Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so daku shine kuyi comment sosai hakan zai bani kwarin giwwar baku shi cikin sati insha Allah*


_Godiya ta musamman zuwa ga_
*Zauren Yar'mutan kankia fan's group*
*Real jameey novel fans 1&2*
*Sansanin Yar'mutan kankia*
*Zee-abu hausa novel*
*Ban raina allura ba fan's*
*zauren manazarta fans*
_Da dai sauransu duk ina maka godiya ta gareku_


*oyoyoyo! Ina maki murnar dawowa duniyar yanar gizo social media kenan, kawata aminiyata wato FJ marubuciyar BAGIJJA, Allah yasa kin dawo sa'a kuma a cigaba da suburbudo mana zafafan novel mana shan karatu❣️*


*Wanann page din naki ne Real eeshow marubuciyar BAN RAINA ALLURA BA! ITAMA KARFE CE kiyi yanda kike so dashi🤗*



Page 1⏩2


Wata macece wanda bata wuce shekara 50 ba zaune a madaidacin parlourn gidansu ba abunda taje sai aikin kuka dan abun duniya ya taro yayi mata yawa, wata yarinya ce ta fito daga cikin wani daki ta zauna kasa kusa da kafar matar itama kukan take, dan ta rasa mai zata ce ma mahaifiyar tata kallonta tayi sanann tace.


"Mama Dan Allah kiyi hakuri ki yafeman wallahi ba zan sake ba, nayi maki wannan alkwarin, wallahi sherin she... Tas! Mama ta wanke ta mari tana nuna ta da yatsa cikin fushi ta fara cewa. "Allah ya tsine maki albarki insha Allah ba zaki gama da duniya lahira ba Khadija, tunda har kika sa na zubda hawaye saboda dake kika jaman zagi a cikin unguwa, Allah ya i... Da sauri Khadija ta rike kafafun Maman tata, tana girgiza mata kai tana hawaye masu ciwo dan kukan ma ya gagareta dan tana cikin tashin hankali ba kadan ba, yanda Maman tata take tsine mata tana mata fatan masifa ta fada mata bayan kuma itace uwa gareta mahaifiya, cikin tashin hankali tace. "Mama dan Allah ki barni haka karda abun yayi man yawa kin tsine man sannan kuma zakiyi man Allah ya isa, nasan ko baki ce man Allah ya isa ba ni tawa rayuwar tazo karshe tunda har ta dalilina kika zubda hawaye, Dan Allah Mama ki yafeman wallahi ba zan sake ba, kiyiman Uzuri Ma... Katse ta Mama ta sake yi ta hana Khadija magana, wurga mata hararar tsana tayi sannan tace. "Wallahi Khadija na tsaneki bani sonki a yanzun bani kaunar ganinki, ke har wani uzuri zan maki Khadija? Bayan cikin shegene a jikinkinki duk tarbiyar da ba baki, abu daya nike so ki sani bani bake har abada, karki sake kirana da sunan Mama ta na yafeki daga cikin ƴa'ƴana, ki kirani da suna HAFSAT dan yanzun ni ba mahaifiyar ki bace, Allah ya tseni maki albarka."


Allah Sarki kuka na sake rushewa dashi dan duniya tayi man kunci bansan ya zanyi da rayuwa ta ba, sannan kuma na tsorata da yanayin da mahaifiya ta take ciki, tashi nayi na koma dakina na cigaba da kukana, wanda tunda jiya mukaje asibiti likita ya sheda mana ina dauki da karamin ciki dan wata wata nake aikin kuka, ba kukan komai nike ba Ila kukan dana sani da biye ma son zuciyata, yunwa naji ta taso man Kuma bani sha'awar cin komai sai dan'wanke da manja da yaji wanda yaji tabarnuwa da kayan kamshi na yaji, tashi nayi na fito parlour tadda Mama nayi zaune tana share hawaye matsawa nayi kusa da ita nace. "Mama yunwa nike ji Kuma dan'wake nike son nace." Ji nayi Mama ta wanke ni da mari cikin zafin rai tace. "Wallahi baki da kwanon abinci a gidan nan, kije wanda wanda yayi maki cikin ki gaya mashi abunda kike son ci, sannan Kuma karki sake kirana da sunan mama na gaya maki tsinanniya lalataiciya dake."

