Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace kiyi shuru kibar kukan haka nan tashi kije ɗaki ki huta ahankali tamike jiki asanyaye tashige ɗaki,




*Bassam* ne ya kalli abbu cikin bacin rai yace abbu me wayan nan mutanan suke nufi?...yace bansani ba *Bassam* amma yanzu tashi muje gidan naji tabakin su, da sauri yamike shima yatashi suna fita suka samu abin hawa.




********"
"Suna isa akai masu iso har falon zaune suka iskesu dad aunty *Bebe* da *Bulama* sai ko mutumin ku wato *Blue* wanda yaci kuka yagaji barci yaɗauke shi agurin sai sauke ajiyar zuciya yake gwanin tausayi, bayan sun zauna angaisa wanda *Bulama* ne ya amsa masu fuska asake sabanin dad da aunty *Bebe* da fuskar su take ɗaure,




"Cikin mutunci abbu yace Dr meke faruwa ne naga *Beenazar* tazo gida...cike da bacin rai yace "ita bata faɗamaka abinda yafaru bane?..ito kasan akwai ƙuruciya tare da'ita don haka bayanin natane banfahimce shiba shiyasa, nace bari nazo dakaina nasake jin karin bayanin daga bakin ka...




cike da hasala yace to y'arka ciki ne da'ita kuma bana ɗana bane shiyasa na koreta taje can tanemi uban shegen cikin ta,




"Abbu yace menene hujjar ka nacewa cikin jikinta" bana ɗanka bane?....yace yau wata uku dayin auren su ita kuma da'aka aunata cikinta watan shi hudu, kaga kenan bacikin Shiba ne sannan ma tayaya wanda bada hankali zaya'iya tarayyar aure eye?.. kawai dai tazo ta lika masane sai Allah yakamata,




"Murmushi manya abbu yayi tare da cewa wannan shine hujjar ka?...eh aini wlh bansan cewa "y'arka Bata da tarbiyya ba dabaz....cikin ɗaga murya abbu yace lah!...kai kasan yaniwa "y'ata tarbiyya me kyau wanda shika gani karokeni nabawa ɗanka auran ta, sannan don ɗanka bayada hankali shikenan sai bazaya iya tarayyar aure ba?...




"eh mana, to wannan ba hujja bace tunda yanada rai da lafiyar jiki dole zaya'iya tarayyar aure da mace har yayi mata ciki, don haka tabbas cikin jikin *"Beenazar* nashine domin na tambaye ta tafaɗa mun rabonta daganin al'ada yau wata uku kenan, kuma alissafi yau watansu uku da auren su harma dawasu kwanaki....




"Dakarfi dad yace to nidai wlh bazan ɗaukar wa ɗana wannan cikin ba tunda bana Shiba ne, wani irin murmushi bacin rai abbu yayi tare dacewa to madallah ni na ɗauka tunda sakakyyar dazakai mun kenan ko?....zanyi maka ko zakai mun?...to shikenan yanzu ya matsayin auren shi dake kanta?...yace ai yasaketa saki ɗaya to yayi kyau abani shaida to,




"Wata takarda dake kusada shi nannaɗe yamika mashi, karba abbu yayi tare fadin masha'allah shi *Bilal* ɗin ne dakansa yasaki *Beenazar* ɗin?...ahasale dad yace eh, to aishikenan saidai dr Lawai inasan kasani komin daran daɗewa *GASKIYA* zata bayyana,




cike da masifa yace ta bayyana mana sai me?..to shikenan tashi muje *Bassam* tashi yayi sukafita kamar zaya kurma ihu dan bacin rai,




"A zuciyace *Bassam* yace abbu wlh karya suke da sauri abbu yace kul! nasake jin kace babba yana karya baku kyau, ciki bacin rai yace to abbu amma dai abinda suka faɗa akan "aunty *"Beena* ba gaskiya bane?




wlh ƙazafi sukayi mata itada bata taɓa kula saurayi ba shine zasu ce haka wlh cikin yah *Blue*, Kuma wlh abbu ba yah *Blue* bashi yarubuta takardan sakin nan ba murmushi karfin hali abbu yayi tare fadin karka damu inshallah gaskiya zatayi halinta kai ya girgiza ahaka har suka isa gida,




kiran *Beena* yayi yaita bata baki sannan bai faɗa mata maganar sakinba domin shibawai ya yarda da sakin bane cikin kuka tace abbu yanzu shikenan mun rabu da yah *"Bilal*?....




"Kai ya girgiza cike da tausayin ta domin yasan zuciyar ta cike takeda kaunar minjinta saidai kuma gawata jarabawa da Allah yaƙaddara mata saidai aimata addu'ar allah yabata ikon cinyewa,




yace a ah baku rabuba tunda gakin nan ɗauke da cikin sa don haka ki kwantar da hankalin ki kinji ko?...kaita gyaɗa tare datashi tanufi ɗaki.




**********
*Hakan *Beena* tacigaba da rainon cikin cike da kewar mijinta da tunanin halin dayake ciki narshin ta kusa dashi, wanda ta tabbatar sai yashiga wani hali kamar yanda itama take ciki,




"Sannun ahankali cikin yashiga wata hudu wanda duk wanda yaganta yasan tana ɗauke da cikin domin gaba ɗaya jikinta ya baiyana hakan, gashi yana matukar bata wahala kusan duk abinda taci sai ta amayar ga gawani irin son kamshin turaren *Blue* datakeyi Allah ya taimaketa cikin kayanta tahaɗo dawata singlet dinshi don haka shi take shaka taji daɗi.




