Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayaji abinda tace,shikuwa wanda aka Bashi ajiyarsa kallon sameemah yayi da alamar gargadi na batasan yan iskan zamani ba fah.
Nuna masa tayi ba matsala tareda cewa,
"Karka damu babu abinda zai faru ,kawai ka bamu waje sannan kace ban yadda koh wani abune yah faru wani yah shigo ba"
"Shikenan tunda kince haka amma duk da haka zamu tsaya a kusa saboda tsaro"
Jawo musu kofar yayi tareda nufar su burgu dan yasanar musu abinda yake faruwa saboda yasan su zasu iyha yi mata magana,amma yana gama bayanin yaga kowa yah cigaba da abinda yakeyi.
Kallo akeyi tsakanin sameemah da saurayin,saurin mike wa yayi yana gyara wuyansa wanda ya bada kara kakkkk,dantsensa ya daga yana murdawa domin bata tsoro,ba karyah kam namiji ne majiyin karfi wanda zai iyha firgita duk wanda yaga dantsennasa amma babu alamar hakan daga wajen sameemah,saima kara matsawa da tayi tana bashi waje ya gama motsa jikin.
Cikin sauri yah shammaceta ya kinsa mata naushi a fuska saida ta juya,dago da fuskarta ta tayi tareda yimasa murmushi kaman babu abinda yah faru,wani naushin yakara kawo mata inda tayi saurin rike hannunsa da nata hannun,jijjiga hannunsa yayi da niyyar janyewa amma yayi yayi yakasa kwacewa,mitsitstsikawa tayi sai ji kake kururrs kurus.
Wata kara ya sake yana kallon yanda yatsuna hannusa suke kokarin tashi a aiki,amma duk da haka yah kara kawomata daya hannun,wannan karon ba iyah Yatsun ta karya ba harda tsintsiyar hannun,sannan ta kara masa da wani duka a akan gwiwarsa hakn yasa
Ya zube a gabanta akan gwiwoyinsa,
"Yanzu mai zaka ce game da aikina,koh kana da wani saurin bayanin da kake son isarwa gareni,idan kuma karaya uku bata isheka ba saina kara maka wani ,hadda wani kawo naushi da karfi kuma wai ga mace koh kunyah bakaji ma"
Saboda ranar ba wani bacin rai takeji ba dan ma taji furucin da yayi ne,gashi a aikin banza yah jawo wa kansa duka.
Dakin da aka kai su kawu shehu ta nufah,suna hada ido da shi yayi saurindauke kai,
"Zaku Zauna anan za'a dan yimuku horo kafin kowa yah tafi gidansu,wanda kuma suke a wani garin za'a saka su motar garinsu"
A wajen park din motarta suka hadu da wanda yake kula da saurayin da yah sha dukan,
"Yawwa kaje ka duba shi ayi masa dorin karayarsa zuwa gobe zamu kaishi wajen yan sanda"
"To shikenan sai gobe toh"
Daga haka ta bar office din ta nufi gida.

Tun a bakin kofar shiga gidannasu da hangi sameerah suna fira da ummaruje sai wani sunne kai takeyi itah a dole ga mai kunya,shikuwa har wanj lekata yakeyi yaan dariyah.
Tun kafin ta fito daga cikin motar ta karemusu kallo tass,duk da abin yabata mamaki amma kawai tah watsar abin aranta dan bata ga dalilin sake tunawa dashi bama.
Kashe motarta tayi kafin tazo bin ta kusa dasu zata wuce,hakan bai ishi sameerah ba ko tana tunannin bata gansu bane,?oho
"Lah sameemah kin dawo ne,ga ummaruje ku gaisa mana,tun dazu nake cemasa bari kizo ku gaisa amma yace wai na daina yimasa zancenki amma bari kiji daga bakinsa ma"
"Ahah basai najiba nima ban nemeshi ba ai,dama kece kike neman na hada ki dashi nacemiki idan kika nemeshi kuka gaisama babu abinda ya shafeni gashi kuma kun gaisa din na gani,kuci gaba da gaisawarku kawai"
Har sameemah ta saka kai zata wuce kuma sai sameerah ta sake cewa,
"Naji ummaruje yace wai dama ke kika je har gidansu wajensa koh?"
