Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko a billboard bata lura da hotunan sa da labaru,jaridu? To wai waye baisan *Umar madaki* ba don ubanta?..... Ka rage wannan zafin ran ai komai ya wuce tunda gashi Alhamdulillah kafar ba rauni.
Nan sukayi fira sai goma ya haye sama,
Umaimah kuwa hajiya ta samu ta fada mata yanda sukayi. Ke umaimah kada fa ta kwace man ke don bazan bata ba, kinga Asma'u tayi aure su fiddausi kuma makaranta.
Tayi murmushi hajiya ba wannan ma ba kina ganin inje ba matsala? Kwarai kuwa babu kije ai duk gida ne nan da can nida ita ai kusan daya ne, gidan su idan zata kai sha biyun dare babu mai cigiya, washe gari ta shirya cikin kayan Asma'u ta saka wani material ruwan hoda taci gayun ta tace ta tafi gidan Alhaji yakuba. Yan kudaden da hajiya ta bata tayi amfani dasu, misalin karfe sha daya na rana, ga mamakin ta kowa ya ganeta akayi mata iso. Ta ware ido tayi ta kallo tana mamakin gidan, saboda tafiya har ta fara tsorata, tana shiga falon yana hayewa sama, yaji motsin shigowa amma bai waigo ba yana rufe kofa ta kalla. Murna tsalle, duk bakin umaimah sai ya mutu har hajiyar tayi mamaki tace yau uwani kinyi shiru.
Tayi murmushi kawai, nan da nan ta fahimceta ke saki jikin ki don Allah ta fara janta da labari, nan da nan ta washe har ana kyalkyatar dariya, dambun nama, kilishi, farfesun yan ciki, kaji, tsoka, peppe chicken shinkafa da miya, shawarma. Kai abinci barkatai umaimah ta kalle su mamah wannan gara haka sai dai kin manta da abu daya, da sauri tace menene?
Ja da yellow maganin zawo. Me zatayi ba dariya ba dariya takeyi har tana kwanciya. Umaimah ta na murmushi tace yo toh.
Wayarta tayi kara tasa hands free mamee ke dawa kike dariya haka? Kada fa kiyi ciwon ciki.
AF zo ka gaisa da uwani nayi tunanin ko kana barci ne,
Ina zuwa zan dauki wata waya mamee ya kashe, suka ci gaba da cin abincin.
Tana gamawa tace zata tafi. Tayi tayi ta jira ayi la'asar tace karfe uku zataje islamiya, ance umar baya da mata to ina aka samo yaran da keta guje guje?
Umaimah zata bar tambaya babu amsa? Tabbb
Mamah yaran waye wadannan wai?
'Ya ya nane kin San akwai kanne na biyu dake zaune da matayen su anan gidan.
Ta girgiza kai.
Ta kwaso mata kaya lesussuka atamfofi , turaruka da kudi masu yawa, aka bata bokitin dambun nama ta kira daya daga cikin yan aikin tace akirawo direba.
A'a hajiya zan hau adaidai ta kin San halin mutane yanzu aga mota ta ajiye ni unguwar mu sai a fara surutu kibarshi kawai. Ta kara yabawa da hankalin yarinyar.
Ta na fita ya fito sorry mamee ina bakuwar zanje meeting Lagos ya fada yana sauri sauri.
Ta tafi , a dawo lafiya. Ta bashi amsa a takaice, ya wuce da sauri, gaba daya layin gidan gewaye yake da sojoji, ta raba can gaba tana jiran adaidaita. Motocin suka raba ta suka wuce wani mugun birki aka ci ba tare da sunyo baya ba taga mutum ya fito yau sanye yake da suite ruwan toka duk da gabanta yau sai da ya fadi amma bata yarda ya gane ba.
Ubanwa ya baki ikon tsayawa layin nan?
Ta kalleshi a wulakance ta tabe baki kayya dai, ga mutum har mutum amma *fanko* yanzu kai baka jin kunyar zagi?
Ke ya daka mata tsawa tare da shako wuyanta ita ma tace kai..... Ko an fada ma wadancen jerin gwanon abokan ka naka zasu firgitani. Tuni nasan baka iya tare fada da kanka sai kayi gayya ga katti can majiya karfi a waje ka kasa biye musu sai ni to gaba da gabanta wallahi sojojin gidanmu zansa yau suyi maka mugun duka. Ya kalleta sakaka sojoji? Ko kana wasa inyi waya?
Yasa kafa ya harbar da bokitin dambun ya tarwatse a titi ya ce sojojin gidan ubanwa?
Ta harzuka na gidan *yaya umar madaki*...........

*Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣0⃣4⃣
......... Ya sharara mata wani kwakkwaran mari. Ta gigice ta kidime ta runtse ido kanta na juyawa ta rasa duniyar da take, tana jin hancin ta na tsiyaya amma bata San shin majina ce, ruwa ne ko jini ba, sama sama take jiyo amon muryar sa. Wallahi wallahi ranar da kika kara ambaton sunan nan da wannan shegen bakin naki sai kin gane kurenki. Ya ingizata tayi baya ta fadi saman bokitin da ya harbar. Kin ga layin nan? Idan kika kara biyoshi na rantse da Allah sai na batar dake Nigeria ko kuwa waye ubanki......
Ya sa kafa ya shuri dambun naman dake baje kasa ya watsa mata ga jiki.
Hazo hazo take ganin tafiyar sa har ya isa inda motocin suke, tafi mintuna ashirin kafin kanta ya fara saisaita, ganin jini face face a jikin hijabin ta yasa ta kara kidimewa. Tayi saurin toshe hancin da sauri cike da tsoron irin jinin dake zuba. Ta rushe da wani irin kuka wannan masifa dame tayi kama ni umaimah?
Yau mashin ta hawo ba inda tayi ma tsinke sai gidan Alhaji yakuba. Hankalin hajiya ya tashi amma sai tayi mata karya da hatsari sukayi a hanya, barin fuskarta kumbure. Wallahi sai na zubda mishi jini nima ta fada a hankali.
Hajiya ki dauki kayan nan na baki idan naje dasu gida kin tabbar masifar da zasu janyo mun.
A a zan dai ajiye miki, babu abinda zanyi dasu nikam,
Wallahi na baki, ai ba roko na kikayi ba hasali ma duka daga ciki ba abinda zan iya amfani dashi.
Shiru kawai tayi mata.
Tana shiga gida ta iske su lubabatu sun fiddo jakar kayan ta suna ta rububin rabawa, tana shigowa rayya tayi saurin tarar ta ina son na jikin ta wallahi na riga.
Ko kadan bataji komai ba domin idan da sabo ta saba tana yin magana iyayen zasu ce tabar musu tunda gobe ma wasu zata samo. Su kuma sai su duba tsofaffi da suka gaji dasu cikin nasu su bata, kai kawai ta girgiza ta wuce tana cewa qala za a fadawa yaya Abba karya da gaskiya ace ta zagi iyayen ta ya lakada mata tsinannen duka da waya.
Ta dauki naira goma ta siyo reza sabuwa ta daure a habar kallabi.
Baban su idan ya fita shidda na safe baya dawowa sai shabiyun dare kasuwa kullum.
Mamar umar kuwa waya ta dauka ta kira hajiya, bayan sun gaisa ta ce bakuwa ta dawo lafiya?
Wane lafiya dan adaidaita ya tandarata da kasa duk ta jeme fuska, subhanallahi tana ina? Ta tafi gida ai da sauki na bata magani nan.
Duk sai ta kidime, kwantar da hankalinki wallahi da sauki, to shi kenan ta ajiye waya, amma ta kasa daurewa sai kawai tace azo a kaita, tana kwance daki suka shigo da goggo, zumbur ta mike, ohh uwani ashe haduwa kikayi da tsautsayi haka? Tayi zuru zuru mutanen gidan chirko chirko....... Mamah da hajiya ta aikeni gidan ki wajen dawowa muka fadi da adaidaita ai da sauki ta karasa maganar tana satar kallon su goggo.
Zata kara magana tayi saurin cewa gasu goggo da yan uwana hajiya.
Ai mun gaisa, ya jikin?
Alhamdulillah,
Zaki shiga wurin hajiyar?
Data zo zatayi magana sai umaimar ta kakalo wata har hajiyar ta fahimta tunda ba yarinya bace, Allah ya bada lafiya ta mike, Don Allah idan mahaifinta yazo ina neman alfarma a bani umaimah tana zuwa tana kama mun aiki ni din yar uwar hajiya....umaimah tayi karaf gidan Alhaji yakuba hajiyar su fiddausi , ta balle jaka ta damtso yan dari biyar biyar ta bawa goggo jummai ga wannan a rabawa yara.
Wufff goggo hansatu ta wafce too too Allah ya biya hajiya za a fada mishi ai duk an zama daya, sukayi daki umaimah ta rakata har mota sannan ta dawo, bata bi ta Kansu ba domin tasan naira babu ita ciki,
Suna isa ta tarar dashi falo a tsaye, yana safa da marwa, mamee ya tunkaro ta rai bace lillahi wa rasuluhi wannan dame yayi kama yaya zaki ringa fita any how na dawo kowa yace baisan Ina... Gidan uwaka naje, wai har yaushe zakayi hankali umar don iyayenka nice na haifeka ko kaine ka haifeni?
Yarinya tazo guna girma da arziki ta yi hatsari sai in ki zuwa dubo ta? Mamee kuma ko waya bazakiyi man ba kin San sarai abubuwan dake faruwa....bazan kiraka ba din na ce anki a kiraka ya wuce cikin fushi sai kuma ya yi sukuku ya bita mamee nifa duk abin nan lafiyar ki nake ji .... Ta juyo a hasale ni kuma lafiyar uwani nake ji....
Sai ya rungumota ta baya wai wacece wannan uwani dake Neman kwace man mamee? Na fara kishi fa ya saketa tare da tirjewa kamar karamin yaro yanda yakeyi mata ta ingijeshi kai tafi can ta shige daki,bya bita yayi ta lallashi har sai da ta washe, na dauko uwani aiki zaka ringa biyanta albashi, yayi murmushi an gama nawa kika yanka mata? Dubu talatin.....talatin mamee hada bangwayen gidan zata ringa wankewa? Idan baka iyawa ni na biyata..... Inji waye ko miliyan kika ce air dole a biya mamee duk sukayi dariya, Karfe biyar goggo ta tasheta, Ke tashi Alhaji ya amince da zuwa aikin ki maza kiyi man wanke wanke don ki tafi da wuri, bata ce komai ba ta tashi bayan ta gama sallah ta hau gyarawa bakwai tabar gidan ta sami hajiya ta fada mata komai har ta na kwallah. Nasan za a rina kawai raina yaban sai ta amsheki , ki kyalesu Kansu suke wulakantawa umaimah kedai ki ci gaba da tsare gaskiyar ki baki sata na shaide ki kada ki yarda ki wulakanta kanki kinji?
Tun daga farkon layi tace a ajiyeta ta fiddo reza ta damtse a hannu ya Allah ka hada ni da mugun nan azzalumi, tafe take amma layin kamar anyi Shara shigowa farkon layin sojoji ne tsare da ba kowa suke bari ya ratso ba itama ansan da zuwanta tun jiya, ta fara hango tsiraran sojoji na kara kaina data fara dumfarar gidan kamar ance ta waiga baya kawai taga mutum na sassarfa da kayan gudu. Ta ware ido wallahi shine tafe kawai sai ta tsaya chak!
Daya, biyu, uku,..... Tara...... Kawai yazo zai gifta ta kunnen sa da ear piece ko alama bai lura da mutum ba hanakalin sa na can hannu tasa ta damko cinyar hannun sa ya dawo baya da sauri kafin ya hankalta ta farde mishi tsakiyar hannu ta kwasa a guje. Jini ya fartso ya dafe hannun innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ya bita da kallo har ta kule, nan ta kwana? Yarinyar nan ko aljana ce ni umar?
Jini ke tarara kamar fanfo haka ya kara gidan yace maza a tado doctor, sai da akayi mishi dinki, azabar duniya ta addabeshi yazanyi da yarinyar nan kada tasa inyi abinda ban da niyya anya bazan kashe ta ba kuwa?
Idanun sa jawur kamar yayi ta kurma ihu, a kidime mamee ta shigo umar rauni kaji? Wallahi mamee Yankewa nayi,
Dami?
Yayi shiru...
Kai dami ka yanke?
Ina jin ko wuka ce?
Kana jin? Baka da tabbas ne? Yayi dabur dabur wuka ce mamee ya ballo magunguna ya sha ta bishi da kallo umar menene ya faru?
Ya kakaro murmushi is okay mamee bari in watsa ruwa ya mike zuwa toilet ta bishi da ido kawai, ya hada kai da bango ya dafe kansa kashe ta zanyi tabbas wani yayi hayar yarinyar nan don ta shigo rayuwa ta negatively I must kill her.....
Mama lafiya? Umaimah ta riketa, kaini yau naga masifa wallahi umar ne yayi mugun rauni, wannan zafin rai na wannan yaro ya Allah ka rage mishi.
Ta zaunar da ita Amin mamah ungo tea kisha ko in kwaso miki kalacin nan?
A a barshi ya shiga wanka daya fito zamu karya. Mama karfe sha daya fa bakyajin yunwa? Ko ina ji dole in jirashi in ba haka ba to bazai ci komai ba zai fita, gashi baya cin abincin ko ina sai nan.
To shi kenan yanzu ni meye aikina, eh wallahi har yanzu tunani ma nakeyi
Ikon Allah umaimah tace a hankali ta mike muje bisa table kafin ya fito. Kema dauko plate ki ajiye nan ta nuna mata kujera jeri jeri haka ake ta zarya zuwa gaida ta ma'aikatan gidan da matan kannen ta, duk Wanda yazo sai tace ga uwani itama daga yau a gidan nan zata ringa zama...... karar rufewar kofar ya antayo wani mugun da dadden kamshi tayi saurin kallon inda karar ta fito zumbur ta mike akayi rashin sa'a kujerar tayi baya a wuntsula tayi saurin tashi tana baya baya a firgice, ke uwani lafiya kai rike man ita mamee ta fada ganin tana niyyar kwasawa da gudu duk ta fita hayyacinta.
Step din karshe idanun sa suka sauka kanta ya kara bude ido ko mafarki yakeyi................

*Maman Abdallah*

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣0⃣5⃣

.....Mafarki yakeyi ko me?
Da gudu ya karasa saukowa ganin ta kwasa guje, karku bari ta fita...... Ya fada da karfi damka daya kawu karami yayi mata sai kawai ta sulale kasa tare da kurma ihu wayyo na shiga uku.........
Mamee ta rikice ganin umar ya finciko 'yar mutane ubanwa kika zo yi anan....kai dakata, ta finciko ta da karfi ta kuwa makalkaleta ki dubi Allah da manzon sa ki ceceni na tuba mugu ne...... Ya zagayo zai damko ta yana huci duk suka juya tare da mameee kai wai meye haka, wallahi yau sai naga bayan yarinyar nan na amince idan ta mutu nima a kasheni.
