Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

_✨UNCLE NE...!!✨_







_✍🏼NIMCYLUV_



*1*






Allahamdulillah Allahamdulillah Thanks to almighty Allah (swt) for giving me opportunity to start this book, Ma sha Allah nasan You have been waiting for me so long,to NIMCYLUV is back sai a KAKKAƁE zani a gyara zama, special greeting to Maimuna Abdullah(heroine) love you wix all my hrt, secondly Hafsat Rano alkairin Allah ya kai maki,Queen Nasmer my sturbbon friend love you,How can I forget my lovely fans...? kuna raina kamar yadda kuke saka ran ganin littafaina thanks for the love and care hrt You all😍 here is my new book UNCLE NE am sorry to say na ajjiye maganar TUGGU BIYU i have a big issues da nayi hakan so guys follow my pen...love my story, dedicated to my papa ALAHAJI SULAIMAN DAGACIN JA'OJI.


wanda bai karanta book ɗin nan ba,bazan ce an barshi a baya ba domin a koda yaushe yana iya karantawa,amma idan ba'a fara dakai ba..it is going to be a hit that i promise You,nayi wannan littafin ne from The very depth of my heart,wani time ɗin nai dry wani lokacin nai hawaye,wani tym ɗin ina jin waƙa.


officially welcome You to the very frist chapter of UNCLE NE..


_Bisimillah_






IBADAN
is the the capital and most populous city of Oyo state in Nigeria.

SANGO AREA

Unguwar Masu kuɗi ce,Unguwa ce da babu wanda ya damu da rayuwar wani,Unguwa ce mai cike da Attajirai,Malamai,haɗi da ƴan boko,Haka kuma Unguwa ce mai cike da ƴan duniya wanda idanunsu suke a buɗe,basa jin wa'azi balle faɗa,haka nan babu wanda ya isa ya tunkaresu da niyyar gaya masu kuskurensu.

Dugun layine wanda yake shimfiɗe da lafiyayyan titi wanda ya ƙara fito da ƙyan unguwar.
Wasu jajaye fitilone sukaiwa titin unguwar ƙawanya,wanda a kullum suke haska unguwar musamman cikin dare,gefe da gefen titin wasu green flowers ne masu ƙyau wanda suke fidda wani daddaɗan ƙamshi.

Can kusan ƙarshen layin wani haɗaɗɗan gidane ginin zamani,tun daga jikin tafkeken get ɗin zaka san tabbas wannan gidan bana ƙana nan mutane bane,ajikin get ɗin anyi rubutu inda aka rubuta hause no 133.

Sosai harabar gidan taƙawatu da kurayan furanni na zamani masu ƙyau da tsari,Compound ɗin gidan cike yake da manyan motoci na zamani irinsu,boggatti,ferari,da sauransu.
Yanayin ginin gidan irin mai sama da ƙasa ɗinanne ma'ana dai ginin bene mai hawa biyu.

Side ɗin parko na gidan wanda ya kasance hawan farko na gidan,babban parlour zaka fara tararwa gefen parlour'n kuma ɗakuna ne masu ɗan yawa kusan bedroom ɗin shida,left hand ɗina nayi domin shine yafi jan hankalina fiye da sauran part ɗin, Tun daga ƙaramin parlour'n dake cikin part ɗin na fara jiyo fitar numfashi mai kama dana zaucewa a hankali na tura kaina cikin bedroom ɗin kasancewar a buɗe yake,saurin tsayawa nayi sabida ganin wata ƙyaƙƙyawar matashiyar mata wacce aƙalla ba zata huce shekara ashirin da biyar ba zuwa shida.

Tana durƙoshe gaban bed ɗin dake ɗakin yayinda hannunta ke riƙe da gadon gaba ɗaya jikinta rawa yake,banda nishi da gurnanin wahala babu abinda ke fita a bakinta,yayinda turtsetsen cikinta ya sauka zuwa mararta banda juyawa da motsi babu abinda “ƊAN” cikin nata yake,da alamu shima ya ƙago yazo duniya,karkarwar jikin tane ya tsananta gaba ɗaya ta jigata ta fita haiyacinta banda kiran sunan Allah babu abinda bakinta yake ke faɗi,Can ƙasan zuciyarta kowa maganar data keson furtawa a saman bakinta tane ta kasa,burinta bai huce bakinta ya buɗe ta samu damar faɗin abinda ke damunta cikin rai da kuma zuciyarta,Runtsa idanunta tayi da ƙarfin sabida wani juyi da abin cikinta yay tare da naushin mararta nan take jini ya ɓalle mata ya soma zuba,cikin yanayin na fitar hayyaci tare da zaucewa haɗi da fidda rai ta ɓude baki da ƙyar tace.

"Ya hayyuu ya ƙayyumuu
ya kaliƙu ya zul arshidd majidd,ya fa'alulluma yurid biraha matika astagisuuu"

Takai ƙarshen addu'ar tana sakin wani fitinanan nishi wanda ya kusa ta fiya da numfashinta ya rabbi nan take wani..


Kamar amafarki Mameey dake ƙwance bisa tangamemen royal bed ɗinta ta jiyo sautin numfashin Zulfa cikin kunnuwanta lumshe idanu tayi tana jin kamar a magagin barci take, da sauri ta miƙe zaune daga ƙwancen da take wani irin hantsilawa Mameey tayi daga gadon zuwa ƙasan gadon,a gigice ta fara gyara ɗaurin zaninta dake kuncewa sabida fargaba,tabbas idan bata manta ba yaune E.D.D Zulfa ya cika gaba ɗaya ta manta,cikin tsoro fargaba kiɗima tashin hankali ta fara sakkowa daga stairs ɗin benen.

Tun a babban parlour ta fahimci aƙwai matsala kuma ta ƙara tabbatarwa kanta Zulfa naƙoda take da sassarfa ta ƙarasa shiga cikin part ɗin Zulfa,cikin sauri Mameey ta ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin,tana shiga ta samu Zulfa durƙoshe cikin jinin wanda ya ɓata jikinta gaba ɗaya,da sauri ta ƙarasa wajanta tana salati tare da faɗin.

"Zulfa mene zan gani haka?kika zauna cikin ciwo kin san illar duguwar naƙuda kowa?ohhh ni Salamatu yau naga abinda yafi ƙarfina wannan wanne irin jinine haka?mun shiga uku",

Ta faɗi hakan tana sakin kukan tausayi halin da Zulfan ke ciki,sabida ganin jinin dake zuba ta jikinta ga kuma yadda numfashinta ke sarƙewa jikinta banda rawa babu abinda yake,da hanzari ta ƙarasa matsawa inda take sabida kan babyn da taga yana fitowa,wata jijjiga Zulfa ta fara idanunta na kafewa.

Ganin hakan yasa Mameey sakinta tare da ficewa da gudu tana tafe tana ƙwala kiran sunan Alhaji!! Alhaji!! Alhaji!!!

Alhaji Kabeer na kishin giɗe saman wata lafiyayyiyar sofa,hannunsa dafe da saitin zuciyarsa,yana jin yadda take buga masa da ƙarfi,ga wani raɗaɗi da ɗaci daya keji a cikin maƙoshinsa,gefe guda kuma yana jin tsoro da fargaba haɗi da zullumi wanda bai san kona menene ba.
Ya rasa dalilin daya sanya yake mafalki mara ƙyau akan Zulfansa mace mafi soyuwa a cikin ransa,tabbas bazai jure ganinsa cikin wannan halin mafalkinba,kamar yadda bazai jure ganin Zulfa cikin wani hali ba.

Saurin buɗe idanunsa yay jin muryar uwar gidansa na kiran sunansa,da sauri ya dira daga kan sofar yana fita sukaci karo da Salmerh a birgice ya kalli Salmerh tare da faɗin..

"Salmerh mene ya sami Zulfa?..kada ki sake bakinki ya faɗi babban kalamai dazai sanya zuciyata bugawa.."