Abinne yabatawa sameemah rai dan rainin hankalin yakuma fara isarta ga kuma gajiyah da ta kwaso yau din,komawa tayi har wajen, kafin ta kankance ido ta fara cewa,
"Ke sameerah wallah in baki rabu dani ba ranki zai baci,me kike nufi shidin daya fadamiki yana tunanin wajensa najene?toh ki fadamasa duk da naga kaman wannan bashine a gabana ba tunaninsa yana wani wajen daban,wannan gangar jikice,toh idan yadawo hankalinsa kice masa ba wajensa najeba,wajen ubansa naje domin yi masa gargadi,kuma dama koda bai fita a rayuwata ba zan fitarda shi,dan ko a farcen kafar mutum din da zai iyah rayuwa dani bai kaiba,sannan ke kuma ...........hmmmm ban ma yi hakuriba ki shigo gida kisameni kawai idan banyi bacciba.
Kwafah taja babba saida sameerah taja da baya kafin ta bar wajen zuwa cikin gidan.
Yawwa shirin yayi aiki akan ta hankalina ya kwanta tunda yanzu baya ranta kaman yanda bata ransa itama yanzu,shikenan zan wataya saboda nasan nawane ni kad'ai. Fadin sameerah kenan acikin zuciyarta.



*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤32❤


Tana shiga gidan yara suka fara kallonta har da manyan,ganin kayan dayake jikinta wanda basu saba ganinta dashiba,saboda lokacin data fita da safe basu tashiba bare suga fitarta.
Duk da yanda suka kewayeta amma bata kula kowanne daga cikinsu ba,domin abu ne mai wuyah mutum yaganta tana kula wani daga cikin yaran gidan.
D'aki ta shiga ta cire kayan kafin tah kwanta,ta dad'e tana tunanin yanda rayuwa take gara mata,amma kasancewarta mace mai nuna juriya yasa babu wanda yasan halin da take ciki.
Kiran sallah akeyi amma koh a jikinta ,gashi yanayin lokaci na magriba ba'a son kwanciyah,amma baga sameemah ba kam,wanda sallar ma batayiba bare kuma ta kiyaye lokacin kwanciyah.
Fiiiiiiifiiiii kake jin feduwa daga zaure,saida ta bayyano kafin ummah tata ta rike baki,itakuwa zata so taga ranar da surayyah zatayi hankali,da kuwa tafi kowa farinciki.
Duk da kallon da umma take yi mata bai sa taji wani koh dar a ranta ba saima kokarin zama da takeyi zata nada labarin abinda yah fafu a wajen aikinnata zuwan farko.
Dakatar da itah tayi kafin tace,
"Kai mai Sunan manyah,wane zama kuma zakiyi bare bada labari,bakyajin ana ta sallah a masallataine,ki tashi kije kiyi sallah ina yaso koma mainenee zanji daga baya"
Kobare fuskar tayi tana dadare da buga kafah a kasa,sai ka ce ba itah ce ta shiga har gidan wasu tah kamo mai laifiba dazu.
Da haka dai ta wuce badan taso ba ta tafi yin sallah.
Idarwar ta keda wuyah taji wayarta taNa kara,kaman mai kiran kuwa yasan sanda zata sallame sallah.
Duba screen din tayi inda sunan burgu ya bayyana a gaban wayar ,dauka tayi tareda murmushi saboda tuna alkhairi dayake mata a kwanakinnan ba dare ba rana.
"Aslm yar ummah ya kika shiga gida lafiyah"
"Lah lafiyah kalau karamin ogah,yah gajiyar aiki"
"Tabi jiki sosai,ki mikamin godiyh a wajen umma mana"
"Zataji sosai"
Da haka suka cigaba da hirarsu suna ta wasa da dariyah,har zuwa wani lokaci.
Tun kafin kowa yah tashi sameemah yau ma tabar gidan.
Saidai yau babu wani aiki sosai saboda jiyah kusan suka kammala ayyuka da yawa daga zuwansu.
Can wajen rana tana aiki a takardu aka cemata ana sallama da itah,bada izini tayi akan a shigo,bata daga kai tah kalli wanda suka shigo din ba har sai da sukayi gyaran muryah tukunna.
Baba umaru ne da Manu da kuma baba munkaila,dayake bayau ta fara rashin mutumci ba fuskewa tayi tana kara daure fuska tareda kishingida akan kujerarta tana juyawa.
"Uhm ina jinku mai yake tafe daku?"