Hankalin mamee ya tashi matuka don haihuwar danayi maka umar ka saurara man.....
Umaimah ta hadiye wani mugun miyau tana tuno maganar sa, *wallahi wallahi ko layin gidan nan kika kara biyowa sai na sanya an batar dake......*

Ta zaro ido abubuwan da suka dunga faruwa suna dawo mata. Na shiga uku na jefa kaina masifa ni umaimah cikin ta ya dunga wani irin rugugi. Yunkuri yakeyi mamee na karewa, mamee ki dubi Allah ki matsa, bazan matsa ba kayi aika aika, to kyale yarinyar nan tabar gidan nan kada in saba umarnin ki yau.
Sai dai in bita mu tafi tare,......ya zaro ido what??

Eh wallahi fitar uwani gidan nan fita fita yau, ya dafe kai wayyoooo mamee kar kija in saba miki yau ki kori yarinyar nan kada inyi kisa.....kisa????
Umaimah tayi sama da numfashi wayyo na shiga uku so takeyi ta kwace mamee ta riketa gamm, ya runtse ido da karfi,
Me ye ya hada ka da ita?
Duk barin miyar da nake zuwa miki dashi 'yar iskar yarinyar nan ce, ita ce.......dazun.... Umaimah ta zaro ido jin zai fadi ta yanka shi tace wallahi mamee shine ya fara watsa man ajiki ni bansan wanene shi ba.... Don ubanki sai kinsan wanene ni zaki mutuntani?
Ta juyo ta bayan mamee ta motsa baki yana kallo *badai ubana ba* sarai ya karanto me ta fada ya zaro ido ya yunkuro ubanme kike cewa?
Kai tsaya yaushe tayi magana?
Wai mamee menene haka yarinyar nan munafuka ce yau sai naji Wanda ya turo ta wurina.... Wazai turo ta umar?
Jikin mamee har ya fara ciwo wannan rigima, kawai sai dubara ta fado mata. Ta fara layi da kai.
Mamee calm down ki zauna karki shiga abinda babu ruwanki.
Na fita ciki kayi abinda kaga dama tunda baza ka saurari abinda zan fada maka ba, kuruciya ce kayi hakuri........ Kawai sai ya yashi fuuuu yayi sama.
Umaimah na ganin haka ta shiga neman takalmi, ina zaki je?
Kiyi hakuri mamah amma bani iya wannan aikin. Saboda baki kaunata uwani? Don kinga na kwallafa rai akanki bani da 'ya mace ganin ki nake tamkar diyata. Ni na haifi umar kina ganin duk sabanin da kuka samu zan yarda ya cuta miki ina kallo? Duk zuciyar sa dole yabi umarnin maganata.
Ki dubi girman Allah ki zauna dani kina debe mani kewa.
Idan aka wayi gari kuma na 6ace wa zai nemo ni? Ta fada a zuci, a zahiri sai kawai ta fashe da kuka wallahi mama kuskure ne.
Na sani uwani nice shaida.
Ki kwantar da hankalin ki zan lallashe shi.
Haka dai ta wuni sukuku, karfe biyar zata tafi tana ta dube duben takalmi dagowar da zatayi daga mutum tsaye kanta. Tayi saurin ja da baya, ya dalla mata harara, zuwa nayi in gargade ki , na rantse da Allah zakiyi ma mamee aiki gidan nan kamar yanda ta bukata idan kika saki ko da gigi na ganki kusa dani sai dai uwarki ta haifi wata haka zalika Qala idan kika ce dani sai kin raina kanki banson ganin ki banson jin maganar ki......ta na gama ji taci gaba da dube dube.
Ya fincikota ko bakiji ina magana?
