Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ali yayi. "Subuhanalillah assha ai kaddara ce kuma hannunka baya rubewa ka yanke ka yarda ku kwantar da hankalinku yanzun nan zan tafi nayi magana da ita komai kenan zakuji ku tashi ku tafi Allah yayi maku albarka." "Amin ya Allah Baba." suka ce sannan suka tafi suna fatan dacewa.


Koda Baba Ali yaje gida wajen Mama bai damu da tarbar da tayi mashi ba, dan daman ba shiri suke ba tunda ya nemi ta bashi Yaya Amina ya rike da Babana ya rasu tace bata ba kowa ɗanta ita zata rike daga nan suke yar'ga maciji bayan sun gama gaisawa yace mata. "Hafsat nazo ne kan maganar aurar da Mamana da kikace zakayi ba tare da izinina ba ni kanan ubanta kinsan nine dai madaurin aurenta kuma an bata aure ko zuwa gaisuwar iyaye babu."? Cikin masifa Mama ta fara yi mashi magana. "Wato Ali zuwa sukayi suka hadani dakai ko? Dan sun kasa to bari kaji wallahi baka isa ka hana wannan auren ba nan da kwana sha ukku za'a daura masu aure, dan ma kun samu Alhaji Salahu zai rufa maku asiri zai aureta a haka, ai nasa bayana zaka goya a matsayinka na mai hankali da hangen nisa ba nasu ba,amman sai naga akasin haka to kasani aura tuni akayi shi aka gama ko dakai ko babu."

Baba Ali Allah yayi mashi zuciya, zuciya gareshi sosai shiyasa shima ya taso mata yana cewa. "Ni kuma wallahi zan nuna maki karfin ikona akan Khadija baki aura mata wannan tsohon banzan kuma ki sani nike da iko sa iyalan Hashim bake ba, tunda ni nono daya muka sha dashi kuma mu biyu iyayenmu suka haifa a fadin duniya ke baki isa ba kiyi mata auren dole dan kawai tayi ciki bayan zubda mata cikin da kikayi bai isheki ba sai kinyi mata auren dole ki godema Allah kece kika haifeta wallahi da sai nayi shara'a dake akan zubda mata ciki da kikayi muna son cikin a haka duk da ba na halak bane mu cikakun musulmaine tunda mun yarda da kaddara." yana gama fada mata haka ya tashi zai tafi itama cewa tayi. "Baka isa ba wallahi Ali nida kai mu zuba mu gani." bai ce mata komai ba ya fitowarshi ya hau motarshi ya wuto asibiti.

Koda Baba Ali yazo asibiti, baice ma su Yaya komai ba ni ya fara dubawa sannan ya tambaye ni jiki nace mashi da sauki, kallon su yayi sanann naga ya fita sai kuma ɗaya bayan ɗaya suka kama fita, take jikina ya bani da matsala su Yaya suke boyeman, hawaye ne suka fara zuboman dan ni yanzun kuka ya zama abokin fira ta, Dije ta kama bani hakuri ba dan na hakura ba nayi shiru sai dan naga yanda itama ta tada hankalin ta shiyasa nayi shiru amman ni kaɗa nasan irin ciwon da nakeji a kasan zuciyata.


Koda suka je wajen Baba wucewa sukayi office din Doctor suka zauna suna kallon Baba suna jiran suji abunda zai gaya masu, dan hankalinsu ba kwance yake ba yanda suka ganshi sunsan ba'a dace ba, numfasawa Baba yayi sannan yace. " na rasa wata irin mahaifiya Allah ya baku Jamilu baki ɗaya Hafsat idan tana abu sai ta koma ƙaramar yarinya wanda bata son komai ba a duniya inba nonon uwarta ba, kuyi hakuri karkuce ina gaya ma mahaifiyar ku maganganu mararsa dadi dole tasa haka har nike fadi ba yanda banyi da ita akan kartayi ma Khadija wannan Auran amman tace sai tayi, sai dai ku kwantar da hankalinku wallahi ba ta isa tayi mata aure ba sai inda karfi na ya ƙare a matsayina na uba a wajen Khadija, karku samu damuwa."


