Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banason rainine kawai shiyasa


Sai da suka shigo suka gaida mama sannan suka fice


Mama tace khairy ki masu iso falon Abba, to ta amsa taja mayafinta ta fice


Cikin natsuwa ta fito ajikin mota tasamesu


Sallama ta masu cikin sanyin murya


TJ ne ya amsa yana tasbihi fa Allah, azuciyarsa yace lalle Ameen baida wayo wannan yarinya haka mai kyau yace baiso atinaninsa Fauziyyah ce


Bismillah kushigo ciki tana fadin haka ta wuce


Sai da TJ yaja hannunsa sannan suka bita abaya har falon Abba...




✍🏻Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] β€ͺ+234 703 448 8635‬: 🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾




Budurwar Qauye πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


July, 2017




1⃣0⃣
Yana fitowa mota ya shige rai bace, nan ya kuma tarar da wani abin haushin


TJ yagani ya ritsa dambun nama yana ci hankali kwance


Har papa ya shigo yana qoqarin yima mota key bai ko kalleshiba sai ma kada kansa dayake alamun naman yamasa dad'i


Wata doguwar tsuka yaja, yace Allahu ya kawo maka sauqi


Sai anan TJ ya dago yace da akayi mefa?


Nan papa yasake quluwa yace bansaniba


TJ ya ajiye bowl din hannunsa, sai daya kora lacasera tukun ya dubi abokinsa yace uhum inajinka meyafaru sarki fushi


Papa bai kulashi ba sai ma tada motar da yayi, sai daya hau hanya tukun ya dubi TJ


Yace kaikam zuwa dakai waje jama kai rainine, imba neman rainiba harda wani zagewa kana zuba surutu kamar wani parrot


Hakanma bai makaba sai ka karbi abin hannunta, naman taraina mu kawai haba


TJ yace kagama


Eh ya fada afusace


TJ yace kasan Allah, gara ka natsu ka amshi zabin Daddy hannu biyu dan wlh yarinyannan tayi ta ko ina


Kanaganin yarinya yar shila ga kyau ga natsuwa


Oh, haka kagani kai ai dik yadda mace take birgeka take shiyasa amma meye abin birgewa awajen *Budurwar Qauye*


TJ yace kasan Allah, ni ko aure na tashi, bazan auri wacce ta rufa 20, swt 16 zan samo na aure


Kuma idanma kanaga taima qanqantane kabata shekara 1, tasamu kiwo malam


Haushi yasa baima kulashi ba har suka iso fada bai kuma cewa uffanba




**********
Bayan sati biyu, yanzun Fauziyyah, bata samun matsala wajen yin waya da yasir


Tinda ta nuna wayar daya bata amatsayin papa ne ya bata, dik tym daya kira zata daga amatsayin papa ne


Yauma kamar kullum yasir ya kirata awaya tana dakin mama, tsam ta miqe ta nufi dakinta


Assalamu alaikum ta amsa wayar


Waalaikumussalam beauty na


Murmushi tayi, tace naam habiby


Dftn beauty ta yini lfy?


Lfy lau, habiby ma dafatan ya yini lfy


Nikam ba lfy ba ya amsa mata


Subhanallah, mene yasameka? Baka da lfy ne? Ta jera masa tambayr arude


Lfy na lau sai dai zuciyata tana cikin wasiwasi, nakasa samun natsuwa my fauzy ina tsoron rasaki




Haba habiby ya kake irin wannan tunanin, insha Allah bana da miji sai kai


Kullum haka kike fadamun, amma koda gidanku, baki taba barina nazoba ko sau1


Marairaice murya tayi, tace wlh dokar Abba ne shiyasa amma na amince ranan da nagama rubuta jarabawa ta ka turo magabatanka wajen Abba, sunemi izinin nema da kuma aurena




Alhamdulillah, abinda nakeso naji daga wajen ki kenanan, wlh har nasami natsuwa, I luv u so much


Jin yadda nan take farin ciki ya lillibesa sai jikinta ya mutu, asanyaye tace I luv u too habiby


Barin fita masallaci, sai zuwa jimawa dan kiraki, bye my queen sai kinji ni


Tace bye habiby


Tanasauqe wayar wasu hawaye masu zafi suka zubo mata , addu'a take Allah yasa burinsu ta cika Abba ya amince kodan ganin girman idon mutane