Ta kalleshi shekeke ikon Allah ina ce kunne keji ko? Ka ce baka son in maka magana to amsar me zan baka. Ka fada naji sai ka shafan lafiya. Ko kuwa yanzu da kazo kiranka nayi nida kai waya tarad da wani..... Ya makaro wuyanta gidana kike hattara....... Yi maza kasheni inyi shahada kai kuma ka karawa kanka bala'i gata dukiya gata kisan kai... Ya ingijeta ta fadi tana tari *mugu kawai* Wanda bai iya fada da katti sai yarinya..... Ya zaburo...kai kai...... Wai umar menene haka?
Zaiyi magana umaimah ta rigashi ina duba takalmi kawai yazo yana ta zagina hada makuremun wuya ya faffalla mun mari....ban mareki ba amma yanzu.....
Ina ce mun gama maganar nan da kai ko? Na lura kafi kaunar bacin raina fiye da farin ciki don haka tunda ka nunawa duniya ban isa dakai ba kaje kayi abinda kaga dama. Ta na fadar ta juya.
Umaimah na ganin ta shige ciki ta buga tsalle ahayye a taba ni asha tsinuwar uwa ta yi mishi gwalo ta ruga.
Duk iyakar bincike yayi ya kuma sanya an mishi akan umaimah amma tabbas babu alamar abinda takeyi wani ne ya aiko ta hasali ma tatihin yarinyar mamaki ya bashi ganin wauta da kasada yarinya marar galihu haka take da *gut* na ja dashi.
Satinsa uku baya zama kullum yana yawon meeting wani ma cikin jirgi akeyin sa.
Hakan yasa umaimah ta saki jiki sosai da mamee ita kadai ke gyara mata bed room da toilet sai ta hana kowa shiga, idan ta gama malamin dake kara ta karatu yazo sai Suyi tare umaimar tafi ganewa don haka idan ya tafi ita ce ke dagewa har sai taga mamee din ta haddace, sannan suci abinci tare kafin a zauna ana labari umaimar na basu dariya da iyashegen ta.
Kowa ya fara sabawa da ita.
Mamee ta kalleta wannan sarkin rashin yardan da zaki je ki gyara mishi daki kafin ya dawo tunda ya tafi da mika'ilu ina da spare mukulli a hannu na tunda bazai gane ba sai muyi shiru da bakin mu saboda cikin sharudan da ya kindaya man ciki hada kada ki kuskura ko matattakalan benen sa kije.
Mamah tunda har yace haka yanzu idan ya dawo kwatsam fa? Daga saman zai tulloni kafin ki zo na zama gari.
Mamee ta tuntsure da dariya kai uwani hoo wai gari. Tayi murmushi Allah kuwa.
Ki barshi da kayanshi idan yazo sa gyara abinsa.
Bazaiji dadin zama nan din ba don mafi yawa idan yayi kwanaki haka to anan yake sauka baya hawa saman sai an gama gyarawa.
Da zaki fara yau zuwa gobe duk kin kammala, shiru kawai tayi ta rasa yanda zata nuna rashin amincewar ta, ungo mukullin ta karba kawai.
Dukan tara tara kirjinta ya ringa yi.
Makeken falo ta tarar daga gefen sa matattakala ce tana lekawa taga swimming pool ne zata kaika da wurin shakatawa wurin kansa abin kallo ne kujeru kala kala group group group. Ta duba dama tabi wata hanya daki ne karo kamar hall da kujeru ta tabe baki meeting akeyi anan ko? Ta dawo baya ta shiga wani daki makeken bedroom yasha kayan alatuta hango kofa ta bude tayi ma kewayen wani kallo ganin jaridu da TV ta zaro ido iyayi..... Watan idan ana kashi ana karatu ko kallo ta tuntsure da dariya tabar dakin, ai wallahi sai naga kwaf kwaf, ta fada wata hanya kayan motsa jiki ta gani ta kale wani keke Tabb ai sai nasha banza Ashe auto ne taji ankwasa da ita guje ana jijjigawa timmmm ta wuntsulo tana haki cike da tsoro ta baro wurin.