Bakinta na rawa tace

"Zulfa haihuwa inajin.."bai bari ta ƙarasa maganar ba ya ƙwasa da gudu zuwa part ɗin Zulfa.
da gudu Mameey ta mara masa baya,suna zuwa tana haihuwa ganin zata danne jaririn ya sanya Alhaji Kabeer saurin isa gareta,yana zuwa ya saka hannu ya gyara mata zama,tare da amsar rezar hannun Mameey ya yanke cibiya,cikin ikon Allah a lkcn mahaifa ta faɗo,yana ganin haka ya saka hannu ya miƙar da ita tsaye cikin murna da farin ciki ya rungometa a jikinsa yana shafa sumar kanta idanunsa fal hawayen farin ciki,bai taɓa tunanin zai samu haihuwa nan kusa ba,sai gashi ubangiji ya azurtashi da ita a lkcn dabai taɓa tunanin samunta ba,tabbas ya yarda da wannan kalmar da ake cewa inda rai da rabo,haka kuma mutum baya fidda rai da samun rahamar ubangiji,domin shine mai bayarwa a lkcn da yaso haka kuma shine mai hanawa a lkcn dayaso,wasu hawayene suka fito daga cikin idanunsa cikin muryar farin ciki yace.

"Thank you soo much my Anuuu,Allah yay maki albarka nagode sosai da ƙyautarki nagode Allah ina sonki Allah ya baki lafiya"

Mameey janye jaririn tayi jin yana tsala kuka a wani zani mai ƙyauta ta ɗaukesa,kana ta zaune bakin bed,catton da zaitun ta fara goge masa jiki da ita,murmushi tayi ganin yadda yake ƙoƙarin sanya hannu a baki da alama da yunwa yazo,sai tsala kuka yake,a cikin ranta take jinjina ƙyan yaron da kuma baiwar da ubangiji yay masa,domin ƙwayar idanunsa ta kasance blue ce,kamarta turawa,ga wani ɗan cindo a gefe yatsanshi.

A sanyaye Zulfa ta rungome mijinta Alhaji Kabeer idanunta na zubar da ƙwalla tace "Yaa rahamanu"murmushi yay tare da sumbatar goshinta,kamar an tsikareta ta sanya hannu ta ture Alhaji Kabeer daga jikinta,a hankali ta fara yin baya ganin hakan ya ƙara matsuwa kusa da ita yana shirin kamata yaji ta fasa wata uwar ƙara,a gigice ya ƙarasa wajanta kafin ya riƙeta tasa hannu ta hankaɗesa tare dayin waje da gudu jinin haihuwa nabin jikinta....



Idan kun bazashi ya amsu wajan mutane za kujine
08119237616
_✨ UNCLE NE ✨_






_✍🏼 NIMCYLUV_


*2*







Duk inda ta taka sai jini ya zuba hakan ya tabbatar masa da cewa ba ƙaramin jini ke zuba a jikinta ba,gudu take sosai tamkar ba mara lafiya wacce ta haihu ba, Yadda take indai ba ficewa tayi daga hankalinta ba babu shakka zai iya cewa aljanunta ne suka ƙara mata gudu ganin yadda take gudun ko joyowa ba tayi, Duk yadda yaso yacim mata kasawa yay sai nisa take masa,kasan cewar harabar gidan nada girma sosai yasa tun daga nesa yake ƙwalawa mai gadi kira,amma ya makara sabida Malam Habu yana ɗakinsa yana sharara bacci kamar matacce,ganin harta isa bakin ƙofar wajan gate tana shirin buɗewa yasa Alhaji Kabeer buɗe murya iya ƙarfinsa jikinsa duk rawa yake cikin kiɗima da firgici yace,
"No!! Zulfa stop kada ki fita bakki ganin halin da kike ciki ne?zoga babbynmu na kuka ke kaɗai yake buƙata,ke ya keso yaji ɗumin jikinki come back please my dear innalillahi wa'inna ilaihir raji'un meke shirin faruwa da Zulfana menene hakan?wanne irin gudu ne haka?ya rabbi ka kawomin ɗauki"
ya faɗa idanunsa na kawo hawaye,ina Zulfa kam sam bata cikin hayyacinta balle taji abinda yake faɗa,domin da zarar tayi niyyar juyawa sai taji ihu da gurnani sun cika mara kunne,can gabanta kuma wata inuwa da kuma tarin bishiyo haɗi da furanni masu ƙyau take ganuwa,abin mamakin idan ta kusa da bishiyoyin sai taga sun ƙara yi mata nisan gaske,hakan tasa take ƙara gudu domin ta isa garesu cikin sauri tasa hannu ta buɗe ƙofar dake jikin gate ɗin,tana buɗe ƙofar ta fice da gudu.

Layine irinna masu kuɗi babu kowa duk suna cikin gida jensu hakan ya bawa Zulfa damar damar gudu a tsakiyar layin a haka harta isa babban titi inda manyan motoci suke shigewa.

Ɓan garan Alhaji Kabeer duk yadda yaso ya buɗe ƙofar gate ɗin kasawa yayi sabida cijewa da ƙofar tayi sakamaƙon rufewar da Zulfa tayi mata da ƙarfi wajan fita,cikin zafin nama yasa ƙafa ya daki ƙofar nan take ƙofar ya buɗe hakan yay dai-dai da lokacin Malam Habu mai gadi ya fito daga cikin ɗakinsa hannunsa ɗauke da gora yana shirin kaiwa Alhaji Kabeer duka a tunaninsa wanine ya shigo gidan kasan cewar bacci yake shiyasa bai gane waye a bakin gate ɗin ba,cikin sauri haɗi da jarumta Alhaji Kabeer ya fice daga cikin gidan tare da soma ke waye layin yana faman ƙwalla kiran sunanta Zulfa!! Zulfa!! Zulfa!! amma babu ita babu labarinta,Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ya fara ambata a fili,ina zashi?ina zai ganta?wazai tambaya?shin mene ma ya fiti da ita a halin da take ciki?menene ya sameta?wannne irin firgicine haka wanda har zai saka ta manta da “ƊAN” data haifa,ya rabbi ka kawomin ɗauke wannan wanne irin abune haka?meke shirin faruwa ne damu baki ɗaya,zubewa yay a tsakiyar layin tare da kifa kansa a tsakanin cinyoyinsa duk yadda yaso ya daure kasawa yay,cikin raunin zuciya ya fashe da kuka,ya ɗauki a ƙalla kusan 30minutes yana durƙoshe kafin ya miƙe da sauri tare da ɗaukan wayarsa dake cikin aljihu ya fara dailing wata number,ringing ɗin farko akai picking call daga can ɓangaren Acp Anwar ya gyara tsaiwarsa tare da saurin ɗaga hannu ya buga ƙafa yace.
"Evening sir fatan lafiya? domin na daɗe banga miss call naka ba"
Numfashi Alhaji Kabeer ya sauke mai ƙarfi tare dasa hannu ya share zufar dake bin saman ƙoshinsa,gaba ɗaya jikinsa rawa yake kallo guda zakai masa kasan cewa baya cikin hayya cinsa,ga kuma tsantsar tashin hankalin dake yawo cikin ƙwayar idanunsa,lokaci guda duk ya sosoce tamkar ba Alhaji Kabeer Mai atile ba,ga yadda narkakkun idanunsa suka sauya kala daga fari zuwa jaa jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa-raɗa,jin yay shuru babu alamun zai magana yasa Acp Anwar ƙara kamewa waje guda haɗi girgiza kai cikin kiɗima shima ya ƙara faɗin.
"Sir are you okey?komai dai-dai ne ko?"
Ya ƙara faɗa cikin hausar shi wanda baya fita sosai,ajjjiyar zuciya Alhaji Kabeer ya sauke tare da fesar da iska daga cikin bakinsa murya na rawa yace.
"Acp munyi missed Zulfa yanzu,ka yaɗa photonta da ba yananta a kafafen sada labarai redio,t.v,social media,gaba ɗaya a baza rahotanni kota ina,wannan ya zama breaking news kada kayimin wasa Anwar rayuwata na rasa,ina tabbatar maka idan har Zulfa tayimin nisa tabbas zan iya shiga wani hali,zuciyata ba zata jura ba,ina gaya maka hakanne domin ina maka kallon ɗa a wajena bana da kowa wanda zai shigemin gaba,ka tabbatar duk inda tashoshin mota,jirgi,suke kasa an rufesu duk da mana da tabbacin zatai nan wajan"
zubewa Acp Anwar yay akan sofarsa dake makeken office ɗinsa,Aunty Zulfa missed?wannan shine tambayar daya kewa kansa amma babu amsa,shi kansa rayuwarsa tana cikin wani hali indai ba aga Zulfa ba,domin itace shedar kawai data rage masa akan damuwarsa itace garkuwarsa wacce zata tseratar dashi tayaya wannan abun zai faro,anya ba sanya hannun wasu akan wannan labarin,numfashi ya sauke tare da faɗin.
"Amma baka ganin aƙwai sa hannun wasu cikin wannan abun?tayaya mace zata gudu a lokacin data haihu lokacin daya dace ta zauna ta huta a kuma kula da ita,tayaya uwa zata gudu tabar ɗanta gaskiya nidai ina shakku akan wannan matsalar"
Cikin ɓacin rai da kuma takaicin abinda Acp Anwar ya faɗa,Alhaji Kabeer yay sauri daga masa tsawa ta hanyar faɗin.
"Kai!! banson zancan banza,shikenan Ubangiji bazai taɓa jarabtar bawansa ba sai ace wanine dalili ko kuma wani yay asiri,babu ruwana da wannan shirman kabarni da abinda na keji kada ka ɗuramin hakkin wasu akaina haka kurum,Allah shi kaɗai yasan abinda yake ɓoye,kafin nan da awa guda ina son na sami labari akan Zulfata"
Yana faɗin hakan ya kashe kiran kana ya juya ya nufi gidansa,yana zuwa ya shige cikin part ɗin Zulfa inda Mameey ke zauna tana faman jijjiga babbyn daya keta faman tsala kuka duk ya cika gidan.

Ganinsa cikin tashin hankali wanda bata taɓa ganin irinsa ba,a duk tsayin shekarun da suka ƙwashe tare da juna,jiki a sanyaye ta sanya hannu ta ɗauki babyn tare da ƙara sawa inda yake tsaye ya sunkuyar da kansa ƙasa,babyn ta rungome a ƙirjinta tare dasa hannu guda ta taɓa kafaɗar Alhaji Kabeer,still bai ɗago ba hakan tasa tayi sauri ƙarasawa gabansa,abinda ta gani yay mugun bata mamaki,zata iya cewa wannan shine karo na biyu da taga hawaye na bin fuskar mijin nata,da lokacin da aka ɗaura masa aure da Zulfa sai kuma wannan ranar,cikin tashin hankalin daya sameta itama tace.
"Dan farin ciki yaywa mutum bai dace yay kuka ba,zaifi ƙyau ace al'wala kayi tare dayin sallah domin miƙawa Allah godiyarka bisa wannan ni'ima da yay maka ta baka ƙyautar mutum mai tarin baiwa,amma kuka sam bai dace da fuskar ƙwarzon namiji kamar ABBOU ba,idan kayi kuka ita Zulfan tayi me?"
Sunan Zulfa data faɗa ya sashi saurin ɗago kansa tare da saka hannu ya amshi babyn ya manna a ƙirjinsa,wata sassayiyar ajjiyar zuciya ya sauke lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka ƙara fituwa ta cikin idanunsa,so yake yay kuka irin kukan nan mai yawa wanda yake tafiya da ƙunci da kuma zafin zuciya amma sam ya kasa,sai ajjiyar zuciya da yake saukewa a jajjere,ganin yanayinsa gaba ɗaya ya sauya kamar ba mijinta wanda ta sani da dauriya da kuma jarumta ba,mai tsayawa akan ra'ayinsa,mutum ne shi kaifi guda babu wani wanda ya isa ya sauya masa abinda yay niya,cikin muryar tashin hankali Mameey ta ƙara taɓashi tare da faɗin.
"Wai lafiya naga gaba ɗaya ka sauya make faruwa ina Zulfa take?tana ina ya kamata ace tayi wanka yanzu sabida jikinta ɗanye ne babu ƙwari"
Sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalleta da jajayen idanunsa cikin wata iriyar murya mara sauti wacce kuka yaci ƙarfinta yace..
"Rayuwata data babynmu tana ciki matsala,zamu shiga cikin ƙunci da baƙin ciki haɗi kuma da kaɗaici,mun rasa farin cikinmu,walwalarmu,jin daɗinmu,uwa uba garkuwanmu,Zulfa tayi mana nisa Mameey nisa mai yawan gaske,ban san ina take ba ban san inda zan sameta ba,aljanu sun hauƙatamin uwar yarona Zulfa ta haukace..."
Cikin wani sabon tashin hankali Mameey ta tari numfashinci ta hanyar faɗin.
"What! hauka fa?tayaya hankan zai kasance tayaya Zulfa zata haukace,nasan cewa naƙuda nasa mutum yay jijjiga amma man taɓa ganin inda ta haukata mutum ba,nasan cewa Zulfa nada mutanan ɓoye amma ban taɓa jin inda aljanu suka haukata mutum ba,mun shiga uku innalillahi wa'inna illaihir raji'un,Allahumma ajirni fil musibati wa'aklifni kairan minha,Ubangiji ka bai yana mana Zulfa cikin ganggawa"
Ta ƙare maganar tana saka wani kuka mai tsuma zuciya,kukan data daɗe batai kamarsa,soyayya dan Allah ta kewa Zulfa,bata taɓa ɗaukanta matsayin kishiya ba,akoda yaushe kallo ƙanwa take mata,hatta lokacin data samu ciki ji take tamkar ita ta samu cikin,haka kuma yanzu kallon babyn take tamkar wanda ta tsuguna ta haifa.
Alhaji Kabeer ƙyawawan idanunsa ya zubawa jaririn ganin yadda yay shuru a ƙirjinsa sannu a hankali kuma bacci yay gaba dashi,halittar jaririn ya kalla,musamman yadda yaga suna muguwar kama da Zulfansa,farine tas irin farinnan na shuwa arab,ga wani dugun siririn hancin daya kawo har wajan bakinsa,uwa uba tulin sumar kan jaririn wacce tai ƙwance abinta baƙa siɗik sai shegeƙi take,ga wani ƙaramin bakinsa wanda yake ɗauke da jajayen laɓɓansa sai sharning suke,kallonsa ya sakko zuwa ga yatsun hannunsa a hankali yasa hannu ya taɓa ɗan cindon dake gefen ƙaramin yatsanshi.
wata zafaffiyar ƙaunar yaronce ta gama ratsa duk wani jini da tsokar dake yawo a jinin jikinsa,a hankali ya sunkuyar da kansa zuwa kunnan yaron,cikin nutsuwa ya manna bakinsa a kunan babyn,kiran sallah ya farayi masa kana yay masa kalmar shada tare dayi masa huɗuba da sunan daya faɗo masa a lokacin dan bazai taɓa tuna inda yasan sunan ba,da kuma kusancinsa dame sunan,kawai dai yana yawan samun kansa da kewar sunan,ba tare da yayi magana ba ya danƙawa Mameey yaron wacce har yanzu dake zaune tana rera kuka,ganin yana bacci yasa ta goyashi a bayanta tare da lulluba masa wani farin showel mai taushi.
wajan wardrope ɗin Zulfa ya nufa tare da ɗaukan wani Album ya zare wani babban photonta yay waje,direct babban compound ɗin gidan ya nufa yana zuwa ya shige cikin wata ash ɗin ferari ya murza mata key yay waje da gudu kasan cewar tuni Malam Habu ya buɗe gate ɗin.




Zulfa tafiya kawai takai a tsakiyan titin,ba tare data fahimci inda take sanya ƙafafuwanta ba,babu abinda yake ƙara hargitsa mata ƙwaƙwalwa wanda yake tunzurata ga gudun take irin kuka da gurnanin haɗi da wani ƙara da take jiyowa a bayanta,a duk sanda tayi niyar juyawa sai taji wani abu ya daki tsakiyan kanta hakan yasa cikin ƙaramin lokaci ta fice a hayyacinta gudu kawai take babu tsayawa,yayinda gaba ɗaya jijin hauhuwar ya gama jiƙa faffaɗar guduwar rigan dake jikinta,gaba ɗaya ta fice a hankali ta zama mahaukaciyar ƙarfi da yaji,musamman idan kayi duba da yadda yalwatacciyar sumar kanta ta hargitse ta bazo a bayanta tare da rufe mata gefen fuskarta,yadda gashin ya rufe mata fuska ne kuma babu tunanin ta gyarashi domin taga hanyar tafiya kai tsaye ta nufi tsakiyar makeken titin a kuma dai-dai wannan lokacinne wata tsaleliyar mota mai shegen ƙyau da kuma tsari ta kunnu kai,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un duk yadda drever'n motar yaso taka birki kasawa yayi,ƙyaƙƙyauwan magidancin dake bayan motar wanda dukkan alamu shiɗin babban mutumne ya fara salati cikin ransa kasan cewar bai fiya magana ba,amma tabbas ya shiga tashin hankali ba kaɗan ba,cikin dauriya da kuma zafin nama ya fara ƙoƙarin wara laɓɓansa wani zazzafan numfashi ya fesar tare da runtsa idanunaa da ƙarfin cikin daɗɗan muryarsa mai sauti yace "Ya subuhanallah!!" a kuma dai-dai wannan lokacinne drever'n yay gaba da Zulfa...