********
Aban garen *Blue* kam tsayawa fadin irin halinda yashiga narashin *Beenan* shi akusada shi bata lokaci ne,




"domin ko yayi mugun shiga wani hali duk yarame saboda yanzu aunty *Bebe* tasamu dai-dai din shi tana cigada dayi masa tsafi to hanyar hanashi barci,




kasan cewar yanzu *Beena* batasa mun yimasa ishasshen addu'a kamar da saboda yanayin datake ciki na laulayin ciki don haka idan kaganshi saiya baka tausayi matuka,




" kasan cewar tun bayan faruwar komai washegari sai ta tafida shi can abujar inji cewarta wai har yamanta da *Beena* koda sukaje sai wata muguwar ƙawarta tarkata gurin wani hatsabibin boka yasake burkuce kan *Blue* din,




domin kuwa wasu baƙaƙen aljanun yasake tura masa don haka yasake komawa tantirin majanuni sannan tace da bokan yarufewa dad baki karyasake maganar wata *Beena*, satin *Blue* biyu ta dawowa dashi, tare dabawa peter wani magani yaringa zuba mashi cikin abinci da abin sha don haka komai yasake jagulewa dad duk yashiga wani hali na damuwa.




**********
"Aban garen su ammu kuwa saida kawu muda yaɗauki tsawon sati uku sannan yahaɗa kan komai yakawo, cikin kwarewa abba yaraba kan komai inda ammu ta tashi da gidaje guda biyar da filaye biyu gida uku anan abuja har da guda acikin anguwar su abban,




"Sai biyu acan zariya da filaye biyu sai zunzurutun kuɗaɗe har naira miliyan bayan antabbatar da komai na nan cikin abujan, sannan yasa akaje can zariyan duk akaga komai sannan sai ta dankawa abba komai,




"Yayinda shikuma yasa aka buɗe mata account kazuba kudin sannan suka shirya dukkasu suka nufo Zariya.



******
Ranan lahadi da misalin karfe 10:30am nasafe su ammu suka iso garin zariya kasan cewar sun taso dawuri, *Beena* tana ɗaki tana barci kasar cewar yanzu batasamun yin barci da dare sai gari yawaye sai tayita ramuwar barcin,




yayinda su *Bassam* suna tsakar gida suna wanki tunda yau lahadi abbu kuma yana gefe yana kallon su sai sugajin sallamar ammu,




Cak! suka tsaya dukkan su suka zubawa ƙofa ido aikam saigata tashigo fuskarta ɗauke da fara'a, aikam suka saki kayan hannun su harda *Bassam* suka nufeta dagudu suka rungume ta suna wani irin ihun murnad dafaɗin ammun mu ayoyo, yayinda abbu yamike zumbur yazuba mata ido itama kallon shi da matsananciyar mamakin ganinshi ahaka,




"Ahankalin yakarasa gurinta cikin tsananin murna yace fatimata kece?...kaita gyaɗa dama sauda yawan lokuta jikina yana bani kina raye ashe hakan ne?...kai tasake gyaɗa mashi yayinda hawaye yake kokarin bin ƙuncinta,




Hannun yaɗaga sama yana me godiya ga Allah daya dawo mashi da matarsa uwar yayan shi sannan yakalli *Bassam* cike da farinciki yace *Bassam* karku kayar mun da Fatima ta mana, dariya sukayi dukan su cike da murna suka saketa sai alokaci abbu yaga su Abba dake tsaye suna kallon su cike da tausayin su,




yace a ah fatima ta ashe tare kike da Baki?..tace eh zuciyar ta cike da tambayoyi abbu yace sannun ku sannu dazuwa ku kushigo mana yafaɗi yana meyi masu jagora zuwa falo, yayinda suka bishi su *Banu* suna rikeda hannun ammu wacce keta kallon abbu dake tafiya lafiya mamaki take ya'akayi?...




Shigar su falo yayi dai-dai da fitowar *Beena* ɗaki tana yamutse fuska domin barcin bai isheta ba gashi hayaniyar su ta tasheta, ganin ammu ne yasata murza ido sai Kuma tabuɗe aikam ammu tagani hakan yasata saki ihun murna tare zuwa ta rungume ta sai kuma tasaki kuka, tana faɗin ammu dama kina raye shine kika barmu?...




"Ɗagota tayi daga jikinta ta ƙura mata ido inda nan take tagano tana ɗauke da ciki gaban tane yai mugun faɗuwa, cikin dariyar karfin hali tace eh to mine kuma na kuka bagashi Allah yadawo Dani gareku ba, sannan ta kalli abba tare dacewa yaya kuzauna mana kasan cewar haka take kiransa,




"Bayan sun zauna sai *Bana* takawo masu ruwa suna cikin sha sai ammu tamike wacce hankalin ta gaba ɗaya atashe yake da ganin yanayin da *Beena* take ciki, kallon ta tayi tare da kiranta ɗaki suna shiga ta kalli *Beenan* kirjinta yana bugawa tace *Beenazar* menake gani ajikin ki?...,




"Cike da rashin fahimta tace ammu mekika gani?... hararan ta tayi cike da bacin rai tace keee! banasan shashancin banza ina tambayar kina tambaya ta?...cikin faɗuwar gaba tace kiyi hakuri ammu ban fahimci kibane,




"Cikin fargaba tace ciki nagani ajikin ki ko?....kai ta gyaɗa kirjinta nacigaba da bugawa ido ammu tazaro cike da tsananin bacin rai tashaƙo wuyan ta tare da cewa....




Muje zuwa




*LUFHAT CE* Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment