Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaje kasa kaji?..., still shuru bai bata amsa ba Kuma bai daina abinda yakeyin ba, hakan ne yasata tafara kokarin jawo tawul din saidai abinda batasani ba tuni yarabata da tawul din hakan ne yasake bata tsoro takoma ture shidaga jikinta cike da fargaba take fadin pls yah *Bilal* ɗagani Mana kaji?...



"Cikin tsawa haɗe da shagwaɓa yace stop it my *Beena* friend, ido tazaro ciki wani irin tsoro da yasake kamata kirjinta yana cigaba da matsananci bugawa, cikin rawar murya tace pls yah *Bilal* zansa kayane fa kaji?.. yace um! umh! wait i want to do something, cike da tsoro tace what?...baice mata komai ba sai cigaba da abinda yakeyi kawai yake,




Wanda kona sakon ɗaya bayason yabari domin haɗuwar jikinsu yasa shi jin wani irin yanayi me daɗin gaske wanda bazaya musaltu ba.




Nikam ganin abinda *Blue* yake wanda ko ba'afaɗa maka ba zaka fahimci, kokarin maida *Beena* cikakkiyar yamace yaka,




amma koshi baisan hakan ba tunda baya cikin hayyacin shi, don haka nayi waje domin bai kamata natsaya ganin abinda zaya faru tsakanin ma aurata ba lol.




*********
Kiran sallar farko ne yafarka Dani daga gyangyaɗin daya kwasheni tun Bayan fitowata daga dakin *Beena*, don haka bari naje ɗauko maku rahoto lol.




Kwance take lullufe da bargo sai rawai sanyi take kallon daya zakai mata kagane zazzaɓi yakamata ko Kuma yana shirin kamatan, yayinda shikuma yake zaune agaban ta rikeda hannun ta tacikin bargon, cike da shagwaɓa haɗe da damuwar ganin halin datake ciki yake fadin pls sorry my *Beena* friend wake up,




ahanka tabuɗe idanun ta dasuka kumbura da'alama tasha kuka, kunnen shi yakama cike da shagwaɓa yace am sorry l hurt ko?...




murmushi karfin hali tayi tare da tashi taja tawul ta ɗaura sannan tazuro kafafunta kasa tamike, wani irin jiri taji yaɗauketa Dan haka takoma gefen gado ta zauna da sauri yariketa kasan cewar tuni shima yamike, kamar zayayi kuka yace I hurt ko my *Beena* friend?....Kai ta girgiza alamar a ah baki yaturo tare fadin I hurt my Beena friend see the blood yana nuna mata bedsheet da sauri ta kalla, gabanta ne yafaɗi ido tarintse koba afaɗa mata ba tasan yau tazama cikakkiyar mace shikenan tashiga sahun manya, kuka ne yakufce mata wanda yasa tafarayi batare da tasani ba hakan yasa jikin *Blue* yai sanyi ahankalin yace sorry I know I hurt bazan sake ba kinji?...




batace masa komai ba da'alama batajin shin don haka sai shima yafara kukan tunda baida wuya agurin shi sautin kukanshi ne yadawo da ita hayyacin ta, da sauri tashare hawayen ta tana murmushi karfin hali tace yah *Bilal* meyasa make kuka?...kallon tayayi yace u are cry because I hurt u I say am sorry kin ƙyaleni, dariya tayi tare fadin lah to aibanji kabane aina hakura barinaje nayi wanka kaji?...




shima dariyar yayi yace to tare zamuyi ko?...shuru tayi sai kuma to muje tare suka tashi still tana ganin jiri riketa yayi sukashiga toilet din.




"A bayi Kam ansha badaƙala Bayan sunyi wanka wanda saida tagasa kanta tukun, sai tayi ninyan yin wankan janaba shikan sai yatashi zaya ɗaura tawul da sauri tace yah *Bilal* bakayi wankan janaba fa,




kallon tayayi cike da rashin fahimta can kuma sai yace mata my *Beena* friend nayi, gabanta ne yafaɗi cike da tsoro ta tuna ashefa bayada hankali cikin sanyi murya tace sauran ɗaya kafaɗa yamake alamar bazaiyi ba kai atakaice dai ɗa ƙyar tasamu yayi wankan janaba wanda saida taimako ta tunda baya cikin hayyacin shi,




Bayan sun fito takaishi dakin shi taciro masa jallabiya dark blue yasa sannan tarakashi yawuce masallaci dake cikin gidan, da ƙyar yanayi yana waiwayenta domin cewa yayi saita jirashi yafito tace to, tana tsaye har yashige masallaci sannan itama taje tashirya tabi jam'i.




*****"***
Washe gari da misalin 10:30am aunty Bebe ce da yaranta suka
tashesu daga barcin, da suka koma tunbayan dawowar *BIue* daga masallaci,




Cikin girmamawa *Beena* ta duƙa tare dacewa Ina kwana aunty?...bayabo ba fallasa ta amsa tana meyi Masa wani irin kallo me cike da tuhuma irin kamar tafahimci wan abu yashiga tsananin su gabanta ne yafaɗi aiko datashiga uku Amma dai bari ta tmby ta acikin hikima,




Su jiddo kuwa tuhi suka ajiye breakfast din da suka shigo dashi suna dariya tareda *Blue* Wanda ganinsu duk daɗi yakashe shi, ganin duk ahankalin su yaɗauku yasa aunty *Bebe* taja hannun *Beena* suka shiga ɗakin ta,




"Zama sukayi agefen gado cikin hikima take tmbyr ta kowani abin yashiga tsananin su da *Blue* tace a ah bakomai, tayi juyin duniya *Beena* tafaɗa masa wani Amma tace bakomai hakan yasa ta yarda eh bakoman har da sauke ajiyar zuciya tayi,



Sannan tafito da magani tabata tare dacewa maganin shine taringa zuba mashi acikin abinci kullum, karba tayi jikinta asanyaye hakanan taji aranta magani bai kwanta mata ba amma bayanda ta'iya,




sannan suka fito Nan suka barsu zasuyi breakfast *Blue* sai jin daɗi yake gashi ga *Beena* Dan haka sai surutu yake zubamata.




*Bayan wata uku*


********
Raruwa ta ɗan sauyawa su *Beena* ita da yan'uwanta tuni suka koma zuwa school, domin tuni dad yabiya kuɗin makarntar itakuma har ta rubuta ɗaya jarabawa wanda dad yaso abiya kudi saidai abata takardu saitace a ah itadai tanason tarubuta dakanta,




Dan haka yabarta taje Wanda tareda *Blue* suke zuwa tunda konan da can baya bari taje batare da shiba, shiyasa komai tare sukeyi wanka ne barci ne wanda tun ranan sukeyi tare kuma kusan kullum saiyayi tarayyãr aure da'ita wanda babu yanda zatayi tahana shi,




"Tunda tafahimci yana son haka dan haka take barmasa jinta yayi yanda yakeso dashi, saida gurin wankan janaba tai ta fama master *Blue*😂.




"Don haka yanzu su *Beena* kam basuda sauran matsala tafannin rayuwa saidai tarashin ammu Wanda kullum addu'a suke idan tana Raye Allah yabayyana masu ita aduk inda take,




Sai kunga *Beena* da *Blue* ku sunyi wani irin kyau sunyi ƙiba musamman *Beena* tayi kyau sosai tayi ƙiba duk ta cicciko musamman kirjinta, kullum cikin addu'a takeyiwa yah *Blue* ɗinta Dan haka ne ma tsafin aunty *"Bebe* baya tasiri agare shi,




maganin data bata kuwa tuni ta jefashi kwandon shara tunda zuciyata bata yarda dashiba, koda aunty *Beena* tazo ta tmby neta sai tace aiyakare haka suke rayuwar su gwanin sha'awa,




"Aban gare aunty *Bebe* Kam komai ya dambale mata yanzu bata gane komai atsafinta kasan cewar aduk lokacin data ɗauko zatayi, sai tukunyar tafara rawa Dan haka saita mayar ta ajiye saboda tsoron karta fashe domiŋ boka dungu yace" idan tabari tafashe duk asirin zaya koma kanta ko kanɗan ta,




gashi wannan bokan tafahimci komai bai iyaba shiyasa tadaina zuwa gurin shi, Dan haka tafara tunani hanyar dazata be danganin taga bayan *Blue*.




******
"Aban gare ammu kuwa tanan har yanzu bata dawo tunanin taba tun sunasa ran zata dawo har sun fidda rai,




Ranan lahadi da misalin 11:00am tafito ɗaki Cikin nutswa ammu ke saukowa daga matakalar bene, sanye take da doguwar riga shadda me ruwan toka, sai kunga ammu kamar ba'itaba saboda kyau da ƙiba data karayi tana Cikin saukowa sai akai kamar anbuge mata ƙafa aikam tafaɗi tafara gangara,




dai-dai lokacin da *Basmati* ta tafito daga kichin hannun ta rike da file cike da indomi, aitana ganin yanda umman take ƙutuntsuron gangarowa yasata kwala Kara tare da sakin filet din tanufe ta dagudu,




koda ta gangarowa kasa tuni kanta yafashe har tasuma jini sai zuba yake, jin kuwan *Basman* ne yasasu Abba da umma da *Bunaya..* suka fito atare suna salati da sauri Abba yace *Bunaya* dauketa sutafi asibiti.




Cikin gaggawa aka karbeta akayi dakîn taimako gaggawa da'ita, suyi nasaran tsaida jinin sannan aka aita ɗakin hutawa duk suna zaune jugun-jugun cike da damuwa *Basma* sai kuka take,




Suna haka har tafarka da sauri sukayi kanta suna sannun ahankali take kallon su ɗaya Bayan ɗaya can sai tabuɗe Baki ahankali tace....






Muje zuwa




*LUFHAT CE*


🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍


🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_


🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍


Page3️⃣2️⃣


WRITTEN
By


🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍


OR


🎍 *MEENAT*🎍


Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*


SADAUKARWA GA


*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*


Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.


_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~


https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/


✍🏼


_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_





"Don Allah ina nake nan Kuma kusu wanene bansan kuba don Allah karku cutar Dani kamar wayan can "mutanan,


"koda yake naga bakuyi kama da masu cutar da mutam ba don haka ku taimake ni kuboye ni kar "mutanan nan su sake kamani akaro na biyu, su halakani wlh inada ahali "y'ay'ana biyar "mijina bayada lafiya yaya "muda ne daga naje karban hakkina shine yace" sukasheni,




takarashe faɗi tare da fashewa da kuka yayinda *Basmatinta* ta tayata cike da tausayin ta, Abba yai gyaran murya cikin sanyin murya me cike da tausayin ta yace" ki kwantar da hankalin kamar yanda kikace mudin bamasu cutar da mutum bane,




maganar hakkin ki kuma kina inda za'akarbar maki abinki da izinin Allah yanzu dai alhamdullahi! mun godewa Allah dakika dawo cikin hankalin ki, da sauri taɗago kai ta kalleshi cike da mamaki yace" bigeki mukai da mota.....



"Daga Nan dai faɗa mataba koshi wanene sannan yabata labarin komai tundaga lokacin da suka bigetan har losing memory ta datayi har irin Shaƙuwar dasukai da *Basma* har zuwa yanzu wanda yau kimanin wata hudu zuwa biyar kenan,



"daga ƙarashe yace don haka karki damu komai zayayi dai-dai inshallah! abinda nakeso dake yanzu zuwa anjima zaki faɗamun komai game da'ake saboda nasan ta'ina zanfara tunkaran shi "yayan naki kinji ko?...kaita gyaɗa sannan taɗaga Kai ta kalli *Basma* wacce taji kaunarta tashiga ranta lokaci ɗaya.




"Cikin sanyin murya tace *Basmatin* umma meyasa kike kuka umuh?.. hannun Tamika mata tare da faɗin zonaji meyasa kike kuka haka umuh?...da sauri taje tafaɗa jikinta cikin kuka tace umma na Ina sonki karki tafi kibarni kinji?...




cike da sonta tace nima Ina sonki Kuma bazan taba barinki ba, *Bunayya* yace tab! amma dai yarinyar nan bakida hankali badole takoma gurin ahalinta ba koba kiji tace" ya'yanta biyar ba sannan babansu bashi da lafiya ba?..



"Cike da shagwaɓa tace to aitare zamu tafi ko ummana?...tace indai zakije zantafi dake ban zantafi da yah *Bunayya* ba, dariya tayi tare fadin yeeee baza'a dakai ba dariya akayi gaba daya yayinda *Bunayya* yace saina rankwashi kannan naki kuma nima sai naje Nan dai aka kama fira.




*******
"Kwanan ammu biyu acikin asibitin aka sallame ta domin taji sauki bayan sun koma gida sai abba yafara Shirin tunkaran kawu muda inda yasa aka aika mashi da sammaci, sannan abba yace da ammu dole tayi hakuri tacigaba dazama har agama shari'ar idan yaso sai takoma gida




"Lokacin da kawu muda yaga sammaci yasha mamaki matuka koda yabuɗe takardan yaga sunan wacce ke karanshi saida ya kusa zaucewa saboda tsabar tashin hankali,




cike da bacin rai yakira yaran dayasa sukasheta yafara zuba masu masifa Wai meyasa basu kashetaba sukace masa aisun kasheta?... sukace wlh tamutu cike da takaici yakashe waya yana zuba bala'i.




"Ammu da *Basma* kam cikin kwana biyu sun sake Shaƙuwa inda duk tabata labarin yaranta inda tace mata ai *Beenazar* ɗinta zasuyi sa'annin juna cike da murna tace aizata zama ƙawata ko?...tace inshallah haka dai suke zama suna fira abinsu gwanin sha'awa,



Yayinda akashiga kotu akafara gudanar da shari'a gadan gadan kasan cewar Abba yanada kwararre lauya shiyasa abin yazo da sauki, domin ko bugun farko kawu ya amsa laifinshi,


daganan shari'ar tafara tafiya dai-dai yanda akeso wanda kana kallon yanda shari'ar ketafiya zaka fahimci ammu batada hakkinshi, koɗaya asalima shikeda hakkinta Dan haka nema batare da ya wahalar da kanshin ba yakuma wahalar da lauyoyi,




"Da alkali yafaɗi gaskiyar iya adadin ƙadarorin da maƙudan kuɗaɗan da mahaifinsu yakari, Abba yace aika juya dukiyar ko?...yace eh ankuma samu riba ko?..



"yasake cewa eh to dole har dasu yakafadi aikam kawu muda yafaɗi, sannan abba yabashi sati biyu yahaɗo Kan komai ya amsa da to cike da wani irin tsoron Abba Daya kamashi, aidole abba kam akwai kwarjini da haiba ga kwarewa akan aikin shi.




*Bayan sati daya*
*********
"Aban garen *Beena* da *Blue* kuwa suna cikin rayuwar su me daɗi kwatsam saiga tauraruwa me wutsiya ganinki ba alkairi ba tazo masu, wato aunty *Bebe*,




"Ranan wata lahadi da misalin 11:30am nasafe ta'iso
dukkansu suna part din dad kasan cewar gurin firan su kenan koda yaushe, musamman ranan asabar da lahadin harda *Bulama* ake haɗuwa ayita fira,




*Blue* nan maƙale da *Beena* wacce yakeji kamar yagoyata, dad yana kan kushin zaune yayinda sukuma ke zazzaune akan kafe ita da *Blue* da *Bulama* kan *Blue* yana kan cinyarta, wai sai tayi masa kitse hakan ne yasa take tafaman jagula lallausan gashin da yake cukurkuɗe, sallamar tane nayan boko yakatse su wato excuse me...., *Bulama* he ya amsa da yes come in.




Zumbur *Blue* yamike cike da murna yana faɗin my aunty *Bebe* oyoyo rungumesa tayi tare da faɗin oyoyo my *Bil* boy, cike da murna dad yace *Bebe* kece ba waya dariya tayi tare fadin dad surprise nace zanyi maku *Bulama* yace gaskiya aunty kinyi mana zuwan bazata,




"Zama tayi kusa da dad tana gaida shi *Bulama* ya gaida ita sannan *Beena* tamatso kusa da'ita tana gaida ita, saidai me tana shaƙar kamshin turaren aunty *Bebe* taji zuciyar ta kamar zata fito take taji wani irin amai yazomata da gudu tamike tanufi toilet,




"Amai tadinga kwarawa ba ƙauƙautawa zumbur aunty *Bebe* ta yamike tabita kirjinta yana bugawa cike da tashin hankali, take faɗin meyasa meki?..



Bata iya bata amsaba domin Aman yaci karfinta, cike da fargaba tace sannun Kai ta gyaɗa mata *Blue* ma wanda tuni ya'isa toilet din sai sannun yake zubamata, tare da riƙeta yana sorry cikin ki yana ciwo ne shima Kai ta gyaɗa mashi bayan tagama aman sai ta wanke Baki da fuska sannan *Blue* yarikota suka tafito,




"Aunty *Bebe* na biye dasu zuciyar cike da tunanin meke faruwa dad da *Bulama* dake tsaye suka fasa xuba mata sannu, cike da damuwa dad ya kalleta yace sannun *Beenazar* dama bakida lafiya ne?...




kanta duke tace dad lafiya ta kalau kawai dai naji zuciya ta natashi sai Kuma naji kaita yana sarawa, yace ayya sorry yanzu yakikeji?...tace umh Ina ɗanjin kaina yana cigaba da sarawa Kuma har yanzu inajin tashin zuciyar,




cike da tsoro aunty *Bebe* tace umh! kamar yadaya kikace kinaji?...zatayi magana dad yace ko zaki dubata ne da sauri tace eh dad ok *Beenazar* kuje kiyi mata bayani tace to dad,




"Ɗaki suka shige cikin hikima aunty *Bebe* tayi tama *Beena* tambayoyi inda take tagano tana ɗauke da ciki, wani irin gume ne yakaryo mata cike da tashin hankali tafita inda *Beena* me biye da'ita kirjinta yana bugawa.




Cike da tashi hankali tace dad akwai matsala cikin tsoro yace meya faru?...tace dad ciki take dashi fa ajiyar zuciya yay tare da murmushi yace Kai *Bebe* to mine bin matsala aciki?...




dad cikin fa watan shi hudu da sati biyu Kuma kaga yau dayin bukin wata uku kenan cif kaga kenan bacikin *Bil* boy bane, yace tabbas haka domin jiya mukayi lissafi da *Bulama* ko?...




kai *Bulama* ya gyaɗa cike da fargaba cike da bacin rai yakalli *Beena* wacce gabadaya tagama rikicewa dajin wannan batu yace.....




Muje zuwa




*LUFHAT CE*


🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍


🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_


🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍


Page3️⃣3️⃣


WRITTEN
By


🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍


OR


🎍 *MEENAT*🎍


Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*


SADAUKARWA GA


*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*


Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.


_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~


https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/


✍🏼


_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_




"Au kina nufin kina dauke da cikin shege kika yarda aka ɗaurawa ɗana ke?...kai ta girgiza cike da tsananin tsoro...., Da sauri aunty *Bebe* tace karya kike dashi aka ɗaura aini tun farko banso auran nan ba Amma dad yakafe saida akayi aiga irinta nan....,




"cikin bacin rai yace ainayi tsammanin yarinyar kirkice kamilalliya ashe bansani ba shashashace marar kamun kai to kisani ni bazan ɗauki wannan shegen cikin wa ɗana ba....,




saboda haka yanzun nan basai anjima ba kitattara naki danake kibar mun gida kije can kinemi uban shegen cikin ki kinji ko?.... aunty *Bebe* tace dadai yafi kam wato da za'a likawa *Bil* boy tunda anga bashida hankali ko?...




"To Allah yakamaki saiki tashi kitafi can da tsiyarki kinji....,wani irin kuka *Beena* tasaki me cike da tsananin firgita da tsoro wannan bakon al'amari dayazo mata rana tsaka, Shikam *Bulama* wani irin gumi ne yake tsatsufo mashi tako'ina saboda tsananin tsoro gaba daya yashiga confused,




"Shikam *Blue* tunda akafara maganar yake rabon idanu yakalli wannan yakalli wannan domin dai baya fahimtar komai, sai dayaga *Beenan* shi tafashe da kuka sannan cikin damuwa yace sorry my *Beena* friend are sick?...




bata saurare shiba kuka kawai take cike da tashin hankali tace dad aunty *Bebe* me kuke faɗane ni kwata-kwata ban fahimce ku ba...., aunty *Bebe* ce ta harare ta tare da cewa ah! dad kaji y'ar raini hankalin yarinyar nan Waima bata fahimci abinda muke faɗaba?...




"Harara ya zubawa *Beena* cike da bacin rai yace rabu da mara kunya aizata gane,. tsaki mtsww! tayi tare cewa bari naganar da'ita kunnen *Beena* takama tare da cewa ciki! cikin!! dake jikin ki bana *Bil* boy bane kije can kinemi uban shegen cikin ki amma ba ɗan uwana ba kinji....?




Cikin tsananin kuka tace a ah aunty *Bebe* idan har ciki ke gareni to wlh na yah *Bilal* domin bantaba tarayyã dawani ɗa namiji ba idan bashib......,da sauri aunty *Beben* tace karya kikeyi taya za'ayi wanda bayada hankali ya'iya tarayyã aure dake?....




"Dad yace abinda nake tunani kenan...yau kaima kafaɗa, cikin rawar murya *Bulama* yace aunty *Bebe* aɗan sake bincike.... da sauri tace wani irin bincike bayan wanda nayi ko kana nufin bansan aikina bane?..da sauri yace a ah ba hakan bane....,




"To kuma na tambaye ta yaushe rabon dataga period ɗinta tafaɗa nayi lissafi inda yanuna mun da abunta tazo don haka ta tafi can tanemi uban shegen cikin ta, Kai kawai *Bulama* yake gyaɗawa kamar kadangare domin yarasa abuncewa ciki tsawa tace dalla gafa malama tashi kibar mana gida da wannan ƙazantar dake tare dake,




"Zumbur tamike cike da tsabar tsoro tana tsananin kuka tanufi ɗaki yayinda *Blue* yabita wanda tuni yafara kuka ganin yanda takeyi, shi duk atunanin shi batada lafiya ne shiyasa take kukan Dan haka yake cewa sorry my *Beena* friend Kisha magani....




"Akwatin kayanta taɗauko daga kan wedrof tabuɗe tashiga ciro kayanta tana sawa still sai kuka take kirjinta yana bugawa tsoro nasake kamata, yayinda shima *Blue* yake kuka sannan yakoma faɗin inazata pls karta tafi tabarshe batare data saurare shiba tacigaba da zuba kayanta cikin akwatin tana kuka me tsanani,




"Bayan tagama tarufe saita ɗauki hijab ɗinta tasa sannan ta ɗauki wayarta wacce dad yasiya mata tasa cikin jaka bayan tarataya jakar sai taja akwatin tafito yana biye da'ita kamar jela yana faɗin ina zata?...Bata tanka masaba domin kuka yaci karfinta,




Har takai bakin kofa zata fita yana biyeda ita da sauri aunty *Bebe* tarike shi, juyowa yayi cikin kuka me haɗe da shagwaba yace aunty *Bebe* I want to go my *Bebe* friend tace no don't follow her...why?...she is a bad person,




fisge hannun shi yayi tare da faɗin no is not my *Beena* zaya bita dad ya daka masa tsawa hakan yasashi tsayawa jikinshi yana rawa, cikin ɗaga murya come here! da sauri yaje still yana waiwayen *Beena* dake kokarin fita cikin kuka yace pls dad zanje *Beena*,




"Cikin tsawa yace sit down! da sauri ya zauna jikinsa sai karma yake hawaye sai zuba yake tamkar anbude fanfo yana fadin pls dad let me go my "*Beena* friend cike da tsawa yace shut up u mouth dasauri yasa hannu yarufe bakin, *Beena* kam tana tafiya tana garzan kuka har tasamu adai-dai tahau tafaɗa masa inda zaya kaita.




**********
"Kasan cewar akwai kuɗi ahannun ta wanda dad da *Bulama* suke bata wai kozata siya wani abu, shine taciro ajaka tabiya me adai-dai ta sannan taja akwatin tashiga gida still tana me cigada kuka, *Bassam* ne yafara cin karo da'ita ido yazaro cike da tsoro yakaraso gurinta jikinsa har yana rawa cikin rawar murya yace la..fi..ya?...




"Bata iyacewa komai ba saidai tasaki jakar tare da shigewa cikin falo da sauri, inda ta'iske abbu dasu *Bana* zaune zubewa tayi agaban abbun tana garzan kuka gabanshi ne yai mugun faduwa dai-dai lokacin da *Bassam* yashigo hannun shi ɗauke da akwatin,




kallon akwatin yashiga yi tare da *Bassam* din su *Bana* kam tsuru-tsuru sukayi suna kallon yar'uwar tasu datake gunji kuka me taɓa zuciyar me saurare,




"Ɗakin yakai jakar sannan yadawo kallon su *Bana* yayi yace mujen ku waje abbu zayayi magana da aunty *Beena* ahankali suka mike jikin asanyaye zusu feta dukkansu,




"Cikin wani irin murya abbu yace da *Bassam* barsu sufita Kai dawo fito sukayi shikuma yadawo yazauna kusa da *Beena* datake tasharɓan kuka, ta ɗauki tsawon lokaci tana kuka batare datace komai ba hakan yasa cikin sanyi murya *Bassam* yace aunty *Beena* kiyi shuru kifaɗi abinda ke faruwa?..,




Batace komai ba Kuma bata dana kukan ba gyaran murya abbu yayi shiyasa ta sassauta kukan sannan cike da fargaba yace *Beenazar* bari kukan nan haka faɗamun meke faruwa?...




Cikin kuka tace abbu sunce" ne nabar masu gidan, kamar yaya *Beenazar* to auren Kuma fa?...abbu nima bansani ba sun daice wai Cikin dake jikina bana yah *Bilal* bane?...




"Cike da bugawar zuciya yace *Beenazar* kinada cikin ne?...abbu haka sukace" ba hakan sukace ba faɗa mun yaushe rabon dakiga al'adarku ta mata?....kanta ɗuke tace tafaɗa masa,




"Tabbas kina da ciki *Beenazar* alissafi yau watan shi uku kenan har da yan kwanaki wanda yai dai-dai da watan nin auren ki kenan, amma menene dalilin su nacewa ba cikin Shiba ne?...cikin kuka tace nima bansani ba da sauri yace kinsani *Beenazar* wlh abbu bansani ba aunty *Bebe* ce" data dubani tace" haka kai ya girgiza cike da wani irin yanayi,




"yace karya kike kinsani karki manta sudin likitocin ne sun san aikinsu don haka faɗamun *Beenazar* kin kauce daga tarbiyyar damukai maki ko?...cikin tsananin kuka tace wlh abbu ban sakeba idan har akwai ciki ajikina to tabbas na yah *Bilal* ne domin tunda nake ban taba tarayyã da wani ɗa namiji ba idan badashi ba,




"Kai ya girgiza cike da gamsuwa da bayanin ta

Please Login or Register in order to submit comment