Yaya Fatima ce tayi karfin halin cewa. " Baba kayi hakuri munja maka Mama ta gaya maka maganganu mararsa dadi, dan Allah kayi hakuri kuma insha Allah muma zamu tayaka yaƙar Mama ganin bata yi ma Auta wanann auren ba."
Murmushi yayi dan Yaran dan'uwanshi suna burgeshi suna ta tarbiya sosai kuma yasan wajen mahaifiya suka samaita, sai dai idan Mama tana wani sai abun yaba kowa mamaki dan abu take kamar wanda bata taɓa zuwa makaranta ba, tashi yayi yana cewa. "Wannan abun dole nane karki damu, ku taso muje dan naga jikin da sauki ya dace ace ansallamaita haka nan."


Yaya Jamilu ne yace. "Eh Baba ɗazun da safe aka sallamaimu, daman kai muke jira kafin mu tafi, mungode Allah ya saka da alkhairy Baba" haka suka fito suna kara tautaunawa akan matsalar Mama, da yanda yazasu shawo kan matsalar ba tare da wani yaji ba har azo daga baya ana yi mana dariya, tunda ba wanda yasan nayi ciki sai yan'uwana sai kuma Alhaji Salahu da Mama taje ta gaya mashi, bayan sun dawo muka hada kayanmu sannan muka taho gida.

Koda muka koma gida kallon banza Mama tayi mana ta watsar, kallon da naga Mama tayi mana shi yasa jikina ya mutu take naji ban da lafiya dan ina tsoron abunda zatayi man, tunda ni daya za'a bari gidan nida ita zaunawa mukayi muka gaidata amman abun mamaki maimakon ta ansa gaisuwar sai ma ce masu tayi. "Wato ni zaku kai ƙara wajen Ali ko? Kunsa Ali ya isa yasani balle ya hanani? Kin nuna man ban isa da Khadija bako? Da har zaku kai ƙarata wajenshi dan nace zanyi ma Khadija... Katse ta Yaya Amina tayi tana cewa. "Mun isa mu kaiki ƙara wajen Baba wallahi Mama mudai ce mashi Khadija bata lafiya kema baki lafiya shine yace bari ya fara zuwa ganinki sannan yaje ya ga Khadija bamu ce mashi komai ba bayan nan ko Yaya Fatima."!? Cikin tsoro ta ida maganar tana kallon Yaya Fatima, take nasan ba lafiya mai Mama zatayi man wanda yasan yan'uwa suka kaita ƙara wajen Baba Ali, nidai kallonsu nike da tambaya a bakina dan inason nasan abunda Mama zatayi man wanda su Yaya basu son nasani, ji nayi Yaya Jamilu yana cewa. "Auta tashi ki shiga ɗakinki ki huta dan naga kamar bacci kike ji, ke kuma Aisha shiga kitchen ki dafa mata ruwan sanyi wanda zata dan gasa jikinta mana." naso nayi gardama amman bani iya yi ma Yaya Jamilu gardama dama Yaya Aisha ce da sai nayi tunda nike bi mata daga ita sai ni, tashi nayi na shiga room din na, ina kallon sanda Yaya Amina ta leko taga mai nike sai akayi sa'a kwance ta tadda ni bisa gado na lumshe ido, ni kuma ina ganin haka nasan magana ta zasuyi amman basu sun naji, tasowa nayi na laɓe jikin kofa yanda zanji komai zasu ce.