Baba munkaila ne ya harzuka dayake dama yah fisu zuciyah,
"Ke seematu kinci gidanku,wajen ogah daya kama mana dan uwa mukazo bakeba sannan dan rashin tarbiyyah kina kallonmu ko gaisuwa babu ko,wai tukunna ma uban me kikeyi a cikin wajennan dakuma kayan ma'aikata"
Duk fadan da yake yi bata cemasa komai ba har yayi yah gama,
"Toh malam duk naji bayaninka ,shugaba da kake nema nice shugabar wajen,batun kuma kama dan uwanku da akayi tabbas anyi haka kuma bazan sake shi ba sai yayi kwana uku kaman kowanne masu laifi da muka kama jiyah,ina fatan ka gama jin amsar tambayoyinka,idan kuma basu gamsheka ba zaka iyah tambayar daya daga cikinma'aikatan,"
Tun kafin ta rufe bakinta kuwa saiga wata yah shigo,da sauri yah duka yah gaisheta tareda mika report zai fitah,Sunan sa ta kira tareda cewa,
"Am zo zaka dan yimin wani aiki mana,wannan zaka raka zuwa dakin da muka ajiye yan kamen jiyah"
"Okay ma'am,"
"Ku bishi ku kalleshi na baku wannan alfaramar"
Dan tsabar mamaki duk cikinsu babu wanda yayi magana,sai kawai tashi da sukayi domin bin wanda tace musun.
KO a jikinta kuwa tah cigaba da abinda takeyi ,kaman dama dai duniya bata san suba.
Bayan tafiyarsu da kusan minti talatin mutane da dama zunzo karbar yan uwansu,dan office dinnata yah cika har wasu suna tsaye,duk maganr da sukeyi bata ko dago kai bare basu amsa.
Su baba umarune suma suka dawo office din bayan sunje sunga baba shehu,wanda bayansa yayi burd'i burd'i da dukan bulala,bakincikine kwance a ransu,musamman ma Manu wanda shi ubansa ne,kuma sa'anni suke da sameemah din ,buga table din yayi har saida takardun wajen suka zube,
"Ke Wacce irin halitta ce wai,tum dazu muke magana amma koh amsa mana bakiyiba,wane irin laifi ubana yayi miki kika yimasa wannan hukuncin,kuma dan zabar ke baki imani kika yimasa dukan dayafi na kowa a wajen,magana nake yi nima amatsayin bansanki tunda naga dan kin sami matsayi tun ba'a je ko ina ba kin watsar da yan uwanki,sun zama sune abin farautarki,butulu kawai wanda bata san zafin iyaye da yan uwa ba"
Cikin zafin nama sameemah tah zabga masa mari dama a tsaye yake a bakin table din ta,wanda hakaan yasashi hadiye sauran maganar dayake shirin amayarwa,tashi tayi ta tsaya lokaci guda tah sauyah daga kamannin da take,nuna shi takeyi da yatsa kafin tace,
"Kai waye da har zakazo office dina kana fadamin magana,koh dan kaga kana dan uwana?,toh baka da wannan ikon kuma bazaka samu ba,a ganinka bansan mai nakeyi ba ne,har zaaka fadamin bansan zzafin iyaye ba kasan mai kai ubannaka yayi da kake jin zafinsa"
Rintse idonta tayi tareda kokarin control din jijiyoyin dasuke kwance akan goshinta,
"Ban so fada maka abinda yah faruba har da mutanen gidan ma banso su sani ba amma shiahhsiginka yasa saina fadamaka inayso duk abinda zaka ji ma kai yah shafa,...........a kwance na ganshi akan karuwa a dakinta suna aikata masha'a ,mai kake tunanin zanyi,dadi zanji kenan,iyah fadaamka danayi nasan zaka ji zafi,amma bazaikai nawa ba tunda kai kwantance zan yi maka amma ni zahiri nagani......"
Tun kafin ta gama fada baba munkaila ya daga mata hannu,dan shima ba kdan ba abin ya bugeshi sosai.
Jan Manu sukayi suka bar office din wanda yazama tamkar gunki,kallonta ta mayar kan sauran mutanen office din wanda yawancinsu daga wanda tazo karbar danta sai mai karbar mijinta ,wata yar ta wani kuma kanwarsa koh kuma yar yayanka da sauransu,
"Ku kuma mai kuke jira da bazaku bacemin daga ni ba,babu wanda zan saki saina ganan masa azaba kaman yanda yaganawa zukatan jininsa,da kuma masu sonsa,dan tsabar baku da hankali wai su bijiremuku su tafi shashahnci amma kuzo kuna yar karamar muryah a sakesu,yaushe duniya zata cigaba a samu raguwar yan banza idan har zuciyoyi bazasu tsaya su kawar da so su hukunta masoyinsu ba.
Ban yards da irin wannan son ba ni "
Da sauri kowa yah fita daga office din babu sauran magana tunda aka ga yamda tayiwa dan gidansu ma,wasu suna cewa ta kyauta wasu kuma suna cewa zaluncine,amma duk da haka babu mai magana *wai an ce fadan dayafi karfinka saika mai da shi wasa*.
Kaman yanda tayi alkawari kuwa saida baba shehu da sauran masu laifin suka cika kwana uku kafin ta sake su,office tace akawo mata baba shehu wanda har saida ya rame a iyah kwana ukun,rigar jikinsa duk tayi wani iri,kansa a sukunye aka shigo dashi saboda kunyar da yake ji.
Wasu kaya na maza yadi ta wullah masa tareda nuna masa bandakinta na office din,
"Ka Shiga nan ka yi wanka akwai ruwa sannan ka sanja kayan jikinka"
Ba uhm ba uhm uhm,sanna babu musu yah dauki kayan yah shiga bandakin.
Ya dan dsde da alamun gasa jikinsa kayeji kafin yah fito.
Abinci tah bashi mai rai da lafiyah yah ci yah koshi,tukunna tace,
"Ina fatan kaga yanda ta kasance koh?,idan har kuna cin kasa ku kiyayi tah shuri,yanzu ba da bane an sauya tsarin kungiyar nan,sauran ma nayi musu gargadi,idan har kuka kuskura nasake kama wani a wannaa wajen ba ma iyah nan ba,toh ba iyah bulala zanyiba,wallahi kawu shehu dandakeka zanyi yanda akeyiwa Akuyah,ai ka tara y'ay'a da sun isheka,toh idan baka kama kanka ba zaka mutu babu mazakutah,ni nan ni zan rabaka da itah,idan kaji kayiwa kanka,yanzu idan ka shirya muje na kaika gida,sai a gyara hali kuma".
Shidai har ta gama abinda zatayi bai ce komai ba har ta fita a office din yabi bayanta shima.
Mota tashiga suka tafi,duk da lokacin tashi ba yyiba amma tabar aikin a wajen mataimakinta kawai.
Suna shiga gidan kowa kallo yah bisu dashi,shikuwa baba shehu kofarsu yazo zai shiga,inna larai ce tayi tsallae ta tare bakin kofar tana masa wani kallon nasan mai yake faruwa.
Bayyi mata magana ba sai tsayawa da yayi. Yana kallomta.
Sameemah ceh da haushi yakamata ganjn zasu fara fadannasu a gaban yara tace,
"Wai kekam inna larai meyasa kike hakane,ke har kina da karfin gwiwar dazaki yi wata magana akan laifin wani,hakan ma mijinki,nagan daman kin san yana aikatawa ba wai baki sanj ba,kawai yanzunne akka kamashi hannu dumu dumu,kaman yanda kema yasan halin dakike aikatawa.
KO kin manta lokacin da kike bin manyan anguwa akan zaki dawo dakinki lokacin da shima ya ganki da malam mai gani har hanji na anguwar kan tudu ya sakeki idan kuma............"
"Ke kinga dakata haka yah isa haka naji ,banason wani tone tone,shegiyar yarinyah kai,sai kace kedin allah da annabi kike bi yanda yakamata,naji zan barshi ya shiga amma ba dai ya tabamin kayan amfani ba sai yah tsarkake tukunna"
Shidai wucewa yauyi ya barta a wajen tana ta sababi kaman aikota.
Can wajen isha ne bayan anyi magriba,baba umaru ya aika a kiramasa dukkan yan matan gidan.
Har bakin turakarsa suka je kowa ta samu wajen zama ta zauna.
Gyaran muryah ya fara tareda godiyah ga Allah tukunna.