Sai kuma ta kama dariya,
Umm bari dai inyi abinda ya kawo ni. Ta shiga gyara ta dunga canza tsarin komi tana kimtsawa gyaran da ya kaita har magariba abinda ya bata tsoro bedroom dinsa durowowi ta ringa gani da kudi shirye , kasan kafet kudi wasu jakunkuna data bude kudi, tana shirin fadawa kitchen taji kiran sallah tayo kasa da sauri. Mama kada dare yayi Gobe na karasa, tana tsaya tsaya amma ina tayi gida.
Washe gari sauri sauri ta gama aikin mamee ta haye saman don ta gama da wuri, ta gyara sosai ko ina ta na yi tana korafi. Musamman kitchen da gani mugun ci gareshi ko ina ka gani kitchen da kewaye an ci ai dole ayi kashi ta bushe da dariya ta gama tsaf ta sa abin kamshi kenan hanne ta hawo da gudu uwani kiyi Sauri ga Alhaji nan inji hajiya........nan tabarta tsaye ta watsa da gudu. Tana isa gaban hajiya yana turo kofa tayi ciki da sauri bai ganta ba, hanne yabi da ido tana saukowa ya daka mata tsawa ke ubanwa kikayo sama? Ni na aiketa mamee ta katse shi.
Ya dade falon har mika'il yagama hawa da kayan ya dawo yallabai an gama. Har ka kimtsa ko ina?
Ai na tarar da kamar ma yanzu aka gama gyara wurin,
Ya watsa hannuwa mamee kenan ya haye sama, gyaran yasha ban ban da Wanda ake masa. Yayi suka bisa gado ya runtse ido yana shakar kamshin dake tashi,
Umaimah kuwa sauri sauri ta bar gidan mamee na tsaya ki taya ni kwance tsaraba tana gobe na gani har takai bakin kofa tace af ke gafa waya dazun na bada aka siyo miki saboda tsaren lalura ta buga tsalle toh tayi waje.
Tana fita ya sauko mamee wa kika sanya yayi mun gyara haka?
Ta zaro ido an maka barna ne?
Da a makaranta ne yanda nayi tambayar nan kika tambayeni punishing din ki za ayi. Kai sai kayi yanzu don kaniyarka, ya kyalkyace da dariya ban isa ba my love.
Yayi kyau kwarai naga abin wani sabo an kara gyara man dressing mirror an shirya flowers an canza ma komai tsari yayi kyau.
To madallah zan ringa sa Wanda nasa yau tunda ya maka. Ya tuno hanne tana saukowa watan ita mamee tasanya.
Ta sauya zancen da ina maganar matar da mukayi kace sai karshen watan nan? To ai yau sha hudu ga, zata kara magana wayarsa tayi kara yace ina zuwa ya haye sama.
Yau ta makara sakamakon wanki da tayi zaune suke bisa table suna kalaci ta shigo gabanta yayi mugun faduwa, ta shigo sukuku mamah ina kwana..... Ya daka mata tsawa mamar ubanwa baki ce mata hajiya yanda kowa ke fadi? .....ina ruwanka da ita? Mamee ta katse shi rai bace,
ta balla mishi harara ta wuce, ya mike wakike yiwa wannan kallo? Tayi ciki da gudu.........

*UWAR ABDALLAH*

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣0⃣6⃣

Assshhha dai, mamee ta kalleshi wannan fa abin kunya kake zubdawa kana kaskantar da kanka, ka fita harkar ta ka kyaleta ka daina biye mata, ka ce ko magana babu tsakanin ku meye na tanka mata?
Na lura dai kinfi kaunar yarinyar can dani ko? To ki zauna da ita........ Fuuuuu ya haye sama.
Ikon Allah ta fada tare da binshi da kallo ga mamakinta taga yana janye da jaka, ina zuwa?
Ya mata banza

Please Login or Register in order to submit comment