_Wannan labarin direct ta farkonsa muka fara, zai iya yi maku daɗi a haka wasu kuma ba lallai ba,amma tabbas wannan salon daban yake,cikin nutsuwa zaku fahimci wanene UNCLE ɗin mene yayi ko kuma mene aka aikata masa,na san in sha Allah za kuyi alfahari dani a Wannan littafin kamar yadda kukai a THE NEW EMIR,babu abinda nake buƙata irin *comments* sai share dan Allah dukkan wanda ya karanta ya share zuwa wasu grps koda ɗaya sabida suma su amfana da littafin😍just imagine over 300 messaged on one day masu yimin magana kuyi hqr in sha Allah zan duba ga dai number ta Whasapp 08119237616 a duk inda kuke zaku samu littafin UNCLE NE,masu wattpad kuma kuyi searching NIMCYLUV Thank you guys share share Please🤲🏻

_✨ UNCLE NE ✨_




https://www.wattpad.com/1073694982?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv&wp_originator=mevhPm7g3%2BBY6kjjW3lOcQab3cIv8D8nHmvVnjCDrhHk4t0XwF3ur1azv66d8V7BkCArOE5%2B3aQTAlH2%2BAXmY880JYZZRpZ2qCzrs%2F2ICX5nfNsNsgZ5M%2BazzcuVa2VZ







_✍🏼 NIMCYLUV_

*3-4*









Ƙarar taka birkin motar da kuma ihun da Zulfa tayi shine yaja hankalinsa zuwa gareta,hannu yasa ya dafe saman goshinsa tare da runtsa idanunsa,cikin kuzari haɗi da sassarfa yasa hannu ya buɗe murfin motar,gaba ɗaya ƙafafunsa ya fito dasu waje tare da zuro da sauran jikinsa,lokacin har mutane sun cika a wajan sun yiwa motar ƙawanya,cikin natsuwa ya fara takawa har wajan da Zulfa ke ƙwance cikin jini,da dukkan alamu tayi muguwar buguwa a kanta domin shike tsiyayar da jini,ɗan tsaki yaja ganin tarin mutane amma babu wanda yay ƙoƙarin taimakonta.
Numfashi ya sauke tare da kallon drevernsa mai suna Joseph cikin jarumtar data rage masa yace "ɗauketa zuwa mota mana" yana faɗin hakan ya juya tare da nufar side ɗin baya ya buɗe,ɗan ja da baya ya bawa Joseph waje domin ya sanya ta a mota, bayan an ƙwantar da ita shi kuma ya kuma mazaunin mai zaman banza ya zauna Joseph kuma ya zauna mazaunin drever.
"Yallaɓai ina muka nufa ne?nasan dai babu maganar wani meeting yanzu saboda condition ɗin da wannan matar ke ciki,Nina gama kamar mahaukaciyace"
Tunda ya fara magana har zuwa lokacin da yay shuru mutumin daya kira da sunan YALLAƁAI baiyi magana ba,zuciyarsa ta tafi wani tunani nada ban,lallai mutum da yana sanin ƙaddarar da za ta samesa tabbas da yayi ƙoƙarin kujewa faruwarta,abinda ya kawo shi wannan garin da ban,amma abinda ya samesa da ban,wannan wanne irin abune.
Mene ya fito da ita? ina zata je?wanne jini kebin jikin?wannan sune tarin tambayoyin da suke zuciyarsa amma ya gagara furtasu sabida nauyin da labɓansa sukai masa.
cikin ƙosawa da maganar Joseph yace "muje UNITY MEDICAL CENTRE HOSPITAL dake nan IBADAN"
Cikin sauri Joseph ya joya motar da taimako map suka samu suka isa asibitin kasan cewarsu baƙi ne a garin.
Suna zuwa asibitin kai tsaye emagency aka shigar da ita,likitoci suka rufu a kanta,bin kican farko suka gano haihuwar da tayi da kuma ƙaruwa da tayi wajan haihuwar,hakan tasa suka yi mata ɗinki tare dayi mata allurar haɗi da sanya mata drip,suna gamayin komai suka fito daga cikin room ɗin da aka sanyata ciki,da sauri drever'n ya miƙe tsaye ya fuskanci babban likitan cikin sonjin abinda ke damun matar yace.
"Dr yaya jikin nata?ta samu lafiya dai?"
Jinjina kai likitan yay tare da juya ƙwayar idanunsa zuwa ga mutumin dake can gefe yana leƙa window,sosai yake mamakin mutumin domin ya hangu zallar damuwa da kuma tashin hankalin dake ƙwance a saman fuskarsa,yana ɓoyewa ne kawai sabida jarumtarsa, murmushi likitan yay kana ya kalli Joseph yace.
"Kada ka damu komai zaiyi dai-dai tasha wahala wajan haihuwa ne,ga kuma ƙaruwar da tayi, amma da yardar ALLAH zata samu lafiya amma ina babyn data haifa?kuma yana da ƙyau ace macace a wajan ta ba maza ba"
Sai a lokacin Mutumin ya juyo zuwa gare su tafiya kaɗan yay yace "Kace haihuwa ce ko?amma macen data haihu mai zai fito da ita kan titi? tabbas bayan haihu aƙwai wani ɓoyayyan tuggu a ƙasa.."
"kana nufin kace baka santa ba?kuma baka san asalin wacece ita ba?"
Dr ya tambaya shima cike da tashin hankali domin shima abin ya fara rikitashi "Amma yallaɓai mai zai hana idan ta farka ka tambaye ta sabida gujewar masu haihuwar cikin shege kuma su yadda shi,jinjina kai yay cikin gamsuwa da maganar Dr yace "ok amma sunana JABIR ba yallaɓai ba,zuwa yaushe zamu dawo muganta domin a gobe nakeson komawa birninmu" jin abinda Jabir yace ya sanya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment