ya waye yanzu duk abinda baki iyaba Allah kekikaso munsame cigaba sosai a rayuwa saboda haka yar uwa ki garzaya kar abarki abaya kizo kina ganin laifin ammiki kishiya. Yo wani namijine zai zauna dake ba iya girki?๐Ÿ˜ nidai manshat ba ruwa nawa aciki shawara nake baki yar uwa๐Ÿ˜‚ *mukoye girki mata*๐Ÿœ๐ŸŒฏ๐ŸŒฎ๐Ÿ๐Ÿ˜œ)

Bayan sun kammala ne Ayman tace "Abi yau Momy tace zaka kaini gun aunty Safiyya" yace "Ok kishirya muje" tace "yeee naji dadi harda malik?" Yace "a'a shi zaiyi kukane idan baiga Momy'nsa ba" Ayman tace "bazamuje da ita bane Abi?" Yace "eh ba yanzuba suma zasuje" tadinga murna tana tsalle

Please Login or Register in order to submit comment