Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta durqusa


Cikin murya mai nuna tsantsar damuwa da tausayi tafara magana


My king tabbas nasan ni mai laifice agareka da naboyemaka gaskiyan alamari ban sanar makaba


Sabida gudun kada ka gujeni gashi kuma abinda nake gudun ya sameni


Nan muryarta tafara rawa cikin kuka tace amma ya kamata katambayeni kafin ka yankemun hukunci


Shidai yana dai jinta amma ko matsi baiba baran ya tanka mata


Cikin kuka taci gaba da fadin


Wannan halin da kasameni aciki badason raina baneba nima


Tun ina jss wani ciwo ya tsiro mun agaba na shine akaini asibiti likitoci sukace sai anmun aiki awajen


Sanadin wannan aiki sukace zan iya rasa budurcina, bayanda aka iya haka akamun aikin dan nasamu lfy


Tasake fashewa da kuka mai tsuma zuciya, cikin sheshsheqa tace lokacinda maganar aurenmu ta taso saida mama tace nafada maka gaskiyar abinda ya faru dani amma sai naji tsoron kada ka rabu dani dan nariga da nakamu da matsanancin sonka


Dan Allah Dr kayafemun laifin dana maka da ban fada maka ba


Nan tadage taketa rusa kuka wane uwarta ce ta mutu cikin kirsa ta dago wayarta tana cewa barin kira mama nafada mata halin dana ke ciki danaqi jin maganarta ta turo ya muzammil ya kawo takardun aikin da aka mun kozaisa kayarda dani


Dik maganar dake cikin kuka takeyi


Tana saka wayar akunnenta sai taji ya wabce wayar ya wurgar akan bed cikin tausayinta ya rungumeta tsam ajikinsa


Itakuwa ganin tarkonta yakama sai tadada lafewa tana cigaba da kukanta




Cikin sigan lallashi yasa hannunsa yana shafa kanta


Yana cewa is ok my queen kiyi shiru nafahimceki nima kiyafemun dana maki mummunan fahimta




Dama nasan bazakitaba aikata abinda zuciya take tunaniba


Maimakon tayi shiru sai sake fashewa da kuka tayi


Wani irin tausayinta ne ya kamshi tabbas baimata adalciba daya bari zciyarsa ta amince da abinda ba gaskiyaba


Ganin yadda take kuka ta gagara yin shiru kawai ya saka bakinsa acikin nata yafara mata salo na musamman




Jin yadda yake bata wasu darusa yasa jikinta ya mutu murus har tayi shiru tana sauraronsa kawai


Shikuma ganin tafara samun natsuwa yasa ya dora daga inda ya tsaya




Ganin labari yafara sauyawa yasa na tattara nawa yanawa na fice na basu waje........




Pls kuyi haquri da wannan




โœ๐ŸปFaty Mmn Faty
[5:20PM, 8/20/2017] โ€ช+234 814 477 8681โ€ฌ: ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017




4โƒฃ2โƒฃ
*3 hours later*
Ahankali na lallaba nadawo dakin papa


Atsaye naganshi gaban mirror yana daure da towel a waist nasa


Da alamu wanka yafito, yana gyara suman kansa


Ta cikin mirror ya hangi juhaina wacce ta bashi full attention nata , ta zura masa idanu sai kallonsa take


Murmushi kawai yayi yaci gaba da abinda yake


Sai da yagama shafe jikinsa tsaf da cream n spray sannan ya wuce wajen kayan daya ciro


Black trouser ne da brown shirt, sun matuqar amsan jikinsa


Dik abinda yake har yanzu idon juhaina na akansa


Yana lura da ita amma ya kamar bai ganta ba saida ya qare shirin sa tsaf sannan ya tako ahankali har bakin bed inda take kwance cikin blanket


Sunkuyo wa yayi saitin fuskarta , hura mata iskar bakinsa yayi afiskanta


Cikin soft voice nasa yace my queen baki gajiya da kallona ne


Sauqe idanunta qasa tayi cikin murya mai cike da shauqin so tace bani gajiya n kuma ban jin akwai ranan da zangaji da ganin kyakyawar fuskar mijina


Cikin murmushi ya kai hannunsa yana shafa fiskanta yace kada kidamu my darling am all urs


Qanqame hannunsa tayi tace thanks my luv thanks a lot


Yace oh no my queen do not say that mana umm, u deserve morethan that, now kifadi mene kikeso kiyi break dashi


Cikin shagwaba tace anything


Umum kifadamun dai mene kikeso yanzun zan tura ayiyo mana take away


Sake shagwabewa tayi tace toh abinda zakaci shizanci


Yace umum my darling kifadi naki inyaso sai muci nawanma kada kizo bakisonshi


Tace toh chips da salad nakeso


N what? Ya sake tambayanta


Tace shikenan


Yace ok barin aika abdu inyaso sai naxo na maki wankan dan naga kingaji dayawa


Yana fadin haka ya juya zai fita sai yaji ringing na wayarta


Amma sai ta share kamar batajiba, shikuma ya zaci batajibane sabida ringing tone ba mai volume bane


Harta katse bata dauka ba


Yakai bakin qofa kenan sai yasakejin qarar wayar kuma batayi yunqurin dauka ba


Atunaninsa ko bataga inda ya ajiye mata wayarbane shiyasa ya dawo baya ya dau wayar ya miqo mata yace gashi aunty safna na kira


Amsa tayi cikin inina tace ko, to, thanks ta qaqalo wani murmushin dabai kai zuciba




Yana fita kira na uku yakuma shigowa,cikin sauri tadauka har hannunta na rawa


Daga dayan bangaren aka ce barka da safiya amarya, dafatan kintashi lfy


Cikin murya qasaqasa tace haba munnir ya zaka kirani da sassafen nan baicin kasan da wuya idan mijina ya fita kuma da kaga kamin missed call daya ban dauka ba ai sai ka haqura tunda kasan dole zan nemeka


Wata dariya yayi yace toh naji yanzu nayi laifi kenan


Tace aa bawai nace kayi laifi bane ba amma pls kada kana kirana


Nizan rinqa kiranka tinda alqawari namaka




Yace toh naji amma dai saiki san yadda zakiyi dani nan da 1 week dan wlh bazan juri rashin kiba




Itama cikin fada fada tace waime ke daminka ne munnir kabani time mana inafa sane dakai kuma wani plan nake son shiryawa yadda zaikasance kullum muna tare kuma gida daya


Murmushi yayi yace yawwa tawan yanzu naji zance mai dadi




Tace toh sai anjima idan nasami sukuni zankira ka anjima




Yace toh bye miss u


Ahankali tace miss u too sannan takashe wayar


Nan tashiga tunanin hanyar da zatabi da munnir kada ya balle mata aure dan tasan zai iyah


Tana cikin wannan tunanin papa ya shigo


Ahankali ta yunqura zata tashi dasauri yaxo ya kamata yace barin taimaka maki kiyi wanka ko




Murmushi tayi kawai dan gaba daya hankalinta na agun munnir wacce hanya zatabi ta kaucewa wayarsa


Haka suka shiga toilet ya taimaka mata tayi wanka


Itama shiryawa tayi cikin wando 3quater da wata qaramar top ta fesa kwalliya nan tyi dass da ita


Tanagamawa papa na shigowa yace madam muje muyi break ko


Murmushi tayi tace ok


Qarasowa yayi ya manna mata kiss a forehead nata yace kinyi kyau my darling


Kwantowa tayi jikinsa tace thanks baby




Atare suka fito inda suka zauna afalo sukayi break cikin kwanciyar hankali




Bayan sun karya maimakon ta tattara tarkacen takai kitchen na dostbeen ta zubar son samuma ta wanke na wankewa


Amma saita ture su gefe gefe ta gyara kwanciyarta akan laps nasa


Duban ta yayi yace my queen pls da kin daga wannan tarkacen anan mana ko


Turo baki tayi cikin shagwaba tace wlh nagaji sosai ga hidimar biki ga taka shiyasa ko motsi banson yi


Shiru yadanyi yace ok barin kaisu kitchen naxo na maki tausa ko zaki dan ware


Yana shiga kichen sai yaga cups da plate na jiyama ba awankeba dan baimayi tsammanin ta shiga kitchen ba


Hadasu yayi ya wanke sannan ya fito


Yana zama ta matso shi sosai tace yanaga kajima yace umm na dan gyara wajen ne shiyaa


Tabe baki tayi tace ok


Nan yadan fara matsa mata qafa ammafa ina juhaina saita canza layi dan ita bata gajiya da wannan lamarin nan suka tattara sukayi bedroom nasa acan suka gama shaaninsu kuma balaifi papa yana samun natsuwa dan baqaramin gyara tasha ba kawai dai waccan abinne da bai taba gyaruwa amma balaifi tana da niima




Sai bayan azahar suka tashi nanma ya aika akamusu take away


Da dare ma haka take away ya masu


Haka haka har kwanansu uku da aure kullum dare da rana sai dai take away kuma idan sunci bazata iya gyara wajenva baran ta wanke abinda suka bata


Daya mata magana sai tace itafa gara dik abinda suka bata asashi a shara inyaso asai wasu amma ita bazata iya wanke wanke ba




Yace toh zai dauko mata mai aiki harta amince amma daga baya datayi tunani saita ce bataso ba yanxu ba




Afannin munir kuwa tace ranan friday ya shigo bh ya kwana a hotel inyaso ranan saturday sai ya qaraso gidanta kafinnan dr yana gida


Nan ta shirya masa plan nata


Kwanan su shida da aure amma gaba daya papa ya kasa gane juhaina wacce irin mata ce


Komai ba ruwanta bata shara bata wankewanke bata girki ko daidai da rana daya bata taba tunanin ta shiga kitchen tamasu girki ba


Haka baruwanta da gyaran daki abinta sai dai toilet kam zata wanke tsaf ta fesa wanka da kwalliya koyaushe tana qamshi abinta


Ga danbanzan son yawo kullum itakam sufita suje nan suje can


Amma bata taba zuwa gidan momcy ba koda yamata zancen sai tace bayanzu ba


Washegari saturday wajen 12 bayan sun karya suna zaune afalo sai juhaina ta dubi papa tace my king anjima kadan wani cousin nawa zai zo fa




Yace ok wane kenan


Tace sunansa munnir yasamu admission anan ATBU


Papa yace ok amma baki taba ban labarinsa ba




Tace umm mamarsa qanwar daddy ce




Yace toh badamuwa sai ya shigo


Bada jiwaba kuwa aka norcking qofa




Papa ya tashi ya bude ganin saurayi matashi amma bazai kai papa ahaifeba yasa papa yagane shine munnir


Hannu ya miqa masa da murmushi yace barka da zuwa


Yawwa barka dai ya fada suna shigowa cikin falon




Da murmushi afuskarta tace yau malam munnir ne agidana


Shima da murmushi afiskansa yace nine dai amarya ba kya laifi




Tashi tayi ta kawo masa ruwa da juice harda snacks da papa yasaya masu sabida baqi


Ganin yadda take wani rawar qafa da baqon daga zuwansa harta kawo masa ruwa ya fahimci lalle baqon yana da muhimmanci awajenta


Nan suka rinqa hira inda takecewa yaushe zaku fara lectures ne


Tabe baki yayi yace wlh nifa kamarma na haqura da school dinnan


Juhaina tace mai yasa kake yin hakane munnir yanzu wannan shekara na uku fa kenan kanasamun admission amma sai kayi wasa tomeye dalilin daxaka bar school din




Yatsina fiska yayi yace nifa kinsan barin iya zama acikin school ba




So inda zamu samu renting din kuma wai lokaci ya qure dik ankama




Sai wani waje da aka nuna mun shikuma gaskiya bai munba so kawai gara na haqura


Juhaina tace lalle ma akan wajen zama sai ka haqura da karatu dama dai bakason ATBU


Yace ahto ba sunqi sukai mutum wajeba sharp2 yaqare ya dawo




Juhaina tace aikaine baka nuna kanason karatun da gaskeba shiyasa amma badamuwa indai wajen zamane zamuyi magana da my king


Anan sukaci abinci rana sannan ya tafi wajen laasar




Da daddre juhaina tana kwance ajikin papa sunyi shirin bacci


Ahankali tace my king




Naam baby na akwai damuwane


Daga kanta tayi alamar eh




Cikin sauri yace damuwa kuma wacce irice baki fadamunba




Marairaice murya tayi tace wlh kaga munnir shine babba agidansu kannensa mata ne acikin su daga wacce yanzu take service sai wacce take shirin gama skull amma shi yaqi yadda da karatu sai yanzun nema aka samu ya yarda




Gashi shine namiji babba kuma shine hope din daddynsu




Pls ka taimaka kabarmasa BQ mana yazauna kona wannan semester mana




Shiru yadanyi kamar mai nazari




Jin yayi shiru yasa juhaina tace pls mana my king kataimaka




Yace ok badamuwa inyaso saiki fada masa gobe yayi parking ba matsala dik abinda kikeso nima inaso




Cikin jindadi ta qanqameshi tace nagode nagode my king


Daga nan suka lula duniyar maji dadi....