Kwanciya tayi tana tuno, papa lalle indai kyau ne babu hadi da yasir, haka Komai ya fi yasir


Kuma inda dan kyaune to tabbas papa zata dauka, sai dai bata son papa koda da kwayar zarra ne


Afili tace inaa barin iya auren mutumin da baisona, maganan arziqi bai taba hadani dashi ba, Allah ka kawo mun sauqi cikin rayuwata


Sai data sha kukanta ta more sannan tayi shiru




*******
Afannin Daddy kuwa ginin gidan papa yasa agaba, inda ya dauko hayar companyn *Buildsmart*, yabasu contract na gini da dik wani abin cikin gidan, tindaga kayan daki, kitchen da Komai


Sannan ya kira Abba awaya ya sanar masa baya buqatar yasayi Komai dan yai order na Komai


Abba yayi godia sosai, Daddy yace haba ai Fauziyyah yarsace koda wani zata aura shizaiyi Komai


Momcy da aunty mabarukha Daddy ya basu isassun kudi suka tafi dubai hado lefe




Yanzu biki saura wata biyu ina ko wanni fanni suka fara shirye2


Ango da amarya kam ko ajikinsu musamman papa da mantawa yake da batun auren


Halinsa kuwa sai abinda yayi gaba dan ba abinda ya sauya


Momcy dai fatanta Allah ya shiryeshi kada wata rana ya shawu ya lakad'i yar mutane


2weeks later
Su aunty niima ne da wasu yan uwan momcy da Daddy suka kai kayan sa rana, nanma kaya bana wasa ba aka kai


Dik abinda ake Fauziyyah ko da wasa bata taba fadawa yasir batun auren da ake shirin yamata ba




Papa kuwa tun wannan lokacin da yaje dambam sukayi fada da Fauziyyah bai kuma zuwa ba


Ya fake da aiki ysmasa yawa, Daddy ya kirashi yace yakamata yabar dik aikin dayake yaje yasami Fauziyyah su tattauna maganar biki


Ya amsa da toh, amma ba har zuciyarsa ba, dan baida niyyar zuwa


Fauziyyah kuma yanzu batada zama sabida exams da suka fara


Cikin ikon Allah har sun gama lfy


Aranan yasir ya nufi gombe cikin dokin Washegari zasu taho da su dad dinsa domin tambaya masa auren Fauziyyah


Tun last 2 weeks yazo gombe yasanarma dad ya kuma amince masa




Tunda yasir ya tafi gombe Fauziyyah hankalinta atashe yake dan batasan yadda abin zai qareba


Ranan kwana tayi batayi bacciba sabida damuwa


Washegari haka ta tashi sukuku kamar marar lfy har mama ta tambayeta ko bata da lfy ne, tace aa lfyrta qalau


Bata gama shiga damuwaba saida yasir ya kirata yace sun taso


Wajen 12pm aka turo ana sallama da Abba, anyi saa kuwa yana gida


Yana fitowa yaga manyan mutane tareda matashin saurayi kuma bai wayesuba


Iso ya musu zuwa falonsa, nan yasa aka kawo musu ruwa da dan abin motsa baki


Suka gaisa cikin sakin fiska, Abba yace gashi ban wayekuba kuma


Alhaji sadi baffan yasir yace lalle baka wayemuba mu baqine wannan ya nuna dad din yasir yace dan uwanane kuma qanina
Wannan kuma amininsane, wannan kuma dansane kuma daga gombe muke munzo.......






✍🏻Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] β€ͺ+234 703 448 8635‬: 🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾




Budurwar Qauye πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


July, 2017




*I dedicated this page to my swt friend Ikhlima (Mmn Safwan)*


*Indeed u r morethan a friend 2 me, much luv 4 u😘😍*




1⃣1⃣
Munzo nemawa yasir izinin nema,


Inbama zakace munyi gaggawaba sai muce harda neman auren Fauziyyah mukazo


Domin yara sun riga sun dai2 ta kansu


Munafatan zaa amshi buqatarmu




Tinda yafara magana Abba yayi shiru yana saura ransa, amma abinda ya daure masa kai da yace wai sun gama dai dai ta kansu


Sai daya kai aya sannan Abba yayi gyaran murya


Yace toh dafarko nayi farin cikin zuwanku da kuma abinda ke tafe daku


Hakanan nayaba da hankalin yasir abisa lura da natsuwarsa da nayi


Sai dai kash kunzo aqurarren lokaci sabida du3 auren Fauziyyah saura sati 5


Tinda Abba yafara magana yasir yake murmushi, amma kalmar Abba na qarshe shiya matuqar girgizashi


Cikin sauri ya d'ago kansa, lokaci guda idanunsa suka sauya launi, fiskansa ta canza alamun tashin hankali qarara suka bayyana


Matsowa kusa da Abba yayi, cikin murya mai rauni yafara magana


Abba kataimakeni, kada kanesantani da Fauziyyah, Fauziyyah itace farin cikina, Abba namaka Alqawari zaka sameni miji nagari Wa Fauziyyah


Sai hawaye sharr, hannunsa yasa ya riqe qafafun Abba


Cikin tausayawa da jinjina irin son dayake Wa Fauziyyah, Abba ya riqo hannayensa


Yace tabbas yasir ganin natsuwarka yasa nayiwa Fauziyyah shaawan ka kasance miji agareta


Tabbas kacancanci dik irin mijin danake fatan Allah ya bai Fauziyyah ta aura


Amma bayanda zanyi dan anriga anmata baiko da wani


Haka da ina da wata 'ya Bayan Fauziyyah dana baka ita, dan nayi shaawar had'a zuri'a daku sabida dattakunku


Amma zanyi maka fatan Allah yabaka mace wadda tafi Fauziyyah


Yasir cikin kuka yace abinda nake tsoro kenan, shike nan narasa Fauziyyah, narasa farin cikina, kuka yake kamar qaramin yaro


Dad ne yadafa kafad'arsa yace ya isa haka yasir addu'a zakayi Allah yasa haka shiyafi alkhair


Abba yace kuyi haquri, bayanda zan warware wancan baikon, idan nayi haka nazama qaramin mutum


Alhaji sadi yace aiba zai yiyuba, kuma munfahimceka sai dai muce Allah yasa haka shiyafi alkhair, Itakuma Allah yasa gidan zamantane


Abba yace madallah nagode sosai, yasir kai haquri ka qaddara Allah bai nufa Fauziyyah matarka bace


Nagode Abba, iya abinda ya iya furtawa kenan ya fice yana share hawayen fiskansa


Dad ma miqewa sukayi, suka sake musabaha atsakaninku


Alhaji sadi yace toh Alhaji mu zamu koma mungode da karramawar mutunci daka mana Allah yasadamu da alkhair


Abba yace nima nagode, ina kuma sake baku haquri, Allah yakaiku gida lfy


Suka amsa da ameen sannan suka tafi




Fauziyyah kuwa tunda taga Abba yasa ankai masa abin motsa baki falonsa, wai yayi baqi


Zuciyarta taketa tsinkewa, dik ta diririce, tarasa natsuwarta dan tana da yaqinin su yasir ne, kuma batasan ya zasu qare da Abba ba


Tana kwance a ad'akinta taji Abba yana kwad'a mata kira, Fauziyyah, Fauziyyah


Zuciyarta ce tayi wani mummunan bugawa, da kyar ta miqe ta fito kamar wadda kwai ya fashema aciki


Afalon mama tasameshi shida mama




Gefen mama ta wuce ta rakub'e da kyar bakinta ya furta gani Abba




Dubanta yayi rai bace yace yanzu abinda kikayi kin kyauta Wa kanki


Shiru tayi bata amsaba, nace kin kyauta yasake tambayarta


Ahankali ta girgiza kanta alamun aa




Mama tace Alhaji kamin bayani mana meke faruwa


Nan Abba ya koro mata bayani filla2




Salati kawai mama keyi, tana tafa hannunta, tace toh Alhaji waye kenan wannan yaron dabamu sanshiba


Abba yace sai dai ita tamana bayanin inda tasanshi har suka fahimci junan




Mama ta dubeta cikin takaici, tace a ina kika sanshi




Idonta na zubda hawaye ta musu bayanin waye yasir


Abba yace amma kina sake sa batun aurenki d Alamin, kika turo mun mutane dan kizubarmin da qimata ko


Danma Allah yasa mutanen kirkine mun fahimci juna dasu, amma kisani kin yaudari yaronnan da kika rufeshi baki fad'a masa gaskiyaba


Ko a tunanin akwai abinda zai sa nacanza raayina akan Alamin




Cikin kuka wadda tunda Abba yafara magana take kuka tace Abba katausaya mun wlh inason yasir, banason ya Alamin


Abba yace bijiremun zakiyine? Toh kisani bakida miji sai Alamin kuma ko Bayan raina ban yadda ki auri wani bayansa ba


Kuma ko mutuwa kikayi sai ankai gawarki gidan Alamin, sha3 kawai


Yana fadin haka ya wuce abinsa, nan taringa kuka kamar ranta zai fita, mama ma tashi tayi ta wuce abinta




Dakinta ta koma ta dau wayarta tafara neman layin yasir, sai dai is not reachable hakan ya tabbatar mata yana kan hanya


Har wajen magriba, trying layin take, kamar wasa taji ya shiga sai d bai daukaba


Takira yakai sau 20 amma yaqi d'agawa daga qarshe ma ya kashe wayar gaba 1




2weeks later, Fauziyyah tashiga cikin damuwa sosai dan har yau yasir bai dauki wayarta ba


Message m ta tura masa ba adadi amma yaqi mata reply




Mama tun tana mata fada yanzu ta koma lallashi


Biki sai Matsowa yake, saura sati uku amma har yau ba ango ba labarinsa




********
Angama aikin gidan papa dake dasspark, su momcy sunje sun gani kuma sun yaba




Gidane mai hawa daya, tsarin ginin turawa ko ina yasha shuke 2


Gwanin shaawa, amma fir papa yaqi zuwa y gani


Masu gadi mutum biyu, irin buzayen nijer Daddy ya dauka aka sa agidan
Hatta IV Daddy ne ya buga sanin halin papa yasa ya nemi TJ ya bashi na abokansu dana amarya


Ya kuma jadda da masa lallai suje sukaima amarya nata




Inda TJ ya yayi ma Daddy alqawarin zasuje aqarshen sati.......




✍🏻Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] β€ͺ+234 703 448 8635‬: 🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾




Budurwar Qauye πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


July, 2017




*Wannan shafin nakine Sis Amina, nagode da kulawarki gareni Allahu ya bar qauna, Mmn Faty luvs u too 😍😘*




0⃣9⃣
Suna shiga Itakuma tai cikin gida, batafi 5mins ba tadawo hannunta riqe da qaton tire, ajiyewa tayi akan center table dake gabansu


Fita ta kumayi nanma da wani tiren ta dawo sai da ta cika gabansu da kayan motsa baki kala2


Sannan ta zauna ina yinin ku tace dasu, lfy iya abinda papa yace


TJ ne ya amsa da faraasa, ya gida ya tambayeta


Lfy lau, ta amsa sannan ta miqe bismillanku fa tace dasu kafin ta fice bata jira amsan suba


Aiko tana fita TJ yace kai mutumina wlh kada kayi Wa kankafa


Wannan yar shilan tayi


Papa da haushi yasake kamashi a kufle yace to mayen mata wadda takai da bata kaibama kaikam awajenka tayi ko


TJ yace gaskiya mutumina bawasa fa kasamu wajen hutawa, wlh wannan taciko baqaramum hutawa zakayiba


Papa yace to sai kayi kuma, dan wannan bama ita bace


TJ cikin sauri yace to waye ce wannan din?


