Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambayan yarana na kasa dole nayi shiru.
      Daga nan Airport muka wucce.
           ***
       Kwance yaƙe shi ɗaya sai juyi yaƙe, kallon yaranshi yayi yaga yadda suka kwanta sai yaji ba dad'i, dan ya fahimci suna cikin maraicin Uwa. Tun da aka daura auren SAFINAH, ya daina fahimtar kome gashi azahiri mutum amma zuciyarshi ta gama cutuwa, lumshe idanunshi yayi yana tuna wasu abubuwan da ya shiga tsakaninsu. Daurawa pillown da kanshi yake nauyin yayi. Iska yaja tare da bud'e idanunsa da suka yi fiki-fiki yayi da idanunshi tare da jin sabon yanayi na musamman, ji yaƙe kamar yayi rashin babba. Itace yasashi kuka, ita ce ta tunatar dashi abinda yake aikatawa, bata barshi a haka ba sai da ta farka dashi barci da yake, sai da tabbatar ya mutu da kaunarta, ta kuma lugwaigwaita masa zuciyarsa da sonta amma tayi masa yankar kauna bayan tace amanar Ruhinsa.
   Yayi imanin babu Macen da zata iya dashi sai ita amma haka ya tsallaka tabar mishi yaransu masu kananun shekaru.

      Gyara kwanciya yayi zuciyarshi na bashi shawaran ya amshi Auren Natashah, dafe goshinsa yayi da hannunsa na dama, sam baya son auren Natashah. Bawai dan bata haɗu bane a'a sai dan ya gama tsara rayuwar shi da Uwar yaransa zai yi, kuma yasan halin matan su larabawa suna da kishin gado, musamman aka zandariya.
     Murmushi yayi sabida tuno wasu abubuwan da suka faru ba ƙaramin masa dad'i yake ba. Can kuma ya tsuke fuska kamar bai taba dariya ba, wani fitinanen kishin tane yake damun zuciyarshi  anya bazai sanya a sace mishi Dr ba??
   *Idan kayi haka har abada bazata yafe maka ba, dan ka cutar da abinda take so.*

      Juyar da kanshi yayi ya kalli yaranshi suke barci. Cikin kwanciyar hankali sauke ajiyar zuciya yayi tare da lalubabar karamar wayar da ya amsa a hannun Ghaniyu ya shiga duba number Amminshi ya lalluba, tana ɗauka ya sauke ajiyar zuciya, tare da gyara kwanciyarsa kafin yace.
"Na Amince da Natashah."
          Murna tashiga yi tare da sanya mishi albarka, sannan tace.
"Zaka zone! Ayi bikin da kai."
      
Kamar bazai ce Wani Abu ba. Ya gyara riƙon wayar, sannan yace.
"Nufa na dawo nan innalillah! Ku kawo ta nan, kuma bana son Jordan su san inda nake don Allah."
             Muryanta na rawa kamar zatayi kuka tace.
"Habibi! Ka dawo gareni"
       
   Cike da tausayi ta yace.
"Kiyi hakuri bawai naki bane, yaran ne bana son suyi kewar Mahaifiyar su, amma zan zo."
          Lallashin Nannah yayin sosai da ya fahimci tana cike da kewarshi, tabbas da ciwo a rayuwar shi, amma bayi da zaɓen da ya wucce.
    Kashe wayar yayi a sannu ya tashi zaune, a tsakiyar gadon zuciyarshi ba dad'i taya zai zauna a Oman Bayan shi yanzun baya kaunar dukkan wata alaƙa da mulki, sam ji yaƙe ina ma bai haɗa Nasaba da mulkin ba, da yafi mishi alkhairi. Zai iya cewa tun tasowarshi bai taɓa niman abu ya rasa ba sai ita, sabida ya taso inda ko kallon abu yayi za a kawo mishi. Da ace ya taso ne a gidan da basu kai haka ba, da bazai tashi a murdadden hali ba,
        Wannan murd'add'en halin ya kai shi ya baro shi dan da bai nunawa Safinah ikon bala'i ba da yana nan tare da ita amma ina ya zauna sai juyata yake son ranshi,

       Toh taya mazata amince min,  ya jima yana saka da warwara,  kafin kuma ya shiga ban daki yayi alola ya fito ya yadda sallah inda zai kai kukanshi gurin me dukkan, dan ya fahimci ba inda yake samun nutsuwa sai ya kai kukanshi ga  rabbi.

Koda ya gabatar da Sallah ya jima yana kai kukanshi, tare da niman biyan buƙatar shi na rayuwa...

Ya jima a gurin sannan ya miqe, zuwa, dan ya fara jin barci.
***
Shakeni wuyar Mamie yayi cikin ɓacin rai yana kara matarsa yana cewa.
"Me yasa! Akan me zaku tashe ni, ina barci na, kusa min muradin wani bani Adam a cikin zuciyata, dole na ɗauki fansa kafin na koma makwancina, dole na cika mishi burinsa, ki tafi gidan ki kai wannan tukunya a matsayin kyautar da ita, Ni kuma zan bata kyautar da na shirya mata, sai na shayar da ita madaran bakin ciki wanda babu irinsu duk fadin duniya, kamar yadda suka sashi ya rasa rayuwarsa sai na sadaukar da ita na zubda jininta ga doran kasa, wucce ki fita kuma ki kawo min kawarki Salmah dan jininta zan sadaukar ga abin da nake bautawa."

Da sauri ta fita tana rike wuyarta tare da shiga ruɗani ganin abinda zata aika ta, jinin Salmah zata bada Innalillah.
"Na shiga uku! Yau na yadda abin da ya dame ni. Ina zan kai hakkin Salmah."
Haka ta dauki tukunyar tare da barin gidan, jikinta a mace.
Dole haka ta faru da su tunda sun nace sai sun jefa rayuwar wasu a matsala gashi Tun basu je ko ina ba tasu ce a matsala, garin k'iyayyar SAFINAH ta wulla kanta cikin cikin damuwa, taya zata kawo karshen bala'in da ta jefa mata rayuwarta, bazata kira haka da zanen kaddarta bane, sabida shi zanen ƙaddara Allah ne ke zana maka, ita kuma wannan ita ta zamawa kanta katon layi me girman gaske, ita kuma wannan ita ce ta zamawa kanta, bata jin badaru da Maryam zasu yafe mata, idan suka ji abinda ta aikatawa yarinyar da sukafi SO duk cikin yaransu, Domin son da suke wa SAFINAH daban ne a cikin yaransu, suna matuƙa mata wani irin sone na musamman.
Wannan dalili ya jefa mata k'iyayyar SAFINAH, dan gani take duk cikin Yaran badaru yafi fiffita SAFINAH akan sauran yaransa.
***
Tun da ta iso gidan dare yayi sosai, dan haka dakinta ta wuce, tare da kwanciya, ko sallah batayi ba,
Washi gari tana tashi. Ko sallah batayi ba ta fito daga gidan da tukunyar, sai gidan SAFINAH inda tasami me kula da gidan suka gaisa tace.
"Mutanen gidan suna nan kuwa?"
"Ayya Hajiya jiya sukayi tafiya."
Safe goshinta tayi cike da jimamin gulma tace.
"Ayyana ban sani ba, amma ga wannan a saka a cikin gidan furene me kyau zai kawata mata gidan. Kace inji Hajiya Kubrah."
Karba yayi tare da godiya, har ta shiga mota sai tayi tunanin kar ya bata matsala ta sai ta zuge jakarta ta ciro sabon yan dari biyar ta miƙa mishi take ya washe bakinsa, yana ta zuba godiya. Murmushi tayi tare da samun nasarar, sauran aikin ya ragewa Anim.
***
Yau kwana uku kenan da shigowar mu Poland, duk meeting din da suka shiga baya taɓa bari ya kai dare dan haka yau ina kwance a jikinshi da wata yakoluelwar riga, hannunshi daya yana aiki da laptop, daya hannunshi yana cikin rigata dai dai cibiyata, yayinda na Daura hannuna akan nashi, a hankali nake shafa hannunsa. Sumbatar kaina yace.
"Beauty! Kina son jiki kamar mage gaki da mugun tsoro, da zancen zamu haɗe yanzun zaki fara zaro min idanu."
Kwantar da kaina nayi cikin jikin shi ina murmushi mishi Sannan nace.
"My Man! Kaine ai baka da sauki da yanzun zance na amince wallahi da kuka zaka kyaleni, shi yasa tsakanin na da kai wasan kada kusadashine ruwa ne,"

"Ba wani nan, Beauty kina b'oye min wani abu, baki san Ni likita bane hala ko kin manta ne, sam baki samun nutsuwa dani, dan haƙa yau sai naga kin samu nutsuwa zan kyaleki."

Rau+rau nayi da idanuna, tare da rike hannunsa nace.
"Wallahi Ni dai ina samun nutsuwa da kai don Allah kar a kuma."
Dariya shi ya gimtse tare da jan hancina, yace.
"Hey! Lady ba zan fasa abinda nayi niyya ba, dan haka ki gama kukanshi an jima sai mun sake kulawa Sama jannati."
Miqewa nayi zan gudu ya riko hannuna yana dariya yace.
"Duk inda kika shiga zan biki dan Ni ɗin ai dai dai dake ne, yarinya ina son ganin yadda kike jan.."
Kamar zanyi kuka nace..
"Don Allah kabar fadan haka, wallahi kunya kake bani.".

"Wayyo Allah na, Beauty Ni kike jin kunya, lallai kuwa. Toh zo na cire miki kunya tunda ban cire ba a can rana, yau kuwa sai na cire naga karshe Kunya."
Aikuwa ya shiga min chakulkuli. Dariya nake har da shudewa, gaskiya Dr Zaki karshe ne a duniyar jiyar da mace soyayya. Bai wani damu da ya nome Ni ba, amma yana nuna a cikin birnin zuciyarshi nice babu wata umma akwai toh ya cireta, ya kuma bani zuciyar.
"Don Allah Baby! Ka bari zanyi fitsari wallahi."
"Karki damu kiyi sai muje kiyi wanka tunda kin bata mu."

"Wayyo cikina zai fashe wallahi ciwon yake min."
Murmushi ya sake, cikin son sanin inda yake min ciwo yace..
" Ina ne ke ciwon nuna min."
Yana cigaba da min chakulkuli, duk na firgice da dariya, dan ya kyaleni na nuna mishi gefen marana, bai fasa sai ma sauya salon chakulkuli da yayi ya shiga daura min tashi karatun zilewa nayi na fadi kasa, ina sauke numfashi.
Kankance idanunshi yayi a raina nace.
*Kai jama'a na hadu da aiki kai kuma naka kalar kenan*
Biyo NI capter din yayi tare da cigaba da murkushe ni.
"Wayyo Dr! Don Allah kabarni bazan kuma ba, wallahi na gaji da salon ka."
"Hmm Ni kuma ban gaji dake ba, ko nace naki wayon, haka kike min kina guduna."
"Allah bani kuma gudun ka."
"Kamar da gaske, Kuma kina ganina zaki fara zare ido kamar mara gaskiya, kawai rufeni idanunki na baki candy pop."
"Allah na koshi dan wannan candy pop ɗin bayi da dadi kai kaɗai kake jin daɗin sa, Ni kuwa bana jin daɗin sa."
"Hmm, zan koyar dake yadda ake jin daɗin, Allah kuma kika dame ni lokacin da kika kwarewa
[22/02 11:08 AM] My 2nd Mtn: Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*

Oum Muwaddah......

MJ
BOOK-2
17-2-2020
Page.🖐️
        Allah Sarki Dr kowa fatar mutuwa yake maka Ni kuma banjin zan dura maka fiya fiya 🤪🤓
     ______________________
"Wayyo wallahi bani kumawa ka barni haka,"
            Sai da ya ganni cikin farin ciki, sannan ya d'ago tare da rungumana, ajiyar zuciya nake ta saukewa sabida dariyar da nayi.
  Shafa cikina yayi cikin wani irin yanayin yace.
"Yaushe zan yi ajiyata? Na kosa naga kin fara laulayi fa."
        Fari nayi da idanuna, tare da tausaya kaina, nace.
"Kai nake jira!"
          Murmushi yayi cikin farin ciki, yace.
"Beauty! Idan Allah ya bamu haihuwa dake, kunsa sunan da zan saka?"
    Girgiza mishi kai nayi cikin son jin sunan waye zai saka, jan hancina tayi sannan Yace.
"Sunanki idan mace ce, idan namijine sunan Dr Kyari zan saka."
        Murmushi nayi tare da gyara kwanciyata a jikinshi nace.
"A'a sai dai mu saka sunan Baba! Mace kuma musaka sunan Amman mu!"
          Birkitoni yayi yana kallon cikin idanuna, hura mishi iskar bakina nayi. Aikuwa ya riƙe haɓɓana da hannunsa yana gogan min hancinsa akan nawa,

              Babban arzikine mace ta samu namijin da zai bada lokacinsa domin ita, ya shirirince sabida ita, ya lalace saboda ita dan ya nunawa duniya bayan ita babu wata, eh tabbas Dr baya kai min, amma farin cikin da nasamu dashi har abada bazan taɓa mantawa ba, Dr ya soni kuma yana cigaba da soma, dan haka babu ta inda zanyi kuka dashi, sabida ya toshe wannan hanyar.
    Sannan Dr Mutum ne me hakuri sosai, koda yake bazan bada shaidan haka ba tunda bamu wani zauna can ba.
           ***
    Dagaske bikin Ashraf ya kankama a Oman, yayinda Ango fit yaki zuwa sai da Abba da Ummi suka sashi a gaba suka tafi, tare da Dudu da Batul Khalil da Khalilah, Har da Abba lawan wanda ya gama jami'arshi. Aka bar Umma da Mamie a gida, sabida Umma tana kasuwanci, Mamie kuma yar zauna gari banza, masu jiran miji ya basu (🤭🤫🤧Ashe Irinsu oo suna nan a duniya🤒)
        
     Sun sami karba Irinta alfarma, tare da hidima sosai. Aka shiga yi musu, abinda ya daure musu kai ba kome bane sai yadda akewa, girmama su, musamman ahali masarautar. Su Aamih kuwa Yaran kamar sunsan suwaye su, dan wani mugun miskilancin sukewa su Ummi, duk sabon su dasu kuwa. Daga Batul sai Khalilah, sune kaɗai suka same yardansu har suke Iya zama a jikinsu.
            ***
   Satin mu biyu, muka shiga shiri bai gaya min inda zamu je ba, sai da muka isa Airport sannan ya mika min jakata, wanda ya riko tun a hotel.
  Yaje ya mika ina zaune, yana gamawa yazo ya riko hannuna muka shiga mall ɗin da yake cikin airport ɗin, Banda kayan kwalama babu abinda yake jida sai abubuwan wasan yara, kome kala biyu pink da purple, daga nan na fahimci gida zamu koma, muna gamawa yaje gurin da ake sayar da wasu gown,  jan hannuna yayi zuwa inda aka jera su, zaba min wata yayi tare da kaini bakin dakin sauya kayan, nasaka, shiga nayi na cire najikina. A cikin sati biyu da muka yi, sai naga nakara kumatu. Nayi cike d'akin da ake, kalar fata ta ya kuma fitowa sosai.
          Saka kayan nayi na fito daga cikin d'akin,👌🏾 yayi min da hannunsa. Alamar nayi kyau, sannan ya kuma mika min wani rigar itama dai ba laifi.
        Sai a na ukune yace.
"Wannan yayi! Dan yafi su kyau."
      Riko hannuna yayi muka nufin inda ake biyan kudi, mika musu katinshi yayi suka diba iya kudin su. Kallon agogon da yayi sannan yaja hannuna muka fita.
Muna zuwa aka fara shiga jirgin, kallon shi nayi cikin zakuwa nace.
"Ina zamu? Naga sai sayayya kake!"
Na kura mishi ido ina son jin karin bayani. Ba tare da damuwa ba yace.
"Bikin Babansu Aamih!?"
Ji nayi kaman abu zai fado daga kirjina, nayi maza na dage kirjin. Zufa ne ke yanko min ta ko'ina, Allah ya taimakeni bai ga halin da nake ciki, kafin ya juyo na kirkiro Faransa dole.
"Baki ce kome ba"
Cikin ƙarfin hali na turo bakina nace.
"Allah ya bada zaman lafiya."
"Amin beauty."
Yace min, babban takaicina ɗaya ne me yasa ya gaya min, ji nake kuka na taso min, amma haka nayi shiru hiran da yake hana naki, biye mishi na cigaba da lumshe idanuna har barci yayi gaba dani,
Murmushi yayi tare da shafa fuskana cikin walwala, riƙon hannuna yayi yana kallon yadda sumar yatsuna suka kwanta, sake kallon fuskana yayi a karon na uku ya ga yadda na ajiye kumatu, kamar bani ce Hajja ke cewa a dauri kashi ko a bata igiyar ba.

Hannunshi ya kai cikin rigana da sauri na bud'e idanuna. Kallon juna mukayi, nice na fara janye idanuna daga gare shi, zuciyata tana tsawatar min abisa butulcin da nake shirin aikatawa, meye haɗin da Ashraf? Da nake shirin fad'awa hallaka sabida shi.
Innalillah nake mai-maitawa, har na samu saukin, daura kaina nayi a kafadar shi, daura kanshi yayi a gefen nawa.
***
Oman...
Tunda Dr ya turawa Dudu sakon gasu nan zuwa, shi kuma ya gayawa Ashraf. Dama yaki ya shirya zasu fita jin zamu zo ya miqe ya fara da wanka.
Ya jima a ciki sannan ya fito, shirya yayi cikin kananun kayan wanda suka fidda yarantashi sosai.
Turare ya fesa sannan ya koma gurin da agogon shi yake, ya dauka tare da zobensa na azurfa.
Takalmin kamfanin Mamata, ya saka sannan ya fito, a hankali yake fitowa. A sannu yake takawa cikin izza da kasaita, uwa uba kuruciya, na dibanshi da wani mugun miskilancin da ya kwanta a fuskar shi tare da tsare gida, yana fitowa ya kalli Dudu.
Sannan ya Basar da shi, kallon wayar shi yayi. Sannan ya turawa Ghani sako.
*Ka tambayi kawunsu Asma'u, karfe nawa jirgin zai sauka.*
Ba tare da ya kalli Ghani ba, ya cigaba da tsayuwar shi.

"Dr karfe nawa jirgin su Uwar d'akina zai sauka."
Cikin ko in kula Dudu yace.
"Saura minti ashirin."
Gaba Ashraf yayi suka take masa baya, mamakin Irin mulkin da Ashraf yaƙe nunawa Dudu yake.
(🙄🙄Dudu kenan ai Yayarka ta aikatu, mutumin da baya iya dogon magana.)
***
Mun iso lafiya sai narkewa nake a jikin shi, har muka shigo a arrival.
"My Man! Na gaji."
Na fada mishi a sanyayye, dan na gajine.
"Toh! Bari muje masauki sai ki kwanta ki huta, ina yaso sai na miki tausa."
Gyada mishi kai nayi, jikina a mace.
Muna fitowa muka haɗu da Dudu, da sauri ya zo ya amshi, jakar hannun Dr, sannan yayi ɗan murmushin jin dadin yace.
"Yallabai me kake bawa Didina ne haka tayi kumatu?".

Murmushi Dr yayi masa, sannan yace.
"Tayani gani, nima dazun a cikin jirgin sai da naso tambayar ta."
Kallona Dudu yayi cikin son ƙarin bayani,
Ban kulasu ba, na cigaba da binsun da murmushi, gabana ne yayi mugun Fad'uwa sakamakon ganinshi ya tsare Ni da ido. Komawa jikin Dr nayi ina tura bakina cikin kunkuni nace.
"Wallahi Ni da anyi shawara dani, bazan zo nan ba."
Shafa fuskana Dr yayi cikin rarrashin yace.
"Bazamu wucce sati ba!?"
"Sati!!! Fa wallahi Ni bazan zauna har sati ba."
Ayya SAFINAH kiyi hakuri mana ko kwana biyar muyi."
"Nifa na gaya maka gaskiya bazan zauna ba."
Dai dai munzo inda yake, kasa kasa yayi Magana yadda babu wanda ya isa yace sani yake domin kuwa, hankali shi na kan Dr da suka riƙe hannun juna suna gaisawa yace.
"Ba sai kin nunawa duniya mijinki bai isa dake ba."
Watsa mishi harara nayi raina a bace banga dalilin zuwana wannan bikin ba, haka kawai an dauko Ni zuwa wani gayyato soɗi, kunun bayan ludayi.

Mota muka shiga, nida Dr da kuma Dudu, sai nashi tare da ghani.
Muna isowa gidan, ya fita tare dayiwa Dr jagora har masauki su, Ni kuma Dudu ya kaini gurinsu Ummi, tunda muka shiga Ummi ke cewa.
"Masha Allah!"
Zuwa nayi na zube a jikinta, ina sauke ajiyar zuciya.
"Sannu gajiya ko!?"
Gyada kai nayi tare da gyara kwanciyata. Nace,
"Khalilah matsa min karama ciwon suke min."
Cikin tausayawa, ita ta kama daya Batul ta kama daya suka shiga min, tausa.

Cikin jin dadi barci yayi gaba dani....
***
"Ayya! Ku duba min beauty."
Yadda ya damesu da beautyn yasa Ashraf barin shashin dan wani baƙin cikine ya cika mishi zuciya, gudun kar yayi abinda zai yi,
Yana shiga dakin shi, ban daki ya wucce, dunkule hannunsa yayi ya kaiwa Madubin cikin ban dakin naushi, haka suka fashe tare da tarwatsawa a cikin banɗakin, haka yayi ta naushin Madubin da hannunsa duk ya jima kanshi ciwo. Idanunshi sunyi wani mugun ja, ga azaba Ben kishin da yake damunsa.
Sai da ya gyara ciwon hannunsa sannan ya fito, hannun daure da bandaji.


Tunda Dudu ya zo yasamu ina barci, yaje ya gayawa Dr, ban tashi ba sai bayan awa ɗaya sannan na farka wanka nayi da alola. Na fito na gabatar da Salla.

***
A cikin kwana uku da muka yi idan kaga Ashraf ya zabge sosai tare da mugun rama, duk da nasan dalilin ransa sam bai wani dame Ni ba, sabida babu wata alaƙa a tsakanin mu.

Yau aka shirya dinner kuma a cikin babban filin masarautar, za ayi dan haka Kowa zai.

Karfe tara aka fara hidimar, dukkanmu mun shirya cikin wasu gown Ni bawa dark green, sai Dr da yasaka suit ashe colour, muka fito.
Hannunmu sarke da juna, muka je inda aka ajiye abin zama muka zauna. Amarya ta riga Ango fitowa.
Yana can ya saka tarukan hannunshi, a fuskar shi yana tunani. Sau uku Nannah tana zuwa da kanta, Amma yana kin buɗewa. Duk wandaake tunanin zai masa magana yaki fitowa, ba dan me Dudu ya gayawa Dr ba sai dai ya tashi ya riko hannuna, muka nufi part dinsa.
Umarni Dr ya bani na buga, amma yaki budewa sai da nakiya aunanshi sannan ya bude kofar, ya fito cikin shirinsa.
Mikawa Dr hannu yayi, suka gaisa sannan muka fito, ina manne da Dr. Kamar bai ga abinda muke ba, nan kuwa idanunshi na kanmu yake. Ranshi na kara ɓaci sam baya jin zai iya yafewa zuciyarshi akan katsalanda da tayi mashi na rabashi da abar kaunarshi,
Har muka zo inda zamu zauna, shi kuma ya wucce gurin zaman shi, hankalin mu kwance muke hira da Dr tare da Dr. Kowa yaga yadda muke cikin farin ciki sai mun burgeshi.

Anyi nisa a shagali na zare jikina zanje ban daki.
....

Har na isa na gama uzurin nafito, a baƙin kofa na ganshi tsaye, tamke fuskana nayi cikin sauri, yayi maza yasha gabana.
"Meye laifina! SAFINAH! Kawo hannunki kiki, SAFINAH mutuwa zan."


Please Login or Register in order to submit comment