Wai wanene *MUNNIR*?
Kubiyoni a next page dan jin wanene munnir kuma meye hadinsa da *JUHAINA*






โœ๐ŸปFaty Mmn Faty
๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017




4โƒฃ3โƒฃ
Washegari da safe juhaina ta kira munnir a waya tasanar masa saqon papa


Da yamma kuwa lis sai gashi nan da kayansa ya dawo inda yasamu ansaka halliru mai wanki da guga ya gyara masa ko ina




*WANENE MUNNIR*
Mnnir shuaibu shine ainahin sunansa, iyayensa sun jima da rasuwa tun yana dan qarami


Ahannun baffansa ya taso wato qanin mahaifin sa


Tun tasowan munnir ya taso da rigima ba ta kadanba


Gashi da son karyan kudi sai dai Allah bai bashi ba


Tunda ya kammala makarantar sakandire bai cigaba ba sabida halin rashin kudi


Daganan bashida aiki sai bin yaran masu kudi sune party sune biki ahaka ya tabe


Watara sunje birthday party na wata budurwar abokin abokinsa anan ya hadu da juhaina lokacin tazo hutun qarshe wadda daga shi ta kammala karatunta


Lokacin da juhaina ta kyalla idanu taga munnir sai taji ya birgeta har tana sonyin alaqa dashi


Daga nan tazo tasameshi inda yake zaune nan ta nuna masa cewar tana sonsa


Shikuma tunda yaganta ya fahimci akwai yayan banki atare da ita nan ya bada kai bori ya hau


Tundaga ranan juhaina suka dinke da munnir itace kemasa komai na hidimar rayuwa


Tasaya masa waya mai tsada


Ta saya masa kayan sawa ta bashi kudin kashewa


Har lokacin komawarta singapore yayi


Bayan ta komane ashe tana da shigar ciki na wata daya, acan ta zubar dashi bayan tafadawa munnir abinsa ya farru




Juhaina sosai takeson munnir dan araayinta idan ta tashiyin aure shidata aura haka shima ya amince da batun aurenta tinda shikam ya samu tana masa komai


Bayan ta qare karatunta ta dawo nan suka dora daga inda suka tsaya itada munnir


Lokacin da papa yazo mata da maganar aure bata boyewa munnir ba


Amma shi saiya ce sam baisan zancen ba kuma ba auren da zatayi ta barshi


Nan tace masa wane shi harya isa ya hanata aure dama itace tace data aureshi kuma tafasa sai yaya


Duban bakida wayo yamata yace wlh intayi aure sai da yardarsa dan zaije ya samu saurayin nata yafada masa gaskiyar abinda ke takaninsu inyaso yaga yanda zatayi


Sanin munnir zai iya bin diddigi ya samu inda papa yake yasa ta lallaba shi dan tana matuqar son papa sosai


Dakyar tashawo kan munnir ya amince amma da sharadin suna tare koda tayi aure


Haka ta amince akan bayan bikinta zata sama masa koda gidane inda zai zauna saiya dawo bh da zama harma ya fara karatu
Wannan kenan


*****
Bayan sallar magribah papa da juhaina suka fita basu jimaba suka dawo dama abinci sukaje sayowa


Bayan sunyi parking Abdu yazo dasauri ko da akwai abinda zai shiga dashi ciki


Cikin girmamawa yace barka da dawowa oga


Aha Abdu shine abinda yafada yana miqo masa abincinsu adaqike yace gashi na hutar dakai fita


Juhaina ta fito da leda guda uku ahannunta yayinda uban gayyar shima ya fito


Har zata wuce sai papa yace my queen


Juyowa tayi ta amsa da yess my king


Inaga mu miqama munnir abincinsa idan munshiga ciki basai munfitoba ko


Ok muje to tashi dashi


Munnir kuwa tunda suka shigo yake tsaye ajikin window yana kallonsu cikin baqin ciki


Dan wani haushin papa yakeji cos y rage masa jin dadi ganin sun nufo wajensa yasa cikin sauri yasauqe curtain ya koma kan cussion ya zauna yana latsa wayarsa


Norcking suka masa


Daga ciki yace yess come in


Suna shigowa dasauri ya tashi cikin murmushin dole yace barkanku da shigowa


Papa yace yawwa amma yana tsaye cos baxama zaiyiba


Miqomasa take away nasa tayi tace bross ga abincinka sai da safe


Allah ya kaimu yafada yana bin bayanta da kallo


Nace sai kayi ai matar wani ce๐Ÿ™„


Bayan sun ci abinci papa ya dubi juhaina amma bada wasa ba yace my queen yakamata kifara dafa mana abinci tunda kinga yanzu ga munnir ma bai dace kullum muriqa bashi abincin wajeba


Ganin yadda yayi maganar bada wasa ba ya kuma sha murr yasa tace shikenan Allah ya kaimu


Washegari da safe ta dafa masu indomie


Sai dai satisfactory haka sukaci dan bai wani test ba


Da rana kuma haka aka kwaba white rice da stew dikda kajin dake ciki amma sam kasa ci sukayi dagashi har ita


Sauran mutanen gidan kuwa banbi takansuba


Ai daga kan dinning yace mata kada tamasu dinner tabari kawai dan yafahimci bata iya girkiba


Haka sukaci gaba da zama ahaka inda azuwa yanzu yafara gajiya da halayenta sam


Gashi bata kunyar idan yace tamasa abu tace bayanzuba


Satin bikinsu biyu TJ ya kwanta rashin lfy fever mai tsanani har saida papa yaje ya saka masa ruwa agida da allurai


Amma abinda ya birgeshi da gidan TJ shine tsaftar matarsa ko ina kyalkyal kamar baa takawa sai qamshi kawai dake tashi ta ko ina


Gashi ya lura da tana son TJ sosai ba irin sonda juhaina kemasa ba tinda dik abinda yakeso shi take masa


Agidan ya wuni ranan bayan tagama abinci ta kawo masu amma TJ sai ya gagara ci


Papa kuwa haka yaci yaqoshi yana santi aransa har yana inama ace matarsa haka take


Ganin yakasa cin abinci dik ta damu sai tambayarsa take mezaici adafa masa


Yace tamasa faten irish potatoe da hanta da alayyahu


Nan da nan ta daho ta kawo masa balaifi yadanci kuwa sai anan hankalinta ya kwanta


Sai gab da magriba ya tafi yana fitowa wayar juhaina ta shigowa


Doguwar tsuka yaja kafin yadau wayar dan


Tun bayan laasar juhaina take kiransa awaya yaushe zai dawo


Cikin jin haushi yace wai meyene kika dameni aidai zandawo ko ko ancemaki bata zanyi yana fadin haka ya kashe wayar dan wani haushinta yakeji yanzu dayaga yarinya qarama yadda ta iya komai da kula da miji


Ita kuwa banda abiya mata buqta batada aiki


Yana tafiya yana tunanin gaskiya dole dasake inma makarantar koyan girki da gyaran gida zata shiga sai dai tashiga dan zamansu ahaka bazai yiyuba


Itakuwa tasamu dama suna sheqe ayarsu da munnir shiyasa ajima kadan ta kira taji koya kusa dawowa kada ya dawo yasamesu atare




Amurtuqe ya shigo gida direct room nasa ya shige sai bayan yayi wanka sannan ya fito


Juhaina ta dubeshi tana zaune afalo tana kallo tace wai lfy kuwa hooney kaketa bata rai


Nakira ka awaya kana wasu magana gashi kadawo kuma ranka abace


Yace eh kawai zamanmu ne yakamata mu gyara


Gyara zama tayi tace toh kamar me kenan


Yace yanxu ace ko girki baza ki iya yimana ba komai idan inason nagani da kyau sai dai inni nayi haba


Kawai nayanke shawara zan maki register a school na koyan girki da kula da gida


Dubansa tayi nan taji ranta ya baci wato raini ne yasa zai zo yana fada mata haka


So kawai gobe zanje na mak........




