Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Y'a tace kawai tayi,kuma hakan bazata sake faruwa ba,amma ba'a kama uwata da makocinsu ba a daki ina"
"Ke dan kutumar ubanki mairo mutsaya iyah kan gidannan banda sako gidan kowa,dan wallhi inta hakane kowa bazai ji dadi ba in toza'afara'za'afara"
"Hehe dama in baki yasan mai zaice bai san mai za'a mayar masaba,kan me uwa da wabi duk uban abinda za'a fada a fada ba tsoro nakeba,abin kunyane kowa gaba yabashi anan wajen ba baya ba,dan babu wanda abin kunya bai lullubeshi ba anan wajen,dan haka kawai ayi sha'ani wai na birni ya cuci na kauye".
Ganin abin zai bacine yasa inna karima korar kowa daga dakinnata ,kowa yayi hanyar kofarsa yana maida nasa zancen.
A wajen su sameemah kuwa lokacin da suka dawo daga gidan alhaji Sama'ila har sunyi hanyar gidan kungiyar tasu,ta bada umarnin a nufi hanyar gidan karagiya inda aka kai labiru dazu da safe,mashin din suka k'uza suna sakin hayaki a duk layin dasuka wuce kafin suka yanka cikin gari inda zai kaisu inda yake.
A zaune suka sameshi yana rarraba ido fuskarsa ta kumbura suntum saboda dukan dayasha,mamakine kwance akan fuskarsa daya ga sameemah a wajen,
"Yayah labiru kayi Mamakin ganina ne,nice dai y'ar kanwar taka"
"Amma mai kike a wajennan,ko dagskene da ake cewa kece shugabar yan dabar garinnan?"
"Kwarai kuwa gashi ka tabbatar da kanka,kafin mukai ga nan,ajiye wannan wasan a gefe muyi abinda yatara mu,miyasa ka aikata abinda nake zarginka dashi"
"Makike zargina dashi iyee,kaika jimin yarinyar nan"
Murtuke fuska sameemah tayi kaman ba itace take dariya yanzu ba,wani irin wawan mari ta sauke masa akan fuskar sa saida dungura jini yana fita ta hancinsa,komawa yayi ya gyara zamansa da Mamakin irin naushin daya fito daga hannun nata kamar wani babban majiyin karfine ya dakeshi,
"Yanzu zaka bani amsa koh kuwa,mai ka aikatawa karamar yarinya dazu da safe?"
Karkarwa jikinsa yafara yana rarraba ido ganin abun dagaske ne ba wasaba,
"Iyyeee na'am wai nnnni .........din"
"Oh tambaya kake,kai burgu ku dan taba lafiyarsa na dan minti talatin da alama bayason lafiyar tasa"
"Ahah su tsaya,kiyi hakuri wayyo,dama kullum tana wajena,ina yin hakuri shine har jiya nakasa toh yau dana ganta shine,na saya mata shayi da biredi bayan ta shanye najata shagon ilu dama bai bude ba,na biya bukata ta,shine kawai"
"Mesunan abinda ka aikata kenan?"
Saida yayi dan shiru ganin zata sake zabga masa wani marin yasashi saurin cewa,
"Fyade,fyade sunansa"
"Kowa yaji laifinsa ko baijiba?"
"Eh munji shugaba"
Suka amsa dukkansu a tare,
"Kai arnen dawa dakkomun abinda nasaka kamin dazu nasan yanzu yayi yanda nakeso,cikin sauri kuwa yabar wajen ,bai dade ba sai gashi da wani kwano abinda yake cikinsa yana turiri,
"Kai burgu kucire masa wando yanzunnan"
Aikuwa kaman jira suke cikin kankanin lokaci suka sutale masa wando,tun baisan mai zai faru ba yafara ihu yana rokonta,
"Shshshsshdh,katsaya da ihun tukunna bari nayi maka wani gargadi,idan ka kuskura nayi maka hukunci kaje gida aka tambayeka mai ya faru ka kira sunana.......,hmmm,saina rabaka gabadaya da abinda kayi amfani ka aikata laifin"
Tun bata gama masa gargadin ba,ta juye soyayyan mangyadan da aka dauko daga wuta akan gaban labirun,cikin kankanin lokaci kuwa fatar wajen tafara sutalewa tun daga kasan cibiyarsa har zuwa rabin cinyoyinsa.
Su kansu yarannata saida suka girgiza da hukuncin da sameemah tah aikata,
"Kuje kujefashi a bayan layin unguwarsu inda yan gidan zasu ganshi,uwarsa saitayi jinyarsa tunda ita ke daure masa kan macijin yake wasa da wutsiyar"
Tabbbnnnnnnn,lallai sameemah!!
Mucigaba dai mutane Nah🤣🤣😂🤣

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤04❤

Ihu yake yana jijjiga kai tun yanayi da karfi har yazamo baya iyacewa komai sai nishi dayake saukewa kaman mai nakuda tazo gargara dan wahala.
Burgune yakalli sameemah wanda har yanzu fuskar sa bata dawo dadai ba da laifin daya ga shugabar tasu ta aikata,
"Amma shugaba wannan hukuncin dakika masa baiyyi tsauri ba kuwa?"
"Toh ka rama masa mana,saina san kaji babu dadi da abinda na yanke,kai wai yaushe kuka fara ma wannan challenge dinnna wa,ne,banason wani iyayi da nuna tausayi na karyar banza a fuskarku,dan tsabar munafurci har kune masu cemin kuna tausayi,da Y'ar gidanku ya farde,ai bansan sanda zakuyi masa aika aika ba saidai naji anakirana a police station naje na fitar da ku,aikin banza kawai inzaku kaishi inda na sakaku ku kaishi in kuma bazaku jeba ku fadamin saina kaishi da kaina"
Sunkuyar dakai sukayi dukkansu suna bata hakuri a tare.
Dalewa tayi kan mashindin burgu saida ta burka yafara kara kafin tace,
"Zanje gida na dawo,ku tabbatar kun shirya shagalin kafin na taho,bayan kun gama cika aikin"
"Bakomai Shugaba bakida matsala"
Fisgar mashin din tayi ta bule kura kafin tayi cikin gari da mungun gudu.
Bayan ta bacewa ganinsune burgu yajuyo yah kalli su arnan dawa tareda cewa,
"Kai dauko buhu musakashi muyi saurin gama aikinnan,dan komawa wajen shagalinnan,kunsan idan harta gama abinda take tariga mu,zuwa toh wallahi bazamuci wannan ganimar ba,nikuwa yanda yawuna yatsinke da wannan gashsshun kajin inban samu na yaga ba akwai matsala"
"Hakane ogah burgu nima tawajennawa haka take yakamata mu hanzarta"
Daukar labiru sukayi wanda yake ta yada kai dan wuya suka zefashi a wani katon buhu,bayan sun dorashi a mashindin arnen dawa suka dau hanya sai anguwar su labirun,wanda sannan yamma tayi,bayan layin ya dauke sawun mutane. Saida suka samu wani rami gefen kwatar gidan kafin suka jefah shi suka tafi.
Parker mash in din tayi a kofar gidan ta shiga tana fed'uwa tareda yin wakar koroso,larai tasamu a tsakar gidan wato matar yayansu manjo wanda yatafi cirani ,wanke hatsin tuwo take a kwaryah,saboda neman magana sai kuwa tace,
"Mutum bashi da aiki sai halayyar maza hakanma a mazan tantirai,allah dai yah shiryah"
Tsayawa sameemah tayi daga shiga dakinnasu na yan mata,kafin ta jiyo ta kalli kulu din,
"Kehh mekikace yanzunnan,kuma Sannan kifadamin dawa kike?"
"Aikin banza Inna fadi da wanda nake ma uwar me za'ayi,karkarinta dai borin koro kunya ko za'a dakeni ne yanda akeyiwa yan dabar iyee"
Jijjiga kai sameemah tayi kafin tayi wani bolll da kwaryar hatsin a kasa.
Ihu larai tafara tana kururuwa tareda durawa sameemah ashar duk wanda yazo cikon bakinta.
"Yar bantan uba ni zaki zubarwa hatsi ko uwarki ceh ta sayamin dazaki zubarmin?"
Shiru ta hadiye wani yawu mukut,ganin yanda sameemah ta saita y'ar wuk'a a makogaranta,
"Kika sake saka uwata a zancenki saina maida y'ay'an ki marayu kuma na maida manjo gwauron karfi da yaji,ki kuma sake ki gani zaki ga ko karya nake ko a'a,banza karya mai bin mazan wasu kawai"
Kwalo ido tasake yi kafin ta ce cikin mamaki ,
"Dama kinsani?,dan allah karki fadawa manjo wallahi yankani zaiyi"
"Banza karamar y'ar iska ashema tsoronsa kike ji,shine ni harkika samu damar shiga harka ta ko?"
"Ahah kiyi hakuri bazan sake ba"
"Kima kara mana kiga aiki da cikawa,mtswww"
Wucewa tayi ta bar kulu tana d'ebe hatsin dake kasa har Sannan jikinta rawa yake saboda kashedin da sameemah tayi mata.
Bakowa a dakin sai salma tana ta danne danne a irin wayar zamaninnan ,daga ganinta kaga irin matan nanne masu ji da kansu duk da cewa kyakykyawace dan inka dauke sameemah duk matan gidan ta fisu kyau,hakanne yasa take harka da manyan alhazan ds yan gidan basayi.
Itah ceh y'ar larai ta fari wato yayar su hanifah,kwanan ta dawo daga bikin kawarta wanda akayi a abuja sune manyan kawaye.
Sameemah koh kallonta batayiba balle ta yimata sallama,kayan jikinta ta cire kafin ta fito daga dakin daga ita sai towel a jikinta.
Fitowartane yayi dadai da shigowar SULEH MAYEH (yayan labiru) gidan abokin manjo wanda tun bayan tafiyar manjo cirani bai daina shigowa ana gaisawa ba.
Lashe baki ya hau yi yana kare jikin sameemah da kallo,dawani gashin bakinsa buzubuzu ga idonnan yasha kwalli dakyar kake ganin kwayarsa dan rinewar idon ,saboda shan sholi.
'Yawwa yau na taki sa'a gaskiya tunda idona yai arba da wannan d'anyar kazar yau,kai rabbana yayi hallitta a wajennan,kaiiii dolema naje nasamu tsohonnan wato baba umaru,na mika yan kudina a bani ke mushiga daga ciki tunda naga ke baka d'ebi romo ka wuce"
Koh kallon inda suleh maye yake bata kallah saima neman ruwa da take wanda zata watsa a jikinta saboda zafin da'ake.
Wani dan yarone yazo wucewa ta kirashi,
"Kai zo nan,jeka kofar uwarka ka d'ebo min ruwa kace injini neh"
Da saurin jikinsa kaman zai kifah da kasa ya karba yayi kofar tasu da gudu dan cika umarnin nata.
Suleh ne yadameta da magana,dan shi a ganinsa tana jinsa,wani shegen kallo ta juya ta watsa masa kafin tace,
"Kai kasan allah duk da nasan ba saninsa kai ba,toh ka tattara yan kafafunka kabani waje,koh kuma yanzu nayi maka wani naushi da saina bajeka anan wajen saidai a zo a daukeka,kaga tsohuwa sai tayi jinyar majinyata biyu"
Karbar ruwan tayi da yaron ya kawo mata ta shige bandaki tana jan tsuka.
Saida ta gama shirinta tsaf kafin ta nufi gidan kungiyartasu,lokacin ana shirin kiran magriba,wasu masallacin kam ma sun shiga amma itah koh a jikinta kaman ma an ce an yafemata sallahr.
Lokacin da ta isa su burgu sun gyara wajen tsaf kaman ba shiba,a kijerar da aka tanada ta hakimce tana wani shan kamshi ,kayan ganimar aka bajemata a gabanta.
Kajine sun sha suya mai kyau jajaye sai turiri suke,gakuma lemo masu sanyi dakuma duulah mesaka mutum ya jishi a sama,wata kururuwa su burgu suka buga dan dadin ganin irin abunda aka kawo.
Hannu tasa ta yagi cinya guda d'aya tasaka a baki kafin kuma kowa yafara yagar nasa rabon,kid'a akasa mai irin buga sautinan kowa yana rausaya wa yana cika bakinsa da d'i,
"Kai shugaba jar wuyah mufah tunda muna kungiyarki mun more fah,wace kungiyace zakaga ana siyan kayan dad'i ana cin wannan dad'in in ba kungiyar seemah jar wuyah ba.
Wani rausayah seemah jar wuyah tayi irin na wanda aka zigashi dinnan,
"Hmm aiku bari kawai saima idan an samu wata hanyar ta bud'e,harka tazo saidai kuji ana kungiyar seemah jar wuya sai ana cika form kafin a shiga"
"Heeeeeeehuuuuu sai seemah jar wuyah"
Dukkansu aka dauki ihu tareda shewa ganin irin kirarin da suka yi mata yah shigeta sosai.
Salame ceh a zaune ana ta tad'i itama a nasu gidan da yamma itada surukanta da kuma kishin balbali,
Hira akeyi wanda duk rabin hirar tasu gulmar gidan gandune, d'aya matarce wadda duk zancen da akeyi bata saka bakiba saida ga baya tace,
"Babar labiru wannan gulmar dakukeyi bata da amfani ko kadan,abinda yake faruwa a gidan abune daya zama tamkar ruwan dare a namu sauran gidajen musamman ma kauyukan mu da kuma iyaye masu san ransu wanda daka yiwa y'ay'an su fa'da gwara komai ka musu,addu'a yakamata mu dingayi ba wai mudinga yayata lafin y'an uwanmu bah"
"Kehh Wallahi kiyimin shiru banason wannan iyayin naki da kutufifi,zaki wani zo kina yimana wa'azi an fadamiki nasiha mukeso,toh muje masallaci mana...........,"
Wani yarone yah shigo da gudu yana kiran salame da karfi,
"Babar labiru babar labiru,wai kizo inji wasu a waje,wai buhu suka gani a bayan gidan can yana motsi,suna budewa sukaga labiru ne wai an konashi da wuta a cikin buhun"
"Kuntun ubah kai meka ce?,dagaske kake Kuwa,yau nashiga uku na lalace wane la'ananne a fadin garinnan ya yiwa labiruna haka wayyyooo na lalaceh"
Amma babar labiru kamata yayi kiyi addu'a ba ki dinga ihu ba"
"Dallah rufemin baki yar kan uwa shegiya wato bazaki barni da wannan wa'azinnaki ba koh,yanzu haka ma dake aka had'a baki inaga,dan dama duk bakin ciki kuke min dani da y'ay'ana"
Ganin fad'an na neman komawa kansune yasa kowa tayi kofarta ,ita kuwa ta rufa hijabinta batasan ko dadai ma tasaka ba,tayi waje har sannan bakinta bai yi shiru ba.
Saida su seemah suka kai wajen karfe dayan dare kafin kowa yayi tunanin hanyar tafiya gidan su,mashin din burgu ta dauka tayi gaba ,yana ta magana amma ko juyowa batayiba bare yasa ran zata dawo masa da mashin din.
Hanyar anguwar su sameemah ba kowa haka ta bi da wannan uban daren ga kuma duhun allah da annabi daya lullube sararin samaniyah,a wannan lokacin babu yanda za'ayi mace kamar kowacce ba irin sameemah ba tafito da irin wannan daren kuma a mashin ita kadai.
Tana cikin tafiyane taji alamun wani abu yah rike mata tayar mashin,tsayawa tayi cak da mashin din amma shiru bataga kowa ba,Murmushin gefen baki tayi da tagane mai hakan yake nufi,
"Tabbb gaskiya an rainani,yanzu harni wani zai rikemin tayar mashin,toh me akeso nayi ihu ko kuma zefar mashin din na barshi a wajen,kafin gobe wani yah lallab'o yasace koh?"
Tura mashin din tayi sai kuma taji tayar ta tafi,wani yunkuri tayi tasake tayar da mashin din kafin tace,
"Yadai fi muku,a saukake dan ni ba addu'a zanyiba dama tunda ba iya wa nayi ba,kuma ba ihu zanyiba tunda ba ganin ku nakeba,kunga bata lokacinku kueyi nima ku bata min nawa,saboda so nake naje nayi bacci kuma sai gobe,aga dame zatazo a tareta ana mika wuyah"
Har taje bakin kofar gidannasu batabar surutunba kaman wanda wani ne a kusa da ita yana jin me take cewa.
Alamun kamar mutum tagani a bakin gidannasu kamar mace tana firah,duba agogon hannunta tayi tana murza ido,karfe biyu ta kusa amma ga wata a kofar gidannasu tana hira,
"K'undun ubancan mai yarinyar nan take a waje a wannan Daren,mu manya ma mungama mun dawo gida amma ita tana waje,hmmmmm bari nazo na sameku"
(Toh fah kunji wai itace manya,su manya gatan wasa)
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤05❤

A manne suke a jikin katangar sun lab'e itada dashi har baka gane me ake kullawa a wajen,sameemah ceh ta sharo mashin din da gudu,suna kallonta kuwa sukayi saurin bajewa da sauri,saida taje ta kafe mashin din kafin ta dawo wajenna su tana gyara zaman gyalen dayake wuyanta da kuma wandonta wanda rigar ta tattare saboda hawa mashin.
Kad'a key din tayi a gabansu kafin ta karewa saurayin kallo,
"Kai uban me kakeyi a kofar gidannan,har karfe biyun dare,duk wanda kasamu da ka lallatsa tun karfe goma bai isheka ba saika kai har karfe biyun dare dan zalama,kawuce ka bar wajennan ko saina saka karnuka sun sanja ma kamanni tukunna,da haka kam ai sai kajata ku shiga cikin gidan zuwa kan gadon baba umaru ku karisa tunda har yanzu bai isheka ba(wato ubannata ma bata barshiba kenan)"
Cikin sauri da alamar rashin gaskiya yabar kofar gidan yana sosa keyah,harara ta bishi da shi tareda cewa,
"Heeeege mai siffar mayu kawai"
"Wai miye hakan zakina wani zagin min saurayi kaman wanda yayi miki sata?"
Buge mata baki sameemah tayi cikin sauri kana ta dora da cewa,
"Har kina da abin cewa keda na kamaki dumu dumu da laifi,a kofar gidanmu saboda ki jawo mana abin magana koh?,nasake jin bakinki ,kin shige gida ko saina yi kwallo dake tukunna"
Cikin kunkuni khadija tafara cewa,
"Kuma wallahi saina gayawa ummah abinda kikamin,naga kema daga yawon ta zubar din kika dawo kuma daga gani shaye shaye kika iyo tunda ga nan warin wiwi a jikinki.....,"
"Mekikaceh wai?"
"Babu komai ba abinda nace"
Tana fadin hakan ta shige gidan da gudu dan ba karamin aikinta bane ta biyota ta kara mata wani dukan.
Sassafe masifar a gidan su labiru ta kare dan yanda salame taga rana haka taga dare ita da labiru da kuma mai maganin tofi ,wanda ta daukoshi saboda yayi ma labirun magani,dan batada arzikin kaishi ko chemist ne bare kuma asibiti.