Ji nayi Yaya Jamilu yana cewa. "Mama dan Allah muna ƙara baki hakuri akan abunda Auta ta aikata insha Allah ba zata kuma ba, sannan kuma dan Allah karki aura mata Alhaji Salahu ki bata dama ta fiddo wanda take so sai a daura mata, amman aurar da ita ga Salahu da kike niyar yi shine barazanar lalacewar Auta Mama." ji nayi hawaye sun zuboman wai ni za'a daura ma wannan tsohon mutumin wanda ko gaidashi baniyi a unguwa tunda na lura da yanda yake kallona idan na fito zani islamiya ko kuma boko, ina cikin yin hawaye na naji Mama tace. "Duk ki tashi ku bani waje wanda basu da hankali sannan kuma sani wallahi sai na aura mata shi nan da kwana goma dan haka ku fita ku bar man gida kafin raina ya ɓaci." tashi naga sunyi nayi sauri komawa bisa gadona na share hawaye dan ban san na nuna masu naji abunda suke cewa haka suka shigo suka kara dubani suka ce na ringa tsarki da ruwan zafi ina gasa jikina dan naji kwari sannan suka tafi gida, ai suna fita naji tashin motocinsu na tashe da kuka mai cin rai, aiko Mama ta shigo ta fara yi man fada akan nayi shiru na tashi na shiga wanka yau bako zanyi.

Ba yanda zanyi haka nayi duk abunda Mama tace harda bani kayan kwaliya nayi , haka yazo ya gama yi man surutanshi ya tafi, ni kuma na fara shirya kayana cikin wata yar'karamar jikka ina jiran dare yayi na tafi na barma Mama gidan tayi yanda zatayi da shi, idan taga ban nan ai sai ta samu wanda zata aura ma tsoho haka na kama hidimata kamar ba abunda ke damuna ana kiran mangariba Mama ta shiga daki danyi sallah ni kuma na dauki jikka da wayata da komai nawa harda sarƙar zinarina guda biyu wanda Mama da Yaya Jamilu suka saya man sai kudi masu dan yawa na fitowata, ina fitowa naga mai naped nace ya kaini tasar jibia.


👇👇👇👇👇👇👇

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃


*Matso kiji ƴar uwa* 👂👂


*Shahararriyar marubuciyar nan wadda tayi ƙaurin suna gurin kasheku da dadaɗaɗan litttatafanta wato Aisha Umar Ibrahim (Real eeshow ) yauma gata tazo muku da wani shahararen book ɗinta wanda ta daɗe tana tanada muku shi cikin farashi mafi sauki wato 200 kacal.*


*Ga sunan book ɗin kamar haka*
👇

🌻 *BAR RAINA ALLURA*
*( Itama ƙarfe ce)*


*Domin neman ƙarin bayani kan wannan book zaku iya tuntuɓar mu a kan lambobinmu kamar haka* 👇
*08108362334 or 08135361133*


*Ƴar uwa karki bari a baki labari domin wannan salon na dabanne kamar yadda marubuciyar take ta daban.*😍😍😍😍


*karki bari kiyi missing ɗin wannan book ɗin hajiya.*



Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD


*Wannan page din nakine Phatermarh kankia Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Deey musy, my Dejja, ki sani nayi missing dinki sosai da sosai Allah ya maido man dake duniya social media lafiya sannan ya baki sa'ar karatun da kikeyi, ina maki fatan alkhairy ta wajena*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 13⏩14

Tunda suka shigo gida suka tadda Mama zaune tayi tagumi ga dukan alamu abun duniya duk ya bi ya isheta, da sauri Yaya Jamilu ya ida isa wajen Mama yana cire mata tagumi da tayi ɗaura kanshi yayi bisa cinyarta yana mata alamun lailashi, suma samun waje sukayi suka zauna duk sunyi shiru sun rasa abunda zakuce ma Mama, Yaya Fatima tayi karfin halin cewa. " Mama kin san dai mutum baya cika cikaken musulmi har sai yayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, itace ake kira da jarabawar rayuwa, Mama Allah kaɗai yasan irin kaddarar da Auta ta zano a rayuwarta kuma ba wanda ya isa ya wannan kaddarar, to mu mai zamuyi ma Auta Mama? Auta a halin yanzun tana bukatar Addu'armu muyi mata fatan faɗawa a hannun na gari." shiru tayi tana sauke numfashi dan halin da ta tadda Mama ta bata tausayi sosai kuma tabbas Mama tana son kula da ban magana mai dadi wanda zai sa hankalinta ya dan kwanta koda ba duka ba.


Kama hannunta Yaya Aisha tayi tana murzawa sannan tace. "Mama dan Allah ki yafe mana sannan ki yafe ma Auta, dan Auta ko tayi kuskure babba da tasa ƙafa ta gudu ta barmu ba tare da tayi wani tunani ba, kuma insha Allah zamu sa a nemo mana ita duk ind... "Aisha na yafe maku itama Khadija na yafe mata, amman ku sani ba wanda zaisa aje neman Khadija tunda ba wanda ya fidda sannan kuma ba'a aiketa ba, tabbas ba zanyi ma Khadija baki ba a halin sa take ciki sai dai nace Allah ya bata sa'a akan abunda tasa gaba nike na fita haƙinta a matsayin ta na marainiyar Allah ni kuma a matsayina na mahaifiyar ta mai son ganin farin cikinta, kuma da ta sani bata gudu ba da yau sai tayi dariya amman yanzun tunda har ta gudu ba baki ba watarana kuka zatayi da idanunta tana da nasani marar iyaka sai dai bani fatan Allah ya barni da rai na har wanann rana tazo, inalillahi wa'inna'alaihijirun Allah kana ganin halin da yarinyar ta samu ciki, ya Allah ka kareta daga sherin duk mai sheri, Allah karka ba wani damar kama ma ɗiya hannu da sunan yin fasiƙanci da ita koda kuwa ita ta kaimai kanta da kanta, ya Allah ka duba rayuwar marainiyarka wanda bata da uba sai uwa da yan'uwanta, Allah.... Kuka Mama ta fashe dashi kuka mai ciwo da ɗaci dan ita kaɗa tasan abunda takeji a zuciyarta.



Yaya Amina ce tayi karfin halin cewa. "Dan girman Allah kuyi hakuri addu'a dai zamu cigaba da yi kuma Mama kinsan jinin ya hau fa inji likita ya dace sausauta wannan damuwar, sannan Mama kika ce da yau zatayi dariya, wace dariya zatayi ko kin fasa aura mata Alhaji ne."? Girgiza kai Mama tayi sannan tace."Aa Amina ina bakata nayi mata aure, bayan Alhaji yazo zun gaisa da Auta sai na tafi nayi mashi rakiya zai koma gida, dan ita Auta suna gama magana ta tashi ta shiga ɗakinta, bayan mun gama ya tafi sai Aminu saurayin Auta yazo ya gaidani yace man ya shigo gari sannan yana ta kiran wayar Khadija a rufe shine yazo Allah yasa lafiya? Nan nace mashi yayi hakuri aure za'ayi mata take ya fara hawaye yana salati yana cewa maiye aibunshi da har Khadija ta fidda miji bata fidda shi ba, ni kuma tausayi ya bani sosai dan naga yana sonta sosai shine na gaya mashi abunda ya faru da ita da auren da zan mata da Alhaji ban boye mashi komai ba, amman abun mamaki maimakon yace bai aurenta sai yace man ai shi yana sonta a yanda take koda kuwa ta haifi cikin to zai aureta bayan ta gama shayar da abunda ta haifa sannan ya rike abunda ta haifa har yayi mashi aure, amman idan har na yarda a fasa auren da Alhaji shi zai aureta, amman sai nace mashi yaje ya dawo yau dan zanyi tunani, sannan ya shiga motarshi ya tafi bayan ya shigo da tsarabar da ya kawo mata, ni kuma ina dawo na tadda ta a parlour zaune, ban kai da yi mata maganar ba aka kira sallah na tashi na shiga dan yin sallah ina fitowa ban tadda ta a parlour ba sai na shiga kitchen na dafa mata abinci na haɗa mata ruwan wanka shigar da zanyi na tadda ta gudu, kuji abunda mukayi da Aminu."


Yaya Fatima ce tace. "Allah sarki nasha gaya ka Auta duk cikin samarinta Aminu yafi sonta amman sai tace ita bata son shi bai'iya soyayya ba, gashi kinga halllacin da yayi niyar yi mana Allah maido ta da hankalinta gida." "Amin ya Allah." suka ansa sannan suka ƙara kwantar ma Mama da hankali kowa ya wuce gida yana tunanin ida na tafi.


*~~~~~~~~~~~~~~*

_HIRJI_

Tun asuba wannan matar tazo ta tadani tace na tashi ankira sallah, sanann ta tafi ɗakinta tashi nayi alwalah nayi sallah da azkar na koma na kwanta sai karfe takwas na tashi nayi wanka na shirya na fito parlour ba kowa a parlourn haka yasa na zauna na kunna kallo dan bansan mai zanyi ba tunda komai na gidan a gyare yake, ban daɗe da zama ba ta shigo taci kwanliya tasa ƙananan kaya matsatso abun dai ba kyaun gani dan duk rabin nononta a waje yake, murmushi tayi man tana zama a kusa dani tace. "Barka da hutawa bakuwa ta." ɗukar da kaina ƙasa nayi nace mata. "Ina kwana Aunty."? Tashi tayi tana cewa."lafiya fatan kin tashi lafiya."? Cewa nayi "lafiya lau" na cigaba da kallona, ita kuma kitchen ta shiga ta dumamana kaza sai flask din ruwan zafi da madara haka muka ci muka koshi sannan na kwanshe kayan na maida kitchen na dawo na zauna, kallona tayi sanann tace. " Yan mata ya sunanki." ce mata nayi. "Khadija." murmushi tayi dan na lura ita mace ce mai yawan murmushi ce man tayi "suna mai dadi, to ni sunan Asiya." murmushi kawai nayi na cigaba da kallona ji nayi tace. "Khady mai ya kawo ki garin Hirji? Ko mamanki ya aikoki wani gida baki gane shi ba." girgiza kai nayi, sannan na share hawayen da suka zuboman nace "Aa kawai nadawo nan ne da zama." ji nayi ta rungumo ni jikinta tana lailashi sannan tace. "Karki damu nima haka naji llokacin da baro gidanmu, amman daga baya kuma sai na dadashe gashi har na yi dukiya, na manta da kowa nawa ina rayuwata yanda nike so, shin ban burgeki ba Khady."? Murmushi nayi na fidda jikina daga jikinta nace "kin burgeni mana."abun mamaki ƙara matsowa tayi a jikina tana cewa. "Kina da kyau kuma kina da abunda akeso a jikinki, amman kinsan mai."?


"Aa" nace mata kawai, dariya tayi sannan tace. "Bakiyi kama da wanda zaki sakarma namiji jiki yana mora sannan ya baki yan-kuɗaɗe wanda bazasu isheki ba, kin ganni nan tunda na fito duniya ban taɓa haɗa kwanciya da wani ƙato ba sai dai mace yar'uwata duk wannan kudin danayi ta haka na samaisu, idan zaki iya sai na koya maki kafin na fara haɗaki da manyan mata yanda zakiyi kudi kema." shiru nayi bance komai ba, ji nayi hannunta na yawo a cikin bireziya ta, da sauri na ɗago kai na kalleta sai naga ta ƙasheman ido tace. "Ki daba kai kawai Khadija zakiji dadi sannan kuma zakiyi kudi sosai. "Ɗaga mata kai kawai nayi sannan nace "ni bansan nayi kudi, sanann bansan ki haɗani da kowa ki barni kawai ina yi maki aiki ni haka ma ya isheni, amman banda niyar sake wani sabon Allah na samu na roki Allah ya yafeman wanda nayi a baya, Auntyna dan Allah karki bani gudumuwa wajen ida lalacewar rayuwata ki tausayaman wallahi zanyi maki aiki ko wani iri idan har na wahala ne."


Murmushi tayi sannan tace. "Ba zan matsa maki ba Khadija, nayi alkwarin ba zan matsama wata ba akan ta shiga harka, kuma ba zan hanaki zama gidana ba, kuma ba aikin da zani baki Khadija zan zauna dake ne da gaskiya da amana amman da sheraɗi ɗaya." cikin sauri nace. "Auntyna wane sheraɗi ne."? Murmushi tayi sannan tace. "Sharaɗin shine zaki ringa bani nononki ina sha duk randa na gadama idan har kikayi man haka shikenan zaki zauna dani kuma daga nononki ba abunda zai taɓa a jikinki nononki sune a matsayin fansar zaman dakike a gidana."


Kuka na fashe dashi ina cewa. "Inalillahi wa'inna'alaihijirun, wayyo Allah na na shiga uku na lalace, dan Allah ki rufaman asiri ki sake man wani aiki wallahi bani iya aikata wannan babban zunibin, wallahi ko namiji ban iya bashi nonona yasha idan ba mahamramina ba, dako nayi haka na bada nonona ansha da sunan soyayya amman banda yanzun dan nayi nadama, nadama kuma ta har abada dan Allah kiyi hakuri." Asiya mace ce mai saukin kai da kuma tausayi yanda taga ina kuka sai na bata tausayi sosai tasowa tayi ta hada bakinmu waje ɗaya ai bansan sanda nayi shiru ba, cirewa tayi sanann tace. "Kiyi hakuri nayi maki hakane dan kiyi shiru muyi magana Khadija, tabbas haduwa take ya tuno man da abubuwa da yawa a rayuwa ta, nima haka nayi lokacin da akayi man tayin maɗigo amman ni na faɗa hannun muguwa da tsiya sai da ta wulakanta man rayuwa har na zama yar'hannu amman ni ba zan ɓata maki rayuwa ba, ko zaki iya gaya man abunda ya baro da ke gida Khadija."? Share hawaye na nayi sanann nace. "Nagode Auntyna, insha Allah zani gaya maki idan har zaki kyaleni na zauna ina yi maki aiki." murmushi tayi sannan tace. "Wallahi ba aikin zakiyi man, zan zauna dake a matsayin yar'uwata" cewa nayi to. "Zan gaya maki labarina....

*kiyi share saboda da Allah ba dan ni ba, idan kina cikin group uku kiyi kokari ki tura masu dan su amfana yar'uwa nima inayi makune dan mu amfana nagode.*

```Need ur prayer, am know feeling better, yau ma dakyal na samu nayi maku sai randa kukaji ni kuma```

👇👇👇👇👇👇👇

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃


*Matso kiji ƴar uwa* 👂👂


*Shahararriyar marubuciyar nan wadda tayi ƙaurin suna gurin kasheku da dadaɗaɗan litttatafanta wato Aisha Umar Ibrahim (Real eeshow ) yauma gata tazo muku da wani shahararen book ɗinta wanda ta daɗe tana tanada muku shi cikin farashi mafi sauki wato 200 kacal.*


*Ga sunan book ɗin kamar haka*
👇

🌻 *BAR RAINA ALLURA*
*( Itama ƙarfe ce)*


*Domin neman ƙarin bayani kan wannan book zaku iya tuntuɓar mu a kan lambobinmu kamar haka* 👇
*08108362334 or 08135361133*


*Ƴar uwa karki bari a baki labari domin wannan salon na dabanne kamar yadda marubuciyar take ta daban.*😍😍😍😍


*karki bari kiyi missing ɗin wannan book ɗin hajiya.*



Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t
*ga link nan ku shiga amman ki tabbatar da zakiyi comment, fan's two ne, fans one ya cika kuma naga kuna man magana akan na saku a group ga shi nan na bude maku wani amman comment dole*

*Wannan page din nakine Dejja musy, ina maki barka da dawowa online, kuma naga comment dinki ina gdy sosai dan comment din ya sani nishaɗi sosai💃, Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Phatermarh kankia , my Temarh, ina maki fatan alkhairy ta wajena*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 13⏩14


Tunda su Yaya suka tafi Mama ta tashi tayi kalaci sannan tayi wanka ta zauna, duk da abun duniya ya isheta amman hakan bai hana Mama yi man addua ba,tana zaune Yaro yayi sallama yace. "Wai Aminu yace yana son magana da Khadija." shiru Mama tayi tana kallon Yaron da Aminu ya aiko sannan tace. "Maza kaje kace mashi ya shigo daga cikin gida." tafiya yaron yayi yana cewa. "To shikenan." bayan ya fita compound din gidanmu ya tadda Aminu jingina a jikin motarshi sannan yace mashi. "Mamanta tace ka shigo daga cikin gida." murmushi Aminu yayi sannan yace. "To shikenan nagode sosai kaji boy." tafiya yaron yayi yana murna, haka Aminu ya shigo har parlour sannan ya zauna ya gaida Mama, ansawa Mama tayi sannan tace. "Aminu ya ka baro gida da kuma mutanen gida."? Cikin jin kunya yace. "Duk suna lafiya Mama, kuma suna gaisheku." murmushi Mama tayi duk da tana cikin damuwa amman tayi kokarin boye ta tace. "Allah sarki ina ansawa, Aminu sai dai kayi hakuri dakai ni mu baki ɗaya, amman Am... "Mama dan Allah karkice ba zaki auran man Khadija ba dan wannan kaddarar ta hau kanta, wallahi ina sonta a haka mudun ba Khadija ba ba zan iya auren ko wace mace ba, na roƙeki karki yi man haka."ya ida maganar yana hawaye, itama Mama hawayen take dan tasan nayi rashin masoyin gaskiya, girgiza kai Mama tayi tana murmushi mai ciwo sanann tace. "Da ina hali da gobe zan sa a daura maka aure da Khadija da na yi imani da kana kaunarta sai dai bani da yanda zanyi dan Khadija ta haɗa kayanta ta gudu ta barmu dan kawai nace zan ɗaura mata Alhaji Salahu." tashi yayi tsaya yana cewa. "Inalillahi wa'inna'alaihijirun, Allahunma'ajirni fi'masifati wa'akirni khari manha(note:-Idan kunga mistake wajen rubuta Addu'a ba laifina bane bani da zaɓi ne dan ba komai na iya rubutawa da hausa ba, dan hausa tana da wahala sosai😢, sai kuyi man uzuri my dear's fan's 🥰) hawaye yake sosai sannan yace. "Mama tunda kin yarda da zaki aura man Khadija nayi maki alkwarin zan nemota duk inda ta shiga a faɗin duniyar nan, dan itace rayuwa ta, Allah ya jarabeni da ciwon sonta dan Allah Mama karkice banda kunya ina faɗin haka a gabanki bason ya zanyi control din son Khadija bane, ni zan tafi neman Khadija Mama." tashi Mama tayi da sauri ta rike hannun rigar Aminu tana hawaye tace. "Aa Aminu ban yarda kaje neman Khadija ba, dan ko kaje ba ganinta zakayi ba kuma Jamilu ya bada cigiyar ta, kaje ka zauna gida idan ta dawo zan gaya maka, idan kuma ba'a ganta ba sai kayi hakuri sannan kayi Addu'a Allah ya baka wanda tafi Khadija." kuka Aminu ya tashe dashi sannan yace. "Mama nine ya dace da nemo Khadija duk inda ta shiga a

Please Login or Register in order to submit comment