Hannu ta daga masa tace heeyheey ya isa haka Alamin kul karkasoma wannan maganar


Da mamaki ya dubeta yace ni kikecema hey har kina dagamun hannu


Tace anfada maka din so what


Kuma ko cemaka akayi mai aikice ni da zaka fara tsiro da wani abu aidai ciyar dani dolenkane


Ko ance maka agidanmu inayin girkine har zakazo kanamun wasu surutai da shouting


Cikin bacin rai ya dubeta yace lalle juhaina nikike fadama haka ba kunya


Tace nice ma kai kajiko


Hannu ya daga zai mareta sai yafasa


Wata dariya ta sheqe dashi tace ya kafasa lalle da kamari mai tsada dan wlh ramawa zanyi tsaf ni banza bazata shani ba


Ko ashaye kazo kada ka taba kwatanta dukana dan ni bazan tolarating nonsense ba




Dubanta yatsaya yi dan baitaba tunanin tasan yana shan wani abu ba tunda boye mata yake


Itama dubansa tayi ido cikin ido tace yess ko ka dauka bansan kana shayeshaye bane kawai kallonka nake so kada kafara abinda zai dameka kaji nafada maka tana fadin haka ta wuce shi tabarshi awajen


Tsabar mamaki da bacin rai yakasa koda motsi kamar wadda aka dasa......




Wai ina labarin mutan Abujane kam๐Ÿค”


Kubiyoni a next page domin jin labarin *Swt Fauzy*






โœ๐ŸปFaty Mmn Faty












๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ




๐ŸŒพ๐ŸŒพ๐ŸŒพ






Budurwar Qauye๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€๐Ÿคท๐Ÿผโ€โ™€


Written by Faty Mmn Faty


August, 2017






4โƒฃ4โƒฃ
Ahankali ya wuce ya nufi room nasa yama rasa wanne irin tunani zaiyi guda daya


Tun daga ranan ya shareta ya fita aharkarta shi atunaninsa zatazo ta basa haquri


Amma har sukayi 5days ahaka itama bata kulashi kamar yadda bai kulata


Abincima sai dai ta tura asayo mata


Papa kuwa abin ya masa yawa wai suna yana da mata amma babu abu daya dayake amfanuwa dashi ata bangarenta


Dan abinda yake samunma yanzu baisamu tunda sun kancake


Gajiya yayi yaje yasameta ya lallaba ta suka shirya


2weeks later
Yanzu hutun daya dauka awajen aiki ya qare hakan yasa juhaina ta bude sabon babin walawanta


Sassafe kafin papa ya tafi aiki munnir yake fita amma yana fita zata kirashi awaya ya dawo


Ta back door yake shiga wajenta yadda bawanda yake sanin shigarsa


Kullum suna shan shagalinsu da munnir hakan yasa yanzu ko papa bako yaushe yake samun biyan buqatarsa


Dan taringa masa hanya2 kenan aa daga tace batajin dadi sai tace bacci takeji


Idan ya matsa mata sai tace toh bata cikin mood din wannan abin


Gashi yanzu tamaidashi kamar ATM mashen sabida kullum acikin ya bata kudi take


Ga yawon tsiya da koyaushe sai dai ta dauki motarta ta shiga gari


Sau da dama haka zai dawo bai sameta ba


Yau dama tun bai fita ba yamata kashedin kada ta fita ko ina idan yadawo office zasuje gida sugaida daddy baiji daddy ba


Bayan ya dawo suka shirya sukaje basu jima ba ta dameshi da sutafi sabida yadda bata samu fuska awajen momcy ba haka aunty niima bata sake mata ba


Bayan sun tafi aunty niima ta dibi momcy tace momcy wlh matar papa ashe bayarinya bace yanzu naqare mata kallo da kyau


Cikin takaici momcy tace wannan ai idan bata girme masa ba toh saidai suzo saanni dan bai isah ya girmetaba


Aunty niima tace wai ya labarin fauziyya ne kam nakai 3days banyi waya dasuba


Momcy lfyrta qalau dazunma munyi waya da mabarukha tacemun tatafi makaranta


Aunty niima tace Allah sarki Allah ya bata miji nagari yarinya mai haquri


Momcy tace insha Allahu Allah zai canza mata da mutumin kirki


Haka sukayita hiransu suna jajanta abinda ya wuce


*****
Juhaina ce tsaye gaban papa ta riqe qugu ranta abace


Fiska a tsuke tace wai Alamin maeke damunka ne dannace kabani kudi shikenan sai kafaramun kididdiga kuma kana dashi bawai baka dashiba