Nasan kunyi Mamakin tara ku danayi ,badan komai bane saidan na gargadeku sannan na baku umarni,a gaskiyah na gaji da ganin masu hira a kofar gida,kaman ku su sameerah,sannan kuma da jawo magana wato irin su sameemah.
Saurayi zainab ya bada uzirin cewa bai gama giniba,ga kuma wani aiki daya samu yana bukatar zuwa service,dan haka ina mai baku umarni kowa a cikinku ta fitar da miji,dan duk tareda za'ayi auren babu wadda zata sake zama na gaji haka sai na jj da masu tasowa.
I'd an kuma baku fitarba toh in lokacin yayi koma waye zan aura ma yarinyah,zabi yarage gana ku.
Ku ta shi Ku tafi na sallame ku.



*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤33❤



Kowa tashi yayi yah nufi harkar gabansa masu surutu sunayi,ita kuwa sameemah hakan bai dameta ba dan duk cikin zancensa babu wanda ta saka a mizanin gaskiyha bare har yah dameta,ai zancene ma ace wai itah ce zatayi aure.
Da haka zancen yah wuce kowa yah cigaba da abinda yake gabansa.
Harkar aikinta kuwa sai abinda ya cigaba,dan koh wata bata cikaba amma suanan ta ya zagaya inda mutum baya tsammani a fadin garin.
Da dare suna kwance dakin shiru kowa yana harkarsa sameemah kamma aiki takeyi a cikin system na wajen aikinta,sameerah ce tah shigo dauke da leda a hannunta sai wani daga kai takeyi,dagargajewa tayu a tsakar dakin tana fito da duk abinda yake cikin ledar.
Da biyu takeyin abinda take dan kawai su salma su gani,
"Kai koh a tarihi ban taba ganin yanda masoyi yake kulada masoyiyar sa kaman umaruje ba,gaskiyah na yarsa ba kyau ne da kwallaiyah yake sa mace tayi farin jini ba,idan itah mai sa'a ce shikenan,saboda bakin jini har ana binsa gida amma ba'a sameshi ba har yah tako har wajena yah zabi sarauniyarsa"
Haka tah cigaba da surutunta da zarar bunu, amma babu wanda yah tanka mata,dan gwara ma salma taja tsuka amma sameemah kam koh daga idonta daga kan system din batayi ba,
"Salma bisimillah ga kayan dadi,wanda ba'a ci a gida fah"
"Ke sameerah iskancin ya isheki haka kodan kinga mu zuba miki idone iye,ta bamaci a gidan kedin ci kikeyi,banza sabun shiga kawai a cikin hakrkar"
Dari yah sameerah ta sheke da itah dan dama so take wani yah tanka mata a cikinsu,
"Sabun shigar shiyasa naga daga shigata da kamo babban kifi dan gidan manya saboda na cika mace"
"Wacce macen kika cika,koh kinace babu wanda yasan asirin da kukayi masa ne keda uwarki,kuka karkatar da hankalinsa daga kan sameemah zuwa naki,ai kowa ma yaga kallon dayake miki yasan ba a hankalinsa yake ba,idan har kina ji da ke macece ai saiki kallameshi tah kissa ba ta asiri ba"
Bakin cikine yah kama sameerah jin abinda salma take fada mata,bata san lokacin da ta kaimata raruma suka fara fada ba,cikin kankanin lokaci duk suka tumurmjshe naman kajin a da lemon a kasa.
Feduwar da sameemah tayi ne yasa su tsaywa sai a sannan suka ga irin ta'adin da sukayi da abincin.
Karnukan ne suka shigo da gudu,dan yanzu harda wani karami ma a cikinsu wanda sameemah tah samoshi a hanya yana halin jinyah,yanzu watansa daya kenan har koma kaman ba shi ba.
Dan dama itah haka halinta yake,yawancin abubuwan da suke karkashinta taimakone yake hadata dasu,shiyasa koda kudi babu wanda yah isa ya sayi yardarta a wake abinda yake nata.
Hannu tah mika tareda nuna musu naman dakaye kasa a babbaje. Sukuwa dama jira sukeyi kare da nama,ai babu batun jira.
Sororo sameerah ta tsayah tana kallon sameemah wanda tah bawa karnukanta naman da saida tah hada da bada jikinta kafin ta samu duk dan tazo tayi burga a gabansu,dan kallon yamda yake mata mutane suke gani,amma har yanzu bata wani mallkaki zuciyarsa yanda take so Ba,kawai idan tayi magana ne yaka aiwatarwa amma dan shi a karan kansa baya yi mata abu dan racayinsa kawai,
"Me kika aikata haka sameemah, nama nawa dana shigo dashi kika bawa karnukanki suke cinyewa"
"Yanzu yah tashi daga naki ai,tunda kin gama dashi ta hanyar zubar dashi a kasa,kinga yah zama na karnuka tunda dama abincin kasa su ake bawa,dan karna wahalar dake ne kawai na basu,menene lafina a ciki Toh?"
Har ta bude baki zatayi magana sameemah tasaka hannunta a baki shshshs da alamar tayu mata shiru .
"Banason dog on surutu aiki nakeyi,kuma nariga na fadamiki dalili,idan har kika sake cewa takk kuma a kan maganar toh umarni zan basu suna gamawa da naman su koma kan naki naman,in kuma kin musa ki gwada"
Ga kwadayi yana cin sameerah ga kuma haushin yanda ta samu naman amma bata ciba,ga kuma takaicin bata da ikon yin komai akan abinda sameemah tayi mata,,dan haka hadiye wani yawu kawai tayi tah fice a dakin,duk da tana ganin salma tana mata dariyar mugunta amma bata,kulata ba.
Dakin inna ramatu ta shiga ta sameta tana ta nade kayan wanki akan gado,daga ido tayi ta kalli sameerah din wanda sai kumbura takeyi dan bakin ciki,
"Ke kuma miye kika tsaya min a kai kaman kububuwa"
"Ummah da na fasa amma yamzu ina so a zartar da aikin kawai,sona ke yanzu duk wani aiki da zai rikitah kwalwalwar sameemah tah haukace to ayi mata,umma idan da dama ma tah daina yin komai a rayuwarta tazama tamkar mutun mutumi"
"Hmm kindawo hankalinki kenan,lokacin danake nuna miki gabar ai yamma kike dosa,dama na fada muku matukar tana numfashi sannan babu wani abu na dauri da akayi mata toh babu wanda zai yi rayuwar farin ciki kaff a cikin gidannan"
"Ummah harda salma ma inaso ayi mata wani abu"
"Keee rabani da taba salma uwarta maba a zaune takeba,sannan itah ba itah ce mataalarki ba a halin yanzu,su kansu mutanen gidan indai akan sameemah ne toh suna cikin tashin hankali idam asirin kanta yah karye,ke kina tunanin iyah ni kadaice kawai mai hannu a cikin aikin? Hmm akwai abinda yafaru wanda iyah mu muka sani kawai,yamzudai a bar wannan zancen tunda kince kin amince shikenan dama tun farko kece kika yimin gardama.
Boka yace baya bukatar kudinmu shidai burinsa kawai ki kwana a wajen sa toh duk wani abu da muke bukata zai tabbata,kinga koma menene sai ki tambayeshi kawai,saidai daga yanzu ki daina tuntubarta da fada,saboda kar ta gano mai yake faruwa"
"Toh shikenan ai gobe ma zan tafi,sai kicewa baba umaru na tafi kauyen kawunki saboda kinsan bayason fitarmu kwana a wani wajen,ai yamzu na tsani sameemah dinnan,dan idan muna zaune da umaruje har kirana yake da sunan fah"
"Yanzudai mungama magana ,kuma sannan ki fada masa yah turo a da maga ba tansa idan kuna hira,saboda da wurwuri ake dukan karfe kafin yayi sanyi"
Yau da safe kasancewar weekend ne babu zuwa wajen aiki,kowa yana gidansu,sallama akayiwa sameemah ana nemanta a waje,sai kace na miji babu alamar wani tambayar wani kafin ta fitah haka ta yafa gyalen abayar da take jikinta ta fita zuwa ganin mai sallamar.
Mamaki tayi da taga burgune da surayyah a bayan mashin dinsa suna kallnta fuskarsu dauke da murmushi,itama karisawa tayi kusansu saidai sabaninsu itah fuskarta babu alamar nuna wani reaction a ciki,
"Menene yah faru na ganku da ranar nana haka?"