Da safe har ya samu ya yi d'an bacci saboda maganin da aka saka masa,saidai fah su labiru babu saka wando zaman daki yakamashi kenan.
Saida safenne saleh maye yah shigo dakin uwar tasa duba labirun,salame ce takalleshi da takaici kafin tace,
"Yau ganshi bawan mace kawai,tun jiya ake ta maganar abinda akayiwa dan uwanka sai yanzu uwartaka ta biyu ta barka kazo ka dubashi kenan,wanda yarako maza duniya kawai"
"Haba Babar labiru yah kike yawa ne,ni ina can bansan ma me ake yi ba,dan sai yanzu na tashi a bacci,shine nace bari nayi hankali nazo na duba shi da jikinnasa,kuma ma dazakice LUBABATU ceh tahanani zuwa,ai kaunace idan ta hanani ma"
Kuka salame takawo ta kece tana fyace majina ga ciwon labirun ga kuma takaicin babban dannata wanda yanzu shida wanda suke turu babu wata maraba mai yawa,
"Dallah ni tashi kaban waje,yanzunnan ba sai anjima kaje ka dau matakin abinda akayiwa labiru dan bazan yadda ba wallahi"
Mikewa yayi da d'an guntun karfinsa yah ciro wata wuka a wandonsa wanda yafita acikin kalarsa saboda daud'a,
"Wannan dolene yanzunnan zanje na koma waye fad'a minshi saina fard'e masa wuya a yau ba sai gobeba,mu daman ai ta irin wannan harkar muka kware"
"Eh naji ana cewa wani a anguwar yaga yaran sameemah wannan shegiyar yarinyar mai kama da y'ay'an aljanu,wai sun ajiye buhun da aka samu labiru a ciki,ina da itace tayi wannan aika aikar ,dan kowa yasan zata aikata"
Suleh ne yajuyo ya kalli uwar tasa tareda cewa,
"Iyee inna banji mai kika ceba,ai seemah dai tawa kike nufi?,kai ba mai taba wannan cikar na kyaleshi ,yanda nakejinta a kashin raina ai koke banajinki,babar labiru itah ceh fah surukarki wanda za'a daura auran kwanannan,so kike idan naje na yanketa akawomiki suruka mai tabo"
"Inalillahi jama'a kuzo ku tayani bakin ciki,wannan d'a haihuwar banza nayi,yanzu nikake fadawa bawanda kakeso sama da ita a duniya,kuma wai harda ni,bayan irin aika aikar datayiwa dan uwanka?"
Turewa sulen tayi cikin bacin rai yah wancakala gefen labiru wanda yake zaune an saka zani an lullube masa gun da ya kone din,sai zazzare ido yake maganar ma wuyah take masa kaman wanda aka kone masa bakin.
"Dan banza ji yanda ka wani baje a kasa dan kawai na bugeka,dama uwar me zaka iyah idan kajedin duk kwaya ta gama hudaka tun daga baki har hanji,wannan masifah da mai tai kama"
"Inna gaskiya karkije gidanannan kiyi musu wannan masifar taki ,gidan surukanki ne fah "
"Innnnnnaaaa ba ita bace tayimin haka ba,karkije kice itace tayimin haka na rokeki innannnnaaaa"
"Yawwa inna kinji abinda labirun ma yace koh?,in ma itace cikin soyayya zan lallameta ta fad'amin"
Dawowa tayi tana karewa y'ay'an nata kallo,daga wanda yake kwance babu abinda zai iyah an nakasa shi sai wanda shida tab'ab'b'u basuda maraba dashi da su.
Cije baki kawai tayi dan takaici ta rasa ma mai zata ce,
"Shashashu kawai in ma asiri tayi muku yau zai karye dan ubansa,zuwa gidan gandu kuwa ba fashi inyaso idan naje ku hadiyi zuciya ku mutu,yau koni koh su a garinnan wallahi,dan bazan tab'a yarda ba,in ta kamama kotu zan maka su,muje ayi ta shari'ah daga nan har kotun k'oleee.