Kasa motsi nayi, ba abunda nike sai hawaye dan ni yanzun na kasa kuka ma, ji nike daman nike kukan da Mama take da naji saukin abunda nike ji a raina, hakuri na sake bata sannan na tashi na koma dakina inajin yanda yunwa take azabzabata na rasa yanda zanyi gashi bani son cin komai idan ba dan'wake ba, haka na wuni a daki a ranar banda sake fitowa waje ba, balle har Mama ta ganni ta sake tsineman, tun karfe 1 nike zaune inajin yunwa har karfe hudun marece yayi, tunowa nayi inada wasu kudi da Nura ya bani tunin dadewa, cikin sauri na tashi na dauko kudin na zura hijab dina dan zuwa nema ma ciki abunda zan sama shi, ina fitowa na tadda Mama da Yaya Aisha sun hada kai suna kuka, Yaya Aisha Yayata ce wanda muke uwa daya uba daya, da yake nice Auta a gidanmu yanda na gansu ne hankali ya tashi dan nasan kukan da suke tsaye nayi ina kallonsu nima a zubda hawaye, kallona sukayi lokaci guda suna man wani irin kallo wannan kallo ba komai bane illa kallon tsana dan Ina ganin tsantsan tsana a cikin kwayar idonsu, ta sowa Yaya Aisha tayi ta nufoni gadan gadan ni Kuma ina ja da baya haka muka kamayi har muka kai karshen bango, kulle idona nayi dan nasan ba dadi zatayi man ba, kamani tayi ta fara wanka man mari tana zagina, nan suka rufeni da bugu ita da Mama, tun ina yi basu hakuri har nazo da na kasa sai dai ido, tun ina gane idan nike har ta kai da bani gane mai akeyi, haka suka kama buguna suka barni kwance sheɗashaɗa cikin jini rai hannu ga Allah, ba su damu da wani hali nike ciki ba, tun la'asar sukayi man haka suka yashar dani suka cigaba da hidimar gabansu, Yayane ya shigo Jamilu shine yana da matarshi kuma shine babba a gidanmu, yana shigowa ya taddani cikin wanann halin kallon Mama yayi sannan yace.


"Mama mai yasamu Auta na ganta kwance cikin jini kuma hankalinku kwance harda ke Aisha."?

Cikin fushi yayi tambayar dan yasan abunda ke faruwa dani likitin da yaga mana ina da ciki shi ya kirashi waya ya gaya mashi halin da ake ciki da yake abokinshi ne, kallon shi Mama tayi sannan tace. "Jamilu Khadija cikin shege tayi gaya maka ne banyi ba, dan na fiddata daga cikin jerin ƴa'ƴana, baku ba Khadija kuma kabarta ta mutu, idan taso nima akashe ba damuwa ta bane."


Kallonta yayi ya fara cewa. "Haba Mama ya kamata ki yarda da kaddara mai kyau da marar kyau shine cikon imani, kisani wannan cikin yana cikin zanar kaddarar Auta dole sai tayi wannan cikin wallahi kaddararta ne, banyi tunanin ganin haka daga gareki ba Mama, kuma ke Ai... Wanke shi Mama tayi da mari tana cewa. "Har ni zaka gaya man kaddara Jamilu, inace nice na haifeka va kaine ka haifi kanka ba, tun kafin ka zama mutun nasan zanar kaddara, balle kace man wata kaddara wallahi Jamilu badan nakai zuciya nesa ba kaima da na tsine maka wallahi mutun banza, ka fita ido na kulle daman ace da ka haifi namiji kwara mace dan ita mace itace tasan kishin uwarta daman ace ciwon ƴ'a mace na ƴ'a mace ne."

Tunda Mama ta mari Yaya Jamilu bai sake cewa komai ba, sai ma zuwa da yayi zai dauke ni ya kaine asibiti domin cito da rayuwata cikin fushi Mama tace. "Mudun ka dauketa sai na tsine maka albarka Jamilu."

Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD

*😂😂😂wai akace soyayar shan minti ake cewa ba soyayyyar minti ba, nidai tom na sake mashi suna🤪*

*Wannan page din nakine Auntyna Binta Umar Abbale ta Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Zainab Abu-Kareem My Zee ina maki fatan alkhairy ta wajena*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 7⏩8


Tunda su Yaya Jamilu suka shiga gida suka tadda Mama bata dawo ba, zaunawa sukayi zaman jiran ta kowa ya shiru da abunda yake sakawa a zuciyarshi.

Ita ko Mama tana zuwa ta tadda Alhaji Salahu bayan sun zauna ta fara magana tana cewa. "Daman Alhaji zuwa nayi ka rufaman asiri kamar yanda Allah ya rufa maka." cikin kuka Mama take maganar dan ita gani take idan ba aure tayi man ba to hankalin ta ba kwanciya zaiyi ba, kallon Mama yayi sannan yace. "Hajiya Hafsat mai yafaru lafiya kike kuka? Dan Allah kiyi shiru ki gaya man abunda ya kawoki a wajena." ce mashi Mama tayi. "Daman Alhaji dan Allah so nike ka auri Khadija idan kana so, dan Allah karkace aa ka rufaman asiri kamar yanda Allah ya rufa maka."

Cikin murmushi da jindadi Alhaji Salahu yace. "Haba Hajiya daman abunda kika zo kice man kenan harda kuka? Ai ba wani abu bane daman na jima da son Khadija a cikin zuciya ta gayawane kawai banyi ba amman ko maiyasa kike son aura man ita." cikin farinciki da sakin fuska yayi maganar dan shi gode ma Allah yake cikin zuciyar shi, cikin tsoro Mama ta fara maganar. "Alhaji ba zan boye maka komai ba tunda kaine wanda zata aura, Khadija dai ciki tayi amman a halin yanzun cikin ya zube tana asibiti so nike tana dawowa ta ida samun sauki sai ayi bikin naku ko lefe karda ka kawo sadaki kawai zaka kawo dubu 20."


Washe kazamin bakin shi yayi sannan yace. "Idan wanann ne ai ba damuwa, shikenan amman ina son a daura auren nan da sati biyu masu zuwa Hajiya." cikin jindadi Mama tace. "Insha Allah, Alhaji nagode sosai Allah ya ƙara girma da buɗe, yanda karufa mana asiri kaima Allah ya rufa maka." washe baki kawai yake haka ya rako Mama har kofar gida yana ce mata sai ya shigo ganina idan muka dawo daga asibiti dan shi baya son zuwa asibiti da can ma yaje ya fara duba lafiya ta, ita ko Mama sai dadi takeji gani take ta gama yi man gata ta samaman wanda zan aura ya rufa man asiri a cewarta.


Koda taga motar Yaya Jamilu da ta Yaya Fatima a kofar gida tasan suna cikin gida shiyasa ta chanza fuska ta dauki mataki tun a waje dan tace ba wanda ya isa ya hanata aura mani Alhaji Salahu koda dangin mahaifinane dan basu tsinata mata tsiyar komai ba lokacin da Babana ya rasu dan haka basu da iko a kanmu daman tasha cewa haka shiyasa ba wani zuminci muke da dangin Baba ba saboda rashin jituwa dake tsakaninsu da Mama.


Koda ta shigo samun waje tayi ta zauna ta kama kallonsu daya bayan daya sannan tace. "Jamilu ya jikin Auta fatan dai komai yana tafiya dai dai."? Kallonta yayi sannan yace"lafiya lau Mama, amman muna son muyi wata magana dake dan Allah Mama." duk da tasan maganar da zasuyi mata dan tasan Yaya Amina ta gaya masu yanda sukayi da ita, amman sai ta wayance tace masu. "Ina sauraranka Jamilu wani abu ke faruwa ne? Duk na ganku kamar ba lafiya kodai wani abu ke faruwa da Auta ne."? Girgiza mata kai Yaya Jamilu yayi yana hawaye, saukowa yayi ya durkusa kasa ya kama kafafunta yana hawaye yace. "Dan girman Allah Mama, ki duba maraicinmu bamu da kowa sai ke, ke daya ce muke gani muji dadi nida yan'uwana mahaifinmu ya rasu, dan Allah Mama munzo neman alfarma a wajenki dan Allah karda kice ba zaki yi mana wannan alfarma ba Mama."ya ida maganar yana kuka dan Mama tasha gaban shi sosai tunda itace mahaifiyarmu dole ya bita a sannu dan ya shawo kan matsalar a sannu da dai ace ba Mama bace wata ce daban to da karfin tsiya sai ya anso man hakina amman yanzun dole su bi a hankali su shawo kan Mama ta fasa auraman Alhaji Salahu .


Kallonshi Mama tayi tana shafa mashi kai alamun lailashi yana daina kuka, sannan tace. "Jamilu inajinka wata alfarma ce wannan zaku tambayeni harka kai kuka suma kuka, karku tadda man hankali mana gaya man ina sauraran ka idan baka iya gayaman sai ke Bintu ke gaya man." shiru Yaya Jamilu yayi sannan yace. "Mama dan Allah karda ki aura ma Auta wannan tsohon mutumin, Mama karkizo daga baya kina cizon yatsa kina da nasani, Mama dan Allah karki ɓata rayuwar Auta da kanki wannan auren da kike niyar yi mata wallahi shine babban kuskuren da zaki aika a rayuwarki sanna... Cikin fushi Mama ta katse Yaya Jamilu tana cewa. "Yi man shiru Jamilu wallahi ko yanzun nayi maka baki, har ka isa kace zan tabka babban kuskure dan zanyi ma Khadija Aura, Auren shine kuskure ko kuma cikin da tayi ta hanyar zina bai zama kuskure ba sai Aurar da ita zai zama kuskure? Dan ubanka gaya man wa zai iya aurenka bayan ta bayar da budurcinta bisa titi? Gatan da zan mata shi ne zai zama kuskure Jamilu? Anya Jamilu kana neman albarka ubangiji Allah kuwa? Ace ni Uwarka mahaifiya zaka sa gaba kana gaya mata magana son ranka kana gaya mata abunda duk yazo bakin ka sai kace kaine ubana."? Kuka Mama ta fashe dashi tana cewa."tabbas haka maganar take da akace baiwa zata haifi uwargiyarta yau ga abun yazo kaina, kunan duk kun haɗaman kai baku yarda na aura ma Khadija Salahu ba ko? To ku sani nan da sati biyu za'a daura masu aure akan sadaki naira dubu 20 kuma ko lefe bance ya kawo ba, sai dai ku mutu idan kun tashi. "


Cikin kuka Yaya Fatima tace. "Wallahi Mama karki ce muna maki rashin kunya amman dole mu gayamaki gaskiya a matsayinki na mahaifiyarmu wallahi Mama mudun kika ce zaki aura ma Khadija wannan tsohon banzan to kin ɓata mata future kuma daga baya sai kindawo kina da nasani marar amfani Mama, ya kamata ki duba wannan maganar tamu idan auran kike so yi mata a bari ta dawo sai ta fidda wanda take so cikin samarinta na tabbata cikin akwai nagari mai sonta tsakani ga Allah, wanda zai aureta koda ko ta haifi cikin da tayi balle ma yanzun da ba cikin a jikinta ya dace kiyi tunani Mama ki duba gaba Mama ba'a duba baya idan ta wuce mun roƙeki wannan alfarmar Mama."



Shiru Mama tayi tana kallon Yaya Fatima yanda ta gaya mata magana har haka, dan a lokacin Mama tayi nisa batajin kira ta dauki abun da zafi ta kasa daukar kaddarar da tazo mana, komai zasu gaya mata gani take rashin kunya suke mata a matsayinta na mahaifiya a garesu, kallonsu tayi su dukansu sannan tace. "Na lura dukanku bakinku daya harda ke Aisha da nike ganin zaki bani hadin kai wajen sama ma yar'uwarki rayuwa mai inganci, amman sai naga akashin haka sun hure maki kunne ko."? Girgiza kai Yaya Aisha tayi tana kuka tace. "Mama ba haka bane gaskiya ne su Yaya Fatima suka fimu, wallahi Mama ni tun yanzun na fara da nasanin abunda nayi ma Auta, Allah ya ganar dani kema Mama ya kamata kiyi imani da kaddara Mama kefa ke cema mu ringa kai zuciyar mu nisa idan zamuyi ma yaranmu hukunci, amman Mama maiyasa ke a wannan karan kika kasa kai zuciyarki nisa wajen yi man Auta hukunci? Hukuncin da kika yanke yayi mata tauri da yawa nasan ba zata iya daukarshi ba." tunda Yaya Aisha tayi wannan magana Mama ta sake fasala cikin fushi tace. "To ku sani wallahi duk garin katsina ba wanda ya isa ya hanani aura ma Khadija Salahu koda hukuma ce kuwa, kuma wallahi duk wanda ta sake zuwa da sunan yi man magana akan karda na aura ma Khadija Salahu to wallahi sai na tsine mata albarka ko waye a cikin ku, dan haka ku tashi ku bani waje marar zuciya wanda basu kishin uwarsu."

Haka suka fita ba wanda ya sake cewa komai, gidan Yaya Jamilu suka ce danyi magana dan basu son suyi magana a asibiti gudun karda naji abunda ke faruwa na tada hankalina har yakai da na samu wani ciwon na daban.