Oho, yace dashi dan yanzu haushi TJ yake bashi akan nuna maitarsa afili idan yaga mace


Jin irin amsan daya bashi yasa yaja bakinsa yayi shiru, kawai


Papa kuwa banda zafi ba abinda zuciyarsa ke masa, me wannan yarinyar ta takane da zata ringa ajiyeni ya tambayi kansa


Kwafa yayi zan dau mataki lalle dan naga raini ya shiga tsakaninmu


Yana cikin wannan tunanin ya tsinkayi sallamanta cikin murya mai dadi


Ko dago kansa baiba baran ya amsa


TJ ne ya dago kansa lokaci 1 yana amsa sallaman


Ya salam shine abinda ya furta aransa yana mai qare mata kallo


Sanye take cikin riga da wando na pakistan masu kalan ja da butter milk, ta yane kanta da gyalen kayan


Fiskannan tasha kwalliya wadda yaqara fidda zallan kyanta dik da yarinyace halittun jikinta basu gama cika ba amma dole ta burgeka


Nan TJ ya hango wautar abokinsa, yace tab ashe wannan har tafi waccar


Sannunku da zuwa, yawwa yawwa madam TJ yafada yana murmushi


Ina yini, lfy lau, munsameku lfy, tace lfy lau


Masha Allah, sai dai bansan sunan amaryar namuba TJ yafad'a cikin zolaya


Murmushi tayi wadda ya sake qawata face nata tace Fatyma amma ana kira na Fauziyyah


TJ yace waw what a nice name, so nidame dan ke kiranki?


Umm dik wadda kake so kana iya kirana


Ok, thanks


Tace ur wlcm


TJ fa Fauziyyah tamasa 100%, gaba d'aya jiyake inama Fauziyyah tashi wlh lallab'a abinsa zaiyi ya gwada mata zallan qauna kawai


Ganin tayi shiru haka Ameen baice komaiba yasa yace Fauziyyah bakisan sunana ba n baki tambayaba


Kayi haquri toh inajinka


Yace nayi toh, sunana Muhammad Tijjani but friends nawa kan kirana da TJ


Tace nagode sosai


Papa da surutun TJ yagama sake qularshi sai wani huci yake wane yaga abokin gaba


TJ kuwa ganin yadda abokinsa yasake b'ata rai yasa yace man barinje waje saika fito


Bakasha ko ruwaba tace dashi Bayan ya miqe


Bari nasha to nagodefa, d'aukan roban lacasera yayi yace barinje nasha a mota


Miqo masa wani bowl da aka raping nasa tayi tace to ka qara da wannan


Toh amarya nagode ya karb'a ya fice


Aiko yana fita Fauziyyah ma tayi fiskan shanu


Ta juya kanta


Keh, yace da ita


Bata masan yanayiba
*Budurwar Qauye* yasake karanta


Nanma bata kulashiba


Akufle yace ana miki magana kinajin mutane, waini me kika takane kike ma mutane gadara, mintuna nawa kika bata kafin kifito toh wlh nasake zuwa kika ce zaki wasting mun time sai dai kifito kisamu nayi tafiya ta yar qauye kawai


Tinda yafara magana tana jinsa saida yakai ayah sannan ta dubeshi da kyau


Sai anan taqare masa kallo tsaf, tace kai haba kacika mun kunne magana ba comma, ba pullstop ko kakira sunana ban amsaba, kamar yadda kake kirana yar qauye to ni kallon danake maka dan dagaudama yafika dan baka cikin irin layin mazan dana kaso, sannan tinda kake zuwa nataba nemoka nace kazo badai kaika ke kawo kanka ba, kaga kuwa dole kajuri dik abinda zan maka tinda kai ka kawo kanka, tawani murguda masa baki da juya idanuwa


Aiko caraf taji an riqo hannayenta dik biyu, ya matsesu waje guda, yasa dayan hannunsa ya murde mata baki


Yace lalle ashe rashin kunyarki gaba yayi, to kisani niba amun rashin kunya kikasake saina fasa wannan bakin yakai hannu ya buge bakin
Sannan yace ko cemaki akayi ni sonki nake, ni mezan dake ko mata sun qare, dubekifa ko mace baki kaiba, ji qirjinki babu wani abin shaawa har kikemun wai yanga, to kisani ninafi qarfinki kika kuma mun rashin kunya zakiga abinda zan miki


Fauziyyah kuwa irin kalan riqon daya mata shiyasa tayi shiru, sannan tafahimci d'an iskane baima da kunya


Data samu ya saketa, tace Allah ya isah kuma wlh nibazan aurekaba, inbakasaniba nama fika qin wannan auren


Yace wlh da kintaimakeni kuma sai na maki babbar kyauta indai kika fasa aurena, yanafadin haka yayi hanyar fita abinsa


Yana fita Fauziyyah ta zube awajen sai anan takejin haushin maganar daya fada mata


Afili tace wlh bazan aureka ba dan iska, uncle yasir baitaba fadamun magana mai kamar wannan bama


Miqewa tayi ta gyara mayafinta sannan ta fice


Dakinta ta wuce, ta dakko kwalin wayar da yasir ya bata ta nufi dakin mama


Waje tasamu ta zauna, tace khairy wai sungaisheki sun wuce


Mama tace ayyah dan albarka ai Alamin akwai ganin mutuncin mutane


Fauziyyah acikin zuciyarta tace hmm dabaki sanshiba ko


Miqawa mama wayar tayi mama ya Alamin ya kawomun waya


Mama takarba tace Allah yasa albarka shikam baya gajiya


Nan ta bude sukayita santi itada khairy


Saida tadawo dakinta sannan tamaida Komai yadda take ta kunna ta sakata a chargy zuciyarta wasai dan tahau matakin farko a plan data shirya na auren yasir......




✍🏻Faty Mmn Faty
[10:40PM, 8/6/2017] β€ͺ+234 703 448 8635‬: 🌾🌾🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾🌾




🌾🌾🌾






Budurwar Qauye πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€πŸ€·πŸΌβ€β™€


Written by Faty Mmn Faty


July, 2017




*Wannan page nakune masoya Budurwar Qauye, nagode Allah ya bar qauna, Mmn Faty luvs u all 😍😘*




1⃣2⃣
Washegari da safe TJ ya kira papa awaya , amma harta katse bai picking ba


Yana shawarin yasake kiransa ko ya barsa sai yataso office su hadu, sai papa ya calling nasa back


Hello man ya fad'a Bayan ya d'au wayan


Yes meri dosty (abokina) am sorry shigowana office kenan ka kira kafin na dauka ya katse


No probs man, dama wajenka nake son zuwa tinda kana office barin shigo sharp2 kafin na wuce office


Alright, saika shigo


Bada jimawaba TJ ya iso, direct office d'in papa ya shigo


Yana shigowa papa ya taso, suka kashe hannu, papa yace ya neto mutumin, jiya daga cewa barinje nadawo kawai sai eh


TJ yace kai bari kawai man, ai popsy ya kasa ya tsare fa, kawai yafa sa ido fa, shine nake masa lamfo


Papa yace amma dan iskanci mai makon ka fad'an gaskiya sai ka d'orani kawai


TJ yace kai dana barka da surry, inama zaka wani tinoni eh


Papa yace barta fa yarinyannan jarabane da ita, da kyar nasamu ta natsu kuma nafad'ama joseph kada yasake barinta ta shigo mun gida


TJ yace ai yanzukam dama kamata yayi ka fita harkan koma wace tinda aure zakayi ko yah


Papa ya cire hannunsa daga cikin na TJ ya koma ya zauna, tare da b'ata rai, yace amma dai kasan ina d'aga ma qafa ko


Inbanda kai babu wadda ya isa yake fad'amun magana son ransa na barsa


TJ yace haba man meye abin b'ata rai, kai da zaka fara cin riba biyu ka more ka kuma sami lada


Amma wlh ka cuceni, a ina zan more kanaga yarinyar da ba komai ajikinta


TJ yace lokacin da zakaga komai d'in yana zuwa


Kai nifa ina da abinyi, kanaga ko patient 1 ban duba ba ka tsaidani fa wasu surutanka marasa amfani


Toh naji aidai kasan nima inada abinyi, na biyo sabida muhimmiyar magana


Toh ina jinka, meyake happening


Cards sa Daddy ya bashi ya ajiye akan tebur dake gaban su
Meye wannan ya nuna Cards d'in da hannunsa


Katin gayyatar bikinku, kai tsaye TJ ya amsa masa


Wata doguwar tsuka yaja yace to meye had'ina dasu kuma nayi me dasu


Toh kanada had'i dasu, sai dai banaka bane, Daddy ne jiya ya bani na amaryane kuma ya jadda damun kan cewar this week yakeso mukai mata


To sai kai kuma kace masa Me?




Ah, na karba tare da alqawarin ending week d'innan zamuje mukai mata, ya amsa masa


Papa yace to kaida Wa zakaje dakace zakuje


TJ yace banson iskancifa, dakai zamuje kuma ranan saturday dasassafe ma kuwa zamu tafi


Hhhhh wasan yara kenan, toh kasan Allah ba inda zani, kaida kaga zaka iya ga hanya asauka lfy


TJ yace yanzun Ameen abinda kake ya dace kenan, ace rabonka da zuwa wajen yarinyannan har ban iya tinawa


Ai dai ko bakasonta albarkacin iyayenta sai kaje ko, susan kasan da zaman yarsu


Amma ace har biki yana qaratowa ba ango ba labarinsa haba abakina kasake tinani


Shiru yayi yana sauraronsa har TJ ya tsammanin ya haqurane, amma sai ya tsuke fuska yace to su riqe yarsu mana su fasa aurarta inhar sai naje




Ganin dagaske papa yake, yasa TJ bashi baki, amma da kyar da sidin goshi ya aminta akan sharad'in bazasu kwanaba




TJ yace dama bazamu kwana ba, da azahar zamu juyo sai kuma biki da yardar Allah


Miqewa yayi yana duba tsadadden agagon dake d'aure ahannunsa, yace man barin wuce sai na tab'oka awaya zuwa yamma




Papa yace ok, sai munhad'u


Har zai wuce papa yace hey waka barma wad'annan sharan


TJ yace bazaka ajiye awajenkaba


Wlh kana barinmun su zansa masu lighter na qone shirme




Dawowa yayi ya tattarasu yace, Allah ya huci zuciyar Dr Muhammad Alamin ango na Fatyma Fauziyyah sha kallo, yana fad'in haka ya fice abinsa bai saurari mai zaiceba




*******
Fauziyyah acikin kwanakinnan dik ta lalace sabida rashin jin halin da yasir yake ciki


Yanzu layinsa datake kira tasamu koda bazai d'aukaba hakan yana kwantar mata da hankali


Amma sam yau wajen kwana uku kenan, baya shiga dik sanda ta switchoff take ji


Sosai hankalinta ya matuqar tashi har , abincima bata iya ci, hakan yasa ta galabaita har ta yanki jiki ta fad'i


Ba mama ba hatta Abba hankalinsa ya tashi sosai


Da kyar da taimakon Allah suka samu ta farfad'o


Mama ta bata tea mai kauri tasha, sai da natsu wata ya dawo tukun Abba ya matso kusa d ita ya zauna




Hannunta ya riqe cikin murya mai rauni yace Fauziyyah saboda bakyason auren Alamin yasaki a wannan halin?


Shiru tayi bata amsa ba sai hawaye dake bin fiskanta


Abba yace tabbas wani babban alqawarine acikin aurenki da Alamin wanda na amince na d'auke tsawon shekaru masu yawa, ataqaice tin bansan zan sameki ba


Nan tabata labarin yadda suke da amininsa da kuma alqawarin da suka ma junansu


Cikin damuwa Abba yace tabbas Fauziyyah na amince da zabinki dan yasir ya kwanta mun arai, sai dai ba yadda na iya ne


Amma ina roqonki amatsayina na mahaifi agareki ki amincemun ki yadda da auren Alamin, sannan kicire damuwa aranki kid'auka haka Allah ya rubuta yasir ba mijinki bane


Kidaure kiyiwa mahaifinki biyayayya kibani had'in kai na cika alqawarin dana d'auka, kada kibari ubangijina ranan gobe ya tuhumeni akan rashin cika alqawari ya kuma sanyani alayin marasa gaskiya


Cikin kuka tace ya isa haka Abba, wlh na amince zan auri ya Alamin har zuciyata ba akan ka tursasaniba


Abba ku yafemun bijire muku danayi, kuma zan nuna muku ni yar halaq ce dan bazan taba barin Allah ya kama mahaifina akan abinda yayi iyaka qoqarinsa nine sanadiba




Mama kibawa Abba haquri, na amince na amince nan kuka yaci qarfin ta




Mama ta rungumeta tana bubbuga bayanta, ya isa haka kiyi shiru Komai ya wuce


Abba yace mama bar kukannan haka Allah ya maki albarka


Haka

Please Login or Register in order to submit comment