"Shugaba alkhairi ne amma ga surayyah nan zaku shiga ciki tayi miki bayani,nizan je wani wajene idan na dawo zan maida ta gidan"
Kallon surayyah tayi tareda cewa,
"Ke Har yanzu kina yawon banzar koh baki dainaba,ba na gargadeki da bawa kowa lokacinki a araha ba,koh baki karanta takardar agreement din mu ba"
"Ahah shugaba wallahi na karanta,kuma ba na bin kowa yawo yanzu,kawai wannan din wanj abune daban kuma zanyi miki bayani"
Daga kai tayi kawai alamar taji kafin ta maida hankalinta kan burgu,
"Kai kumaa dama dazu nake shirin kiranka akN batun taron daza'ayi na senatoci ran Monday,ku tabbatar kun shiryah wajen kulada zirga zirgar mutane da cike hanya saboda kae a samu matsala"
"Shikenan zan samesu muyi maganar"
Sauka surayyah tayi daga kan mashin din tana kallon sameemah da idanuwanta so innocent kaman ba itah bace mai filllah rashin mutunci,itama sameemah kallonta tayi sau daya tareda zuyawa cikin gidan.
Ganin ta tafine yasa surayyah sake kallon burgu da alamar tambayar tabi ta kuma ta tsayah,
"Ki bi bayanta kawai kinga tayi mikk nisa,tunda Kika ga tayi haka tana nufin ki bi bayanta ne,saboda kimsan ba magana zatayimiki ba kaman sauran mutane"
Dahaka surayyah da dan gudu gudu saboda tayi mata dan nisa,tana yiwa kuma burgu bye bye wanda yah tada mashin din yana shirin barin wajen.
Tun daga shigarsu take ta kalle kallen cikin gidan,wanda yakeda kofofi da yawa a ciki,tana jin labarinsa amma wannan shine zuwanta na farko.
Wata kofah taga sun nufah sai gasu a dakin su sameemah,a bakin gado tah zauna yayinda sameemah ita,kuma tah fita waje sai gata da pure water a plate.
Ajiyewa tayi a gaban surayyah wanda ta hade jikinta waje dayah tana ta kalle kallen wajen ,
"Ke Kallon mai kike ne tunda zu,kincemin akwai abinda zaki fadamin kuma naga kinzo kinyi shiru baki ce komaiba"
"Ah Toh dama shugaba,ko na ce anty sameemah dama nida Ahmad(burgune )muke soyayya toh shine bamusan yanda abin zai faruba,sai muka yanke shawarar fadamiki tukunna duk yanda kika yanke akai"
"Nikuma nice mai yamke wa abinda yake cikin rayuwarku,ni babu ruwana da hakan saboda babu wanda nakeyiwa dole a cikin tsarina bare kuma saka shi dole sai yabi tsarina,saidia idan har ya yarda da cewa zai zauna dani toh wannan kuma daban"
"Eh dama ba haka bane anty sameemah,nice ma nace dole sai mun fadamiki,saboda iyayena sun amince da zamana a wajenki,duk da sunsan ba abune mai kyau ba nake niyyar yi amma kuma sun yarda dake ba niba,sannan tunda dukkanmu nidashi a karkashinki muke inaga ke yakamata ki shige mana gaba wajen hada kan iyayenmu da yimusu bayani,dan allah karkice a'a,ke kadai nake ganin zan samu goyon baya,wani abin a rayuwata rashin yar uwa mace da kuma rashin samun abokiyah ta gari mai hankali shiya fara saka raywata cikin hakan,saidai a yanzu ni ba ganinki na ke a iyah shugabata ba harda ma yar uwata,dan allah inaso ki daukeni a matsayin hakan"
Numfasawa sameemah tayi kafin tace,
"Shikenan inshaallah zanyi kokarin hakan tunda kin saka yardar ki a gareni"
"yawwa nagode anty sameemah Allah ya biyaki"
Daga haka suka bar zancen akan zata yi musu nata kokarin amma suma su sanar da iyayenna su akwai meeting dazasuyi da itah.
Dadine yakama surayyah har bata saN lokacin da ta rungume sameemah dan farinciki.
Tad'i suka dan fara yi bayan wannan zancen wanda kusam rabin maganar surayyah ce takeyi,dan itah bata iyha a zauna ana tadi ba irin na mata.
Sai wajen la'asar kafin burgu yazo yah dauketa suka tafi,wanda duk zamanta a dakim su salma basu kulata ba itama kuwa da ba baya bace a rashin mutunci sai abin yatafi a balance

Please Login or Register in order to submit comment