Zama sukayi a parlourn Yaya Jamilu sannan Yaya Amina tace. "Yaya mai zai hana muje mu gaya ma Baba Ali ba wata ƙila idan shi yayi mata magana zataji ta fasa wannan jagulalan auren."? Shiru Yaya yayi yana tunanin mafita cewa yayi. "Amina kinsan dai ko yaje ba wani ji zatayi ba, karshe ma suyi fada kinga ba dadi dan Mama na lura tayi nisa cikin wannan lamarin ta daukeshi da zafi bayan kaddarar Auta ne a haka bata isa ta tsalake kaddarar taba haka ta zano tata kaddarar kowa da yanda ya zano nashi kaddarar, amman Mama ta kasa gane hakan." cewa Yaya Fatima tayi. "Hakane Yaya amman maganar Amina abun dubawa ce idan bashi muka kaima kukan mu ba wa zamu kaimawa dan ba kotu zamu kai mahaifiyarmu ba, dole dai hakan zamuyi Yaya." shiru Yaya yayi sannan yace. "Haka maganarki take Fatima, amman ku tashi ku tafi gidajenku mangariba na matsawa ni kuma zani wuce asibiti na kara ganin lafiyar Auta na kai masu abincin dare komai kenan gobe sai mu tafi gidan Baba Ali din muji yanda za'ayi." ba dan sunso ba suka tafi gida shi kuma Yaya asibiti ya wuce ya kawo mana abinci da kanshi ya zuba abincin ya matso kusa dani ya zauna ya fara bani abincin da kanshi da naso na ƙici amman sai na daure naci yana gama bani ya bani magani nasha sannan yace. "Auta dan Allah kiyi hakuri kisama dangana a ranki ki yarda da kaddara haka taki kaddarar take Auta kuma mu yaiyanki mun yarda da kaddara kuma mun ansheta hannu biyu wallahi Auta muna tare dake nidai fatana ki fidda komai a ranki ki cigaba da rayuwarki yanda kikeyi a da, sai dai kiji tsoron Allah kinga izinar da hau kanki sai ki kiyaye kinji Auta."?


Cikin jindadi nace ma Yaya. "Insha Allah Yaya nagode sosai da kulawarka amman Yaya wai da gaske bani sake haihuwa."!? Na karasa maganar ina zubda hawaye, sha fa kaina Yaya yayi sannan yace. "Aa Auta ba'a fidda rai ga rahamar Allah, kuma shi Dikko baida tabbacin baki sake haihuwa saboda ba wanda yasan ikon Allah dan Allah Auta karkisa wannan a ranki kinji? Komai yayi farko yana da karshe." tunda yayi man maganar hankalina sai ya kwanta nan mukai ta labari dashi sai da kai isha'i sannan yace shi zai tafi gida sai gobe zai dawo haka ya tafi ya barni hankali kwance muma labari muka sha da Dija sannan muka kanta.

Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD
*Ga link nan ku shiga, kuma ku tabbatar zakuyi comment idan kun shigo dan gaskiya na daina yin posting a kowane group inba group dina ba zuwa wasu mararsa yawa dan haka duk mai son karanta a sanadin soyayyar minti kan lokaci cikin sauki ya shiga ga link nan, sannan kuma comment dole kuma kiyi dan Allah*

*magana ta biyu naji ana cewa zan maida soyayyar minti na kudi🤔, to ba haka bane soyayyar minti a kyauta nayi niyar baku shi, comment dinku shine bayanku idan kuma kuka daina comment kamar yanda kuke, to ba na kudi zai koma ba sai na na ajiye rubutun kunga sai mu hutu mu dukanmu ko🤗*

*Wannan page din nakine Hajiya Ruƙayya Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Fadeelah marubuciyar Rayuwar Husna, my Fadellah ina maki fatan alkhairy ta wajena*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 11⏩12


Tafiya mai naped yake amman ni ba abunda nike idan ba kuka ba, sai zuciyata ta bani ko naje gidan Yaya Amina sai kuma naga kamar Mama taje ta dauko ni ta daura man aure da Salahu haka na kama saƙesaƙe ina hawaye dan ni yanzun so nike na kurma ihu na kama kuka ko naji saukin abunda nike ji a zuciya ta, amman ba halin yin haka haka muka shiga kofar guga har cikin tashar jibia sannan ya saukeni na bashi kudinshi ya bani chanjin, aiko nan aka fara zuwa aka anshi kayana akasa cikin boot din mota sannan na shiga, ɗari uku na bada kudin mota ba wani daɗewa nayi ba motar ta cika mu tashi zuwa garin jibia, tafiya mukayi mai dan nisa sannan muka iso magamar jibia nan nace zan sauka aiko aka saukeni na dauki kayana, a cikin wani novel na taɓa karanta sunan gari mai sunan HIRJI daga magama ake yanke hanya ake shiga cikin garin Hirji .


Garin Hirji gari na karuwar duk wata karuwa maiji da kanta ita karuwa ce to a garin Hirji take zaune, nima garin Hirji na nufa dan ban iya zama naga Mama tayi man auren dole kwara naje hirji nima na zama karuwa nayi zaman kaina ba kwalkwasin wani ba.
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD


*Wannan page din nakine Ɓingel Allah ya kara daukaka da girma gami da lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Yar'malam My Yar' Malam ina maki fatan alkhairy ta wajena*


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 9⏩10


Washe gari da safe Yaya Aisha ce ta fara zuwa asibiti ita da mijinta da yake ita bata da mota sai tare suka shigo dan ta gaya mashi komai ya faru dani ina zaune muna labari nida Dija sama sama sai gasu sun shigo suna shigowa muka gaidasu sannan suka zauna wa'azi mijin Yaya Aisha yayi man sosai sannan ya tafi yace zuwa mangariba zai dawo ya wuce da ita gida, rakashi tayi sannan ta dawo tace. "Auta ya jikin naki."? Da yake haushinta nikeji bugun da tayi man, dan komai ya faru dani a yanzun gani nike itace silar komai shiyasa bance mata komai ba na kauda kaina gefe, samun waje tayi ta zauna sannan tace. "Khadija nasan kina kullace dani akan abunda nayi maki amman ki sani a lokacin hankali ya gushe shiyasa na biye ma Mama mukayi maki haka, dan Allah Khadija kiyi hakuri ki yafeman ko naji saukin abunda nikeji a zuciyata mudun baki yafe man ba wallahi Khadija ba zan sake farinciki ba, dan Allah Auta ki yafeman."hawaye take yi tana maganar, kinsan ace yar'wa rabin jiki ba'a shiga tsakanin yan'uwa take nace na yafe mata har abada kuma ya wuce wajena muna cikin haka Yaya Amina da Yaya Fatima suka shigo lokaci guda suma da breakfast dinsu haka muka gaisa sukayi man ya jiki sannan suka saman abincin naci suna ban labarin ban dariya har na koshi nasha Magani, waya suka kira Yaya sukace kar yazo da abincin rana sunzo dashi, likita yazo yayi man allura yace masu zuwa anjima zai sallamaini dan yaga jikin da sauki sosai sannan sai sun kara kula da lafiya ta sosai sannan ya fita, bayan Yaya yazo ya sake dubani sannan yace masu su taso su tafi nan suka ce man zasuje su dawo kafin anjimar sannan suka tafi.


a asibiti suka bar motar Yaya Amina suka tafi da mota biyu, gidan Baba Ali suka nufa da yake a kwaɗo katsina bayan sunyi parking suka shiga suka fara gaisawa da matanshi sannan suka shiga parlourn shi samun waje sukayi suka zauna sannan suka fara gaidashi bayan sun gaidashi shiru ne ya biyo baya sannan Yaya Jamilu ya fara magana.


"Baba daman munzo ne mu gaya maka wata magana." kallonshi Baba yayi sannan yace. "Jamilu maike tafe daku Ku dukanku? lafiya kuwa dan naga kamar baku cikin natsuwarku."? Yaya ne yace. "Ba lafiya Baba, daman munzo mu gaya maka Mama ce tace zatayi ma Auta Aure kuma wai Alhaji Salahu zata aura mata." cikin zafin nama Baba Ali yace. "Wai ni maike damun Hafsat ne dan Allah dan Annabi? Ita Mamana rasa masoya tayi shiyasa zata hadata da sa'ar haihuwata ko ta isheta ne."? Girgiza kai Yaya yayi sannan yace. "Aa Baba kaddara ce ta hau kan Auta, ciki tayi amman ya zube yanzun haka tana asibiti, to dan tayi ciki shine tace zata aura mata shi wai dan ya rufa mata asiri ba yanda bamuyi da ita ba amman sai tace idan muka sake yi mata maganar sai ta tsine mana albarka." cewa Baba

Please Login or Register in order to submit comment