KO safiyah bata gama waye ba,dan wasu ma ko karyawa basu gama yiba salame ta doko sallama cikin gidan gandun,
"Salamu alaikum gafaranku dai,ko bakowa a gidanne"
Wani yarone ya fito daga kofar su larai din yace,
"Suna nan amma kowa yah kofarsu"
"Inane kofar su sameemah wannan shegiyar yarinyar"
Tun kafin yayi magana larai ta leko domin ganin wace bakuwar da safiyanannan,dan tun a jiya da daddare suka baro asibitin saboda yanayin sha'ani na kudi,
"Kutt dama kece,kin hutasar dani dama ina shirin zuwa gidannanki muyi duk wacce zamuyi dake amma tunda kinzo shikenan sai a fara"
"Mekike nufi da cewa muyi wacce zamuyi ,toh ni ba wajenki nazo ba ,wurin yar dabar gidannan nazo da ta lahantamin d'a yana nan a kwance kaman bazaiyi raiba"
"Ayyyirirri koma wa kike nufi tamin dadai duk da bashi zai hana na fasa abinda nayi niyyah ba"
"Kehh duk abinda yafaruma larai ki bari sai daga baya yanzu ba wajenki nazoba"
"Ohh kina nufin bakiji abinda dannaki la'ananne ya aikata ba,koda yake bazakijiba saboda ba y'arki yayiwa ba,yanzu dayake shi akayiwa aika aika aikin ji har kinzo neman ba'asin labarin.
Toh in ma baki sani ba kisani danki labiru y'ata hanifa ya farkata,kaman yasami fanko saboda tsabar tashanci kuma yayi gado,toh bazan yadda ba,yanzu dakike cewa yana jinya toh yana warkewa zan bawa gardawa sadaka su sake maidashi kwance,dan jinin y'ata billahillazi bazai tafi a banza ba"
"Ke wai dankinga nayi shiru ina jiran ki fadi abinda yake bakinki,aikin banza saboda gadon kwadayi yasa ina kuke lik'a masa ita,dama aka ce ai k'uda wajen kwadayi akan mutu,kuma dazakice wai gado dan ma abin kunyar kowa yana da shi a gidansu ,ko kin manta tsoho wanda baya saka wando sai babbar riga kawai saboda bin bazawaran kauye"
Hayaniyar ce tafara yawa inda matan kofa ko wacce take lekowa dan kashe kwarkwatar idon ta.
Da abin yayi yawa fad'ane ya rukume tsakanin salame da larai kowa yana tsinewa kowa albarka kaman wasu zakaru.
Saida mazajen suka fito kafin aka samu aka rabasu dakyar kowa tana huci kaman shanu.
"Kai kai mai yafarune haka,mu gidannan babu dama mu tashi a ji shru kaman kowane gidan saidai Koyaushe da masifar dazata kunno kai"
Kawu KAMILUNE,mai magana yah fito zai tafi gona,dama shi bai fiye zama a gidanba kl yaushe yana wajen neman kidinsa,matansa ma yahanasu shiga duk wata cakwakiyah da ake a gidan indan yakama wata kuwa da hannunta a ciki toh saidai ta nemi wani gidan badai nasa ba.
Jin muryarsane yasasu salame tsayawa fad'an sauran matan kuma kowa ta koma gefe ta kasa kunne dan taji mai za'a ce,dadai lokacin ne kawu shehu shida baba umaru suma suka shigo daga wajen mai shayi da alama wani yaronne yaje ya kirasu,
"Wannan yar rainin hankalince mana,dan tsabar su dangin marasa kunyane duk abinda danta yayi bai isheta ba hada zuwa tana wani kumfar baki wai an illah ta mata d'a a gidannan,kuma illatawa bata ga komai ba ma saina tashi yanke nawa hukuncin ehhe"
"Hukunci kin dade baki dau hukuncin ba abinda akayi masa ma na yanzu ba shiru zanyi ba barekuma kiyi tunanin daukar wani matakin"
"Kai ya ishemu haka wannan yarintar,kun girma ku ba yara bane amma baku da maraba da yaran kuma abin kunyar ma a gaban yaranku kuke wannan abun,ke salame mai akayiwa dannaki kikazo tada fitina da safennan"
Baba umaru ne yadaka musu tsawar cikin bacin rai da kuma k'osawa da halinnasu na yau da kullum,
Jin an tambayeta ne yasata fashewa da kuka tana shareewa da gefen zaninta kafin tace,
"Dan tsabar rashin imani bakuga aika aikar da akayi masa ba,tun daga kasan cibiyasa har zuwa rabin cinyoyinsa an konesu da man gyada mai zafi,babu komai sai fatarsa a waje kawai,kuma anfadamin wani marar imaninne a cikin gidannan yayi masa dan haka bazan yadda ba wannan ai niyyar kisan kai akayi ,yanacan katon saurayi a kwance sai abinda akayi masa tukunna"
"Allah ya kara baiga komai ba ma,in duninsa halin bunsuru"
Larai ce tayi sauri ta fada tareda d'ane baki kaman ba itah ce ta fad'a ba,
"Keh larai banason shiririta ana kwantar da wuta kina kara mata fetur koh?"
Baba umaru yana rufe baki kawu shehu yadora da cewa ,
"Laifinta Toh kagani yayan umaru,bayan abinda dannata yayiwa yar mutane kuma taxo tana fadan wai wani yah nakasa mata shi,ina ruwanmu toh,in zatayi hakuri tayi in kuma bazatayi ba ta kai kara ,muma saimu kao karar in yaso ayi ta shar'ar tunda ita take so ayi tayi,
"Ahah baza a kai har haka ba,ke salame tunda kinji mai danki yayi sai kije gida kiyi jinyarsa tunda kinga suma jinyar tasu yar suke,kowa sai yayi hakuri yaran zamanine sai hakuri ka haifesu baka haifi halinsu ba,muma kuma iyayen da na mu laifin ta wani wajen ,allah dai kawai yah shiryamu gabaki daya"
Dakyar su kawu kamilu suka kwantar da fitinar salame ta tafi gidanta tana kanana nan maganganu wanda allah ne kadai yasan ranar dazata bari.
Sameemah kuwa duk abinda akayi a gidan bata sani ba,saida wayarta tayi Ring ne kafin ta juya ta kalli screen din ,tareda tsuka saboda tashinta a bacci saboda tasaka wayar a kusa da kunnenta,
"Alhaji bala"
Shine sunan da ta fad'a cikin muryar bacci kasa kasa..........

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤06❤
"Heelloo alhaji bala yah hidima?"
Seemah ta fada cikin muryar barci,wani irin mika alhaji bala yayi jin yanda ta amsa masa cikin sanyin muryah kaman ba sameemah daya saniba,
"Lafiyah kalau madam yah hutu da jin dadi"
"Lafiyah kalau,wani abune yah faru?"
"Ahah babu abinda yah faru gimbiya kawai na kira ne naji lafiyar ki,sannan kuma na sanar dake inkin shirya ko yaushene to kiyi min magana zan aiko mota har kofar gidanku a dauke ,kizo mushakata muji dadin mu,saidai ina rokonki dan allah naji kiran shiryawarki da wuri,dan baki san yanda nake jinki a cikin zuciyah ta bane,akanki babu abinda bazan iyah ba,kawai hadin kanki nake bukata shine kawai cikar burina"
Saida ta tabe baki tukunna tace,
"Naji alhaji yanzu ina kwance banason a takuramin ka bari idan na tashi nayi tunani zaka ji mai na yanke ,kuma karka sake kirana sai na nemeka tukunna"
"An gama gimbiya,ai duk abinda kikace shi za'ayi

Please Login or Register in order to submit comment