Shima cikin fada yace ai banace bazan bakiba but i just want to know mezakiyi da kudinne ke kullum cikin abaki kudi kuma banga me kikeyi dasuba


Ahasale tace idan bazaka bani bane kawai kafadamum bawai kana wani kwana ba


Kallonta yayi dakyau sannan yace toh bazan bayarba ki kwata


Ok is that what u said tace dashi tana wani turo qirji


Yeah haka nace kin wani tsareni kamar wani danki kina turomun tsumma


Kutt qirjinawa ne tsumma ta fada cike da bacin rai


Adaqile yace toh meye acikin ido banda ruwa ni bani hanya kiga ina da abinyi


Naqi nabaka hanyan marar mutunchi kawai kuma ahakan kake kwantar da kwadayinka ba


Ya tsina fiska yayi yace eh arashin uwa ba


Nan sukayi tsiya tsiya kamar zasu daki junansu


Da kyar yasamu ya shige dakinsa ya kulle dan shakkar juhaina yake kuma ya tabbata idan ya daketa zata iya ramawa shiyasa bayi attempting dukanta


Kwanaki na tafiya, watanni sun shude


Haka rayuwa yaci gaba da tafiya tsakanin papa da juhaina


Zaman lfy da kwanciyar hankali sun qauracem papa kullum yana yawon wajen cin abinci kuma itama dole ya kawo mata nata inba haka ba bayi da kwanciyar hankali


Kudi kuwa ko yaso ko yaqi dolensa ya bata


Abunda yafi daminsa yanzu yawo da ta qara couse akai yakuma rasa inda take zuwa tunda bata da yan uwa bauchi amma kusan kullum bata yini agida


Munnir kuwa yanzu yayi sabuwar budurwa


Dazaran juhaina ta bashi kudi ita yaje zuwa ya kashewa shiyasa kullum acikin tambayarta kudi yake


Time to time kuwa yana zuwa kd yayi two weeks harma fiye da haka


Yanzu haka mota juhaina tamasa alqawarin zata canza masa


Itama can wajen yawonta tayi sabon kwarto shiyasa yanzu bata damu da mumnir ba


Ita yanzu hanyar da zata samu ta koreshi take nema shiyasa takeson tacanza masa mota ta lallaba shi ya koma kd


Wasa gaske yanzu aurensu ya doshi shekara amma shiru ko batan wata bata tabayiba sabida kwayoyin hana daukar ciki datakesha


Dan bata shirya haihuwa yanzuba acewarta zata tsufa da wuri kuma ma ita bata shaawar yara dan wai takura garesu


Ya zuwa yanzu dik wadda yake tare da papa zai fahimci akwai abinda ke daminsa kawai dai bai fito ya fada bane


Amma acikin zuciyarsa yafara danasanin auren juhaina tunda bai qareshi d komaiba


*****
Aunty mabarukha nagani tsaye ajikin mota da alamu fita zatayi unguwa sai dai kamar jiran wani abu take


Fauziyyah ce ta fito cikin shiga ta alfarma wadda sai danayi da gaske naganeta


Taqara haske taqara girma


Wata arabian gown ce pusher pink wacce ta matuqar shan adon duwarwatsu masu kyallin gaske


Ta rolling veil din rigan akanta hannunta riqe da wata waya mai dan banzan kyau


Cikin sauri ta qaraso wajen aunty
Tana cewa am sorry aunty nabarki kina jirana


Aunty tayi murmushi tace no badai kin gamaba muje bazama mujima ba zamu dawo sabida kada su daddy sudawo daga islamiyya


Ok ta fada tana shiga mota


Gidan wata qawar aunty sukaje suka karbo wasu kaya tadawo daga dubai


Bayan sundawo yara ma sundawo daga islamiyya suna hira afalo


Aunty ta dubi fauziyyah tace Fauziyyah inaga tinda yanzu kina SS2 kawai kizana SSCE inyaso bazaki fasa zuwa school ba


Idan paper yayi kyau sai munemi admission kawai


Fauziyyah tace

Please Login or Register in order to submit comment